*SUN YI MIN ILLAH*
*SUMMY M NA’IGE*
*FIRST CLASS WRITER’S ASSO…*
*SHAFI NA ƊAYA*
Da ma ashe haka duniya take mai halin ɗan mangwaro? Me na yi musu ko sun manta kowa da ƙaddararsa a tsarkakken allo. Ban san inda zan saka raina na ji sanyi ba. Ya zan yi na sauya ƙaddarata ko zan kasance yar adam kamar kowa lallai sun yi mini babbar illa wadda har duniya ta naɗe ba zan daina cin gajiyar raɗaɗin ƙonar zuci ba.
Cikin sauri ta shiga gidan, bayan matar gidan ta karɓa mata sallama sannan ta fito. Gani ta da ta yi ne lokaci ɗaya ta ɓata fuska haɗi da jefa mata tambaya, “me ya kawo ki gidana?”
Ƙasa ta yi da kanta sai da ta yi raurau da ido kamar mai koyon magana ta ce,
“Daman na zo ne ko akwai aikatau?”
Kallon ta ta yi a walaƙance sannan ta ya tsuna fuska ta ce,
“Za ki iya wankau na yara kala naire goma!? idan ba za ki iya ba bi ta inda ki ka fito.
Ta faɗi haka haɗi da nuna mata ƙofar fita da yatsa.
Kanta ta yi ƙasa da shi, haɗi da tunanin baya, gashi baya bata dawo wa bare ta yi ƙoƙarin gyara kaddarata, dama duniya haka take me halin ɗan magoro, yaranta da ta tura makaranta ta tuna da su, kuma gashi sun tafi makaranta ba abin da suka ci, sanin suna kan hanyarsu ta dawo wa ne ya sa ta ɗago kanta cikin hanzari ta ce,
” Zan iya Hajiya”.
Tsaki wannan matar ta yi sannan ta shiga ɗaki ta ɗauko kayan yara masu muguwar dauɗa, kamar waɗanda aka yi wasan tsere da su.
Haka ta duƙa ta fara wankau har sai da hannuta ya ji ciwo, sosai ta sha wuya kafin ta kammala, tana idarwa ta gayawa matar, dubu ɗaya ta ɗauko ta bata, ta ce,
” Ƙuɗinki ɗari uku ne, ki cire kuɗinki ki kawo min sauran canji”.
Sai da ta rusunan kamar maroƙi ya je bara sannan ta karɓa haɗi da yi mata godiya. Cikin hanzari ta nufi mai shago, garin kwaki ta sayo iya na kuɗinta sannan ta shiga ta bawa Hajiya canjinta, gab da za ta fito gidan ƙofar gidan ta riƙe ledar garin ya zube ƙasa gaba ɗaya. Lokacin da idonta suka sauka kan abin da ya same ta ba ta san lokacin da hawaye suka sauka a idonta ba, zazzaɓin da take ji ne tun safe ya sake rufeta, da ƙar ta iya tashi ta koma gida cikin tashin hankali. yaran ta tuna me za su ci idan sun dawo? Musamman Afiyya da bata da haƙuri, sosai ta san Afiyya ba ta da hakuri, don halinsu ya babbanta da na Husnah, kamar yadda sararin samaniya ya yi hannun riga da ƙasa, to haka ta san halin su ya babbanta. duk da wannan halin da take ciki ta yi alƙawarin ba za ta nemi taimakon kowa ba, bale har a koma yi mata lllah.
Tana cikin wannan halin ta ji sallamarsu, cikin hanzari ta miƙe da ga kwanciyar da ta yi haɗi da goge hawayen da ke mata kwaranya.
” Ammi! Ammi! Ina abincinmu yunwa nake ji ?”
Abin da ta ji Afiyya na faɗa kenan tun kafin ta ƙaraso cikin ɗakin da take.
Cikin ƙarfin hali ta tashi haɗi da faɗar,
” Kun dawo?”
Husnah ta ce,
“Mun dawo Ammi”.
Tun kafin Afiyya ta sake buɗa baki ta yi magana Ammi ta ɗau mayafinta ta ce, “zan je na karɓo muku abinci, kar ku fita kun ji”.
Haka ta faɗa jikinta sai rawar zazzaɓi yake kamar wadda ta ji tashin gangar makiɗi. Tun kafin su yi magana ta fice gidan, ko da ta fita ta jima tsaye ta rasa ina zata dosa, wa zai taimaka mata ya kawo mata a gaji, duk da ita aka yi wa illah amma kowa ya gojeta, ko sana’a ta kasa ba mai saye ina zata sa kanta ta ji daɗi. Tafiya take tana tunani har ta kusa fita unguwarsu, a haka aka fara kiran sallah magarb waje ta samu ta rakuɓe ko zata samu ta gabatar da sallah.
Hankalin Husnah ya tashi lokacin da ta ga Afiyya ta fara rera mata kuka yunwa take ji, kuma gashi har duhun dare ya kama amma Ammi har yanzu babu ita babu labarinta.
Suna cikin haka sai suka ji sallamar Ammi, da hanzari suka isa gare ta, ledar da ke hannuta suka karɓa, tun a tsaye suka fara ci, hannu baka hannu ƙwarya, da ƙyar Ammi ta samu suka zauna suka ci gaba da ci.
Dankali da ƙossi ne, haka suke ci suna korawa da ruwa kamar mayunwata daji. Kallonsu take cike da tausayi, numfashin ta ne ya fara yin sama-sama, ƙoƙarin jawo shi take amma ta kasa, basu ankara da halin da take ciki ba har ta kai kwanci. Husnah ce ta kai duba wajan da take, jinin da taga yana fita ta hancinta ne ya ankarar da su halin da take ciki, da hanzari suka yi kanta suna faɗar,
“Ammi! Ammi Kar ki mutu!.
Haka suka riƙa faɗa suna jijjigarta suna kuka.
Amma shuru ko mutsi bata yi ba bare su sa ran zata farka. Suna cikin haka sai wata mata ta shigo gidan sai sababi take, ta shanyata kamar kayan wanke zata karɓar mata ƙosai da dankali ta ce ta jira ta….bata ƙarasa maganar ba ta ankara da ita kwanci jini sai fita yake a ƙofar hancinta, irin yadda ta ga yara na jijjigarta yasa ta fahinci da matsala. Ƙoƙarin guduwa ta fara yi, sai kuma taga haka ba shi ne ma fita ba, ba ɓata lokaci ta kira mai adaidaita aka sakata har yara suka nufi hospital.
Irin yadda a shigo da ita ne likitoci suka karɓe ta, ba ɓata lokaci aka fara bata taimako, lya mai ƙosai na ganin haka ta sulale ta bar asibitin gudun kar ace a saye wani abu.
Afiyya da Husnah kawai ke zaune suna jiran ko Ammi zata fito ɗakin da suka ga anshiga da ita?
Takarda magani aka rubutu, ko da nurse suka fito neman ƴan uwanta ba kowa sai Afiyya da Husnah, tsaki suka yi haɗi da faɗar,
“Duk lakacin da ƴan uwanta suka zo za a dubata idan sun sayo magani.haka Ammi take halin mutuwa ko rayuwa har sa’a biyu.
Haka suka cigaba da aiki ba wanda ya bi ta kanta. Suna cikin haka wata likita ta shigo cikin azama don ta duba wata marasa lafiya da ta bari, sosai ta ga jikin matar da sauƙi don haka ta kama hanyar da zata fita ganin dare ya yi mata kan hanya, har zata fito ɗakin idonta suka sauka kan wannan matar da ke halin rai ko mutuwa, gabanta ne ya faɗi haɗi da sake duba gyafin da take, sosai hankalinta ya tashi ganin mara lafiya na neman taimakon gaugawa amma ba ko wani likita akanta, wajan da likitoncin suke ta ƙarasa ta fara musu masifa, irin yadda suka ga ranta ya ɓace ne suka yi mata baya ni ba kowa nata wanda zai sayo mata magani ko ya je a yi mata test , cikin ɓacin rai ta dube wata Nurse ta ce,
” Ina sauri zan tafi gida, amma duk abin da ya kamata ayi mata ayi mata”.
“In sha Allahu Aunty”.
Tun bata fita ba suka fara bata taimakon gaugawa, duk abin da ya dace sun yi mata, cikin ikon Allah numfashin ta ya dawo daidai, duk wani gwaji anyi mata, typhoid da older ce suka yi mata mugun kamu wanda sanadin haka jininta gaba ki ɗaya ya ƙone har sai da suka yi mata ƙarin jini. Duk wani maganin ko allora sun yi mata, cikin ikon Allah kafin safe ta farfaɗo. Afiyya da Husnah ta fara cin karo da su agyfinta, godiya ta yi ma Allah sannan ta fara tunanin ya aka yi ta zo asibiti, waya kawo mata su Afiyya da Husnah? Ta san ita tunda mai ƙosa ta bata bashin ƙosai da dankali bata san inda take ba, mi suka ci?. Hawayen da taji suna ɓuɓɓugowa a fuskarta ta goge, duniya ke nan wanda bai zo ba ma jiranshi take.
Tana cikin haka likitoci suka zo aka bata magani sannan aka duba lafiyarta. Nurse ɗin da ke kula da ita ta sa wata ma’aikaciya ta gyara su Afiyya haɗi da kawo musu abin kalaci, bayan sun ci har Ammi ita ma ta ci sannan wannan Nurse ta yi musu sallama ta yi tafiyar ta.
Sai da rana ta fito sannan ta shigo asibitin ta duba marasa lafiya da dama sannan ta zo wajan wannan matar da nurse ke ƙoƙarin sauya mata wasu drip , irin yadda ta ga suna yi mata, alamo sun nuna tana jin zafi haka yasa ta yi sauri ta ƙarasa wurin don karɓa ta sama ta, wata razananiyar ƙara taji an yi mata haɗi faɗar,
“dakata! Kar kubari wannan yarinyar ta taɓani!”.
Cikin hanzari ta kai kallonta ga wannan matar wadda muryarta ke mata amo a dudun kunnuwa, saboda ko mutuwa ta yi aka tasheta bazata manta wannan muryar ba.
Yatsun hannuta ta sa tana nunta da shi, bakinta sai rawa yake amma ta kasa magana.
Ganin Ammi na ƙoƙarin kwanci ruwa da aka ɗaura mata, kuma haka daidai yake da taɓa lafiyar ta, cikin hanzari wannan likita ta fice da ga wannan ɗakin gabanta na dukan uku uku. Iya ruɗuwa ta ruɗe da ma ashe Ammi na raye? Tabbas duniya ta nuna mata cewa yaro da babba duk tana daidai da su!.
_Wannan labarin ciki yake da sarƙaƙiya, ban tausayi da wata rikitacciyar soyayya mai wahala, labarin nan ya kunshi abubuwa da dama musamman rayuwar da muke a wannan zamani, amma ba za ga ne haka ba sai ka biyo ni sannu ahankali zaka yi katari da illah da aka yi._
_Littafin kuɗi ne idan akwai mai buƙata 300 ne ta account 3191016467. Sumayya Almustapha, first bank. za ki turu shaidar biyanki ta wannan Number 07062118047 only whatsapp, idan katin ne 300 MTN._
*UMMU JA’AFAR✍️*
*SUN YI MIN ILLAH*
*RUBUTA LABARI:-*
*_SUMMY M NA’IGE_*
*SADAUKARWA:-*
*RAHAMA SABO USUMAN*
_(Abar ƙaunata😘)_
*FIRST CLASS WRITER’S ASSO…*
*SHAFI NA 2*
Cikin hanzari ta isa wajen da ake parking ɗin mota motarta ta buɗe ta shiga, sai wani zarar ido take kamar an kama ɓarawo a gidan biki. Cikin mutuwar jiki ta kunna motar, da mugun gudu ta ja motar kamar wadda za ta je wasan tsere.
Gudu take kan titi hankalinta bai jikinta, wani gumi ke zubar mata kamar wadda ta yi wanka jego. Iya ruɗu ta shige shi, sautin muryar Ammi ke mata amo a dodon kunne, a haka har ta isa titin unguwarsu, gab da za ta shiga kwanar gidansu sai ta ji ta bige wani abu da ƙarfi, idonta ne suka sauka kan wata rantsattsiyar mota sabuwa dal, irin ɓarnar da ta yi wa motar ne ya sa ta dawo duniyar tunanin da ta tafi.
Hannu ta ɗaura saman sitarin motar haɗi da faɗar, ” Yau naga ta kaina”.
Gabanta sai dukan uku-uku yake, hawayen idonta sun ƙafe, tsananen baƙin ciki ya hana ma hawayen sauka, kallo ɗaya zaka yi mata kasan tashin hankali ya zarar da ita kamar mage ta kama ɓera.
Hayaniyar mutanin unguwarsu ne ya ƙara tayar mata da wani tashin hankalin da take hango ina ma a ce za ta mutu yanzu. Wallahi kar ka haƙura don yarinyar nan bata da mutunci ko kaɗan ba ta san girmma muta ne ba sai masifar girman kai, kullum haka take gudu kan wannan titi kamar jami’in tsaro ya biyo ɗan maye. Haka kunneta ya ji mata abin da ƴan unguwarsu ke faɗa.
Saitin zuciyarta ta dafe dake mata falfalniya kamar za ta fito waje.
Duk inda ranshi ya kai ya ɓaci, ayi masa ɓarna amma dan rainin hankali har an ɗau lokutta ba a zo bashi haƙuri ba! Wani mutum ne mai sun barin numfashi cikin ƙanƙanin lokaci, lalle ko wanene ya ɗauko ruwan dafa kansa.
Irin yadda mutanen unguwarsu ke masa magana ne ya sa ya fito don ya ga wani ɗan girman kai ne, don wallah ko wane raƙumi ne bai isa ya ja da kura ba. Ba abin da ba su ce da shi ba don kar ya barta, shi ma a yanzu ranshi ya yi mugun ɓace.
Gabanta ne ya yi muguwar faɗuwa lokacin da ta ɗago kai idonta suka sauka kan mamalakin wannan motar, kallon da ta yi masa kaɗai ta gane cewa shi ɗan masu yatsu da yawa ne. Motarshi ta sake kai duba gare ta, ta san ko ana muzuru ana shahu ba za ta iya sayin motar ba, amma ta fauwalawa Allah komai, duk hukunci da ya ga ya dace da ita zai iya yi mata shi. Ta na cikin wannan tunanin ta ji wani kamshi turare mai sanyaya ruhi ya ziyarci ƙofofin hancinta, “Ya Allah”.
Ita ce kalmar da ta fito bakinta “.
Bata kula da shi ba idonta na rufe sai tunanin ƙurar da ta tunkaro ta take, ina za ta sa kanta, lallah ya yi mata illah da har mutuwarta ba za ta daina jin raɗaɗin ƙonar zuci ba. Mutsin da ta ji ne yasa ta buɗe idonta haɗi da dawo wa duniyar tunanin da ta tafi. Rau-rau ta yi masa da ido lokacin da suka yi ido huɗu da shi mamalakin motar da ta yi ma ɓar na, sai a lokacin ta ji saukar hawaye a idonta, kanta ta yi ƙasa da shi don ba ta san mi zata ce da shi ba, a halin yanzu ko baki bazata iya buɗewa ta yi magana ba, da zaran ta yi yunƙurin buɗa baki ta yi magana sai ta ji kamar ta amayo zuciyarta saboda ɗacin rai da tashin hankali.
Sosai jikinshi ya yi sanyi lokacin da suka yi ido huɗu da ita, saboda tsaf ya hango damuwa da gagarumin tashin hankali a ƙwayar idonta, haka kawai sai ya ji ta bashi tausayi. Motar ta ya duba ya ga ko ita duk ta samu rauni a motar, don haka bai ce komai ba ya ɗau waya ya ƙira. Ba ta ji abin da ya ce ba sai sunan unguwar da ya faɗa, aikuwa ƴan unguwar na ji ya faɗi sunan unguwar suka fara murna don sun haƙiƙance cewa jami’in tsaro ne ya kira. Ko ita da ta ji haka ta saduda Jami’an tsaro ne ya kira.
Ta na cikin wannan tunani sai ga wata rantsattsiyar motar ta danno kai saman wannan titi, bata tsaya ko ina ba sai daidai wannan wajan.
Direba da ke cikinta yana parking ya yi hanzari ya fito, wajan wannan matashin saurayi ya ƙaraso haɗi da rusunawa kamar wani bafadin sariki. Gaishe shi ya yi sannan ya bashi makullin motar da ya zo da ita, ban san mi ya ce da wannan direba ba, makullin motar kawai ya karɓa ya shiga ya yi gaba ba tare da ya ce wa kowa komai ba.
Abin da ta ji ƴan unguwarsu na faɗa shi ne ya dawo da ita duniyar tunanin da ta sake afkawa. Amma anyi tsinan nen mutum, mutum ya yi maka ɓarna kuma ko haƙuri a kasa baka sannan ka barta batare da wani hukunci ba, lalle anyi a sararre a wannan waje waya sani ku karuwarsa ce.
Cewar wani matashin daccijo.
“Mai gida ya ce ki ba da mukullin motarki za a kai wajan gyara”.
Kamar ruwa ya cita haka ta kasa buɗa baki ta yi magana, cikin azama ta ɗau makulli ta bashi haɗi fitowa cikin motar. Har zata bar wajan sai direban ya ce,
“Ki ba ni number wayarki ko an gyara sai na kira na kawo miki”.
Bata ce da shi komai ba, wayarsa ta karɓa ta sa sannan ta shiga kwanar gidansu ta bar mutanin unguwa kowa na faɗar albarkar bakinsa.
Haka suna kallo aka je motar ta da ta wannan saurayi aka tafi wajan gyara.
Tana shiga gida kai tsaye part ɗinta ta wuce bata ma kalle part ɗin iyayenta ba bare har ta yi sha’war shigar sa. Da shigarta kayan jikinta ta cire ta shiga ɓanɗaki, ruwa ta fara kwararawa kanta, duk sanyi ruwan amma zafinsu take ji, duniyar tunani ta faɗa, ƙarar wayarta ce ta dawo da ita duniyar da ta tafi. Sai da ta gama abin da take sannan ta fito, har yanzu wayarta rure take. Kamar ba za ta ɗauka ba kuma sai ta ɗauka haɗi da karawa a kunnenta.
Hayaniya ta fara ji tun kafin ta yi magana, nurse ce ta kira ta ce,
” Likita wallahi matar nan tun fitarki sai ƙoƙarin kwanci ruwan take don ta gudu, yanzu haka idan kin ga yadda take sai ki ce tsohuwar mahaukwaciya ce”.
Maganar ta da ke zuciyarta, amma rashin son magana a yanzu ya sa ta ce ,
” Kar abarta ta fita, kuyi mata allurar bacci sannan a sauya mata ɗaki, a kula da ita sosai duk abin da ake so ki yi na baki wuƙa da nama, wannan amanata ce!”.
Zuciyarta ce ke mata raɗaɗi, ta na kai ƙarshin maganar ta kashe waya baki ɗaya ba tare da ji mi wannan nurse zata faɗa ba.
Saman gadonta ta faɗa sai rera kuka take ita kaɗai haɗi da tunanin rayuwarsu ta baya.
Ma’aikatan asibiti sun yi fama da Ammi kafin su samu su yi mata allurar bacci, bayan sun yi nasarar yi mata allura ne suka sauya mata wani ɗaki ita da su Afiyya waɗanda sai kuka suke kan ganin Ammi a cikin wannan hali.
Haka wannan nurse ta ci gaba da kula da lafiyar Ammi ba tare da Dr Rahama ta sake dawo wa asibitin ba.
Duk wannan halin da Ammi take cike lya mai ƙosai bata sake waiwayarta ba, bare mutanin unguwarsu su yi tunanin zuwa dubiyarta.
Dr Rahama tun da ta dawo asibiti ranar bata sake fita ba, halin da ta shiga ne yasa ta ɗau hutun kwana biyu wajan aiki, iyayenta sun shiga wani hali ganin ƴarsu cikin damuwa, amma sun yi tambayar duniyar nan ta ce musu ba komai, don haka suka sa mata ido.
Yau ko da ta tashi sai ta ji ta na muradin ta je ta ga halin da Ammi ke ciki, don haka ta shirya don ta tafi. Sam ta manta da babu mota hannuta sai da ta shiga ta yi ma Mamarta sallama akan zata tafi unguwa. Cikin sauri ta isa bakin get, wayam ta ga ni babu mota, lokacin ne ta tuna da abin da ya faru da ita kwana biyu da suka shuɗe.
Napep ta shiga ba ɓata lokaci ta isa asibiti ɗin. Kai tsaye ɗakin da aka kai Ammi ta nufa, bakin tagar ɗakin ta tsaya wajan da ba za a ganta ba ta na hango Ammi, irin yadda taga Ammi ta koma ne yasa ta fara sharar ƙwalla, baƙin ciki ya rufe mata zuciya haɗi da tarin tambayoyi akan ta, tambayar da tafi tsaya mata a rai ita ce,
Ina Ammi ta samu waɗan nan yara ƴan mata? alamu sun nuna su ba ƴaƴan tsintuwa ba ne don tabbas suna kama da ita. Kai ta girgiza haɗi da ƙorar sheɗa akan abin da ya hasko mata. Kuka ne ya kuɓuce mata, hakan yasa ta bar wajan cike da ƙunar zuciya.
Sosai Ammi ta samu lafiya, don yanzu haka zaune take ta kafawa waje ɗaya ido kamar mai tunani, su kuwa su Afiyya da Husnah sai wasa suke don basu da wata damuwa yanzu.
Ammi kallon yaran ta yi irin yadda suke wasa, murmushi ne ya kuɓice mata mai tare da ruwan hawaye
_Wannan labari ciki yake da sarƙakiya_
Littafin kuɗi ne idan akwai mai buƙata 300 ne ta account 3191016467. Sumayya Almustapha, first bank. zaki turu shaidar biyanki ta wannan Number 07062118047 only whatsapp, idan katin ne 300 MTN.
*SUN YI MIN ILLAH*
*RUBUTA LABARI:-*
*_SUMMY M NA’IGE_*
*SADAUKARWA:-*
*RAHAMA SABO USUMAN*
_(Abar ƙaunta😘)_
*FIRST CLASS WRITER’S ASSO..*
*SHAFI NA 3*
Dr Rahama na barin wajan kai tsaye office ɗin su ta isa wajan Nurse Ruƙayya, bayan sun gaisa ne ta ke cewa da ita ta na son su yi magana. Bayan Nurse Ruƙayya ta natsu sannan Dr Rahama ta ce,
” Ya fama da mai jiki? Ina fatan ta samu lafiya?”
Murmushi nurse Ruƙayya ta yi sanna ta ce, “Alhamdulillah gaskiya ta samu sauƙi sosai, don ko yanzu za’a iya sallamarta, amma na ce ba za a sallameta ba sai na gaya miki, daman ko ba ki zo ba zan neme ki”.
Murmush Dr Rahama ta yi mai nuna farin ciki tsintsa sannan ta ce,
” Haka na ke son ji daman, sai dai wani hanzari ba gudu ba, ina so kar a sallameta yanzu, ina son har sai ta gama shan maganinta kafin a bata sallama, zan turu miki kuɗi a ci gaba da bata kulawa kamar yadda ki ka san za ki kula da Babarki, to haka nake so ki bata kulawa sosai, bayan ta gama shan maganinta, ina so ki ɗauke ta da kanki ki kaita har gidanta, don ina son na san inda take rayuwa yanzu, ki yi haƙuri Ruƙayya na san zaki ji maganata bambara ƙwai, bazaki ga ne inda na dasa ba sai nan gaba, fatana dai ki ci gaba da taimaka min har in samu mafita”.
Ta kai ƙarshin maganar kamar ƙwalla ta zubu mata.
Hannu Ruƙayya ta bata sannan ta ce,
” Karki da mu Rahama, ni da ke ai mun wuce haka”.
Godiya ta yi mata haɗi da tashi don komawa gida, har ta isa ga ƙofar fita ta juyo ta ce,
” Nurse na ce ko ta sake miki magana ta kuwa?”
” Ba ta sake ba tun ranar”.
Murmushi mai ciwo Rahama ta yi, fita ta yi daga office ɗin haɗi da shafi ƙwallar da ta zubo mata ta ce,
” Ya zan yi da Ammi har ta gane illah ya yi min?”
Wayar ta ce ta fara rure ita ce ta katse mata kukan da take yunƙurin yi. Number ce ba suna, kamar ba za ta ɗauka ba, kuma sai ta ɗauka haɗi da karawa a kunne. Ba ta yi magana ba, sallama a kayi mata ta karɓa.
” Ranki shi daɗe, kin ji ni shuru ko, don Allah ki yi haƙuri mun yi tafiya ne kwana biyu, yanzu ina so ki kwatantamin gidanku sai na kawo miki motar saboda an gyara”.
Sai a lokacin ta ga ne inda ya dosa. Kwatancin gidansu ta yi masa sannan ta shiga napep ya dawo da ita gida.
Ba ta jima da dawo wa gida ba sai ga kiran wayarsa, ɗauka ta yi, tun ba ta yi magana ba ya ce,
” Ina ƙofar gidanku”.
Datse wayar ta yi ba tare da ta ce komai ba, hijab ta saka sannan ta fita, mota biyu ce ta gani a ƙofar gidansu, ba ta gane motar ba sai da ta dube number motar, saboda sosai aka yi mata gyara, har fintin motar sai da aka sauya, sosai motar ta yi mata kyau. Ta na cikin haka sai ta ji an ce,
” Barka dai ranki ya dade”.
Haka ta ji an faɗa ta na cikin kallon motar kamar wadda ta yi katari da sabon wata.
Dubansa ta yi, murmushi ɗauke a fuskarta, amsawa ta yi sannan ya ce,
” Tare muke da ƴallaɓai”.
Ido ta ɗan zare kamar mai tunanin wani abu sai ta ce,
” Ya na ina?”.
Motar da ke kusa da ta ta ya nuna mata. Ba bata lokaci ta ce ka ce masa ya ƙaraso.
Ko da ya je ya sanar da mai gidan na shi sai ya ce, A’a muna hanya ka ce ta zo mu gaisa”.
Haka ya ce da shi ba tare da ya ɗago kai ya dubesa ba.
Cikin mutuwar jiki da faɗuwar gaba ta isa gaban motar bayan saƙon sa ya same ta, da sauri direban ya buɗe mata gyafe ɗaya ba musu ta shiga sannan ya rufe.
Sallama ta yi masa, sai kuma ta kasa gaishe da shi, don jinta take wata iri kamar wata budurwar ƙauye.
Sai da ya ɗago kai ya dubeta tsaf sannan ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya mai ƙarfi, ya jima ya na kallonta, a halin da ya ke ciki yanzu jinshi yake kamar ya rungumuta amma ba hali. Duk ta tsargo da kallon da yake mata, har ta yanke shawarar fita daga motar don yanzu ita tsoron maza take kuma an dasa tsanarsu a zuciyarta, shi ya sa duk in da namiji ya ke ba ta cika gaishe shi ba, bare har wata mu’amala ta shiga tsakaninta da su.
” Barka da wuni”.
Haka ta ji ya faɗa cikin wata sirariyar murya kamar ba ta namiji ba.
Gabanta ne ya faɗi, kawai sai ta kasa amsawa saboda ta daburce kamar wata baƙauyer daji.
Jin bata karɓa ba ne ya sa ke cewa,
“Ga motarki nan ki duba ki ga ni, idan gyaran ya yi to shi kenan, indan bai yi ba sai a sauya”.
Sai da ta daidaitar da fitar numfashinta sannan ta ce,
“Na gode Allah ya saka maka da gidan aljannah”.
Abin da ta faɗa da shi kenan ta fi ce a motar.
Tun da ta buɗa baki ya rufe ido yana saurarin zazzaƙar muryar ta. Sam bai ji fitar ta ba sai da ya ji ƙarar rufe ƙofar motar.
Ido ya ware lokacin da ya ga har ta fice, wani abu ya tsaya masa a zuciya, shi dai yana roƙon Allah ya kawo mi shi sauƙi akan wannan al’amarin da ya same shi cikin kwanan nan.
Yana cikin haka ya ji direba ya tashi motar za su bar unguwar. Ido ya zuba ko zai sa ke ganin ta, amma babu ita babu labarinta, don tana karɓar makulli ga diraba ta shige gida har su tafi kafin ta shigo da motar gida, saboda ita sam ta tsani mutum ya riƙa kallonta.
Sai da ta ji sun bar ƙofar gidansu sannan ta zo ta buɗe get ta shigo da ita cikin gida, sosai komai na motar ya sauya ciki kuwa har da kukanta, ma zaunin motar ta ajeta, sannan ta koma part ɗinta, tunani ta shiga ya za ta yi da Ammi!.
*******
A hankali suke tafiya har su ka shiga wata unguwa wadda babu hayaniya a cikinta, daidai wani gida suka tsaya haɗi da yin horn, ba ɓata lokacin mai gadi ya buɗe wawakeken ƙyaurensa sululuf, ba ka ji mutsin ta ba, kallon ƙofar kaɗai ya wadatar da kai ka gane cewa gidan ma su yatsu da yawa ne.
Wajan da ake parking ɗin mota ya tsaya, sai da aka ɗau lokaci sannan ya fito sai hurar da isaka yake a baki, kai tsaye ɓangarin Kakarshi ya nufa.
Zaune ya sameta, idonta sanye da tabarau mai ƙara ganin ido, jirida ce a hannunta, kallo ɗaya zaka yi mata ka gane cewa tsohowar akwai wayewa atare da ita. Sallamar jikan na ta ya sa ta aje jaridar da ke hannuta haɗi da mai da hankalinta gareshi. Dubanshi ta yi tsaf sannan ta ce,
” Me ke faruwa da ɗan Daddynsa?”
A jiyar ya zuciya ya sauke mai ƙarfi ya ce,
“Hajiya na samu matar aure”.
Ya faɗi haka idonshi a rufe sai hasko masa ita suke.
“Ikon Allah! Haƙuri maganin zaman duniya”.
Abin da Hajiyar ta ce haɗi da cire tabaraun dake kan idonta.
“Wace mai sa’a ce wannan?”
“Ba mu daidaita da ita ba, yau shi ne gani na biyu da na yi mata, in fatan zaki taya ni da addu’a ko da za ta soni kamar yadda nake jin sonta a cikin raina”.
“Kwantar da hankalinka jikana, ina da tabbacin ba wata ƴa mace mai lafiya wadda ba za ta so ka ba, ina fatan dai ita ɗin ƴar nagartaccin gida ce?”
Bai ce da ita komai ba ya mike ya bar falon. Godiya ta riƙa wa Allah haɗi da yi masa kirari, cikin lokaci kaɗan ta sa aka haɗa abin sadaka.
******
Bayan sati ɗaya Ammi ta wartsake kamar babu ciwon da ya sameta, sosai take jin daɗin jikinta, yanzu ma zaune take ta gama ninke kayan da aka wanke mata ita da su Afiyya da Husnah, tunani take to waya ɗauke nauyin ta har ta samu lafiya don har yanzu ba ataɓa cewa ta saye magani ba, ko dai sun bari ne har ta ji sauƙi? Ta na cikin wannan tunani sai ga Nurse Ruƙayya ta shi go ɗaukin ɗauke da fara’a a fuskarta.
Bayan sun gaisa da Ammi ne take shaida ma Ammi yau za’a sallameta, don haka ta shirya, zuwa awa ɗaya zata zo ta kaita har gidanta, sosai Ammi ta ji daɗi haɗi da yi mata godiya da yi mata addu’a Allah ya tsareta daga sharrin zamani.
Da Amin Ruƙayya ta karɓa sannan ta fice. Har ta fice Ammi na kallonta, wani abu ta ji ya tsaya mata a rai, saukar hawaye kawai ta ji a fuskarta.
Comment ɗinku shi zai saye wannan Labari, tabbas rashin comment shi zai sa a mayarda shi na kuɗi.
*Commet and share*
*UMMU JA’AFAR✍️*
*SUN YI MIN ILLAH*
*RUBUTA LABARI:-*
*_SUMMY M NA’IGE_*
*SADAUKARWA:-*
*RAHAMA SABO USUMAN*
_(Abar ƙaunta😘)_
*FIRST CLASS WRITER’S ASSO..*
*SHAFI NA 4*
Nurse Ruƙayya na isa office ta kira Dr Rahama a waya. Tashin ta kenan daga bacci, don yau ta makara sosai, saboda ko sallah sai da rana ta fito ta yi, kuma har yanzu idonta taf yake ɗauke da bacci kamar wadda ta sha kayan maye. rurar da wayar take yi ne ya tashe ta, ganin sunan nurse Ruƙayya ne ya sa ta ɗauka cikin hanzari haɗi da karawa kunnenta. Bayan sun gama gaisawa ne Ruƙayya ke cewa da ita,
“Yau fa zan kai Ammi gida, saboda yanzu ta samu lafiya sosai”.
Hamdala ta yi ma Allah haɗi da sauke sassanyar ajiyar zuciya ta ce,
“To Ruƙayya nagode sosai, bani wasu ƴan daƙiƙu yanzu zan ƙaraso cikin asibiti”.
” Ina jiranka”.
Abin da Ruƙayya ta faɗa kenan a taƙaice.
A gorgoje ta tashi tashiga banɗaki ruwa ta watsawa jikinta sannan ta fito, man shafawa kawai ta shafa sannan ta shirya ta fito. Part ɗin iyayenta ta nufa, zaune ta same Mumy ta tana kalaci, bayan sun gaisa ne ta ke gaya mata inda zata tafi, kallonta ta yi tsaf sannan ta buɗa baki ta ce,
” Na fa gaji da ganinki haka Rahama, kin ce sai kin kammala karatu, to karatu ya ƙare gashi har kin fara aiki, muddin kina son na ci gaba da jin daɗi to ki sani sai ranar da naga kin yi aure, halin da na ke ciki aurenki kaɗai nake son na gani”.
“In sha Allahu Mumy zaki gani, fatana dai ki ci gaba da yi min addu’a”.
Ta faɗi haka haɗi da tashi ta fice daga falon.
“Shekaran jiya bakin yi baƙo ba? Ko shima kin koreshi?”.
Haka maganar ta faɗo mata a kunne daidai lokacin da ta sanya ƙofarta ƙofar fita daga falon.
Batare da ta juyu ba ta ce,
,”A’a Mumy, idan na dawo za muyi magana”.
Da ido Mumy ta rakata har ta ɓacewa ganinta, ita bata taɓa ganin yarinyar da bata son ko ayi mata maganar aure ba kamar Rahama, ita dai ta na roƙon Allah ya kawo mata agaji acikin lamarin yarinyar.
Kai tsaye motarta ta shiga ta fice, a hankali ta ke tafiya har ta fice titin unguwarsu tun ranar da ta ji abin da suke cewa take ƙafa-kafa da su.
Wai yarinyar can ba ƴar maye ba ce”.
Cewar wani saurayi da ganinshi kallo ɗaya zaka yi masa ka gane cewa shi ɗan ruwa ne.
” Malamar asibiti ce kar ka yi mata sharri”.
” To tana min kama da wata shugaban masu safarar kayan harka”.
Sun faɗi haka daidai lokacin da motarta ta bar titin unguwar. Bata tsaya ko ina ba sai asibiti, ko gaisuwar da ma’akata ke mata bata wani tsaya karɓawa ba saboda Ruƙayya da ke jiranta, ko da ta isa office ɗinsu ta na shirin fita, bayan sun gaisa ne ta ce,
“Ga kayan sawarsu can na zo da su, ki zo na saka miki cikin mota har ma da abin cin su”.
Ta kai ƙarshin maganar haɗi da buɗe zip ɗin jikarata, kuɗi ta ɗauko aƙalla za su kai dubu ɗari ta ce,
“Ki haɗa musu da wannan su yi anfani da su zuwa wani lokaci”.
Da kallo Ruƙayya ta bi ta, don ita ta san halin Rahama, ba kowa take kulawa ba bare har ta san matsalarsa, amma duba waɗan nan mutane tun zuwan su komai ita ce. “Miye alaƙarki da su?”
Abin da Ruƙayya ta ce da ita idonta cikin nata.
Murmushi ta yi sannan ta ce,
” Karki da mu da sanin ko ita wacece, nan gaba da kanki zaki gano komai ba ta re da na gaya miki ba”.
Motarta ta buɗe sannan aka saka mata kayan da ta zo musu da su. Ita ko kai tsaye ta wuce ɗakinsu Ammi, ko da ta shiga ɗakin sun shirya ita kaɗai suke jira, ganinta ya sa Ammi ta mike tsaye ta ce,
“Ta fiya za mu yi?”
Murmushi ɗauke da fuskar Rukayya ta ce,
“Eh”.
Ta faɗi haka haɗi da fitowa, bayanta Ammi ta biyu hannuta riƙe da na su Afiyya da Husnah, haka suka bin bayan ta har suka isa gaban motarta, bayan sun shiga sannan itama ta shiga suka bar asibitin. Duk wannan abun da ake akan idon Dr Rahama komai ya faru, lokacin da suka wuce wasu zafafan hawaye suka zobu mata, ji take kamar ta bi bayansu, kasa haƙuri ta yi don haka cikin hanzari ta mike kamar wadda aka tsokarawa allura, motarta ta shiga haɗi da kiran Nurse Ruƙayya, hanyar da suka bi ta faɗa mata, a hankali suke tafiya har ta kamu su.
Duk yadda Ruƙayya ta so su yi magana da Ammi hakan ba ta samu ba, don yanzu Ammi mutane sun mata hankali, ba lalle ne ko sun yi mata alhairi ta iya amincewa da su ba. Saboda ta haka ne aka yi mata illah. Ta haka har suka kawo ƙofar gidan, bayan Ammi ta buɗe gidan, a yadda ta barshi haka suka same shi, sai ƴar ƙorar da ya yi. Almajirai Ruƙayya ta sa suka shiga da kayan abinci har ma da na sawa. Bayan sun kammala ta yi musu alhairi sannan ta shiga gidan. Duk wannan abun da ya faru Dr Rahama na nesa da su tana kallon komai ta na shafe ƙwalla, “Miya dawo da Ammi wannan unguwar”.
Haka ta faɗa lokacin da take shirin barin unguwar.
Bayan Ruƙayya ta shiga gidan sun ƙara gaisawa da Ammi ne sannan ta ɗauko waɗan nan kuɗin ta ba ta, ƙawar da kai Ammi ta yi haɗi da faɗar bazata karɓa ba.
Saboda gudun husuma tsakaninta da Ammi ne Ruƙayya ta ce,
” Ranar da ki ke kwance wasu suka kawo zakka ga marasa lafiya, to halin da ki ke ciki ne suka ɗauke nauyinki har ma da waɗan nan kaya, ƙarshe dai suka ce a baki waɗan nan idan kin farka kya ja jari”.
Godiya Ammi ta yi ma Ruƙayya sannan ta ƙarɓi kuɗi haɗi da cewa Ruƙayya ta ɗau wani abu daga ciki, godiya ta yi ma Ammi haɗi da yi mata sallama saboda ina jiranta. Har ƙofar gida Ammi ta raƙuta haɗi da yi mata godiya.
******
” Wai duk abin da za mu yi sai mun haɗa da ita!? ni fa har ga Allah ban sun harka da yarinyar nan don ƴar ranin hankalice kamar kyauta za ta bamu ba kuɗi zamu bata ta sayar mu na ba”.
Haka ya rinƙa ta zuba kamar ɗan takar da ya faɗi zaɓe.
Ɗayan abokinsa, sai da ya bari ya kai aya sannan ya ce,
” Duƙawa wada fa ba gajiyawa ba ne, kuma sannu-sannu bata hana zuwa sai da mujima ba a kai ba, yarinyar nan da ka ke gani ita kaɗai ke lokaci akan wannan harka, kuma in ka lura ita bata fiye hulɗa da ƙananu irinmu ba sai dai da manya irinsu mai gida, kana ganin ko su mai gida yadda take musu bare mu ƙanan ƙwari, ita fa yarinyar nan da ka gani ko manyanmu duk’a mata suke saboda ita tauraruwarta ke haskawa a yanzu, ita kaɗai ce ke iya tsallaka ƙetare ta zo da kayan harka batare da an tuhumeta ba, wallahi yarinyar nan ta wuce duk wani tunaninka, kawai ka haƙura ka ta shi muje mu sa meta club don muka ja lokaci ba za mu sameta ba sai wani sati, sa’ar mu na ɗaya ta shigo cikin garin”.
” Mi ya kawo ta garin kano?” ya faɗi haka ya na furzar da isaka kamar wani kumurcin maciji sannan ya tashi suka tafi.
” Idan mun je ka tambayeta”.
Haka abokinshi ya ce da shi kafin su tafi.
Ƴan mata ne masu jini ajika, mafi yawansu kitson attache ne kansu, sanye suke da ƙananun kaya sai rawa suke abin su, kallo ɗaya zaka yi musu kasan cewa duniya ta ƙulla ƙawance da su.
Can na hango wata kyakyawa yarinya fara ce sul, sanye ta ke da wata ƙaramar riga da wani wando jeans, sosai suka ɗamemata jiki, a hankali take zuƙar sigari tana hurar da iska waje cike da ƙwarewa. Waje ɗaya take kallo, alamu sun nuna cewa ta ziyarce duniyar tunani.
“Kayan harka muke so”.
Hakan da ta ji shine ya dawo da ita a duniyar tunanin da ta afka, sosai ranta ya ɓace saboda an katse mata tunanin abin da ya fi mata komai!.
Comment and shera
*UMMU JA’AFAR✍️*
*SUN YI MIN ILLAH*
*RUBUTA LABARI:-*
*_SUMMY M NA’IGE_*
*SADAUKARWA:-*
*RAHAMA SABO USUMAN*
_(Abar ƙaunta😘)_
*FIRST CLASS WRITER’S ASSO..*
*SHAFI NA 5*
Ido ta d’ago don ta ga su waye suka katse mata tunanin da take, wasu samari ne idonta suka yi arba da su tsaye kamar gunki, ba ta gama kallonsu ba sai ɗaya da ga cikinsu ya yi ƙoƙarin zama kusa da ita, cikin hanzari ta mike tsaye kamar wadda ta ga mushin kare haɗi da kama hanyar barin club ɗin baki ɗaya.
Cikin azama ɗaya da ga cikinsu ya ce,
” Don girma Allah ki ba mu minti ko ɗaya ne mu isar da saƙon da ya kawo mu wajanki”.
Ya faɗi haka kamar wani mai roƙon gafara.
Ba don komai ya yi haka ba sai don sanin in ba nan ba bai san inda zai ganta ba bare har ta bashi lokacin magana da ita.
Ƙoƙarin korarsu yaranta suka fara yi, can kuma sai ta ce,
” Wani saƙo ne za ku isarmin?”.
Ta faɗi haka daidai lokacin da take saka tabarau a fuskarta.
“Daman kaya muke buƙata ko za mu samu shugaba?”
Ya faɗi haka kamar ya rusuna mata.
Kallonsu ta yi sosai da sosai, tsab ta gano cewa su ƴaƴan marasa ƙarfi ne, kawai sun faɗa wannan harka ne don jin daɗi, kuma ita ba ta faɗa wannan harkar ba don ta sayar wa da ƴaƴan marasa ƙarfi ba, ta faɗa harka ne don ɗaukar fansa ga ƴaƴan musu yatsu da yawa, sune suka yi mata ILLAH ba ƴaƴan masu ƙaramin ƙarfi ba idan har ta canka daidai.
” Babu kaya a ƙasa”. maganar da ta fito bakin ta kenan.
Cikin hanzari ya sake rutsuna mata ya na mata magiyar kamar maroƙi ya ga ruwan ƙuɗi da ta taimaka masa, ita kuma akwai abin da ya sa ba ta son ba shi kaya, amma bari ta yi an fani da shi wajan ta ya ta aiki”.
“Garin nan ka ke?”
” Eh Shugaba”.
Kai ta girgiza sannan
Haɗi da miƙa masa hannu, cikin azama ya ɗaura mata kuɗi a tafin hannunta sannan ta ce da yaranta a bahi kaya, sosai ya yi godiya haɗi da magiyar da ta taimaka masa da number wayar ta.
Kai ta girgiza, sanna ta ce,
“Zaka iya bada numberka, idan ina nemanka ni zan kira ka”.
Cikin hanzari ya bata number sannan ta yi gaba.
Mota tashiga ita da yaranta biyu, ɗaya ya ja motar ɗaya ya zauna kujar mai zaman banza bayan ya buɗe mata motar ta shiga.
Ba su tsaya ko ina ba sai wani gida wanda kallonshi kaɗai zaka gane ƴaƴan banki sunyi kuka, mai gida ya buɗe musu wawakeken ƙyaure gida sannan suka shiga, motar na tsayawa tun ba a buɗe mata mota ba ta buɗe ta fice, kai tsaye falon gidan ta isa haɗi da buɗe firj ta ɗauko kwalbar barasa sannan ta zauna.
Ta na buɗewa ta fara zoƙar barasar haɗi da kunnan sigari tana zuƙa. Zuƙa take amma ba abin da ke ɗauwai niya da ita sai ɗacin rai, lokacin da hankalinta ya fara barin jikinta sai sambato take tana faɗar,
”Zaki yafe min ko?, sune suka yi min illah ba laifina ba ne!”.
Haka tariƙa faɗa har bacci ya yi awon gaba da ita.
Kallo ɗaya zaka yi mata ka san ba baccin lafiya ne take yi ba, asubar farko ta tashi, bayan ta gama tsarkake jikinta sannan ta fara nafilfili kafin akira sallah, ta jima kan sallaya, tana idar da sallah asuba ta ɗauko azkar ɗinta ta fara karatu, sai da haske ya fito sannan ta fito, kai tsaye motarta tashiga ba tare da ta bar kowa ya rakata ba, wata unguwa ta isa mai ƙaracin jama’a , nesa kaɗan da wani gida ta yi parking motarta, sanye take da babban hijiba, haka ne ya bata damar fitowa ta tsaya wajan wata mai sayar da ƙosai da fanke, kuɗi ta bata ta ce ta na son a bata, da yake akwai mutane a wajan hakan ya bata damar da sai ta jira.
Tsaye take sai kallon wani gida take, tunanin yadda zata shiga gidan take amma ta san ko ina muzuru anshawo ba zata iya shiga ba, fitowar yaran ƴan mata ne ya dawo mata da hankalinta, gabanta ne ya yi muguwar faɗuwa lokacin da idonta suka sauka kansu, da hanzari ta fara tafiya don ta kamosu, tafiyar yaro da babba ba ɗaya ba ce, don haka takon da bai wuce biyar ba ta kamosu, hannun ɗayar ta roƙo, tsayawa suka yi su biyu, kallo ɗaya zakiyi musu ka gane cewa su tawaye ne, komai na su guda, durƙusawa ta yi ƙasa haɗi da faɗar,
“Husunah Afiyya ina Ammirku!?”
Hawaye ne suka zuba a iɗonta daidai lokacin da take faɗar haka, cikin hanzari ta jawo su jikinta, ido ta runtse, kowa ce ƙofa ta jininta son yaran na ziyarta ta.
” Affiya mutafi makaranta Ammi ta ce kar mu tsaya”.
Maganar Husnah ita ce ta dawo da ita duniyar tunanin da ta afka.
Hannu Afiyya Husnah ta je domin su tafi, cikin hanzari ta ce,
“Ku zo ga mai ƙosai can na karɓar muku”.
“Ammi ta ce duk wanda ya ba mu abu kar mu karɓa”.
Cewar Afiyya lokacin da suka fara tafiya.
Wasu zafafan hawayen bakin ciki ne suka fara sauka a idonta, ganin su Afiyya za su ɓacewa ganinta ne yasa ta bi bayan su har suka isa makarantarsu.
Dawo wa ta yi cikin ƙonar rai da alwashin ɗaukar fansa, ko ƙosan bata karɓa ba ta ce ayi sadaka sannan ta bar unguwar sai abubuwan da suka faru da ita baya take tunani, lallai sunyi mata illah!.
*****
Ƙokan da take ne yasa ta gane bashi ne mafita ba, don haka ta yanke shawarar gwara ta sameshi ɗakinshi ta yi masa baya ni wallahi ba halin ɗanta ba ne, an yi misa haka ne don ayi masa illah.
Wanka tashiga ta yi sannan ta gyara jikinta sosai haɗi da feshi jikinta da wasu turarukka masu ƙanshin gaske, sosai ta ji daɗin jikinta, don rabonta da ta yi wanka bare har ta sa wani turare tun ba’ayi wa ɗan ta illah ba, duk da ta yi kyau, amma kallo ɗaya za ka yi mata kasan tana cikin damuwa
Da fara’a ta isa falonshi, zaune yake yana kallon labaru, sallamar ta da ya ne ya maida hankalinshi gareta haɗi da karɓa mata sallama.
Irin yadda ta ga ya karɓa mata ne yasa ta ji ƙwarin gwaiwar faɗar abin da ya kowota, kusa da shi ta zaune haɗi da gaisheshi cikin kwantar da murya.
Amsawa ya yi haɗi da Kallonta sannan ya ce,
” An gama fushi da ni sannan aka samu damar zuwa gare?”
Idonta ne ya kawo ƙwalla ya yi da ta tuna wannan abu da aka yi ma ɗanta, cikin rawar murya ta ce,
” Ba na fushi da kai mijina, zuciyata ce ba daɗi, amma ka yi min affuwa”.
Ta faɗi haka daidai lokacin da wasu zafafan hawaye ke kwaranya a fuskarta.
Ƙasan kujerar da ya ke ta sauko haɗi da riƙe kafarsa ta ce,
” Mijina ka taimake rayuwa ta, su kaɗai ne jinina da zan kalla na ji sanyi, ban da kowa sai kai, ina tabbacin kasan haka, ni kaɗai na ke a duniyata kamar kafitar da kwallon magoro kan titi yana shawagi haka nake a duniyata, ka yi min rai mijina ka dawo muna da ɗanmu”……tun bata rufe baki ba ya ce,
“Muddin ki na son ci gaba da zama da ni sai kin daina danganta shi da ni. Bari kiji, jikina ya fara ba ni ba nini ubansa ba!”.
Jin wannan kalmar ne yasa ta sanya wata ƴar ƙara haɗi da ƙanƙamewa jikinsa, duk yadda ta su bu ɗa baki ta yi magana ta kasa, saboda zuciyarta ce ta ji zata fito waje saboda ɗacin rai Sai da ta ci kuka har ta ƙoshi sannan ta samu damar buɗa baki ta ce,
” Alhaji ka yi min adalci, tun ina ƴar shekara goma ka ɗauko ni, a duniyar nan ban san kowa ba sama da kai, kuma sanin kankane ban taɓa mu’amala da wani ɗa namji ba bare ka yi min tunanin na taɓa zina!”……

Leave a Comment