Hausa Novels

Prince Sadeq Hausa Novel Complete

[1:12PM, 11/1/2017] β€ͺ+234 815 661 8140‬: πŸ‘‘πŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ‘‘

*PRINCE SADIQ*

πŸ‘‘πŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ‘‘

*Na Billy Ladan*

*01*

Bayine ke ta zarya acikin babban masarautar *MAHBUSA*, matan sanye suke da riga da zani da dankwali duka navy color yayinda mazan ke sanye da riga da wando shima navy color. Takun da bayin suka jiyo shi ya sa su juyowa, suna ganin meh zuwar naga sun durkushe sun sadda kai kasa har sai da wannan meh zuwar ta karaso inda suke,batareda sun dago duk suka mata gaisuwa irinta sarakuna,bayin da ke biye da ita ne suka amsa tareda basu umarnin su cigaba da aikinsu sannan sukayi gaba. Daidai wani kayataccen fili suka tsaya tareda cewa “a fito lafia ranki shi dade” ko amsawa batayi ba ta shige dan tunda ta ji kirar sarki a rude take, zaune ta samesa yana nazarin wani mujalla ta karasa da sallamarta, batareda ya rufe mujallar ba ya amsa mata,bata jima da zama ba sai ga wani dan saurayi shima ya shigo,gaishesu yayi tareda zama,sunfi mintu biyu a haka sannan mai martaba yayi gyaran murya yace “Hajja Zinatu ba komai yasa nayo kiranku ba sai akan batun Sadiq, na gaji da korafin da ake kawomun akan yaron nan,na iya bakin kokarina a kansa amma abun yaki ci yaki cinyewa dan haka na yanke shawarar turasa aikin soja” a razane duk suka dago dan abun ya rikitar da su, “Allah ya ja da ran sarki” cewar Hajja Zinatu “wannan abu da ke kokarin aikatawa bai dace da dan sarki ba a masa duk wani hukuncin amma wannan ya mai tsauri, shi kadai gareni bazan so na rabu da shi ba, kayi hakuri in abunda na fada ya bata ma ranka shi dade”
“Hajja Zinatu ba shawara na kiraku dan muyi ba,tunda wannan yaro ya zabi ya tozartani a idon dunia, ya zabi ya zubar mun mutunci toh banga dalilin da zai sa bazan turasa aikin soja ba ko in yaje yayi hankali” cewar mai Martaba, cikin wani yanayi Hajja Zinatu ta dubi dan saurayinnan tace “Sadiq maza bawa mai martaba hakuri tareda mai alkawarin bazaka sake ba” sai sannan Yarima Sadiq ya dago ya kalli mahaifiyar tasa tareda cewa “banga abun bada hakuri ba kuma a shirye nake da in tafi aikin sojar dan yafi mun wannan rayuwar da nake anan, atleast zan samu freedom a can ba kamar a nan da komai zakayi idon mutane na kai ba kuma bakada say sai abunda aka gaya maka” hannu Hajja Zinatu ta daga ta wankesa da mari yayinda hawaye suka taru a idanunta, rike kuncinsa Prince Sadiq yayi tareda sadda kai kasa “amun izini ni zan koma ciki” batareda ya jira amsarsu ba ya fice daga lambun, bawansa da ke jiransa yana hangosa ya taso da wuri ya gyara mai takalminsa ya sa sannan ya bi bayansa suka bar wajen.

Koda Prince Sadiq ya koma daki kasa zama yayi, kayansa ya canza ya dauki daya daga amintaccen bawansa suka fice, ba shi ya dawo gidan ba sai can cikin dare, ba karamin mamaki yayi ba ganin mahaifiyarsa tsaye gaban dakinsa da alamar jiran zuwansa take tana ganinsa ta yo kansa,cikin baccin rai tace “daga ina kake? Maimakon ya amsa mata ya bi ta gefenta zai wuce ta riko hannunsa tareda juyo da shi tace “magana nake maka koh baka ji bane” murmushin gefen baki yayi tareda kawar da kansa yace “since when did u care? Rike kanta hajja Zinatu tayi ta dubi bayin da ke wajen tace ku barmu, suna barin wajen ta riko hannunsa tace “am ur moda Sadiq, ofcourse i care about u,dts y na zo gayama na shawo kan sarki u r not going to d army cos i wunt have dat, av worked so hard to see that kai ka gaji sarki bazan zauna inga dan uwanka ne ya hau ba” wani daria Prince Sadiq yayi sannan yace “ol u care about is d bloody damn throne, i dnt gv a damn about it, i dnt wanna rule, ma bro can have it, plus am going to the army” yana gama fadin haka ya cigaba da tafia, shan gabansa ummansa tayi cikin bacin rai tace “U”ll do no such tin swthrt, bazaka je ko ina ba and from today u r grounded, an haramta ma barin masarautar nan, naga alama ka manta waye kai bazan zauna ina kallo ka sa training da aka kwashi shekaru ana ma ya tashi a banza ba, wannan zance na mata da ka sa a gaba bashi zai taimakeka ba, from tomorrow u start a new training, ka aje zancen soyayya ko wani shirmen mata a gefe in lokaci yayi ni da kaina zan nemoma nitsattsiyar yarinya yar sarauta in aura ma” dago jajayen idanunsa yayi naga har kwalla sun taru a idonsa,cikin sanyi yace “ni ba yaro bane banga dalilin da za a tsare ni a gida ba, n wani training za a mun bayan wanda na sha yi, sumtyms i wonder if uv eva loved me or dad, cos ol u care about is d bloody throne, maybe abunda ya sa kika auresa…….marin da ta sauke mai shi yasashi yin shiru, nunasa tayi da yatsa tareda cewa “in ka manta matsayina bari in tuna maka, mahaifiyarka nake, nayi rainon cikinka for gud 9 months and kwana biyu nayi ina labour kafun in kawo ka dunia so u dnt gt to stand infront of me and talk to me anyhow, kuma u”ll do as i say ba shawawarka nake nema ba, muddun ka fita a gidan nan ko na samu labarin ka ma trainer inka rashin kunya zaka hadu dani,mu kwana lafia”
[1:12PM, 11/1/2017] β€ͺ+234 815 661 8140‬: πŸ‘‘πŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ‘‘

*PRINCE SADIQ*

πŸ‘‘πŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ‘‘

*Na Billy Ladan*

_Akwai dan gyara da nake son inyi kan in cigaba, masarautar su Sadiq itace *MASARAUTAR WURSAMA* wanda dama tun fari shi naso sawa, sabida littafin gaba dayansa dan mutanen masarautar wannan kauye nayi, up up d *YIRINGAU’s*_

*2-5*

*Sarki Marwan* shine mai mulkar garin *WURSAMA*, matarsa daya hajja Zinatu,
daya garesu Prince Sadiq wanda bayan shi Allah bai sake basu wani ba. Tareda dan uwansa Yarima Mahmud suka taso wanda ya kasance da ga wan mahaifinshi wanda shine asalin sarkin masarautar, bayan rasuwar mahaifin nashine sarautar ta dawo hannun sarki Marwan. Hajia Maryama itace mahaifiyar Yarima Mahmud. Akwai rashin jituwa sosai tsakanin hajja Zinatu da hajja Maryama sabida kowannensu nason dansa ya gaji sarautar wanda hakan yasa iyayen suke nasu small version na Game Of Thrones a masarautar dan kowannensu ya dau aniyar dansa ne zai gaji Sarki Marwan. Hakan ya sa suka dauki gaba tsakanin junansu,sam babu jituwa a tsakaninsu yayinda yaransu kuwa suke matukar son junansu, dan duk iya kokarin iyayen na su ga sun shiga tsakaninsu abun ya gagara.

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

Bayan kwana biyu Hajja Zinatu ta nemo trainer wa Prince Sadiq kamar yanda tayi alkawari. Ranar da zasu fara yana kwance yaji ringing wayansa, raba jikinsa yayi da baiwar da ke kan gadonsa ya daga wayan, yana ganin ummarsace ke kiran ya ja wani tsaki ya yi rejecting tareda kashe wayar gaba daya. Bubbuga baiwar ya shiga yi ta tashi a firgice, wani banzan kallo ya watsa mata wanda ya sata durowa daga kan gadon bata ma damu da cewa ba kaya a jikinta ba ta shiga bashi hakuri “tuba nake ranka shi dade” gyara kwanciyarsa yayi tareda juya mata baya tareda cewa “kar in juyo in ganki a wajen nan kiyi maza ki bace mun dagani” hannunta na rawa ta shiga jawo kayanta ta fara sawa amma tun kan ta ida taji an banko kofar da karfin tsiya, Prince Sadiq cikin bacin rai ya juyo dan ganin wanda ya masa wannan dabbanci,ganin Hajja Zinatu ya sa shi sadda kai kasa dan yau an kamasa red handed amma dukda hakan bazai nuna kamashi da tayi yasa yaji wani abu dan haka ya juya mata baya yayi kwanciyarsa, wani wawan kallo Hajja Zinatu ta yi wa Baiwar da tun shigowarta ta sa hannu akai tana kuka, bayi ta kira ta ce su dauketa su tsare mata ita, rarrafowa tayi ta zo gabanta tana mai kaskantar da kai “ranki shi dade tuba nake, ki yi mun rai, wlh wlh bazan sake ba” ko kallonta batayi ba ta ma bayin ido alamar suyi waje da ita, har sun sa kai zasu fice *Prince Sadiq* ya dago yace “ku kyaleta” cak suka tsaya dan sun san halinsa sarai ko mai martabane ya bada umarni baya shakkan karya wannan umarni, saukowa yayi yana mai rufe jikinsa da bedsheet in gadon, wardrobe nasa ya nufa ya ciro wani jallabiyarsa baki ya zura sannan ya juyo ya dubi bayin dake tsaye yace “meh kuke yi anan haryanxu,kaman nace ku bace mun dagani ko” har suna buge juna suka fice tsantsan tsoro, hannu ya daga wa baiwar dake durkushe bakin kofar alamar itama ta fice, godia ta mai sannan itama ta fice tana mai kara gyara kanta, sai da Hajja Zinatu ta tabbatar sun fita sannan ta dubesa cikin bacin rai tace “wats d meaning of dis Sadiq? Ta ya zan bawa bayi order sannan ka hanasu aikatawa, wat r u trying to prove, kasan illan hakan kuwa, do u tink dos slaves zasu cigaba da ganin kimata tunda har dan da na haifa ban isa inyi da shi ba” ko kallonta baiyi ba ya nufi bakin fridge nashi ya ciro ruwa mai sanyi ya fara sha, ji yayi an buge robar ya fadi kasa, juyowa yayi ya dubi ummarsa da ta canza ta dawo kamar kura sabida bacin rai “how dare u walk away from me wen am talking to u, ds should b d last tym u do such tin if not zan manta da cewa kai danane inma hukunci mai tsauri, kuma maza ka shirya ka fita ur trainer is waiting n FYI daga yau duk wani hidiman da bayi mata ke maka an dauke musu, an haramta musu zuwa side naka tunda na fahimci sam hankali bai isheka ba, u r a Prince for Gods sake or do i nid to kp reminding u, ka rasa wanda zakayi shekiyancin naka dasu sai bayi, u disgust me Sadiq, u dnt act like sum1 who has d blood of royalty at ol n dt mks me feel lyk gvn up on u sumtimes, bt dt wl mean u win ova me hajja Maryama gt wat dey want n i wunt sit and let dat happen so get going” bai ko kalleta ba ya dauki towel yayi hanyan toilet, jawosa tayi tareda juyasa ta sauke mai tagwayen mari a fuskarsa, he seemed unaffected with d slaps he received from his mum cos he didn’t even flinch n hs face holds a blank expression, nunosa tayi da yatsa tace “yanxu na gama warning akan cewa u dnt walk away wen am talking to u n u gt to answer me, i gave u and order and u must follow, if u want obey me as ur mum den u obey me as ur Queen, i giv u five minutes to clean and present urslf b4 ur trainer” tana gama fadin haka ta juya ta fice ta bar dakin.

A corridor suka hadu da Mahmud yana shigowa, gaisheta yayi ta amsa mai babu yabo babu fallasa yayinda a zuciyarta take godia wa Allah da ya sa bai zo lokacin da baiwar nan ke tare da Sadiq ba.

Da Sallamarsa ya shiga dakin dan’uwan nasa, Sadiq na jiyo muryarsa yayi sauri ya share hawayen da ya sauko kan kuncinsa tareda tashi, yana shigowa ya karasa wajensa suka rungumi juna suna dariya, sake juna sukayi tareda fara kare ma juna kallo, dariya Mahmud yayi sannan yace “bro av bn gone for just a week,stop looking at me dat way,but it seems uv lost weight” ya fada yana kare mai kallo, ajiyar zucia Sadiq yayi tareda zama a kan gadonsa yace “bro kai ma kasan mutum bazai taba jiki a masarautar nan ba, while u wia gone d king even threaten to send me to d army if i dnt bhv but d Queen didn’t agree to dat, i”ll hv bn better of in d army” murmushi Mahmud yayi tareda zama a gefensa tareda cewa “speaking of the Queen i saw her while coming in,she dsnt luk fine” yar gajeriyar daria Sadiq yayi sannan yace “wen r dey eva fine, ai tsoffin nan dnt knw how deadly n tiring d game of thrones is, but dey wil neva gv up, plus she cot me red handed with one of d slaves in here today dts y she is pissed, not bcs i did sumtn bad but cos i did it wt a slave” ya fada yayinda ya tashi ya nufi toilet, “way to go bro” cewar Mahmud, “duk ajinka ka kare a kan baiwa, gaskia ka bada maza” baki bude Sadiq ya kallesa sannan yace “who r u n wat have u done wt my broda, cos wannan da nake gani isn’t my bro, my broda wuld hv start his daily preaching after hearing dis” dariya Mahmud ya fara har yana rike cikinsa, tashi yayi shima ya nufi hanyar kofa yace “i beta liv b4 d Queens hv our heads for breakfast, but zanzo inga training inka zuwa anjika”, “please do” cewar Sadiq sannan sukayi sallama

Ko da ya fito daga toilet, bayi yaga tsaye hannun dayan rike da wani set na kaya dayan kuma takalma ne a hannunsa, koh bai tambaya ba ya san aikin ummansa ne, tsane jikinsa yayi tareda zama ya shafa mai, hannu ya musu alamar su kawo mai kayan suka karaso suka aje mai a kan gado, “zaku iya tafia” yace da su, suna fita ya dago kayan ya kare musu kallo, tabe baki yayi a xuciyarsa yace training inma har da wani uniform, bayan ya sa ya dauki turare ya feshe jikinsa da shi ya fito inda bayin ke jiransa, can wani fili mai fadi suka nufa inda trainern ke tsaye yana jiransu. Dan nesa da wajen bayin suka tsaya yayinda Sadiq ya karasa wajen mutumin wanda yana ganinsa ya karaso ya miko mai hannu sukayi musabaha, kujera ya nuna mai tareda cewa “my prince if ka shirya sai ka zauna mu fara” bayan ya zauna ne ya ciro wani katon takadda ya aje mai a gabansa, murmushi ne ya so yayi escaping lips nasa dan shi abun ma daria ya basa, tunda ya taso ake jibga mai ire iren irin wayannan takaddun wanda ya kunshi ethics and manners of royalty amma ace haryanxu bai huta ba, malamin nasa shi kadai yake ta kidansa yayi rawansa dan Sadiq was just there ne kawai ya dai kura mai ido ne amma sam hankalinsa bai wajen, har ya gama ya zo ya aje mai wukan katako ma bai san yanayi ba sai da ya dan tabasa sannan ya dawo hankalinsa, grunting yayi ganin abunda ya aje mai tareda daukawa ya tashi ya fito filin. In ka dubi fuskarsa ma zaka san he’s uninterested with d training stuff amma ya ya iya dole yayi besides his fighting skills r extremely bad ko dan kare kansa dole ya koya dan a yan kwanakin nan ana yawan kawowa masarautarsu hari. Kusan minti biyar suka dauka suna fadan dan Sadiq na enjoying, juyowar da zai yi ne ya hango Mahmud tafe shi da wata yarinya, manta wa yayi da wani training da yake ya kafesu dan ido dan yanason ganin ko wacece suke tahowa da Mahmud……….

Ji yayi malamin nasa ya sa buge wukar da ke hannunsa tare da sa mai nasa a wuyansa, juyowa yayi ya kalli malamin wanda ya mai murmushi tareda cewa “rule number one, neva pay attention to a distraction” murmushi shima Sadiq in yayi sannan yace “zamu iya tsayawa a nan for today? Dan bowing malamin yayi tareda cewa “as u wish my Prince” bayan sunyi sallama ya maida hankalinsa kan su Mahmud, sai sannan ya gane yarinyar da ke gefensa, wani yar gajeriyar tsaki ya ja tareda komawa ya zauna, hannu yayiwa bayinsa da ke tsaye suka kawo mai ruwa a bottle da handki, balle murfin robar yayi ya kafa a bakinsa, bai sauke ba sai da ya kai rabi sannan ya watsa sauran a fuskarsa sannan ya tsane da yar karamin towel. Basarwa yayi ya maida kallonsa gefe dan karma ya nuna ya san da zuwansu, sallama suka mai ya amsa batareda ya juyo ba, kujerar da ke fuskantar tasa yayinda yar budurwan ta zauna a gefen Sadiq, dan dafasa tayi tareda cewa “My Prince” duk da yaji maganar wani iri dan murmushi yayi tareda cewa “Ya akayi Jiddo,yaushe kika zo? Cikin karya murya tace “came in sum minutes ago ina fada da su Umma shine akace kana training shine nazo in kalli mijina” tarine ya kufce masa jin abunda ta fada, matsowa tayi ta rikesa tana mai sannu, cikin dabara ya janye jikinsa daga rikon da ta mai ya kalli Mahmud da ke gintse dariyarsa. Tashi yayi ya dubeta yace “excuse me ki dan ban few minutes yanxu zan dawo” alama yayi wa Mahmud akan ya biyosa yaga ya basar yana wani murmushi,toilet da ke gefen wajen ya shiga ya ciro waya ya mai text akan ya zo ya samesa a toilet

Bai jima ba ya ji karar bude kofa, dan lekowa yayi ya ga Mahmud ne, karasawa yayi ya rikosa yace “bro wai meh ke faruwane? Dan dariya Mahmud yayi tareda cewa “abunda ya faru da baiwar nan ya je ga kunnen mai martaba, yanxu haka suna can ana tsara bikinku da Farhana, dan naji ma ita tazo knan bazata bi iyayen nata ba dan already ma inaga ynxu suna hanyar airport” wani tsaki Sadiq yaja tareda buga hannunsa da bango, bai damu da zafin da hannunsa yake ba ya juya ya bar cikin toilet in, da gudu gudu Mahmud ya iso sa ya riko hannunsa ya tsaida shi,rike kafadansa yayi tareda cewa “calm down bro, kasan in ka tunkari mai martaba haka zaka kara tunzurashi ne” furzar da iska Sadiq yayi tareda kallon Mahmud “toh bro ya kake son inyi, at my age dai bazan zauna a ce za a mun auren dole ba, tym da nake rokonsu su mun auren ina ki sukayi sai yanxu da suke ga illar abunda sukayi shine za a kwaso wancan tanbadaddiyar ace za a aura mun,toh wlh ba dani ba, n if suka ce zasu tilastani toh sai dai duk ranmu ya baci” kan ma Mahmud ya sake magana wani bawa ya durkushe agabansu tareda gaishesu, cikin tsawa Sadiq yace “fadi abunda ke tafe da kai ba gaisuwarka muke so ba” cikin rawan jiki bawan yace “mai martaba ne yake son ganawa da kai ranka shi dade” wani tsaki yaja bai kara bin ta kan kowa ba ya wuce ya nufi fada, ko kallon inda Farhana take beyi ba dan wani haushinta da yake ji, dama can ba wani shiri suke ba dan shi a rayuwarsa ya tsani mace mara kamun kai da shegen surutu, sai ita kuma Allah yayita hakan.

Ko da isa fada ya iske sarki da wasu suna zantawa, waje ya nema a parlor ya zauna, sai da ya ga fitarsu sannan ya tashi ya nufi cikin fadan, dan nesa da mai martaba ya zauna tareda gaishesa cikin sakin fuska mai martaba ya amsa mai tareda cewa “matso mana siddiqu”
Dagowa yayi ya kalli mai martaba jin yanda ya mai maganar, murmushi mai martaba ya sakar mai tareda nuna mai gefensa ya zauna, cikin sanyin jiki ya taso ya zauna a gabansa tareda nade kafarsa, dan shafa kansa yayi tareda cewa “ya training in naji dan uwan naka yace kana training” “lafia lau” sadiq ya mayar mai batareda ya dago ba, shiru ne ya biyo baya na wasu dakikai kafun mai martaba yayi gyaran murya ya fara magana “Siddiqu na tabbata kaga yar aminina Farhana kuma na san Mahmud ya ma maganar dalilin zuwanta, tabbas nida mahaifiyarka bamu kyauta ba da muka hanaka aure lokacin da ka bukata wanda yanxu gashi nan muna ganin illar hakan, ka yafe mana Siddiqu” yanda mai martaba yayi maganan yayi bala’in kashema Sadiq Jiki, dagowa yayi a hankali yace “ai yawuce,Allah ya yafe mana baki daya”
“amin” mai martaba ya amsa sannan ya cigaba da cewa “dalilin kiranka shine in sake tabbatar maka cewa zancen Mahmud gaskiane, na yanke hukuncin hadaka aure da yar aminina Farhana da fatan bazaka bani kunya ba” Sadiq samun kansa yayi da kasa yin musu da hakan dukda har ranshi baiji dadin wannan hadin ba dan ko kadan baya son Farhana, jin yayi shiru yasa mai martaba sake magana sai sannan ya dan dago yace “insha Allahu bazan baka kunya ba” albarka mai martaba yayi ta sa mai sannan ya bashi izinin tafia dan ya samu ya cigaba da zantawa da yan fada.

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

*KAUYEN SHIKA*

Wata yar yarinya na hango wanda bazata wuce shekaru goma sha biyu ba tana dale a saman bishiya, ta ja kwari da bakarta tana jiran abun harbawa, wani zomo ne yazo wucewa ta ja bakarta tana shirin harbawa kawai taji muryar mahaifiyarta na kwala mata kira “Khairatee! Khairatee!!”
Hannunta ta sa a fuskarta ganin zomon nan ya gudu, durowa tayi ta nufi inda dokinta ke daure ta kunce tareda haurawa ta kada tayi hanyar gida. Tana isa ta daure dokin nata ta shige yar tsohuwar gidan nasu. Cikin sanda ta karasa falonsu ta nufi inda kakarta ke zaune ta rufe mata idanu, “bude mun ido khairatee tun kan ki karasamun su” kakar tata ta fada ta cigaba dacewa “dama duk a rube suke jira suke a taba su fado” daria khairatee ta fashe da shi tareda zagayowa ta zauna a gefen kakartata tace “Nanna kiyi addu’a inyi kudi in canza miki su”
Tabe baki Nanna tayi sannan tace “yarinya sai shegen dogon buri, a yar kauyen nan ne zakiyi kudin har ki canza mun idanu” matsowa khairatee tayi ta dan rungumeta tareda fadin “Insha Allah Nanna wataran zan bar kauyen nan,Allah zai turomun da prince charming ina wanda zai daukeni ya kaini birni, sai nima daga baya inzo in daukeku mu koma can da zama duka” tabe baki Nanna tayi tace “ke kika san wani pirins” dariya khairatee ta yi sannan ta dubi kakartata tace “Nanna ina nufin samrayi daga birni” baki bude Nanna ta kalleta tace “ka ji min ‘ya fa,toh shi shamawilun ina zaki saka shi” turo baki tayi dan ita sam ta tsani wannan hirar, cikin dan bata rai tace “Nanna nifa bana sonshi” bugu Nanna ta kai mata ta kauce tana dariya,nunota Nanna tayi da yatsa tace “wlh baki isa,baki sonsa ki ka sa aka karbi kayansa” Tashi tayi ta fara rangwada gabar Nana tana “dubeni fa Nanna ai banyi kalar kauye ba,bari ma kiga abba in yazo tare zamu koma birni sai ya sani a makaranta” ummanta da ta shigo falon ne ta dubeta tace “ummulkhairi ki bar wannan fantasy in da kike cos ntn like dt is going to happen, ba wani prince charming da zaizo ya kaiki birni n u knw ur dad who hates u isnt gonna buy d idea of u going to d city with him” idonta ne ya kawo kwalla dan an tabo mata inda yake mata ciwo, sai da ummanta ta gama maganar abun yayi hitting inta,ko kadan bata son ganin bacin ran tilon yar tata amma yau tayi subul da baka ta fama mata ciwo, dagowa tayi ta dubi yar tata da hawaye ya fara gangarowa a fuskarta, cikin i’ina tace “khairatee i didn’t mean…… Kada mata kai khairatee tayi sannan tace “i get it mum, ba wani dan birni da zai soni koda na je birnin bcs am poor n ugly just like dad use to say” tana gama fadin haka ta juya tayi dakinta da gudu ta kulle kanta a ciki tacigaba da kukanta, ajiyar zucia ummanta tayi tareda zama a gefen Nanna tana sharar kwalla itama “I didn’t mean to mk her cry” ta fada in btw tears “ta cika dogon buri ne kuma ban so ta kwallafa rai akan abunda ba samu zatayi ba, wa take tunanin zai fitar da ita daga kauyen nan, ubanta da bai sonta ko shamawilun da ba wani aikin kirki garesa ba” dafata Nanna tayi tareda cewa “komai zai daidaita insha Allah, har yanxu ita yarinyace wataran zata fahimci inda kika dosa” murmushi ta mata sannan ta tashi ta koma kitchen dan cigaba da shirya abincin da zata tarbi mijinta da shi.

Khairatee kuwa bayan ta gama sharbar kukanta ta tashi ta isa gaban yar mirror da ke manne a bangon dakinta, kallon kanta ta tsaya yi a zuciyarta tana cewa “am not dt uglybut mesa abba baya sonta” jin tsayuwar mota ne ya katse mata tunani ta nufi window ta leka, abbanta ta gani ya fito daga motarsa, da gudu ta nufi hanyar waje, a bakin falo suka hadu ta karbi jakarsa cikeda murna tareda mai sannu da zuwa, murmushi kawai ya mata sannan suka karasa falon. Gefen Nanna ya zauna suka gaisa sannan ya wuce dakinsa yayinda Khairatee ke biye da shi, jakansa ta aje mai sannan ta fara mai hira tareda mai tambayoyi gameda birni. Jakansa ya jawo ya cire wani novel ya miko mata tareda cewa “dts for u,nw liv me i nid to rest” yana gama fadin hakan ya kwanta tareda juya mata baya, cikin sanyin jiki ta bar dakinsa ta wuce nata ta rufo kanta ta bude sabon babin kuka. Ko da aka zo kiranta taci abinci yi tayi kamar tana bacci dan bata son ganin abban nata. Sai can cikin dare ta fito ta debi abincinta ta wuce daki ta ci abinta.

Washe gari tun 5 da ta tashi bata sake komawa bacci ba, da ta gaji da kwanciya ta fito parlor inda ta fara jiyo hayaniyar ummanta da Abbanta, cikin sanda ta nufi kofar dakin dan jiyo meh suke fada, muryar ummanta ta fara ji tana cewa “jiya fa kazo n u didn’t even spnd gud 5 mins with her, in bazaka zauna dan komai ba,stay for ur daughter she is rily hurtn” cikin murya da ke nuna bacin rai abbanta yace “in kinason in zauna den gv me a male child”
“Abban ummulkhairi ai kaji mai doctor ya fada, i wil neva conceive again,ya kake so inyi toh” ta mayar mai, cikin bacin rai yace “figure it out, ni zan wuce” cikin murya da ya nuna ta fara kuka tace “at least ka jira ta tashi ka mata sallama mana” tsaki ya ja sannan yace “u can do dt for me wen she wks up ni bnda lokacin hakan” jin ana niyyar bude kofar ya sa khairatee barin wajen ta nufi dakinta, tun tana danne hawayenta ta barsu suka fara gangarowa,dunkulewa tayi a kan gado tana kuka mai cin rai, ta rasa gane irin wannan tsana da mahaifinta ke mata,he was d reason she is bhvn like a tomboy amma hakan bai sa ya sota ba sai ma kara tsanarta da yake, ina ma da a namiji ta fito dan ta tabbata rayuwarta wil b more easy dt way. Tana jin karar bude mota ta leka ta window with d hope dt zai kalli dakinta so dat ta gansa kan ya tafi, har ya shiga motan ya bar wajen bai ko kalli gefen dakinta ba, tausayin kanta da ummarta ta fara yayinda sabbin hawaye suka fara bin kuncinta, jawo takarda da ya kawo mata tayi ta duba taga romantic novel ne, murmushi tayi dan ko ba komai zai debe mata kewa.

*UmmulKhairi Bala Mu’azu* shine asalin sunanta amma anfi kiranta da Khairatee wanda sunane da Nanna ta sa mata. Yarinyace yar shekara goma sha biyu. Suna nan zaune a kauyen Shika wanda ba kowane ya san da mazauna wajen ba dan tana can cikin daji. Ita kadai iyayenta suka haifa wanda bayan ita basu sake samun haihuwa ba, tun abbanta na hakura har ya zamto ya fara nuna rashin hakurinsa wanda har ya jawo ya fara tsanar khairatee dan ya tabbata yanxu barai samu ‘da da yake burin samu ba, hakan yasa yanxu sam bai cika zama da su ba. Duk wani kulawa da ya kamata ya bawa khairatee sam bai bata, ko makaranta ma ya ki ya sata, ummartace tun tana yar karama take dan coaching nata a gida in da yanxu tasan abubuwa dayawa tunda har tana iya karatu.
[1:12PM, 11/1/2017] β€ͺ+234 815 661 8140‬: πŸ‘‘πŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ‘‘

*PRINCE SADIQ*

πŸ‘‘πŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ‘‘

*Na Billy Ladan*

*6-7*

_wannan shafin nakune *Hausa Novel Lovers Group*, a gaskia ba group da nake jin dadin zama dasu kamar wanga group, kuna sani nishadi sosai musamman *Hauwa DY*, *Ashwal* da *Khairateena*, ina sonku sosai sosai,Allah ya barmu tare ya kuma kara dankon zumunci_
*Ana Mugun Tare*🀝

 

Tunda abbanta ya koma take kulle kanta a daki, ba abunda ke fita da ita sai cin abinci. Ba yanda Ma da Nanna basuyi ba amma sam taki saukowa dole suka hakura suka barta.

Tana zaune a daki tana karanta daya daga cikin novel da abbanta ya kawo mata Ma ta turo kofar dakinta ta shigo, zama tayi a bakin gadon tareda rufe takaddar da Ummul Khairi ke karantawa tareda fadin “Khairatee ki fito kici abinci sai in aikeki gidansu Shamawilu”
“Toh Ma” kawai tace sannan ta tashi ta canza kayarta tareda rataya gyalenta a gefen kafadarta ta bi bayan Ma. Tana gama cin abincin ta dauki plates in ta kai kicin ta wankesu sannan ta fito ta daure kanta ta karasa gun Ma dan karban sakon,kallonda Ma ke mata ya sata bin jikinta da kallo,dan turo baki tayi sanin cewa Ma maganar kayan jikinta zatayi, tabe baki Ma tayi tareda cewa “jeki ba sai kin turo mun baki ba nima na gaji da miki magana akan wannan shigar taki, yarinya Allah yayiki mace amma ke ki ce dole sai kin maida kanki namiji” ganin inta cigaba bata bakinta kawai zatayi ya sa ta mika mata sakon tareda cewa “karki jima”

Khairatee na fita ta dauko gorarta ta fice tana yar wakenta. Wasu samari biyu dake zaune suna hangota dayan yace “gafa can mata maza” sannan suka tsuntsire da dariya, kallon gefensu Khairatee tayi taga sun sake kwashewa da daria, hawaye ne ta ji yana kokarin zubo mata tayi sauri ta wucesu.

Tafia kadan ne tsakanin gidansu da na shamawilun, kai tsaye ta kutsa kai ta shige, ta budi baki zatayi sallama taji kamar ana ambatarta hakan ya sa ta ja bakinta tayi shiru tareda rakubewa dan jin hirar da Shamawilu da mahaifiyar tasa ke yi, muryar innar shamawilu ta fara jiyowa tace “yanxu Shamawilu ka rasa wanda zaka kwallafa ranka sai wancan kwailar, yarinya sai bakin muni da yin abu kamar maza, ni wallahi tsabar muninta ko hada hanya banso inyi da ita, na tabbata muninta shi ya jefa mu cikin wannan bala’i da muke ciki a kauyen nan tamu, yarinyar da ko uban da ya haifeta ba sonta yake ba ai kasan wannan annobace” daria Shamawilun yayi sannan yace “toh ai Inna baki sani ba, nifa ba wai wani sonta nake ba kudin ubanta kawai nakeso, na tabbata in na rabasa da ita ba karamin alheri zan samu wajensa ba”

Hawayen da Khairatee ke dannewa ne suka fara zarya a fuskarta, kalamansa ba karamin sosa mata rai yayi ba duk da itama ba wai sonsa take ba, pasa aikan tayi ta fice da gudunta ta bar gidan, bakin wani bishiya ta zauna ta hada kai da gwiwa ta hau rusa kuka, tausayin kanta ne ya mamaye zuciyarta, ta rasa gane irin tsanar da ake mata a kauyen, ko da yake bata ga laifinsu ba tunda uban da ya haifeta ma ba sonta yake ba, sai da ta sha kukarta mai isarta ta tashi ta kade kayanta ta nufi gida, koda ta isa gida ledar ta aje gaban Ma ta wuce dakinta ta kulle kanta a ciki.

Cike da mamaki Nanna da Ma suka bita da kallo, duba ledar Nanna tayi taga abunda ta bata ta sake dawowa da shi, tashi tayi ta bi bayanta a zuciyarta tana tunanin koh me ya hanata kai sakon.

Sheshekar kukarta da ta jiyo tun daga bakin kofar ya sata juyowa ta koma falo ta zauna dan bata son abunda zai sake tada hankalin tilon yar tata
Kallonta Nanna tayi tareda cewa “lafia dai ko” ajiyar zucia tayi sannan tace “Nanna kuka take kuma bazai wuci maganganun mutane bane ya sata kukan nan, na sha gaya mata ta aje wannan shiga ta maza da take amma sam bata ji, toh ya zanyi Nanna, kauyen nan baka yi bama ba a barka ba ina kuma ga ka basu abun magana

Tashi Nanna tayi ta nufi dakin jikartata, a hankali ta turo kofar dakin ta hango Khairatee tana rakube kan gadonta ta hada kai da gwiwa tanata sharban kuka, karasawa tayi ta zauna a gefenta tareda jawota jikinta ta shiga rarrashinta, cikin kuka khairatee ta dago ta dubi Nanna tace “Nanna meh aibuna, meh na tsarewa kowa da aka bi aka tsaneni, shin laifina ne da Allah ya yini baka, ko son kai nane da na fito mummuna, shin dagaske ni annobace a wannan kauyen tamu, is dt y evryyone hates me” ta karashe tana kuka mai cin rai
Jijjigata Nanna ta cigaba dayi sannan ta dago tace “koh daya khairatee, bakida laifin komai kuma ke ba annoba bace, ke Rahamace Khairatee kuma wataran zaki fahimci hakan kuma yan wannan kauyen ma zasu gane cewa ke Rahama ce a garemu baki daya, ki daina barin kalaman mutane yana shiga kanki har yayi tasiri a xuciyarki sannan kuma ki daina nunawa kamar maganganunsu na damunki dan hakan shi zai basu damar cigaba da musguna miki, sannan ina so ki sani ke ba mummuna bace kina da kyau kyawun da ba kowa Allah ya bawa idon gani ba, kin tuna hirar mu na kwanakin baya da kike cewa wani pirins ne ko menene zai zo” dariane ya kufcewa Khairatee jin yanda Nanna ke kiran Prince, sai da ta yi mai isarta sannan tace “Nanna Prince ake cewa” tabe baki Nanna tayi tareda cewa “koma menene, toh nima a jikina naji Allah zai kawo miki mai share miki hawayenki, wanda zai so ki so na tsakani da Allah ba dan wani abu naki ba, ke dai ki dage da addu’a kuma nima xan tayaki” Ma da ke tsaye bakin kofar dakin ne ta share guntun hawayenta tareda shigowa itama ta kwantar mata da hankali, ganin bawanda ya tambayeta takamamman abunda ya faru ya sata yin shiru amma a zuciyarta ta gama yankewa akan cewa ko sama zata hade baxata auri shamawilu ba.

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

Sadiq ne zaune da Mahmoud suna yar hirarsu, hango Farhana Mahmoud yayi, ya dan bugi Sadiq yace “gafa amarya na zuwa” dagowa Sadiq yayi ya kalleta tareda jan wani uban tsaki, tashi Mahmud yayi tareda cewa kaga ni bari in shige ciki dan wannan amaryar taka ba kunya gareta ba, riko hannunsa Sadiq yayi tareda cewa “kar ka mun haka bro, dan Allah kar ka barni da ita, in tana ganinka bazatayi wani abun ba” janye hannunsa yayi yana daria tareda cewa “ai matar taka ba kunya gareta ba kaima ka sani, koh ina nan ba pasa tabaka zatayi ba sabida haka gwara in tafi kar inga abunda zai sa idanuna zubowa

Tana karasosu duk sukayi shiru, gefen Sadiq taje ta zauna har jikinsu na gogan juna, cike da so da kulawa tace “My Prince inata nemanka tun dazun ashe kana nan kana shan iska ka barni, haka zaka ke mun in munyi auren,ace muna gida daya amma ko nemana bakayi inba ni na nemaka ba” ta karashe tana mai hade hannuwansa tareda kallon fuskarsa, murmushi ya sakar mata tareda cewa “abubuwane suka yi yawa Jiddo ban cika zama ba, yanxu ma da kika ganni nan gudowa nayi in dan huta kafun in koma bakin aikin” dan turo baki tayi tareda cewa “gaskia a canza tsari, toh me amfanin zuwana, ai ya kamata ka waremun tym ina na musamman so dat we gt to knw each oda more tunda aure zamuyi” sabida baison maganartata tayi nisa yace “toh zan duba jiddo” unexpected Peck yaji a kumatu sannan tace “dts my prince” baki bude ya kalli Mahmud dake ta kunshe dariyarsa, tashi yayi ya ce “bro bari in shiga ciki inje in huta” fuskar tausayi Sadiq yayi yayinda yake rokonsa da ido alamar kar ya tafi shi kuwa Mahmud sai dariyar mugunta yake, matsowa daidai kunnansa yayi yace “wlh bro Farhana ce daidai kai, ashe dama duk iskancika akwai wanda ta fika” rikosa yayi yana mai harara sassauta muryarsa yayi yace “amma kaifa mugune yanxu tafiyan zakayi ka barni” janye hannunsa Mahmud yayi tareda cewa “av seen enuf, gwara in tafi kan in ga abunda zai daga mun hankali” yana gama fadin haka ya juya ya nufi ciki yana daria. Farhana na ganin tafiyar Mahmud ta dada matsowa kamar zata shige jikin Sadiq

Shafasa ta fara yi ya dago yana mata wani bamzan kallo, maimakon ta bari sai ta fara kokarin hada bakinta da nasa, hannayensa ya sa ya tureta tayi baya kamar zata fadi, cike da mamaki da haushin tureta da yayi ta dago take kallonsa “Sadiq wannan wani irin wulakancine, sai kace wanda bai wayeba, am sure abunda yafi wannan ma kanayi amma sai kaketa wani forming, bara dai kace mun har ka kare karatunka a outside baka taba taba mace ba sabida haka imma zaka barmun forming gwara ka bari” haushi,mamaki da takaicine suka gauraye zuciyar Sadiq, shikam ya shiga uku, iyayensa basu mai adalci ba da suka hadashi da Farhana a matsayin matar da zai aura, yarinya ba kamun kai ko na miskala zarratin, sam bai dace da ita ba, duk da shima ya san wani lokacin ya kan kauce hanya amma natan yayi yawa, shiyasa ma tun wuri ya nemi a mai aure bawai don auren ya damesa ba sai dai dan gudun fadawa halaka, amma a rasa wanda za a bashi sai wannan tambadaddiyar, shi yanda yake gani ma in an barta raping insa zatayi, tsakin da ta ja ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, wani banzan kallo ya watsa mata sannan ya nunota yace “look Farhana karki ga wai dan zamuyi aure ki samu damar raina ni, ds should b d last tym da zaki mun tsaki kuma koda wasa kar ki sake gigin taba mun jiki in ba haka ba sai kin raina kanki, mara kamun kai kawai” tabe baki tayi tareda cewa “Amma anyi gara wlh dan in ba gara ba wa zaiga mace irina tana binsa har ya kauce, anya ma kai namijine kuwa, da kuwa an cuceni hadani aure da kai da za” ayi” yanda zuciyar Sadiq ke tafarfasa in ya tashi zai iya doketa hakan yasa ya cigaba da zama,kamar bazai tanka ba sai ya budi baki yace “ai Jiddo ni aka cuta da aka hadani da ke dan sam baki dace da ni ba, na farko gaki ba kamun kai, ba alkunya da aka san mata da shi, mafi munin kuma kina nan kamar tsinke ba oyoyon ba ba bye bye in ba, ban san ma meh zanyi dake in an auramun ke ba tunda dama bawai dan so zanyi aure ba sabida So batada muhalli a rayuwar Sadiq, dama dan hutawa kawai zanyi auren kuma sai aka hadani da shamulet amma ba yanda na iya dole inyi managing” yana gama fadin hakan ya gyara kwanciyansa kamar ba shi yayi maganar ba, ko bai dago ya kalleta ba yasan maganganunsa sun tabata, ba mamaki ma ta fara hawaye, yana jinta ta tashi ta zura takalminta tayi cikin gidan da sauri, ko bata fada ba yasan kararsa zata kai gun Ummarsa, sake gyara kwanciyarsa yayi dan yin bacci.

Mahmud kai tsaye sashin ummarsa yayi, tun daga bakin kofar yake sallama amma sam basu ma jisa ba dan sunyi nisa a abunda suke tattaunawa, hajja Maryama ce ta fara ganinsa tayi saurin yima jakadiya ido alamar tayi shiru, da yake ta kware ta wannan fannin sai ta juye hirar tasu ta dawo ta wani abu daban
Jikinsa ne ya bashi wani abun ake kullawa amma sam bai nuna ba, zama yayi a dan gefe tareda gaida mahaifiyar tasa ta amsa mai cikin sakin fuska, jakadiyace ta juyo ta fara mai kirarin da ta saba mai a duk sanda suka hadu:
“Barka da isowa Yarima Mahmud, dan sarki jikan sarki
Lafiyarka dama da hauni
Lafiya toron giwa
Lafia baya goya marayu
Lafiya bango madafar bayi
Lafiya ba hau da wani ba sauke wani
Lafiya kwankwason jimina mai wuyar shafawa…………..”

Daga mata hannu yayi yana dan murmusawa tareda cewa “ya isa haka jakadiya, ina godia sosai” murmushi tayi tareda cewa “Allah ya kara ma lafia Yarima Mahmoud Sarki mai jiran gado” sake murmusawa yayi tareda cewa “amin jakadiya amma na karshen nan ba da ni ya dace ba, wa Sadiq zakiyi na san kuwa ba karamin kyauta zai miki ba” ya karashe yana daria a can kasar xuciyansa sanin ba abunda Sadiq ya tsana kamar ace mai hakan amma da biyu ya fada dan ya tabo ummarsa kuma dan Jakadiya ta samu kasonta gurin Sadiq dan ya tabbata ita ke sa ummarsa yin wasu abun, harara hajia Maryama ta bisa da shi tana cewa “Toh shanyau, ai jakadia kinga abunda nake gaya miki, tabbas dole in tashi tsaye dan naga alama Zinatu da d’anta sun shanye mun kai, toh ta Allah ba tasu ba, indai ina raye toh mulki kamar ta dawo hannunmu tunda dama a hannunmu take, lokaci yayi da zaka karbi mulkin masarautar nan tunda ubanka ne yake kai kan ya mutu sabida haka kai ya dace ka mulki wannan masarautar sabida haka sai ka fara shiri dan nagaji da zuba musu ido dan banji suna da niyyar baka gadon ubanka ba” tunda ya sadda kai kasa bai dago ba, sosai kalaman Hajia Maryama suka bata mai rai, shi ya rasa gane jarabar son mulki da iyayen nasu keyi alhalin su da ake dominsu sarautar bata damesu ba, meh sa toh iyayen nasu bazasu hakura ba, maganar mahaifiyarsace ta katse mai tunani ta hanyar cewa “banji kace komai ba, ko bakin naka ma sun saye ne” kada mata kai yayi alamar a’a sannan tace “toh tashi ka bamu wuri mu gama tattaunawa” cikin sanyin jiki ya tashi ya nufi hanyar fita yayinda a zuciyarsa yake cewa koma meh za a tattauna yasan ba alkhairi bane, Allah dai ya dada ganar da iyayensu,amin ya amsa wa kansa addu’ar da yayi. Har ya kai kofa yaji ta sake kiransa tace “tun dazu ina kake na aika sau biyu a yo kirarka akace baka nan, sai ma yanxu nake tunawa” dan juyowa yayi tareda cewa “ina tareda Sadiq ne a can sashinsa” tabe baki tayi tareda cewa “Allah ya kyauta” amin ya amsa mata tareda karasa fita yayinda hajia Maryama ke cewa a zuciyarta dole ta raba tsakanin Mahmud da Sadiq dan ta tabbata inba tsakaninsu ta shigaba bara ta taba cimma burinta ba dan shakuwarsu da son da sukewa juna zai iya kawo mata cikas…………………..

 

Billy LadanπŸ–Š
[1:12PM, 11/1/2017] β€ͺ+234 815 661 8140‬: πŸ‘‘πŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ‘‘

*PRINCE SADIQ*

πŸ‘‘πŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ€΄πŸΌπŸ‘‘

*Na Billy Ladan*

*8-9*

Baccinsa yake cikin kwanciyar hankali, nauyin da yaji a kansa ne ya sashi juyowa tareda bude idanunsa a hankali, wani dogon tsaki ya ja tareda tashi “kai mahaukacin ina ne zaka zo ka tsayawa mutane cirko cirko akai suna bacci” bawan da ke tsaye a kansa russunawa yayi yana “Allah huci zuciyar yarima” harara Sadiq ya watso masa sannan ya fara gyara jikinsa, shi kadai yasan irin dadin da baccin yake mai kan a tada shi, juyowa yayi yaga haryanxu bawan na nan, wani banzan kallo ya mai tareda cewa “meh kuma ka tsaya kake mun bayan ka tadani, bace mun da gani kafun insa a tsare mun kai” jiki na rawa ya tashi yace “a gafarceni ranka shi dade, mahaifiyarka ce ke son ganawa da kai” yana gama fadin hakan ya juya cikin sauri ya bar wajen

Sai da ya shari kusan minti biyar a wajen sannan ya tashi ya nufi side insa, wanka yayi ya shirya cikin jamfa ya fito sai kamshi yake ya nufi sashin Hajia Zinatu

Zaune ya sameta itada Farhana da akayi kicin kicin da fuska, kallo daya yayi mata ya karasa gefen Hajia Zinatu tareda gaisheta, yanayin da ta amsa mai ya nuna ranta a bace yake wanda ya tabbatar mai Farhana ta gaya mata komai, tun da ya zauna bai dago kansa ba, ta gefen ido yake lura da irin kallon da mahaifiyarsa ke mai, gyaran murya tayi tace “Sadiq dago ka kalleni, wani cin mutuncin naji ka yiwa Farhana” harara ya watsawa Farhana sannan ya dubi Hajia Zinatu yace “wani abun tace na mata? Kallon kar ka raina mun wayo ta mai tareda cewa “kai Sadiq ban son rainin hankali, wai ka manta yarinyar nan aurenta zaka yi ne da kaketa yaba mata irin wannan maganganu marasa dadin ji” dan bata rai yayi tareda cewa “kema fa cewa kikayi aurenta zanyi umma amma kuma ake mun fada gabanta kamar yaro, ai sai ta rainani, kuma ita bata fada miki abunda tayi mun bane? Tabe baki Hajja Zinatu tayi tareda cewa “in ta raina kan ma ai kai kaso, da bakayi abun fadan ba bazan tasaka a gaba ina ma fada ba, kuma nasan halinka Sadiq tsaf ka aikata abunda Farhana ta fada, kar ka kuskura in sake jin makamancin hakan ya faru in ba haka ba sai nayi mugun saba ma” takaici ya ma hanasa amsa mata, ta ya zata tsaya tana gaya mai irin wannan maganganu a gaban wanda ake ikirarin zai aura, in ba salon ta rainasa ba, mamaki ma yake da bata ji ta bakinsa ba ta hau balbaleshi da fada, maganar da yaji tana yi ya sashi dagowa, “tunanin meh kakeyi da baka amsa min ba”
“naji umma” kawai ya iya fada, kokarin tashi ya fara yi yaji Farhana tace “Hajia ni inaga ma ba da son ransa yake wani abun ba kamar zugasa Mahmud yake, dan ko da naje tare suke a zaune kafun daga baya ya tashi ya barmu amma sai da ya tsaya gaya mai abu a kunne tukun, na tabbata shi ya zugasa ya mun wannan cin mutuncin” kallon tuhuma Hajja Zinatu ta bishi da shi, yayinda shi kuwa yake watsawa Farhana wani irin kallo, “eh dole kake kallonta kamar zaka hadiyeta, saboda ta taba ma rabin ranka ko, ina rabaka da yaron nan amma sam baka ji, kai a ganinka so na tsakani da Allah yake ma ne, in baka sani ba toh ka sani kujerar ubanka yake hari kuma da zarar ya cimma burinsa daga ni har kai ba mai tsira a hannunsu, gwara ka farka ka san inda dare yama” iya baci ran Sadiq ya baci, wani tsana da haushin Farhana ya rinka ji dan shi sam ya tsani abunda zai shiga tsakaninsa da dan uwan nasa shiyasa sam basa jituwa da mahaifiyar tasa dan tun basu mallaki hankali ba take kokarin rabasu amma har yau Allah bai bata iko ba, rai a bace yace “ni zan wuce umma” kallonsa tayi tareda tabe baki tace “yanxu dan an tabo dan gold in naka shine kake wannan hade ran, ni gani nake ko ni da na haifeka baka mun irin son da kake wa wannan shegen yaro, toh wlhy sunyi kadan komin maitarsu sai sun sake mun d’a……..bata ma karasa ba Sadiq ya tashi ya fice dan wani irin suya da zuciyarsa keyi, baki bude Hajja Zinatu ta bishi da kallo, kai ta kada tareda cewa ” ah lalle, dole in tashi tsaye dan mutanen nen basu barka a haka ba, kallon Farhana tayi tareda cewa “kema zama bata kamaki ba, dole ki tashi tsaye ki taimaka wa mijin naki dan sun gama shanye shi, dole ki shigo tsakaninsa da Mahmud in ba haka ba kina ji kina gani, sai yanda Mahmud yace yayi zaiyi dake”

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

Zaune suke a kan yar dining in tasu suna cin abincin dare suna gamawa khairatee ta dauka ta nufi kitchen dan wankewa dan ita ta saba koyarwar Ma kenan sam ba a barin kwanuka da datti, tana gamawa tayi musu saida safe ta wuce dakinta, shiryawa tayi cikin irin shigar da yan mata keyi in zasu taron da ake a dandali kowace daren asabar, sai da ta tabbatar su Ma sun shige daki sannan ta fito cikin sanda tayi waje.

Dandalin cike yake da yan mata da aka caba ado, yan matan sun raba kansu group group yayinda wasu sun kebe suna hira da samarinsu. Duk da darene mutane sai jifanta da kallo suke wanda har ya sa taji dama bata fito ba,amma ya ta iya Allah yayita da maitan son ganin wasar da ake a dandalin. Cikin sanyin jiki ta rinka kutsa kai duk inda tayi ana kallonta, wasu ma har nunota suke yayinda wasu daria suke mata kasa kasa, cije lebenta tayi dan hana hawayenta zuba dan tayi alkawarin ba mai sake ganin hawayenta a kauyen. A haka har ta karaso gungun su Jummai wanda gungu ne ya yan mata da suke ji da kansu a kauyen, kusa da su ta cire kodaddiyar takalminta da ya sha dinki ta zauna akai tana jiyo hirarsu, dan hirar tasu da take ji ya sata tayi ta matsowa har bata san lokacinda ta shige cikinsu ba, Jummai ce ta fara ganinta tayi wani irin shewa tareda cewa “ahayye! Cin danko har da su kaza, juyowa sauran yan matan sukayi su kalli Khairatee tareda yin shewa suka tafa da junansu, cikin sanyin jiki khairatee ta tashi ta koma mazauninta na da yayinda zuciyarta ke mata wani irin zugi, kasa tashi tayi sai ma cigaba da jin hirar tasu da take yi. Jamila da ta lura da hakan ta dubi Jummai tace “Jummai yanxu ke har kika yarda Shamawilu ya hadaki da wannan kwailar mai zubin samudawa” dariya jumman tayi tareda cewa “kefa ba sonta yake ba, ubanta ne ya lika masa ita dan an rasa mai dauka, bayanda shamawilu bai kauce wa tayinsa ba amma sai ya hadashi da makudan kudi akan cewa in har ya yarda zai na biyansa kudi kamar dai yanda yan birni ke diban kudi duk wata haka zai na bashi kinga ai ba wanda zai kalli wannan arziki yaki karba, kuma na san da zarar mun tara dukiya mai yawa sakota zaiyi ta koma inda ta fito” daria duk yan matan wurin sukayi tareda cewa “ni wlh da nice ita kashe kaina zanyi tunda har uban da ya haifeni yake hantarata haka ai banga amfanin rayuwa ba” kan sauran su amsa mata Jummai tace “kunga ma dan halak gashi can zuwa” ta fada tana nuno Shamawilun “yanxu zaku tabbatar da abunda nake fada muku” gyara daurin dankwalinta tayi ta kafeshi da ido har ya karaso inda suke shida abokansa biyu
Kallo daya yayi wa Khairatee ya kawar da kai tareda maida hankalinsa kan Jummai da ake ta wani fari da ido, abokan jibril da ilu ne suka fara kodata suna “sai kinyi amarya kuma uwargida a gidan oga shamawilu” kallon kawayen nata tayi tana kinne musu ido alamar kun gani koh, Ilu da ya lura da Khairatee ne ya taba Shamawilu ya nunata da ido, yar gajeriyar tsaki yaja tareda mikawa Jummai hannu yace “mudan kebe ko” hannu ta mika mai ya dagata tana wani yauki suka bar wajen, wani irin shewa yan matan sukayi duk dan su dada kular da khairatee, iya baci kam ranta ya baci sai dai ba abunda shamawilun yayi bane ya bata mata rai.

Ashe dama tsanar da abbanta ke mata ya kai haka, ashe dama shi ya roki Shamawilu ya aureta, ita kam wannan wace irin rayuwace, ina ma da Allah zai dauki ranta da ya fi mata da wannan kunci da take ciki, ko ta huta da wannan karan tsanar da ake mata, cikin sanyin jiki ta tashi ta zo ta wuce dan zuwa gida, gindin wata bishiya ta hango Shamawilu da Jummai sun hade tamkar mutum daya, wani bakin ciki ne ya gauraye zuciyarta, hawayen da take kokarin dannewa ne suka fara tsere a fuskarta dan abun ya mata nauyi ita daya, da kyar kafafunta suka iya kaita gida.

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

Tun ranar da Sadiq suka zanta da mahaifiyarsa yake kulle kansa a daki dan ko kadan bai son abinda zai sake hadashi da ita ko Farhana. Yau yana kwance a daki Mahmud ya shigo, yaye bargon da yake ciki yayi tareda bude labulayen, ranar da ta haska fuskarsa ne ya sashi tashi, hararar Mahmud yayi tareda cewa “amma kaifa dan iskane, mutum yana cikin baccinsa mai dadi kazo ka tayar dashi” jawosa Mahmud ya shiga yi yana daria yace “koh ma meh ka kirani da shi, na gaji da wannan zamar naka a daki kamar amaryar kulle sabida haka ka tashi kayi wanka akwai inda zamu” pillow ya dauka ya wurga masa ya kauce yana daria tareda yin hanyar fita yana cewa “get dress kan in dawo” tashi yayi ya shige toilet ya yi wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya, yana feshe jikinsa da turare Mahmud ya dawo, kallonsa yayi yana murmushi yace “ko kai fa” harara ya watso mai tareda cewa “ai na shiryan sai ka gaya mun inda zamu” riko hannunsa yayi ya fara jansa har sukayi waje

Filin da suka saba xuwa dan shan iska ya kaisu, baki bude Sadiq yake kallonsa “yanxu nan zamu zo dama kasani yin wannan kwalliyar” bude hannayensa Mahmud yayi yana jin dadin ynda iskar ke shiga jikinsa, bugu Sadiq ya kai mai a baya, gefe ya ja yana “wayyo bro ka karya mun baya, ai kaine kasa nama hakan, kawai kaje kana ta kulle kanka a daki” kada kai Sadiq yayi tareda zama, Mahmud kuwa sai da ya gama shirmensa yazo ya zauna a gefen Sadiq yana cewa “bro nikam meh zamuyi a bikin ne gashi sai gabatowa yake bamu shirya komai ba gashi we hv just a week now” tabe baki Sadiq yayi tareda cewa “wannan kuwa kai ya shafa, matsalarkuce,ku bikin ta shafa kuje can ku karata dan ni barin ma garin zanyi” daria Mahmud yayi tareda cewa “pls b serious bro” juyowa yayi ya kallesa tareda cewa “am damn serious, bazan iya auren Farhana ba dan sam bata dace dani ba, duk da ba dan so zan aureta ba bnji zan iya zama da ita ba, so tonyt zan bar masarautar nan kuma bazan dawo ba sai after a week by then nasan mai martaba ya hakura da zancen auren” kallonsa Mahmud yake yana kada kai “Mehsa ka fiya taurin kai ne Sadiq, kayi tunanin halinda mai martaba zai shiga in kayi hakan, ba karamin matsala za a samu ba in har kaki auran Jiddo, hakan kan iya bata alakar da ke tsakanin mai martaba da mahaifinta” ware hannu yayi yana daga kafada tareda cewa “duk damuwarsu, ai basu bi ta kaina ba kan su yanke shawarar hadani aure da ita, da nayi hakurin yin biyayya amma yanxu banji zan iya ba, hanyar da suka bi suka hada auren shi zasu bi su warwareta in kuma za ayi aure ba ango ne toh duk matsalarsu nidai yau bazan kwana masarautar nan ba” ya karashe yana tashi, ido Mahmud ya kura mai tareda tashi shima yana cewa “yanxu dagaske kake” kai Sadiq ya gyada mai tareda cewa “12 midnight on d dot kazo dakina ka duba ko zaka ganni” kada kai Mahmud yayi sanin waye Sadiq, ya san tsaf yanda yace zaiyi kuma ba abunda zai yi dan hanasa aiwatar da abunda yayi niya. Daren ranar a dakinsa sukayi hira, sai goman dare ya mai sallama tareda mai Allah kiyaye hanya sannan ya fice.

πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘πŸ‘‘

Wasu kartin maza ne su biyu tsaye da wani wanda baka iya ganin fuskarsa sabida kayan da ke jikinsa ya rufe tundaga fuskarsa har zuwa kafarsa, cikin wani irin murya mai shi ya fara magana “Ku tabbatar in yafita ya bar masarautar nan ya fita kenan har abada, shabiyu daidai zai fita dan haka ku tsare shi har sai kunga fitarsa kan ku bi bayansa na tabbata shi daya zai fita, bana son mistake wannan karon, kansa nakeson gani in mun sake haduwa” kai kawai suka kada sannan suka juya dan zuwa aiwatar da umarnin da aka basu.

 

Leave a Comment