Uncategorized

Soyayyar Yusuf Da Fadeela Hausa Novel

*SOYAYYAR YUSUF DA FADEELA*
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

*TRUE LIFE STORY AND SHORT STORY.*

 

LABARIN BAI DA YAWA, IDAN YA YI TSAWO TO YA KAI 10 PAGE, DA FATAN ZAKU BANI HAƊIN KAI.

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

 

*Page 1-2*

Mafarin labarin.
Sanyayyer iskar damina ake kaɗawa me ciki da lullumi da ban sha’awa, misalin ƙarfe biyu na yamma ne, amma sai ka ɗauka irin huɗowar asubahin nan ne, ko kuma gab da magrib, saboda yadda garin ya yi sanyi da duhu ga iska me shiga jiki, sakamakon hadarin da aka haɗa ruwa zai iya sauka a ko wanne irin lokaci.
Tuƙi ya ke cikin kwanciyar hankali da nishaɗi, domin daga Katsina ya dawo cikin garin Kaduna. Duk da tafiyar da ya sha, amma fuskarsa na cike da annuri, wataƙil ko dan an dawo gida ne, dangi masu daɗi musamman idan kana da uwa a raye.

Har ya doshi hanyar komawa gida, sai kuma ya fasa ya nufi gidan abokinsa, damon sun daɗe basu haɗu ba sai ta waya saboda tafiyar nan da ya yi zuwa Katsina.

A ƙofar gidan ya kira wayarsa, fitowa ya yi cikin kwalliya kamar me shirin fita.

“Abokina halan fita zaka yi?” Yusuf ya tambayi abokin nasa me suna Ƙasim bayan shugowarsa motar. “Eh zani Dinner ne, sai Allah ya kawowa bikin wata ƴar uwata ake”

Yusuf ya ce”Cikin hadari irin wannan zaka dinner?”

“Dinner ce ta gida, dole ne shiyasa zani” cewar Ƙasim.

“Ayya to badamuwa bari na saukeka a hanya sai na wuce” Yusuf ya faɗa yana ƙoƙarin data motar, sai da suka hau titi Ƙasim ya ce”Yusuf amma wasa ka ke? Ai dole ma mu shiga wajen Dinnern nan da kai”

Yusuf bai ce komi ba, kai tsaye ya shiga gidan wani mai da ke hanya ya cika tankin motarsa da mai sannan suka doshi wajen Dinner da ke kusa da Masallaci Al-mannar da ke Kaduna.

Ma sha Allah amarya Sa’adatu Aliyu Yola tayi ƙyau domin ƙanwa ta ke a gurin Ƙasim abokin Yusuf.

Suna zaune akan tebura suna shan coca-cola idanuwan Yusuf suka sauka a kan wata baiwar Allah ƙyaƙƙyawa son kowa, tuni yaji zuciyarsa ta bugu, zuba mata idanuwa ya yi dan da alama tana cikin dangin amaryar ne.

Kasa jurewa Yusuf ya yi domin sosai yarinyar ta tafi da imaninsa, a natse ya tashi ya fara tafiya cikin natsuwa da kamala, dan Yusuf ba dai ƙwarjini ba. sallama ya fara mata.

A hankali ta dago idanuwanta, sai da Yusuf yaji wani shock, da sauri ya daidaita natsuwarsa,

“Ƴan mata barka da yamma” ya faɗa cikin sanyin murna.

“Barka” ta faɗa cike da natsuwa da jan aji.

“Da farko da sunana Yusuf, maganar gaskiya kin mini, kallo ɗaya naji kin shiga zuciyata ina ƙaunarki, fatana ki zamo uwar ƴaƴana.”

Yusuf baƙi ne amma ba sosai ba, yana da ɗan tsayi amma ba can ba, a kwai idanuwa ga hanci bakinsa madaidaici me jerin zubin haƙora ƙyawawa, ba laifi Yusuf kyakkyawa ne kuma kallo ɗaya zaka masa kasan yana da ƙyirki da iya mu’amula da mutane.
A minti biyar ta ƙare masa kallo ya yin ta furta “Ni kuma sunana Fadeela”

“Ma sha Allah, suna me daɗi” Yusuf ya furta yana sake kallon Fadeelar wacce sai dai muce masha Allah dan tana da ƙyau ba laifi, fara ce siriri amma ba can ba, tana da idanuwa ga hanci tubalkalla laɓɓanta ƙyawawa da madaidaicin bakinta, gaskiya Fadeela ta tara duk kan wani abu da Yusuf ke so a jikin ƴa mace. lokaci ƙanƙani har mun ɗan saba a lokacin na tambayi lambar wayarta ta ba ni.

Bayan an tashi daga Dinner, hadari ya ƙara haɗuwa har an fara yayyafi, hakan yasa Yusuf kiranta a waya “Fadeela idan bazaki damu ba, kizo na rage muku hanya”

Cikin muryarta me sanyi ta ce”A’a kayi haƙuri kar na takura maka”

“Kar ki damu Fadeela babu takura anan, kice ku fito ana kamar harda su Aunty sai na kai ku gida”

“To mun gode” ta faɗa sannan suka fito na kai su gida, Aunty sai godiya ta ke masa domin zuwa lokacin tuni aka tsugage da ruwa…..

Mu haɗe a page na gaba.

*MUMMY AYSHATU CE*🖊️

*SOYAYYAR YUSUF DA FADEELA*

 

*TRUE LIFE STORY AND SHORT STORY.*

RUBUTAWA:
*MUMMY AYSHATU*😎

 

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

 

*Page 3-4*

Cikin ƙanƙanin lokaci, soyayya me ƙarfi ta shiga tsakanin Yusuf da Fadeela. Hakan ne ma yasa kai tsaye Yusuf yaje Malumfashi da ke jahar Katsina ya nemi izini a gurin magabatanta kuma suka yadda suka amince da soyayyarsu.
Nan fa sukaci gaba da soyayya ba kama hannun yaro, sosai Yusuf ya yi farin jini a cikin dangin Fadeela ƙannanta maza da mata kowa Yaya Yusuf.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya sosai shaƙuwarsu ke ƙara wanzuwa har ta kai lokacin da akace Yusuf ya turo magabatanshi, ba musu ya doshi hanyar Katsina domin da gaske ya ke auren Fadeela ya ke so yayi daman shi a Kaduna karatu ya ke a salinsa ɗan jahar Katsina ne kamar yadda ita ma Fadeela a Malumfashi aka haifeta tana zaune ne a gaban Auntynta.
Ya faɗawa iyayensa kuma sukayi na’am da batun aka sa wa abin albarka, sannan kai tsaye akaje neman auren Fadeela daga gidansu Yusuf, Sun amshesu cikin karamci inda aka bashi kuma aka saka aure wata goma masu zuwa.
Gaskiya ƴan uwanta da ƙannanta suna son Yusuf sosai, saboda hannunsa a buɗe ya ke, mutum ne shi mai yawan ƙyauta.
Duk ranar da basu ganshi ba kuwa sun dingi tambaya kenan, “Yaushe Uncle Yusuf zai zo?” ɓangaren Yusuf ma sosai ya ke ƙaunar Fadeela ko ɓacin ranta baya so, haka mahaifiyar Yusuf tana ƙaunar Fadeela sosai. Fadeela na son Yusuf ita ma kuma tana tsananin kishinsa har ba taso ta ga wata me suna mace kusa da shi, soboda tsantsar ƙaunarsa da kishinsa da ta ke, a kwana a tashi babu wuya a gurin Allah haka lokacin bikinsu ya yi ta ƙaratowa duk da a lokacin Fadeela tana karatu ne a School of health tech makarfi, shi kuwa Yusuf tuni ya kammala karatunsa a KASU yanzu kasuwanci ya ke kuma ba laifi yana samu, yana da rufin asiri daidai gwargwado, haka lokacin biki ya zo ranar wata asabar aka ɗaura auren YUSUF NUHU da amarya FADEELA AHMAD…..

Domin jin yadda za’a gudanar da shagalin bikin mu kasance a page na gaba.💃💃💃
*MUMMY AYSHATU CE*🖊️

*SOYAYYAR YUSUF DA FADEELA*

RUBUTAWA:
*MUMMY AYSHATU*

*TRUE LIFE STORY AND SHORT STORY.*

 

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

*PAGE 5-6*

Biki wan shagali, Biki ne na Ƴaƴan gata. An ɗaura auren Yusuf da Fadeela sannan anata gudanar da hidimomin biki.

Anan Kaduna duk akayi wasu shagulgula, in da amarya da ango sukaci ado kamar a sacesu a gudu, da ka gansu zaka hango tsantsar dacewarsu da juna, a ranar bikin aka gudanar da ƙayatacciyar dinner wacce ƴan uwa da abokanan arziƙi suka halatta, komi tsaf amarya taci adonta cikin wani material Ash colour da akawa ɗinkin riga da siket, taci make up, ƙyawun da tayi ma faɗa ɓata baki, ango kuwa cikin ɗanyar gezna shadda riga da wando harda malin-malin, shima Ash wacce ta zauna cif a jikinsa.

Maganar gaskiya amarya da ango sun sha kyau, in da aka gudanar da fatyn cikin kwanciyar hankali, anci kuma an sha sosai, har taro ya tashi lafiya cikin jin daɗi da farinciki.

Da dare aka kai amarya ɗakinta, in da ƴan uwanta suka mata rakiya bayan nasihohin da iyaye suka mata, a Kawo aka ajiye amarya.

Ma sha Allah komi ya yi, dan ɗakin amarya kam Alhamdulillah ya yi ƙyau, two bedrooms da toilet sai kitchen, sai ƙaton parlournta da yaji kujeru na alfarma, komi cif-cif gwanin ban sha’awa.

Da dare abokai suka rako ango Yusuf, in da aka haɗu da ƙawayen amarya akayi ta barkwanci daga bisani kuma akayi addu’a tare da yiwa ango da amarya nasiha, in da suka tafi suka bar ango da amarya cikin shauƙi da mararin wannan rana me tarihi a gare su.

Ma sha Allah Yusuf ya ke furtawa domin jin daɗinsa da wannan rana da Allah ya nuna musu, sunyi sallah raka’a biyu tare da addu’o’i domin nuna godiyarsu ga Allah da addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya, tun a lokacin Fadeela ta ce”My love, ɗana na fari in har namiji ne to ina so mu saka masa suna YUSUF” cike da jin daɗi Yusuf ya amsa “To in sha Allahu Allah ya bamu masu albarka” ta amsa da amin.

A wannan dare Yusuf da Fadeela sun kasance cikin farinciki da farantawa juna rai sosai.

Washe gari da safe, sai shi ya temaka mata tayi wanka tare da sallah, bayan shima ya dawo masallaci da kansa ya shiga kitchin ya temaka mata sanna bayan kammala komi ya koma ɗakin, kwanciya ya yi sai wajen goma na safe suka farka, tare suka yi wanka sannan ya jata suka karya tana ta mamakin ashe ya iya girki (Ummu Affan ta ce Fadeela ruwan shayin ne girki? Dan shi kaɗai ya dafa, sauran duk a sarrafe suke, sai ƙwai da ya soya.🤪)

Sosai Yusuf ya ke nunawa Fadeela kulawa da tattali watansu guda da aure Fadeela tacigaba da karatunta.

*Ku biyoni a shafi na gaba in sha Allahu*

*SOYAYYAR YUSUF DA FADEELAH*

RUBUTAWA;
*MUMMY AYSHATU*

*TRUE LIFE STORY AND SHORT STORY*

 

Leave a Comment