Hausa Novels

Ruwa Biyu Hausa Novel Complete

[11/13, 8:05 PM] My Zahrah: ๐‘๐”๐–๐€ ๐๐ˆ๐˜๐”
<๐‘ฒ๐’‚ ๐’”๐’‚๐’š๐’Š ๐‘ซ๐’‚๐’š๐’‚ ๐’Œ๐’‚ ๐’”๐’‚๐’Ž๐’Š ๐’…๐’‚๐’š๐’‚ ๐‘ฒ๐’š๐’‚๐’–๐’•๐’‚>

โ„๐”ธโ„ค๐”ธ๐•‚๐”ธ ๐•Žโ„๐•€๐•‹๐”ผโ„’๐•Š ๐”ธ๐•Š๐•Š๐•†…

Bismillah Rahmani Raheem.

https://my.w.tt/EcTsIaOy2ab

_Allah subhanahu wata’ala ya halicci d’an adam domin ya bauta mishi, kuma bawai zaka kare shi da kome bane! Sabida babu abinda zaka yi dan ka biya shi wannan kyautar da yayi mana! Koda miskala zarratin bazamu tab’a karen shi da kome ba! Haka zalika ba zamu rage shi da kome ba!ย  An karbo hadisi daga d’an Abbas, yace Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya fada mana cewa! Da zamu hadu mutanen farkon mu da mutane karshen mu, mu roki Allah. Dukkan mu zai amsa bukatar mu! Ba tare da ya manta daya min mu ba! Ashe kuwa dole bawa ya kasance mai godewa Allah da ni’imar da yayi mishi! A duk cikin halittun da Allah yayi. Babu wanda Allah ya karrama shi kamar D’an Adam, a cikin Alqur’ani mai tsarki Ubangiji yayi batu da yawa akan Dan Adam!ย  Ya kuma bashi labarin kanshi a cikin Alqur’ani! Ubangiji yana sane yayi mu masu banbancin Halitta. Wasu farare! Wasu bakakke! Wasu kuma zabiyoyyi! Kuma yana sane da banbanta mana ra’ayin mu akan addini! Sannan ya kaddara wasu fararrun alamari zasu iya shigowa tsakanin mu!ย  Dan haka da wannan nake kuma godewa Allah da ya bamu ni’imar da bamu isa mu saya ba sai dai mu gode mishi!_ Alhamdulillah!

1989/ July/ 21
Jigawa state

Hadeja General hospital.

0๏ธโƒฃ1๏ธโƒฃ

“Dan Ubanki idan kika kuma shigowa rayuwar Ma’aruf sai na saka an yanka min ke. Anyi minย  Gunduwa Gunduwa da namarki, bake mayya ba sai na cofin Babanki yar shegiya, tsinaniya. Kai idan na kuma see you a najeriya, a go cofin kan uwarki bake magret ba toh ko markade kike babu sassauci a tsakanina da ke, yan banza me manyan idanu, maza take yor culot maki sakawa ki bar garin nan dan uwarki kar na kuma ganin yor lege, a garin nan yar banza me manyan idanu.” Cikin shashekar kuka matar da bazata wuce shekaru ashirin da hudu ba, ta durkusa a gaban wata mata wacce idanunta Babu alamun rahama tace cikin bagwaren hausan da bai gama rike bakin ta ba,
“Riฦ™o yaro sai Maman shi don Allah ku bani baby na, i swear ba zan kuma came back to Ma’aruf ba, please baba”

Tauuu suka dauke ta da mari sai da ta dungura, dai dai shigowar Nurse dakin da aka kai Magret, cikin jin haushi Nurse din tace.
“Amma baku da imani, taya mace daga haihuwar ta ko hutawa bata yi ba, zaku zo ku sakata a gaba! Kuna cin mutuncin ta, haba ku kuwa!” Kallon jelar gashin Magret a hannun Surayyah tayi. Cikin mamaki take kallon tsantsar rashin mutunci a idanun su. Takowa ta yi tare da d’ago matar cikin tausayawa ta ce.
“Mutanen na basu da imani, kuma zasu iya cutar dake, idan kika tsaya sai sun baki yaronki. Kiyi hakuri kinji.” Kallon kayan jikin jikin Hauwa. Riko hannunta tayi suka saka kai zata fita, ta kwace hannunta, tana kuka tare da fadin.
“Karku rabani da Yarona, ku bani Yarona.” Haka Nurse Salamatu taja ta suka fita. Kuka take kowa ya ganta sai ya tausaya mata, har suka bar ward din, sannan ta kaita wani daki ta bata kaya ta saka, riga daban zani daban. Sai dan kwali, da ta daura. Hawaye na zuba mata. Ta ce mata.
“Please ga Yarona a hannun Allah yana kuma hannunki, ki saka ido akan shi, ki kuma bani layin asibitin nan zan tafi idan na isa, US zan kira ki. Don Allah karki cire idanunki akan shi yaro karami sun hanani shi.” Haka ta riko hannun ta suka fita sai da ta samu wani a koru kura, ta sakata wanda zai kaita Kano.

***
Bayan tafiyarta Suka dauki yaron suna kara jin haushin Hauwa wacce yar asalin ฦ™asar Amurika ce, tafiyar Ma’aruf can karatu ya hadu da ita, inda suka yi aure sannan ya dawo da ita, Magret William yar wani shahararren attajiri neย  a garin newyork, ita kadaiย  ya haifa, uwarta ta mutu ta barta, shi ne ya dauki son duniya ya daura mata, ya nuna mata wata irin SOYAYYA kamar me, sai dai zuwan Ma’aruf Adamu Hadeja, ya sata juyawa Soyayyar Mahaifinta baya tace tana son Ma’aruf, duk yadda Uban yaso karta fada mugun rayuwa, haka taki fir. Sannan aka yi aure tsakaninta da Ma’aruf, sai da suka shekara biyu. Sannan Ma’aruf ya gama karatu, yace zasu zo ganin gidan zai dawo da ita. Tunda suka biyo jirgi suka dire a kano, taga yadda kasar Najeriya yake, take tsoron barinta ฦ™asar Iyayenta ya kamata, tunda suka shigo hadeja. Ta haษ—u da Muguwar uwar miji, da yan uwan miji, tare da Yayar mijinta, da farko sun dawo da arziki me mugun yawa, wanda Baban Magret ya basu, kafin su koma, amma suna zuwa Yaya Hindatu ta kwashe kome hatta kayan sakawar Hauwa sai da suka kwace. Suka wurga mata wasu matattun kaya, haka ta yi ta rayuwa, watan su biyar aka daura mishi Aure da Surayyah. Yar mijin Yaya Hindatu, tunda ta shigo gidan suke. Mata cin mutuncin, tare da wulakantata. Sun dake ta, sun zage ta. Gashi Ma’aruf yana dawowa zasu fadi karya da gaskiya babu bincike zai hauta da duka, wahala tayi wahala. Tun bata jin Hausa har ta koya dan dole. Abin takaici da ban tausayi, tana samun ciki zasu zubda mata shi, shi yasa wannan cikin tana samun shi ta boye musu baya gayawa kowa ba, har ta fara zuwa asibiti a sace. Zuwa lokacin da ta haihu. Sun kwace yaron ne, wai dan karta tafi dashi dan burin su. Tayi nesa da Ma’aruf karta zauna dashi domin ko sun hada su, sukan shirya. Kuma sun san idan ta tafi da yaron Ma’aruf zai bita, idan kuma suka sake ya bita, sunce zata rike musu shi. Da wannan nazarin Yaya Hindatu ta zuga Baba Mero ta kora keyar Hauwa.
Dan haka lokacin da Ma’aruf ya dawo,ย  Baba ta fashe da kuka tana kallon shi tace mishi.

“Dama sai da muka gaya maka, Ba zata tab’a sonka ba, gashi nan ta gudu ta bar yaron da yake cike da bukatar soyayyarta, tur da wannan rayuwar, abin tausayi yaron da aka haifa ko dumin Mahaifiyarshi bai ji ba ta tsallake shi” a zuciye ya amshi yaron, sannan ya zuba mishi ido, kwalla na zuba mishi, ya sumbaci goshin yaron sannan ya kalli Mahaifiyarshi yace.

“Gashi nan sunan shi Aamil! Zan tafi na nima mishi abinda za a na bashi, yana sha. Ita kuma Hauwa Ubangiji ya min Sakayya, Ni da Yarona.” Ya mike a hankali ya bar dakin. Murmushin mugunta tayi sannan tace.
“Babu shegiyar da zata mallake min Yarona.” Ta cigaba da kula da jinjirin. Har Baban shi ya kawo madarar da za a cigaba da bashi.

A wahale Aamil ya taso, ga rashin uwa. Yaron haka yayi ta fama da cututtukan, irinta Yara. Lokacin da ya fara rarrafe, haka zai bata jikin shi da kashi, Baba cikin jin haushin kulawar da Uban yaฦ™e mishi zata zage karfin ta ta zabga mishi duka, wani lokaci ya shiษ—e. Wani lokaci haka zai yi shiru, yana sauke ajiyar zuciya. Zai yi wuya ta dake shi bai kwanta ciwo ba.

Duk da gidan da suke family house ne, me cike da sassa masu yawa, shi yasa babu wanda yake sanin uฦ™ubar da Baba Mero da Hindatu suke bawa Aamil.

A hankali yaron yake girma, sai ya taso baya shiga cikin mutanen gidan nan. Sai ya zama na ya taso da mugun tsoron mutanen gidan. Kullum yana cikin dakin, yana da shekaru biyar, Baban shi ya samu aiki a Jigawa. Dan haka da ya tashi komawa da matar shi Surayyah, sai ya dauki yaron, dakyar Baba ta barshi, ya dauki Yaron, suna komawa can kuwa ya saka yaron a makarantar boko da islamiyya.
Sai dai idan ya tafi aiki, Surayyah bata taษ“a bawa Aamil abincin matukar Ma’aruf yana gida zata cika mishi kwano har yana zuba, idan kuwa baya nan toh, wallahi azabar duniya sai ta bashi, ta dake shi ta kona mishi hannu. Ta zuba mishi gishiri, haka zai ta kuka tana dariya. A hankali ya fara shanye irin azabar da take mishi, idanun shi ba bushewa.ย  Yana wani irin kangarewa, tare da zama mafadaci. A bayan gidan su yan shaye shaye suna zama, idan ta daidaici dawowar Baban Shi zata kora shi gurin, yana Shigowa gida zata ce.
“Yaya nifa na fara gajiya da halin Aamil idan zaka zaga gurin yan shaye shayen nan yake zama. Ka duba ma!” Yana zuwa zai same shi a gurin su, riko Yaron yake zuwa gida yayi ta dukar shi, kamar wani baba.

Ita kuma haka na mata dad’i, haka zata yi ta murna. Gashi Allah bai bata haihuwa ba, duk wanan azzabar ta take bawa Yaron.

A hankali yake girma, rashin jin shi yana kara bunkasa, fitinar shi na kara hauhawa.ย  Har zuwa lokacin da ya cika shekaru talatin cif a duniya..
โค‡

Wani irin bakin ciki ne ya tokare mishi kirji, kallon Aamil yayi wanda ya fito daga ban daki, ga budurwa da ta kwana a d’akin shi tana shafa mai, Ganin Alhaji Ma’aruf yasata mik’ewaย  tana kare jikinta, dauke kai Aamil yayi tare da kallon yarinyar yace.

“Dan Ubanki ba nace kar na same ki a waje ba, ki fita kafin naci Ubanki!” Ya daka mata tsawa. Da sauri ta, dauki kayanta, tare da fita zata saka. Abban shi ya matsa mata. Ta fita, tana mita ganin sai lokacin Aamil zai gabatar da sallar asuba. Karfe bakwai saura Kwata. Wani abin yaji ya tsaya mishi a rai, kwalla na cika mishi ido. Yana tsaye har ya idar da sallah,kallon shi yayi sannan yace mishi.
“Ubangiji kana ganin Bawanka, na fita hakkin shi na bashi tarbiyya, na kuma bashi ilimi. Ya Allah ban san me nayi ka bani shi Zakka ba.”
Cikin jin haushin Abban shi yace mishi..
“Idan baka bukata ka kore ni mana kamar yadda kuka raba Ni da Uw…” Tass ya wanke shi da mari, sai da yaji marin sosai, dan haka ya juya tare da cewa.
“Yau zan bar maka gidanka, na shiga duniya, nasan akwai mutanen da zasu rike ni, kasan aka kaunata ka samar dani, baku da wani aiki sai aibata Mahaifiyata, toh wallahi zan bar maka gidanka, tun tasowata ban san soyayyar kowa ba. Ban san dadin Kowa ba, haka na taso cikin kunci da rayuwa mara amfani, idan nayi abu kace ba tarbiyyar da kayi min ba kenan, ka tsane ni, bayan baka san meye yake faru da ni ba, taya nima bazan dasa maka bakin ciki ba, zan tafi na barku ku zauna da mutanen da suka fi maka ni?”.
.daga haka ya fice ya bar dakin har ya isa bakin kofar, Baban Yace mishi.
“Kaje kaga Sidrah?”ย  Cikin zafin rai ya juyo yana huci yace mishi..
“Abba kace baka kaunata mana! Wancan yarinyar da babu wanda ya kaita muni itace zan aura! Yarinyar da bata wuce Jaririyar ba kake cewa naje na ganta! Yar shekaru tara, wallahi ko a yar wanke wanke gidana bata kai ba balle yar da zan aura, Ni babu ita a cikin rayuwa, duk da ana gaya min cewa mahaifiya baturiya ce, karshe sai ka Hadani da bakace, meye nayi da zafi da zaku rasa kyawawan mata, ku bani sai wancan mummunar me kama da kwarangwal, yarinyar da kafin namiji ya moreta sai bayan nan da shekaru ashirin.

Wallahi idan zaka nimawa Ali ita ba laifi, amma.”

“Tabbas da kai za ayi auren! Ko kana so ko baka so! Aamil sai ka auri Sidrah, domin ba zan lamunci zubda min mutuncina da kake yi ba, kaka dauko yaran mutane kana lalata tarbiyyar su.

Sanan naka hankoron mace kyakyawa, su matan da kake lalata su ba kyawawa bane? Ko iyayen su basu kaunar su ne? Toh wallahi ka wuce hadeja gurin kaga Sidrah Wallahi ka kuskura na samu labarin baka je ba, tabbas sai na hukuntaka, dan ba zaka zubda min mutuncina ba, wanda nayi kai shekaru aru-aru ina tanadin su, sabida kai na da kimata.” Daga haka ya mai da hannun shi baya. Tare da barin d’akin.. wani uban ihu ya Aamil ya buga tare da dukar Kofar dakin shi.
*Alhamdulillahi gani nan na dawo a wani Lovestoryย  labarin yasha banban da saurar. Ku biyo Alkalamina……๐Ÿคฉ. Kuyi hakuri Daulaย  biyu! Insha Allah sai sabon shekara zaku ji ni, Ruwa biyu kuma Insha Allah! Ko na cigaba a watan da zamu kama ko kuma, A karshen shekara Insha Allah! Ya danganta da lokacin da na samu ne!* *Nagode ๐Ÿค sosai*
#Mai_Dambu
[11/13, 8:05 PM] My Zahrah: ๐‘๐”๐–๐€ ๐๐ˆ๐˜๐”
<๐‘ฒ๐’‚ ๐’”๐’‚๐’š๐’Š ๐‘ซ๐’‚๐’š๐’‚ ๐’Œ๐’‚ ๐’”๐’‚๐’Ž๐’Š ๐’…๐’‚๐’š๐’‚ ๐‘ฒ๐’š๐’‚๐’–๐’•๐’‚>
https://my.w.tt/U2ZCTqQj4ab
โ„๐”ธโ„ค๐”ธ๐•‚๐”ธ ๐•Žโ„๐•€๐•‹๐”ผโ„’๐•Š ๐”ธ๐•Š๐•Š๐•†…

Bismillah Rahmani Raheem

0๏ธโƒฃ2๏ธโƒฃ

“Taya za a ace min na auri ugly girl. Me zanyi da mace munmuna irin Sidrah yarinyar da bata wuce Jaririyar ba. Idan na yarda na shiga Lazza a daure.” Ya kuma kaiwa kofar duka, tare da make kanshi. Yana wani haki dan masifa, a fusace ya saka kayan shi ya fito daga dakin.

Tsakar gida ya fito, yana kallon yadda yaran gidan kowa ke shige da fice. Gyara zaman hular kan shi yayi tare da nufar cikin gidan, duk abinda ya gani a gaba shi ball yake dashi.ย  Ba tare da ya damu da koma meye ba, yana isa kofar da zata shiga da shi tsakar gidan su, ya ja tunga ya tsaya. Tare da zabgawa Hasnah wani irin kallon banza, sannan ya kauda kan shi, ya taka a hankali isowa inda Hajiya Surayyah take soyar kosai. Ya gyara zaman facing cap din shi yadda zai kafta rashin mutunci a silale ba tare da ya kalli fuskar kowa ba. Gyaran muryan yayi duk yan kanen shi suka dare, tare da komawa can gefe suna zare ido. Domin sun san shi hukuma ne, bai da mutunci ko na miskala zarratin, bayi da hakuri kamar rina haka yake, fushinsa yafi na mayunwacin zaki, idan yana yinka duk duniya babu wanda ya isa yace baka kai ba, haka idan ba ya yinka babu wanda ya isa yace kayi balle yayi ka, wato Aamil ruwa biyu ne..yana da sassayar hali, kuma yana da baudaddiyar hali, yana iya zama na tsawon watanni bai yiwa kowa magana ba, idan kuma aka kuskura yana gida yara suka cika shi da Hayaniya zai kama yaro yayi ta bashi azaba kamar yadda suka mishi. Mutum ne mai mugun don abu me kyau. Sai gashi ya kasance gidan su bakake ne! Musamman Familyn su.

Shi kuma ya kasance ruwa biyu, Mahaifiyar shi baturiyar Amurka, mahaifin shi bahaushen hadeja. Aamil zai iya juya harshen sa ya dai na magana da kowa cikin harshen Hausa, sai English ba tare da yaji ko dar ba. Sannan yana iya zuwa kofar Church ya zauna, duk bala’in da Christian zasu mishi ba zai tashi ba sai lokacin da yaji a ranshi ya tashi zai tashi.

A duniya ya tsani mutane uku! Baba Mero wacce suke kiranta da Hajiya. Sai Yaya Hindatu, wacce suke kiranta da Goggo hinde, sai Hajiya Surayyah wacce suke kiranta da Hajiyar mu. Dukkan su da sunan su yake kiran su. Sai dai Hajiya Uwani wacce ta kasance matar Alhaji Ma’aruf ta biyu, sai Amarya shi wacce suke kiranta da Hajiya Amarya.

Alhaji Ma’aruf yana da mata uku cif, Hajiya Surayyah uwargida sai Hajiya Uwani wacce take Binta, sai Hajiya amarya wacce take karama, A gidan Sun ware Hajiya Uwani basu yi da ita, gashi itace kusan Alhaji Ma’aruf yake ji da ita, domin itace take jibance da al’amarin Aamil kasancewar ita tayi karatun boko da na addini, sai ya zama na tana kokarin ganin ta karkato da hankalinsa kan karatu. Hajiya Surayyah da Hajiya Amarya wacce sunanta Karimah. Basu da mutunci. Kuma suna tare da Yaya Hindatu da Hajiya. Yanzun hakaย  gidan cike yake da yara Domin wani irin haihuwa ake kirin na gasa. Idan wannan tana da ciki toh Insha Allah ko Shayarwa kike sai taje ta kwaso ciki.

Sabida jahilci, idan ka cire Hajiya Uwani wacce take tsarin iyali. Saboda tana koyarwa a jami’ar jihar Jigawa,kuma tana yawan tafiya course. Dan haka ta cewa Alhaji Ma’aruf.
“Yallabai! Zaka yi hakuri gaskiya, bazan takura kai na da haihuwa akai akai ba, sabida ni ma’aikaciya ce, kumaย  ina yawan tafiya karo ilimi, kaga ba zan iya tara yara ina barin su a gida babu kulawa ba, dan haka zan iya daukar lokaci zuwa lokaci kafin na haihu.”

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya riko hannunta, ya ce mata.
“Babu laifi! Nima da ace wadancan zasu bani hadinย  da mun samu tazarar Haihuwa, domin Kinga Karimah sai da aka min magana a haihuwar Yusuf, aka ce mahaifar tana bukatar kulawa da hutu. Da kaina na kaita aka bata maganin da zata na sha na wasu watanin, amma kawai wata biyar sai naji wai tana da ciki, wallahi abin ya dame ni, kuma ba kome ya kawo haka ba. Sai kishi tunda taji Surayyah na da ciki shi kenan, magana ya kare.”

Murmushi tayi sannan ta ce.
“Manta da batun kowa, ni bana son damuwa, kai ne a gabana!”
Yaran Hajiya Surayyah, goma ga cikin na sha daya,
Ali shine babba.
Ghali ya yake binshi.
Jamila take bin Ghali.
Sadiya, Harira, Mariya,
Dejangala, Haruna, Muttaka, sai Halima.
Hajiya Uwani kuma duk yaranta biyar ne. Muhammad Aashiq, Aseed, Abdus Samad, Jalil da Jalal, Twins ne. Amma basu kama da juna ko daya.

Hajiya Amarya itace kuma take da yara mata huษ—u. Zakiyah, Ihsan, Mufidah, sai Muwaddah. Sai Yusuf. Da kuma ma cikin jikinta.

Yaya Hindatu, tana da yara biyar. Musa, Sai Dayyabu da Abdullahi, sai Hasnah da Baria. Gidan Alhaji Ma’aruf, yana da matukar kokari. Domin bayan Kanwar shi akwai matasa kusan guda bakwai a cikin gidan. Da suke karatu a karkashin kulawar shi. Faruq, Mujaheed, Sulaiman. Ismail, Mahmoud, Saleh. Bala. Isah. Duk suna zama mishi a shagunan shi da suke cikin kasuwar Dutse.

Duk yadda zan muku bayani akan gidan Alhaji Ma’aruf, ba zaku fahimta ba. Domin gida ne wanda baya rabuwa da baki daga kauye. Shi yasa yake noma, yana noma shinkafa, dawa, gero, masara da kuma wake da wanke suya. Sannan yana noman rani. Inda ake fidda mishi kayan lambu. Har da ya’yan itace. Sannan tsarin gidan Alhaji Ma’aruf, a bayyane yake. Domin shi baya bada kudin kome akwai duk abinda ake bukata. Kayan miya idan lokacin shi yayi. Sawa yake a kawo mishi. A yanka wasu a shanya, wasu kuma a markade su a zuba a babban deep freeze,ย  maggi kuwa kullum ake kawo laida daya daga kasuwa. Mangyada da Manja, ana kawo rabin jarka yalo ne. Sai bushashen kifi, da ake kawowa daga numan.

Duk ranar girkin mata, zata jika gero da dawa, a markade shi. Sannan a tacce shi. Washi gari kuma da sassafe yan matan gidan da masu aiki zasu tashi da gyaran wake, kafin karfe bakwai matar da take da girki ta fara soya. Masu aiki na tayata, babu batun masu aiki su zasu miki kome dole ki fito. Sannan kafin ya fita zai tara yaran shi da kuma matan ya tambayi kowacce abun da take bukata, ya ajiye musu dubu uku uku, yaran kuma dubu daya daya. Sai ya shiga dakin mahaifiyar shi ya bata dubu biyar, kanwar shi dubu biyu. Yaranta dari biyar biyar..

A kasuwa kuwa, idan ka cireย  Ghali, wallahi hatta Aamil cutar mahaifin shi yake, domin suna diban dukiyar shi, bana wasa ba. Sai dai bai da ikon ya kore su, domin yana da yakinin idan bai mutu ba, Allah zai bashi wanda zai kare mishi dukiyar Hauwa. Dan ba nashi bane, na Hauwa ne. Gashi Allah ya sanya albarka a cikinta. Duk yadda suka kai da su b’arnan Allah sai ya duba niyyar dake cikin zuciyar shi ya kuma bunkasa dukiya. Ba zai tab’a mantawa ba, duwatsunta masu daraja, ta dauka ta bashi lokacin da yake faffutikar niman aiki, bai san dasu ba. Ta cire tace mishi.
“Ma’aruf! Gashi nan ina ga zasu saya da daraja, ka fara yin kasuwanci mu gani kafin ka sami aikin gwamnati, dan ko mahaifina da kasuwanci ya fara aikin gwamnati.”ย  Guda goma sha biyu, ta rike sauran sha biyun dan guda ashirin da hudu ne.

Wannan kenan..
Kerere yayiwa Hajiya Surayyah a kai, tana zuba kullu a wuta ya kalli wanda ta kwashe sunyi kyau murmushi ya sake mata, kafin ta fahimci me, ya juye tass a filet ya kuma dauki wani mug ya cika da ruwan zafin da aka dafawa Abban su. Sannan ya mike tare da nufar kitchen ษ—in gidan ya dauki gwagwanin milo ya zuba son ran shi, sannan ya kuma juyawa ya zuba madara. Bai damu da sugar ba, dan yasan suna dafa ruwan zafin da sugar. katon bread ya gani ya yanki wanda zai iya ci. Ya fito tare da nufar dakin Hajiya uwani, yana Shiga Aseed yaja mishi Center table, ya daura abin karyawan.

Cikin nutsuwa ya kalli Hajiya Uwani da suke karyawa ita da yaranta, yace mata.
“Ummi! Yau ba zaki jira Uwar Aliyu bane?”
Murmushi tayi sannan ta ce.
“Bari kai dai, ina sauri ne. Kuma bana son su makara ne, dan seven saura kadan.”

Bai kuma magana ba, ya cigaba da karyawan shi, yana cikin cin abincin Ya jiyo muryan Hajiyar mu tana cewa.
“Wallahi idan baka shiga tsakani na da Aamil ba, wallahi zan saya Ghali da Ali su mishi mugun duka, dan iskan yaro. Ka ja mishi kunne ko kuma nayi Abin da zai damu da kanshi.” A zuciye ya mike zai fita. Hajiya uwani ta ce mishi.
“Dawo ka zauna!”ย  Dan dole ya dawo ya zauna, ta cigaba da karyawa, tana gamawa ta shige d’akinta tare da dauko sabuwar Shadda, ta ajiye mishi sannan ta juya tare da cewa.
“Jalil,Aseed, Ashiq, Abdul Jalal maza ku fito. Ina jiran ku zan muyi latti!” Da sauri suka fito tare da ษ—aukar school bag dinsu, suna zuwa kusa da Aamil suka karasa gurin shi, tare da rungume shi suna fadin.
“Brother! Idan naje hadeja ka cewa Aunty Sidrah muna sonta”

Abin ya bashi mamaki, zai yi magana tasaka hannu a baki.
“Duk da na gari, burin shi ya farantawa iyayen shi da sauran mutanen gari. Dan haka ga shaddar nan, ka dauka kaje ka ganta, sannan ga jakar can na kayan kwalliya ce, Please And please, karka kunyata mu, a gaban Baban Atiku don Allah kaje lafiya ka dawo lafiya. Muna jiran sakamakon mai Kyau.”

Gyada kan shi yayi cikin nutsuwa, yana cizon lips d’inshi. Tabbas sai yaci kutmar kaniyar yarinyar da ake bashi sallahun ya gaida ta.

Tana gama gaya mishi haka ta ficcewarta, dan akwai wani key a hannun ta, idan ya tashi zai ja mata kofar ta ne. Yayi tafiyar shi.

Tana tafiya ya mike tare da fitowa tsakar gidan, yaji ana kus-kus aย  shashin Hajiya, kamar ba zai magana ba, kawai ya leka domin sun saba cin mutuncin juna yana shiga ya kalli Hasnah da Musa, suna musu akan shi. Bai damu ba, ya shiga dakin da yaji ana gulmar dake window ta baya take.
“Ai Hajiya ina gaya miki ba yace baya son Hasnah ba, toh wallahi yar gidan Iro marigayi za a kwaso miki a jikan da kike cin alwashin sai yar gidan gwamna zai auro miki, domin Sidrah ba budurwa bace yarinya ce karama.”

“Ke hinde! Ba dai Sidrah wacce take hannun Lantana ba, wallahi zan kuwa ci mutuncin Ma’aruf. Ni zaiwa bakin cikin.”
“Hmm! Ai gwara yayi miki bakin cikin, mata baki san kome ba sai tsantsar mugunta, wallahi ba dan wancan mutumin yaron ki ne ba, sai na karya miki kafarki. Ke kuma Hinde maza ki tattara wadancan gardawan na dawo hadeja muka yi ido hudu dasu sai na baki mamaki, munafukai kawai.”

“Bana son rashin kunya ni Kanwar Ubanka ce!”ย  Ta faษ—a mishi cikin tsawa.

“Dalla yi min shiru, wallahi nazo na sami yaran sai na karya kafafun su, tunda gidan Uban na ne.” Ya faษ—a.
“Toh kwashashe, Zuri’ar masu fitsari a tsaye, dan banza jinin masu jan kunne. Zan ci uban mangofak ma. Dan haka ficce min a daki.”

_Assalamun Alaikum sisters! Wannan labarin ruwa biyu! Rayuwa ce irinta malam bahaushe! Wanda yake tafe da manuniya biyu! Tsarin hausawa da tsarin turawa! Don Allah idan bai miki ba, karki b’ata lokacin ki gurin karantawa! Domin zaki iya haduwa da abin da bai miki ba kiji Haushi na! And salon shi daban ne da sauran labarai daga sunan kawai zaki fara fahimtar haka thank You ๐Ÿ’๐Ÿ’–_
#Mai_Dambu
[11/13, 8:05 PM] My Zahrah: ๐‘๐”๐–๐€ ๐๐ˆ๐˜๐”
<๐‘ฒ๐’‚ ๐’”๐’‚๐’š๐’Š ๐‘ซ๐’‚๐’š๐’‚ ๐’Œ๐’‚ ๐’”๐’‚๐’Ž๐’Š ๐’…๐’‚๐’š๐’‚ ๐‘ฒ๐’š๐’‚๐’–๐’•๐’‚>
https://my.w.tt/pvpSrJ4R5ab

โ„๐”ธโ„ค๐”ธ๐•‚๐”ธ ๐•Žโ„๐•€๐•‹๐”ผโ„’๐•Š ๐”ธ๐•Š๐•Š๐•†…

แด๐š๐ข_แด…๐š๐ฆ๐›๐ฎ

Bismillah Rahmani Raheem

_Dedicated to all Black beauty๐Ÿ™๐Ÿฟโ€โ™€๏ธ
Daga manyan har kananun idan ke baka ce Wannan shafin naku ne!๐Ÿคฉ๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜_

0๏ธโƒฃ3๏ธโƒฃ
Ball yayi da wani jug wanda yake dauke da kunu. Yana huci tare da kallon Hajiya yace mata.

“Wallahi sai na karya kafarki, munafukar mata, kamar yadda kuka rabani da uwata, Allah sai na rabaki da naki d’an.”

Ya juya tare da barin gurin su. Yana jan tsaki, tun da ya shiga shashin sa, me dauke da dakuna biyu da kuma kitchen sai dan tsakar gida, da baranda, tare da kitchen ษ—in waje, da kuma wani a cikin falon gidan, sai dan gurin wanki da wanke wanke a waje, sai kuma dan backyard da yake dan bayan gidan inda zaka ayi shanya idan aka yi wanki.

Gidan zaman mace daya ce, babu wani abu da za a kara bayan haka. Gidan yayi kyau sosai, domin na yaran da ake ji dasu ne aka mishi. Tsaki yayi tare da kaiwa bangon, yana kuma jan Allah ya isa tsakanin shi da mutanen da suka raba shi da mahaifiyar shi. Dan haka yayi wanka ya shirya tsaf, sai ษ—aukar kamshi Oud 24hrs yake, cikin Izzah y kalli madubi yaga yadda Allah ya zuba halittar shi bai san lokacin da ya sake wani irin murmushi ba, dan yayi imani kaf Jigawa babu hadadden gaye irin shi, most ontop population guy, in Jigawa. Penny loafer shoe kiran kamfanin vinci ya saka,. takalminย  da shaddar sunyi match yayinda hular shi zanna bukar ya tafi da zaren aikin rigar shi.

Wani sarka ya saka a hannun shi kamar kaca, bayan yaย  ya saka agogon shi. Cikin kuzari irin ta jajjurtacce namiji yake tafiya tare da cilla key din motar shi sama, yana cafkewa.ย  Turuss ya tsaya dai dai lokacin da ta bude mishi zig din rigarta.

“Aamil! Sai yaushe zaka dai na guduna? Yanzun duba fa, ina haukar ka, baka ciwo na. Ina matuฦ™ar kaunarka” takowa yayi ba laifi yace a ranshi. Kallonta yayi sama da kasa, yarinyar tana wuta.ย  Kallon boons ษ—inta yayi wanda suka ฦ™asance kamar an hura balloon, sun leko daga kayan jikinta suna mishi wani blush! Fincikota yayi cikin nutsuwa yana kallon fuskarta! Kashe mata ido yayi sannan yace mata.

“Gaskiya bazan auri yar Hindatu ba. Da dai kin nemi muyi Shagali ne zan iya gayyatar ki d’akina, amma aure.” Hade bakin su tayi tare da saka hannu a keyar shi,yana kaunar shagali. Rike bayanta yayi. Tare da gyara mata tsayuwa, sannan ya rungume ta suka fara takawa bata san inda yake kai taba, har sai da ya dangana da cikin gidan, Ana gulmar Hajiya Uwani suka hango Aamil rungume da mace.

“Innalillahi wa’inna ilaihi rajioun! Amma wannan yaron anyi kwasa she. Yar waye ka samu zaka lalata musu ita, shine dan ka cika dan isk…” Ture Hasnah yayi tare da takowa gaban Hindatu yace mata.

“Idan zan yi Shagali da Yan mata, Yaran manyan nake nima. Wacce Ubanta zai boye abin kunyar da tayi dan kare martabar ba yar da babu wanda yasan inda dangin Ubanta yake! Ke kuma na kuma kama ki!” Shafa wuyar shi yayi alamun babu abinda ba zai faru ba.

Daga haka ya bar musu gidan, karshe gulmar da aka rufe kenan, daga hmm sai hmm yar me gulma tayi ciki.

***
Hadeja
Unguwar Gandun Sarki.

Babban gida ne mai dauke da tarihi, kuma me dauke da mutane kusan dari da wani abu, maza da mata yara da manyan, a takaice family house ne nasu Alhaji Ma’aruf, gidan Sassa ne daban-daban, gida ne da yake dauke da matan aure sama da arba’in da uku. Domin kowani shashin ba zaka raba shi da mata uku zuwa huษ—u ba.

Shashin Haliru nan ne shashin babban Yayan su Alhaji Ma’aruf, sai shashin Baba Mamman! Da shashin Baba Idi, sai shashin Marigayiย  kamilu wanda rikicin Jos ya ritsa dashi tare da Matar Shi da kuma yaran shi biyu. Sidrah ce kadai Allah ya tsiratar da ita, inda aka samu yan hadeja suka ce sun san familyn ta .
… Kasancewar ana sanyi sosai, duke take jikinta yana rawan sanyi, hawaye na diga a cikin ruwan wankin da aka sanyata yi, gashi ana busa wata irin iska me shiga jiki. Lantana ta leko cikin sababi tace.

“Yau naga abinda ya ishe ni bai ishe Allah ba, zaki gama kizo ko karya ko sai nazo naci kan uwarki, shegiya mara kunya, wankin da bai wuce awa daya ba kin dakile sama da awa biyu a gurin.”

A tsora ce ta kalle inda maganar ke fitowa tace.
“Innah yanzun zan gama!”
“Kar ma ki gama shegiya me ruwan mutanen daji.”
A sanyayyeย  take gurje kayan tare da kai hannunta daya tana sosa kanta, zuwa wuyar ta.ย  Yarinya ce da bata wuce shekara goma sha daya ba.

Baka ce irin bakin nan da zan iya kiran shi Golder Black! Domin fatarta ya nuna haka, baka wuluk ce, mai wani irin sheki fatarta, sai dai kashh. Ba zaka ga wannan shekin ba, sabida zunzurutun Datti da dauษ—a da suka lullube kyakyawan fatarta,

Yanayin jikinta Dan Karami ne, bata da auki dan siririya ce, mara auki. Daga fuskarta hancinsa dogo har baka, amma sanadin makeron da ya cinye rabin fuskarta ya sanya baka hango kome sai wasu irin kuraje kananu.

Wuyarta kuwa zuwa kanta, Ya ilahi. Wasu jerin gwanon kuraje ne wanda kwarkwata take haifar da shi idan yayi yawa akan mutum, hannu bibbiyu ta saka tana sosa kanta, wanda yake dan kare da kitso zanen yawo wanda yau kusan watan shi biyar tun auren Yayanta Atiku wanda yake dab sanda ne a garin Kwara.

Bakinta kuwa wanda ya kasance dan Karami, ya farfashe sabida sanyin hunturun da ake fama dashi,. Hannunta da ta saka duka biyu akanta, wasu irin Kano suka yi, dan fatar hannun har wani tashi yake, da za ayi dace a saka sosan karfe ( ๐Ÿคญ๐Ÿคฃ๐Ÿคฃ๐Ÿคฆ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ๐Ÿคฃ๐Ÿ˜‚ Wallahi Aamil ina baya ka buhun ubata ๐Ÿค”๐Ÿ˜๐Ÿ˜’๐Ÿ˜Ž๐Ÿ™†)

Toh tabbas zasu tashi, kafarta wanda suka kasance kananu, wasu manyan faso ne, wanda tsabar girman su, da za a saka Naira ba makawa zasu shiga ciki, kuma su sami mafakar siyasa. Haka samar kafarta ya tsatsage, sabida rashin kulawa. Rigarย  jikinta kawai zaka kalla ka fahimci, wata tsohuwar roba ce, da tasha gwagwarmayar duniya. Wato da zaka kalli yadda rigar yake, tasha dinkin zare da allura, amma a haka bai hanata yagewa ba.

Domin kuwa, hannun rigar zuwa wuyar rigar reto yake. Tayi futufutu, ta fita hayacinta ga wani abun yunwar da take ji kamar ba zata rayu ba. Dan jin take uwar hanjinta yana wani irin murษ—awa. Tana tsakiya da sosa kanta, aka sake mata rankwashi,. Tsakiyar kanta tana cewa.
“Shegiya algunguma, wato kece kawai malam ya damu dake shine zai hadaki da Bature mu kuma gamu banza ya, zaki ci uwarki mara mutunci kwasheshiya kawai.”.ย  Rike kanta tayi hawaye na zuba mata. Tana kallon Innah Azumi da gefen idanuntaย  tausayi. Can sai ga Iya Larai ta shigo ta samu tsakiyar bayanta, dai dai tana wankin ta dirmata dundu. Cikin jin haushi tace.
“Munafuka me kama da mayu, a rasa wacce ta dace da Amil sai ke, yar banza me muni kamar kashin dare.”ย  Kafin ta gama wankin matan gidan sun mata likis. Dakyar ta samu ta gama wanke kayan ta kuma ษ—aukar bokiti ta nufi cikin gidan domin dibo ruwan wanke wanken da zata yi.ย  ย  A hankali take tafiya cikin tsarin yanayi. Me dauke da nutsuwa da hankali, take takawa. Tana zuwa bakin rijiyar ta dauki guga ta fara jan ruwan sai ji tayi an make kiyarta kamar zata fadi ta juya.ย  Cikin tsoro tace.
“Yaya Ummu!” Buge mata bushashen bakinta tayi sai ga jini, rike bakin tayi, sauran yan matan gidan suka fito, sai da suka mata duka, sannan suka watse aka barta a kwace a bakin rijiya. Zuwan Lantana da Kande tace mata.

“Toh fa Lantana yar sarki mulki take ji gata can gindin rijiya kwance.”. Kwafa tayi sannan tace mata.
“Bani faskare naje na sheme yar banza yarinya, Ni zata janyowa tereren Bankad’a, biyar bashin dan kishiya. Wai me yasa da aka zo kashe danginta suka bar mana yar banza me manyan idanu kamar na gurjiya.”
“Hmm! Wai ai dan ma baki ganta ba, sai kace itace ke sayan omon wanki.”
Abinda ya kuma fusata Ran Lantana kenan, ta kuma janyo faskare tayo waje tana rantsuwa sai ta sheme yar banza ayi auren da toshe. Koda ta fito hango Baba Mamman yasata juyawa da itacen gida, ya dawo da Sidrah. Ya kalli Lantana yace mata.
“Kiji tsoron Allah! Duk Yaranki suna daki, sai Sidrah kika tura diban ruwa, Inda Kamilu da Safiya suka tafi muma wata rana muna gurin, bai dace ku hana yarinya hutawa ba. Ke jeki dauki abincin kici.” Yana gama fadar haka ya juya abin shi. Ya fita haka ta rab’e a jikin bango. Tana jiran a bata bakin rabonta.

Wani kofi Lantana ta nuna mata, wanda kuษ—a suna gama gaษ—ษ—a akai wanda kunun ciki ya kasance kadan ko kasar kofin, sai tukunyar dumame wanda yake gurin wanke wanke.
“Ki dauka Jikar jikar azakafi.” Jikinta yana rawa ta nufi gurin wanke wanke, ko hannu bata wanke ba, ta soka wasu mugayen faratan ta, masu ษ—auke da mugun datti. Ta fara cin abincin kamar wacce ta samu nama.

Sai da Lantana ta bari hankalin Sidrah yayi nisa da cin abincin kawai ta rufeta da duka, sai da ta mata likis, tana huci sannan ta barta. Bayan ta gama jin dukarta ta mike taje ta dibo ruwan wanke wanken, ta zauna tai tana yi ana b’ata kwanukan, har aka gama abincin rana bata tashi ba, kasancewar dambun tafasa ce, tana samu ta mike aka nuna mata cikin tukunyar dambun, tace mata.
“Sai ki kankara na san zai isheki!” Gyada kai tayi tare da zama ta kankare, sannan ta fara ci a hankali. Tana gama ci tasha ruwa, a gurin ta baza hakarkari sai barci.

(Kyakyawar gabatarwa Jarumar mu! Kuyi hakuri jaruma ta bata kai ๐Ÿ’ฏ dan bata cikin most ontop population Celeb! Bahaushiya ce yar yankin Kasar hausa)

Tunda ya nufi Unguwar, yake yatsina fuska, domin ya tsani shigowa garin Hadeja, musamman unguwar kakanin shi,. A hankali yake tusa kan motar shi, kasar wata bishiyar durumi, wasu irin yara ya hango yan gajajjeru masu rusa rusan ciki, da shafefen duwawu, fuskarsu da kuwa, tagwayen majina ce, wacce ta bushe. Hade da bushashen kunu, sannan kansu gwandal gwandal,ย  gashi sunyi fari sol da kasa, sakamakon hunturun da ake bugawa na kata’i, idanun Aamil ne ya sauka akan wani yaro wanda majina kore shar ya sauko daga kofar hancin shi, aikuwa ya janye ta tare da jan hancin, ya kuma laso inda (๐Ÿคฃ๐Ÿ˜‚๐Ÿคญ Wallahi ban tab’a labari me ban dariya irin wannan ba, ina dalili an sani karewa yaran cikin gari tanadi)ย  da harshen shi kofar hancin shi.
. Wani irin amai yaji, tare da kauda kan shi akan yaran,ย  hango wata yarinya yayi tana cusa hannunta a cikin kofar hancintaย  tana sakace tasono, zata kai baki ai bai san lokacin da ya nemi sauke amai ba, da sauri ya fita tare da barin gurin bayan ya rufe motar.

Cikin gidan Ya nufa, inda ya hadu daย  Sahiya tare da Harira, suna ganin shi suke fara sake mishi murmushi da yalayalan hakoran su. Daure fuska yayi, tare da kauda kan shi. Ya nufi cikin gidan. Bakin shi dauke da sallama, a hankali yabi sassan gidan ya gaishe su, sannan ya nufi shashin Baba Haliru. Da sallama ya shiga cikin gidan. Ya tsaya a bakin kofar.
“Lale maraba da zuwa! Sannu mutanen dutse Barka da zuwa.”

Murmushi yayi sai da Khaleesah ta had’iye yawu, dan tana karanta littafin hausa, bata tab’a cin karo da wanda aka tab’a fasalin namiji Irin Aamil ba, kai ko zata mutu ta dawo, tayi imani zata fi wancan sakaryan da aka bashi yarinyar da ko girma bata yi ba, nan aka shiga jera mishi ruwa, da abinda zai ci. Shi dai idanun shi na nima mishi gimbiyar da ake ihun yaje ya ganta.
Sati Uku da suka gabata.
Alhaji Ma’arufย  shi da Wan shi da suke Uba daya suke tattaunawa akan yanayin cigaban da ake samu na kasuwancin shi anan yayi shiru cikin damuwa kafin yace wa Malam Haliru.
“Wato Yaya wannan dukiyar da ake kasuwancin dashi ba nawa bane! Na Hauwa ne! Ina son Aamil ya nutsu ya kuma rike dukiyar Mahaifiyarshi, amma abu yaci tura dashi ake wawar dukiyar ma. Gashi baya jin magana shine kwaso yan mata kwaso samari azo a cika min guda da shaye shaye.”

“Toh kayi mishi aure mana!” Kallon wan yayi sannan yace.
“A ina zan sami wacce zata iya zama dashi?”

“Akwai mana! Ba za a rasa ba. Ni zan duba mishi ko nace na duba Mishi. Akwai Yar Kamilu. Yarinyar, tana shan azaba a cikin gidana, idan nayi magana kamar na kuma kunna mata azabar ce. Bata da wani girma sabida bata wuce goma zuwa sha daya ba.

….idan aka bashi ita, zata zame mishi karfen kafa, domin zata zame mishi reno zai yi. Kafin ya gama haukar shi ta shiga jikin shi. Wanda haka zai sanya. Ya gane cewa ana hakuri dashi, idan tayi mishi kuskuren kuma ya had’iye. Amma kayi nazarin abun yarinyar tana wahale na gaji da ganinta cikin kangin rayuwa….
#Mai_Dambu..
[11/13, 8:05 PM] My Zahrah: ๐‘๐”๐–๐€ ๐๐ˆ๐˜๐”
<๐‘ฒ๐’‚ ๐’”๐’‚๐’š๐’Š ๐‘ซ๐’‚๐’š๐’‚ ๐’Œ๐’‚ ๐’”๐’‚๐’Ž๐’Š ๐’…๐’‚๐’š๐’‚ ๐‘ฒ๐’š๐’‚๐’–๐’•๐’‚>
https://my.w.tt/sGJtOL2t7ab

โ„๐”ธโ„ค๐”ธ๐•‚๐”ธ ๐•Žโ„๐•€๐•‹๐”ผโ„’๐•Š ๐”ธ๐•Š๐•Š๐•†…

แด๐š๐ข_แด…๐š๐ฆ๐›๐ฎ

Bismillah Rahmani Raheem
#Abun ki
0๏ธโƒฃ4๏ธโƒฃ
Raba idanun shi yake, a hankali yana niman inda halittar zata fito mishi. gefeย  guda kuma yana sauraron kus-kus din da mutanen gidan suke. A ranshi yace.
_Ashe ko ina ba a rasa wahalallu_

“Ke Altine! Ina Sidrah take?” Tura baki yarinyar tayi sakamakon tambayarta da Babatar tayi mata, ta juyawa tayi ta tab’e baki tare da nuna mata Kofar madafin tace mata.
“Innarmu gata can ya she kamar asara a gidan biki”

Juya idanun shi yayi ya sauke a can arewa maso yamma na gidan ya hango wata buntuntuna, tana kwance sai barci take. Tun bai ga fuskarta ba yaji amai ya taso mishi, dakyar ya mike tare da cewa.
“Toh zan tafi.”
“Toh Alhaji karami, dan bature. Mungode yanzun zata zo.” Yana fita Inna Lantana tana bin shi da mugun kallo.

Sabuda mugun kyashi da hassada da ta sakawa ranta, Sahiya ta nufi inda Sidrah take kwance ta kifa mata mari, tare da shureta da kafa tana fadin “algungunman kawai. Bak’ar kaddarar kin hana kowa farin ciki, gwara ma ki mutu da yanzun nice da wannan zukekken ganyen!”

Tashi tayi jikinta na rawa, tace mata.
“Ya…” Kifa mata mari tayi sai da ta daina gani.
“Kiyi hakuri ba zan kuma ba!”
Ta faษ—a tana shasheka kuka,
“Maza dauki wancan kazamin hijabin An dubu kije gurin shi jaka kawai.”

Daga haka ta fita jikinta na rawa, har ta kusan fita waje sai da Ado da ฦ™arara, kamar wacce ta mishi magana. Ya samu gaban Hijab din, ya watsa mata tare da guduwa. Kaษ—e jikinta tayi tare da fita. Tun daga nesa ya hango ta.

Bakin cikin da yake ji, kamar ya kashe kan shi dan haushi. Yana ganinta ya shiga motar tare da nuna mata inda zata zagayo. Daga cikin zauren gidan Sahiya Ummu, Mabaruka, Kibษ—iya, suna kallon su. Ganin ta shiga motar shi basu san lokacin da suka ja wani mugun tsaki ba, sabida sun gama mutuwa akan shi.

Wani irin wulakantaccen kallo yayi mata sannan yace.
“Ba zan kuma zuwa ba, idan kuma na kuma zuwa ki sani zan baki kyauta mutuwa ce! D’aga min rigar ki na gani!” Jikinta na rawa ta shiga cire hijab din jikina wanda yasha mugun dattin Bala’i.

Sannan gaban Hijab ta yage har kasa, wuyar hijab din ne a rike da hijab din, sannanย  wani irin zarni da warin Datti yake fitarwa, sabida rashin wanki da kulawa.ย  ย ย  Wani banzan kallo yayi mata me kunshe da bakin cikin kana da kyakyamintaย  wani karin malolon takaici ne ya tsaya mishiย  me cike da tashin hankali, sannan yace mata.

“Dama a haka suke tunanin zan zauna dake? Babu kome a kirjin ki? Toh idan kika ce zaki aure ni yankan rago zan miki keee!”
Ya but mata tsawa, wanda ya sanya ta zabura, take fitsari ya fita a jikinta, zunzurutun tsoron shi da ya kama ta, wani irin ษ“aci rai yaji kamar ya rufe ta da mugun duka, aikuwa ta d’ago dagwala dagwalar idanunta akan shi.

Dukar motar yayi cikin tashin hankali ya juya tare da watsa mata wani mugun kallo tare da bude aljuhun motar shi ya fidda kudi yan dari biyar, ya watsa mata, sannan ya kuma ce mata.
“Bude min rigar ki na gani?” Ya faษ—a yana bude mata idanu, cikin cool Voice tace mishi.
“Malam ya ha..!
Toshe hancin shi yayi tare da kakarin amai, ya bude motar ya shiga sheka amai, kamar wanda yaci mugun abu. Sororo ta tsaya tana duban shi. Kallon me cike da tsoro yana juyawa yace.

“Na shiga uku na lalace, meye nayi da zafi aka hada ni da wacce zata kashe ni, ke sidira kike ko Sidrah, billahil azim zan b’atar dake matukar aka kuma ce miki zan zo ki gudu kawai, domin zan kai ki inda ake yanka mutane na sayar da wannan karamin kanki, su yanka ki.”.

Shiru yayi cikin takaici da jimamin wannan hadin gwarmai da aka mishi, kamar wanda aka ce Mishi ya kalle ta yaga tayi hamma, “innalillahi wa’inna ilaihi rajioun Ya Allah, ke fitar min a mota!” Ya daka mata tsawa.
Wani irin abu taji ya tokare mata wuya, cikin zubda kwalla tace mishi.
“Kayi hakuri bazan kuma ba!”

Sake tozali da yayi da red teeth ษ—inta wanda suka yi wani tsatsa daga jikin dasorinta, ya dashi cewa da ฦ™arfi. “Am deeply death, ke zombia ce, idan mutum yayi kuskure kika cije shi da wannan hakoran ki, zama dodo zai yi dan haka fita idan na kuma zuwa garin nan a sanya ni a Lazza a daure.

Munmuna me kama da, dark ghost get out.” Ya daka mata tsawa, ai kuwa ta juye mishi sauran fitsarin dake cikin maranta. Ji yayi kamar yayi ta kurma ihu, tare da jibgarta ko zai samu sassaucin abinda tayi mishi.

Allah Sarki, tana fita ta koma bayan durumi ta zauna tare da cusa kai a tsakanin cinyoyinta, ta fashe da kuka tana faษ—in.
“Me yasa baku tafi dani ba? Me yasa da zaku mutu baku janyo ni mun mutu tare ba?

Mama na gaji da kome bana so kudawo ku tafi dani, wallahi bani son zama a nan.” Ta fada cikin kuka me ban tausayi, yadda take kukan sai jikin mai sauraro ya mutu.
“Ke Sahiya ga munafuka, ko kumar uban me take? Shegiya annamimiya,ย  dama nan kika fito ina kudin da ya baki?”

Cikin rawan jiki da rashin dabara ta mika musu kuษ—in,suka kuwa rufe ta da duka, tare da jan ta a kasa, zuwa cikin gidan.
“Lantana! Kizo Kinga abinda Yaya Bature ya bata, Shegiya munafuka take zata haฦ™a rami ta binne, sabida uwarta da Ubanta sun biyaki kadan renonta.

Kai wannan yarinya akwai bakin ciki yar banza me gadon tsiya, ince Ubanki ma da ya tafi cirani, abin arziki bayi wa kan shi ba balle ya ajiye miki. Toh wallahi Lantana sai ki dage domin rijiya ta bada guga ya hana, yarinya da mugun hali, ace a baki wannan makudan kudaden ki fara tunanin b’oyewa Yo Allah na tuba idan aka yi auren ai ruwan gidanki ma sai mun roka ki bamu. Hattara dai Lantana domin kifi na ganin ka me har koma, kinyi renon wahala.”

Inji Iya Larai, wani irin bakin ciki ne ya turnuke Lantana. Ta kamo Sidrah, ta shiga dukarta tare da kwallon da ita, tana faษ—in.
“Dan uwaki nan aka kawo min ke, an kashe iyayenki wato bari na gama wahala dake, shine xaki gode min da boye abin da saurayi ya baki yar banza dangin asara toh wallahi bani isa ba, koda zaki mutu dan bakin hali sai nasha arzikin gidan ki, yar banza me mugun nufi, zai kare akanki maha’inci.”

Tsabar duka ko motsi bata iya yi, sannan ta watsa mata ruwa, wanda ya d’ago da dattin tare da kaikayin ฦ™arara da Ado ya watsa mata, ihu take na birgima babu wanda ya kuma bin ta kanta, duk suka watse abin su, suka barta a cikin wannan yanayin. Har sai da. Allah ya kawo Sabitu, dan Lantana na uku, ya ga halin da take, nan ya dibo ruwa a rijiya ya zuba yayi mata wanka shima ba ace wanka ba, dan da toka ya mirza mata tayi wanka rabonta da wanka tun auren Atiku. Shima sabida ganin Idanun jama’a yasa Lantana ta bata wata ajiyayyen kaya da akaย  b’oyewa.

Saratu, yar ce Lantana kenan. Itace Sa’ar Sidrah.ย  Komawa gefe tayi tana sauke ajiyar zuciya, shekaru biyar kenan da kawo ta Hadeja, tun bayan rasuwar Iyayen ta, bata kuma samun kulawa ba, wani irin kuka ne ya ke zuwa mata, amma bata da ikon yi. Sabida sanyin da ake busawa yana shiga jikinta, tare da rawan sanyi. Wata riga da skirt na Amintako aka bata, skirt din yayi mata yawa sosai, sai da ta daure k’ugun. Sai rigar shima har gwiwarta, sai wani baฦ™in pant me shegen datti, ta saka tare da komawa gefe tana ajiyar zuciya. Haฦ™oran ta yana haduwa da juna.

—
Yayi tsaki ya kai sau hamsin zuwa sittin, sabida bakin cikin, haka yake tukin gangancin tare da nazarin al’amarin. Cizon lips d’inshi yayi, tabbas dole ya nemi mafita dan ba zai tab’a sadaukar da Rayuwar shi a tare da yarinyar can ba.

….. Zaune suke a tsakar gida, Hajiya Surayyah, ta mike ta barsu dama sun hadu ana zagin Hajiya Uwani ce, sai Hajiya Surayyah ta mike zuwa ban daki. Kamar jira Ya Hindatu take tace.

“Ban da rashin girma da hankali, ai ko cewa Surayyah aka yi ta haihu ba zata yarda ba,ย  dube fa nan da sabon wata za a kan kayan auren Ali da Ghali, ga Yan matan ta nan suma aurar dasu za ayi amma matar nan ta baza zani ta kuma dauko ciki. Gaskiya budurwan zuciya tana damunta.”

“Hmm! Yaya kenan, ai ita burinta ta tara dukiya, dan ta sami kason gado. Kome zata yi da shi oho, yara goma ina zaki kai su, Ahtoh maji ma gani. Na mu ido.”.ย  Hajiya Amarya na dire aya Hajiyar mu na fitowa, hannunta dauke da lakar inyamurai, wato farar kasa. Zama tayi tana leka hanyar waje, suma kuma ba zaka tab’a yarda anyi gulmarta ba. Kallon Agogon wayarta tayi sannan tace.
“Karfe biyu! Uwar yan boko an kusan dawowa. Ai matar nan ina kallon ikon Allah, karfi da yaji. Ta hana Alhaji bada cefene fa, amma ai da shi yake bada cefene.”

Cabewa Hajiya Amarya tayi sannan tace.
“Yanzun kayi magana ta nuna maka ita tafi karfin ka, kiga lokacin zuwan mu bikin Atiku hadeja, kin bin motar mu tayi karshe dan bakin munafunci sai gata a motar Alhaji..wai ta tsaya aiki shi yasa ta rasa motar mu.

Kuma karki manta nice da girki fa!”

Jin hayaniyar Yaran gidan sun taso daga makaranta, yasa su katse hirar,ย  mik’ewa tayi tare da nufar kitchen, tana duba dafuwarta, amma tana tana sauri dan kar su yi gulmarta.ย  Tana barin gurin Ya Hindatu tace.
“Ke dai zaki sani, sakarya kome sai kin nuna son a sani, sai kace ba a nan aka hanata Daukar ciki ba, sabida matsala amma dan rashin sanin ciwon kai ta kuma kwaso ciki, yaron da ko shekara daya da da rabi bai yi ba.

Ita nan sai tayi goggaya da mutane.”
“Ai na fahimce ta, ko zani na sauya sai tayi ki duba shekaranjiya nake bawa kafinta sauran kudin kujerun da za a min sabida bikin yaran nan ashe matar nan.”.
Shiru tayi, sakamakon fitowar Hajiya Amarya tana zare idanu, tare da shan jinin jikin ta, alamun nayi da ita, ganin babu kome a fuskar su, yasa ta karasowa dan a cigaba da zaginย  Hajiya Uwani.
“Ina gaya muku, wallahi badan bana son damuwa ba, ai da sai na nunawa Uwani iyakarta. Domin ranar abun ya bata min rai, taya ni da mijina ke ki makale mishi.”

Fakon idanunta Ya Hindatu tayi ta mata gatsine (๐Ÿ˜‚๐Ÿ™๐Ÿฟโ€โ™€๏ธ๐Ÿคฆ๐Ÿผโ€โ™€๏ธ please don Allah kar mu zama fitinannun a cikin al’umma! Mu zama mutanen kirki wanda duk rintsi zaka ji ana bada shaida akanka, ina dalili a lokaci guda ya Hindatu ta haษ—a gulma tayi da Amarya a bayan Hajiyar mu, tayi da Hajiyar Mu bayanย  Amarya,kuma yanzun ta zauna ana yi da Ummi. Me muke nima? Ace baka da aiki sai gulma, Allah ya kyauta.”

Leave a Comment