*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[01]
……..”Goje ka saka mana menene haka wai?”
Uwaisu ya faɗa cike da jumuɗin yanda cacar yauɗin ke shiga masa zuciya.
Dular da take bakinsa ya kawar mai kauri anyi mata naɗin manya,banda tashin hayaƙi babu abinda yake,ga wata hula zungureriyah a kansa,ta fita daga cikin hayyacinta saboda bala’in dauɗar da tayi sosai. Gashin bakinsa duguza duguza kamar gazagi.
Cikin shaƙaƙƙiyar murya yafara magana,kana jinsa kaji tantiri ɗiban fari.
“Tsoho shin kana nan akan bakarka zakayi cacah dani,kasan fah ba’a wanyewa lafiyah,sannan idan nayi nasara ko ranka ne billahillaxi saika bani shi,babu abinda ya dameni,naga kuma da alama ko ƙwandala baka maganinta a jikinka”
Hantar cikin Uwaisu ta kaɗa da maganar goje,amma kuma ta wani bangaren yanajin ƙamshin samun nasara,musamman ganin yanda yataralakato asa iri ɗaya a hannunsa,gashi kuma bugu da ƙari goje yasaka shanunsa dayake kiwo jingina,idan ya cinye wasannan yana da shanu fah kenan sukutum.
Goce hular kansa yayi gefe ɗaya tareda gyara zama akan buzun buga cacar,mutane maza da mata ƴan duniya suna zaune kowa na harkar gabansa a wajen.
“Hhhhhh goje kenan ai tunda nake bantaba fara caca na tashi banƙare ba,ko a cini kona ci bana bata baya,gaba na bata bana tsoro kota mutu kokuma tayi rai,ai ninan uwaisu ɗan marka,dan caca muke rayuwa,caca da rufamana kuma da yaye mana bargon asiri,anci mana mutunci kuma an yabemu,a cikinta muka buɗi ido tun kai yana baƙi,gashi har yayi furfura bamu dainaba,dan haka babu jada baya shiga wasa yaro”
Uwaisu yagama faɗa cikeda gadara da kuma yarda da kai,abokinsa Manga sai kirari yake masa.
Shafa ƙeya goje yayi tareda rishe ido yana dariyar gefen baki,kana ganinsa kam kasan yaci dubu sai ceto.
Fara zarar katin yayi yana ajiyewa ɗaya bayan ɗaya har yagama ajiyesu a gaban uwaisu,babu musu kana kuma babu tada jijiyar wuya,kowa yaga wasan indai ya iya wasan yasan goje ya cinye wasan.
Fitar da kwarkwaron wiwi ɗin bakinsa yayi kana ya miƙawa uwaisu dafaffafen hannunsa gabansa.
“Tsoho rai kokuma dukiya,cikin ɗaya dole zaka bada ɗaya yanzunnan bakuma sai anjima ba,dan haka saika hanzarta”
Rawa jikin uwaisu yafara tamkar an jona masa lantarki,don ko ba’a faɗamasa ba daga ganin soyayyun idanun goje toh fah bazai taba haƙura ba sam.
Juyawa yayi ya kalli manga dayake gefensa,suna haɗa ido manga ya kalli wani gefen tamkar bai san Uwaisu na wajen ba.
Bai sare ba dai cikin razananniyar murya ya tambayi Manga.
“Manga yaka juya,domin Allah idan kanaga kuɗi a wajenka ka Taimakamin dashi,zan baka idan mukaje gida”
“Kai kaji wani zance a wajen Uwaisu inada kuɗinne zaka ganni anan ina hamma kaman wani ɗan tsuntsu,sanin kanka ne a gabanka dai wancan satin nasaka injinnawa a caca aka cinyeshi,yanzu bana cass bana ass sai Ladi tagama abincin sana’arta take zubamin bayan tagama yimin tujara.”
Duk maganar da suke goje yana jinsu bai motsaba,kana kuma bai ɗauke hannunsa daga miƙashi da yayi ba.
In ran uwaisu ana ganinsa toda kuwa ya sau fitsari a lokacin,gaba ɗaya tunaninsa ya kulle,shin a ina zai samo kuɗi yabawa goje.
“Hehehe tsoho kenan,dan kaga ina maka dariya koh,to aradu da kake gani nan ba mutuncine dani ba,ko ka bani kuɗina kwatankwacin kuɗin saniyar dana saka,wato dubu ɗari da hamsin,kokuma na tale ka nan wajen na sutale maka fatar jikinka,kuma banga ɗan matar da zai iya hanani ba kaf garinnan,in kuma kana ganin wasa nake kada ka fito da kuɗinnan yanzunnan”
Shuru uwaisu yayi yana muzurai,sai lalleƙawa yake yana rarraba ido ko zaiga wanda zai kwaceshi a hannun goje,amma babu alamar akwai wanda ya kulada mai suke a wajen.
“Wa kake kallo zatonka akwai mai ƙwatarka a wajennan ne heee,kanama bata lokacinka ne sannan kuma kai baka san dokar kuɗina ba ma,duk bayan minti uku idan ya ƙara toh zan ƙara dubu ɗaya akai,dan haka zaka bani kuɗina ko saina cire maka yatsu tukunna”
Yafaɗa yana ciro wata wuƙa ƙugunsa mai kaifi,har wani lashe baki yake kaman maye yaga nama.
Caraf ya canfki hannun Uwaisu yana shirin cire masa yatsu,wani ihu ya kurma tareda fara dadare,dama gashi da ƴar kibarsa ba ramamme bane kaman gojen,amma yanda ya riƙeshi yakasa kwacewa kasan goje bakaramin bushashshen ƙashi ne dashi ba.
“Wayyo wayyo do Allah ka ƙyaleni wlh zan baka kuɗinka amma kada ka ciremin hannaye,kafadamin bayan kuɗi mai kake so zan baka ka rufamin asiri”
Magana yake yana kururuwa mutane har an fara taruwa,amma kaman kurma yana nan rikeda hannun uwaisu,har yafara saka masa kaifi a hannun na wuƙa,dan dagaske yake haiƙan sai ya yanki hanunnan.
Taruwa akayi wasu na jan goje wasu kuma suna jan uwaisu daga hannunsa,banda huci babu abinda yake yana sake riƙo uwaisu,idanuwansa sun kaɗan sunyi jawur.
Ranar Uwaisu yaga hairazin kam,don yahada gumi shirkif ta ciki.
Cikin shaƙewar murya na mai taurin kai goje ya yunƙura tareda watsar da mutanen dake riƙe dashi,wawuro uwaisu yayi a karo na biyu tareda cewa.
“Ohh zatonku ina wasane,to duk wanda yafasa rabamun ma ya goya kura ba wando a cikinku,kuma duk mai son uwarsa da haifi wani kokuma ya kwana da pillown ƙasa bana matarsa ba to ya sake zuwa zai rabamu da wannan tsohon najadun”
Yana maganarne yana nuna dukkan mutanen wajen ɗaya bayan ɗaya da wuƙar hannunsa,ɗaya hannun kuma ya riƙe uwaisu camau baya ko motsin kirki,ko ya akayi ma yasamu wannan masifaffen ƙarfin oho.
“Kaikuma shin zaka bani ƙudina kokuma na karbi ranka yan………”
“Tsaya tsaya na baka ƴa ta Sumaimah a matsayin kuɗinka, dan Allah to ka ƙyaleni”
Shuru goje yayi yana zare ido kaman mai nazari,mutanen wajen sunyi mamaki da kuma sakarci irinna uwaisu,wanne irin abune zaisa uba ya dauki ƴar sukutum mai lafiya da kuma hankali yabawa mutum irin goje,hakan ma bata hanyar dadai ba wai fansar kansa yayi da ita a wajen caca. Saidai kuma ta wani wajen hankalinsu zai kwanta,dan da alama goje zai ƙyaleshi da ransa.
Bayan yagama nazarin ɗagowa yayi da sauri kaman zaucacce tareda sake kallon uwaisun,saikuma ya buɗe baki yana jijjiga kai.
“Kai shashasha ka maidani dan kaga ina shaye shaye,a tunaninka ni marar hankaline,taya ƴarka zata fanshi saniyata buleliya da ita ta kiwatu,ina kaita kasuwa kuɗi za’a bani,ƴar ka fah uban wa zai siyeta idan na karbeta,ko sadaki da masu aure ke bayarwa ma dubu ishirinne,saboda ka maidani bunsuru bari ka hadani da mace koh,na maka kama da wanda yahaɗa hulɗa da mata iyeee”
Wannan karon uwaisu kasa magana yayi,sai mutanen wajenne sukayi ta maza.
“Haba goje ba girmanka bane haka ai,tunda har yace zai auramaka ƴarsa a maimakon kuɗinka kayi haƙuri mana,ai mutum yafi kuɗi koh,kaga tunda innarka tafara tsufa basai tana yimuku girki bah?”
Wani a cikin mutanen wajen yafaɗa ta sigar lallashi,da alama kuma hakan yafara tasiri akan sa,dan yaɗan saki wuyan uwaisun ba kaman ɗazu ba.
“Ehh kuma mutum kace wani abun,dama inna kuwa ƙafafunta suna ciwo,bata gama mana tuwo da wuri mutum sai yunwa taci ta cinye masa,saita samu mai mana girki,nizan wuce madakatarmu daga nan,ku wanketa ku kaita gidannamu gobe,idan kuma kasake wata rigimar tasake haɗamu…..hmmmm feɗeka zanyi na bawa su durwa,tsohon banza kawai,gobe ma kasake kasadar shiga caca babu kuɗi,idan ita sa’ar wasanka ce,gajaman kawai”
Haka yagama yiwa Uwaisu tass yashuri wasu takalmin fatarsa yabar wajen yana bobboƙarewa kaman wani mutumin itace. Sudai kowa na wajen ajiyar zuciya yayi,komai yasaka Uwaisu ma yin caca da wannan oho,mutumin da sai yayi wata churr a jeji ba’a ganshi ba idan suka iyo sata ko fashi.
Kowa a wajen masu cewa Allah yakara sunfi yawa,yayinda wasu kuma tausayin Sumaimah sukeyi,baiwar Allah tana ganin rayuwa ta wani irin uba da Allah yahaɗasu dashi,abin takaicin dama sauran yaranne aka bawa gojen da sauƙi,amma Sumaimah ya mahaifiyarta zataji,ita kadai ce kaff cikin yayansa ta fitada zakkah na hankali. Kodan yasan ita ba uwarta a gidan,in badan haka ba taya zai fara wannan abun.
Bagazan bagazan babu kunya bare nadama Uwaisu ya shuri shima nasa takalman yana baza uwar riga yayi hanyar gida,lokacin cin abinci yayi,zaije duk wacce takeda girki tagama yimasa tujara ta zuba masa.
_***_
Leƙawa tayi ganin yamma tayi sosai yasa tafara tattara robobinta na abincinta duk da kuwa bata siyar ba da sauran, dama hakan yakasance al’adar ta ne,bata yarda koda wasa tayi dare a wajen siyarda abincin,yau shakararta ɗaya kenan da fara tallen,tunda akayi auren ƙanwarta Shaheedah itace takeyi yanzu,lokacin da tanaji tana gani tabar karatunta tafara talle tayi kuka sosai da sosai,saidai kuma shin ya zatayi ne,idan bataje tallenba wanene zai bata abinci taci a gidan,ammi ce dama kaff cikin matar mai ɗan dama dama,itace kuma take riƙe da ita,taji daɗi ma da bata gaji da ita ba ai. Sa’arta ɗaya bata tsangwamarta amma kuma bata sakata a zuciyarta kaman sauran ƴaƴan nata. Hmmm wannan jinkirin aurennata yana damunta sosai.
A yanda aka san yanayin dai wacce taƙi kama kanta itace bata auruwa,amma ita kuma anata kaddarar kama kanta da tayi tafita zakkah a cikin gidannasu shine ya hanata auruwa.
Sallama tayiwa abokan tallennata wanda sukam yanzu ma suka fara siyarda abincin,dukkan su ƙannen bayanta ne sosai da sosai. Saboda kowa cewa yake ta rako mata tayi kwantai,amma kuma tasan hakan baya wuce nasaba da tuggun dasu inna lami ke yimata a gida,kasancewar tafi sauran yaransu kyau da kuma soyuwa a wajen kakarsu wacce ta rasu waccar shekarar.
Tafiya take da tunani fal a ranta,haka kawai takejin faɗuwar gaba wacce tarasa dalilin faruwar hakan. Botikin shinkafane akan ta saikuma na miya hannunta ɗaya,gefen kunkiminta kuma ta saƙale bahon data zuba plate da cokala a ciki.
Tazo daidai saitin anguwarsu taji yara sunayi mata magana,amma kuma yafi kama da tsokana,tohh ita kuma ba mahaukaciya ba kai yakawo haka,ko duk rashin aurennata da wuri ne yazamo haka.
Waiwayawa tayi ta kallesu,ba wasu yara bane ƙanana da hankalinsu sarai.
“Yee ga matar goje nan tadawo,ohh kowa yaki aurenta sai goje,shima biyansa kuɗin cacarsa akayi da ita wooo”
Gabanta ne yayi dummm,wannan karon har yafi wanda takeji ɗazu,duk da bazata ce ta gaskata maganar tasu ba,amma kuma tasan hakan abune da zai iyah faruwa,tunda ita kanta tasan halin ubannata,babu wanda bai masa shedar caca ba,hattah kayan ɗakunan iyayensu duk ya ƙararsu a cacah,sunyi kukan sunyi bakin cikin harsun gaji,babu ma ya ita Kaman duk abin ya fi damunta.
Cikin sanyin jiki kaman babu laka a jikinta taahiga zauren gidannsu,gidane na iyaye da kakannu mai ɗauke da ƙofofi da dama,dan su kansu ma sunkusa su talatin yayan vabannasu,banda ƙannen babanta da kuma ƙannensa da kofofinsu.
A gidannsu akwai tsakar gida mai matsakaicin faɗi,duk anan kowa ke fitowa dashi da yaransa yayi harkarsa.
Tana shiga gidan da idanuwa barkatai tayi arba dukka sun watso mata shi,kana gani dai kasan wani abun tabbas yafaru ko kuma yana faruwa.
Sauƙe idanuwanta tayi tai ta maza ta wuce ta gabannsu zuwa ƙofarsu,dan tunda taga dukkan matan a wajen iya amminta ce bata nan,kuma dama itace mace ɗaya a gidan da bata shiga harkar mutanen gidan sosai,badan bataso ba saidan hakan ba halinta bane.tasan duk yanda akayi tana ɗakinta dan haka can ta nufah. Tanajin ƙananan maganganu a cikin kunnenta daga bakunan ayarin matan wajen,amma tayi saurin toshesu a cikin kunnenta,dan a halin da takeji batada ƙwarin wannan zuciyar najin abinda suke faɗa ba yanzu badai tukun ko zataji ma.
Babu kowa a ƙofar tasu,dan haka kai tsaye ta ajiye shirgin hannunta ta nufi ɗakinnasu.
A durƙushe tasamu durƙushe ta ammin ta kifah kanta akan katifar da ita kaɗai ta rage a cikin ɗakin.
Ko ba’a faɗawa mutum ba yasan kuka takeyi na takaici da kuma baƙinciki.
Cikin rawar murya da duk wanda yajita yasan saida akayi jarumta wajen furtata Sumaimah tayi sallama a bakin ɗakin.
Saurin ɗagowa Ammi tayi tareda goge hawayen idanuwanta ta kalli Sumaimah ɗin.
“Ohh har kindawo ne”
Ɗaga mata kai tayi kafin itama ta jefeta da tata tambayar.
“Am…mmi ddd….dagskene baba ya badani ga goje a wajen cacah?”
Shuru ammi tayi tareda runtse idonta,shin taya zata bata wannan zazzafar amsar tayaya? Saidai kuma hakane dagaskene bazata iya cemata ba haka bane,dukda kuwa abinda zuciyarta keson faɗa kenan.
Ɗaga mata kai tayi tareda saurin kawar da kanta,dan a yanda takeji duk da ba ita ta aikatawa Sumaimah hakan ba kunyar haɗa ido da ita takeji, ji take da tanada iko to zatayi koma menene wajen ganin hakan bata faru ba,saidai wacece ita,tayi magana a goranta mata kan cewar ƴar tace,kawai dan ta reneta.
Shuru Sumaimah tayi itama tana nata tunanin.
Wani abin ma Ita data kame kanta daga dukkan munanan ɗabi’u,yanda dan iska bazaizo yace yana sonta ba,to shikuma ɗan kirki koda yana sonta bazaizo ba saboda halayyar mahaifinta da kuma gidansu da bana mutunci ba. Wannan sai taji ma da kwanda tunda ta amince da wani sakaran ba wannan dodon da ake shirin ƙulla rayuwarta da tasa ba.
Siraran hawayene suka zubo daga kuncinta,bata taresu ba bata kuma tsaida su ba,barsu tayi lokacin su ne suyi ta zuba kawai dan in akwai wata ƙofar ma da wani hawayen zai zubo da ta barshi ya zubo……..
“Kiyi haƙuri kawai Sumaimah,hakika banji daɗin abinda ya aikata ba,amma kuma banida tacewa akan hakan,dan har yanzu ma ni ban ganshi ba bare yamin bayanin abinda ya aikata,saboda yasan banida matsayin da dole saina sani ne inaga. Kije madafa abincinki yana can,barina yi sallah.
Kashh akan zamu dagata a sabon littafin na sanadin cacah…. Ya kukaji to kuna so?
Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
09035784150
VTU ta nan
2347068390570
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
—————————————————-
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[02]
Duk da cewar tabi zancen ammin ta tashi ta ɗauko abincin,ta daɗe tana rike dashi bata ajiye ba ballantana kuma tafara ci.
Haɗa ido sukayi da ammi wacce ta idar da sallah,itama ita take kallo. Maganar bata wuce ba koda yake sannan aka fara,maganganun da suke yimata yawo akai tafara fitarwa.
“Ammi amma meyasa baba zaimin haka,yanzu duk abinda yakeyi bai isaba sai ya wargaza rayuwata,meyasa saini ammi uhm. Kinsan kuwa ma wanene gojen koda yake waye kaf garinnan bai sanshi ba ma. Ammi kaman mahaukaci fah yake in kika ganshi,wlh ko lungun danaga yabi bana bi saboda tsoronsa,shine fah ya yankawa Ubaidu kafaɗa suna faɗan daba,ku…..kuma yanzu ace da wanann zan zauna a matsayin miji?”
Kuka ta rushe dashi tareda gyara zamanta a tsakar ɗakin,ta dade danayi ammi bata hanata ba,ina takeda ƙwarin gwiwar hanata kuka,itama kanta kukan take toh.
“Ammi wlh kasheni zayyi in kuka kaini wajensa,wayyo nikam tawa ta ƙare wlh dana sani ba dana amince da Bashir dayazo neman aurena wansan shekarar,duk tsiya gwanda mai neman mata da mahaukaci wlh,wanda a kowanne lokaci zai iya kasheka”
Hannunta Ammi ta jawo ta rike cikin nata,saida ta tattara nutsuwarta kafin tafara cewa.
“Kiyi shuru haka Sumaimah,Inshaallah bazai kasheki ba,Allah ma zai kawo rabuwarku dashi kina zaune,dan kame kanki da kikayi da kuma Addu’arki bazata sauƙa kasi a banza ba,dan haka ki kwantar da hankalinki kinji.”
Suna nan zaune Uwaisu ya shigo ƙofar tareda bankaɗa kyauren ɗakin,rarraba ido yafarayi akan su kamar marar gaskiya,ganin basu ɗaga ido sun kalleshi ba yasa yace.
“Ke amminki ta faɗamiki mai yake faruwa koh,da gobe zanmiki aure tunda ƙinki kawo miji,amma yanzu shi yaron innarsa tace a bari sai wani satin,dan haka ki shirya nan da wani satin zan miki aure”
Cikin ɗaga murya da borin kunya yake maganar,daga ammi har Sumaimah babu wanda ya tanka masa har yayi ya gama.
Har ya saki labulen sai kuma yaƙara buɗewa.
“Yawwa Ammin yara ni akwai abincinnan ne,ɗazu ina waje naga Sumaimah tashigo da botikin da sauran abinci bata sayar ba to koh…….”
“Babu na yara ne,yau banyi dakai ba”
Tafaɗa a daƙile cikin fushi,duk da Sumaimah ba ƴar ta bace amma abin yabata haushi sosai,duk abinda akewa Sumaimah a gidan bai wani dameta sosai ba indai ba ƴaƴanta aka taba ba,amma kuma na yau ya ƙona mata rai,musamman yanda tasan ƙoƙarinta da kuma son iliminta,yanzu duk yatashi a banza saboda rayuwar daza’a jefata.
Ita kanta Sumaimah abin yaso bata mamaki yanda ammin ta tsaya mata a wanann karon,kuma hakan yamata daɗi sosai,yau dai kam taji tanada uwa,duk da dama ba mugunta take mata ba tun tana ƙarama.
“Kaman ya yau babu nawa,wai dan wannan abin daya faru ne,laifina kika gani a ciki,so kike na barshi ya kasheni bayan inada abin bayarwa,ko kin manta ƴa tace kuma ikona ce,duk kiwonta danayi tayi a gidan menene amfaninsa in bazata yimin rana ba uhm”
“Kiwonta,harkana da bakin cewa kai kayi kiwonta ma,to naji ikonka ce bance kuma ba ikonka bace,in abinda mutum yakeyi daɗine ya cigaba dayi maza,batun abinci kuma nima ikona ne shi,sannan kuma wanda naga dama zan baiwa ina ko”
Daga yanda yaga take magana yasan ranta ya baci da abinda yayi,tabb inaga kuma ƴar ta yabayar,yasan ma bai isaba ai,Sumaimah dai itace karkatacciyar kukar tasa mai daɗin hawa.
Sakin labulen yayi yai waje yana kumbure kumbure kaman wani zaki.
Dama daga masallaci ya nufi cikin gidan,daga nan kuwa majalisarsu kai tsaye ya wuce.
Sallama yayi zauna a kusada Manga aka fara taɗin duniyah.
“Yadai Baban amarya naga kana tsuka”
“Uhm kaidai bari kawai,Deejah(ammi)ce ta ɗauremin fuska tamau abinci ma ta hanani yau,wai dan saboda nabada auren Sumaimah”
“Ahhh to ƴarta ce,ba ikonka bace,lamarin babu daɗi amma in sun kula kaima ai ba yanda zakayi ne,yau jimin mata da kilaroro…..amma dai Uwaisu zata daɗe bakaje gidan caca ba koh”
Manga ya faɗa dan yaji mai uwaisu zaice..
“Bazanje gidan caca ba? Akan me saboda wannan ƙaramin lamarin da mukayi da yaro,abinda yafi wannan ma ai yafaru munje ballantana kuma wannan,ai gobe ma banda ranar kasuwa ce zamuje sana’a da zuwa zanyi,amma ka taimayeni jibi zaka ganni”
Dariya Manga yayi kafin kuma yasake ɗago masa wani taɗin.
“Toh ya maganar kuma kayan ɗaki dazakayiwa ita amaryar,kasan dai baka kaita haka ba ko”
“Saboda ni wani abun zai bani inna bashi ita komai,ai yanda take haka zata bishi babu abinda ya dameni,karka manta bazai bada sadaki ba fah kaman ko wanne,wannan kuɗi daya hau kaina shine sadakinta,kaga kuwa haka zan kaita,dan inba aman kuɗi zanyi ba to bana maganinsa daka ganni nan,innarsa da kuma ita deeja da take tada jijiyar wuya suyi ruwa sannan suyi tsaki,babu abinda ya dameni.”
Yafada yana kaɗe rigarsa.
___***___
Ɗaga cinyar kazar yayi a hannunsa yana juyawa,Taska ya kalla wanda yake ta aikin ciro gashashshen naman daga cikin wuta.
“Kai taska a ina kuka samo kaji nan”
“Uhm ogah goje a sansanin wani ɗan fulani ne nan gefe da gari”
“Dama akwai kaji kuka gasa mana zomo jiyah,hadda cemin babu komai cikin garinnan banda waɗancan karashiyoyin?”
Cikin bacin rai yayi maganar yana hararar taska,wanda yake mazari yana sunne kai. Al’adarsu ce dama a babbaka wuta a gasa kajin mutane da kuma awaiansu idan sunyi dare a waje basu koma gida ba,duk garin kowa yasan yaran goje da cinye dabbobin mutane,gashi babu wanda ya isa cewa kanzil,kaima da ana ci babbaka zasuyi su cinye. Yaran su samari masu tasowa duk ya maidasu yaransa sai abinda yace,wani abun takaicin kakai ƙara wajen sarki babu abinda za’ayi,dan in dukane ko ɗauri yanda kasan ka ɗaure itace haka zaka gani,shikansa sarkin ƴaƴansa uku duk yaransa ne,sai abinda yace shi zasuyi bana ubannasu ba,idan aka masa horo haka zai hanasu zuwa gida har tsawon wata guda,matansa haka zasu ɗaga masa hankali dole sai ya janye abinda yace.
A zaune yake akan wata kujera a tsakar dajin ta fatun awakin mutane,da ba shine shugaban dawar ba,wani mutum ne mungu baƙiƙƙirin dayazo daga sudan. Gabaɗaya duk ya takuramusu komai shi sai kansa,goje ko shekara biyar baiyyi da zuwa garin ba shida iyayensa.
Tunda farko dama bai ɗauki rainin hankalin Damazau ba,shugabansu a lokacin.
Kullum cikin sa’insa suke,har goje yayi nasarar yanke maƙogaransa wata rana yazama shine sarkin dawar,shekara biyu baya. Abubuwa da dama sun faru lokacin,kowa a garin banda kama sunan goje babu abinda yake,matsi da takuri ya ƙara yawaita a cikin garin,yayinda su kuma yaransa suka fara fantama sunayin yanda suka ga dama,saboda yanda goje yabasu lasisin yin yanda ransu yake so a duk sanda sukaga dama.
Tura cinyar kazar yayi a bakinsa ya zuge tsokar kafin ya wullar da ƙashin.
“Shege dama yanada kazi bula bula haka muke cin zomaye,indai bayyi ƙara ba ku dunga ɗebo mana uku a kowacce rana,in yayi magana kuce yazo yasameni,ƴan kare da jajayen kunne sai suyita tara dabbobi yawun mutum yana cinƙewa in yagani,su basuci ba basu bawa mutum ba.”
“Angama ogah goje,ai saima ka gansu da rai,manya manya fah,naji ance wai kawun Ragarus neh”
Yafaɗa yana kallon wani saurayin bafulatani a gefensa riƙe da kwari da baka a hannunsa.
“Ragarus kace dukiyarku ce muke shirin hawa kai,kaji nace bakwa ci koh,to yazanyi hakan kuke saika saka sorry fah”
“Ogah kenan ai bai daɗe da dawowa ba ne,dani kaina saina fi haka,dan a bayan kwanaki kam dole zan more”
“Sheege ɗan kawu,to tsugunna ka dangwali arziƙi”
“Ai ogah wani dangwalar arziƙin ma sai matar ogah tazo gida,zamuyi shagali”
Dariya suka saka da shewa,amma lokaci ɗaya goje ya turbune fuska yana muzurai,wani kallon tsare rai yayiwa taska,har hakan yakasa sakashi haɗiye naman daya saka a baki.
“Taskaaah ka iya bakinka fah in kana son kwana da fatar bakinka,yaushe raini yafara shiga tsakani da har kake haɗani da mace, harda wani zakuyi shagali……hmmm ai naji haushi ɗazu,wai me yasaka ma ban cirewa wannan tsohon ƴan maraina bane,kamanni yayi caca dani bashi ko sisi,kuma har yana saka ran cinye saniyata wai,kutt Sailuba fah yakeson cinyewa wai a caca,kuma ma harda fansar saniyata da wata gajarabil ɗin ƴar sa,kai ya jawo mata ma aradu,zataci ƙaniyar tane muddin da taka gonata”
“Ayi haƙuri ogah bazai sake faruwa ba”
Taska yafaɗa yana sunkuyar dakai.
Jefah naman dayake hannunsa yayi kan ganyen dayake gabansa,tashi yayi daga kan kujerar tasa yana gyara zaman wandon jikinsa. Ta saman wutar ya tsallaka maimakon yabi ta gefe.
Bai waiwayo ya kallesu ba har ya ƙule cikin jejin.
Dukkan sauran yaran kowa taska ya kalla yana jiye masa.
“Kai taska wlh jagos ne,kalli fah yanda ka kunnashi,kasan fah yau ya juƙi hayaƙi dayawa a sama yake over. Da alama tunda ya nufi gidansa na cikin jeji to saita Allah kenan,ranar fah dana fishi gurnani naji yanayi a cikin ɗakin,anya kuwa ogah goje mutum ne kuwa?”
Dukkansu mai bayanin suka zuba ido,saboda jin abinda yafaɗa.
Ɗaya daga cikinsu ne wanda tun ɗazu bayyi magana ba yana gefe,wato Tunga,kuma shine na hannun daman goje,yafi sanin sirrinsa fiyeda su.
“Kai Ragarus kafiye fah surutu,da alama so kake yasaka shuru na har abada,kuma inna sakejin kana bibiyar sawunsa na abinda yake saina faɗa masa tamm. Mazaje mugama mu tafi gida,ogah nasan bazai dawo ba sai gobe,kunsan kuma munada ƴar tsamar da zamu buga da ƴan solo gobe,tunda sun ƙalubalance mu.”
Dukkansu shuru sukayi da zancen,amma daga yanda Tunga yayi magana to akwai ƙamshin gaskiya a maganar Ragarus kenan.
___***___
Tafiya yake kansa tsaye zuwa cikin dajin,duk da dare da kuma rashin haske,da kuma hanyar duk ciyawa da itatuwa,amma haka yake jefah ƙafafunsa ko jikinsa,kana gani kasan yasan hanyar da yarda ƙafafunsa su kaishi.
Yaɗanyi tafiya mai nisa kafin yafara haɗa hanya yana dafe kai,wani numfashi yafara saki daga cikin ƙirjinsa wanda yake bada sauti mai diri.
A haka yana tafiyar da ƙyar cikin jarumta har ya isa gaban wata bukka ita kaɗai a cikin dokar ɗajin. Buɗe ƙyauren yayi ya faɗa cikinta,ɗakin vaƙiƙƙirin yake anyi masa yabe da baƙin fenti, na shuni,wani buzu ne a tsakar cikin bukkar shima baƙi,bayan haka babu komai a cikin ɗakin.
Faɗawa yayi kan buzun yana riƙe kai,tareda fitar da wani ƙaraji kaman na karshiyah.
Ya daɗe a wannan yanayin yana birgima kafin ya fara fitar da wani numfashi mai nauyi.
Buɗe idanuwansa yayi wanda sukayi tamkar garwashi saboda jan da sukayi.
Ɗakin ya zubawa idanuwan kaman mai nazari,can kuma sai ya tashi ya zauna. Buzun ya ɗaga ya ɗauki tabar wiwi ya kunna mata wuta,zuƙar hauka yakeyi mata tana shiga cikin kansa na tsawon lokaci.
Kaman an tsikareshi yasake jefar da itah yana riƙe kai,da alama dai wata ƙarace yakeji wanda kunnuwansa basason hakan sam.
Sakin kunnen yayi ya faɗi a wajen tamkar matacce,ko numfashi bayayi na kirki………..
Ku nima na shiga ruɗani,mai yasameshi haka,suwaye suka fara yarda da maganar Ragarus🤣🤣🤣.
Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.
3131951977
Auwal Sadiya
First bank
Ko katin mtn ta nan
09035784150
VTU ta nan
2347068390570
Ƴan niger ku tuntubi wanann number.
+227 97 21 16 15
—————————————————-
Sadi-sakhan ceh
09035784150
Share please
*SANADIN CACA*
Mallakar SADI-SAKHNA
PROFICIENT WRITER ASSOCIATION
*USERNAMES*
FACEBOOK PAGE:Sadisakhna
WATTPAD:@SAKHNA03
AREWABOOKS:@sadeesakhna
PHONE NO:09035784150
________________________________
*Book 1*
Chp[03]
[Sumaimah a mahangar gani]
Dare yayi sosai,bakajin komai sai ƙarar jemagu da kuma karnuka,wasu na gidanne na yayunmu,wasu kuma na maƙwantane. Banason haushin karnuka ko kaɗan,to amma kuma yazanyi da saurayin kakata,shikansa wanda ake shirin ɗaura ƙaddarata da tasa yafi kowa yawan karnuka a yankinnamu.
Tashi nayi na zauna ina kallon ɗakinnamu,ba wani girma ne dashi ba,amma yaran dasuke ɗakin Allah yayi yawa dasu,basuda wani takamaimai yawansu,saboda wani lokacin suna raguwa,yayinda wani lokacin kuma yawansu ke haura misali,kaman dai yau.
Dan duk matar gidan da mijinta yake ɗakinta nan take koro ƴar ta ta kwana,su kwana suna birgima suna fitsari,a barni da gyaran ɗakin kullum kaman ibada.
Duk cikin ɗakin nice babba,nayi rayuwa a ɗakin da ƴan matan gidan,a hankali aka fara aurensu har suka ƙare kaff sauran ni kaɗai,saikuma bazawarai wanda suka dawo daga gidan nasu auren amma su basa yarda su shigo wannan kurkukun kwana.
Ba ƙarar haushin karen ko kuma gwartin yaranne ya hanani bacci ba,bace abinda ya faru,tun ɗazu nayi nayi na runtsa amma na gagara,ko nayi niyyar baccin babu abinda nake gani sai fuskar goje mai kama da dodo,inaga kaff gidannamu babu wanda yakaini tsoronsa,bansani ba ashe dashi zan ƙare rayuwata.
Ahh anya kuwa nabari a kaini wajennasa wani satin? Zuciyata wacce take suya tayimin wanann tambayar.
Abu biyu sukazo cikin kaina,shinna gudu kokuma na na kashe kaina?. Dukkansu ba abune mai kyau ba,amma idan na bari aka kaini in shi ya kasheni shikenan na rataya a kansa koh?
Tashi nayi daga kan katifar bayan na ɗauke cinyoyin yaran da suke kaina,tsakar gidan na fito ina kallon taurari da kuma farin wata,sukam sunji daɗinsu sai haske sukeyi,ko yaushe zanga haske nima a rayuwata oho.
Hankalina yana wajen kallon saman saikuma najiyo kaman alamar matsin mutum a kewayen dabbobi na gidan.
Gaba nane naji ya buga,mai mutum kuma yake a tuken dabbobi da tsawon darennan.
Da kaman vazan ƙarisa ba karnaje aljanine nayi gamo,saikuma to zuciya da zon gulma,na dayyi ta maza na nufi kewayen.
A hankali nake tafiya ina sanɗa har na iso daidai wajen ta baya,tsugunnawa nayi na kara kaina tareda nutsuwa,domin naji mai ake cewa.
Muryar Inna rammah kuma matar baba ta biyu? Itada inna atika, matar kawu Ɗahe. Mai kuma suke a kewayen dabbobi da daddare,naga dai in wajen dabbobi ma sukaje sukam babu nasu aciki,awakin ammi ne a wajen sai kuma ragunan mazan gidan da suke kiwo.
Wata zuciyar ce tabani kaddai satar dabbobi zasuyi,ko kuma suyi musu illah,,dan hakan ba wani babbane daga cikin aikinsu ba,daga su har ƴayansu ba mutuncine ko tausayine dasu ba,nikaɗai sai Allah muka san baƙar izayar dana sha a hannunsu,damma wai a hakan basamin wani abun saboda a wajen ammi baba ya damƙani lokacin daya kawo ni gidannan ina ƴar ƙarama,kuma suna shakkarta itada kayanta.
Kaina na ɗaga kaɗan ina leƙawa domin naga wacce akuyah zasu ɗauka,saidai ga mamakina ba akuya suke ɗauka ba,rami sukayi a wajen suna binne wani abu da bansan menene ba.
Can kuma sainaji inna rammah tafara magana.
“Ke wai fah hakanma munyi da gaske,da tuni ƴayan mu suna nan zaune itakuma tayi aure,da ai bamu yarda da zancen Ƴar boka ba,datace mana muddin wannan ƴa tana gidannan to ƴayan mu bazasu auru ba. Naji fah kaman cewa yake ɗazu wai inna gonarsa zai siyar ya kaiwa goje kuɗin,yafasa bashi itah,kiji kayan baƙin asirin da uwartata tayi mata na farin jini ya yaye tahana ƴaƴanmu masu tasowa aure”
“Iyi kuma fah,bare ma ni mai yara ƙanana ai dole na tashi tsaye ki gafah shekarar da muka mata maganinnan shikenan sai ƴayanmu suka fara auruwa kaman ana musu ruwan mazaje daga sama,da kuwa ita kaɗai suke gani da gashi a gidannan,kallon maza sukeyiwa yayanmu”
“Hmm yanzu dai mungama da wanann,muddin yayi aiki to Baban su Hajjo bazai sake yin wani maganar fasa aurenta ga goje ba,suje can in ma babbakata zayyi ya babbaka ta. Itama Deeja(ammi) munafuka saikace bada ita aka haɗa vaki ba lokacin yimata magani na farko,saboda taga duk samarin ƴaƴan ta ita suke so,yanzun kuma dan taga dukkan manyan ƴaƴanta sun ƙare shine tace wai yanzu ba ruwanta”
“Wlh ƙarya take kedai bari asiyanta ta taso yanda take ji da yarinyar nan,tun yaushe ta tashi tsaye idan taga bazata auru ba, to yanzu idan Baban su hajjo yaƙi aurarta ga goje ya zamuyi kenan?”
“Wlh indai wanann kam ya karye toh haukata ta zanyi,yarinya jarabbabiyah ga kyau kaman mayyah irinna uwarta,keda bamu kauda uwar ba ai da yanzu bazamu samu kansa ba,yanda yake son ta kaman zai mutu…..maza ai munafukaine”
“Ko itama mu aikata wajen uwartata ba,duk da bansan Zinarunba amma in haka take kaman ƴarata kam dole zai jauce akan ta,haka suke da ƙira kaman su sukayi kansu”
“Zakuwa mu sanja mata kamanni,ke nifah na tsani ƴar nan,menene bamu gani ba a wajen baban hajjo akan ta,indai wannan karon bata bar gidannan ba to kuwa zamuyi babban shiri,in ma Deejah ce yanzu takeson kareta to da ita zamu haɗa………..”
Bangama jin mummunan labarin da suke ba na sulale a wajen,saboda yanda ƙafafuna suke rawa bazan iya gama ji ba sam.
Hawayene kawai yake zirara a idona,yayinda dukkan wani abu dayake amfani a cikina ya dauƙi yajin aiki na wasu daƙiƙu.
Tun inajin hayaniyarsu da shewarsu har na daina ji da alama sun bar wajen,na daɗe ina zargin mutanen gidannan namu basu san Allah ba,amma yau kam na tabbatar.
Gari yafara haske asuba ta gabato,kafin na bar wajen na nufi ɗakinmu,ikon Allah ne kaɗai ya kaini ɗakin.
Dana kwanta ma ba bacci nayi ba,zuru nayi har assalatu tayi.
Ɗankwalin danake yin sallah dashi na ɗauka na fita daga ɗakin zuwa inda nake sallah,a canne ƙofar wani baban yayanmu wanda yagina ƙofarsa amma bayyi aureba,a wajen nakeyin sallah,saboda ɗakinmu kam nasan bazzayi sallah ba.
Bayan na idar da sallahr na daɗe ina roƙon Allah kaman yanda na saba,yau kam banyi karatun Ƙur’ani dayawa ba,saboda yanda bacci ke fizgata,ban samu damar komawa ɗakiba anan bacci yayi gaba dani.
Zafin rana ne yafara cin ƙafafuna,hakanne yasa na tashi na zauna,safiya tayi ashe har rana tafito bansani ba.
Ajiyar zuciya nayi dan ma yau banice dayin wanke wanke ba,shara kawai zanyi sai ɗora abincin siyarwar ammi. Dan haka cikin nutsuwa na tashi na ninke abin sallahr tawa zan bar ƙofar.
Motsin mutum naji hakanne yasa na ɗaga idona.
Da yaya Musbahu na haɗa ido yana tsaye yana kallona.
Rusunawa nayi na gaisheshi,yanada mutunci shikam sosai,dan ko hayaniyar gidan bata wani dameshi ba,shine babban ɗan ammi,yayi diploma yana koyarwa a makarantar secondry ta garin.
“Sumaimah lafiya kikazo nan kina bacci,na dawo daga sallah naga kinyi bacci anan”
“Ahh bakomai kawai baccinne ya ɗan daukeni”
“Ohh toh,kiyi haƙurifah da abinda baba yayi miki kinji,in kika jure komai zai wuce kinji,yau ma nayi masa maganar a masallaci, amma sai ya hauni da faɗa,kuma jiya da mukayi masa magana yace zai bashi kuɗin yafasa aura miki shi,amma kuma yau da asuba ya dage sai ya aura miki shi,abin yabani mamaki”
Idon ne ya cicciko lokacin danaji abinda yaya Musbahu yace,maganar dasu inna rammah sukayi jiyace ta faɗo min araina,wato su yayah Musbahu ne suka tausheshi akan aurar dani ga wancan dodon,har ya yarda su kuma waɗannan matan suka sake juyar da kansa.
Saurin share hawayen idona nayi tareda jijjiga masa kai.
“Babu komai yah Musbahu in hakan shine ƙaddarata banida zabi illah na rungumeta,dama dolene bawa yayarda da ƙaddara mai kyau ko kuma akacin haka.
Har nazo fita daga ƙofar tasa yasake yimin magana.
“Kije ammi tana ta nemanki kinji,ga wannan kuma ki boye ki dunga siyan koko,an bani albashina jiyah”
Yafaɗa yana miƙomin naira ɗari biyar.
Wani kukane ya tahomin lokacin dana saka hannu na karba,wannan karon ban tare shi ba nayita kunza kayana,tun yana rarrashi na har yabari yabar ƙofar.
Allah ne kaɗai yasan yanda nake ƙaunarsa a cikin yan uwannanwa,da kuma yanda yake birgeni,shikam ya fita zakkah a gidannan.
Harna isa ƙofar ammi ina kwarara masa ruwan Addu’a ta samun nasara a raina,Allah ya haɗashi da mace tagari ba irin matan gidannan ba,dan daga kan iyayen har surukan kaman an cuɗasu an rabasu haka suke.
A baranda na sameta tana tsince shinkafar daza’a dafa in anjima,wajen kaca kaca da miyar tuwo da kuma kunu,ina yara suka zuzzubar lokacin da suka karya.
Gaisheta nayi kafin na leƙa ɗakin inna rammah mah. Tanata masifah da yaranta suna rashin ji.
Fuskarta dauke da murmushi da amsamin,kaman ba itace ta gama faɗin kalaman da mutumin dayasan zai mutu bai kamata ya furta ba.
Tuwo nah na ɗauka naci nakai kwanon wajen wanke wanke.
Bishirah da asiyah ne suke wanke wanken,ƴar rammah da kuma ammi.
Harara ta Bishirah tayi dana ajiye kwanon cikeda tsiwa.
“Wai mutum bazai ci abinci da wuri ba dan mulki,sai an kusa gama wanke wanke ya kawo kwano”
Kunnenta na riƙe ta bangaren danake,dan abin yayimim ciwo,yarinyar da in auren shekara sha biyu zanyi saina kusa haifarta take faɗamin wannan maganar.
“Ke wato kin iya rashin kunya koh,yaushene ma kuke wanke wanken,naga saikuyi sati bakuyi ba nina ke,dan an fara baku shine har kun fara tsiya koh?”
Maganar inna rammah najiyo daga bakin ɗakinta lokacin da Bishirah ta kwanɗa ihu kaman ina zare mata rai.
“Sake mata kunne to ƴar gadon marasa mutunci,baƙin cikin menene haka da har zaki cire mata kunne,so kike ki nakasata tayi zaman gida kaman ke?”
Sakin kunnennan ta nayi,yayinda maganganunta kemin zafi a rai,kallon baki isheni ba nayi mata kafin na ɗau tsintsiya na fita share harabar ƙofar tamu,duk abinta dai nasan bazata dakeni ba,da dai ta dakeni komai ma tayimin,amma yanzu na wuce duka,saidai tayi min muguntar boye ta asiri.
Abinda yafarune ma ya faɗomin a rai,hakanne yasa na nufi kewayen dabbobin kaman da niyyar cewa shara zanyi.
Akan wajen da sukayi binne binnen idona ya sauƙa,tabbas kam ba mafarki nake ba..
Jan lilon ƙafafuna nayi zuwa wajen,tsugunnawa nayi idon kyam akan abinda ƙarfi da yaji yakeson rabani da gidanmu.
Harna saka hannun zan tone wajen saikuma na tuna maganganunsu,wataƙila inna tone asirinnan ya karye baba yagane kuskuren da yayi a caca,har ya nemi kin auramin goje,to amma su inna rammah fah,zasu barni na cigaba da zama harna samu miji daidai dani nayi aure. Tabbas ba karamin aikinsu bane su aikata abinda sukayi iƙirarin faɗa.
Inkuma yanda suka fada dagskene na tarewa ƴaƴansu farin jininsu wanda nasan bokane yafadamusu dan ya ci kudinsu,toh zan tursasa ammi sake cutar dani muddin akan ƴar tane Asiyah.
Wanda hakan zai zama abune da bazanso ya kasance ba.
Maida kasar dana fara tonewa nayi na binne wajen cikin sanyin jiki,na zabi barin gidan kawai,koma mai zaimin yayimin Allah ne ke riƙeda rai na ai,wuya kuwa bata kisa sai kwana yaƙare.
Tashi nayi na barbaje ƙasar tareda fara share wajen,banyi niyya ba amma inna ƙiyi kar suyi tunanin naga abinda sukayi jiyan.
Wannan wace irin rayuwa ce,ace wai aisiri akayi maka amma ka ƙwammaci ka barshi ya hau kanka……ke duniyah.
Littafi na ɗaya ne dana biyu kaman yanda na sabayi,na ɗaya bati siddan,na biyu kuma Naira 300 ne dan haka zaka iya biya tun yanzu kafin a shiga kashi na biyu.

Leave a Comment