Hausa Novels

Ruwa Da Kankaru Hausa Novel

.سم الله الر حمن الر حيم
*______________________________*

*💧💦RUWA DA KANKARA⛈⛈*

*NA HADIZA D/AUTA*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The notion}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________________*

*PAGE ONE*

*********************

Wani dattijo ne tafe akan keken shi, da ciyawa a bayan kariyar sa wadda ya daure da igiya, yana ta sauri saboda yana so ya k’arasa gida, saboda hadarin dake barazanar tasowa, ga wani duhun damana da ya mamaye fadin sararin samaniya.

Aiko duk saurin shi na son yaje gida kafin afara ruwan, sai da suka fara sauka tareda wani iska mai karfi dake kadawa, ya karawa keken shi gudu yana tafe yana sharce ruwan dake zuba akan fuskarshi.

Tun daga nesa yake jiyo sauti kamar na kukan jariri, acikin al’jabi ya k’ara kasa kunnuwan shi, saboda yana so ya gasgata abunda kunnuwanshi suka jiyo masa, acikin fargaba yake tafiya saboda jin kukan yana k’ara kusantoshi, sai raba ido yakeyi domin ya ganema idanunshi abunda zuciyarshi ta tabbatar masa.

Karaf idanunshi suka hango masa wani k’aton kwali dake ajiye acikin ciyayi, inda ko tantama babu acikinshi ne wannan kuka na jariri yake fitowa.

Gabanshi ya k’ire ya fad’i, ba shiri ya tsaida keken shi ya sauko, tareda furta kalmar:

“INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI’UN YA HAYYU YA KAYYUMU BI RAHMATIKA ASTAGISU, A’UZU BI KALIMATILLAHIT TAMMATI MIN SHARRI MA KHALAKA”

Bai tsaya anan ba har saida yayita jero addu’o’i yana shafe jikin shi, sannan ya tunkari inda kwalin yake ajiye, acikin jarumta ya saka hannu ya bud’e kwalin bakin shi d’auke da bismillah, da sauri yaja baya ganin abunda ke ciki, alokaci d’aya aka tsuge da ruwan sama masu k’arfi, har ya juya acikin sauri da nufin yaja keken shi ya bar dajin.

Aiko jinjiri ko jinjirar dake cikin kwalin ta kara k’wallah wani kuka saboda ruwan saman dake sauka acikin kwalin suna jik’a masa/mata jiki, da sauri dattijon ya waigo yana k’ara maimaita addu’a acikin zuciyarshi da bakin shi.

Da hanzari ya dawo ba shiri, ya k’ara zurawa jinjirin/jinjirar idanu, alamu duk sun nuna a bayyane cewa mutum ce/ne, amma ganin farin da tsantsar kyawon halittar ya sakashi jin tsoron kar fa ace diyan aljanu ne, azuciyarshi yace:

“Nayi niyyar taimako don Allah koma menene Allah Ubangiji ya kare ni da sharrin dake ciki”

Aikuwa duk wani tsoron da yake ji ya gushe azuciyarshi, acikin kuzari, yayi bismillah ya saka hannu ya d’auko abunda ke cikin kwalin, ya aza akafad’arshi, ba shiri jinjirin/jinjirar yayi shiru tareda sauke wasu ajiyar zuciya ajere da juna.

Yana kai idanunshi acikin kwalin, yaga kud’i ajere k’asan kwalin, sanadiyyar towel d’in dake shimfid’e aciki da ya janye a gefe d’aya yayin d’auko jinjirin/jinjirar, da sauri dattijon ya maida jinjirin/jinjirar acikin kwalin ya rufe, aiko ba shiri ya k’ara k’walla wani kukan, jiki yana rawa dattijon ya kinkimi kwalin ya azashi agaban kekenshi sannan ya gyara mata zama ya fara lula gudu, duk da k’arfin ruwan dake sauka, acikin k’warewa yaketa balbala gudun, hannunshi d’aya rik’e da kwalin d’aya yana tuk’a keken, wanda har izuwa lokacin jinjirin/jinjirar bata daina kukan ba.

 

 

 

Tofa dandano daga abunda ke cikin littafin:

*RUWA DA KANKARA*

 

Akafta🙊

 

Nice dai taku har kullum :

D/Auta👌🏻

.سم الله الر حمن الر حيم
*______________________________*

*💦RUWA DA KANKARA⛈*

*NA HADIZA D/AUTA*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The notion}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________________*

*ASSALAMU ALAIKUM DA FARKO INA MIKA SAKON GAISUWATA AGAREKU TAREDA SAKON TAYA JUNA BARKA DA SALLAH ALLAH YA MAIMAITA MUNA*

*PAGE TWO*

********************

Jiki yana rawa dattijo yakai k’ofar dan madaidaicin gidanshi,bayan waige waige da yakeyi don yana jin tsoron tuhumar ‘yan unguwarsu, ba shiri ya sauke ajiyar zuciya, ya godewa Allah da wannan ruwa da ake tayi kamar da bakin k’warya, wanda k’arar saukar ruwan ya hana ajiyo sautin kukan jinjirin/jinjirar.

Abakin k’ofar gidan ya ja burki, Wanda a kallo d’aya zaka gano gidane irin na rufin asiri, amman fa akwai babu a gidan, duba da yanda k’ofar shiga gidan ta kasance ta langa langa duk ya hunhunde ya taso wanda idan bakayi a hankali ba yayin shiga gidan tsaf langa langar zai yage maka kayan dake jikinka.

Da dubara ya sauko hannushi d’aya rik’e da kwalin da jinjirin/jinjirar yake ciki wanda duk ya jik’e sharkaf, saboda ruwan da ake ta tsulawa har izuwa lokacin, yayinda shima jaririn/jaririyar har izuwa lokacin bata daina kukan ba, amman ga dukkan alamu daga yanayin kukan da yake ko take ta gaji sosai, saboda tasha kuka har muryarta ta dusashe.

ya samu ya jingine keken, sannan ya ciro kwalin dake gaban keken ya rungume da hanzari ya fada gidan a sukwane kamar anjefo shi.

Kai tsaye ya wuce wani d’an madaidaicin d’aki, yayin da iya kulu dake baiwa akuyoyinta k’asari ta bishi da kallo baki asake, tana mamakin kukan jaririn da tajiyo, haka kawai zuciyar ta tabuga ba shiri, da sauri ta d’auraye hannunta ta nufi d’akin da taga ya fad’a, jin sautin kukan jaririn muraran ya k’ara kid’imeta.

Ba shiri ta afka d’akin ko sallama babu domin ta ganewa idanunta abunda ke faruwa, da sauri wata tsohuwa dake zaune tayi tagumi tareda wannan dattijon suka bita da kallo.

Ido abud’e iya kulu tace:

“Malam me nike shirin gani?”

Da sauri tsohuwar ta katseta da cewa:

“To tonanna maza kiyi sauri kiyi shela har mak’ota su ji, tunda ke ba’a sirri dake”

Jiki asanyaye iya kulu ta rakub’e gefe tareda tsurawa masu kallo in ta kalli malam ta kalli Dada ‘yar tsohuwa, tanason taji ba’asin abunda ke shirin faruwa.

Dattijon nan mai suna malam wanda ga dukkan alamu, wannan tsohuwar itace mahaifiyarshi, duba da yanda kamar su ta fito abayyane.

Ya saukar da ajiyar zuciya tareda cire tagumin da yayi, ya duk’a ya d’auko jinjirar dake cikin kwalin ya rungume ajikinshi, tareda sauke ajiyar zuciya, jinjira kam saboda sanyin da ya ratsa jikinta, da sauri ta ratsa kuka, ba shiri Dada ta karbeta hannunu malam ta janyo zane ta goyeta tana jijjigata tana bubbuga bayanta, tun tana kukan har taji gumin goyo tayi bacci.

Iya kulu dai tana tsaye sai rabon idanu takeyi, Malam ya k’ara sauke ajiyar zuciya ya fara yimasu bayanin yanda akayi ya tsinto ta.

Iya kulu ta rafka salati da k’arfi tace:

“Yanzu malam haka kawai kaga d’iya acikin daji an jefar kai kaje ka kwaso muna jaraba ka kawomuna acikin gida, muna zaman zamanmu ka jaza muna hitina, yanzu in d’iyar aljanu ce fa?, shikenan kasa mu shiga uku”

Dada saboda hararar da take yimata, kamar idanunta su fad’o, amman duk da hakanan sai da iya kulu takai k’arshen maganarta, malam ya d’auke kallonshi daga kanta yace:

“Ko aljanar ce nayi niyyar taimako don Allah kuma bazan fasa ba, saboda bazan iya ganinta acikin wannan halin ba, ace in kasa taimakon ‘yar jinjirar Allah ba, bazan tab’a yafewa kaina ba, idan har ban taimaketa ba, ki kwantar da hankalinki za’ayi cigiyar iyayenta, idan ansamesu sai mu basu ‘yarsu salun alun, don ga dukkan alamu wannan ‘ya bata k’ananun mutane bace, duba da yanayin shigarta, sannan da wad’annan mak’udan kud’in da na sameta tareda su”

Jiki yana rawa inna kulu ta zaro ido tace:

“Kud’i? Kud’i fa kace malam”

Malam ya tabbatar mata, sannan yace da ita ta bud’a kwalin ta gani, aiko jikinta yana b’ari ta bud’a da sauri ta d’auki kwalin ta rungume baki har kunne tace:

“Bari inje in b’oye su malam tun kafin ‘yan unguwa su gano munada wad’annan kud’ad’en a gidanmu su samu abakin duniya”

Da hanzari Dada ta karb’e kwalin tace:

“Ta ina suka zamo kud’inmu?, waya baku?, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak’i, to gani nan bari nan saboda bamuda hak’k’i da wad’annan kud’in har sai anje wurin mai unguwa abunda duk yace shi za’a bi, saboda gudun abunda zaije ya dawo kafin agano iyayen yarinya su karb’i ‘yarsu”

Iya kulu ta b’ata fuska tace:

“Dada fa kowa ya samu ta kanshi yakeyi, yanzu saboda Allah sai ad’auki wad’annan zundumayen kud’i akaiwa mai unguwa, haka kawai ya cenye su ya barmu sake da baki, kura da shan bugu gardi da kwasar kud’i”

Dada ta rik’e baki tace:

“‘yar kuluwa wallahi kiji tsoron Allah ki rage son kud’i, tun kafin su halako ki abanza”

Iya kulu ta fita fuu alamun ranta ya b’ace, don tasan k’arshen abun in ta biyewa Dada ranta ne kawai zaiyita b’aci akan hakan, malam dai ya bita da kallo ya girgiza kai, saboda inda sabo ya saba da ganin rikicin da yafi haka tsakanin Dada mahaifitarshi da Iya kulu matarshi.

 

Muje zuwa mutanena🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀

Akafta😝

Taku ce har kullum

D/Auta👌🏻

[8/22, 1:55 AM] Auntyna: .سم الله الر حمن الر حيم
*______________________________*

*💦RUWA DA KANKARA⛈*

*NA HADIZA D/AUTA*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The notion}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________________*
*HAPPY EIDUL FIDHIR FOU YOU ALL MY FAN’S💃🏻👍🏻*

*PAGE THREE*

**********************

Malam ya maido da kallonshi akan dada yace:

“Idan an d’auke ruwa zamuje mu kaita wurin mai unguwa, domin abada sanarwa koda Allah zaisa adace asamu iyayenta”

Dada tayi shiru na d’an wani lokaci, sannan ta sauke ajiyar zuciya tace:

“Ban tari numfashin ka ba, amman jikina yana bani wannan ‘yar ba’a yankin nan namu take ba, akwai lauje acikin nad’in da yayi jagora wajen ya rabata da mahaifiyarta, don ga dukkan alama bawai gama garin yanda ake jefar da yara bace, akwai wata sark’ak’iyar da tayi tsanin wannan bak’ar aika aikar, domin na tabbata duk inda iyayenta suke insha Allahu, suna cen acikin tashin hankalin neman ta ruwa k’ok’o ”

Malam ya nisa sannan yace:

“To ke Dada su nemeta akan mi? bayan sun nuna daman cen neman maraba sukeyi da ita, idan akayi la’akari da kud’in da aka saka tare da ita, ana nufin an baiwa wanda ya tsinceta ladar tsintuwa kenan?”.

Malam ya k’are maganar acikin jin haushin, wad’anda sukayi wannan ta’adi, tareda janyo kwalin kud’in ya fara fiddo dasu awaje, saiga wata farar takarda aninke, ta jik’e sharkaf da ruwa tayi laushi, da sauri ya d’auko ta ya fara bud’a ta da dubara, don gudun kada ta yage, sannan ‘ya harhad’a d’an guntun bokon shi na yak’i da jahilci, ya fara karanta abunda ta k’unsa abayyane domin Dada taji yace:

“Assalamu Alaikum
Wannan jaririya ayau kwana hud’u da haifuwarta, diyar sunnah ce gaba da bayanta, ga kud’i nan a kula da ita sosai arik’eta amana.

Bakin dada yana rawa tace:

“Maganar ka gaskiya ce Ayuba, don haka dole ne mu kaita wurin mai unguwa domin mu cire kanmu a zargin ‘yan wannan gari namu, sabo…. ”

Kafin ta k’are maganar jaririyar ta fara mutsu mutsu tana son tayi kuka, da sauri Dada ta kwanto ta daga goyon da tayi mata, aiko yarinya ta fara saka hannu abaki tana tsutsa tana bud’ar baki sannan ta saka kuka, Dada ta kalli malam tace:

“Nono take nema kuma gashi ana wannan ruwan ina za’a je asiyo mata madara?”.

Malam ya shafa goshin sa sannan ya tashi tsaye jikinshi yana rawa yace:

“Bari inje in gani in d’an liti yana shagon shi in siyo mata madara sai abata”

Dada tayi hanzarin fad’in:

“Wannan madara ba itace ake baiwa jarirai ba, ka jira zuwa gobe idan Allah ya kaimu, sai kaje birni ka siyo mata, saboda madarar da ake baiwa jarirai daban take, na ganta ana baiwa yaran gidan Alhaji murtala, don kasan uwar batada isashen nono”

Malam ya dawo ya zauna acikin damuwa yace:

“To yanzu Dada me zaa bata tasha ne?,tunda gashi tana jin yunwa?”

Dada ta yunk’ra ta tashi tsaye tana girgizata sannan tace:

“Akwai yanda za’ayi, kira man ‘yar kuluwa, tazo ta tatso muna nonon Akuyarta da tayi sabuwar haihuwa, sai abata, amman yanzu idan kace kaje birni a yanzu to yaushe zaka dawo ne?, gashi yamma tayi sosai, gara dai abari gobe ido yana ganin ido sai kaje ka dawo a mutunce”

Malam ya zaro ido yace :

“Dada yanzu kina ganin ba wata matsala, a nonon akuyar idan an bata?”

Dada tayi murmushi tace:

“Da akwai matsala da tuni kai ne ka fara fuskantar ta, saboda kai ka fara sha kafin ita, gashi kuma Har yanzu ba abunda ya sameka”

Malam yayi murmushi sannan yafita yana cewa:

“Yau tsohon tarihin ya tashi kenan?”

Dada tana dariya tace:

“To wa ya janyo tashin ba kai ba”

Malam ya fito yaje rumfar da akuyoyin iya kulu suke ad’aure, sannan yace da wani yaro wanda bai wuce shekara takwas ba yace :

“Kai garzali je kira man iyarka”

Aiko saigata ta fito tana cin magani sai kumbure kumbure takeyi, malam ya kalleta yace:

“Dauko man kofi mai kyau ki kawo, zan tatso nonon akuya ne abaiwa yarinyar”

Iya kulu ta washe baki tace:

“Yawwa malam na nawa kakeso in tatso maka?”

Jikinta yana rawa ta d’auko kofin ta fara tatso nonon har saida yayi rabin kofin sannan ta rufe ta mik’a masa baki har kunne tace:

“Kawo hamsim na raga maka don sani da sabo”

Malam ya karb’i kofin kota kanta bai bi ba ya koma d’akin dada ya kai mata, aiko tasa d’an k’aramin cibi ta fara bata nonon, yarinya kam sai sha takeyi har sai da ta k’oshi sannan ta b’ingire tana ta baccin ta hankali akwance sai maida numfashi takeyi acikin natsuwa, Dada ta maida ta abaya ta goya, ta d’auko towel d’in da aka tsinto ta dashi ta lullub’eta, sannan ta janyo zanenta da take yafawa ta yafa ta kalli malam tace:

To yanzu muje wurin mai unguwar tunda ansamu ruwan sun tsaya kafin su dawo”

Malam ya d’auko kwalin suka fito, iya kulu tana barandar ta atsaye taga fitowar su, da sauri ta k’araso awurinsu tace:

“Yanzu da gaske kai kud’in zakuyi?, munaji muna kallo ayi muna sama da fad’i dasu?”

Dada ta galla mata harara sannan tace:

“A’a barmaki za’ayi ki tusa su agaba kiyi ta kallo tunda gadon gidan ku ne”

Iya kulu ta b’ata fuska ta kalli malam tace:

“Nidai bani Hamsin d’in kar ka mance”

Malam ya kalleta don baya buk’atar tada jijiyoyin wuya yace da ita:

“Kin biyoki”

Suka fita suka barta, sai ga garzali aguje ya biyosu yana fad’in:

” Baba ina zakuje?, ina zuwa”

Dada tace:

“Zo muje shalelena, inda dai wancen mai kan mangwaron ne da ko k’ofar takashi bazanje dashi ba, halin uwarshi kaf shi ya kwashe”

Tofa ita iya kulun🤣🤣🤣

 

Akafta😜

 

Taku ce har kullum

D/Auta 😅
[8/22, 1:55 AM] Auntyna: .سم الله الر حمن الر حيم
*______________________________*

*💦RUWA DA KANKARA⛈*

*NA HADIZA D/AUTA*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The notion}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________________*
*BARKA DA SALLAH MY FAN’S ALLAH YA MAIMAITA MUNA*

*PAGE FOUR*

******************

Dada yar tsohuwa agaba malam da Garzali suna biye da ita suna tafe suna tattauna matsalar har k’ofar gidan mai unguwa.

Ba tareda b’ata lokaci ba suka samu damar ganin shi, bayan sun k’are gaisawa ne, malam ya fara koro jawabin abunda ke tafe dasu, gabaki d’aya d’akin kowa jikinshi yayi sanyi k’alau, da jin wannan badak’alar da ta faru acikin garin nasu, mai unguwa yayi gyaran murya sannan yace:

“Ina jaririyar?”

Dada ta ta ciro yarinyar daga goyon da tayi mata, wanda sai alokacin duk wad’anda ke d’akin suka gano da d’iyar abayanta, saboda baccinta takeyi sharkaf,har da su ajiyar zuciya alamun taji dad’in goyon.

Malam ya karb’i d’iyar ya mik’awa mai unguwa, Mai unguwa ya k’ura mata kallo na tsawon lokaci yana nazari, sai ga hawaye suna kwaranya akan fuskar shi, saboda ta bashi tausayi sosai, kasancewar shi mutum mai tsananin tausayi, saboda yanda ya ganta fara jajir babu d’igon baki ajikinta kyakkyawar yarinya son kowa k’in wanda ya rasa, don rashin imani irin na mutanen mu, ace ad’auke ta akaita daji a yadda, tamkar an yaddo kashi, afakaice ya share hawayen shi, sannan ya mik’awa Dada ita yayi gyaran murya ya fara magana kamar haka:

“Malam Ayuba”

Malam yace:

“Na’am ranka shi dad’e”

“Yace naji duk abunda ka fad’a ina takardar da kace ka gani acikin kud’in”

Malam ya ciro takardar ya mik’a masa, mai unguwa ya baiwa wani wanda yake wurin yace ya karanta masa yaji, saboda shi mai unguwa baiyi boko ba,tiryan tiryan aka karanto takarda, mai unguwa yace:

“Malam Ayuba zaka iya rik’e wannan yarinya a hannun ka?, ko zaka barta ahannu na ne har zuwa lokacin da za’a sami iyayenta?”

Malam ya kalli Dada, tayi masa umurni da ido, atake ya d’au hannu yace:

“Zan iya rik’eta a hannu na ranka ya dad’e har zuwa lokacin da aka samu iyayenta”

Mai unguwa yaji dad’in furucin malam yace:

“Alhmdllh na amince dakai ayuba tun ba yau ba shiyasa ma ban musa wannan takardar da kace ka gani aciki ba, saboda amanar ka ce ta saka har ka bayyana kud’in aka san da akwaisu, nasanka mutum ne kai mai gaskiya da rik’on amana, saboda haka na amince da zata samu kula sosai a wurinku, Allah ubangiji ya taya ka rik’o, kuma ya baku ladar taimakon da kukayi”

Duk d’akin aka had’a baki da cewa:

“Ameen”

Mai unguwa ya bada umurnin akawo goro a rarrabawa mutanen dake d’akin, akayi kamar yanda ya buk’ata, sannan ya kalli malam yace:

“Wane suna kakeso asawa ‘yarka?”

Malam yaji dad’in wannan karamci na mai gari, baki awashe yace:

“Ina son asa mata suna IZZATU”

Mai unguwa yayi murmushi sannan yace:

“Daga yau an rad’awa ‘yarka suna izzatu,sannan kud’in kaje dasu kaci gaba da kula da ita kamar yanda aka umurta, gobe sai kuzo da ita akaita asibitin birni aduba lafiyar ta, sannan abata magunguna irin nasu na jarirai, sai a azata akan madarar da d’orata akanta adinga shayar da ita, insha Allah zamu shiga binciken su wanene iyayenta, Allah ya rayata akan tafarkin musulunci Allah ya zamo gatan ta damu baki d’aya”

Gaba d’aya akace “Ameen”

Daga nan taron ya watse su Dada suka fito, bayan sunyi sallama da mai unguwa, suna tafe Garzali ya kasa hak’uri yace”

“Dada ita wannan jaririyar yanzu a gidanmu zata zauna?”

Dada tana murmushi tace:

“Ko baka so ta zauna gidan in maida masu da yarinyar su?”

Garzali yayi saurin fad’in :

“Cab ai ni dada naso ma ace iyarmu ta haifeta wallahi da naji dad’i, baturiya a gidanmu, ai kina bani ita in d’auketa ko Dada?”

Ya k’are maganar acikin tsantsar farin ciki, Dada tana masa dariya tace:

“In kana son inbaka ita ka d’auka, to dole sai ka bada nera biyar”

Garzali yayi tsalle yasha gabanta yace:

“Zan baki in d’auki d’iyar indiyawa wallahi”

Ba Dada ba har da malam sai da yayi murmushi yace:

“Daga turawa sai indiyawa to sai munji gaba kuma k’ilan ta koma ta larabawa”

Firar da sukeyi kenan har suka shigo gida, iya kulu tana ganin su ta ajiye aikin da takeyi da sauri ta sha gabansu tace:

“Allah dai yasa bai karb’e kud’in ba”

Dada ta harareta tace:

“To mutu kud’i bai karb’i ko k’wandala ba, yanzu ke nawa kikeso abaki naki kaso tun kafin su k’are”

Iya kulu tasan halin Dada tas bak’ar magana ce ta buga mata, shiyasa nan take tayi kalar tausayi ta kalli malam tace:

“Bani Hamsin d’in asiyo ma awaki na dussa”

Malam ba musu ya saka hannu aljihu ya mik’a mata nera d’ari yace:

“Ki ajiye hamsin har da na gobe”

Ya wuce abinshi ya barta anan tsaye sororo da nera d’ari a hannu, tana tunanin me yake nufi, ta watsar da zancen ta koma kan aikinta.

Dada dai tana k’ara yab’awa iya kulu magana ta barsu anan ta shigewar ta ad’akin ta, Malam ya shigo cikin d’akin da sallamarsa, sannan ya ajiye kwalin yace:

“Ga kud’in nan ki ajiye hannunki”

Dada ta girgiza kai tace:

“A’a je ka ajiye su ahannunka, duk lokacin da ake buk’atar wani abu sai ka bada”

Malam ya duk’a ya raba kud’in uku ya saka kashi d’aya a aljihu, ya tura mata kashi biyu yace:

“Ki ajiye a hannunki saboda tsaro”

“Dada tace to Ubangiji Allah ya bamu ikon rik’on wannan yarinya tsakani da Allah, amman ka sanar da ‘yar kuluwa abunda ake ciki”

 

Akafta😅

 

Takuce

D/Auta👌

.سم الله الر حمن الر حيم
*______________________________*

*💦RUWA DA KANKARA⛈*

*NA HADIZA D/AUTA*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The notion}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________________*

*PAGE FIVE*

******************

Malam yana fita Dada ta fito itama, ba tareda tabi ta kan iya kulu ba, ta fara kici kicin aza ruwan zafi, da sauri iya kulu tazo tana baiwa Dada hak’uri akan taje ta zauna ita zata aza ruwan zafin, Ba musu Dada ta bar wajen, tareda fad’in:

“Wanka za’ayiwa Izzatu, idan sunyi zafin ki kawo man d’aki”

Iya kulu ta bita da kallo acikin mamakin jin sunan yarinyar da taji abakin Dada, saboda suna ne na d’iyarta da ta haifa, wadda watan yarinyar hud’u a duniya tace ga garinku nan, sanadiyyar rashin lafiyar da tayi ta fama da ita kafin ta rasu, gashi yarinyar ta shiga zuciyar kowa agidan, tun daga kanta iya kulu bata sake haihuwa ba, ko b’atan wata bata sake yi ba shekara hudu kenan da rasuwar izzatun, amman har izuwa lokacin bata fidda tsammani ba, akan cewa zata sake samun wata izzatun
sai gashi kwatsam yanzu izzatun ta fad’o daga sama.

Agurguje ta gangand’a kara da guntu guntun itace, ruwan sukayi zafi ta juye ruwan ga wani bokitin karfe, ta had’a da katuwar roba takaiwa Dada ad’aki, sannan taje ta d’auko tsohuwar ajiyar ta, da take ta tsimi da tanadi, wato kayan jarirai na mata set biyu ta kawo ta ajiyewa Dada agefen gado, sannan tace:

“Ga kayanan idan anyi mata wankan asaka mata, amman fa d’ari hud’u na sayi d’aya, d’ayar kuma d’ari uku da hamsin, idan an had’a kud’in gaba d’aya zasu kama d’ari bakwai da hamsin, sai abada d’ari bakwai d’in na yafe hamsin”

Dada dake kici kicin cirewa izzatu kayan dake jikinta,wanda tunda iya kulu ta fara magana bata fasa abunda takeyi ba, aikin gaban ta kawai takeyi, har saida taji ta dire zancen ta, sannan ba shiri ta d’ago fuskarta ta kalleta, bakin ta yana rawa tace da ita:

“Kibar kayanki ai ba rok’ar ki akayi ba ko?, balle ki fara yiwa mutane wani lissafin ki cen na shirmen da kika saba”

Tana k’are zancen ta fara yiwa izzatu wankan acikin natsuwa tareda k’warewa, tana wanketa lungu da sak’o.

Iya kulu ta b’ata fuska tace:

“Dubi kayan dakyau Dada masu kyau ne fa, ayi hak’uri asiye mata su kawai, saboda zasuyi mata kyau sosai”

Dada bata koma bi takanta ba har ta k’are yimata wankan, sannan ta saka zane ta goye ta, tana k’ok’arin fitar da kayan,ne, iya kulu tayi saurin kwashe kayan ta fita dasu, saigata ta dawo da garwashin wuta acikin wani kasko ta ajiye, Dada ta saukar da izzatu ta fara yimata gashin cibiya, sannan ta kalli iya kulu da kyau tayi murmushi tace:

“Da zaki ajiye son kud’inki ‘yar kuluwa to da kinji dad’in rayuwar ki, amman ina kullum abu sai gaba gaba yakeyi, Allah ya jik’an ‘yar dubu, don itakam batada son kud’i irin naki”

Iya kulu ta tashi tsam ta fara tafiya zata bar d’akin, fuskar ta kicin kicin saboda maganganun da Dada take yab’a mata ba k’aramin zafinsu takeji ba, Dada ta kira sunan ta, ta waigo, sannan tace :

“Kinbar kayanki, ko kin barmata kyauta ne?”

Da sauri tace :

“Na zaci an siye mata ai?”

Dada tace :

“Tafi da kayanki, insha Allah gobe zaaje asiyo mata wasu”

Iya kulu ta duk’a ta d’auki kala d’ayar da tace ta siye d’ari hud’u, sannan tace:

“Ga kala d’aya nan asaka mata”

Dada tace :

“Yafi maki dai kam, kiyi don Allah koda zaki samu lada”

Iya kulu ta fita tana takaicin rashin siyen kayan da Dada batayi ba, acikin zuciyarta tace;

“Malam ne zai biya ai, don ni ba mai cin kayana abanza, sai dai in wuta bal bal ce za’aci, inaji ina gani ga kud’i dami guda, abani hak’k’i na ankasa saboda kawai inyi magana, asani abakin duniya, to wallahi dole ne abiyani kud’in kaya na, dari ta uku bazata tafi a iska ba, dank’ari bazata sab’u ba don kuwa yasin zasu saiman dussar kwana biyar in baiwa akuyoyi na”

Idanunta arufe saboda b’acin rai, ba zato kawai taji tayi karo da malam, da sauri ta fara borin kunyar cewa:

“Ai kayan zasuyi mata kyau gaskiya, ni ko d’ari biyu ma aka bada ba komi”

 

Oh ni dije🤔

 

Akafta👍🏻

 

D/Auta ce👌🏻

.سم الله الر حمن الر حيم
*______________________________*

*💦RUWA DA KANKARA⛈*

*NA HADIZA D/AUTA*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The notion}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*________________________________*
*BARKA DA SALLAH MY FAN’S ALLAH YA MAIMAITA MUNA*

*PAGE SIX*

**********************

Malam ya kalleta da kyau, saboda yasan iya kulu ciki da bayan ta, batareda ya bi kan maganar ta ba yace:

“Ina su Garzali ne?”

Iya tayi saurin saita natsuwarta tace:

“Shi yana wajen Dada, Abu ko yana d’aki, ai tunda aka fara ruwan sama ya fara bacci har yanzu bai tashi ba”

Malam ya fara tafiya yace:

“Ki tadashi dai kinsan ba kyau baccin marece”

Iya kulu tana tsaye har sai da taga shigewar sa ad’akin Dada, hannun ta agaba sannan ta sauke k’atotuwar ajiyar zuciya tace:

“Wai Allah ya soni baiji ba, da na jawo wa kaina jangwam”

*SHIN WAI SU WANENE WADANNAN AHALI?*

Malam Abdulkadir jelani mai almajirai, shine ainahin sunan Baban malam Ayuba, mijin mairo wadda kuka fi sani da suna Dada, wanda mutane suke kiranshi da sunan malam jelani, kasancewar shi babban malami, wanda yayi suna acikin garinsu da kewayen shi, saboda almajirai da ake kawo masa yana karantar dasu.

Yayi hidima sosai ga addini alokacin rayuwar shi, wanda har manyan dattijai na garin duk yana basu karatu acikin gidanshi, wanda har izuwa yanzu wannan tarihi bai goge ba acikin zuciya da idanun mutanen garin, saboda ahalin yanzu malam Ayuba shima malami ne masani akan harkar addini, don dattawan garin masu ra’ayin neman sani akan karatun su, to awajenshi ne suke d’aukar karatu, asati sau biyu ne sukeyin zaman .

Malam jelani matarshi d’aya ce ta aure wato mairo, yana da ‘ya ‘ya biyu rak da Allah ya albarkace shi dasu, wato Malam Ayuba da hurere, wadda ake yiwa lak’abi da suna hure, wad’anda su kad’ai ne suka rayu amatsayin ‘ya’yansu, saboda matsalar da Mairo (Dada)take ta samu awurin haihuwa, da ta samu ciki ya lalace.

Wanda alokacin aka canfa aljanu ne suke shanye abun d’an cikin cikin, saboda yanda malam jelani har maganin aljannu yana badawa, shiyasa mutane suka canfa hakan, ganin da ta sami cikin sai yak’i tsayawa, ak’arshe ma haihuwar ta d’auke d’if aka barsu tareda yaransu biyu Ayuba da hure.

Ayuba yayi aure da iya kulu wadda ake kira da suna ‘yar kuluwa, alokacin ganiyar budurcinta, suma Allah ya albarkace su da yara biyu Garzali da Abubakar, sai izzatu da suka haifa wata hud’u ta rasu, tun daga kansu har zuwa yanzu tsit, ko b’atan wata.

Hurere kuwa itama tayi aure da yaranta hud’u biyu maza biyu mata, don ko yanzu cikine da ita yau ko gobe, inna hure kenan itama kunji labarinta.

*DANGANTAKAR DADA DA IYA KULU*

Dada da mahaifiyar iya kulu uwa d’aya uba d’aya suke, wadda ake kira da suna halima amman ana yimata lak’abi da sunan (‘yar dubu).

Yar dubu ta rasu wajen haihuwar ‘yar kuluwa, ta barta tana jaririya ahannun Dada, itace ta rik’eta har zuwa girmanta, saboda kiriniyar ‘yar kuluwa da mugun son kud’inta, yasa Dada tashin hankali ba kad’an ba, alokacin da girma ya fara zo mata samari sukayo mata caaa, amma ita kam ba wanda yayi mata acikin su, don ita ayuwarta, tafi son ta auri mai kud’i, shiyasa gaba d’aya samarin k’auyen nasu ta rena su.

Saboda ganin k’awarta da suka taso atare, wani alhaji abirni yazo ya aureta, shiyasa ta k’wallafa ranta akan bata auren kowa sai mai kud’i, itama ta fantama yanda k’awarta takeyi, musamman in tazo k’auyen ankawota da mota, suje suyita shafa motar suna k’auyanci, tayita rok’on k’awar tata akan ta nemo mata miji d’an birni itama tayi aurenta acen itada k’auyen sai dai idan zata wuce ta hango shi, aiko suka kitse magana atsakanin su, batared sanin kowa ba ‘yar kuluwa tabi k’awarta abirni cen inda take aure.

Hankalin su Dada ya tashi, gari ya d’auka kulu ta b’ace, sai cen aka ji labarin tabi k’awarta abirni, jiki yana rawa iya tasa aka kaita har cen gidan na k’awar tata, ta taso k’eyar ta suka dawo k’auyen su, bayan tasha duka ba na wasa ba ahannun Dada, saboda takaicin hakan yasa ta nemi alfarma awurin dangin baban ita kulun.

Akan tana son ad’aurawa Ayuba aure da ita kulun, saboda tana jin tsoron abunda zaije ya dawo,na aibi ga rayuwar kulu, domin yanda tasawa zuciyar ta k’aunar kud’i, zaiyi wuya idan ta k’ara girma ashawo kan matsalar, alokacin ko bacci takeyi, mafarkin kud’i takeyi.

Ba tareda sanin Ayubaba bale kulu aka d’aura auren su, da yake shi ayuba mutum ne wanda yasan darajar iyaye ko afuska bai nuna yaji haushin auren ba, duk da ba ita yaso ya aura ba, amman yayi biyayya ya rungumi ‘yar uwarshi kulu sukayi ta zaman auren su, duk da botsare botsaren da kulun ke yimasa, bai fasa kyautata mata ba, har izuwa yanzu lokacin da suka hayayyafa, iya kulu bata saduda da son kud’in ba, har saima abunda yaci gaba.

*To kunji tarihin su sai adawo gundarin labarin🏃🏻‍♀wanda shine mak’asudin wannan littafi mai suna RUWA DA KANKARA*

Ci gaban labari

Malam ganin yanda Dada ta shirya izzatu tsaf tareda maida mata da sock’s d’inta da hularta da aka tsinto ta dasu.

Farin ciki kwance akan fuskar malam yace:

“Rik’o man ‘yata garzali, kabi ka kanainayeta, kamar wanda za’a k’wacewa ita”

Garzali yana murmushi ya taso ya mik’awa Abba y’ar, sannan yace:

“Da ka ganta ni zaka maida wa ita ko?, ba dada ba”

Malam yayi murnushi yace:

“Hannun amsa ai hannun mayarwa”

Dada tayi dariya tace :

“Dani kake zancen yaro, bayan ka mance da marairecewar da kayi ne a yanzu, akan in baka ita nak’i, to gobe ko zan baka ita yaro kasani sai in kana da nera goma”

Garzali yayi saurin saka hannu ya karb’e izzatu a hannun malam yana dariya yace:

“Allah ya soni na d’auketa har da na goben, kinga goma ta sai ta huta”

A haka sukayi ta barkwancin su Garzali da Dada, suyi fad’a sudawo su shirya, malam dai iyakacin shi murmushi idan sunyi abun dariya, har zuwa lokacin da iya kulu ta k’are abinci, anan ta kawo masu suka baje sukaci abincin su.

Hadari ya k’ara had’uwa aka yita malala ruwan k’ank’ara gundum gundum gwanin ban firgici, domin kuwa atarihi kaf basu tab’a ganin irin wannan al’ajabi ba, su malam suka rud’e sai zuba addu’o’i sukeyi, garzali da Abu kam kuka reras suka sha, saboda tsoro, ita kanta iya kulun, sai da tazamo tamkar wata sabuwar balaraba saboda salati da hailalar da takeyi.

Sai kace ba itace mayyar kudin nan ba😹🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀

 

 

Taku ce

D/Auta👌🏻
*💦RUWA DA KANKARA⛈*

*NA HADIZA D/AUTA*

 

بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*

*PAGE SEVEN*

*********************

Itama kanta jaririya izzatu sai kuka takeyi, Dada tana ta lallashinta tana kiran:

“Tsarki ya tabbata ga ubangijinmu, wanda yake sauko muna wad’annan RUWA DA KANKARA, lalle ke ‘yar baiwa ce, samunki alkhairi ne awurinmu, Allah ya bamu ikon rik’on ki da gaskiya”
Su malam sukace: “ameen”

Haka dai akayita ruwan k’ank’arar guma guma, anraba dare ana ruwan sannan ahankali suka fara ragewa har suka tsaya cak, zuwa lokacin iya kulu da su Garzali har sunyi bacci, amma Dada da malam suna tsaye kai da fata sunata addu’o’i tareda jinjina girman wannan iko na Ubangiji,.

Bayan komi ya lafa Dada tace da malam “suje d’akunansu su kwanta, saboda gobe zasuyi sammakon zuwa birni domin sukai izzatu asibiti domin aduba lafiyarta”

Haka ko akayi Malam ya tada iya kulu suka ja yaransu suka fita tareda yiwa junansu sai da safe.

Bayan fitarsu Dada ta sauke izzatu ta lallab’a ta kwantar da ita, tareda tofeta da addu’o’i, sannan ta rab’a agefenta ta d’an gincira, aiko ba shiri bacci mai nauyi ya d’auketa.

Asubar farin izzatu ta tada Dada daga barcinta mai dad’i da takeyi, ta hanyar kwantsama kukan da tayi tayi, dole Dada ta farka ba shiri.

Da dubara ta samu tayi sallah, sannan ta
dawo hidimarta, akayi dai dai malam ya shigo domin ganin meke faruwa, saboda yaji kukan izzatu,haka kawai yakejin son yarinyar tamkar shine ya haifeta, da sallamarshi ya shigo idonshi akan izzatu yana yiwa Dada barka da safiya.

Bayan sun gaisa ne Dada tace dashi:

“atatso nono aba izzatu tasha saboda yunwa ce ta tada ita daga bacci”

Malam jikin shi yana rawa ya fito, bai ko bi takan iya kulu ba yaje ya tatso nonon da zafinshi yakai aka bata, sai da tasha ta koshi sannan ta koma bacci, hankalinsu ya kwanta.

Malam yana shirin fitowa d’akin ya had’u da iya kulu ta fito tana kiciniyar had’a wuta, domin ta aza ruwan zafin da za’a yiwa izzatu wanka, malam yace da ita:

“Na tatso nono anbaiwa izzatu tasha”

Iya kulu tayi saurin d’agowa daga hurin wutar da takeyi da bakinta tace:

“To ai kuma ba’a bada kud’in ba ko anbiyo ne?”

Malam ya kalleta sororo sannan yace:

“Na jiya da na baki asusu nace ki saka su halan?, yanzu ke don Allah tun da sassafe zaki saka mutane d’aga jijiyoyin wuya, to daga yau ma ta daina shan nonon sai ki dinga kasa shi a kasuwa kina saidawa idan kinso, amma nikam babu ni aciki”

Yana k’are maganar ya wuce abinshi zai shige d’akinsa, iya kulu ta bishi da kallo tareda murgud’a baki ta fara gungunin cewa:

“Mutum da abunsa bazaiyi tambaya ba?, waya saya mun akuyoyin?, ai da kud’in adashe na ne da nikeyi na sayi kayana, don haka bazan tab’a lamunta aci da hak’k’ina ba, ko don kai ke bani kud’in zubin adashen, shiyasa zakayiman gadara, to ai kyauta ka bani ba ranko aciki”

Bayan ta k’are ‘yan surutanta sannan tayi saurin biyar shi abaya tana bashi hak’uri, saboda ta fahimci ransa ya b’aci akan hakan, baija zancen da tsauri ba yace da ita: “taje bakomi”.

Sannan ta fito ta nufi d’akin Dada domin ta dubo ya suka kwana.

Bayan sun gaisa ne taje ta juye ruwan zafin ta kawo akayiwa izzatu wanka, sannan Dada ta shafeta da man kad’e tas sai k’yalli takeyi, ta k’ara shiryata ta goyeta.

Saiga Garzali ya shigo kamar an jefoshi, yana mutsu mutsun idanuwa, sai rabasu yakeyi domin ya hango izzatu, amman bai ganta ba, acikin tashin hankali yace :

“Dada ina izzatu yanzu shikenan ank’waceta ta tafiyarta bazamu sake ganin ta ba?”

Acikin mamaki Dada da iya kulu suka bishi da kallo, ganin yanayin kallon da suke yimasa yasa ya gasgata mafalkin shi ya fara kuka yana sanbatun cewa:
“Yanzu shikenan sun karb’eta don mugunta”

Da dai Dada ta fahimci inda ya dosa, tayi saurin cire lullub’in zanenta da ta rufa wanda shi ya hana shi yaganta a goye, aiko yana ganinta kafin Dada tace wani abu yayi saurin washe bakin shi yace:

“Laa ashe basu tafi da itan ba”

Dada da iya kulu suka tuntsure da dariya, Abu dake bayanshi, saboda ya biyoshi yaji me ya firgitashi acikin bacci, jin abunda yake fad’a ayanzu shiyasa yaji haushin sa, don shi sam yarinyar batayi masa ba, ba shiri ya buga tsaki yabar d’akin, Dada ta gallawa k’ofar da ya fita harara tace:

“Kai kam duk wanda yaga girmanka sai yaga fad’in rai, bak’in hali k’arara tun kana d’an k’aramin ka to ina ya ka girma?, Allah dai ya shiryeka amman kam akwai aiki”

Iya kulu ta b’ata fuska tace:

“Zai daina ne ai”

Dada ta kalleta tareda yimata wani kallon reni tace:

“Daman aike baki so aga laifin d’anki, kuma dole ne a nuna masa kuskurensa ko don gobe ya gyara, don in har aka barshi da tarbiyar ki, kece zaki kwana aciki inya girma, donmu alokacin ma bamu araye bale muga kayan takaici”

Iya kulu ta zunb’uro baki ta fitowarta, Dada tace:

“Ai komi da Abu yakeyi gado yayi awurinki, bai yar ak’as ba, don haka daga ke har shi Ubangiji Allah ya shirye ku”

Bayan sun karya ne suka fara shirin zuwa gidan mai unguwa domin ahad’a su wad’anda zasuyi masu jagora zuwa birnin, aiko daga zuwan su ba wani tsaiko daman su kawai ake jira suka lula sai asibitin birni.

Bayan duk wasu gwaje gwaje da akayiwa izzatu an tabbatar batada matsalar komi, amman sun rubuto mata magungunan da za’a rik’a bata tanasha, masu inganta jiki, sannan an fad’a masu madarar da zasu dinga bata wacce take d’auke da wasu sinadaran da nono yake d’auke dashi.

Malam ya nemi alfarmar wata nurse da ta rakashi yaje yayi ma izzatu siyayyar abubuwan da zata buk’ata, aiko ba musu ta d’auki excuse suka garzaya sai wani babban shago, nurse d’innan ta zage damtse tayita lodowa izzatu kaya, tun daga b’angaren sutura da pampas, da madara hatta kayan wasa idan ta k’ara girma duk saida ta d’auko, malam dai iyakacin shi ido, duk da yana da ‘yar wayewarsh dai dai gwargwado, amman kam wasu kayan ko ganinsu bai tab’a yi ba balle yasan me akeyi dasu.

Bayan sun gama siyayyar ne, nurse d’in tayi masa bayanin duk wani abu da ya shige masa a duhu, malam yaji dad’i sosai yayi mata godiya, sannan suka dawo inda su Dada suke jiransu, ganin uwar siyayya ledaodi manya manya ya saka Dada tambayar malam akan cewa “duk me ya siyo har haka?”.

Malam yace: “Ta jira idan sunje gida zai yimata bayani”

Nurse d’innan tayi masu sallama zata tafi, Dada tace da ita:

“Dawo ‘yar nan, kigayamuna sunanki, ko don mu k’ara yimaki godiyar irin wannan hidima hk”

Ta dawo tana murmushi tace:

“Suna na Aisha”

Dada tayi murmushi ta fara yiwa nurse Aisha wak’a tace:

“Sannunki shatu shatulle, indo A’i farar d’iya, baki aure k’auye kisha wuya, daga birni sai babban gari, sai ko wani babban malami, koko wani babban attajiri”

 

Indo an wasu🤣🤣🤣

 

Akafta😜

 

 

D/Auta ce👌🏻

بسم الله الرحمن الر حيم
*__________________________________*

*⛈RUWA DA KANKARA💦*

*NA HADIZA D/AUTA*

☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀

FCWA

*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*

https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*

*PAGE EIGHT*

********************

Aiko BA shiri nurse Aisha ta washe baki har kunne, saboda taji dad’in wak’ar da Dada tayi mata, aiko ta samu wuri ta zauna sai fira ta b’alle atsakaninta da Dada,har zuwa lokacin da izzatu ta fara kukan neman abinci, Dada ta kalli Aisha tace:

“Na shigesu ni mairo, ko ina zan sami nonon akuya inbaiwa wannan yarinya?”

Aisha ta zaro ido awaje tace:

“Nonon meye?”

Dada acikin tabbatarw tace da ita:

“Nonon Akuyoyi”

Aisha tayi murmushi tace:

“Jirani minti biyu inzo”

Aiko saigata ta dawo da Flack’s na ruwan zafi da cup da spoon ta ajiye agaban Dada, sannan ta bud’a ledodin siyayyar ta fiddo da gwangwanin madara d’aya don guda uku aka siye, saboda tazarar dake tsakanin k’auyen SU da garin.

Sannan ta fiddo fida babba taje ta wanko ta tas, sannan ta zuba madarar akofi ta tsiyaya ruwan zafi dai dai madarar ta jujjuya,har saida ta hade gaba d’aya, sannan ta juye madarar afida ta rufe.

Dada dai da sauran wad’anda ke wurin, sai binta da kallo sukeyi, acikin mamaki dada tace:

“Yanzu shikenan za’a iya bata tasha ahaka ba sai in dafa awuta ba?”

Aisha tayi ‘yar dariya tace:

“Haka akeyi akullum idan za’a bata yanzu ad’an jira ta rage zafi sai abata”

Aiko farin ciki ya wadatu afuskokin su gaba d’aya, musamman Dada da malam da suka if kowa shiga damuwa akan kukan da izzatun takeyi, suna tunanin yanda zasuyi, saiga mafita asauk’ak’e Allah ya kawo masu.

Aiko saboda kukan da izzatun takeyi, Aishar ta d’ebo ruwan sanyi akofi ta jefa fidar madarar tana juyawa, minti k’alilan madarar ta huce aka bata sai zuk’a takeyi, kamar ta saba sha, kafin kace me har ta shanye fidar gaba d’aya, sannan tayi gyatsa sai bacci.

dukansu sunyi mamakin madarar da tasha, shiyasa aka sake kad’a mata wata madarar, koda zata falko kafin suje gida.

Sukayiwa Aishar godiya sosai sannan suka mik’e zasu koma k’auyen su, anan ne Aishar take tambayar a’ina suke, dada tayi mata bayanin sunan k’auyen da suke zaune, nurse Aisha tayi mata alk’awali duk lokacin da ta sami dama zataje har k’auyen ta dubo izzatu, saboda yarinyar ta shiga ranta sosai ta burgeta.

Dada taji dad’i sosai tayi ta yimata adduar gamawa lafiya,aiko da ita Aishar aka sakawa su Dada kayan su amota, daga nan sukayi sallama, akan sai watarana, suka rabu acikin kewar juna.

Tafiyar da bata gaza minti arba’in ba itace ta kawo su d’an k’aramin k’auyen su, kai tsaye aka wuce dasu Dada har gidan mai unguwa, bayan sun k’are yimasa bayani abunda ya wakana acen asibiti, suka nuna masa siyayyar da akayowa izzatu, ya jinjina masu sosai tareda saka albarka acikin duk wani nufi nasu na alkhairi akan jinjira marainiyar Allah izzatu.

Bayan sun k’are ne mai unguwa ya saka aka jidi kayan nik’i nik’i aka kai masu gida tun kafin su K’arasa agidan.

Suna shiga suka iske Iya kulu tayi fillah fillah da kayan ak’ofar d’akinta sai kallo takeyi, inta duba wannan at ajiye ta d’auko wani har takai kan gwangwayen madarar da aka siyowa izzatu, ta d’aga gwangwanin tana kallo sai jujjuyashi takeyi, saboda tana son ta k’ara tantance shin miye aciki, ta girgiza taji k’arar garin madarar dake aciki yana sukuf sukuf, batareda tunanin komi ba ta saka hannu ta b’alle murfin, saiga wannan ‘yar silbar takarda dake rufe da bakin gwangwanin.

Ba shiri ta b’urmama farcen ta atsakiya aiko sutuf ya fad’a kasancewar akaifarta da take da itace tayi saurin walshe takardar, aiko bata tsaya wata wata ba ta yage takardar gaba d’aya ta jefar, ta saka hannu ta kwaso madarar ta kai abaki zata afka saiga sallamar Dada da Malam sun shigo, aiko ba shiri ta guma madarar, sannan ta jawo murfin gwangwanin ta rufe tana k’ok’arin maida kayan acikin ledodin.

Baki asake Dada ta bi iya kulu da kallo, saboda gaskiyar ma taxi mata yawa, malam kam k’arasowa yayi ya dinga tama ta suna maida kayan, Dada saboda haushi kasa magana tayi ta shigewarta d’akinta.

Malam yana ganin shigewar Dada, iya kulu ta kawo hannu zata d’auki wani tissue ta mayar leda, da sauri ya bangaje ta, ba shiri ta fad’i ak’asa warwas, aiko madarar dake bakinta ta dunk’ule mata mak’oshi ta sark’e, ta fara tari ido suka gwalalo awaje sai nuni takeyi da hannu akan ya taimaka mata da ruwa.

Malam kam yana k’are maida kayan, ya nufi d’akin Dada yabarta anan tana neman agajin abata ruwa, ya fahimceta kar amma yayi banza da ita ya tafiyarsh, acikin zuciyarshi yana cewa:

“Indai hak’k’i ne to kad’an kika gani”

Da rarrafe taje wurin tukunyar ruwanta, ta kandamo tayi masu muguwar zuk’a aiko saigata da k’walla k’ara tace:

“Wayyo wuyana!”

Saboda yanda ta had’a ruwan sukayi muk’ut suka fad’a da k’arfi tareda dunk’ululun madarar da ya tsaya mata amak’oshi, saiga su Garzali sun dawo inda ta aikesu.

Da sauri Garzali ya k’araso idonshi akanta yace:

“Iya lafiya idanunki sukayi ja haka?”

Iya kulu ta had’iye miyau tace:

“Bari kaidai d’an nan, kwad’ayi da dad’i amman akwai wahala idan rana ta b’ace aka rutsa da mutum”

Sai jin muryar Dada tayi tana fad’in cewa:

“Ai dama ance duk wanda ya hau motar kwad’ayi, to ba inda zata saukeshi sai tashar wulak’anci, duniya dai ce ta ishi kowa riga da wando, wanda bai zo bama jiranshi takeyi”

Iya kulu tayi sum sum ta fad’a d’akinta, saboda ita kanta bata ji dad’in riskarta da akayi ba, amman dai kam taji dad’in madarar ba kad’an ba, shiyasa afili ta furta cewa:

“Anji kunya ansha dad’i

Leave a Comment