Hausa Novels

Noor Iman Hausa Novel Complete

🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•

*’Yar mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*01*

Tafiya kawai nakeyi sam ban san inda nake jefa kafana ba bare na kula da hanya, hawaye kawai ke kwaranya daga cikin kurmin idona zuwa kan kumatu na.

Tsananin damuwan da nake ciki be sa na kula da kan hanya na jefa kaina ba seda naji wani wawan bugu yayinda students na arean suka saki salati wasu na ihu, runtse kyawawan idanuna kanana nayi cikin jin zafin bugun tun daga kafana har tsakiyar kwakwalwana amma ko kad’an zafin be kai na zuciyata ba.

A hankali na waiga na kurawa bakar meserati wadda gabad’ayanshi baki ne har glasses d’in ido don ganin ko ze fito ya bani hakuri amma ko motsi kofan motar be yi ba bare ayi alamun bud’ewa.

Mikewa nayi na d’ingisa kafana da nasan yayi mugun buguwa na koma gefe na zauna, wasu na min sannu wasu kuma cewa suke Allah ya kara dama yarinyan kullum tana tafiya kaman mahaukaciya sam bata da hankali a kanta me makon a kaita psychiatric amma an kawo ta nan makaranta ko me zata d’auka oho.

Kuma runtse ido na nayi ba su kad’ai ba duk inda zan gilma sau d’aya sau biyu zasu ce psycho ce ni ba wai dan wai yanayin shigar jikina ba, a’a tsantsar rashin natsuwa da damuwan dake d’auke a yanayina da fuskana ke sa su zaton haka duk da sanyi na a abubuwa dayawa.

Karan wucewar motar da speed shi ya dawo dani daga duniyar tunani na, kafana na riqe da zarazaran yatsotsin hannuna na dinga matsawa har naji dama dama amma na tabbatar akwai matsala jin irin azabar dake shigana.

Agogon dake d’aure a tsintsiyar hannuna na kalla 7:50 ajiyar zuciya na sauke kan na mike na ci gaba da tafiya a hankali Ina d’ingisa kafan na nufi auditorium sbd achan nake da lectures karfe takwas gashi yanzu 7:50.

Ban isa auditorium ba se takwas da kusan mintuna takwas hall d’in tsit kaman anyi ruwa an d’auke a hankali na tura kofan na shiga bakina d’auke da sallaman da iyakarshi pink lips d’ina a hankali na ci gaba da takawa da nufin karasawa ciki In samu wurin zama.

Seda nayi tsakiyar hall d’in kan naji an ce “who the heck did yhu think yhu are!!! Will you get out of my class jor” sam muryanshi bata da hayaniya dukda tsawa yayi ba don microphone da yake amfani da ita ba ko rabin ajin baza su ji tsawar nashi ba bare lectures d’inshi.

Juyawa nayi na mishi kallo d’aya yayinda shi kuwa idonshi ke kan damin lecture note d’in hannunshi.

‘Fa tabarakallahu ahsanul khalki’ na furta akan lips dina ban kara gangancin kallonshi ba na juya na fita a sanyaye still cikin d’ingishi kujeru irin na zaman d’alibai dake gaban hall d’in na samu na zauna Ina sauke ajiyar zuciya.

A rayuwana ban ta’ba ganin namiji me irin kyaunshi a fili ba sede a tv, tv d’inma se tashoshin larabawa ko indiyawa kwata kwata ban san yadda zan fasalta kyaun shi ba sede na san yana da bala’e’en kyau ga fari me d’aukan hankali.

Share tunaninshi nayi sbd damuwana ya fi karfin tunanin kyaun wani halitta, ya zanyi da rayuwana, wai laifin me na aikata da ake hukunta ni da abunda ban san hawanshi ba bare saukanshi? Why always me? A shekaruna na 23 a duniya nayi aure sau hud’u duk ba wadda na mishi kyakyawar wattanni biyar.

Yes inada kyau daidai misali amma kyauna ba me d’aukan hankali bane sbd fata me duhun haske ce dani wato ‘chocolate’ color ba kallo d’aya zakamin ka fahimci kyaun da surar da Allah ya bani ba shiyasa tun ina shekaru sha takwas a duniya samari suka min rutututu kowa so yake ya mallakeni.

Ashe ni kam maza sune kaddarana ganin kullum za’ayi sallama ace ana kiran Noor Iman yasa baba na yanke shawaran In fidda miji ya min aure.

Dukda bana so sbd Ina matukar son karatu kan aure amma ba yadda na iya kasancewata me tsananin biyayya yasa na fidda wani saurayina da ya nace min tun Ina jss class ba ‘bata lokaci a randa na cika sha takwas cib a ranar aka d’aura min aure da bello sede abun takaici a ranar da aka kaini gidanshi a ranar Bello ya dankara min saki har uku ba tare da na san laifi na ba.

Cikin tsananin tashin hankali na dawo gida da safiyar ranan amma se babana da ‘yan uwanshi suka rufu akaina da duka ba tare da sunji ta bakina ba, ba don mama ba ‘yaddiko na, wato kishiyar mahaifiyata’ da inaga ban yi rai ba a ranan.

Bakaken maganganun da na sha ko seda nayi dana sanin zuwa na duniya dayawa suna cewa rashin kai budurcina gidan mijina yasa ya min wannan wulakncin yayinda maganan yayi tasiri akayi ta yad’ata unguwa da ‘yan uwa.

Amma abun takaici ko kallo ban ishi umma na ba, bare sannu ko kuma ta ajiye ni taji damuwa ta hakan yafi komai yimin ciwo a rayuwa ban san daad’in uwa ba, ban san abinda ake cewa uwa ba a kaina kam sede Ina ganin yadda take kula da kannena kaman zata maida su ciki.

Abun na min ciwo fiye da tunanin me tunani, mutuwar aurena na farko yayi sanadiyar tashinmu a rijiyar lemu, muka koma gadon kaya da zama sbd ban isa fita ba haka ‘yan gidanmu, Babana na matukar sona kan faruwan mutuwar aurena na farko, wani irin so yake min da ban san iyakarshi ba.

Sbd tausayin da nake bashi, komai sede kishiyar uwata ta min, tun Ina karama umma ke banzantar da ni wai ita alkunyar ‘yar fari a yadda baba ya fad’amin kenan amma har yau ban yarda ba sbd abun yayi yawa.

Ban san kula ba se a wurin mama, ban san yadda ake shagwa’ba a gaban uwa ba se a gabanta, ban da wadda zan kaiwa kuka na se mama, da farin cikina da bakin cikina duk tare muke rabawa se ince ta fini shiga damuwa akan mace macen aurena.

Hayaniyar d’alibai masu fitowa daga auditorium hall ya tabbatar min da an gama lectures d’in, d’ago idon da zanyi se ya fad’a cikin nashi ko second idonshi be yi a kaina ba ya manna bakin space akan sparkling brown eyes d’inshi tare da nufar motanshi cikin takun isa da kasaita, se a lokacin na gane ashe wadda ya kad’e ni a hanyar shigowata shine lecturer d’inmu na yau.

Kallonshi nake yadda farinshi ke d’aukan ido ga baki wuluk d’in gashin kanshi dake kwance lublub har kasan keyanshi se sheki yakeyi, irin gashinne cike da giranshi haka sune gargasan dake kwance a hannunshi zuwa saman kirjinshi da ya fito kad’an sbd V neck black shirt da ya saka.

Ina mamakin wannan bawan Allahn anya d’an nijeria ne? Bakaken kananan kayan dake sanye a jikinshi ya kara fitar da farin fatarshi, kananan maganganun da d’alibai suka fara akanshi ne yasa ni kauda kaina daga kallonshi na mayar kasa Ina me kokarin sake zundumawa duniyar tunani na naji an zauna gefe na.

A hankali na waiga se naga wata kyakyawar matashiyar yarinyar da tunda na fara zuwa makarantan take yawan ce min sannu bayan ita ban ta’ba magana da wani d’an ajinmu ba, alhalin Ina cikin sati na hud’u kenan da na fara zuwa makarantan ta BUK inda nake karantar B.sc Ed Biology.

“Sunana Zarah Ahmad Malabo and yhu?” Da kyar na iya yi mata yake don murmushi wahala yake min nace “Saudah Hafeez ana kirana Noor Iman”.

*•Assalamu alaikum ‘yan uwa ga fah Gureenjoh da sabuwar littafi hope zaku so shi kaman sauran books d’ina, promise yhu will never regret reading my book, in shaa Allah, comments for more pages•*

 

🖤Gureenjo🖤

🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on Wattpad•

*`yar mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*02*

“Wow nice name, kiyi hakuri fah da abinda Dr. Abdurraheem ya miki haka yake da wulakanci ga dizgi wai shi In har ya shiga aji to ba me shiga a bayanshi, amma ke baki jima da fara zuwa ba ko? Gashi an ci rabin semester na san baki yi catching up wasu abubuwan ba, zan dinga koya miki karki damu daga yau mun zama friends”.

Lord!! Wannan bade surutu ba mutum kaman aku, na raya a raina a fili kuwa murmushi na mata Ina son inyi karatu sossai inga na zama wata a duniyan nan yanzu ban son aure ban son wani magananshi karatu kawai hakan yasa nake son yin kokarin yaki da zuciyata In kuma kau da tasiri da maganan mutane ke min inyi karatu tukuru.

Dama asalina me surutu da kazar kazar ce rayuwa ne ya maida ni miskilar karfi da yaji, kallonta nayi nace “yanzu d’an wannan yaron ne doctor kina nufin ya kammala doctoring degree d’inshi?” Zarah ta ta’be baki kan tace “kwarai kuwa ke abunki da wadda be yi karatu a nigeria ba firrrrrr ya tafi ba wani delay balle strike duk degrees d’inshi a kasar waje yayi kuma daban daban”

Jinjina kai nayi don son kawar da magananshi na ce “Toh yaushe zaki fara koyamin karatun?” Tace “duk sadda muke da interval tsakanin lectures se mu dingayi ko In mun gama da wuri kuma bamu da wani se mu d’an yi kan mu tafi” wannan karon murmushin da na mata tun daga cikin zuciyata ya fito, wara brown eyes d’inta kad’an tayi kan itama ta saki murmushi tace “wow I like your dimple and your wushirya” na kuma yin murmushi nace “nice meeting yhu zarah”.

Tace “same here” hira ta ci gaba damin ni kam se nodding da d’an murmushi tunda na shiga 18 zan iya rantsewa ban ta’ba mintuna biyu ba tare da damuwa ko tunani ba amma gashi yau samun mutum a kusa dani kuma me faran faran ya sani sakewa da ita sossai har na manta da damuwana na wani lokaci.

Eleven nayi muka shiga another lectures na chemistry sossai na maida hankali kuma ba laifi na fahimta don ni d’in ba laifi me d’an kwakwalwa ce.

Karfe d’aya muka fito muna fitowa zarah ta kalleni tace “har anzo d’aukana muje mu sauke ki a gida ko Ina Gandun albasa kike kikace?” Kai na gyad’a mata Ina d’an murmushi nace “nop ke kam yi wucewarki, se in mun had’u gobe” na san irin gulman mutane yanzu a fara rad’e rad’en na fara bin maza ana saukeni a manyan cars dama yanzu ma ban tsira ba.

Ba yadda zarah batayi ba amma naki haka ta tafi ni kuma na ci gaba da takawa a hankali sbd kafana da ya d’an suntuma zuwa lokacin, ban wani ‘bata lokaci ba na tare napep na shige tare da fad’a mishi inda zani.

Bayan mun iso na sallameshi na fara takawa cikin taka tsantsan kaina a kasa kaman kullum daga gefe majilisan ‘yan unguwa ne na samari gaba kad’an kan gidanmu na tsoffi.

Kullum In har zan bi ta wurin na wuce se na zub da kwalla dayake mutuwar aurena har biyu a unguwan na Gandun albasa ne, ‘ka ganta nan ashawon, ta fito yawon karuwanci da sunan makaranta’ runtse ido nayi Ina jin zafin sunan amma daga yanzu nayi alqawarin bazan kara yi musu kuka ba.

Ina jin wani daga ciki yace ‘wai itace me aure auren?’ Wani yace ‘kwarai kuwa aurenta na farko sako ta akayi a daren farko sbd bata kai budurcinta ba’ da sassarfa na karasa wucewa dukda zafin da kafana ke yi, haka zuciyata kaman an saka a tukuban tsire.

Ina isa wurin manyan mutanen na duka har kasa na gaidasu suka amsa ba yabo ba fallasa amma nayi musu farin sani na san ina bada baya za’a dasa maganata dukda ba koyaushe sukeyi yadda zanji ba amma sun hana ‘ya’yansu kap huld’a dani wai zan ‘bata su.

Ina shiga gida hawayen da nake rikewa ya fara gangara umma ta na tsaye jikin igiya tana shanya baba zaune a kan taburma kasan bishiyar umbrella (almond) yana shan iska don ya dena fita majalisa sbd habaice habaice da bakar maganganun da ake ya’ba mishi gashi ya ci alwashin baze ta’ba chanza wani unguwan ba sbd ni, rijiyar lemo da Gadon kaya sun isa.

“Umma barka da gida” da “yauwa” kawai ta amsa ni ba tare da ta ko kalle ni ba, girgiza kai nayi inajin hawayena na karuwa na rasa dalilin kasa sabawa da wannan hali na ummana a shekaruna na 23 a duniya.

Har kasa na duka gefen taburman baba nace “sannu baba Ina yini?” Kau da kaina nayi daga kallon banzan da yake watsa min Ina jin yadda ya ja dogon tsaki, gwiwa a sage na mike na karasa kofan mama nayi sallama daga ciki ta amsa ni tana cewa “lale lale ‘yar albarka barka da dawowa” murmushin yake nayi na karasa parlorn na zauna.

Ikhram da ikhlas dake zaune saman kujera suka ce “sannu da dawowa yaya iman” nace “yauwa” mama ce ta fito tana kallona tace “naga kaman duk kin gaji tashi kije kiyi wanka ki zo ga abinci nan kizo kici” wani yaken nayi Ina mikewa nace “Toh mama na gode” taku d’aya biyu nayi naji ta saki salati tsayawa nayi na san sbd kafana ne itace kad’ai!!

Itace kad’ai a duniyata da zata ganni da damuwa ta magance min, ita ce kad’ai me sona nan duniya haka nima Ina sonta har raina sbd son da take min ban damu da kasancewarta kishiyar uwata ba “na shiga uku Iman me ya samu kafankin?” Na juyo Ina murmushi nace “mama bugewa nayi” tace “ashsha zo muga” wurinta na koma tana gani ta waro ido “maza juya mu fice gidan malam iro ya gyara miki daga gani gurd’ewa ce ko tsagewar kashi”.

Baki na turo Ina shirin mata musu har ta shige d’aki tana fitowa ta sani a gaba muka fice zuwa tsakar gida ta kalli baba tace “malam yarinyarnan Noor Iman ta samu matsala a kafanta bari muje gidan malam iro ya duba mata” bata jira cewar shi ba muka wuce don ta tabbatar ba amsa ze bata ba inde akan maganan da ya shafeni ne kaman yadda nima na san da hakan.

Muna isa ya tabbatar da gocewar kashi ne a rike ni ya gyara da kuka da komai aka gyara mama se mita take wai na cika ragwanci, biyanshi tayi muka fito muka dawo gida ina share hawaye, wanka nayi na shirya cikin riga marar nauyi duk a d’akin mama komai na yake don ban ci darajar a bani d’aki na ni kad’ai kaman sauran ‘yan matan gidan da yanzu suke gidan mazajensu ba.

Ido na a lumshe nake taryo rayuwarmu na baya, Malam Musa Muhammad d’an asalin kauyen wudil ne na nan jahar kano yana da mata d’aya da yara takwas ya jima yana sana’an driver kuma har Allah ya kar’bi rayuwanshi sana’anshi kenan, da Sana’an ya sayi gida anan hayin rigasa suka dawo nan da zama anan cikin kano gabad’aya yaranshi sukayi karatu kasancewarshi me son boko, dukda shi be yi ba, baba shine na hud’u a cikin ‘ya’yanshi yana da kanne hud’u.

Goggo Kamila, goggo saratu, goggo hindatu, se bappa Audu.

Yayyunshi uku duk maza ne bappa Yushe’u, se bappa Mu’azu se bappa sama’ila kan baba, duk mazan sunyi karatu daidai gwargwado iyawar mahaifinsu kan rasuwarshi inda babana yayi diploma d’inshi a fannin mass com, ya auri ummana (Aisha) ne a chan garin malumfashi na nan katsina inda ta kasance ‘ya d’aya tilo a wurin iyayenta batayi wani karatun kirki ba iyayenta suka cireta suka aurar da ita.

A lokacin ya fara aiki a matsayin karamin ma’aikaci a gidan rediyon freedom, suna son junansu don zaman amana da soyayya sukeyi wadda jigonshi ya kasance hakuri, har ummana ta shekara hud’u bata ta’ba koda ‘Batan wata ba, hakan yasa su goggonina da inna mahaifiyar baba suka matsa ya karo aure yaki sam amma se suka fi karfinshi inda ya auri kanwar matar bappa yushe’u.

 

 

🖤Gureenjo🖤

🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo on wattpad•

*’yar mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*03*

Hadiza wato mama kenan, zuwan mama da kwanaki kad’an ciki ya bayyana a jikin ummana sossai baba ya d’auki son duniya ya d’aura akan cikin, su inna kam da suka ji labari se kunyan yadda suka dinga mata ya baibayesu suka dawo suna son cikin suma kaman su janyo ran haihuwanshi.

Kwarai umma ta wahala a wurin haihuwa na har Allah ya sa ta sauka lafiya inda ta sameni ba karamin farin ciki su inna da baba sukayi da hakan ba, har mama kaman zata had’iyeni zan iya cewa son da take min yafi na ummana a ganina fa kenan, aka saka min sunan inna “saudah” yayinda mama ta saka min inkiya “Noor Iman” shekaruna biyu a duniya ummana ta kara haihuwa nan ma mace “hafsa” sunan mahaifiyarta ce bata yarda kuma a boye mata suna ba.

Bayan hafsy da shekaru biyu ta haifi Nafeesah daga ita da shekaru biyu ta samu Al’amin se Ihlam yayinda ikhlas ta kasance auta, har rana yi ta yau mama bata samu haihuwa ba kuma sam bata nuna damuwanta akan hakan tunda ta d’aukemu a matsayin ‘ya’yanta itama karshe ma kyauntana sukutum baba ya bata ganin yadda take kulawa da ni kamar ita ta tsuguna ta haifeni.

Mun girma da son boko kaman yadda baba ya tusa mana ra’ayin kanmu a had’e yake da sauran ‘yan uwana mata yayinda suke tausayamin ganin yadda umma ke nuna halin ko In kula da rayuwana zan iya cewa ban ta’ba mintuna biyu cikakke muna magana da ita ba kwata kwata bata san komai nawa ba.

A haka har na girma nayi wayo maimakon In ji na tsaneta amma sonta da son ta kulani suka shigeni, se in dinga shishige mata tana hantarana watarana har dukana takeyi In na matsa mata da magana In ka shigo gidanmu kaga yadda takemin zaka rantse ‘yar kishiya nake a gareta, ban san daad’in uwa ba sam ban san d’uminta ba, ko d’akinta na shiga se ta korani waje.

Ko kitso takeyiwa kannena In naje bazata min ba dukda kwarewar ta a harkar, se de in zauna daga nesa Ina ganin yadda take wasa da dariya da kannena wani lokacin har ‘buya nake a bakin kofan ta In ta kallonta Ina hawaye, bata ta’ba sakemin fuska ba wadda nake yawan mamakin ‘Anya uwa ce’.

Ina girma suffan jikina na kara bayyana da kyaun da Allah ya bani wadda In ka ganni da ummana kaman photocopy banda kiba haka kuma banda rama jikina a murje yake da kalar fatata me d’aukar hankali sbd a chocolate dinma me tsada ne don haka yawan mutane suke fad’a Ina da dimple guda d’aya a ‘bangaren kumatuna na dama.

Hakwarana farare sol kanana da su daga tsakiya kuma wushiryace me kyau, se madaidaicin hancina da kuma madaidaitan fararen idanuna na, Ina da cikar kirji da kuma hips yayinda gashin kaina ya kasance marar tsawo har chan amma baki sidik ga laushi.

Ina jss 2 maza suka fara layi a kofar gidanmu don Allah yayini da farin jinin samari hakan yasa baba ya sha alwashin aurar dani da na gama secondary dukda yadda yake so nayi karatu don nice ta gaban goshinshi yana son cika min burina na zama babbar lecturer a duniya amma yana shakka yadda ake zuwa mishi da magana na har tsoro yake bashi.

Kaman yadda na fad’a a baya tun jss 2 bello ya fara takuramin da nuna yadda yake sona ya kuma tabbatar min baze iya rayuwa ba ni ba, tun Ina shareshi har na fara sauraranshi, Ina cikin zana jarabawata ta kare secondary baba ya kirani ya tabbatar min ba zan ci gaba da karatu ba ze aurar dani In miji na ya yarda inci gaba so in turo da wadda nakeso.

Ba ‘bata lokaci na gabatar da bello ya ko yi farin ciki sossai kaman ze had’iyeni da aka bashi ni a kuma lokaci kankani, Ina gama neco aka aura min shi, amma kayan takaici a daren ya sakeni ba tare da wani kwakwaran hujja ko dalili ba, wadda hakan yasa baba da sauran ‘yan uwanshi kusa kasheni.

Basuyi la’akari da laifin nawa ne ko ba nawa ba, abunda ya fi yi min zafi kuma son da nakeyiwa bello amma aikin gama ya gama a shekaruna na sha takwas har na zama bazawara, tun baba na had’e min rai bayan dawowanmu gadon kaya, har ya daina ya fara min nasiha a kullum da yadda rayuwa yake da kuma fa’idan zaman aure duk laifina yake gani ba laifin bello ba.

Abun takaicin kuma yawancin nasihanshi na karkatuwa ne ga girman laifin zina wato shima ya yarda da rashin kai budurcina ya sa bello sakina hakan na sani kuka sossai da kunar rai, bayan mutuwar aurena da bello da watanni bakwai na had’u da Ahmad matashin saurayi me ji da kud’i a asibiti muka had’u bamu wani jima muna soyayya ba ya nemi turowa na fad’awa baba ya dinga ci min albarka.

Ba ‘bata lokaci aka yi buki aka d’aura min aure da Ahmad, bayan d’aurin aure angwaye sun kasance suna turowa amarensu sakon jin daad’insu amma ni sakon bakin ciki da takaici Ahmad ya turo min, bayan an watse ya kirani a waya ya ci min mutunci akan ni bazawara ce bamu fad’a mishi ba muka cuce shi ashe ni ‘yar iska ce, wai ashe yawon iskancin da nakeyi yasa mijinan chan ya sakeni.

Nayi kuka har na gaji da wannan sharrin haka aka kaini tunda aka kaini kullum wulakanci har dukana yana yi sede be ta’ba kusantata ba bare ya san gaskiyata na wahala sossai a gidan Ahmad na wata shidda kan ya sakeni na dawo gida, a lokacin hawan jini ya kama baba, kaman aurena na farko har gida su goggo kamila suka zo gabad’ayansu suka lakad’amin na jaki.

******

Ta’bani da mama keyi yasa ni dawowa daga duniyar tunanin da na fad’a “Iman tashi kinyi bacci bakiyi sallahn isha ba gashi har karfe goma, tashi maza kiyi sallah” salati nayi ina mikewa daga kwancen da nake na fad’a bayi, alwala nayi na fito na samu mama ta gama shiryawa zata tafi d’akin baba da yake itace dashi, sallama mukayi ta fita ni kuma nayi sallahna kan na koma gado na kwanta.

Ruri wayana ya fara yana neman agaji a kasalance na sa hannu na d’aga, Haka kawai wani lokacin se in manta Ina da waya sbd ba me kirana en uwana se na kirasu sbd duk haushina sukeji har gwara hafsy amma sauran kannena da sukayi aure ba me kirana haka goggonina ko na kirasu ba d’agawa sukeyi ba, na rasa kaddarannan kam ni na d’aurawa kaina ko ko Allah ne ya d’auramin.

Sake shigowar call wayana ya dawo dani daga tunanin da na fad’a da sauri na d’aga “salamu Alaikum” na furta cikin sanyin murya, murmushi na saki jin muryan zarah tana cewa “Amma baki da mutunci Noor Iman yanzu bakiyi saving number na ba? Don daga jin yadda kikayi sallaman nan baki san who’s in the line ba” cikin murmushi nace “sorry zarah, wallahi shap na mance banyi saving ba amma karki damu yanzunnan zanyi”.

“Ni de Allah nayi fushi tun fah d’azu nayi saving numbernki da my besty amma ke bakiyi ba” cikin mamakin halin sangarci irin na zarah nace “amma ke zarah ‘yar autace ko?” Tace “yes Anty Rumah, ya Abdul, ya hafeez, Anty kalthum duk auta suke ce min har ummu da Abbu” na lura zarah yarinyace don na tabbatar zan bata akallah shakaru hud’u zuwa biyar amma zan d’auketa kawa don tana da daad’in zama kuma ma ni ta fini kiba da tsawo don duguwace sossai ba kaman ni da nake tsaka tsaki ba.

Itama na tabbatar da ta san asalin shekaruna sede ta fara kirana da Anty, ga aurarrakin da nayi, “Lallai auta nima haka zan dinga ce miki” I bet ta turo baki kan Tace “ni de bazan yarda ba sede my besty” nace “ohkey besty duk yadda kikeso haka za’ayi” “ke gobe fah muna da lectures d’in Dr. Abdulraheem kuma 8, dan Allah kizo da wuri karki yi letting ya koreki” cikin sanyin jiki nace “Ohk dear in shaa Allah se mun had’u, bari na zo na kwanta”. Sallama mukayi na kwanta bacci.

 

🖤Gureenjo🖤

🥀NOOR IMAN🥀

*Fatima Muhammad Gurin*
•Gureenjo6763 on wattpad•

*’yar mutan Adamawa*

💫ANNUR WRITERS ASSOCIATION
(Home of peace, honor, charity and super writers)

*04*

A Karo na biyu na kuma dunfaro class d’inshi 6mins past eight, dayake ban samu bacci cikin dare sossai ba sbd period pain da nayi fama da shi ban samu salama ba seda jinin yazo gabannin asuba kan nayi bacci.

Bani na farka ba se karfe bakwai, kan nayi wanka na shirya na taho takwas da mintuna shidda, zuciyata na dukan tara tara sede banjin zan iya komawa da baya sbd bana son samun matsala da course d’inshi sam gashi yanzu attendance na biyu ke shirin wuceni.

Nannauyar ajiyar zuciya na sauke kan na tura kofan a hankali na sa kai, muryanshi dake tashi a hankali cikin sanyin da yake naturally ne ya doki dodon kunnena wadda har seda naji faduwar gaba da na rasa dalili, ba tare da na kalli inda yake ba na nufi karasawa cikin ajin sede ko taku biyu ban yi ba na ji shi yana cewa.

“Hey yhu!!!! Get out of my class” ‘Dago eyeballs dina nayi da niyyar bashi hakuri amma me? Bakina kwata kwata yaki bani had’in kai wurin motsashi har muryan ya fito, sbd hardewa da idanunmu yayi cikin na juna.

Wani irin disgusting look yake jifana dashi da ya sa ba shiri na juya na fice jikina na tsananta rawa, Ina jin tsakinshi cikin microphone kan ya ci gaba da bayanin cikin natsatsiyar muryarshi me tafiyar da hankalin me saurare.

Wuri na samu na buga tagumi cike da jimamin sake makara a class d’in bawan Allahn nan Dr. Abdulraheem kaman yadda zarah ta ambaci sunanshi, ina nan zaune har ya gama lecturing ya fito kaman jiya yau ma bakaken kananan kaya ne a jikinshi ko don ya san suna mishi kyau ne yasa yake sakawa? Oho, idona na kanshi har ya bud’e wata Mercedes benz ya shige itama baka yaja da gudu kaman de jiya ya fice.

Ajiyar zuciya na sauke tare da kauda kaina daga hanyar da motar ta bi jin hannu a kafad’ana, kallon me hannun nayi murmushi na saki ganin zarah, fuskantan nan a turbune kaman zatayi kuka cikin dariya nace “lafiya autan ummu?” Kara turo baki tayi tace “yhu know what yhu did is not fair right? Me yasa kika zo late plz, wallahi dr. Abdul cewa yayi In baka da 75 percent attendance d’inshi you will not sit for his exams”

Matsa mata nayi ta zauna Ina me sauke ajiyar zuciya nace “In shaa Allahu bazan kara ba, yau ma da dalilin hakan” girgiza kai tayi tare da cewa “and in kin san kinyi late karki dinga shiga wallahi it hurts to see him humiliating yhu In public ba mutunci ne dashi ba” girgiza kai kawai nayi shiru ya d’an ratsa kan nace “tashi muje mosque mu d’an yi karatu tunda se 2 muke da wani lectures din”.

Mikewa tayi muka fara tafiya muna ‘yar hira har muka isa masallaci daga chan baya muka zauna muka baje handouts na chemistry ta fara koyamin duk abinda ban gane ba, ba mu muka motsa daga nan ba se karfe d’aya muka yi sallah muka fito zuwa cafeteria abinci muka ci wadda zarah ce ta biya kud’in duk da yadda nayi kokarin hanata.

Multipurpose muka nufa mukayi education 2-4 wadda sossai na fahimta kuma lectures din ya min daad’i har nake jin nan gaba karatun ze iya d’aukemin duk wata damuwana, “muje muyi sallah kan azo d’aukanki ko?” Na fad’a Ina kallon zarah dake chatting a wayanta kirar iphone 11pro ba tare da ta kalleni ba tace “yes sure, kin san kanon nan in yamma tayi holdup d’in bala’i ne da ita kan ka isa gida past five”.

Murmushi kawai nayi ina mamakin surutun zarah Abu d’aya zaka tambayeta amma ta baka amsa sama da ashirin, a natse muke takawa musamman zarah ‘yar gayu da tafiyarta ma kad’ai abun kallo ne, ga shiganta ba wai me nuna tsiraici ba a’a kawai de da ka kalleta zaka san daga gidan arziki ta fito hutu ne ko ta Ina a jikinta.

Kallon jikina nayi ba laifi sanye nake da material doguwar riga da bakin hijab da bakin takalmi se bakin agogo da d’an side bag d’ina, daidai gwargwadon talaka me madaidaicin karfi, na san mutane zasuyi ta zagina da zund’en na makalewa ‘yar masu kud’i wasu dayawa suna son kawance da zarah amma na kula ko ta kansu bata bi.

Bayan munyi sallah mun fito muka nufi hanyar barin school din tun kan mu shiga ta kira driver d’inta akan yazo ya d’auketa hakan yasa bamuyi wani nisa ba muka hangi motar wadda ni ban ma gane ba dayake ba da shi aka zo d’aukanta jiya ba, yau ma tayi tayi dani In shiga su saukeni naki har fushi tayi ta tafi.

Hmm zarah kenan da kin san irin maganan da shiga motar gidanku ze jamin da baki fara min tayi ba, na raya a raina Ina tarar machine da yazo wucewa ciniki mukayi dashi kan na d’ane yaja muka tafi.

*****

“Amincin Allah da yardarshi su tabbata akanki yake ma’abociyar kyau da kwarjini” dakatawa daga saurin da nake nayi ba tare da na juyo ba har seda me maganan ya sha gabana ya tsaya ajiyar zuciya na sauke ina me d’auke idanuna daga kan kamilalliyar fuskan shi, “Baki amsa ba ranki shi dad’e” a hankali na ce “Wa’alaikassalam warahmatullah”.

“Yauwa ranki shi dade….” “Noor Iman” wara ido yayi kan yace “masha Allah suna me daad’i, kar na ‘bata miki lokaci gashi na tsaidake a titi na san ba mutuncinki bane amma ba yadda na iya ne” ajiyar zuciya ya sauke yana tuna irin maganganun da aka gayamishi akanta tunda ya fara zuwar ma abokinshi da zancen yana son yarinyar.

“Sunana Hamza Noor Ina sonki, so na tsakani da Allah kuma aurenki nake son inyi” hawaye ne ya ciko idona tun bayan barina gidan Ahmad ba wani namijin da ya ta’ba tarana da sunan so se hamza sbd wani irin bakin fenti da jama’a suka shafamin ba tare da sun san kaddara bane kuma yana kan kowa, “aurena biyu, ni bazawara ce” ga mamakina murmushi naga yayi yace “ko menene kike ni Ina sonki kuma zan aureki ba wadda ze iya hanani se Allah se kuma idan baki sona sarauniya”.

Murmushi nayi kan na ce “ni ban ce ba, Allah ya za’ba mana abinda yafi alkhairi” cikin jin daad’i Hamza yayimin godiya yayinda ya rakoni har gida don dama na shigo layinmu, soyayya me tsafta ce ta shiga tsakaninmu da hamza dukda irin maganganun da ake gayamishi a kaina ya toshe kunnuwanshi iyayenshi kuma masu fahimta sam basu nuna kina ba se adu’ar Allah ya tabbatar da alkhairi.

Matarshi da kannenshi ne suka so tada fitina amma dashike ya isa da gidanshi da kuma kannenshi abin beyi nisa ba, iyayenmu sun gana inda baba ya kuma tabbatar musu aurena biyu sun nuna sun sani aka sanya mana rana, kullu yaumin baba ze ajiyeni yamin fad’a sossai akan wannan aure da yake ta gabatawa In har na kashe to wallahi sede In nemi wani uban ba shi ba.

Har na gaji da jin wannan kalaman nashi, na san kaddara ni ko shi ba wanda ya isa hana Allah abinda yaso In har rubuttacce ne a cikin shafin kaddarana, wasa wasa lokaci ya matso inda walima kawai nayi shima don tirsasawar hamza, rana bata karya a ranar 17 ga watan d’aya 2019 aka d’aura aurena da hamza da karfe goma na safe, a kuma lokacin Allah ya kar’bi ran Hamza bayan an gama shafa fatiha.

Mutuwar da yamin ciwo fiye da komai a duniya nayi kuka har kaman raina ze fita sede ba yadda na iya ba iya dawo dashi zanyi ba, har abada bana jin zan manta wannan rana zan kuma manta wannan rashi na mijina me kaunata tsakani da Allah, se namijin kwarai ne irin Hamza ze iya jurar irin maganganun dake yawo a kaina ya toshe kunne yace duk duniya se ni.

Nan kam ba yadda baba da ‘yan uwanshi suka iya tunda mutuwane amma fah maganganun mutane na watakila Ina da miji cikin jinsin aljannu ya fara tasiri akansu sbd abun akwai d’aure kai, nide nawa adu’a na tabbatar ba wani aljannin da ya aureni kawai de haka Allah ya tsara mini, bayan wata da mutuwan Hamza su goggo hindatu suka fara kawo min magani da wasu jike jike wai na kariya duk suka nan ba sha nakeyi ba sede In ajiye mama ma sam bata goyi bayan In sha ba suna tafiya zata tayani zubarwa.

Ummana!!! Hmmm umma bata ta’ba nuna ko digon damuwanta akan lamarina ba hakan yasa na lalace na kara fad’awa, Ina rayuwane cikin duhun kai dukda na san mama na sona amma akwai abubuwan da se uwa ce kad’ai zata iya ma d’anta zan iya cewa ko azkar wannan banayi iyakacina lokacin da nake zuwa islamiyya In naje nayi karatun qur’ani achan ban sake bud’ewa se kuma In na sake zuwa yanzu da na bar islamiyyar ma se ayi sati biyu ban bud’e alqur’ani da sunan karantawa ba.

********

“Malama!!! Baiwar Allah!! Baiwar Allah!” Firgigit nayi na dawo daga duniyar tunanin da na fad’a ashe ma mun iso tuntuni yayi magana har ya gaji hankalina be kanshi se hawaye wasu samari ne suka tayashi dawo dani cikin tunani na, sauka nayi nace “kayi hakuri baba” don babba ne me acha’ban murmushi yayi yace “ba komai d’iyata ki dinga kokarin boye damuwarki duk wani tsanani yana tare da sauki komai maganinshi Allah, ki dinga kaiwa Allah kukanki kinji?”.

Gyad’a kai nayi Ina mika mishi kud’in shi “In shaa Allahu na gode” da sauri ya girgiza kai “barshi ‘yar nan je ki Allah ya kawo miki mafita” nace “Ameen Ameen na gode Allah ya saka maka da alkhairi” jan machine d’inshi yayi ni kuma na tsallaka kan na juya kuma ban hangeshi ba ko da gilmawanshi, ban damu ba na nausa cikin layinmu.

 

Leave a Comment