Books Reviews & FAQs

Triplets Hausa Novel Complete

*_( ROMEO )_*

 

*Story & Written*
⬇️
*Star Lady*

 

The writer of
*DUK KARFIN IZZATA*
And now
*_💋 TRIPLETS 💋_*
*_( ROMEO )_*

_Assalamu alaikum warahmatullahi taala wa barkatuhu masoyana masoyan *DUK KARFIN IZZATA* masoyan Hiyana da Brigadier general Safras ina muku fatan alkhari da godiya mai tarin yawa ba zan taɓa mantawa da kuba har kullun kuna rai na ya Allah ya tsaremin ku daga sharrin duk wani abun halitta_.

Da farko dai wanna littafi book 1 sadaukarwa ne ga My dear Amira My sister kuma my P.A😹ina kaunar ki lodi lodi 🥰

BOSS BATURE!!!much kauna 💖 masoyiya munarh much love ❤️

Kamar Yadda na fara littafin nan lafiya ina rokon Allah subhanahu wata’ala daya bani ikon Kammala shi lafiya Allah ya bani ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abunda bazai amfani al’ummar Annabi ba.

🤲Ya Allah ina rokon da ka tsaremum alkalami na daga rubuta abun da zai lalata tarbiyyar ƴa’ƴan mutane Allah ka bani ikon isar da sakon da nake son isar wa

*Gargarɗi*

_Ban amince wani ko wata yayi amfani da wani sashe na book ɗin nan ba ta kowace siga, ko akaranta mun shi a youtube batare da an nemi izini awurina ba ko a haɗamun document ko amin Edit Idan kunne yaji jiki ya tsira ko da Allah nabar mutun zaibi mun haƙƙina_

San nan ina jiran daɗaɗan comments naku masu karamin karfin gwiwa ta hanyar daddaɗar comments naku ne zan iya gane ya kuka ɗauki littfin Ina godiya Allah ya bar zumunci 🥰

Share fisabilillah👏👏

Mai neman karin bayani ya min magana ta wan nan number 09162620621 or 09075846926 Please iya WhatsApp ban da kira

 

💋THE BEGINNING 💋

Let’s get started

Episode 1

KATSINA STATE

Unguwar farin yaro

Misalin karfe 4 na yamma anguwar tayi shiru babu wani motsin kirki kyakkyawar yarinya ce Chocolate colour doguwa tana da kyakkyawar fiska ɗan ma dai dai ci mai ɗauke da dogon kyakkyawar hanci mai tsini har baka ga manya manyan dara daran idon ta masu design na kifi farare ne tas kamar madara masu ɗauke da dogayen gashin ido kamar wadda tasa eyelashes bakin ta ɗan karami dai dai da face nata lallausan laɓɓan ta launin pink color, lips nata nasama design of heart ne tana da baƙi lallausan saje kwance a gefen lalausan kumatun ta lallausan kwantaccen bakin gashi siɗif a goshin ta kamar na larabawa tana da gogayen yatsun kafa masu ɗauke da kunba (farce) farare tas kamar madara sanye take cikin blouse gown pink color mai bala’i kyau ta sanya ɗan karamin hijabi baki a kanta a shekaru bazata wuci 13 years ba kallon ɗaya zaka mata ka san tafito daga gidan hutu da jin daɗi amma sai dai ga fuskar ta ɗauke da bushesshen hawaye alamar tasha kuka. Rike dake da matches (ashana) a hannun ta kyakkyawar kafar ta na sanye cikin kyakkyawar flat shoe baki kalan hijabin ta kyakkyawar gaske ce dan idan nace zan tsaya zayyana muku kyan yarinyar nan to sai mu kwana mu wuni bamu gama ba dan ta ko ina ta haɗu.

Sauka tayi daga kan titin da take tafiya ta keta ta cikin wani lungu taci gaba da tafiya tana tangal tangal alamar ta gaji.
Dai dai zata shiga wani kwana wani matashin saurayi yace “Jimana ƴanmata” Juyowa tayi tana kallon sa zaune yake cikin motar sa kofar motar a buɗe ya zuro kafafunsa waje, Ji tayi kamar kar taje sai kuma ta tuna da zancen mum ɗin ta in da take cewa “Ba kyau wulakan ta ɗan adam dan baka san in da zaka haɗu da shi gaba ba” tuna hakan ya sanya ta nufesa tana ɗaure fuska.
Da ga ɗan baya ta tsaya da zazzakar voice nata tace “Gani nan” tayi maganar rai a ɓace fitowa yayi daga cikin motar ya juya gabas ya juya yamma lungun babu kowa shiru cikin sauri ya zaro handkerchief daga aljihun sa ya kaɗa mata a fuska, nan take ta yake jiki zata faɗi cikin zafin nama ya taro ta ya turata cikin mota gidan baya, ya shiga gidan gaba ya tada motar da gudun gaske ya fito daga lungun ya miƙi hanyan. Gudu yake zubawa sosai kamar zai tashi sama yara uku ne a cikin bayan motar da ita 4 dukkan su a sume kuma dukkan su mata ne.

Agogon Nigeria karfe 4:30pm ta buga.

Gidane ɗan ma dai dai ci mai ɗauke da ɗan ƙaramin kofar shigowa, bazaka kira gidan da gidan talakawa ba haka zalika bazaka kirashi da gidan masu kuɗi ba, za dai a sashi a layin gidan masu rufin asiri sai dai duk anguwar gidan tafi kyan gani da tsari da fasali. Ɗakuna biyu ne a cikin gidan sai yar karamar kitchen dake tsakar gidan ta ɓangaren hagu, daga gefen dama kuwa toilet ne awajen, gidan yana da ɗan filin tsakar gida mai ɗan girma.
Kyakkyawar mace ce zaune a tsakar gidan saman tabarma, kallo ɗaya zaka mata kaga jikin hutu ta mike kafa tana tsintar shinkafa a bai bai kana kallon yadda take tsintar shinƙafar kasan bata iya ba sanye take cikin dankareriyar lace baki mai ratsin ja hannun ta da wuyar ta sanye suke da sarkan gold mai matukar kyau da tsada farace tas kyakkyawa ajin farko, cikin sanyin murya ta ɗago kai tace”Jehan!! Jehan!!!”daga cikin ɗaki wata zazzakar murya ta amsa da “na’am Mum” “Kizo ki je ki dubamin Rimsha tun ɗazun da ta fita siyo matches bata dawo ba kin san dama ba wani sanin hanya sosai tayi ba, kiyi sauri dan mu samu mu ɗaura girkin nan yamma tayi sosai” “Mum ni gaskiya na gaji shekaran jiya fa tare da ita mukaje shagon na nuna mata hanya ba daman kince tafini ƙwaƙwalwa ba to sai ta gane hanya da kan ta ba sai na nemota ba ta dawo gida” tayi maganar cikin harshen turanci ta kai karshen maganar tare da fitowa waje daga cikin ɗakin.

“`Jehan“`
Kyakkyawa ce ajin farko farace tas doguwa mai kyakkyawar fuska dake ɗauke da dogon hanci har baka ga manya manyan idanun ta masu design na kifi farare tas kamar madara gashin idon ta dogaye a tsai tsaye bakin ta ɗan ma dai dai ci tana da lallausan laɓɓa pink color,sanye take cikin blouse gown pink color kanta ba ɗankwali ta zubo gashi har baya bakin kirin mai tsantsi da laushi an mata kananan kalba a kan nata a karshen kitson an sanya mata bit manya manya kowani kitso ɗaya bit uku aka sa idon ta abushe yake bata da tsoro ko kaɗan a shekaru ba zata wuce 15 years ba. Jehan yarinyace shagwaɓaɓɓiya a jin farko ga rashin tsoro iyayi rashin kunya rashin ji izza ba’a mata ta kyale rashin hakuri saurin fushi rashin son mutane.

***** “Ina ɗankwalin ki Jehan?” Cewar mum tayi maganar da ɗan karfi, turo baki Jehan tayi cikin shagwaɓa tace “Mum nifa nagaji da sanya ɗankwalin nan ni yanzu ma Mum fruits nake son sha” tayi maganar da harshen turanci “Jehan!! Jehan!!! Saunawa na kira sunan ki? Ki wuce kije ki sanya hijabi kije ki nemomin Rimsha kin san yarinyar nan ba in da ta sani tun da muka dawo nan bata taɓa fita ba sai shekaran jiya idan kika bari na mike Allah sai jikin ki ya gaya miki” “Kai Mum ni wlh kin takuramin yanzu fa mun kai 5 days da zuwa garin nan idan ma ban da dakikanci irin na Rimsha ko ba’a taɓa nuna miki waje ba ba zakije ki dawo ba bare mun taɓa zuwa to ni waye ma ya nunamin ba da kai na naje ba?” tayi maganar cikin kwaɓaɓɓiyar Hausar ta, Shiru Mum tayi bata sake cewa komai ba, ita kuwa Jehan waje ta samu saman dakalin soak away dake kusa da windon toilet ɗin ɗakinta ta zauna tana tura baki.

Wata kyakkyawar farar mata ce mai ɗan kiba ta fito daga cikin ɗaya ɗakin tana faɗin “Haba Jehan ɗin daddy yi hakuri kije ki dubo yar uwarki kinji idan ta ɓata fa? Ya zaki yi?” Tsaki Jehan taja kafin tace “Goggo ni fa I can’t go anywhere ta ɓata mana ni ina ruwana da ita? Please Mum let’s go back to our real house I don’t like this house it’s too local, I want to see my dad I miss him” Ta kai karshen maganar tare da miƙewa ta nufi ɗaki tana faɗin “Tunda kun dame ni na shige ɗaki” kallon mum goggo tayi, yayin da mum ta ɗaure fuska tana zancen zuci “Koma me Jehan tayi baku kuka batata ba baku kuka mai data hakan ba” wucewa goggo tayi tabi bayan Jehan dan taje ta rarrashe ta miƙewa Mum tayi ta nufi kitchen tare da shinkafar da take tsinta.

Shiru shiru har karfe 6 na yamma gari ya fara duhu Rimsha bata dawo ba Mum ta fara tsorata ta ɗauko mayafinta ta fito wajen gidan dan ta dubo Rimsha kallon gabas tayi ta kalli yamma ita kan ta bata san ko ina ba a unguwar dan tun da suka zo bata leka ko kofar gida ba. A hankali ta zuro kafafunta ta fara takawa ta rasa ina zata bi Jehan ce kawai ta san unguwar chan ta hango majalisan samari suna zaune suna hira cikin sauri ta karisa wajen tare da yi musu sallama, cikin fara’a uku daga cikin su suka amsa mata Sallamar har suna haɗa baki, sauran ukun kuma fiska a ɗaure
“Dan Allah bayin Allah baku ga ƴata ba wallahi tun ɗazun na aiketa siyo ashana shiru shiru har yanzu kuma bata dawo ba mu sabbin zuwa garin ne batasan ko ina ba sai shagon shima sau ɗaya ta taɓa zuwa” ɗaya daga cikin sune ya miƙe yana faɗin “Kai subhanallah yadda siyasa ta gabato dinnan satar yara ake sosai kamar me ya Allah yasa ba gaba da ita akayi ba bari mu duba miki ita Mama ya take yarinyar ina nufin tsawon ta da kalar kayan da tasa tayu ko ta ɓata hanyane tun da sabon zuwa garin ne ku” da sauri Mum tace “Chocolate color ce shakarun ta 13 tana sanye cikin dogon riga pink color da karamin hijabi baki sunan ta Rimsha” “Yusuf, Sha’aban kuzo mu rabu mu duba ta ko Allah zai sa mu ganta Mama ke kuma ki koma gida idan mum ganta zamu kawota har gida kinji?” Mum bata da zaɓi dan in tace ba zata koma gida ba bata san ko ina ba bata san ta ina zata fara neman Rimsha ba dole tabi maganar Sadiq hakan yasa ta gyaɗa masa kai ala’mar to sanna ta wuce jiki ba kwari ta nufi gida zuba mata ido Sadiq yayi har sai da ya ga gidan da ta shiga sanna yace “Sha’aban Yusuf muje mu duba mata ƴar nata mana” a tare Sha’aban da Yusuf suka mike kallon sauran Sadiq yayi yana faɗin “Hafeez kufa muje mana me kuke jira” a gatsale Hafeez yace “babu in da zamuje gayyan soɗi neman gindin zama daga ganin baki har ka fara shishshige musu to dai kabi a hankali dan da ganin matar nan wlh batayi kama da talaka ba me ya kawota anguwar talakawa?” Shiru Sadiq ya yi bai sake magana ba ya wuce tare da Sha’aban da Yusuf suka kutsa cikin anguwar neman Rimsha.

Lokacin da Mum ta koma gida an fara kiraye kirayen Sallar Mangariba, a tsakar gida ta isko Jehan da goggo suna zaune wuce su tayi zata shiga ɗaki goggo tayi saurin cewa “Maryam lafiya ina Rimsha ɗin take?” Mum na kokarin yin magana Jehan ta rigata da cewa “Mum I’m feeling hungry I want to eat something very soft” Kallon Goggo mum tayi kafin tace “Aunty Aisha ya kamata ki sanar da Jehan yanzu fa mum shiga halin rayuwa ko mutuwa ne dan na lura tafi jin maganar ki batun Rimsha kuma bamu ganta ba yaran unguwar nan sun fita tayani neman ta” kallon Goggo Jehan tayi dan ita ba wani jin Hausa sosai take ba iya mum ce ka ɗai ke musu magana da Hausa sai kuma goggo da take musu kaɗan kaɗan time to time Daddyn su turanci da Larabci kawai yake musu” goggo where is Rimsha? I’m seeing like Mummy is not happy why is she talking like this everyday she’s shouting and abusing me?” “Jehan you have to be very very careful now kina jina? Our life now and before is very very different” cewar goggo shiru Jehan ta ɗan yi kafin tace “okey na gane kaɗan now ina Rimsha take nake son sani kafin na tambayi Daddy” Hararar wasa Goggo ta mata kafin tace “Ba tun ɗazun akace kije ki nemo taba kika ki maybe ta ɓata hanya ne” Mikewa Jehan tayi ta nufi waje tana faɗin “Bari nayi checking nata mu gani ko zan ganta amma fa sai ta sha very very good slap idan na ganta dan ta ɓatan rai” ita dai Goggo bin ta da ido kawai tayi har ta fice.

Tana fita sukayi karo da su Sadiq suna kokarin shiga gidan “Who are those peoples kuma?” ta tambayi kan ta tare da ruke haɓa da hannu ɗaya ta tsaya a bakin kofar shigowa ta tare musu hanya, cikin nitsuwa sadiq yace “Sannun ki bari mu wuce” a wulakan ce ta masa kallon uku goma kafin tace “From where to where?” kallon su Sha’aban dake bayan sa yayi san nan ya dawo da kallon sa kan Jehan dake tsaye ta rike kugu tana musu kallon banza “Yi hakuri ni bana jin turanci kiyi magana da Hausa” cewar Sadiq dogon tsaki taja kafin tace “daga ina? kuma ina zaku je?” tayi Hausar a kwaɓe kallon ta Sadiq yake a ransa yana mai mai ta yadda ta kwaɓa hausar wai ita a dole tayi magana “wajen mamanki muka zo” cewar Yusuf, kallon wulakanci ta masa kafin ta musu nuni da hanyar komawa da hannu ta a wulakance tace “Ku wuce ku bani waje wasu dirty Boyz daku ne zakuce wajen Mum kuka zo to Mum ta muku me please leave this place before I open my eyes” ta kai karshen maganar tare da jan dogon tsaki tana tofar da yawu. Har ga Allah yadda take magana ba karamin tafiya da Imanin Sadiq tayi ba dan shi a rayuwar sa yana son mace mai izza tana burge shi sosai.

“`Sadiq“`
Sadiq matashin ne mai jini a jiki wadda ba zai wuce shakara 24 ba ba laifi yana da kyau dai dai gorgodo yana da hali mai kyau baki ne amma irin bakin nan mai shegen kyau yana da ɗan ma dai dai cin hanci da manya manyan ido

Fusata iya fusata Yusuf ya fusata da abun da Jehan ta musu yarinya yar karama zata tsaya tana faɗa musu magana cikin kunan rai yace “Yaya Sadiq muje dan Allah idan ba haka ba zan iya sumar da yarinyar nan” kallon banza Jehan ta watsawa Yusuf ba tare da tayi magana ba, juyawa Sadiq yayi yana kokarin yin magana, Mum ta fito dan duba su tun da taji shiru shiru gashi har an gama sallar mangariba, ganin mum yasa Sadiq ya ɗan sunkuyar da kan sa kasa dan tun da yaga Jehan ya ji ya fara jin kunyar mum “Mama wallahi mun duba bamu ga yarinyar nan ba” Salati Mum tasa tana kokarin yin magana Jehan ta rigata da cewa “They are lying Mum ina zata je da za suce basu gan taba” Yusuf ji yake kamar ya kwashe ta da mari dan haushi ita kuwa sai kallon rai ni take musu ko shakkan su babu a idon ta bare tsoro “Bayin Allah ina ne police station na ku bari na kai Report tun wuri, cikin nitsuwa da girmamawa Sadiq yace “Mama kiyi hakuri zuwa da safe sai muje amma da zakiji shawara ta da baki je police station ba dan last 2 weeks aka sace wata yarinya a nan kin san zaɓe ya kusa haka iyayen ta sukayi ta yawon zuwa police station ƴan sanda suna anshe musu kuɗi basa masu aiki kin dai san yadda kasan nan ya zama yanzu sai a hankali ba talakawan ba ba masu kuɗin ba kowa baya son gaskiya mafi yawancin su kan su kawai suka sani amai ma kon ki kwashi kuɗi ki kai wa yan sanda gwara ki ɗau kuɗin ki kai masallaci a sayi buta ayi sallah ayiwa yar ki addu’a sanna ki biya kuɗi a miki saukan Qur’ani mai girma dan Allah shi ka ɗai ne mafita, a yan kwana kin nan an sace yara zasu kai 3 a layin nan” Jin haka yasa hankalin Mum ya kara tashi sosai dan atunanin ta Rimsha sai dai ta kauce hanyar gida ta sauya hanya bata taɓa tunanin za’a iya sace ta ba amma jin bayanan Sadiq yasa hankalin ta yayi mugun tashi cikin ruɗu da fargaban in da Rimsha take tace “Yaro muje yanzu nan afara yi mata addu’a ka kai ni in da malaman ku suke mu baki ne a garin nan bamu san kowa ba” “Mama ki bari sai da safe mu kara dubata zuwa azahar tun da ku baki ne tayu ba sace ta akayi ba ɓata hanya tayi idan mun dubata gobe zuwa azahar bamu ganta ba sai mu fara rabawa malamai kuɗi su fara addu’a” shiru Mum tayi kamar mai tunani zafafan hawaye ne suka fara bin kuncin ta da yake wajen ya fara duhun mangariba su Sadiq basu lura da hawayen da take ba, ita dai Jehan sai kallon ban za take musu a duhu tana yamutse fuska tare da ɗage dogon hanci tan nan dan bata gane abubuwan da su Sadiq ke tattaunawa da Mum ba dan ba wani jin Hausar kirki take ba sama sama ta iya shi ma sai idan ita tayi kayan ta take gane me take faɗe idan Hausa ta wuce zo tafi zauna ina zuwa zansha ruwa da sauran kananan word to ba wani ganewa take ba. Da kyar mum ta iya cewa Sadiq “Bawan Allah ya sunan ka? kuma inane gidan ku dan gobe nazo muje neman nata tare” Murmushi Sadiq sarkin murmushi yayi kafin yace “Ga gidan mu can mai kofar kwanon nan sunana Sadiq wayan nan biyun kanne nane Yusuf da Sha’aban Yusuf Maman mu ɗaya Sha’aban kuma ɗan kanin Baban mu ne” “Na gode kwarai da gaske Babana dan sunan babana gare ka Allah ya biyaku da gidan Aljanna” murmushi Sadiq yayi yana faɗin “Ba komai Mama sai da safe” ya kai karshen maganar tare da juyawa suka bar wajen, Hannun Jehan Mum ta riko dan su koma cikin gida “Where are we going mum?” harara cikin duhu Mum ta wurga mata kafin tace “cikin gida” “Mum which kind cikin gida kuma? Where is Rimsha what about her?” Shiru Mum tayi dan bakin ciki ji take kamar ta wanke Jehan da mari haka Allah ya kaddara amma ko mai ya faru Jehan da Goggo ne sila “Mum please talk to me now” “Jehan wallahi ki fita ido na idan zaki rabu da wanna shegiyar yaren turawan ki kama Hausa gara miki ki kama yaren ki kina yar fulani shuwa arab Daddyn ku cikakken bafulatani ni cikakkiyar shuwa arab amma dan iskanci baki iya yaren mu ko ka ɗan ba sai aron yare ki bi ki addabi mutane to wallahi tun wuri ki fita harkan yaren yahudawan nan ki kama yaren uwar ki da uban ki kai kaji min ƴa” “Mum what are you saying? why are you shouting anytime everyday” Dogon tsaki mum taja ba tare da ta sake magana ba ta ja hannun ta suka wuce cikin gida dan tasan idan ta biyewa Jehan haukata ta ta zatayi.
A tsakiyar gida suka isko Goggo na alwala sallar issha sakin hannu Jehan Mum tayi tare da wucewa ɗaki abun ta kallon Goggo Jehan tayi tace “My Goggo please where is Rimsha” da sauri Goggo ta ɗago kai tana faɗin “What are you saying Jehan? You mean up til now they didn’t see Rimsha?” gyaɗa mata kai Jehan tayi ba tare da tayi magana ba ta nufi cikin ɗaki “Jehan kizo kiyi alwala” cewar goggo “No goggo ba yanzu zan yi sallah ba sai an jima” daga cikin ɗaki mum tace cikin harshen turanci “Wannan ne kuma wane uwar ki baki isa ba wallahi ko ki wuce kije kiyi alwala kizo kiyi sallah a gaba na ko kuma na fito na same ki a wajen” Shiru Jehan ta tsaya ta kasa cigaba da tafiya dan mum bata taɓa mata magana a irin wanna sigar ba juyowa tayi ta kalli goggo “Ni ma dai Jehan awan nan gabar ba zan bi bayan ki ba duk wanda baya sallah bai da wata amfani a duniya da kuma lahira sanna idan baki sallah a kan lokaci idan kin mutu kunama da maciji ne zasu yi gadin ki a cikin gabari ki kuma wutar jahannama zaki tafi saɓanin mai sallah akan lokaci da Mala’ikun rahma ne zasuyi gadin sa a kabarin sa su buɗe masa kofar aljanna ya rinƙa shakan kamshin aljanna sanna ya shiga aljanna” Ta kai karshen maganar tare da mikewa ta wuce ɗaki.

Ɗaki Jehan ta shiga ta ɗauko wayar ta kirar iPhone 14 ta kunna wutar wayar ta dawo tsakar gida ta ɗauki buta tana bin butar da kallo aranta tana faɗin “Disgusting gaskiya ba zan iya wannan rayuwa ba dole na koma asalin gidan mu” kitchen ta nufa ta ɗebo ruwa a butan ta dawo wajen da goggo tayi alwala, ita ma tayi alwala ta wuce ɗaki tana turo baki kamar biro tana kunkuni.

Tana shiga ɗaki ta ajiye wayar saman yar gadon su ta ɗauki ɗan karamin hijabi ta shifiɗa dadduma ta tada Sallah abun mamaki a nitse tayi sallar tare da karanta manya manyan surori a Qur’ani irin su suratul Yusuf da Aaraf a nitse tayi sallar nata sai dai hijabin nata ne bai gama rufe mata hannu ba a haka tayi Sallar.
Bayan ta idar ta ɗaga hannu sama tayi addu’a mai tsawo sanna ta shafa ta mike ta cire hijabin ta mai da saman trolley ta tare da naɗe daddumar ta ajiye saman hijabin nata ta ɗauki wayar ta, ta fito waje nan tsakar gida ta isko mum da goggo sun tasa abinci a gaba sun kasa ci dukkan su sun buga uban ta gumi suna tunani ga wayar mum a gefen ta kirar I phone 13 ta kunna wutar wayar tana haska musu wajen. Kallon Abincin Jehan tayi shinkafa’ce da miyar steew da naman rago yaji ganye irin su lettuce cucumber cabbage da dai sauran su dogon tsaki taja ta nufi hanyar fita gidan babu hijabi” Jehan ina zaki je? Cewar mum “mum I’m feeling hungry kuma ni gaskiya i can’t eat this dirty food I want to go and withdraw money from my Account to buy something that I will eat” “Jehan karki kashe kuɗin cikin Account na kin nan saboda bamu san me gobe zata haifar ba kiyi hakuri ki ci abincin nan yau kam kinji? Cewar mum kallon goggo Jehan tayi tana faɗin “ni gaskiya I can’t wallahi” “Ok naji bazaki ci ba na yarda amma karki fita da daddaren nan kinga yanzu ma bamu ga Rinsha ba ko? Ki bari na je na ciro kuɗin na sawo miki ko me kike son ci” girgiza kai Jehan tayi kafin tace “No mum bana so, ki zauna i will go by myself” tana kai karshen maganar ta fice da sauri mum na faɗin “To ki dawo ki sa hijabi” ina kan mum tayi magana ma Jehan ta fice abun ta kallon mum goggo tayi tace “Maryam kiyi hakuri kici Abincin ki kinji ko?” girgiza kai mum tayi tana faɗin “Aunty Aisha ba zan iya cin Abincin ba bakina ba daɗi ina Rimsha take? Wani hali take ciki? Hannun su wa take? Mutane na gari ne ko na banza? Taci Abinci ne? ko bata ci ba? Wanna tunani ba zai barni na iya cin Abinci ba Aunty A’isha” dafa kafaɗar ta goggo tayi cikin tausayin uwa da ƴa tace “Na sani Maryam dole ki shiga tashin hankali muma muka shiga tashin hankali bare ke amma ki daure ki ci Abinci nan In Sha Allah babu abun da zai samu Rimsha zata dawo gare mu cikin koshin lafiya” da kyar mum ta iya cewa “Aunty A’isha ina ji ajikina duk in da Rimsha take bata lafiya tana cikin tashin hankali da damuwa” “A’a Maryam ki dai na faɗin hakan ki mata Addu’a domin Addu’ar Uwa bata faɗuwa haka kasa banza kinji? Yanzu dai dan Allah kici abincin” miƙewa Mum tayi ta nufi ɗaki tana faɗin “Aunty A’isha sai da safe ba zan iya cin komai ba” ta kai karshen maganar tare da shigewa ɗaki dafe kai goggo tayi tana salati da ambaton sunan Allah a ranta. Tana kokarin miƙewa Jahan ta shigo gidan babu ko sallama, kusa da goggo tazo ta miƙa mata ledoji biyu farare masu ɗauke da takeaway da drinks a ciki ta wuce da leda ɗaya ɗakin ta in da sabo goggo ta saba tun da su kazo garin nan Jehan bata cin Abincin da suke girkawa sai dai taje restaurants tayo musu takeaway kuma bata taɓa saya ita kaɗai guda huɗu take saya kullun goggo tasha ruman mamakin ganin yau ta sayi guda uku sai daga baya ta tuna ashe Rimsha bata nan, jiki ba kwari goggo ta mike taje ta rufe musu kofar gida sanna ta dawo ta wuce ɗakin mum saman gado ta isko mum kwance kamar mai barci ajiye mata wayar ta da kuma leda ɗaya daga cikin ledojin da Jehan ta sawo musu abinci goggo tayi, ta juya ta fita ta nufi ɗakin Jahan kasan cewar ɗakuna biyu ne a cikin gidan mum da Rimsha take kwana ita kuma goggo da Jehan zaune a tsakiyar ɗaki ta isko Jehan tana cin abinci fried rice da pepper chicken ajiye nata Abincin goggo tayi ta haye gadon su ta kwanta dan ita ma bata jin yinwa ko kaɗan ɓatan Rimsha ya tsaya mata a rai sosai, Addu’a tayi ta yiwa Rimsha akan duk in da take Allah ya tsare ta da haka har barci ɓarawo yayi awon gaba da ita. Ita kuwa Jehan sai da taci tayi nak sanna ta kwanshe kayan ta gyara wajen dan ita mace ce mai son tsabta bata son datti ko kaɗan. Sai da ta gyare wajen tsab ta sauya kayan jikin ta izuwa na barci ta haye gado kusa da goggo ta kwanta tare switch off na wayar ta ba jimawa barci yayi awon gaba da ita dayake ba tare da Rimsha suke kwana ba sai bata wani damu da rashin Rimsha ɗin sosai ba.

Misalin karfe 1 na dare duniya duk sunyi barci Mum na zaune tsakiyar gadon ta ta kifa kai da gwiwa tana sharar kuka tana cikin matsanancinyar damuwa da tashin hankali ɓatan Rimsha, sosai take kuka damuwa sun haɗu sun mata yawa ga yanayin Jehan ga ɓatan Rimsha har karfe 2 na dare tana zaune tana sharar kuka.
Sai 2:30 ta mike ta ɗauro alwala a toilet na ɗakin ta tazo ta fara sallah tana kai wa Allah kukan ta.
Kamar yadda ta ga rana haka taga dare dan ta kasa rintsawa gani take kamar Rimsha zata dawo komai dare.

Washegari tun karfe 6 mum ta fita ta nufi gidan su Sadiq yayin da ita kuma Jehan ke sharar barcin ta goggo na fama da Aikace Aikace gida tana kokarin ɗunɗuma musu abincin daren su na jiya da basu samu damar ci ba dan suci da safen.

Da sallama mum ta shiga gidan su Sadiq yana tsaye a tsakar gida shi da maman sa da alama wani magana suke jin sallamar mum yasa suka juya a tare, ganin mum yasa Sadiq ya ɗan saki murmushi yana faɗin “Sannu da zuwa Mama ina kwana?” “Lafiya lou babana” kallon Mum Maman Sadiq tayi cikin mutuntawa tace “Sannu ki da zuwa yanzu Sadiq ke faɗa min abun da ke faruwa na ɓatar ƴarki Allah sarki Allah ya bayyana ta” da sauri mum tace “Amin ya Allah” “Mama bari na kira su Sha’aban muje mu duba gidajen masu anguwanni ko Allah zai sa mu dace muga yarinyar” “To Sadiq Allah Ubangijin yasa ku ganta Allah ya bada Sa’a” “Amin” Sadiq ya amsa da shi sanna ya dubi mum yace “Mama ki koma gida zamu dubata gidajen masu anguwanni da dai duk in da ya dace” girgiza kai mum tayi cikin sauri tana faɗin “A’a babana muje tare ba zan iya zama a gida ba hankalina ba zai taɓa kwanciya ba”. Ba yadda Sadiq bai yi da Mum akan ta koma gida ta jira su ba amma taki har Maman Sadiq ta sa baki amma mum taki haka Sadiq ya hakura suka tafi cikin jin kunya ya jera da mum suka fito ya shiga ɗakin su dake zauren gidan ya kira Sha’aban da Yusuf suka fito suka jera a tare suka fice daga gidan.

Gidajen masu anguwanni suka fara zuwa suna tambaya, duk in da suka je ace musu ba’a ganta ba sunje gidajen masu anguwanni 5 amma shiru shiru ba labari mum ta gaji iya gajiya dan bata saba tafiyar kafa ba ga yinwa da take ji tun jiya da rana rabon ta da Abinci amma saboda tana da yakinin za’a iya ganin Rimsha ko da a hanya ne yasa ta danne duk wani abun da take ji ta jure ta cigaba da bin su Sadiq. Duk in da Sadiq yake tunanin za’a ga Rimsha sunje amma shiru daga karshe sai ya yanke shawarar suje su kai wa malamai kuɗi afara yi musu addu’a. Haka kuwa akayi malamai biyar mum ta rabawa dukka kuɗin hannun ta akan ayiwa Rimsha saukan Al Qur’ani mai girma sanna tayi sadaka da ɗan kuɗin da suka rage mata, jiki ba kwari ga gajiya da yinwa suka juya suka dawo anguwar su cikin mutunci da girmama juna sukayi sallama dasu Sadiq ta wuce gida da kyar take jan kafar ta duk kafar nata sun kunbura sun yi ja.

Da sallama ta shigo gidan a tsakar gida ta isko Jehan da goggo suna zaune goggo tayi jugumi tana tunani, ita ma jehan tana zaune gefe ta buga nata tagumin, ganin mum yasa sukayi saurin miƙewa Jehan ta fasa kuka tana faɗin “Mum whare is my Rimsha?” “Maryam ina Rimsha ɗin take?” Cewar goggo wuce wa mum tayi ta zauna saman tabarma tana mai da numfashi kamar zatayi kuka cikin sauri goggo ta koma ta zauna tare da dafa kafaɗar mum tana faɗin “Maryam ki faɗa mana ina Rimsha kar ki sa zuciyar mu ta buga” shiru mum tayi tana mai da numfashi ta kasa magana.

To masu karatu sai mun haɗu gobe idan mai dukka ya kai

💋Star Lady💋

Share fisabilillah 👏

💞💕
💕💞💕
💕💞💕💞
💞💕💞💕💞

Mai bukatan karanta book ɗin*TRIPLETS* daga farko har karshe yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number 09162620621 ban da kira please

STAR 🌟 LADY..✍️

*💋The beginning💋*

Episode 2

____Komawa itama Jehan tayi ta zauna ta dafa mum kamar zata yi kuka tace “Mum please where is Rimsha?” Har lokacin mum bata samu damar yi musu magana ba hasali ma dukar da kanta kasa tayi tana sauke ajiyar zuciya, hawaye Jehan ta farayi dan duk wan nan rashin shiri da suke da Rimsha tana bala’i kaunar kanwar nata.
Almost 30mins mum ta ɗauka san nan ta ɗago kai ta kalle su cikin karyewar zuciya ta fara magana “Aunty A’isha banga Rimsha ba babu ita duk in da muka san zamu ganta mun duba bamu gan taba” tashin hankali iya tashin hankali goggo da Jehan sun shiga cike da matsanancinyar damuwa da tashin hankali goggo tace “Ai zama bai ganmu ba tashi za kuyi mu wuce police station mu kai Report” girgiza kai mum tayi tana faɗin “Aunty A’isha kin manta abun da Alhaji Shitu yace mana ne?” “A’a Maryam ban manta ba amma ai yanzu ya zama dole ne muje police station dan wan nan ba karamin case bane kin san dai idan Allah yayi Nawazudden ya zo yanzu ba zasu kare da shi ta daɗi ba ko?” “Nasani Aunty A’isha na sani amma to ya zamuyi bamu isa muje police station ba jiya ma da nace muje ido na ne ya rufe gaba ɗaya ban da haka da ban isa in yi wani zancen police station ba” “Maryam yanzu to me abun yi?” “Aunty A’isha sai dai fa mu zubawa sarautan Allah ido mu ci-gaba da yiwa Rimsha addu’a amma batun muje police station ko mu fita neman ta ma ya kare daga yanzu dan gudun ukubar da zamu shiga kin ji dai abun da Alhaji Shitu yace mana ko?” Shiru goggo tayi tana tunani ita kuma Jehan sai ruwan hawaye take wani na bin wani tana mai dana sanin kin zuwa aikan da tayi har a ka aiki Rimsha yanzu gashi yar uwar ta ɗaya tilo a duniya ta ɓata innalillahi wa inna ilaihir rajiun, jugum jugum sukayi dukkan su ba mai iya yiwa ɗan uwan sa magana kowa da abun da yake tunawa a ran sa amma kallo ɗaya zaka musu kaga tsananin tashin hankali a kan fuskokin su.

KANO STATE

Katafaren two storey building gida ne mai matukar kyau da tsada iya haɗuwa gidan nan ya haɗu kai da ganin gidan kasan masu rayuwa cikin wan nan gidan ko dai wani babban kusa daga gomnati ko wani babban ɗan kasuwa gate ɗin gidan kawai abun kallo ne ɓangaren biyu ne a cikin gidan ga wani ɗan ma dai dai cin pool a tsakar harabar gidan daga gefen hagu katafaren parking space ne mai ɗauke da katon rumfa ga dankara dankaran motoncin uku a wajen kirar *Mercedes-Benz* *McLaren solus GT.* *Roll-Royce boat Tail* motocin kawai abun kallo ne daga gefen dama kuma shuke shuken fulawowi ne awajen masu matikar kyau da ban sha’awa launin ja da yellow daga ɗan gefen parking space wani Katafaren wajen hutawa ne dake kewaye da glass wajen ɗauke yake da tampatsa tampatsan kujeru masu numfashi set ɗaya launin sky blue a tsakiyar kujerun wani haɗaɗen sofa table ne mai ɗan girma a wajen da gefe guda kuma ga makeken fridge a wajen dake ɗauke da lemukan sha kai ko ta ina gidan nan ya haɗu ba karya.

Wani kyakkyawan puppy dog ne fari tas mai yalwataccen gashi a jikin sa ya fito da gudu daga katafaren kofar da zata sadaka da babban palo na gidan da
Da gudu wata yar matashiyar yarinya ta fito daga kofar wadda a shakaru ba zata wuci 13 to 14 years ba tana sanye cikin wandon jeans guntu zuwa guiwa da yar riga baki mara nauyi kanta ba ɗankwali ta saki gashi har zuwa bayan wuyar ta, an zuba mata kananan kitso a kan nata kyakkyawace sosai chocolate color tana da dogon hanci da kyakkyawar fuskar ga manya manyan idon farare tas kamar madara yar siririyace ba kuma siririya sosai ba yar ma dai dai ciya,
da gudu ta biyo puppy dog ɗin tana faɗin “My Dolly ki tsaya mana haba Dolly na so ki ke nayi kuka ne” gudu Dolly take sosai yarinyar tana bin ta a baya har sai da suka kai wajen wasa dake gidan waje ne mai girma ga gefen buga basket ball a gefe ga wajen lilo ga wajen hawa dokin wasa da motoci na yara na wasa da dai sauran su wajen ya haɗu iya haduwa. Saman lilo Dolly ta hau ta zauna da gudu yarinyar ta kariso wajen tana haki tana mai da numfashi ta tsaya ta rike kugun ta da hannun ta dukka biyu tana kallon Dollyn ta yayin da itama Dolly ita take kallo “Why Dolly kika wahalar da ni me na miki?” Tsalle Dolly tayi ta faɗo jikin ta hannu yarinyar ta sa tana shafa jikin dolly ɗin tana kallon face nata. Dai dai lokacin wani babban Alaji ya iso wajen kai da ganin sa kasan Naira ta zauna masa kyakkyawa ne sosai fari tas da shi kamar balarabe ga kyakkyawar saje da gemu dogo da ka ganshi kaga Ustadz yaji hutu fatar jikin nan nashi ta kwanta luwai luwai da shi, yana sanye da jallabiya Brown a jikin sa ya kariso wajen yana faɗin “Baby jelly kizo muje kiyi breakfast a gaba na kafin na fita” make kafaɗa jelly tayi cikin shagwaɓa da murya kamar mai kuka tace “Dady ni ba zan iya cin komai ba dan dolly na tun jiya taki cin abinci fushi take da ni fa dady” ta kai karshen maganar kamar zata yi kuka rungumota dady yayi tare da dollyn nata yana ɗan bubbuga bayan ta cikin sigar rarrashi yace “Haba babyn dady muje ki ci abinci zan kira doctor Sadiq ya duba dolly ɗin sai muga meke damun ta yasa taki cin abinci” make kafaɗa tayi tana faɗin “Ni dady idan baka kira dr yazo ya fara dubata ba bazan iya cin komai ba” “Okey muje na ɗauki waya ta na kira dr ɗin ko dan ki samu kici abinci nima na samu na fita ana ta kirana a office tun ɗazun kuma nasan inna tafi ba cin abinci zaki yi ba” to tace masa ya kama hannun ta tana rungume da dollyn ta suka wuce cikin palon. Katafaren palo ne mai girman gaske mai ɗauke da manyan sofa set, set 2 launin Milk da Brown sai wani kyakkyawan table ɗin cin abinci mai ɗauke da kujeru 6 daga gefe ga wani makeken Tv plasma manne a bangon. Palon yaji komai da ake buƙata.
Saman kyakkyawar table ɗin dady ya wuce rike da hannu jelly sai faman turo baki take table ɗin cike yake da kayan abinci kala kala zama yayi tare da zaunar da ita saman kujerar kusa da shi ya ɗauko wayar sa dake saman table ɗin ta gefe ya shiga contact ya laluɓo wata number da a ka yi saving da Dr ya fara kira.
Bugu ɗaya dr ya ɗaga cike da cikin nitsuwa dady yace “Assalamu alaikum” daga ɗayan ɓangaren Dr yace “Waalaikumussalam Alhaji Ya gajiya?” “Lafiya lou dr daman nace idan kana kusa ka zo ka duba mana dolly taki cin abinci tun jiya” “To alhaji gani nan zuwa” “Ok sai ka zo” ya kai karshen maganar tare da katse kiran ya mai da wayar ya ajiye a gefen sa ya ɗauki spoon da ya fara cin abincin sa da shi kafin ya fita kiran jelly ya ɗibo abincin ya kai sai tin ɗan bakin jelly yana faɗin “Ci ko my baby” turo baki tayi tana faɗin “No dady ni ba zan ci ba gaskiya sai Dolly na taci” “Haba my baby kinji fa dr yace zai zo ya duba ta, to ki ci naki ke ma kafin dr yazo ya dubata kinji? Yauwa babyn dadyn ta” a hankali ta buɗe ɗan bakin nata ya zuba mata ta fara tauna a hankali hankali tana turo baki a haka har ta haɗiye ya sake ɗebowa ya kai mata bakin ta, ta ansa ta fara ci haka ya rinƙa lallaɓata har taci ta koshi san nan shi ma yaci ya koshi kafin ya miƙe ya riƙo hannun ta suka haye sama tana rungume da dollyn ta suka shige wani haɗaɗe bedroom mai ɗauke da katafaren gadon kwanciya dake shinfiɗe da white bed sheet na alfarma sai makeken drawer sanya kayan su,
Sai da suka isa tsakiyar ɗakin ya saki hannun ta ya nufi toilet yana faɗin “Let me bath my baby ki zauna idan kinji dr ya shigo sai ki kai masa dolly ya fara dubata kafin nazo, wucewa tayi ta haye saman katafaren gadon su ba tare da tayi magana ba shi ma ya wuce ya shiga toilet

Da zaman ta ba’afi 10mins ba dr yazo jin dr yazo yasa ta fito da gudu tazo ta miƙa masa Dolly tana faɗin “Uncle ka dubata taki cin abinci kwata kwata” tayi maganar kamar zata yi kuka tun daga nesa dr ya kura mata ido yana kallon ta har ta kariso gaban sa tana miƙa masa Dolly hankalin sa na kan kyakkyawar face na ta bai ma san tana miƙa masa wani abu ba sai magana take masa amma bai ji taba hankalin sa yayi nisa kallon face nata kawai yake, tana kokarin sa masa kuka dady ya fito yana faɗin “dr Sadiq har ka iso?” Yar firgigit dr yayi kafin yace “Eh na iso” yayi maganar tare da ansan dolly da jelly ke miƙa masa cikin sauri ya fara dubata da gudu jelly ta wuce ta rungumi dady tana faɗin “Dady bana son a yiwa Dolly ta allura” rungumeta dady yayi suka koma saman kujera mai zaman mutun 2 suka zauna shi ku ma dr yana aiki yana satar kallon jelly
““`Dr““`
Babban mutun ne wadda a kalla zai kai 35 year a duniya yana da kyan sa dai dai gwargwado ɗane ga abokin dady suna shiri da dady sosai.
Miƙewa dady yayi yana faɗin “My baby zauna ki kalli Dolly ki dr na duba ta bari na yi shirin zuwa office ko” jinjina masa kai tayi tana faɗin “To dady” wucewa dady yayi yana faɗin “Sadiq dan Allah ka duba mana dollyn nan da kyau muji ainihin meke damun ta yasa bata cin abin ci kaga kwana ki ma haka ta mana to dan Allah wan nan karon kam ina son sanin asalin a bun da ke damun ta” ya kai karshen maganar tare da hayewa saman ya shiga bedroom na shi dan shirin zuwa office.

Dady na tafiya dr Sadiq ya dubi jelly da ta buga takumi ta tsare sa da manya manyan idon ta tana kallon yadda yake duba dollyn nata ɗaga ido yayi ya kalli sama ganin cameran palon a kunne ne yasa ya ɗan ɓata rai tare da mai da kan sa kan dolly ya ci gaba da yan dube duben sa ita dai jelly ta zuba masa ido tana kallon sa.

Wacece jelly

Jalila kenan ya ɗaya tilo ga Alhaji Abdul Malik Salman Sultan tun jelly na da shekara biyu mahaifiyar ta ta rasu dadyn ta kuma yaki kara yin wani auren ya ci gaba da zama da yarsa su biyu suke rayuwa cikin wan nan Katafaren gidan sai masu musu girki Nana da Zuwaira Alhaji Abdul Malik bai cika zama sosai a gida ba wan nan dalili yasa ya sanya camerori a gaba ɗaya longu da sako na gidan sa dan ya rinƙa ganin halin da yar sa ɗaya tilo take ciki yana bala’i son jelly sosai fiye da ran sa, duk abun da take so shi ma shi yake so yana son farincikin ta kasan cewar ita ka ɗai ke garesa yan uwan maman ta sunyi sunyi ya bari su ɗauke ta su rike ta a wajen su amma yaki san nan anyi anyi da shi ya kara wani Auren nan ma yaki karawa dan gani yake duk wadda zai auro ba zata rike masa jelly yadda ya dace ba shi yasa yayi zaman sa daga shi sai ita sai masu aiki.
Wan nan shine ta kai taccen wacece jelly.

Shirye cikin wata dakakkiyar shadda sky blue dady ya fito ya sanya hula da takalma farare sai kamshi yake zubawa yayi kyau sosai, in da ya bar jelly nan ya dawo ya same ta ta buga tagumi tana kallon dollyn ta kusa da ita dady ya dawo ya zauna yana faɗin “My baby kar ki damu dolly zata samu lafiya ta dawo normal” kwantar da kan ta tayi saman cinyar sa tana faɗin “Dady ina jin kamar zan yi kuka” kallon dr dady yayi kafin yace “Dr Sadiq ya ake ciki meke damun dolly ɗin namu” satar kallon jelly dr yayi kafin ya fara magana “Alhaji zaka fitane?” Gyaɗa masa kai dady yayi “To muje tare sai na sawo mata magungu nan da suka dace ko? Dan gaskiya dolly bata da lafiya tana da matsala a zuciya amma In Sha Allah tana shan maganin nan zata samu sauki” “Okey to muje mana amma ni zan wuce Office idan ka sawo maganin sai kazo ka bata” “Miƙewa dr yayi yana faɗin “Ba damuwa zan dawo na bata maganin jelly a kula da dolly sai na dawo yanzu zan zo na bata magani ta warke taci abinci kin ji ko? Da fara’a ta amsa da “To uncle sai kun dawo” . A tare dady da dr suka fice daga palon kowa ya shiga motar sa driver yaja dady shi kuma dr ya ja kan sa suka fice daga gidan suka bar jelly rungume da dolly tana jiran dr.

KATSINA

washegari haka su mum suka tashi cikin kunci da jimami a kwana biyu da ɓatan Rimsha har mum tayi mugun rama saboda tunani.
Yauma kamar kullun zaune suke tsakar gida saman tabar ma sunyi jugum jugum kamar wayan da aka aikowa da sakon mutuwa Jehan na zaune daga ɗan gefen su saman yar ƙaramar kujera tana rike da wayar ta tana kokarin yin posting na hoton Rimsha a shafin ta Facebook. Tana gab da ɗora hoton sai maganar mum na jiya ta faɗo mata a rai in da take cewa Aunty A’isha kin san dai Alhaji Shitu ya gargaɗe mu kan zuwa police station ko, tuna hakan yasa gudun karta jawo wata matsala yasa ta ɗago ta kalli mum murya cike da damuwa tace “Mum ina son in shearing hoton Rimsha ya shiga duniya ko Allah zai sa in samu wan da ya gan ta” waro ido waje mum tayi kafin tace “Ki dai tona mana asiri ina ga Jehan kin gaji da zaman duniya ne shi yasa” cikin sauri goggo tace “Karki kuskura kiyi wan nan ganganci yanzu duk wani old account naki na media ma ki sauke sa ki buɗe sabo kuma karki kuskura kiyi posting na face na ki dan kin san dai ba wan da bai san face naku ba a kasar nan” jiki ba kwari Jehan ta sauke hoton Rimsha ta fasa ɗaurawa tayi shiru tare da buga takumi tana tunanin yar uwar ta “Jehan ki tashi ki ɗauki bokiti kije gidan su Sadiq ki ɗebo mana ruwa mu ɗaura girki dan yau duk gidan nan ba mai cash ko biyar” cewar goggo, a sukwane Jahan ya ɗago kai tana kallon goggo mamaki ma ya hana ta magana sai tambayar kan ta take a cikin ran ta “Wai shin mafarki nake ne ko da gaske ne ni Jahan zanje ɗebo ruwa ya Allah idan mafarki nake kasa nayi gaggawar farkawa” ganin tayi shiru ne yasa goggo tace “Jehan dake fa nake ki tashi mana” a kule tace “Wai goggo mafarki kike yi ne? Ni Jahan ɗin ne zanje ɗebo ruwa kina jin me kike faɗe kuwa goggo?” Tayi maganar cikin harshen turanci Kallon ta da kyau goggo tayi kafin tace “Kiyi hakuri Jehan kinga kuɗin hannun mu ya kare ne yau duk gidan nan ba wanda ta tashi da ko sisi” “To goggo ba akoi kuɗi a Account ba? Ai bani ATM zaku yi naje na ciro muku” “A’a Jehan yanzu kuɗin da suka rage manan nan lallaɓasu zamuyi ɗan su ɗan rike mu na wani ɗan lokacin kafin muga me Allah zai yi yanzu duk abun da bai zama dole ba ba zamu rinƙa fitar da kuɗi dan sayan sa ba” Cewar mum “Maryam wai nawa ne ma ya rage a account nakin?” Cewar goggo “Aunty A’isha kuɗin ba yawa kinga mun saya gidan nan mun sayi gado da sauran kayan buƙata bai fi 300k bane ya saura a ciki kinga idan muka ce komai saya zamu yi a yadda zamanin nan ya zama komai ta ninka kuɗin sa wallahi kafin nan da next week kuɗin zai kare” “Hakane Maryam shi yasa nace tun da akoi rijiya gidan su yaron nan Sadiq sai Jehan ta rinƙa ɗebo mana ruwan aiki ko?” Gyaɗa kai mum tayi tana faɗin “Haka ne Aunty A’isha kuma ruwan rijiyar tasu ba laifi wallahi maman Sadiq na da tsabta sosai” mum na rufe baki Maman Sadiq ta shigo da sallama ɗauke a bakin ta a tare mum da goggo suka haɗa baki wajen amsa mata sallama, ita dai Jehan ta buga tagumi tana tunanin yar uwar Rimsha duk wan nan zancen da su mum suke baya shiga kunnen ta, saman tabarmar da suke Maman Sadiq ta zauna suka gaisa cikin girmama juna san nan tayiwa mum jaje tare da fatan Allah ya bayyana Rumsha “Jahan ɗin dady ki tashi ki je mana” cewar goggo kallon sama da kasa Jehan tayiwa goggo kafin tace “Wai ke meyasa goggo baki son zaman lafiya ne? Wai da gaske kike ni zan je ɗiban ruwa?” Tayi maganar cikin harshen turanci goggo na kokarin yin magana mum ta riga ta da cewa “To shike nan Jehan tun da ba zaki je ba bari ni na tashi naje da kai na” ta kai karshen maganar tare da miƙa wa ta nufi kitchen ta ɗauko wata yar bokiti baki na roba ta fito ta ɗauko mayafi a ɗaki, ta na kokarin nufan hanyar fita Jehan tayi saurin miƙewa ta rike bokitin tana faɗin “are you serious mum? yanzu daman da gaske sai kije ɗiban ruwa da kan ki? Haba mum wai me yasa kuke yin hakane okay let me go and withdraw money from my account sai na sawo ruwan ko?” Kallon ta da kyau mum tayi tana mugun tausayawa yaran nata rayuwar da baka saba da ita ba rana ɗaya ka tsinci kan ka a ciki akoi wahalar ɗauka cike da tausayi mum ta fara magana cikin harshen turanci “Jahan bana son ki sake taɓa kuɗin Account na kin nan kinji? Kinga bamu san in da dadyn ku ya ke ba kuma kin san muna cikin haɗari a gaban ki Alhaji Shitu ya faɗimana komai kin san komai kin san meke faruwa kina dai ji Alhaji Shitu cewa yayi mu ɓoye kan mu karmu bari a san in da muke idan muka kashe kuɗin hannun mu waye kike tunanin zai bamu a wan nan wahalar rayuwa da ake ciki ko so kike mu fita nema har a ganmu a kashe mu ne eh? Ina son ki zama mai godiya ga Allah a duk halin da kika tsinci kan ki kin ji ko? Wan nan rayuwa da muke yanzu ma wata aya Allah ya nuna mana da muna zaune cikin daular dukiya da jin daɗi bamu taɓa sanin halin da yan kasan nan suke ciki ba amma kin yanzu ko ba komai mun samu karuwa munga halin da talakawa suke ciki idan Allah ya bayyana dadyn ku kuma Allah ya cika masa burin sa ya ci zaɓe kinga ai zamu faɗa masa halin da talakawa ke ciki ba sai na kusa da shi sun rinƙa masa karya ba” shiru Jehan ta ɗan yi hawaye na bin kuncin ta da kyar ta iya buɗe baki ta fara magana cikin harshen turanci “Mum yanzu shike nan dady ba zai dawo ba wai ma ina yaje ne mum kinga kafin ya fita fa yace min yana zuwa zai dawo da wuri kuma naji da uncle yazo yana ce miki bayi da tabbacin dady zai iya kuɓuta mu dai mu gudu Please mum ki faɗa min meke faruwa menene gaskiya abun da ya faru da dady na ko dai dady ya rasu ne?” “No Jehan ban san in da dadyn ku yake ba amma koma me ina da tabbacin bai mutu ba kuma ina sa ran zai dawo gare mu zai nememu ina jin hakan a jiki na” ta kai karshen maganar tare da sanya hannun ta ta gogewa Jahan hawayen dake bin kumatun ta tana faɗin “Ya isa kukan haka kiyiwa dadyn ku da Rimsha addu’a kin ji ko? In sha Allah zasu dawo gare mu komai zai wuce” rungume mum tayi tana faɗin “Mum ba zan iya dai na kuka ba sai dai na tsagaita” ɗan bubbuga bayan ta mum tayi tana faɗin “Hakane Jehan na san ba zaki iya dai na kuka ba dan uba da yar uwa ba wasa ba amma addu’a shine best thing da zaki rinƙa yi musu yanzu dai ansa bokiti kije ki ɗebo mana ruwa muyi abinci kin ji” ba musu ta ansa bokitin ta saki mum tana goge hawaye ta nufi hanyar fita “Jehan ki dawo ki ɗauki hijabi kin ji ko?” Cewar mum ɗin girgiza kai Jahan tayi kafin tace “No mum ni ban son hijabin nan gaskiya” “Jehan nan fa ba Abuja bane” Cewar goggo shiru Jahan tayi kamar bata ji me suka ce ba ta fice daga gidan kan ta ba hijabi sai wani ɗan karamin ɗankwali mai kama da handkerchief ta ɗaura a kan ta haka ta fice. Sai da ta fita san nan tace “bismillahi tawakkaltu alallah wala haula wala kuwata illa billah”
بِسْمِ اللهِ، تَوَكَّلْتُ عَلَى اللهِ، وَلاَحَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ

kallon goggo mum tayi kafin ta dawo kusa da maman Sadiq ta zauna tana faɗin “Jahan kenan” murmushi maman Sadiq tayi tace “Ai yara sarakuna ne” da yake cikin harshen turanci mum da Jahan suka yi magana hakan yasa maman Sadiq bata ji me suka ce ba girgiza kai kawai mum tayi bata sake magana ba shiru wajen yayi kamar ba mutane dukkan su sun shiga duniyar tunanin.

“`Jahan“`
Tana tafiya tana yamutse fuska tana kallon dattin unguwar kasan cewar Anguwar talakawa ne sosai akoi datti ta ko ina kallon banza ta fara yiwa mutane dake wucewa a harabar unguwar duk in da ta wuce sai ta tufar da yawu ko ta toshe hanci.
Tun daga ɗan nesa ta hango su Sadiq da wasu samari saannin sa suna buga kwallo dogon tsaki taja kafin tace “Dirty people” ta kai karshen maganar tare ta tufar da yawu a ranta tana faɗin “Allah ya kiyaye naci abincin da su Goggo zasu girka da ruwan gidan su kazaman yaran nan” Ta shagala cikin tunani da zancen zuci bata ma san ta iso wajen su sadiq ba sai ji tayi kwallo ya bugeta a kafaɗa da karfi har sai da tayi tangal tangal kamar zata faɗi kasa, a zafafe ta juyo tana kallon matashin da ya bugo kwallon, matashi ne mai jini a jiki yana da ɗan kiba da tsawo wadda akalla zai kai 24 to 25 years.
Kallon banza mata shin mata kafin yace “Ke ki wuce ki bamu waje kinzo kin tsayawa mutane a waje” Bata ma fahinci me ya faɗa ba ta dai fahimci faɗa yake mata, A kule ta fara magana cikin harshen turanci “Kai banza kazami idan ban da kai wawa ne ma taya za’ayi kuzo kuna buga ball a kan hanyar wuce wa jibeka wani katon banza da kai cikin yara duk kafi su girma kazo kana shiga cikin yara ko kunya baka ji” ta kai karshen maganar tare da jan dogon tsaki fusata iya fusata matashin nan ya fisata kasan cewar yana jin turanci sosai a fusace ya nufota gadan gadan tana tsaye ko motsi ba tayi ba sai ma kallon rai ni da take masa,.Yana iso wa wajen ta bai yi wata wata ba ya ɗaga hannu zai wanka mata mari cikin sauri Sadiq ya rike hannun sa yana faɗin “Haba Fadil me yayi zafi zaka yi yunkurin marinta” Fadil na ƙoƙarin yin magana muryan Jahan ya katse su cikin harshen turanci tace “Lallai kuwa wani kaza mi da kai ne kake yunkurin taɓani aiko da kayi kuskuren marina da baka sake mafarkin marin wata ba da kayi nadamar zuwan ka duniya” A fusace Fadil ya kwace hannun sa daga rikon da Sadiq ya masa yana kokarin kai mata mari Sadiq ya sake rike sa yana faɗin “Ki tafi in da zaki je kiyi hakuri” kallon banza tayiwa Sadiq kafin tace “I can’t go anywhere please ka sake shi ya mare ni idan ba shi da hankali wani wawa kazami da shi sai wari yake” tayi maganar da kwabaɓiyar hausar ta, ta kai karshen maganar tare da tufar da yawu tana yamutse fuska, a fusace Fadil ya ture Sadiq har sai da yayi baya baya ya faɗi kasa cikin zafin nama ya ɗaga hannu zai mare ta

Leave a Comment