*🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠*
Masarauta
Mallakin
*INDO CE..*
Marubuciyar
SIRRIN K’ETA.
A JINI ‘DAYA.
🎠ELEGANT ONLINE WRITER’S🎠
*Page~1*
بسم الله الر حمن الر حيم
A WANI YANKI NA INDIA.
KUDU MASO YAMMA..
Gudu take na fitar hayyaci tana k’wala masa kira da iya k’arfin ta bata da burin da ya wuce ta cimmasa tana zuwa gaff dashi wata gagarumar iska me had’i da guguwa ta fara kad’awa.
Hakan yasa yayi taga-taga k’afar sa ta zame yayi baya ya fad’a k’asa.
Cikin ihu ta furta sunan sa tana k’ara waro gwara gwaran idanun ta, cikin sanyin jiki da wani irin taku ta k’arasa wajen tana lek’awa, ganin da gaske ya fad’a d’in yasa ta dafe k’irjin ta tana wata irin shak’uwa idanun ta suka k’ara firfitowa ko k’yaftawa basayi,, zubewa tayi a wajen kamar sumammiya ta durk’ushe akan k’afafunta.
Wani mutum ne ya zagayo ta bayan ta ya kama damtsen Hannun ta ya fara janta k’irrrr kamar ba mutum.
Babbar Harabar TAJMAHAL PHURLA.
Cike take da mutane iri daban daban bayi da hadimai haka ma dogarai mawak’a da masu bushe bushe.
Ko ina kid’a ne ke tashi da wata irin busa me d’auke da wani take da wani kyakkyawan salo da k’warewa.
Rukunin y’an mata sun sha ankon riga da wando burguza burguza sunyi k’awanya a tsakiya suna rawa da karairaya cike da k’warewa da kuma sabo.
Gefe guda kuwa sai watsi ake da furanni da garin fure da kuma kaloli.
Da alama ana gudanar da wani babban shagali ne a wannan masarauta.
A cikin Mahaal a hawa na bakwai.
Wani k’ayataccen d’aki ne wanda yaji ado irin na sarauta ta ko ina, acan ciki,
Zaune take bisa wani katafaren lilo yana lila ta cike da isa gami da izza ba’a iya ganin fuskar ta sakamakon juya baya da tayi.
Gefen ta kuwa wata kyakkyawar Hadima ce tsaye kanta a k’asa tana wasa da yatsun Hannun ta, cikin sanyi da kuma zak’in murya tace, “Hazoor Ki yafe ni, amma masarauta ta cika ta ko ina ke kawai ake jira”
Ba ta ce komai ba sai mik’ewa da tayi cikin wani irin salon mulki da gadara.
A take fitinanniyar surar ta ta bayyana kanta. Budurwa ce me ji da lokacin ta,
Kyakkyawa ce ta azo a gani jajur da ita kamar ka ta’ba jini ya fito jikin ta ko ina kayan ado ne na gwal da azurfa sark’ok’i duk wani sassan jikin ta babu inda babu su hakan yasa duk wani motsin ta sai kaji k’arar su bare kuma idan ta taka, ta had’e cikin wani Saarie ruwan ganye, kore, yayi matuk’ar kwanciya a jikin ta tayi kyau kamar ba gobe kasancewar ita d’in kyakkyawa ce, babu wata kwalliya a fuskar ta sai kwalli da yaji bajau a idanun ta hakan ya k’ara musu kwarjini da wata irin barazana.
Wannan hadimar ta kalla, take ta sako wani shu’umin murmushi ta kauda kai cike da izza, a hankali ta lumshe idanun ta tareda motsa bakin ta alamun magana, cikin dadd’ar muryar ta ta furta Arjulaa???
Wata tsuntsuwa fara tass ce ta nufo inda take suuuu,, itama kanta tsuntsuwar kyakkyawar gaske tana zuwa ta sauka akan kafad’ar ta tana wani kuka tareda karkad’a jela, hakan yasa ta saki murmushi.
Kamar me tsoron k’asa ta fara takawa a hankali idan tayi taku d’aya sai ta girgije sannan zata k’ara d’aya a haka tayi gaba, Hadimar tabi bayan ta kanta a k’asa.
Hannun tasa ta janye tufafin jikin ta ta d’anyi sama dashi sakamakon jan k’asa da yake sannan ta sako k’afar ta a wajen d’akin.
Tin daga k’ofar d’akin sojojin masarauta ne rerass baka iya gano iyakar su, suna ganin ta na farko yayi wata irin busa, daga can ma wani ya k’arayi haka abun ya d’auka har ya fito harabar masarauta wane gayawa wane, ai kuwa take Salo ya k’ara canjawa yanayin kid’i da busar da akeyi ya canja zuwa wani salo me bala’in d’aukar hankali.
Da takunta irin na wahainiya har ta fito harabar duk inda ta ratsa zubewa suke kan guiwoyin su tareda sunkuyar da kansu k’asa su k’ame kamar abu mara numfashi har sai ta wuce tabar wannan sashin sannan zasu mik’e, mata da maza manya da yara haka sukeyi.
daga can wani d’an bene aka tanadin gurin zaman ta ita da na kusa da ita, kai tsaye can ta nufa kafin ta zauna ta d’aga musu hannu a take gurin yayi tsittt kamar ba sune suke hayaniya ba.
Sihirtaccen murmushin ta ta sakar musu.
Hakan yasa kowa da yake gurin murmusawa sannan suka dunk’ule hannayen su na dama suka d’ora kan k’irjin su gami da d’an rank’wafawa, kansu a k’asa.
Jinjina kai tayi taja wani yalwataccen numfashi.
Wanda yake da alhakin sanar da umarnin ta yayi busa hakan yasa kowa ya d’ago, masu kid’e-kid’e suka fara kid’a da busa me sautin taken ta.
Zama tayi ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya, tana kallon ko ina da fararen idanun ta,, bayan wani lokaci ta tuna da Hadimar ta da take a tsaye kallon ta tayi fuska a sake tace, ” Farhanaa zauna”
Wadda aka kira farhanaa ta sadda kai k’asa cike da ladabi tace, “ina godiya Hazoor”
Bata sake kallon inda take ba taci gaba da kallon mutanen ta, wato mutanen masarautar Phurlaasirie.
Bayan an d’auki lokaci ana wannan sai aka tsagaita.
Yayin da idon kowa kuma ya dawo kanta.
Wata kuyanga ce ta turo wani abun saka jarirai na gargajiya wanda yasha ado ganyayyaki kala kala jaririn sai baza ido yake yana kallon kowa, a gaban ta aka ajiye shi kuyangar tayi gefe tana me sunkuyar da kanta k’asa.
Wasu mace da namiji ne suka k’araso duk kansu yana k’asa suka kwashi gaisuwa ta musamman sannan sukayi gefe suka tsaya, cike da ladabi namijin yace, “ranki ya dad’e wannan d’an mu ne nida matata wanda a dalilin haihuwar sa ne kika shirya mana wannan gagarumin shagalin, mun gode da wannan karramar Hazoor, wannan d’a mun sadaukar dashi gare ki duk abunda kika yanke a kansa mun amince ba dan kanmu muka haifeshi ba sai dan ke mun mallaka miki shi ranki ya dad’e.
Kyakkyawan murmushi tayi tareda mik’ewa tayi tsaye akan jaririn,, ido ta zuba masa shima ya zuba mata ido suna kallon-kallo har wani lokaci kafin tasa hannu cikin nutsuwa ta d’auke shi ta rungume, kallon iyayen sa tayi cikin k’asaitacciyar muryar ta tace, ” menene Lak’abin sa???
Uwar yaron tace, “ranki ya dad’e yanzu ba namu bane naki ne duk hukuncin da kika zartar akan sa ya zama dai-dai ko da kuwa yanka shi zakiyi ki sadaukar da jinin sa ga abun bauta”
Baban yaron yace, “ranki ya dad’e mu mun kasance bayi ne a wannan masarauta tin iyaye da kakannin mu kuma har yau bazamu gajiya da hidimta muku ba bakin rai bakin fama nayi alk’awari ga abun bauta zan mutu ina me bautawa wannan masarauta”
Murmushi tayi ta d’an yi taku biyu kafin ta juyo, girgiza kai tayi tace, “na k’aunaci yaron nan dan kuwa yana da k’warin zuciya tamkar mahaifin sa bazan bawa kowa shi ba shi d’in mallaki na ne kamar yadda kuka mallaka min shi dan haka zan rad’a masa suna yanzu.
Share hawaye mahaifiyar yaron tayi har cikin ranta tana jin kewar d’an ta wanda ba lallai ta sake ganin sa ba.
Ita kuwa lumshe ido tayi tana motsa baki da alama addu’a takeyi bayan ta kammala ta hura masa iskar bakin ta a kunne,, hakan yasa yaron ya k’ara zazzaro ido tareda k’ank’ame jikin sa, bud’e idon ta tayi ta zubawa yaron su, tana murmushi tace, ” AbdulKareem”
Da sauri baban yaron ya d’ago kai yana wani irin murmushi tareda k’walla jikin sa har rawa yake ya mai-mai-ta AbdulKareem??
Zubewa yayi kan guiwoyin sa yana kuka yana cewa, “mata ta na gode miki da kika haifa min AbdulKareem, Ranki ya dad’e kin biyani ubangijin AbdulKareem ya saka miki da mafificin Alkairi.
Uwar d’an kuwa jin sunan da d’an ta yaci yasa ta dena sharar k’wallar bak’in cikin rabuwa da shi , farin ciki ya wanzu a tattare da ita itama ta zube a k’asa tana mik’a godiyar ta.
Fure ta dank’a ta watsa musu tana murmushi tace, ” ina muku fatan samun wani d’an bayan wannan kunyi babbar sadaukarwa bayan tarin shekarun da kuka samu ba tareda kun samu d’a ba kuma kun haifa kuka sadaukar dashi gare ni tabbas kun cancanta da komai a gareni Udday”
Mik’ewa Udday yayi cikin d’aga murya yace, “ku saurara kowa ya maida hankali,,, ni Udday d’aya daga cikin bayi kuma y’an bayi na wannan masarauta na sadaukar da d’a na da na haifa ga Uwar wannan masarauta, Uwa me adalci ta sanyawa yaro suna AbdulKareem!!!!!!!!!!!
Sai da wajen ya girgiza gaba d’aya saboda fad’ar wannan suna take wasu suka fara zubda hawaye wasu kuwa razani da firgici gami da rud’ani ya d’arsu a zukatan su, wasu kuwa jikin su har kakkarwa.
Wani tank’amemen faranti wanda aka lullu’be da wani k’yalle me ado da Hatimin Phurlaa Mahaal ta kar’ba a hannun wata baiwa tana murmushi ta mik’owa Udday sannan ta kar’bi d’ayan ta bawa matar sa.
Farin ciki da murna ba kama hannun yaro,,, ba su kad’ai sukaji dad’in wannan kyauta ba har da sauran jama’ar wajen,, take aka k’ara rud’ewa da fad’in, ” Godiya ta musamman da jinjinar ban girma ga Uwar Masarauta”
Shagali akeyi sosai ko gajiya basayi.
Mik’ewa tayi da zummar komawa tana rungume da AbdulKareem, ta fara tafiya kenan wata murya ta dakatar da ita, cikin d’aga murya ba tareda tausasawa ba ya kira sunan ta.
“Mahalakhshmie???????
Juyowa tayi tana waro masa idanu cikin wani mugun zafin nama ta d’auke shi da wani gigitaccen mari, cikin tsawa da kuma kwarjini tace,
” MAHARANIE MAHALAKHSHMIE ”
sassauta murya tayi tak’ara cewa, “ka sai ta harshen ka ba’a kiran sunan Uwa haka kawai”
K’asa yayi da kansa zuciyar sa na rad’ad’i kafin yayi wani yunk’uri yaji an sark’e k’afafunsa da wasu mazajen sark’ok’i ido ya zazzaro yana kallon mahaifiyar sa wadda itama idanun ta suke warwaje.
Da sauri dattijuwar matar ta k’araso ta durk’ushe a gaban ta cikin k’ask’antar da kai tace, “kiyi hak’uri ki yafi d’a na k’uruciya tana damun sa shiyasa kiyi hak’uri Mhaa”
Da hannu tayi musu alamar su sake shi.
suka kwance shi suka ja baya.
Nuna shi tayi da yatsa tace, “RamRaj shine kawai sunan ka rik’e matsayin ka”
K’ara yin k’asa da kai yayi tareda cewa “zan kiyaye”
(Kuci gaba da bibiya ta a cikin wannan k’ayataccen labari domin jin ya abun ze kasance. Wacece
Maharanie mahalakshmie?? Shi kuma RamRaj waye shi?? Meyesa baya girmama sunan ta kamar kowa?? Shin meye yasa ta kasance uwar masarauta duk da kasancewar ta k’aramar yarinya budurwa?? Wannan sunan da ta rad’awa yaron Udday sunan waye?? Meyesa wasu suke farin ciki dashi wasu kuma suka razana?? Waye shi in ya girma??? Duk amsoshin suna cikin gundarin labarin sannu sannu bata hana zuwa,ku biyo ni domin jin yadda zata kasance..)
Taku.
INDO Ce
*🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠*
Masarauta
Mallakin
*INDO CE..*
Marubuciyar
SIRRIN K’ETA.
A JINI ‘DAYA.
🌼ELEGANT ONLINE WRITER’S🌼
*Page~2*
بسم الله الر حمن الر حيم
Cikin tsantsar izzar ta taci gaba da tafiya har ta koma sashin ta, kafin ta zauna ta mik’a Abdullkareem ga Hadima Farhanaa ba tareda tayi magana ba.
Hadima Farhanaa tace, ” Maharanie?? Umarnin ki nake jira”
Murmushin gefen baki tayi ta tsurawa Arjulaa ido ba tareda ta kalli Hadima Farhanaa ba tace, “ki kula dashi ”
Hadima Farhanaa ta kalle shi sannan ta kalli Maharanie tace, “kiyi min Hak’uri Hazoor amma sai naga kamar abun yayi min yawa in kula da jariri in kula da mamallakiyar jaririn, bazan iya ba”
Fuska a had’e ta kashe ta da idanun ta masu bala’in kaifi, taku d’aya biyu tayi kafin ta juyo,, ta kuma juyawa sannan tayi magana cikin k’asaitacciyar muryar ta tace, “kiyi duk yadda zakiyi dashi ko da bazaki iya ba in yaso ki jefa shi a ruwa ya tafi dashi, sai ki sani ko lafuci ya samu yaron nan ranki ne fansa”
Ido Hadima Farhanaa ta zaro a razane tace, “Hazoor ki gafarce ni da alamu an samu rashin fahimta ne,, ina nufin ba nice zan rene shi da kai na ba amma, Maharanie ki dena saurin ambaton kisa kai tsaye hakan yana girgiza jikima ta”
Y’ar dariya tayi tana ci gaba da takawa ta k’arasa wajen taga tana lek’en k’asa gami da shak’ar kyakkyawar iskar da take kad’awa kamar me koyon magana ta tattaro kalmomin tace, “ke kad’ai ce kike da nasara a zuciyar Maharanie ina jin ki tamkar k’anwa ta ta jini, shiyasa nake iya hak’uri da duk wani shirmen ki ba dan haka ba da tuni na hukunta ki hukunci me tsauri akan abubuwa da dama,
Ki nemi amintacciyar Hadima ki bata renon Abdulkareem sannan ki kula da ita da duk wani takunta bana so wani mummunan abu ya faru dashi hakan ze sa rayuka su ‘baci, wannan nake nufi”
Murmushi Hadima Farhanaa tayi tace, “ina Godiya Uwar masarauta, nasan matsayi na a gurin ki ya wuce na kowa hakan ne yasa nake da damar fad’a miki duk abunda yazo kan harshe na ba tareda tsoro ba dan nasan in anjima zan kasance me nutsuwa ko Maharanie??? Nima tamkar Yaya ta nake jin ki,
Ni kad’ai ce kike zama kiyi doguwar magana dani, ni kika amincewa na shiga hurumin ki ta ko wane fanni,
Ni kuwa me ze hana nayi miki duk abunda kika so??
Na d’auki alk’awari wa wannan masarauta zan kasance amintacciyar ki komai wuya bazan ta’ba juya miki baya ba”
Murmushi Maharanie tayi tasa tafin hannun ta ta shafi kumatun Hadima Farhanaa, juya gwarazan idanun ta tayi zuwa sama kafin tace, ” ki d’auka cewa Abdulkareem d’a na ne wanda na haifa tareda miji na, irin wannan kulawar nake so ya samu a ke’bantaccen gurin da ba kowa ne ze san inda yake ba, nima zan kasance me bibiyar sa a lokacin da ya dace”
Hadima Farhanaa tayi k’asa da kai tareda cewa, “ubangiji na ya sakanya miki da Alkairi Maharanie yadda kika ce haka za’ayi”
Daga haka ta fice ta nufi sashin Hadimai dan kuwa ita tasan wadda zata bawa shi komai ya tafi dai-dai.
Wata dattijiwar Mata ce tana zaune tana sa’kin wani abu na zaren itaciya, tana ganin Hadima Farhanaa ta mik’e tana dai-dai ta kanta tareda cewa, ” sannu Hadimar Hadimai a gaida Hannun daman Uwar marayu”
Murmushi Hadima Farhanaa tayi tace, ” Uwar Hadimai Urmiey sannu da gida,, rik’e wannan jariri na Maharanie ne”
Ido Uwar Hadimai ta zaro tace, “Maharanie Mahalakshmie???
Jinjina kai Hadima Farhanaa tayi tace, ” AbdulKareem shi d’in jinin Udday da Surekha ne iyayen sa sun kasance masu bautar gunki shi kuma ze kasance Mabiyin Addinin Islam ne ubangijin Da nake bautawa shima shi ze bautawa”
Kar’bar AbdulKareem Uwar Hadimai tayi tana cewa, “Barakallah AbdulKareem ibni AbdulKareem?? Masha Allah,
Tinda ka kasance musulmi da hakan ya kamata na sa maka albarka duk da ni ba musulma bace, amma
Hakan yana nufin kenan akwai daru a Mahaal?? Meyesa Maharanie ta aikata haka, itace tace miki Musulmi ne???
Hadima Farhanaa ta jinjina kai tace, ” Maharanie tinda ta rad’a masa sunan musulmi tabbas musulmi ne baze yuwu yayi wani addinin ba bayan wannan”
Uwar Hadimai Urmiey tace, “abun bauta ne kad’ai yasan abunda ke k’unshe a cikin wannan Mahaal har ma da wanda yake ‘boye a zuciyar Maharanie da bainar duniya baki d’aya amma akwai alamar bayyanar wani abun me k’arfin da ze girgiza wannan Mahaal”
Hadima Farhanaa tace, “koma meye nayi imani da ubangijin Amintacce Almustafha kuma nasan yana tare dani harma da Maharanie nasan baze bari mu tagayyara ba ze ku’butar da ita a ko wane irin hali domin kuwa tana yawai ta Bauta masa tana yin azumi tayi sallah duk ranar Jumu’at duk da bansan dalilin hakan ba amma da alamu akwai wani sirri ne dangane da hakan dan kuwa bayan wannan ranar bata yin wani abu da ya kasance yayi koyi da dinul’islam sai dai a wannan ranar kuma bata fashi indai har ranar tayi to zatayi wannan bautar”
Uwar Hadimai Urmiey ta jinjina kai tace, “akwai k’ulle k’ulle rifaffu a wannan Mahaal dan dai ke a yanzu kika zo yarinya ce ke, amma anan gaba ma akwai gagarumar k’urar da take tinkaro mu”
Sosai jikin Hadima Farhanaa yayi sanyi ta yarda da maganar Uwar Hadimai Urmiey dan kuwa tasan bazata yi mata k’arya ba kuma akwai abubuwan al’ajibi da ta kasa gane me suke nufi.
Fuskar ta a rufe take hakan yasa baza’a iya gane wacece ba, da sauri take tafiya har da gudu-gudu ta nufi wani ‘bangare na TajMahaal, kasancewar duk masu tsaron yankin sun sani yasa basuyi k’ok’arin tare ta ba duk da cewar fuskar ta a rufe take,
Cikin wata turaka ta kutsa kai ba tareda neman izini ba.
yana kashingid’e hannun sa d’auke da wani kyakkyawan kofin azurfa yana kur’bar ruwan inibi yanayi yana lumshe ido.
Tsaye tayi a kansa ba tareda tace komai ba har sai da ya ankara, da sauri ya tashi ya zauna tareda bud’e mata hannayen sa alamar ta rungume shi, fad’awa tayi jikin sa tana murmushi.
Ya ajiye kofin tareda gyara mata zama a jikin sa ya fara lalubar ta yana wani mugun murmushi, cikin wata murya me cike da mugunta yace, ” gaya min me yake faruwa??
Hannu tasa ta shafi sajen sa kafin tace, “TajMahaal ta rikice saboda Maharanie Mahalakhshmie ta rad’a wa yaro AbdulKareem kowa yana cewa meye fa’idar hakan, ina ganin dama ce ta zo mana cikin sauk’i da zamu iya juya zancen”
Ture ta yayi daga jikin sa a burkice ya mik’e yana cewa, “Me ne??? Kika ce ta rad’a AbdulKareem????? Meyesa!?????
Ya jefo mata tambayar cikin tsawar da sai da ta razana.
“K’warai yaron Udday yaci wannan sunan”
Jingina yayi jikin garu yana maida numfashi a take wani gumin wahala ya shiga keto masa, ya lumshe idon sa ya bud’e sannan yace, “meyesa ta kasa sallamewa kanta wannan masoyiya??
Wadda ya kira masoyiya ta gyara zama kafin tace, ” dad’i na da magajin karaga saurin fushi, da kayi shiru baka firgita ba da sannu zakaji mafita ta fara zuwar maka cikin tunanin ka”
Dawowa yayi ya zauna kusa da ita cikin salon yaudara ya rik’o hannun ta yana d’an murzawa cikin sassanyar murya yace, “fad’a min menene??
Murmushi tayi tace, ” zamuyi amfani da hakan mu jefa rud’ani cikin zukatan mutane ta yadda zasuji sun tsane ta”
Yace, “kin kawo magana yaci ki samu kyauta me kike so na baki??
A kunne ta rad’a masa kafin suka kwashe da dariya sannan suka ci gaba da shirya yadda zasuyi su rusa Maharaniey.
Idanun ta a lumshe suke yayin da take k’ok’arin d’aure gashin ta da wata kyakkyawar sark’ar azurfa har ta kammala, Hadima Farhanaa tana gefe ta zuba mata ido har ta gama sannan tace, ” gaskiya Maharanie ke kyakkyawa ce”
Murmushi kawai tayi ba tareda tace uffan ba.
Hadima Farhanaa taci gaba da cewa, “Hazoor kenan yanzu ina zakije???
Jin batayi magana ba yasa Hadima Farhanaa ta canja magana dan kuwa tsananin baiwar surutun da Allah yayi mata baze barta tayi shiru ba.
Cike da son k’arin bayani Hadima Farhanaa tace, ” Maharaniey?? Shin meye dalilin da yasa kike hidimtawa Addinin muslumci lokaci lokaci???
Sannan kuma waye Abdullkareem??
Akwai abubuwa da dama wanda na kasa fahimtar su daga gareki har sai yaushe zakiyi min bayani?? Kin barni a cikin duhuwar da na kasa gane gaba da baya”
Kamar baza tayi magana sai kuma ta murmusa sannan tace, “baya tarihi ce gaba kuma gwagwarmaya, gani yafi ji dan haka ki tsammaci zuwan lokacin da zaki gani da idon ki, tarihi kuma ba abunda ya zama wajibi bane kiyi k’ok’arin yin tunanin gobe ba jiya ba dan ta riga ta wuce tariyar ta ba amfani, idan ta riga ta dawo kuwa ba lallai abun yayi kyau ba”
Ta k’arasa maganar tana zuba mata idanu.
Gyad’a kai Hadima Farhanaa tayi tace, “kenan dai ba dama?? Haka zan ci gaba da rayuwa kenan ba tareda nasan iyaye na ba?? Bansan wacece ni ba kenan a haka zan gudanar da rayuwa ta?? Ina buk’atar sani musamman akan mahaifi na”
Kamar wadda take tsoron yin magana tace, “da haka kika taso idan kin ci gaba da rayuwa a haka ba damuwa”
Mik’ewa tayi tana takun ta irin na giwa cikin nutsuwa ta nannad’e jikin ta da k’aton mayafin Sariey wanda ya sha ado ko ta ina ba ta kalli inda Farhanaa take ba sai ma kiran Arjula da tayi suka doshi hanyar fita.
Da sauri Hadima Farhana ta biyo bayan su.
Suna fitowa kowa ya d’au saiti.
Kai tsaye wani ke’bantaccen guri ta nufa wanda kai tsaye za’a kira shi da kurkuku, cikin nutsuwa take takawa har tabar harabar kurkukun ta shiga wani d’aki bayan me gadin d’akin ya bud’e mata.
K’arewa d’akin kallo ta shigayi kafin ta k’arasa a hankali ta tsugunna a wani waje.
Duhun da d’akin yayi yasa ba’a ganin komai bazaka iya gane menene a ciki ba.
Cikin wata irin murya kamar ba ta-ta ba tace, ” Yaushe???
Taku.
INDO CE..
[25/02, 10:41 a.m.] INDO CE..: *🎠🎠🎠 TAJMAHAAL🎠🎠🎠*
(Masarauta)
Mallakin
*INDO CE..*
Marubuciyar
SIRRIN K’ETA.
A JINI ‘DAYA.
🌼ELEGANT ONLINE WRITER’S🌼
*Page~3*
بسم الله الر حمن الر حيم
“Yaushe ne zakiyi magana???
Meyesa bazaki bani amsa ta ba??
Sai yaushe ze zo???
Kinyi shiru ki fad’a min!!!”
Tayi maganar a tsawace.
Me gadin gurin ne ya shigo da fitila yana haskawa..
Wata Mace ce a tsakure a jikin bango ta had’e kai da guiwa gashin ta yayi buzu-buzu kaca-kaca ga tarin datti,
Tsawar da Maharaniey, (Sarauniya) ta daka ce tasa ta d’agowa tana zuba mata firgitattun idanun ta wanda sukayi jajur,, daka ganta ka ga mahaukaciya saboda irin d’aud’ar da take jikin ta da kuma yanayin ta.
Ido ta zuba mata suna kallon kallo ba tareda tayi magana ba.
Maharaniey ta k’ara da cewa, “kiyi magana kafin ranki ya ‘baci, ki fad’a min mana, meyesa kika dena magana ki bud’e baki kiyi min bayani”
Jijjiga ta ta shiga yi tana cewa, “kiyi magana ki fad’a min yaushe ne???
Hadima Farhana ce ta matso zuciyar ta na k’una cikin ‘bacin rai tace, ” gaskiya ranki ya dad’e ta wata fuskar ke muguwa ce, sai yaushe zaki dena azabtar da wannan matar??? Meyesa zaki za’ba mata wannan rayuwar?? Shin menene abunda kike so daga gareta da har kika kasa jin tausayin ta dan tak’i fad’a miki?? Wannan be dace ba”
Da mamakin maganganun da Hadima Farhanaa ta gaya mata ta juyo a fusace tana zazzare mata manyan idanun ta, cikin Hasala tace, “ki rufe min baki, kece zaki fad’a min abunda ya dace ne?? Yaushe ne kika samu matsayin da zaki duba tsabar idanu na ki fad’a min irin wannan maganar??? Me kika taka ne Farhanaa????????
Hadima Farhanaa tace, ” ban taki komai ba tinda ni bani da mulki bani da dalilin sa, amma gaskiya ce nake fad’a miki me wannan matar tayi miki da zaki kulle ta anan shekara da shekaru?? Kuma ace bazan fad’a ba ya kamata kiyi adalci, kullum kin takura mata da tambaya, shin ranar mutuwar ki kike tambayar ta ne ko meye????
A fusace Maharaniey (Sarauniya) ta zaro wata takobi da akayi mata mazauni a jikin bangon d’akin wanda aka gina shi da zallar dutse,
Cikin tsananin Fushi ta kai mata Takobin da niyar raba kanta da gangar jikin ta ba tareda tunanin kuskuren da take shirin aikatawa ba.
Wani irin gurnani matar tayi tareda yunk’urawa ta mik’e tana girgiza kanta da iya k’arfin ta tana fizge fizge, tana wani irin ihu, kamar me cutar iska.
Dakatawa Maharaniey, (Sarauniya) tayi jikin ta na rawa saboda tsabar ‘bacin rai, ta dad’e a haka kafin tayi wurgi da takobin ta kalli Hadima Farhanaa, cikin Izza tace, “Farhanaa ki dinga banbance matsayi na da naki, karki manta nice silar zuwan ki duniya, ki dena d’aukar kanki a wata abu ke ba komai bace face baiwa ta”
Daga haka tasa kai ta fice daga kurkukun a fusace, kai tsaye bayan masarautar ta nufa bakin wani k’aton kududdufi k’oramu suna ta gudana da ruwa ta ko ina ga sanyi da yake tashi a wajen tsuntsaye sai yawo suke suna lelewa, tsayawa tayi ta rungume Hannuwan ta cikin k’irjin ta tana babbaza ido, har wani lokaci kafin zuciyar ta ta fara yin sanyi.
Hadima Farhanaa ce ta k’araso wajen cike da nadamar abunda ta aikata, durk’ushewa tayi kan guiwoyin ta- ta maida hannuwan ta baya ta hard’e su, kanta a k’asa tace, “Hazoor, (Ranki ya dad’e) ki gafarce ni idan har zuciyar ki zata iya hakan, idan baki huce ba ki d’auki mataki a kaina na d’auka, tabbas nayi kuskure ama sharrin zuciya ne ba da son rai na ba, kwata-kwata bani da niyar ‘bata miki rai bansan hakan zata faru bane”
Lumshe ido tayi tareda sauke wani zazzafan numfashi, ba tareda ta kalle ta ba tace, “ina Abdullakareem???
Hadima Farhanaa tace, ” yana nan cikin kwanciyar hankali ba abunda yake damun shi”
Jinjina kai tayi ba tareda tayi magana ba ta juya ta koma cikin Tajmahaal.
Da tsakar dare ta tashi ta shiga wani d’aki,
babu haske sosai sai kad’an-kad’an, tarkace ne na abubuwan da suka fi kama da na tarihi, kan kujerar da ke tsakiyar gurin ta zauna ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya tana d’an karkad’a ta a hankali, k’arewa d’akin kallo ta shiga yi kafin janyo wata akwati ta bud’e ta, zuba wa akwatin ido tayi har wani lokaci kafin ta saki murmushi, cikin wata maraitacciyar murya tace, “yaushe zaka dawo??? Meyesa zaka guje ni?? Sai yaushe zaka zo gareni???
Murmushi tayi ta k’ara cewa, ” nasan zaka zo, ko ba dad’e ko ba jima, nasan fushi kake dani, nima yanzu na canja na dawo kamar yadda kake son gani na meyesa bazaka zo ba??
Ita kad’ai take y’an surutan ta har wani lokaci sannan ta tashi ta koma turakar ta.
Babbar Fadar Masarautar Phurlasirie,
Cike take mak’il da jama’ar masarautar yayin da kowa yake hirar sa cikin nishad’i da walwala hayaniya ce kawai ke tashi.
Shiru fadar tayi kamar wucewar tsawa, sakamakon busar da ta iso cikin fadar wadda take nuna alamar Maharaniey mahalakhshmie ta doso cikin fadar,
Kowa tashi yayi tsaye ya k’ame tareda sunkuyar da kansa k’asa gami da dunk’ule hannuwan su na dama suka d’ora gefen k’irjin su,
ba babba ba yaro haka tsoho da tsuhuwa haka maza da mata, kowa mik’a ban girma yake gareta.
Tsaye tayi a bakin fadar ta lumshe idanun ta, cikin wata irin siga take motsa bakin ta a hankali ba tareda sautin abunda take fad’a ya fito ba, sai da ta d’auki d’an lokaci a haka kafin ta bud’e idanun ta, take suka k’ara rikid’a suka k’ara wani irin kwarjini da razanar da duk wanda yayi gigin tsoma nasa idon cikin su,
Idan baka lura sosai ba bazaka ta’ba cewa tana k’ifta su ba sai in kayi mata kallon k’wak’waf hakan kuwa ba kowa ne yake iyawa ba,
Cikin takun ta me cike da zallar izza da gadara ta saka k’afar ta ciki tareda k’ara rarraba idanu tana kallon mutanen da suka koma kamar basa motsi,,
Har sai da ta dangana da kyakkyawar kujerar mulkin ta ta zauna sannan kowa ya zauna.
Kowa yayi shiru yana tsammanin abunda ze fito daga bakin.
An kwashi lokaci sosai kafin tayi magana cikin d’aga murya tace, “ina buk’atar sanin duk abunda yake gudana a ciki da wajen masarauta”
Da sauri Wanda suke da Alhakin hakan suka taso tareda hawa kan tudun da ke gefen kujerar wanda aka tanada saboda su.
Subbhu ne yayi gyaran murya kafin yace, ” Ranki ya dad’e wasu daga cikin mutanen masarauta suna cewa sun kasa gane dalilin da yasa kika rad’awa yaro Abdulkareem sannan kuma kin enta Udday fiye da ko wane bawan ki ta dalilin haihuwar wannan yaro basu fahimci meye hakan yake nufi ba, har wasu suna cewa ko dai kina da alak’a ta jini da yaron”
Jinjina kai tayi tareda zubawa Hadima Farhanaa ido.
Hadima Farhanaa ta sunkuyar da kai cikin sanyin jiki.
Kamar baza tayi magana ba sai kuma ta mik’e, ta fara takawa cikin k’asaita hannun ta rik’e da gefen mayafin Sarin ta,
Juyowa tayi tana fuskantar jama’ar ta, cikin d’aga murya tace, “abu ne me kyau kaso wanda ya so ka da gaskiya, kyautatawa ga wanda ya kyautata maka abune me matuk’ar muhimmanci, kar ku manta da waye Abdulkareem kar ku zama butulu saboda wasu y’an tsirarun mutane suna son hure muku kunnuwan, ku tsarkake zukatan ku a koda yaushe kar ku bari wani yayi tasiri a zuciyar ku, ya kasance kuna yin komai da yak’ini ba tareda bin fad’ar wani ba, idan kun kasance wanda basu san waye shi ba kuyi tambaya ga iyayen ku da kakannin ku, nasan ma ba lallai ne ace baku san da hakan ba,
enta wanda ya enta ka shima abu ne me kyau, be zama dole sai wanda ka had’a jini dashi ba zaka kyautatawa, akwai su da yawa wanda su d’in jini na ne amma a hakan sune suke tunzura ku dan su jefa ku cikin wasi-wasi,
Komai na yiwa udday ban biya shi ba domin kuwa shi kyautar d’an sa yayi min, har gobe shi mutum ne me daraja a idon masu daraja, yaro kuma na d’auka a matsayin d’ana ne, kuma wani abunda baku sani ba, koda bana raye ku sani Abdulkareem bin Abdulkareem shine magajin karaga ta,
Yafi kyau ku maida hankali wajen kishin kanku da y’ancin masarautar ku da kuma yankin ku domin dubban halittu suna son ganin bayan Tajmahaal wadda kuka taso cikin ta tin kakannin kakannin ku,
Ni dai na aminta kuma na tsaya ga al’uma ta na fansar da raina gurin kare su da basu y’ancin su, ban yarda da zalumci ko nakasu a wannan masarauta ba, duk wanda yayi k’ok’arin hakan?? Yasan meye hukuncin duk wani kaifi a fadar nan”
Shiru tayi tareda k’ara taku biyu zafafa tana kallon su d’aya bayan d’aya.
Shiru fadar ta k’ara yi kowa da tunanin sa, jikin su yayi sanyi matuk’a domin kuwa sun san a cikin zantukan ta babu na watsarwa.
Wasu kuwa furucin ta na mallakawa Abdulkareem karaga shine ya k’ara hautsina tunanin su yayin da zuciyar su ke raya musu duk yadda akayi Abdulkareem d’an ta ne.
Babbar tambayar kuma itace da wane mijin ta haifi Abdulkareem????? Kuma a yaushe????
Subbhu ne ya d’akko wata takarda yana dubawa, cikin d’aga murya yace, “ku saurari k’orafin da Shugabar mu zata saurara da kuma hukuncin da zata yanke a yanzu”
A take nutsuwa ta k’ara wanzuwa a gare su kowa ya cigaba da sauraron su.
Subbhu yace, “Hazoor !! ( Ranki ya dad’e) “Janela tana d’auke da juna biyu wanda ya kasance ya samu asali daga Narayan,
Sakamakon keta haddin ta da yayi saboda son zuciyar sa ba tareda son ranta ba, iyayen ta sun mik’o kukan su gareki tareda sa ran samun adalci”
Udday yace, “wanda suka san dasu ake su fito gaban shugaba”
Fitowa sukayi suka durk’usa kamar yadda tsarin masarautar yake suna tsammani daga gareta.
Zama tayi tareda lumshe ido ta sauke ‘boyayyar ajiyar zuciya kafin ta bud’e su ta juye akan Narayan wanda jikin sa yake kyarma saboda tsabar tsoro da fargabar azabar shugabar tasu, a Take wani abu ya fara kwaranyowa cikin tunanin ta,
Jinjina kai tayi tace, “wajibi ne auren ta gare shi bayan yayi zaman kurkuku na adadin lokacin da zata rabu da abunda yake jikin ta, kullum ze d’auki hukuncin bulalai hamsin ba tareda ya motsa ba,
Bayan wata d’aya sai a koma yi masa duk mako d’aya,
Ban da shan ruwa sai me zafi abinci kullum sau d’aya,
Kulawa da d’an sa da matar sa ya wajabta a kansa indai ya ‘bata mata rai ko ya goranta mata koda na lokaci d’aya hukuncin kisa ta hanyar jifa ya tabbata gareshi”
Daga haka ta mik’e da niyar fita daga fadar jiki a muce.
Tashin hankalin abunda take fad’a ya hana shi aiwatar da abunda yaso k’addamarwa akan ta, idanun sa sun kad’a sunyi jajur saboda azabar rad’ad’in da zuciyar sa take masa ya kafe ta da idanu yana wani irin huci, zuciyar sa tana raya masa irin mummunan matakin da ya dace ya d’auka a kanta.
(Waye?????????
Mu had’e a next page insha Allah)

Leave a Comment