💅NIDA YAYA OMAR💅
(short story)
✍SUMAYYA (MMN HIBBAT….)
№ editing❌
Episode 1&2
“Zauna ne suke suna d’an ta’ba hira suna dariya sosai, suke jin dad’in firar mummunan labarin da yarinyar take ba su wacce ba za ta wuce shekara sha bakwai ba, ka na ganinsu za ka san ‘ya da uwa ne sabida tsabar kamar da sukeyi….
“Lahhh KURSUM!” “Na’am AMMIY meya faru?”,” na manta tun d’azu OMAR ya dawo” kuma ban bashi abinci ba, maza ki tashi ki kai mishi abinci kinga tun d’azu ya dawo.
Fuska ta kwa’be dan Allah ya sani bata san zuwa ‘dakin yaya Sabida muguntarsa shi ko,ba kai mai laifi ba, sai ya san yanda ya ci zalinka shiyasa bata san zaman shi a gida,babu yanda ta iya dole taje tunda Ammiy ce ta sata,.
tashi tayi tana zumb’uro baki gaba..Tana zuwa ta ga kofar d’akin a bud’e, alamun yana ciki babu wani bata lokaci ta ku tsakai Cikin d’akin zaune yake yana, ‘yan rubuce² da alama ma bai ji shi gowarta ba..”Yaya ga Abincin na ka” ta fad’a tare da turamai filas d’in abincin, Wani, mugun’, kallo ya watsa mata tare da jan dogon tsaki, Baki ta zumb’uro gaba tana gunguni k’asa-k’asa, shi mutum “kullin fuskarsa a d’aure take sai ka ce, wanda ake aikowa da mala’ikan mutuwa komai a kai mai ba a, iya ba” ta ja tsaki’ wanda bata san ya fito fili ba..
Saukar marin da ta ji ne ya dawo, da ita daga zancan, zucin da ta ke yi, YAYA OMAR ne a tsaye A gabanta, yana huci sai kace wani Zaki. Ba ta gama warkewa daga marin da ya shinfid’a mata ba, yasa k’afa ya kwasheta, sai ga ta A ‘kasa wata k’arah ta saki,ta ri’ke kanta da hannu bibbiyu, sabida zafi da rad’ad’i da gurin yake mata, Amma bata isa tayi kuka ba yanxu sai ya k’ara yi mata wani dukan..”Ke wacce iriyar mahaukaciya ce za kizo kinamin ihu A kai” ya ‘karashe maganar Cikin tsawa, wanda hakan ya k’ara firgitata Bata san sanda wani kuka ya kufce mata ba, tayi saurin toshe bakinta,gudun karya k’ara mata, ta san halinshi,sarai ba ‘karamin mugu ba ne, tsaf zai iya karairayata ya zubar A banza, gashi babu Ammiy a kusa bare ta ceceta…
Tashi ki fice min daga d’aki ‘kazamar banza dubeki kowaye zai ci wannan ja gwal gwalon naki da ki ka gama tattofa yawu da majina, yarinya sai ‘kazantar masifa ke ko kunya ma bakya ji….
Da sauri ta mi’ke harta tana tuntub’e da dokin kofa ga zugin da kafarta take mata.. Allah ya isa ta shiga jero mai tana zaginsa “mugu azzalimi ni ban
san me nayiwa wannan mutumin ba ya tsaneni haka”…
Sai da ta, kusa, zuwa, d’akin, Ammiy Ta saka kuka mai gunji, Ammiy da ke zaune tana, linkin kayanta da ta wanke ta jiyo kukanta da sauri ta mi’ke har tana neman fad’uwa A bakin k’ofa suka cikaro, sai ko ta fad’a jikin Ammiy tare da sakin kukan shagwa’ba..Cikin kuka ta kwashe komai ta gayawa Ammiy, rarrashinta Ammiy tayi tace “ta barshi da Allah…
Babu yanda ta iya illah tayi ha’kurin dan ta san ba iya ramawa za ta yi ba kuma ta san AMMIY ba, tare mata za ta yi ba iya ka ci dai ta bata ha’kurin. Shiyasa ta ja bakinta ta tsuke, Cikin ranta ko sai ja mai Allah ya isa take,tana Addu’ar Allah yasa, ya koma,gurin aikinsa gobe ko ta sakata ta wala, in dai yana gida to fa bata sakewa yanzu,sai ya hau jibgar ta kamar ya samu jaka “mugu kawai” ta fad’a a fili. kallan’ta AMMIY tayi tace “KURSUM, kenan ke gaki da Rashin kunya shi kuma da xuciya kamar turuku, kullin Cikin fad’a kuke ba za ku zauna guri d’aya ba tare da kunyi Rigima ba, ni har mamaki kuke ba ni musamman OMAR da kullin baya gajiya da duka ko an gaya mai nan bariki ce da zai ringa, Doke-doke, haba’ wannan abu yana damuna Sosai” AMMIY ke fad’a kamar ta Ari baki…!
Ana Cikin haka sai ga.. OMAR ya shigo kallo d’aya yayiwa AMMIY ya gane na fad’a mata Abin da ya faru, tunda yaya ya shigo Ban yarda mun had’a Ido da shi ba, Sabida tsoro dan ma Allah ya temakeni AMMIY na kusa ai’da sai ya kasheni dan da, za’a bashi dama Ace ya kashe wani To ni ce wadda YAYA, xa fara kashewa Sabida, tsantsar tsanar da yayi min.Shi kuwa OMAR sai hararata yake yana so had’a Ido Amma ta ki yarda.sai kawar da fuskarta ta takeyi. “Tashi ka bani guri tunda kai Kurma ne”. Gaba d’ayansu suka d’ago suna duban AMMIY, da ta mur’tike fuska kamar ba AMMIN da suka sani ba. Wacca suka d’auke ta tam’kar kakarsu. Lallai ran AMMIY ya b’aci ba kadan ba Shi kanshi OMAR da yake sarkin fushi sai da ya sha jinin jikinsa, AMMIY na fushi da shi fushin da bai tab’a ganin tayi ba, zai iya Rantsewa da Allah bai ta’ba ganin b’acin ran AMMIY ba tun da ya zo duniya, kullin fuskar ta Cikin fara’a ta ke…!
Jiki a mace ya mi’ke ya k’arasa inda AMMIY, take, zama yayi a ‘kasa tare da Ruk’o, Hannuwanta dika biyun kana yace “Don Allah AMMIY kiyi ha’kuri ki yafe min plsssss AMMIY na karki fishi da ni fushinki zai, I’ya zama nak’asu A rayuwata wanda na san ba za ki so, hakan ta kasance ba. Ina me rokanki AMMIY da ki duba girman Allah,ki dena fushi dani..!”
Allah,sarki dama ance tsakanin d’a da mahaifi sai Allah, nan da nan zuciyar AMMIY ta karye sai taji tausayin shi ya kamata dik dama ba fushi takeyi ba ta yi ne dan ta samu su dena,kyamatar junansu Sabida nan gaba…..!
“Karka damu OMAR na yafe maka Allah ya yafe mana gaba d’aya Allah yayi muku al’barkah”..gaba dayan suka amsa da Amin. Sosai yaji dadi A ransa da AMMIY, ta dena fushi da shi kuma ta sa mai Al’barka ji yake tamkar an sashi A aljanna..!
Salama ya yi wa AMMIY, Sabida yana da aiki sosai a gabansa kuma ba ya so gobe ya makara a gurin ai’kinsu sabida suna da wani babba mitin da zasuyi kuma shine jagora…!
Yana zuwa sai’tin da, KURSUM, take zaune yasa k’afa ya murje mata’ ‘yan yatsu sannan yayi ‘kasa da murya yanda AMMIY Ba za ta ji ba yace “KURSUM, na tsaneki na tsaneki bana sanki ba zan tab’a sanki ba, tunda kika had’a ni da AMMIY, Tunda nake ban tab’a ganin AMMIY A Cikin ‘bacin rai ba sai a sanadinki….!”
Azaba rad’ad’i gaba daya sun tarar mata, gashi yaki ya dena murza mata yatsu a k’asa gashi hannunta ya fashe har ya soma zubda jini, hawaye ne kawai yake ambaliya a fuskar’ta gashi bata son AMMIY ta sani kuka ne yake neman kwace mata, tayi saurin toshe bakinta wasu hawa’ye masu zafi suna surnano mata, gaba d’aya fuskar’ta jike da hawaye da majina. Sai da ya tabbatar da ya wahalar da ita sannan ya kyale’ta yafice daga d’akin ya barta da Axabar da hannun’ta yake mata,ko daga shi ta kasayi abinka d farar fata.. kan kaceme hannun’ta ya kumbura yayi suntum….!
Mmn hibbaty ce✍🏻
*💅NIDA YAYA OMAR💅
(short story)
Episode 3&4
Saida tagasa hannunta sannan tasamu sassaucin azabar da yake mata. Koda wasa batasake yin k’urin sake fitowa ba sai washegari..
Koda ta fito abin karin ta iske Ammiy tayi murmushi tayi ta soma karyawa tana Cikin karyawa tajiyo k’amshin turaransa dasauri ta d’auke kanta dan bata fatan wani abu yasake had’asu.,
Cike da izzah yazauna a dainin din copy yad’a yasomasho yana yamutsa fuska kamar wanda akayiwa dole..
Tagefan ido KURSUM take kallansa tana makakin irin halinsa shi komai nasa saiya nuna k’arfin izzah kodan yana soja shiyasa yake wani tak’ama yana hura hanci. Abin bak’in Cikin ma kwata kwata baya fara’a killum fuska aturb’une saikace wanda ake aiken mutuwa kullin.. tsaki taja wanda bata ya fito filiba..
Shan yayyun idanunsa ya zubamata yace Keeeeey ubanwa kikewa tsaki, jikintane yadauki rawa kofin hannunta yafad’i kasa ya tarwatse tsawa ya kuma daka mata yace badake nakeba?”
Tsabar gigicewa datayi bata sanda tasaki fitsari ba..
Gashin kanta yacafka da k’arfi harseda tayi k’ara ingijeta yayi tafad’i k’asa hawaye nabin fukarta. tsabar azaba kukanma kasayi tayi sai ruwan hawaye take,..
Komawa yayi yaci gaba da shan copy dinsa hankali kwance. Har yagama karinsa yashiga yayiwa Ammiy sallama bata motsaba..
Haka Ammiy tazo tasameta Cikin wannan yanayin tambayar duniya Ammiy tayiwa KURSUM Amma taki tanka mata aganin gaya mata bashi da wani fa’ida tun ba mataki zata d’auka..
Dole Ammiy ta rabu da ita tai shigewar ta d’aki da kyar ta iya kai kanta d’aki wannanka tayi sabida fitsarin da tayi kokaya bata sakaba tayi kwanciyar ta bacci barawo yasaceta..
Omar
tunda ya isa barek d’insu baizaunaba ya shiga shirya mutanan da xasuyi tafiyar domin gurine mai had’ari..
dole sai sun shirya, sosai sabida yanta addar sunada mugayan makamai.. aiki yake Cikin kwarewa dazafin nama,. fuskar nan babu annuri ko kad’an sunyi shiri sosai, sai fatan nasara akemusu..
Har bakin mota akarako OMAR. sabida girmamawa nan suka soma tafiya,..
lokacin dasuka tunkari dajin Omar yashiga karanto ayoyin tsari dik da ba wannan ne karan farkon shigarshi daji ba amma wannan yasha ban ban da sauran..
Wayarsa yazaro dg aljihunsa number Ammiy ya danna kamar jira ake aka dauka murmushi yayi. Yace Ammiy na ajiyar xuciya ta sauke tace UMMARU. kana lpy dai ko?”
lpy nake Ammiy saidai ina buk’atar addur ki yanxu hk muna gab da shiga dajin dan allah Ammiy kisani Cikin addu arki,.
Wacca nasan da itane zan samu nasara.
Addu’a Ammiy tayimai sosai. yaji dad’i sosai sannan sukayi sallama..
Cike da kwarewa Omar suka shiga cindajin suka bi kowaca kurwa sukasa na k’ura wacca suke da tabbacin “yan ta addan sunan sabida ba aguri d’aya suke zauna ba.
Asannu yasoma bincike har yasamu san saninsu wajan kashi uku. Nanan ya kar kasa sojo jinsa, tare gargad’insu subi komai asannu. Karsuyi gaggawa. nan suka ansa da Yessssssa.
Nan suka kar kasu Cikin dajin kan kaceme dajin ya har gitse sosai sojo jin suke iyakar k’okarinsu domin ganin sunci nasara. Anyi d’auki ba dad’i kafin allah yabawa su OMAR, sa’a suka tar watsa san sanin” suka kwashe maka man yanta addan. suka kama ogansu dik da bulet d’inda yake jikinsa hk suka jefashi a’mota.
Tun a’hanya ake bogowa OMAR waya anatayashi murnar samun nasara.
Koda suka isa barek ensu tarb’a akayi musu iri ta sojoji,. Dik wani mai fad’a aji na k’asar saida yazo gurin.
Shikuwa general Omar. Baibi ta kansu ba ya wuce Oppice ensa tare da bada umar nin kai shugaban “yan ta addan sukama hospital sabida suna san samun wa ensu bayanai agurinsa game da dajin san bisa wanda yake da had’ari shigar shi saida da dabara da sanin makamar aiki wannan daliline yasa general OMAR, barinshi araye”
ƙarfe huɗu na yamma ya ɗauki hanyar gida. koda yashiga gidan baiji motsinsu a farlo ba hayayi hanyar ɗakinsa yajiyo motsi a,kicin ammiy yagani bataji shigowarsa ba saijitayi an rungumeta ta baya har seda ta ɗan raxana. tare da tureshi tace yau kuma tsoratani xakayi, murmushi yayi yace waneni na isa na tsorata ammiy na gashi kuwa kayi..”
wai ammiy meyasa kike wahalar da kankine,. wajan girki al.halin a kwai wannan muna fukar ita meyasa baxatayi ba wllh ammiy kina sangarta ta dayawa..
koda yake ita xatasha wuya intayi aure ga ƙazanta wllh mijinta yashiga uku,.
ya faɗa yana barin kicin ɗin.
ɗakin KURSUM yanufa yanaxuwa ya hankaɗa ƙofar jikake garammmm. kan gado ya hangota tana ta sharar baccin ta yajima a’tsaye yana kallanta ransa na ƙuna jiyake kamar yashaƙeta ta mutu… yadaɗe yana ƙitssima muguntar daxe mata.
Kan gadon yayima tsinke. baiyi wata² ya dank’i gashin kanta yayi jifa da ita jikake timm k’ara tasaka tare da rik’e kanta..tana rusa ihu. Bai tsaya b’ata time ba yashiga kwalla da ita, tuni bakinta yafashe yasoma xubada jini. Amma bai dena dukanta ba. saida yayi mata lilisss yabarta nan kwance.
Dik abinda suke Ammiy najinsu saida babu yanda ta iya. tasan a kwai lokacin da kokud’i akabawa Omar baze daga hannunsa yakai jikin KURSUM da nufin duka ba.
Mmn hibbat ce✍️
*💅🏻NIDA YAYA OMAR💅🏻*
(Short story)
_Godiya ta musamman ga d’auka cin masoyana musamman fans din ina godiya da yaba k’okarina da kuke allah yabani ikon gama wannan book din lpy Ina mik’a sako gaisuwa ga d’auka cin masoyana wanda nasani da wandama ban saniba ngd ngd ngd👏🏻_
✍🏽 *SUMAYYA (MMN HIBBAT….*
№ editing❌
Page 5&6
“fitowa yayi daga d’akin ya koma kicin d’in fuska kamar ta shanu yace wllh dik wannan laifin nakeni ke kike sangarta yarin yar nan yanxu fisa bidillahi haka zaki cigab d xuba mata ido tana abinda ta gadama yarinya sai k’azantar tsiya a’haka zakiyi mata auran bata iya girki ba Wllh kinji na rantse babu wanda zai aureta garaki samu ko almajirine kibashi sadaka shima saidai yayi maneji..!
‘Hummm Omar kenan kagama. to dan allah idan mijin yaxo kakoreshi. Kaga inxa’a fasa.
Kuma da kake cewa inbawa almajiri ita wllh “yata tafi k’arfin almajiri saidai mai kud’i kajima nagaya maka…!
Murmushi yayi yace zamu gani ai,kwarai zakagani kuwa dan kama sani nanda wata biyu ko uku KURSUM na tazama matar aure.. fuska OMAR ya had’e yace wllh in kina xan cannan xuciyana ta. tafar fasa yakeyi” ya fad’a tare da ficewa daga kicin din kamar wani kububuwa.!
Tsaki Ammiy taja tace kayi kagama wannan xafin rannaka sai ya kaika yavaroka atashar dana sani taja tsaki,.
Yaro sai kafiya da taurinkai kamar mutanan farko..!
Omar
Kuwa d’akinsa ya koma ya kwanta haka kurum in yaji Ammiy na manar auranda zatayiwa KURSUM saiyaji ransa yana suya,…
Tsaki yaja. Afili yace komeye abin damuwa ma Ohoooooo nida bama san ganinta nakeba k’azama da ita”
Saida Ammiy ta gama girkinta tassss. Ta gyra ko ina sannan ta shiga dakin KURSUM wacca take kwance, ta k’urawa sili ido da alama tayi nisa Cikin tunani saida Ammiy ta tab’ata sannan tayi firgigit ta tashi…!
Tuna nin me kikeyi haka?”Ammiy ta tambayeta.. hawayene suka sintiri a Kuma tunta kamar anbud’e famfo….
Tace yanxu sabida allah Ammiy kina ganin, yanda ya kukkumbura min jiki amma kin kasa yimai magana nifa ina ko kwanto anya ni jininki ce Ammiy a’nya. Babu wani b’o yayyan abu da ban sani ba..!
Kursum ni kike gayawa haka na yarda abinda OMAR yake fad’a ninake sangartaki shiyasa kikeyin abinda kika gadama…
To tunda bani nahaifeki ba saiki nemi wata uwar”
kuka ta kuma fashewa dashi tace nifa ba haka nake nufiba, tome kike nufi ai magana ce kika fad’eta a free ba k’arya akayi miki ba….
Nidai yanxu kigayamai baruwanshi dani yadena dukana yanxu ba da bane. saikace wata jaka yo ko baiwa ce sai haka dukan yau da ban nagobe da ban sabida ba k’aunata yake ba Wlh Ammiy bana sanshi kuma baxan tab’a sanshi nifa jinake kamar na kash….!
Dasauri Ammiy tarufe mata baki kana tace ashe baki da hankali,. Harkike ikirarin kisa to kishiga hankalinki.kindaiji na gaya miki…!
To kiyi gaggawar cire wannan batun aranki sabida gaba karkixo kina cixon yatsa.Kedashi babu wani bam banci duk d’aya kuke agurina. karna k’ara jin wannan maganar aba kinki kai tad’aga mata alamar to,.
Yawa kokefa maxa tashi kishiyar kici abinci kisha magani ko kyaji dadin jikinki, tashi tai tashiga toilet tayo Wanka Ammiy ce ta tai maka mata tashirya kanta..!
Tare suka fito Ammiy ce, taxuba mata abin cin kad’an tasha ta kurb’i ruwan lemo. tasha magani kan kujera 3st ta kwanta tana maida numfashi. baccine ya kwasheta ganin hka yasa Ammiy ta koma d’akinta..
Jin ana,kiran sallar la’asar ne yasashi mik’ewa, yatafi masallahci ana idarwa yadawo. gida a’farlo, ya yada xango. sam bailura da KURSUM datake sharar baccinta hankali kwance kuma da alama tanajin dad’in baccin…..
Wayarsa yazaro daga aljiunsa, yana latsawa” munsharin da yajine yasashi saurin kallan gurin waxe gani inba KURSUM ba wacca ta k’ara bajewa ga yawun bacci na dalala.”
Tsikar jikinsa ce ta tashi dik duniya OMAR yatsani wa innan abubuwan munshari.. k’azanta da kuma yawun barci diddiduniya sune sukafi d’agamai hankali,.
Shiyasa baya iya kwanciya kusadamai irin wannan matsalar Amma fa acewarsa…
Wayarsa ya mayar cikin ajjihunsa yamik’e. yana ta kunsa na k’asaita wanda yaxamemai jiki.. hannunta da yasauka daga kan kujerar yasa k’afa ya murje. Araxane tamik’e tana ihu, sosai ta gigice. Tama rasa ina zata dosa bai barta ba ya kara mata da mari harsau biyu d’if kakeji tadena ihun.. silalewa tayi k’asa sumamma..!
Ammiy dake Cikin d’aki tana laximi. tajiyo ihunta bashiri ta fito tana tambayar ba’asi, maganar ce ta mak’ale, ganinta kwance bata motsi.ga OMAR atsaye yana huci kamar kumurcin maciji…!
Ruwan sanyi ta dakko a’freexa ta kwara mata.ajiyar xuciya tasauke..
Kafin hawaye susoma gan garowa ta gefan idonta.
Ammiy kuwa dik tarud’e tamarasa ta ina zata soma Shikuwa gogan kota kansu bebiba yayi shigewarsa daki yasaki dan yasan yau yab’atawa Ammiy rai yasan a’kwai daru….

Leave a Comment