Uncategorized

Tazara Hausa Novel Complete

[1/29, 1:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: FIKRA WRITERS ASSOCIATION

TAZARAR DA KE TSAKANINMU🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

MABUƊI

Kashim Ibrahim library (KIL) babban ɗakin karatu ne cikin Jami’ar Ahmadu Bello da ke birnin Zariya. Kamar kullum yauma ɗakin karatun cike ya ke fal da ɗalibai maza da mata kasancewar lokacin jarabawar zango na farko na shekarar (first semester) ya matso. Ɓangaren da ta san ya fi kowanne rashin hayaniya ta samu ta raɓe. Sanye ta ke cikin shuɗin hijab dogo har kasa. Sam ba ta damu da ta shafa ko hoda ba bare a kai ga jambaki, irin bakaken matan nan ne da su ka amsa sunan “black beauty”. Duk yadda ta so ta mayar da hankali ta gane karatun da ke gaban ta, hakan ya gagara ba dan komai ba sai dan zaman da wani ya yi kusa da ita. Zuwan ta be fi da awa daya ba sai gashi shi ma ya zo, kuma ya rasa in da zai zauna sai kusa da ita duk girman library din, mitar da ta ke yi cikin ran ta kenan tana mai jan tsaki ɗaya na bi ma ɗaya.
Tana cikin wannan halin ne ta ji kamar an gogi kafar ta wanda hakan ya sa ta saurin janye kafar da sauri, a fusace cike da alamar tambaya ta kai kallan ta gare shi. Tsintar idanun ta cikin na sa ya tabbatar mata da ya na sane ya sanya kafarsa ta gogi na shi, ko shakka babu irin ‘yan iskan mazan nan ne ma su yiwa mata goge, da be sami dama ba shi ne ya ke bin ta da kafa.
Kallan da ta ke masa ne ya sanya shi janye tashi kafar da sauri tare da faɗin
“Sorry Mama na! …”

Maimakon ta ji sanyi cikin ran ta, sai ma daɗa tunzurata da yayi, wato yana nufin bai ma san kafar sa na gogan na ta ba ne, ko tsabagen shaiɗana ne da zai wani kira ta da “Mama na” tunda ya sami kafar tsohuwarsa ai dole ya goga. Take ta ji karatun ma ya fita daga ran ta, cikin zafin nama ta haɗa ya nata ya nata, har ta na bugewa da tebur tsabagen ɓacin rai ko gaban ta ba ta gani da sosai.
Fuuu ta fice a fusace. Kai tsaye Queen Amina Hall ta nufa inda nan ya kasance hostel ɗin da take.
Da ke bayan isha’i ne, ɗalibai samari da yan mata wanda su ka sha karatu da wanda ba ma su sha ba duk sun taru mararrabar hostel sai cafta ake. Sam ba ta kula da su ba, bare ta damu da sheƙe ayar wasu daga cikinsu ke yi na rungume rungume da shafe-shafe da ta ke jin labarin wasu kan yi, kan ta a kasa ta ke gifta su, zuciyarta na mata tuƙuƙi don gaba ɗaya niyyarta ta shanye handout biyu na course din da za su yi jarrabawa ta gaba. Daf da za ta shiga hostel din ta ji an tab’o kafadar ta, tsayawa ta yi cak kafin ta jiyo a hankali saboda jin da ta yi hannun namiji ne mai taɓo ta, wa za ta gani? Wannan mutumin nan ne dai ya biyo ta, har ya iya daga hannun sa ya taba ta cikin mutane……ji ka ke tas!!! Hannu ta sa ta dauke shi da marin da sai ya ga wuta a idon sa ba tayi tunani kafin aiwatarwa ba don gaba ɗaya ji ta yi banda cin mutuncin matatantaka da yayi har da musulunci da hijabin da ke jikinta ya ci wa mutunci.
Gaba ɗaya hankalin jama’ar wajen ya dawo kansu, hasken lantarkin da ke ci a wajen kamar an ƙara masa haske don ya sadar da abin da ta aikata ga bawan Allahn nan. Jikin kowa yayi sanyin ganin wanda ke tsaye gaban ta hannun sa bisa kunci, bai yi zaton haka daga gareta ba hakan ya sanya marin zuwa masa a matsayin ba zata kamar yadda ya zo masu a hakan. Sanannan saurayi ne cikin Jami’ar wanda hatta wanda su ka shigo Jami’ar a wannan shekarar sun san da zamansa saboda shuhura.
Ga mamakin kowa har ita mai marin wacce ta yi mutuwar tsaye ba tare da ta yi Dana sanin marin da ta yi ba, don tsayuwar da tayi jira ta ke kome ma zai faru ya faru don kwatakwata babu nadama ko karaya a tare da ita, sai gani kawai ta yi ya mika mata abu, ko da ta ware ido da kyau ta dubi abin da ya ke miko mata sam bata gaskata ba, a hankali ta mayar da kallan ta ga fuskar shi wanda ke dauke da murmushin da ya sanya kwarjini da kyawun fuskarsa bayyana, cikin nuna halin ko in kula da marin da ya sha ya furta
“Ga shi, wayar ki ne da ki ka manta…”
Hannun ta na rawa ta karɓa ba tare da saurari cigaban abin da yake shirin faɗi ba. Ta na karba ya juya, cike da takama da ko in kula ya ke tafiya yayinda ta bi bayan sa da kallo, shin wannan waye shi?
“Ya Allahu ka rufa min asiri ni Amatullah…”
Cewarta, a hankali ta juya ita ma cikin sauri ta na harhaɗa kafafu, daliban da ke gurin nan su ke ta cece ku ce akan abin da ya faru gaban su, daga masu ba ta kyauta ba, sai masu da su ne sai sun tattaka ta, sai masu Allah shi Kara

” Toh ai shi Dee Yusuf ya ɗauka kowacce mace ce ta rako mata, wallahi ta burge ni da ta kwashe shi da mari” ta ji wasu na faɗi daga bayanta.
“Dee Yusuf!” ta so ta sake faɗi amma ina, zancen zucin da ta ke ya sa ta dena ji yadda ya kamata, kwakwalwarta ta dena sawwara mata daidai har ta isa ɗakin kwananta da ke gini na takwas ɗaki na goma sha biyu (block 8 room 12).

***

Littafanta kawai ta ajiye saman gadonta, buta ta ɗauka ta fice ba tare da ta ce da Ahalin ɗakin uffan ba, kama ruwa ta je tayi sannan ta yi alwala, ɗakin ta koma ta gabatar da wutiri, sai a lokacin ta samu ɗan natsuwa, duk da haka ba ta motsa daga saman dardumarta ba, sam bata lura da kallon da kawarta ke mata ba.
“Amatullah! Amatullah!! Amatullah!!!” sai a kira na uku ta ji ko dan ƙawar ta ɗaga muryarta ne ba ta sani ba.
“Zulaikha sai ki firgita mai rai wallahi, ji tsawar da kika min” ta karasa tana mai jan gajeruwar tsaki, mamaki a karo na biyu ya sake kama Zulaikha saboda ta tsaki na ɗaya daga cikin ɗabi’un da Amatullah ta tsana.
Tashi tayi ta ninke dardumarta, sannan ta haye gadonta da ke saman na zulaikha ba tare da ta ce da ita da ke jiran bayani komi ba.
Ɗauko takardunta tayi don ta cigaba da dubawa amma ina babu abin da ke shiga, ga shi jarrabawar da za su yi gobe na physics department ne da duk wani mai karanta abin da ya jibinci kimiyya da ke aji ɗaya a jamiar yake yinsa, sannan adadin wainda ke maimaita jarrabawar kan fi rabin adadin masu rubutawa a karo na farko, saboda haka dukkan su ke tsorace da darasin.
“Zulaikha na sadaƙar kawai zan sake physics dinnan” tace cikin karyewar zuciya.
“Allahumma Ajirna” Zulaikha tace iya karfinta.
“Kin shigo kafin lokacin da kika ɗibar ma kanki, kin shigo a firgice kin yi gamo ne?” Zulaikha tace tana shafa hannunta cikin sigar lallashi.
“Marin wani Yusuf Dee yake ko wa nayi fa anan gaban Amina” tace iya gaskiyarta, yayin da Zulaikha ke hango kwantacciyar firgici a idon ƙawarta. Ba Ta dena shafa hannunta ba, ba ta ce komi ba kuma, so take ta tuna in da ta san sunan Yusuf Dee din, kamar wacce a ka raɗawa ta tuna.
“Wai Dee Yusuf kika mara? Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, me ya kai ki Amatullah?” ta haɗa duka ta faɗa mata ba tare da ta jira amsar cewa shi ɗin ta mara ko wani ba.
Hawayen da ta ga Amatullah na fitarwa ya kara tsinka mata zuciya. Zikiri take a hankali duk wanda ya zo bakinta, yayin da Zulaikha ta haura saman gadon tana lallashinta.
“Kinga ba wani abin damuwa bane, Shine Sec Gen na SRC (Student Representative Council) Watau shugabanin ɗalibai masu wakiltar sauran ɗalibai, kuma shine in charge of student affairs department.
Wasu sun ce bafullatani ne wasu sun ce babur amma kin tuna Halima ta statistics kin san yar Margi ce, toh ita na ji tana faɗin ɗan garin su, kin san yadda ake rububinsa hakan ya sanya masa girman kai, kuma Kinga kudin SRC na ɗiban su, amma ina jin kamar faculty of medicine yake na ji dai ana fadin first class guy ne, yana dai da yan kora ni shi ne kawai tsoro na amma banda haka bana jin komi” Zulaikha ta ƙarasa cikin tabbatar da abin da ta ke fadi. Kallon ta Amatullah take cike da mamaki, ta san ajinsu ɗaya, kawarta ce, tare su ke komi a ina ta san duk waɗannan bayanan da ita ba ta taɓa sani ba, ƙarshenta ma za ta iya rantsewa ba ta taɓa ganin wani halitta irin ta wanda ake kira da Dee Yusuf ɗin ba.

 

*ZAI DINGA ZUWA MUKU RANAKUN LARABA DA LAHADI NA KOWANE SATI INSHAALLAH*
[1/29, 1:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: FIKRA WRITERS ASSOCIATION

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♂

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

BABI NA ƊAYA

Allah ya yi dare gari ya waye, jarabawar dai da ta fi firgita Amatullah yau za ta rubuta shi a matsayin jarrabawarta ta farko a jami’a wato ta kimiya Physics 131 (PHY131/ZAKS 131). Course ne da kowani dalibin aji daya da ke karanta wani abu da ya jiɓinci ɓangaren kimiya ke jin tsoro, balle kuma ita da ke ɓangaren Phamarcy, ba don komai ba sai don course ne da ake masa laƙani da “chain prerequisite for pharmaceutical chemistry (Pharm chem)” . Idan ɗalibi ya fadi shi ba zai taɓa yin na gaba da shi ba sai ya gyara wanda ya faɗi haka na nufin tabbatacciyar sake shekara (spill over) ce mai zaman kanta tun ana aji daya.

Amma duk da tsoron faɗuwa sai gashi gaba ɗaya hankalin Amatullah ba ya kan Course din, ita babban tashin hankalinta bai wuce marin Dee Yusuf da ta yi ba gaba ɗaya shi ya hana ta karatu a daren jiya ga kuma wani ciwon kai da ya saka ta gaba. Zulaikha ta ce Faculty of medicine ya ke, kuma SEC GEN na SRC hakan ya sa hankalin ta ya dan kwanta ba don komai ba sai don ta na kyautata zaton ba lalle ta kara haɗuwa da shi ba, domin kowa in dai yanda ta faɗa daidai ne ya kamata a ce yanzu Shika ya ke ba nan Samaru ba, duk tunaninta shaf ta manta akwai wasu fannoni a facultyn da su ɗin gaba ɗaya rayuwar su a samaru ne. Haka dai ta lallaɓa ta shiga jarabawar, da ya ke ta safiya ce, karfe 8:30 zuwa 11:30, ko karyawa ba ta samu ta yi ba, yadda ta saba shigar nan na ta cikin hijabi har kasa yau ma hakan ta yi, ba ta zame ko ina ba sai ɗakin jarabawa da ake kira FSLT.

Dan wuyar jarabawar, ba ita ta fito ba sai da lokacin kare jarabawar ta yi, aka karɓe tana mai takaicin rashin kammala wasu lissafin. Da sanya tafukan kafar ta waje da sarawar da kan ta yayi lokaci daya ne, sanadiyyar rana mai zafi da ke shirin ƙwallewa. Daga jikin ta har garin babu abin da ke mata dadi, don haka kai tsaye ɗakin kwanan dalibai ta nufa ba tare da ta tsaya magana da kowa ba, balle masu mayar da magana kan jarabawar in ban da fargaba da ɓacin rai babu abin da za su kara mata. Da rokan Allah ya mata katangar karfe da haɗuwa da Dee Yusuf ta ke tafe, zuciyar ta na dukan uku uku. Har ta wuce ta gaban Ribadu hall, ta dau hanyar da zai sada ta da Amina Hall, Sai kuma ta sake shawarar biyawa ta cikin social center ta siya abinci domin kuwa ba karamin yunwa ta ke ji ba, kuma yanda ta ke jin kan ta ba za ta iya tabuka komai ba, gashi idan akwai abin da Amatullah ba ta wasa da shi ya na bayan cikin ta.
Social center babban matattaran dalibai ne a cikin jami’ar, wanda ke dauke da shaguna iri-iri, wanda ya hada da business center ne, wajan aski, shagon dinki, shagon dinki, wajan kallan dalibai(Cinema), shagon kwalama da makulashe da dai sauran su. Ba ta da takamamman wajan siyan abinci saboda ba ta fiya siya ba dafawa ta ke, dan haka nan ta fara rarraba ido domin neman restaurant daidai kudin ta. Ko da ta bi gaban wani restaurant da ake kira “Frizllers” wanda kaf social center nan ne matattara cin abincin dalibai ma su ji da kan su, tuni gaban ta ya shiga faduwa. Da sauri har ta na tuntube ta wuce restaurant din, dan kuwa yauma kamar kullum cike ya ke da samari da yan mata. Wani wajen siyar da abinci dan gaba da Frizllers din ta tsaya ta siya shinkafa da miya da salad.
Hankalinta na kan wayar ta dake fama ringing ta fito daga restaurant din, wayar ta daga ta kara kunnan ta yayinda da ta shiga amsawa. Daidai gaban Frizllers Kamar ance daga kanki, nan su ka yi ido hudu da shi, Sanye cikin kanan kaya, jar riga da bakin wando, tare da ‘yan mata uku sun saka shi tsakiya. Hannun shi na hagu rataye a kugun daya daga cikin su. Idanu ya kafa mata ba ko gizo tuni bugun zuciyar ta ya karu tsabagen firgici, duk yadda ta so ta dake ta kasa hannun ta sai ya ɗau rawa. Ba shiri ta katse wayar da take, ita kan ta ba ta san sanda ta juya ba, restaurant din da ta sayi abincin ta nufa ta na mai jera addu’oi yayinda kanta ke sarawa fiye da da.

Shigar ta restaurant din kujera ta ja ta zauna. Ganin yadda ta zauna hannun ta rike da kan ta ya sa daya daga cikin yaran wajan ta zo ta ce da ita
“Lafiya kuwa?”
Ba ta kai ga amsawa ba ta ji an ce
” Ina fa lafiya ta ga katon saurayin da ta mara a tsakiyar mutane…..toh laifi na ne dai har yau ban sani ba fa Mama na…. ” ya karasa yana maida akalar maganar ga Amatullah.

Baki bude yarinyar ke kallan Amatullah cike da mamakin furucin Dee Yusuf wanda ta ke da yakinin zolaya ce dai irin tashi, ganin yadda Amatullah ta yi tsuru-tsuru da idanu, yayinda tsoro ya ƙara bayyana fuskarta domin kuwa ba ta san ya biyo ta ba. Yanayin da ta gan Amatullah ne ya sanya yarinyar mayar da kallan ta ga Dee Yusuf, wanda kallo daya za ka ma sa ka tabbatar da jin daɗin yanayin da ya jefa Amatullah ciki, domin kuwa murmushi ne kunshe a fuskar shi. Ganin abin ya fi karfin ta sai ta yi gaba abinta ta bar Amatullah da Dee Yusuf da ya sa ta gaba ba tare da ta ƙara ce da su kanzil ba.
***
Wasa ta ke da ledar abincin da ke hannun ta, neman hanyar guduwa take don ba ta ƙi ta buɗe idanu ta ganta a kan gadonta ba. Gyaran murya yayi wanda hakan ya sanya ta daga ido ta kalle shi. Ta tsinci kanta ta na mai nazartar fuskar shi a karo na farko, Fari ne amma ba irin sosai din nan ba, ya na da dogan hanci har baka, yawan suman kan shi da wanda ya zagaye fuskar shi ne zai tabbatar ma ka da wadatar sumar da ke tattare da halittar shi.
“Kyakkywar fuskar da na mara kenan”
Furucin Amatullah a zuci kenan, kamar ya sani ya ce

“Ke na ke sauraro? Me na yi da na cancanci mari? Ki fada min Mamana”

Kamar an aje dutse “uhum” ba ta iya furtawa ba balle ta bashi amsa, sun kai kusan minti biyar a haka, ita dai ta sunkuyar da kai ta na wasa da ledar hannunta, shi kuma ya tsare ta ido. Tun da ya ke a rayuwar shi be taba ganin yarinyar da ta tsaya ma sa a rai ba kamar wannan da ke zaune gaban shi, ga ta dai da ka gan ta ka ga mai karancin shekaru, amma yanda ta iya duban tsabar idanun shi ta sharara masa mari babu gaira babu dalili shi ne babban abin da ya tsaya ma sa a ran shi. Wai shi Dee Yusuf mace ta mara a cikin Samaru, ba ma jama’ar wajen ba shi kan shi ya na jinjina abin, dan ma in da Allah ya taimake shi ba tare da abokan sa ya ke ba, su ma labari su ka ji daga baya da ya kade har ganyen sa, yanzun ma neman yarinyar da ta mari Dee Yusuf su ke ido rufe.

Wayar shi da ta fara kara ne ya katse masa tunanin da ya ke. Ganin wanda ke kiran sa ne ya sanya shi sake duban Amatullah tare da fad’in
“Wannan uzuri ne babba, amma za mu sake haduwa, lalle na cancanci a min bayanin dalilin da ya sa aka mare ni Mamanaaaa” ya ce yana mai jan kalmar karshe.
Da wannan ya juya ya fita yayinda ya shiga amsa wayar ta shi. Sai bayan fitar shi da kusan minti biyar ta iya sakin ajiyar azuciya, a sannan ta lura da irin kallan da jama’ar wajan ke mata, idanun kusan kowa na wajen kanta ya ke. Da saurin ta mike tsaye, ta na mai fatan Allah Kar ya sake hada ta da wannan bawa na shi. Allah kuwa ya amshi addua’ar ta har ta kai hostel babu shi babu alamar shi.

Shigar ta daki ta yi sa’a babu kowa ciki, daga wacce ta tafi karatu sai wacce ke jarabawa. Bisa gado ta kwanta, gaba daya abuncin ma ya fita kan ta, Dee Yusuf da furunci sa ke mata yawo, tsoro na shigarta a hankali, duk iya tunaninta ta kasa gano mutum ɗaya a dangin ta da zai tsaya mata in zancen zai kai ga hukuma.
Tunawa da artabun da aka sha kafin Baban Sasa ya amince da karatunta kaɗai ya sanya ta cikin tashin hankali. Daɗin ƙarawa rikicin nata ba da mace ƴar uwarta ba da namiji, tilawar da ta haddace shine “babu ke babu ɗa namiji, mijinki saifullahi na dawowa daga Rasha zan ɗaura aure ku” karatu ne da duk ta je gaida baban Sasa sai ya biya mata, yanzu kuma sai a ce gata an kore ta daga jamia saboda ta yi faɗa da namiji.
“Me ya kai ni fitan karatun dare” tace hawaye na zubo mata sannu a hankali, hakan ya sa yin kuka ma’ishi sannan ta fara tuna asalinta don gaba ɗaya ta sadakar koranta za ayi

***

28th September 1989

Gidan Jamoh babban gida ne a unguwar Amaru cikin birnin Zaria. Gida ne ginin ƙasa wanda ke da sassa daban daban. Sun kasance cikin kason zage-zagi da aka fi sani da mallawa, wainda tarihi ya nuna suna cikin jinsin Zazzagawa uku da ke da gadon sarautan ƙasar Zazzau watau Mallawa, Katsinawa da Barebari.
Babba da yaro da ga tsatson gidan Jamoh na da kwale bibbiyu a duka gefen fuskarsu kamar kowane Bamalle.
Sanyin iskar damuna ke kaɗawa ƙarfe tara na safiyar Alhamis na ashirin da takwas ga watan Satumba shekara alif ɗari tara da tamanin da tara, Hakan bai hana tsoho Jamoh zama akan kujerarsa ta azara da yake shan hantsi duk safiyar duniya yana mai sauraren radiyo a ƙasar bishiyar da ya yalwata Inuwa a tsakiyar gidan.
“Baban Sasa! Baban Sasa!!” yaro ɗan kimanin shekaru takwas ya sheƙo da gudu yana faɗi.
“Ja’iri! Sai kace ni ubanka ne, karar min da sunan za ka yi” tsohon ya faɗi cikin sigar wasa. Dariya Yaron yayi yana mai zama akan cinyarsa.
“Innarmu ce tace in zo in faɗi maka Goggo Mairo ta sauka an samu yarinya” yace cikin murna yana yi yana wasa da gemun tsohon nan.
“Madallah ka ce mun yi mata, dena ja min gemu salon ta ce kai take so ba ni ba” ya karasa yana mai ɗaga Yaron sama ba za ka ce yana da karfin ɗaukan Yaron nan ba in ka kalli furfuran da ya rufe masa fuska. Sashin ɗansa ƙarami a maza ya je don ganin abin da aka haifa, saboda ya san ƙaidar sa ce duk aka haihu da an kimtsa shine mutum na farko da yake fara gani, Hakan aka yi a haihuwa talatin da uku da yaransa maza su ka masa ciki kuwa har na yau.
Addu’a yayi mata haɗe da huɗuba tare da raɗa mata suna kamar yadda yake yi a saura, in yayi ba ya faɗi ma kowa sai babban Ɗansa Zubairu.
Alhaji Jamoh Bamalle ne Usul, sannan shine cikakken ma’anar maraya, don yana da shekara ɗaya da rabi mahaifiyarsa ta rasu, bai cika shekaru biyu ba Allah ya ma mahaifinsa rasuwa.
Ya taso cikin gararanba a tsakar gidan babban gidansu, cikin ikon Allah lokacin da aka zo aka bukaci masarauta su ba da sunayen wainda za su je karatun boko wani kawunsa da ke aiki a fada ya bada sunansa.
Hakan ya sanya yayi karatu har ya kammala makarantar Barewa College wanda a lokacin sunansa Kaduna college kafin daga baya ya zama Govt college Zaria kafin daga baya ya koma Barewa college.
Tun bayan da ya kammala da shahadar grade II ya samu koyarwa a firamare bai sake komawa aji ba, da albashin sa ya auri matansa uku, da albashin sa ya raini yayansa goma sha shida inda ciki biyar ne mata saura duk maza ne, da Albashin sa ya mallaki filin nan har ya gine in da ya zama musu babban gida a yanzu a nan yaran sa duka goma sha ɗaya ke zaune da iyalinsu.
Hajiya Sahura itace uwar gida, yaranta takwas, Zubairu shine babba, sai Idris, sai Hamza, sai Hadiza, Madina, Bilkisu, Yusuf sai autanta Salihu.
Hajiya Talatu ce mata ta biyu a gidan ita yaranta shida duka maza, Anas, Dahiru, Yunusa, shuaibu, Mahmuda sai ƙaraminsu Muhammadu.
Amarya da yaran ke kira da Goggo Kadarko tun da ta haifi yan biyu Hasana da Husaina Allah ya mata cikawa, haka hajiya Talatu ta haɗa da nata yaran ta rike.
Daga Salihu sai yan biyu a tsarin shekarun yaran gidan Hakan ya sanya su ka taso su uku kamar yan uku, yana da shekara goma sha biyar su yan biyu na da sha uku aka tashi auren yan biyu, yayi kuka kamar ransa zai fita saboda shaƙuwa da ke tsakanin su, tun bayan aurensu ya maida hankali a karatun bokonsa don yana ganin shi kaɗai ne zai ɗebe masa kewa.
Yayi karatu har matakin digiri a Fannin sadarwa sannan ya samu aiki da radiyo Nijeriya Kaduna kafin yayi aure.
Aurensa na cikin auren da aka yi shelarsa a jihar Kaduna saboda duk maabota sauraron radiyo sun san Salihu Jamoh da shirye shiryensa masu ƙayatarwa musamman shirin jakar magori.
***
Aurensa da mairo ya samar da karin arziki ta wajen sa don bayan auren ya samu ƙarin girma a wajen aiki, sannan gidan an samu yalwan arziki sannan ita kanta kullum cikin yi ma mutane ihsani take da kaɗan din da ta mallaka. Hakan ya sanya surukan son mairo fiye da sauran matan yayan.
Tun ana ƙirga watannin auren har aka fara ƙirga shekaru Mairo ko ɓatan wata ba ta yi ba, nan matan yan uwa Salihu su ka sa mata karan tsana, amma duk sanda su ka jefeta da sharri sai ta maida musu da Alkhairi. Yayin da Allah ya azurta ta da cikin sai su ka fara zunɗenta suna fadin ƙaba ke damunta. Hakan bai sa ta canza musu ba ko ta neme su da sharri kullum dai Alkhairi, babu inda ta ke jin sanyi sai wajen matar Anas mai suna Hama, ita ce ta tsaya mata har ta sauka lafiya sannan ta aika ɗanta Saifullahi ya je ya isar ma kakansa Jamoh albishir ɗin haihuwa.
***
Ranar suna aka sanar da sunan jaririya a Amatullah, an yanka rago an ci abinci a wadace an sha kowa yana cikin farin ciki.
Rayuwar Amatullah ta kasance cikin gata, haihuwarta ta buɗe ma iyayenta samu yaya don duk bayan shekara biyu sai Goggo mairo ta haihu.
Amatullah na da shekara uku ta fara bin yayyinta na gidan zuwa makarantar Allo, tun ba ta fahimta har ta fara ɗaukan karatu.
Ko da ta kai shekaru shida aka sanya ta a makarantar islamiyyah kamar sauran yayyinta, gaba ɗaya rayuwarta sai ta zama daga sallan asuba za ta je Allo, ana tashin su karfe bakwai da kwata, nan za su dawo su karya sannan su tafi makarantar boko, su taso karfe ɗaya su ci abincin rana su huta ƙarfe hudu su tafi islamiyyah sai kuma shida, bayan sallan isha’i kuma su yi karatu da dare in da yayyinsu ke musu bitar karatun islamiyyah da Allo.
Amatullah hazikace mai saurin fahimtar karatu sannan ba ta da mantuwa Hakan ya sanya da wuya a yi jarrabawa ba ta zo na ɗaya zuwa na uku ba. Da wannan kokarin ta kammala firamare ta shiga sakandire na boko da islamiyyah.
Tana da shekara goma sha hudu aka aurar da sa’oi’inta da ke gidan bayan sun kammala hadda izu arba’in, da kyar Baba Jamoh ya amince da cigaban karatun Amatullah Shima bisa Yarjejeniyar ba ta da miji sai Saifullahi a cewar sa tun kafin ta kama nonon uwarta ya ma Saifullahi alkawarin auren Amatullah.

***

Da taimakon fitar Saifullahi karatu ƙasar waje ya sanya Amatullah kammala karatun sakandire, samun kyakkyawar sakamako ya sanya mahaifinta rokon Baba Jamoh akan barinta zuwa jami’a, da kyar ya amince bisa sharaɗin ko bayan ba shi aka aura Amatullah ga wanin Saifullahi bai yafe ba.
Wannan alkawarin Salihu Jamoh yayi shi a gaban dukkan yayyinsa da ita kanta Amatullah da mahaifiyarta.
“Ni dai in karanta pharmacy shi ne damuwata, ko wa Baban Sasa ya so ya aura min” tace a ranta tana murnar amincewar kakanta tsoho mai ran ƙarfe mai ikon akan Ahlinsa.
Bisa wannan Alkawari ta fara karatun Pharmaceutical science a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, nisa da rashin son zarya ya sanya mahaifinta tura ta hostel cike da yaƙinin za ta kama kanta kuma za ta zo da sakamako mai nagarta.

Wannan kenan.[1/8, 11:26 PM] Safiyya Ummu-Abdoul Writer: *previous post da ɗan kuskure*

FIKRA WRITERS ASSOCIATION

TAZARAR DA KE TSAKANINMU 🤦🏼‍♂🤦🏿‍♀

✍🏾KHADIJA SIDI & SAFIYYAH UMMU-ABDOUL

BABI NA UKU

A bakin gate ta iske abokan tafiyarta, nan su ka mata caa kowa da abin da yake tambayarta.
“Cewa yayi yana sonki hala” shine tambayar da ya fi tsaya mata, Zulaikha dai bata ce komi ba don ta san ita ɗin mai laifi ce.
“Haka kawai sai ya ce yana so na? A wajen photocopy fa muka haɗu kwanaki banda canji ya bada Naira 20 din ni shaf na manta ma” ta samu kanta da zabga ƙarya don bata son wani abu ya fito na abin da ke tsakanin ta da Dee.
“Har na fara murna, don wallahi ko ni da nake matar aure ina kyasa Dee Yusuf, in fa ya ce yana sonki mu ɗin gaba ɗayanmu za mu shiga wani sawu na masu aji ne” Faɗin Zuwaira da su ke kira da maman Jaafar. Ajinsu ɗaya, a shekarun za ta girme su amma kuma ƙawarsu ce, yanzu ma kasuwar da za su shiga ita za su raka siyayya.
Ba ta ce komi ba amma ita da ta san alkawarin da ke kanta ta san hakan ba mai yiwuwa bane ko da a ce shi ɗin kimtsattse ne ba tambaɗaɗɗe kamar yanda ta ke kallonsa ba.
Da hirar Dee Yusuf su ka isa kasuwa, ita dai jin su take yi don ba su isa kasuwa ba har sai da kawayen ta su ka hasko kalan yaran da za su haifa in aurenta da Dee Yusuf ya tabbata.
Daga kasuwa gidajensu su ka wuce suna fatan Allah ya Raya su zuwa sati biyu da karatun zango na biyu zai kankama. Sai a lokacin Amatullah ta samu ta keɓe da Zulaikha saboda su biyun hanyarsu ɗaya.
“In kashe ni za a yi ma kawai a kashe ko? ke babu abin da yayi tsalle ya tsinka miki mari” Amatullah ta ce tana hararar Zulaikha.
“Afuwan bibty, kin san na yi tunanin in na tsaya saura ma za su tsaya kuma ba zamu iya daƙile zancen ba, me ya ce miki?” ta ƙarasa tana mai neman karin bayani akan abin da ya wakana tsakanin kawarta da dodonta.
“Me kuwa zai ce min, da na gaji da tsayuwa ba tare da ya ce komi ba na yi wucewata na bar shi tsaye” Amatullah ta samu kanta da yin ƙarya a karo na biyu.
‘wai me ye kike ɓoyewa ne’ ta samu zuciyar ta da faɗi.
‘ai sirri da daɗi’ ɗayan sashi na zuciyar ta ke bada wannan amsar.
“Toh Allah shiga tsakanin nagari da mugu” ta tsinkayi zulaikha da faɗin haka. “Aameen” tace tana canza labarin su zuwa ga batun jarrabawar da su ka yi a ranar.
***
Sai da la’asar ta shiga gidan su, nan ta iske yan uwa da iyayensu kowa yai mata murnar kammala jarrabawa da fatan samun nasara.
“Baba mun dawo, ya karfin jikinka” tace yayin da ta shiga ɗakin baban Sasa, Shima addu’a ya bi ta da shi sannan ya ce da ita
“Ina so na shaida aurenku Baiwar Allah! Na ce a kira min Saifu, don ba zan so ƙasa ya rufe ido na ban cika ba, tun da har Allah ya bani tsawon ran kaiwa lokacin da duk kuka isa aure” jin sa take yi yayin da idanunta ke kallon laɓɓansa yana faɗa mata su, sai a lokacin ta ga tsantsan kamanninta da shi, sai a lokacin ta ke yarda da zancen da ake na suna kama da Saifullah don tun tana yarinya ta haddace babu mai kama da Baban Sasa sama da Saifullah.
“kin yi shiru Amatu” yace yana taɓo ta.
“Baaba, ashe haka nake kama da kai” tace tana dariya ƙasa ƙasa, shi ma sai ya shiga dariya.
“kin ga kenan duk wanda ya shiga gidanku zai tuna da ni ya min addu’a” ya ce cikin dariya. Haka su ka dinga tsokanar juna cikin nishadi, kiran sallan magariba ne ya tayar da ita bayan ta sa masa ruwan alwala a buta.
***
Yana zaune a harabar sashin su a jami’ar kimiyya na gwamnatin ƙasar Rasha da ke birnin Moscow watau MATI Russian State Technological University Moscow, tattaunawa su ke yi da abokan karatunsa akan sabuwar injimin da su ke kerawa don wani baje koli da jami’ar ke shirin aiwatarwa nan da kwana biyar, a nan wayarsa ta ɗauki ƙara. Kamar ba zai ɗauka ba amma jin kiɗan da ya tanadar ma jininsa ne ya sa shi saurin ɗauka, tsoronsa kar a ce Baban Sasa ne ya rasu, don shi ya san son da yake ma tsohon nan ko iyayen sa albarka.
“excuse me” ya ce yana mai zuwa gefe tare da tattara duk wani natsuwa da ya mallaka ya doka sallama bayan ya ɗaga.
“Saifuna ba zaka dawo in ganka ba” yace cikin halin ciwo.
“Alkawari Baba ba zan ƙara sati biyu ba, kai dai kar ka yarda ka bi su ko sun zo ɗaukan ka” yace cikin shaƙiyanci hakan ya sanya baban Sasa tuntsirewa da dariya. Ya tambaye shi jikin sa, da sauran ahlin nan ya amsa yana mai ƙara jin jinjina masa zancen zuwansa. A haka su ka yi sallama, ya koma wajen abokan karatunsa yana mai ba su hakuri.
Kwana goma ya ƙara akan ranar da su ka yi waya jirgi ya sauke shi a filin jirgin sama na murtala Muhammad da ke birnin ikko ƙarfe goma sha biyu da rabi na dare.
Kallo ɗaya za ka masa ka san bakin fata ne duk da rinewar da fatarsa ta yi ya rikiɗe kamar wani bakin bature. Shi ɗin ba wani dogo bane sannan babu mai kiransa gajere, zanensa na mallawa na kwance a gefen fuskarsa hakan na ɗaya daga cikin abin da ke ƙara maida fuskarsa abin kauna ga mata kamar yadda wata budurwar sa ta faɗa masa.
Daga ikko jirgin da ke tashi zuwa Kaduna ƙarfe shida na safiyar washegari ya bi, daga nan ya ɗauki shatar mota har Amaru.
Babu zato su ka tsinkayi muryarsa yana sallama, nan gida ya kacame da murna, duk ihun da ake Amatullah na zaune a ɗaki bata ko motsa ba cike take da fargaba da tsoro, cigaba da karatun ta tayi a cikin littafin Nurturing Eeman in children na Dr Aisha Hamdan. Wannan shine ɗabi’ar da ta fi so in ba ta komi toh ta samu littafin ƙaruwa na addini ta dinga karantawa.
***
Tun da ya shigo gidan idon sa ke kan yan matan da yake gani yana kasa kunnen wacce za a kira da Amatullah, dukkansu babu na yarwa saboda wasun su na da gaɓa-gaɓan jiki wasu kuma yan firit amma duk kyawawa ne daidai misali.
Bai manta hotonta da ya gani ƙarshe shekarun goma da suka wuce ba, ko a lokacin ya san ita din mai kyauce da abokansa za su yaba da ita. Bare kuma yanzu da aka ce ta shiga Jami’a, ya san zai same ta da wayewa, dan shi a rayuwar sa ya na san wayayyiyar mace.
Sunaye mabambamta ya ke ji ana kira duk babu Amatullah har dai ya hakura tare da sa ran ko tana makaranta ne.
Washegari Zulaikha ta kawo mata ziyara tare da duba jikin Baban Sasa, sun fito za ta raka ta ne su ka ci karo da shi a ƙofar gida. Sun gaisa cikin mutunci su ka wuce yana mamakin yanda duk in da ya gilma cikin zaria mata sanye da zumbura zumburan hijabi, su wainnan ma abin takaici har da safa ko me su ke rufewa oho ‘watakila kutare ne’ ya samu zuciyar sa da fadin haka. Tsaki yayi ya cigaba da abin da yake a kan wayarsa, a haka ta dawo, ta sanya kafa ɗaya kenan a cikin gidan kenan ta jiyo muryar yar gidan goggonsu ta bayanta tana fadin
“A’ah su Amatullah yan boko ne a garin” Hakan ya sanya ta juyowa cikin fara’a tace
“A’ah su matan aure ne a garin” nan su ka sa dariya, Hakan ya zama sarar su duk suka haɗu sai su yi amfani da kasancewarsu abokan wasanta su gasa mata magana akan rashin aure da boko. Shi ke nan da sun kira ta yar boko sai ta kira su matan aure.

Gaida Saifullahi tayi ya amsa kamar ya haɗe su ya maƙure, bakin cikin da ya saukar masa ba ƙarami bane don kwata-kwata bai sa ma ransa ko a mafarki aure zai haɗa shi da bagidajiya ba.
“Kai impossible!!!” ya faɗi Yana mai mikewa zuwa cikin gida don dai ya tabbatar wannan mai lullube jiki kamar raguwar kuturta ce matar da yake hasko su tare.
Yaro ya gani a yana wasa a tsakar gida daidai inda yake wajen zaman baban Sasa, tuno murnar da yake ciki lokacin da ya faɗi albishir din haihuwan yarinyar da aka ƙaƙaba masa da ada murna yake amma a yau gani yake babu bakin fata sama da haka.
“kai shiga ka kira min Amatullah” yace ma Yaron cikin tsawa-tsawa, a firgice Yaron yayi cikin gida yana mai kiranta.
Sai da ta ɓata kusan minti talatin kafin ta fito wanda hakan yayi nasaran ƙara harzuka shi.
Sanye take cikin hijabi ruwan bunsuru ko ganin atamfar da ke karkashi ba ayi, baƙar safa ce a kafafunta hannayenta duk suna cikin hijabi Hakan ya sanya babu abin da ya bayyana a gareshi face fuskarta.
“Assalamu Alaikum” tace cikin sanyin murya, kallon ta yake, fuskar nan nata sai sheƙi yake yi saboda rashin hoda, amma hakan bai hana kyawunta fitowa ba.
“ina yini” ta ƙara duk da kunnuwanta ba su ji ya amsa sallamar da tayi ba. Nan ma bai amsa ba, sai ta basar ta tsaya abin ta. Kallonta yake tun daga kai har ƙafa yana jin wani kyankyaminta na cika shi.
“Kinga, this will be the first and the last time da magana zai haɗamu, you better find your self a husband, amma ba Saif ba!, ki sani cewa akwai Tazara a tsakanin mu! Bana na san kauyanci! Ba na san gidadanci!! Kinga malam Sambo da ya kika yi allo a wajensa, shi yafi dacewa da ke not an engineer” Yana gama faɗi ya tsidda miyau ya wuce ya barta a daskare. Da kyar ta iya jan kafafun ta ta shige gida, idanun ta cike da kwallar bakin ciki, shin ita bagidajiya ce? Toh me mai ta ma sa na kauyanci da gidadanci?. Abun da ta ringa jinjinawa cikin ranta kenan.
***
Tun daga ranar ba su sake haɗuwa ba, ta kiyaye haɗuwarsu ta maida hankali a karance-karancenta.
Yau ma kamar kullum zaune take tana karatun “You can be the Happiest woman in the world” na Dr. Aid Al-Qarni, ta baje a falonsu, sanye take da riga da skirt dinkin zamani da ya ɗame ta, nan ta jiyo sallamarsa, bai jira amsarta ba ya kutso ciki, wani irin tsalle tayi ta jawo hijabinta da ta sarkafa a jikin ƙofa ta shiga kokuwan sawa, da ya ke hankalin sa na bisa wayar sa da ya ke ta faman dannawa nan ta ci sa’ar sanya hijabin kafin ya ankara da ita, har dan nufashi ta ke mayarwa cike da godiyar Allah. Kallon ta ya ke cike da kyama ya furta “Ina goggon”
“Suna wajen baban Sasa” tace masa. Har ya juya zai fita sai kuma ya sake dawowa, idanun sa kan ta ya kira sunan ta
“Amatullah!”

Daga idanun ta ta yi ta dube shi ba tare da ta amsa ba, irin kallan wulakancin da ta gani a idanun sa ya sa ta yi saurin kawar da kai. Bai gushe ba, ya cigaba da magana cike da nuna isa.
“Ina so ki fahimce ni, ba na son ki ba na kaunar ki, sam ba ki min ba, akwai yarinyar da na ke so…..”
Kamar takobi haka ta ji maganar ta shi ta soki kirjin ta. Shi kuwa ko a jikin sa ya kara da “dama biyayya ya sanya da zan yi jihadi na aure ki, toh amma sam ban yi tsammanin haka ki ke ba, ni wayayye ne, ina bukatar wayayyiyar mace cikin rayuwa ta!! Na tabbatar cikin samarin unguwar nan ba za a rasa local champion da ke son ki ba, ki rufa ma kan ki asiri ki fito da shi, na tabbatar idan su ka ga dukkannin mu da wanda mu ke so, Baban Sasa zai janye wannan alkawari na shi mai muni, kin gane ko?”
Har ya kare maganan shi idanun Amatullah na kan ƴan yatsunta da ta ke wasa da su, tun da take a rayuwarta ba’a ta taba wayan gari ta na ƙin wani ko wata cikin ran ta ba, sai na wannan bawan Allah da ake shirin ɗaura ma ta aure da shi, ba don komai ba sai don kyama da ya nuna kiri kiri gare ta.
“Ba da ke na ke magana ba?”

Shiru ta masa kamar ma ba ta san yanayi ba wanda hakan ba karamin sosa ma sa rai yayi ba, Wai yarinya bagidajiya bakauyiya sai shegen girman kai da jin kai. A fusace ya furta

” Wato ki na ji na ba za ki tankaba ko? Toh ki saurare ni da kyau! Muddin ki ka bari aka ɗaura wannan aure tsakaninmu, ki ka shigo gida na wallahi sai na lahira ya fi ki jin dadi!!! Bagidajiya sakarya kawai!!!!!!!”
Ya na gama magana ya fice a fusace, nan Amatullah ta kwantar da kan ta bisa kujera yayinda kwallan da ta yi kokarin rikewa su ka shiga gasar kwarranya daga idanun ta, fadi ta ke
“Inna lillaahi wa inna ilaihi rajiun, ya Allah ban iya ba, ya Allah ka iya min! Ya Allah min takangar karfe da wannan bawa na ka Agithnee Yaa mugithu!”

A wannan halin Gwaggo ta same ta, cikin tashin hankalin ganin halin da Amatullah ta ke ciki ta shiga tambayar ba’asi. Duk zurfin ciki irin na Amatullah ba ta boye mata ba, ta kwashe duk yanda su ka yi da Saifullahi tun daga ranar da su ka fara magana har zuwa yau. Jikin Gwaggo yayi sanyi, ta na mai duban Amatullah wacce in banda sauke ajiyar zuciya babu abin da ta ke yi tsabagen kukan da ta sha. Cike da tausayawa ta ce
” Amatullah ni na haife ki, ba zan so na cutar da ke ba, Baban Sasa mai kaunar ki ne, ba zai cutar da ke ba, ina mai baki shawara ki karfafa addu’a ga ubangijin ki, Allah zai fishe ki alkhairi. Amma ko da wasa kar ki tunkari Baban Sasa da wannan batun, shi Saifullahi da ya ke ganin an ma sa ba daidai ba shi ya je ya same shi ………”
“Wallahil azim Gwaggo ba na san shi nima!!”
Amatullah ta katseta cikin kuka.
“Shhhhh! Kar na sake jin kin furta haka, ki dai yi addu’a, ki rufa mana asiri kar a ji wannan magana daga bangaranmu, ki bari shi can ya je ya shaida mu su, kin ji ko?”
Kai ta gyada alamar “eh”

“Tashi ki yo alwala ki yi sallah na san ko azahar ba ki samu kin yi ba, Allah ya yi miki albarka, kar da ki yarda maganar ta dame ki, idan ya rasa ki shi yayi rashi babba, babu kauyanci ko gidadanci tattare da ke Amatullah, sai tarbiya, kunya da yakana. Allah wadar wayewar ta shi da ya ke so. Inshallahu Allah zai shige mana gaba”

Da haka ta sami kwarin gwiwar dauro alwala. Nan ta kalli gabas ta shiga kai kukan ta ga mai duka.

***
Amatullah ba ta sake jin dadin gidan nan ba sai ranar Allah ya sa ta koma makaranta. Duk yanda kalaman Saifullahi su ka so tunzurata ta sami Baban Sasa ta akan rushe maganar auren su abin ya ci tura, ta yi kokarin jurewa ba dan komai ba sai dai alkawarin da daukarwa kan ta da Gwaggo, na duk kiyayyar da take ma Saifullahi ba dai a ji maganar daga bakin ta ba kamar yadda ya ke da buri, sai dai aji daga wajansa. Sati biyun da ta yi a gida har ta rame, ta rage walwala da kuzari. Kullum cikin tunani ta ke hatta lectures ma ba ta samu ta mayar da hankali ta gane a cikin aji. Tun Zulaikha na tambayar abin da ke damun ta, har ta gaji ta zubawa sarautar Allah ido.
Yanzun ma daga aji su ka fito, tun da Lecturer ya shiga har ya fita babu abin da ta gane, gaba daya hankalin ta ba ya ajin. Tunanin lafazin Saifullahi na cewar idan ta sake aka aura ma ta shi sai na lahira ya fi ta jin dadi ne ya addabi rayuwatar.
“Haba mana Amatullah!!!”
Zulaikha ce ta faɗa ta na me jijjaga kafadar Amatullah, wacce ta yi firgit ta dawo daga kogin tunanin da ta tsunduma. Ajiyar zuciya ta saki ta na mai duban Zulaikha ta ce
“Afuwan yar uwa, me ki ke cewa?”
Cikin damuwa Zulaikha ta furta
“Wai me ke damun ki ne Amatullah? Yau sati guda da dawowar mu na lura gaba daya kin canza, kai wannan damuwar da ki ke ciki har tafi sanda ki ka mari Dee Yusuf…..”
“Dee Yusuf…..”
Amatullah ta maimata, ikon Allah ashe akwai damuwar da zai sa ta manta da Dee Yusuf duk tsoran sa da take ji, abun da ta fada cikin ranta kenan, ta tsinci kan ta tana kewan ganin shi, a zahiri kuma cewa ta yi
“ke ni na sha’afa da lamarin wannan mutumin shaf, Allah ya amsa addu’a ta ya min katangar karfe da shi”
“Idan ba Dee Yusuf ba menene damuwar ki Amatullah”
Zulaikha ta sake tambaya. Kallon Zulaikha ta ke cikin nazari, kamar yanda ta ke sanye da hijabi, ita ma Zulaikha hijabin ne jikin ta, har kasa kuwa. Kai ta girgiza ta na mai fadin
“I’m very fine, kar ki damu dani kawata, bari na je KIL akwai wani littafi da na ke nema, daga nan sai na bi wannan course din da mu ka yi wallahi, wallahi sam ban gane shi ba”
Cikin nuna rashin gamsuwa Zulaikha ta amsa ma ta da “Ba dai za ki faɗa min abin da ke damun ki ba, ai shikenan duk sanda ki ka shirya magana ina nan Amatullah, adawo lafiya, Ni ban zuwa KIL daga dawowa ta makaranta”
Dariya Amatullah ta yi jin furincin Zulaikha na ba za ta je library ba. ” Dama ai na san ba zuwa za ki yi ba shi ya sa ban mi ki tayi ba, kin ga tafiya ta, sai na dawo”
“Allah ya raba ki da ganin Dee… ” Cewar Zulaikha cikin zolaya, juyawa Amatullah ta yi ta na murmushi, akaro na farko da ta ke jin da za ta gan shi ma ai ba wani abu ba ne, duk kauyancin ta ya na jure tsayuwa da ita, ba kamar Saifullahi ba ….
Nan ta kwabi zuciyar ta daga tunanin Dee Yusuf har tana gama shi da Saifullahi. Cikin sauri kan ta a kasa ta nufi hanyar da za ta sada ta da KIL. Ta gaban library ta hangi taran samari, dan haka ko da ta zo dab da su sai ta yi kasa da idanun ta, kafafun ta har hardewa su ke tsabagen tsarguwar kar dai kallon ta su ke, musammam yanzu da ta san ita ɗin bagidajiya ce yar kauye a cewar Saifullahi. Ilai kuwa ashe tun tahowar ta ya kafa mata idanu, gaba ɗaya hankalin sa na kan ta yana mamakin yanda a duniya ya sha ganin mata ma su saka hijabi ba wai a ABU kadai ba, amma bai taɓa ganin wacce shigar ke mata kyau ba kamar Amatullah. Ta gaban su ta gifta, ya tabbatar ba ta lura da shi ba, hankali kwance ya daɗa gyara tsayuwa, cikin ran sa faɗi ya ke

Leave a Comment