🌹 *_QADR_* 🌹
( _The story of Rukayya_ )
Written by *Zeeneert*💞
*Zeeneert*@wattpad
Bismillahir rahmanir rahim. In the name of Allah,the most gracious and the most merciful.
*PROLOGUE*..Khilishi
*APRIL,2018*…
Dakine madaidaici dake daukeda katuwar katifa shimfide kasa se wardrobe irin na katakonnan dake manne jikin gini ta gefe daya. daga daya bangaren kuma akwatuna ne guda uku inda aka jerasu daya kan daya,daga gefen akwatunan kuwa handouts da notebooks ne jere neatly gwanin ban sha’awa sekuma yar madaidaiciyar madubi da’aka manna da gum jikin bango. tsananin ringing din da wayarta keyi ne yasata tashi daga nannauyar baccin datakeyi hakanan cikin magagin bacci tadaga wayar tana kokarin wartsake idanunta don ganin wanene wannan me shegen kiran kamar wani kayan jaraba,ganin sunan *Habiba* datayi jikin screen din wayarne yasata tashi zaune kafin ta daga call din cikin sauri ganin kiran yakusa tsinkewa,tunkanma tayi magana taji Habiba daga daya bangaren tana fadin “wai lafiyar ki kuwa Rukayya? Inata kiranki bakya dauka. ina kika jefarda wayartaki ne wai?” hamma budurwar da aka kira Rukayya tasaki tana lumlumshe idanu alamun baccin begama isantaba kafin akasalance tace “Habiba am bacci nikeyi sanda kikayita kira,banmasan kinyita kira ba sabida seyanzu naji ringing din wayar.
Daga daya bangaren cikeda mamaki Habiba tace “bacci fa kikace?” Rukayya tace “Eh bacci nikeyi,akwai laifine aciki? naga yau ba makaranta public holiday ne”.
Habiba da haryanzu take cikeda mamaki tace “wai bakiga text dina bane jiya da daddare?” cikeda rashin damuwa Rukayya tace “bangani ba Habiba,nayi bacci dawuri ai” Habiba tace “lallai kam toh wallahi kitashi kishirya kishigo school yanzu yanzunnan muyi submitting assignment din Dr. Isma’il dan yace 10:00am dot yakeson kowa yakawo,dukwanda baizoba kuma bazai karba ba sannan zero zaisaka mai batareda yadamu ba”.
Aitunda Habiba ta ambaci Dr. Isma’il Rukayya taji dukwani guntun baccin da yake idanunta sun wartsake,ta dafe kirji tace “nashiga uku, Habiba wallahi banga text dinki ba anma ganinan zuwa kuma dan Allah kujirani muje in group” Habiba tace “kidai yi sauri kizo. Inbakizoba yariga ki zuwa submitting zamuje muyi gamunan zaune duk jiransa mukeyi yazo,kindai san halinshi” daganan Habiba ta kashe wayar dif. Rukayya daketa faman yimata magiyar tadai jirata suje taren taji takatse call din,duban wayar tayi kafin tayi wurgi da’ita kan gado sannan tadubi wall clock din dake manne jikin bangon dakin 9:48am,wani irin dukan uku uku zuciyarta yashigayi,yanzu tayaya zata isa BUK kafin goma?kafin tafita daga layinsu tasamu titin samun abun hawama aikine barekuma inta isa school dinma dole tayi traking zuwa department din wanda shima wani nisanne.
Ganin tsayuwar da takeyidin wani bata lokacin ne yasata karasawa jikin wardrobe dinta tabude tadauko wata doguwar riga ta atamfa tasaka cikin sauri batareda tacire riga da gajeren wandon baccin dake jikinta ba. bandaki tashige cikin sauri ta kuskure bakinta tareda dan watsa ruwa afuskarta sannan tafito tadauko hijabinta tasaka,ta rataya jakarta na makaranta datake da tabbacin assignment din naciki sannan tadauki niqabinta dake kan akwatunan dake jere gurin tatsaya gaban yar karamar mirrorn dake manne jikin bangon dakin tana daurawa.
A parlour tasamu *Sajeed* yaron dabazai wuce shekaru takwas zuwa taraba yana kwance gaban TV yana kallon cartoon tace “Sajeed my boy?” cikin sauri yadago yana kallonta sannan yace “Aunty Ina zakije? bayau ba makaranta ba?” Kaman me shirin sakin kuka tace “Sajeed assignment zanje submitting,be a good boy,banda barna and kazo karufe kofa inna fita sannan dukwanda ya kwankwasa kofar karka bude seka tambaya wayene kaji?” Yace “Toh Aunty” kafin yatashi yabi bayanta don rufe kofar wanda alokacin ita harta fice daga gidan.
Sanda ta’isa bakin titi tasamu abun hawa 9:54am,tabbas duk saurinta tasan bazata isa kafin 10:00am ba,ga nisa,ga hold-ups din garin kano gakuma traking din dazatayi inta isa makarantar ma wani abune. Fatan ta daya Allah yasa shi malamin karya isa makarantar dawuri.
Sa hannunta tayi cikin jaka don laluma wayarta takira Habiba tasake rokonta kanta jirata anma wayam babu wayan,seyanzuma tatuna ashe akan gado tabarta garin sauri. Wani irin takaicine yaziyarceta hakanan takejin kamar takarbi tukin napep din tayi ganin baya sauri, cikeda kosawa tace “Mallam don Allah ka kara gudu,ina sauri ne” Mai napep dinma dake dan iya bakar magana ne yace “haba Hajiya duk wannan saurin danakeyi? Inbadai sokike inatashi sama bane kuma toh?” Itadai batakulashi ba ahaka harsuka Isa makarantar tasallameshi inda tawuce department dinsu. harabar makaranta shiru kaman ba Monday ba inbanda tsirarrun dalibai dake wulgawa dai dai bakaganin komai,abakin kofar department dinsu taga wani security dake zaune yana sanye da uniform tagaida shi tareda tambayar shi lokaci inda yacemata “10:21am” zare idanu tayi kafin tayi gaba tanayi mishi godiya.
Tunda tadoso office dinnasa bataga alamar colleagues dinta ko dayaba da alamar sunyi submitting sunwuce gida kenan,dukan uku uku zuciyarta yashigayi yayinda takarasa jikin kofar office din tasa kunnenta don jin ko akwai wani aciki anma shiru dukda tanada tabbacin shidin yanaciki tunda ga karan Ac tanaji akunne.
Gefe daya tasamu najikin office din tajingina da jikin gini tareda lumshe idanunta tanajin yanda zuciyar ta ke racing haryanzu. jitayi anja kujera daga cikin office din alamun yatashi kenan yayinda taji kakkausar muryarsa nayima wani magana daga ciki yace “Mallam Hamisu kagama hada dukka assignments din guri daya?” jitayi wanda aka kira da Mallam Hamisun yace “Eh Yallabai nahada” tanaji yayima Mallam Hamisun godiya kafin yace ya ajiye masa cikin drawer inda shikuma yanufo kofa yana jadaddama Mallam Hamisun da ya rufe masa office kafin yafito.
Cikin sauri tashige wani lungu dake gefen office din ta rakube guri daya ayayinda yabude kofar office din yafito inda Mallam Hamisuu ke biyedashi yanacewa “Yallabai nima bazama zanyiba. gida zanwuce yanzu”.
Haka suka fito Mallam Hamisu yarufe kofar duktana boye cikin lungu tanaji suna hirarsu sama sama,ga kamshin turarensa daya zame mai natural kamshin shi haryanzu tanaji yana ziyartar hancinta. Idanunta suna lumshe haryazo yawuce wanda ba foot steps dinshi bane yasa tagane a’a kamshin turarenshi daya kara kusantan tane and that genuine feeling datakeji aduk sanda yazo guri. bata ankara ba taji Mallam Hamisu na tambayarshi koyana bukatan wani abune ganin ya tsaya cak daga tafiyar dayakeyi din.
Shiru yayi nawasu dakiku kafin yasake dawowa baya yanadan dube dube kaman meneman wani abu,cankuma yadubi Mallam Hamisu yace “nikam akwai yarinyar datazo ne bayan daliban nan suntafi?” girgiza masakai Mallam Hamisu yayi alamun a’a kafin yayi gaba.
Jin footsteps din Mallam Hamisu ne yasa tagane suncigaba da tafiya,lekowa tayi ahankali tana binsu da idanu hartadaina ganinsu ayayinda idanunta ke zubda ruwan hawaye masu dumi. ta gwammace tayi loosing marks dinnan than taje submitting assignment din itakadai. haka tabar department din weakly takoma gida.
Koda tadau wayarta missed calls din Habiba ne ba’adadi batadamu dabin kiran nataba don kota kira dinma batada abun cemata, it’ll only make matters worst because the more she think of submitting this assignment the more complecated it’ll be for her life shiyasa ma tayi deciding ta hakura.
Washegari Tuesday schools sukayi resuming don daman hutun good Friday da Easter Monday aka basu and hutun yakare tunda yau Tuesday. seda tayi dropping Sajeed a school sannan tawuce BUK,koda tashiga makarantar ko’ina very busy, student nata kai kawo cikin harabar makarantar alamun kowa yadawo normal daily activities dinshi nada. Straight museum din department dinsu tawuce kasancewar batada lecture se 12:00pm. katon room ne dake daukeda bencina da kujeru farare gwanin ban sha’awa sekuma side daya da akayi gini da katako inda akasaka glass amatsayin kofar daza’abude gurin in anyi sliding dinta.
Different kinds of specimen ne na fossils acikin daya gefen glass din yayinda dayan sashin kedauke da samples na different types of rocks da akadauko daga field. babu kowa cikin museum din kasancewar lokacine da yawancin dalibai kedaukan lecture and moreover inba specific reason ba daman daliban basucika zuwa museum din department dinba.
Samun daya daga cikin kujerun tayi taja tazauna sannan ta ajiye jakarta kan desk din tana kokarin fiddo da drawing materials dinta da wayarta don fara assignment din Professional Ahmad daya basu sanda yazo, aranta tana fadin “gwanda inyi yanzu inhuta tunda inada time dan inna tsaya wasa sede inji mutumin nan yasake dawowa” dayake visiting lecturer ne dayake zuwa daga ABU Zaria.
PDF dake dauke da questions din yaturama class rep dinsu inda shikuma yatura musu a WhatsApp group. tunda tayi downloading batabi takan questions dinbama seyanzu datake budewa,maps ne yabasu sunfi kala ashirin yayinda yace sufidda *Geologic Cross section* din kowanne,wani irin ajiyar zuciya tasaki tana ayyana wahalar course din ” *Structural geology* ko wahala? “.
Wuraren goma da rabi sega call din Habiba nan yashigo wayarta,dagawa tayi suka gaisa kafin Habiban tatambayeta inda take fada mata tayi kafin sukayi sallama,ba ajimaba kuwa sega wata madaidaiciyar budurwa dabazata wuce shekaru ashirin da dan dori ba tashigo,karasawa tayi kusa da Rukayya fuska daukeda fara’a tana fadin “kekam kinmin wayau kinata assignment dinki inacan inata shashanci agida” murmushi Rukayya tasaki wanda dukda niqabin dake fuskarta hakan baihana bayyana fara’ar fuskarta ba tace “naga banida abunyi ne yanzu shiyasa nayi deciding nazo narage ko kadan ne” Habiba tace “Aiko kinkyauta ma kanki nima ba infara nawa kafin time din *Geophysics yayi* “.
Haka Habiba tashiga kokarin ciro nata drawing materials din daga jaka tana fadin “nayita kiranki jiya bakya dauka” Rukayya tace “kibari kawai nabar wayan agidane fah tsabar rudani” Yar dariya Habiba tayi sannan tadubi Rukayyan dakyau tace “Anma dai kinsamu kinyi submitting koh?” Jiki sanyaye Rukayya ta jijjiga mata kai alamar a’a cikeda mamaki Habiba tace “how comes? bakizo bane?” Rukayya tace “nazo mana Habiba” Habiba tace “bakisameshi ba kenan?” Rukayya ta gyada matakai alamar eh don tafara gajiya da questions din Habiban and it’ll be worst inta nuna mata bata yi submitting dinba Habiba tace “sede inhakan dan yatambayeni ke,yacemin Ina wannan kawartawa mesa niqab?meya hanaki zuwa? nace masa bakisani baneba amma nakira nafada miki you’ll be on your way” Habiba takarada “Ke wallahi yabani mamaki. ashe duk tsare fuskarsa da jan ajinsa yana noticing dinmu inbahaka ba ya akayi harya sanki yake tambayarki Rukayya?” Rukayya datakejin kamar zuciyarta tayi exploding tayi karfin halin cewa “Waya fadamiki noticing dinmu yakeyi? yadai gane nine sabida issues din dayita hadamu a field dakuma farkon zuwanshi” Habiba tayi murmushi sannan tace “kumafa kinada gaskiya dan wannan mutumin yanda fuskarsa ba annuri hakanan yana shasshan kamshi bana tunanin zai rike fuskar kowa,kedinma dan kinasa niqab ne shiyasa yake ganeki may be” itadai Rukayya bata kuma cewa komai ba hakanan tanata kokarin yaki da zuciyarta da tadaina raya mata abubuwan da basu baneba.
Muryar Yunusa colleague dinsune yafiddo da’ita daga duniyar tunanin datashiga yace “tundazu niketa nemanki Rukayya” da mamaki tadubeshi dankuwa basabawa sukayi ba bare ace wani abun zai hadasu dahar zainemeta hakanan duk yan ajin nasu ma babu wanda take interaction da inba Habiba ba sannan dukansu sunsaka mata idanu kancewa itan tanada girman kai da kyale mutune bayan itakuma bawannan ne dalilinta naqin sabawa dasuba,she has a good reason,reason dinda itakadai tasan abunta dakuma mahimmancin yin hakan.
Haryanzu mamaki baibar fuskarta ba tace “bangane kana nemana ba,meya faru?” fuska ba yabo ba fallasa yace “Dr. Isma’il ke kiranki yace kisameshi a office dinshi yanzu yanzunnan” daganan Yunusa yajuya yayi tafiyarsa batareda yajirajin amsar Rukayya dinba. wani irin jirine taji yazo mata lokaci guda hakanan take jin zuciyar ta na race.
Habiba dake gefenta secemata takeyi tatashi tajeta anma ina hankalinta baya jikinta, she’s in the outta world for a moment. jijjiga ta Habiba tayi ganin yanda ta sandare guri daya tanafadin “bakiji me Yunusa yace banewai?”.
Jiki sanyaye tace “naji” Habiba tace “Toh kitashi kije mana,am sure dan assignment din yake kiranki tunda nafada masa uzurinki jiya” gyada ma Habiba kaitayi kamar wata wawiya kafin tashiga tattara takardunta tasaka ajaka tayi gaba,tasan ko giyan wake tasha Habiba bazata rakataba sabida tsananin tsoronsa dasukeyi.
Harta isa bakin kofar office din batadaina zullumi ba. tunda yazo makarantan bata taba yarda tahadu dashi itakadai ba sede tareda Habiba ko da other colleagues dinsu inwani abu yakaisu office dinsa shiyasa yaudin takejin wani irin nervousness,she’s afraid her heart will explode infront of him, she’s afraid actions dinta na’iya sawa yagane ta yau din bayan duk kokarin datayi wurin boyemasa kanta for more than two months now.
Folding hannayenta tayi a kirji in order to get hold of herself,bata ankara ba taji Mallam Hamisu tsaye kanta yana fadin “Rukayyatu lafiya kike tsaye nan?” cikin sauri tadago tadubeshi yana tsaye da alama yazo zaishiga office dinne yaganta tsaye murya narawa tace “lafiya Mallam. Ina kwana?” Mallam Hamisu yace “lafiya Lau. bakisami H.O.D dinnaku bane?” yayi maganar yana pointing windown office din Dr. Isma’il din cikin sauri tagyada masakai tareda juyawa dan tafiya inda Mallam Hamisu yabude kofar yashiga ciki, ganin office din Ogannasa bude kuma yana hangoshi daga inda yake yasa yakoma waje yana kiran Rukayyan yace “kidawo yananan,ashe bakima duba ba”
Dole tadawo badan tasoba gashi bugun zuciyarta se karuwa yakeyi. abakin kofa suka kusa yin karo da Mallam Hamisu zaifita inda hannunshi kedaukeda wasu files da alama abunda yadawodashi office dinnashi kenan.
Seda yawuce kafin tashige,daman Mallam Hamisu shine secretary din Dr. Isma’il wanda seka bi tagurinshi kafin kasamu office din Dr. Isma’il din dake can ciki. daga inda take tana iya hangoshi zaune dayake kofar office dinnashi bude take.
Karasawa tayi tayi sallama inda ya amsa batareda yadago yadubeta ba.
Shiga tayi tarufe kofar daga ciki sannan tashiga gaishe shi cikin muryarta dake karkarwa,amsawa yayi ayayinda yadago yasaka idanunshi cikin nata saurin sauke nata idanun kasa tayi. Matashin saurayi ne dabazai wuce shekaru talatin da dan doriba,shiba fariba shiba baki ba. zadai mu’iya kiran kyakyawan fatarshi dayake smooth da chocolate colour dinnan,kala mai tsada.
Kallo daya zakayi mishi kagane bafulatani ne usul gaba da baya sabida yanayin fuskarshi,karamin bakinshi dayake shiba pink bakuma bakiba,hancinshi dayake very pointed kamar karas yayinda idanunshi kenan medim dashi gwanin ban sha’awa,sajenshi kadai Inka gani zai tabbatar maka da kyawun gashin kanshi. yana sanye da coffee brown gezna datasha dinkin zamani yayinda kanshi kedauke da hula shima me touch off din coffee brown din. Idanunshi nasanye da medicated glasses daya karama fuskarshi haiba da kwarjini.
Murmushi yasaki ganin tasauke idanunta kasa yana mamakin yaushe tafara jin kunyar ganin cikin idanunsa,dan gyaran murya yayi yakoma bossy type dinshi lokaci guda kafin yace “Your friend told me that you were not aware za’ayi submitting assignment jiya. Why?”
Batareda tadago tadubeshi ba tace “I was not informed” yace “But your class rep posted on your WhatsApp group,don’t you have an Android phone?” yanzunma kanta na kasa tace “Yes Sir” kallon dayan hannunta dake rikeda Android phone yayi wanda tanajin intense gaze dinsa kan wayar,cikin sauri ta boyeta abayanta nervously.
Murmushi yasaki sannan yace “where’s the assignment?” jiki narawa taciro jakarta daga kafadunta tajefa wayar ciki dasauri kafin tashiga neman papers din datayi assignment din”.
Mika mishi tayi yakarba ya ajiye tana fadin “Thank you sir” ayayinda muryarta na karkarwa gyada matakai yayi yayinda tajuya don fita,harta isa bakin kofa zata bude taji yace “Nanaah”
tsayayawa tayi cak kaman statue tana kokwanton abunda taji din,jin baisake cewa komai ba yasa tayi tunanin ko imaginations dinda takeyi kullum ne yaudinma……
Sa hannu tayi kan handle din kofar zata bude takuma ji yace “Nanaah” shiru yayi nadan wasu dakiku kafin yayi magana yace “Atunaniki bazan ganekiba?” wannan karan araunane yayi maganar,muryarshi na nuna how much he missed her and how much he yearns to call that special name.
Yatashi daga zaunen dayake yadawo yatsaya tsakiyar office din yayi folding hannayenshi a kirji tareda zubama bayanta idanu yanajin yanda kukanta ke ratsa duk wani sassa na illahirin jikinshi,cikin wata iriyar murya mecikeda kewa,tausayi,pain dakuma kauna yace “indai kinyi tunanin banganekiba tunsanda nafara daura idanuna cikin naki bakiyima soyayyar danakeyi miki adalciba,bakiyima connection din dake tsakanin mu adalciba,bakiyiwa bond din dake tsakanin mu adalciba sannan bakiyiwa alkawarin damuka daukar ma juna adalci”….
Baima kai ga karasa zancenba tasa hannunta jikin handdle din kofar tabude tafice aguje tana kuka maitsuma zuciya. Zuciyar ta nada rauni akan wannan bawan Allah,indai tacigaba da sauraronsa toh tabbas zata iya manta duk wasu abubuwa dasuka faru abaya takarbe shi hannu bibbiyu bayan kuma things are not like before.
He deserve someone more better.
Adaddafe ta’isa gida,straight dakinta tawuce tarufo kofar daga ciki sannan tazube jikin kofan tana rusan kuka haryanzu.
Miyasa zaidawo cikin rayuwarta alokacin da ta ajiye past dinta agefe tafara sabon rayuwa? tariga tadaukar ma kanta alkawarin nisantar dukwani dayake da alaka da past dinta dayake cike da kunci,nadama,bakin ciki dadai sauransu. miyasa zai tuno mata da pains dinda haryau inta tuna suna hunting dinta?
She thought she started afresh,a new life where babu wata gwagarmaya na rayuwa datasha abaya sede kash! yau gashi mutumin da taji anakira da Dr. Isma’il yadawo cikin rayuwarta,ya tuno mata daduk wasu pains dinda tayi going through a rayuwarta,a pain that’s she’s been carrying in her heart for more than 8years now,pain dinda itakadai take gwagwarmayar dashi acikin ranta batareda tayi sharring dakowaba even though it hurts,even though she needs a shoulder to cry on wanda tanada tabbacin inta fadama wani it’ll be like a relief, it’ll ease her pain. Toh anma wazata fadamawa? waye takedashi dazai iya tausayi mata yace “Rukayya kiyi hakuri everything will be alright”….
Ayanzu batada kowa dazata iya sharring wannan tarihin dan dukwanda take tareda su din tayi musu karya for years dabazata iya gogeshi ba yau kadai. idanunta sunyi cazir sun canza launi hakanan tanaji yana knocking kofar yana kiran sunanta anma ko gezau batayiba harya gaji dan kanshi yatafi.
Idanunta ne suka sauka kan litattafanta dake jere gefen akwatunanta and then an idea came right away. tashi tayi jiki ba kwari takarasa gaban litattafan nata sannan tadauki katuwar long note dinda tasaya tun last week don practicing drivations na *Geophysics* tadauki pen cikin jakanta sannan takarasa kan study table dinta dake can wani gefe a dakin…
Zama tayi ta ajiye littafin kan study table din tareda bude first page tana tunanin “may be inta rubuta tarihin rayuwarta taji sauki aranta,may burden dinda take carrying for more than 8years yaragu,may be her heart will somehow be at ease for a moment da inma takamane she’ll published the book and distribute it to the world,taba ma mutane su karanta suji tarihin rayuwarta,su tausaya mata suce Rukayya ke jaruma, Rukayya kinyi kokari Allah ubangiji yasaka miki, Rukayya you’ll have a better future ahead” and may be intaji wadannan motivational words din zataji sauki aranta,zata samu courage din cigaba da rayuwarta batareda past dinta gacigaba hunting dinta ba.
Goge hawayenta daketa zuba kan littafin tayi kafin tayi turning zuwa next page ganin page din farkon yajike da hawayenta tadaga bironta tafara rubutu inda takejin rayuwarta na shekarun baya dasuka wuce sunfara dawowa filla filla.
*Waye yakeson Jin labarin Rukayya dake cikeda dimbim al’ajabi da mamaki? waye yakeson Jin labarin Rukayya dake cikeda kunci,kiyayya, yaudara,cin amana dakuma tsagwaron soyayya mecikeda tsafta da alhini?*…
Toh Kubiyo *Zeeneert* cikin littafin *Qadr* dazai fara 1st of August in Allah yakaimu darai da lafiya.
Ina masoyana suke?
Inakuma masu amfana dakuma karuwa daga littatafaina? I know you’ll always patronize me and stand by me sabida duk maisonka yake kaunar ka dakuma amfana dakai bazaiyi kyashin kaima ka karu dashi ba😄…..
Like you always have trust and believe In me wannan Karan ma bazan watsa muku kasa a ido ba Insha Allahu. *QADR* Littafine danakeda yakinin duk wanda yakarantashi bazai yi dana sani ba.
🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_)
Written by *Zeeneert*💞
*Zeeneert*@wattpad
*One*
Free page
Sunana Rukayya Umar Shattima,nida iyayena da wasu daga cikin dangin mahaifina muna zamane a cikin garin Bauchi. Asalin mahaifina bafulatanin Giyaɗe ne dake under Bauchi state wanda most of his family members suna zama acan,mahaifin Babana wato kakana babban malami ne acikin garin Giyaɗe da babu inda zaka shiga agarin Giyaɗe katambayi waye “Mallam Abubakar Shattima” ba’a kaika har gidansa dake hade da tsangayarsa na almijiran dayake koyarwa ba. Kakana nada mata huɗu wanda kuma cikinsu babu wanda bata haifa masa ɗa ba, ƴaƴansa ɗai ɗai har goma sha huɗu,maza tara mata biyar wanda agurin mahaifiyar Babana “Innani” mahaifina da kanwarsa “Suwaiba” kadai tahaifa Allah ya karbi ranta. Kaf cikin ƴaƴan Kakana mutum huɗu ne kawai suka maida hankali kan western education yayinda sauran daga sunyi primary suke watsar da karatun su koma na alloh dakuma harkar gonan mahaifinsu. Kawu Idrissa, Kawu Sani,mahaifina sekuma autansu a maza Kawu Adamu ne kadai sukayi karatun boko sosai wanda acikin sunma Kawu Idrissa ne kadai yakai har matakin gama jami’a inda sauran ukun primary, secondary da diploma kawai sukayi. duk karatun dasukayi mahaifinsu beki goya musu bayaba dan kuwa sauran ma yaso suyi karatun haɗin kaine kawai basu bashi ba, Kawu Idrissa daya gama karatunsa besamu aiki atake ba shikuma bayason komawa zaman kauye dan yariga yasaba da rayuwa cikin garin Bauchi tunsanda yake degree dinsa,kuma aganinsa inyakoma candin kaman ci bayane don wannan karatun alloh da noman ne zekoma taya mahaifinsu,wannan dalilin yasa yasamu mahaifinsu yanuna masa yanason yafara business cikin garin Bauchi kuma yagoyamai baya ɗari bisa ɗari. Haka Kawu Idrissa yasaida dabbobinsa dankuwa kaf ƴaƴan babu wanda baida gona da dabbobin sa nakansa gakuma na mahaifin nasu daban. Shago yabude akasuwa inda yafara bussiness din kayan sakawa,kama daga kayan Yara readymade,shaddodi,atamfofi dadai sauransu while on the process yana kuma neman aikin gwamnati ko Allah zaisa adace.
Wannan dabara da Kawu Idrissa yayi shiyayi motivating sauran kannensa da sukayi karatun bayan sungama sukanemi abunyi abirni suma,Kawu Sani shagon kayan abinci yabude cikin kasuwa wanda gradually yadinga bunkasa inda Kawu Adamu suka haɗa jari da Kawu Idrissa sukacigaba da kasuwancin saida sutura dan daman dakinsu daya kuma daga baya Kawu Idrissa yazo yasamu aikin gwamnati shiyasa.
Mahaifina saida kayan miya, vegetables da fruits yazabi yi dan bashida burin saida duka dabbobinsa, he still have passion for kiwo awannan lokacin. wannan dalilin yasa yasaida kadan daga cikin dabbobin nasa donsamun na jari yayinda yabar sauran ma kanwarsa Suwaiba data riga tayi aure acikin garin Giyaɗen tahada da nata tanakula musu dashi. tare akayi auren Kawu Idrissa da Kawu Adamu sekuma kawu Sani daga baya,mahaifina baiyi aure dawuri ba sabida har lokacin baisamu wanda takwanta masa arai ba.
Tunda su kawu Idrissa suka fara tara ‘Ya’ya suka yanke shawarar suda suke gari daya why not su sayi katon fili suyi gini kowa da apartment dinsa, atleast suna zaune guri daya kuma kan iyalansu bazai rabuba,koda suka tashi sayan filin seda sukayima mahaifina magana dukda kuwa baida aure kuma ya amince ɗari bisa ɗari,yabasu kudinshi suka hada hannu aka tada gini. ba’a jima ba kuwa mahaifina yahadu da mahaifiyata dake zuwa daga kauyen *Babban Buli* saida nono cikin kasuwa inda gefen inda yake saida kayan miyarsa ne,anan yayaba da tarbiyarta yakuma ji takwanta masa arai yafara nemanta,sanda aka gama gininsu yasa iyaye suka shiga cikin maganar.
Har Babban buli akaje aka nema masa auren mahaifiyata *Hauwa’u* inda akabasu aka kuma saka rana kasancewar Kakanmu sananne ne shiyasa ba’ayi wani dogon bincike ba.
Bayan aure mahaifiyata da mahaifina suna zaman lafiya cikeda so da kaunar juna. Matsalarta daya ne batajin dadin zama da matan Kawunaina,sun tsangwama mata,sun hade kai sun sakata agaba kasancewar tunda can su sunriga sunsaba,ga ratan shekaru dasuka bata dankuwa mahaifiyata tayi aurene at a very your age,inban mantaba mahaifina yacemin agidansa ma tacika shekara sha biyar.
Kuma duk wannan takunkumin yasamo asali ne tunda sukaga son da mahaifina yakeyi mata. dukda shine me karamin karfi cikin kawunai na,bai rageta da komai ba dan kalar abincin datakeci itadashi ma ya banbanta danasu gashi kullum inzai dawo seya kawo mata tsarabar,tsire ko nama kowani abun marmari dai hakanan baya boyema kowa sonda yakeyi mata, barinma data samu ciki na. duk wani aikin wahala hanata yakeyi sabida cikin yazo da gardama,shizaiyi musu wanki,yayi shara da wanke wanke kullum kafin tafita dankuwa data fara wanke wanke take fara amai sabida batason kamshin sauran abinci alokacin,itakanta bason tayatan takeyiba anma haka yadage dole ta hakura. Girkin abinci kawai takeyi musu se ɗan ninke kayansu dadai ɗan abunda baza’arasaba.
Wannan shiya kara jamata tsana wurinsu dankuwa su basu samu irin wannan kulawarba sanda sukeda nasu cikin gashi ko yanzun ma bakaman yanda shi mahaifina yake kula da mahaifiyata ake kula dasuba wannan yasa suka sakata gaba,duksanda mahaifina da kawunai na suka fita haka zasuyita sakata aiki suna tsangwamarta,itakuwa bata taba fadama kowaba dan mutum ce me juriya,hakuri dakuma sanin yakamata aganinta koba komai sun girme mata nesa ba kusaba.
Haka zatayi musu aikin dasuka sakata takoma daki tayita kela amai wani sa’in harda zazzabi anma kosau daya bata taba sanar da mahaifina halin da ake cikiba har cikin yagirma sosai yarage wahalarda ita.
Tun sati biyu to zata haihu mahaifiyata take nakuda tana daurewa dan wurin sau uku suna zuwa asibiti ana dubata ace dasaura. Ranar wata juma’a mahaifiyata tatashi garas da’ita babu ciwo wanda hakan yabama mahaifina kwarin gwiwar fita kasuwa inda ya jaddada mata intaji batajin dadi tashiga gurin matan yan uwanshi tasanar dasu tace “Toh” bayan yafita baijima ba cikinta yafara murɗa wanda dafari taso daurewa anma abun yaci tura wannan dalilin yasa adaddafe tafita zuwa sashin Matar Kawu Sani dake namu sashin yafi kusa da’ita awannan lokacin,tasanar da’ita halin datake ciki anma sece mata tayi ita aiki takeyi bazata iya yimata komai ba,wayasani ma ko shegen rakin ta ne yatashi zatawani ce nakuda,jiki sanyaye takoma sashinta dan tasan sauranma kusan thesame excuses zasu bata.
Harbayan azahar tana kwance tana fama da ciwon ciki wanda ayanzu tagama galabaita. mahaifina daman yakanzo gida cin abincin rana daga kasuwa kullum sabida yafi gane yaci girkin mahaifiyata,to yau ma hakan ne tafaru,sanda yazo gida da sallama yashigo amma da mamakinsa mahaifiyata bata amsamai ba kamar kullum.
Cikin sauri yakarasa cikin parlourn inda yaganta yashe kasa,cikeda rudani yashiga kwala kiran sunanta harya isa gareta yana tambayarta meke faruwa wanda ko magana ta kasayi,dole haka ya samo mata hijabi yasaka mata ya sunkuceta se bakin titi yana neman taxi wanda daganan suka wuce asibiti.
Anfi awa biyu tsaye kanta kafin akasamu tahaifeni and unfortunately for me she loose her life. Sanda nurses din da suka karbi haihuwata suka sanar da Baba bakaramin tashin hankali yashigaba,haka yakarbeni ya rungume ajikinsa yana kuka me tsuma rai. Tsabar tashin hankali ma kasa kiran kowa yayi dole ɗaya daga cikin Nurses ɗin ne ta karbi wayarsa ta kira Kawu Idrissa da Kawu Sani suka sanar dasu halin da ake ciki
ganin sunayensu ne mafi kusa a call log dinsa.
Kankaceme segasu a asibiti cikeda mamakin wannan al’amari dan cikinsu babu wanda yakawo wa baiwar Allahn mutuwa,sede abunda basu sani ba shine shi mutuwa ba’ayi mishi haka,babu ruwanshi da babba babu ruwanshi da karami,babu ruwanshi da mai lafiya Babu ruwanshi da marar lafiya,Babu ruwanshi damai kudi ko talaka hakanan babu ruwanshi da burin mu bayin Allah. In lokacin tafiyan yayi dole atafi,babu gudu babu ja da baya,we’re all just struggling without knowing our final destination,tafiya mukeyi batareda munsa ranar tsayawan muba. Allah ne kadai yabarma kansa sani kuma muna fatan yasa muyi kyakyawan karshe.
Rayuwa kenan. Cikin mintuna kalilan akayi ma mahaifiyata sutura aka kaita gidanta na gaskiya
Leaving us in a world where we can never get someone like her dagani har mahaifina,sabida babu kamar uwa arayuwa hakanan babu kamar soul mate ɗin da mutum yayarda dashi ɗari bisa ɗari,babu abunda yakai abunda ranka keso muhimmanci arayuwa kuma shima yakesonka in return. Shiyasa mahaifina was shattered sabida gani yakeyi bazai sake samun kamar mahaifiyata ba.
Gida yacika sosai ankuma yi zaman makoki yayinda ni kullum cikin ihun kuka nikeyi asanda akabani labari hakanan dukwanda yakarbene seyaji tausayina.
Dangin mahaifiyata sunso karbana bayan komai ya lafah anma dake gwaggo Suwaiba tariga tanuna tanason rikeni yasa dole suka hakura,haka gwaggo Suwaiba tatafi dani Giyaɗe tahada da ‘Ya’yanta take kula dani inda mahaifina yake zuwa akai akai ya dubani har tsawon shekaru uku.
Bayan nan nayi wayau sosai nafara magana nakuma fara gane waye nawa waye ba nawa ba, alokacin gwaggo Suwaiba nike gani matsayin mahaifiyata dan cikin gidan babu wanda take nuna min banbanci dukda kuwa nasan Mijinta ba mahaifina bane tunda kullum in Baba yazo gwaggo Suwaiba nacemin shine mahaifina itakuma kanwarsa ce anma yarinta baibari nasan komai ba. Alokacin ne kuma Baba yanuna yanason mayardani gurinsa sabida kewa dayake cike da’ita na nida mahaifiyata,his home feel so empty without us wannan dalilin yasa yasamu Kakana da maganar anma fir yaki yace ta’ina zaitafi dai bayan babu mai kula masa dani? inkuma yadage seya tafi din to sede in yasake aure atleast tarbiyata zaikoma hannun wata tunda shi bazama yake agida koyaushe ba.
Sabida son komawana gida da mahaifina keyi yasa ya yarda zai Ƙara auren dukda kuwa bashida wanda yakeso. Kakana dakanshi yasamo mishi mata gurin wani malami ɗan uwansa a cikin garin Giyaɗe,haka akayi aure tatare dan itama bazawara ce aurenta biyu tana fitowa,tunda nadawo gida nake zaune da Yadikko na nadaina jin dadin rayuwa even though I was a child anma ainasan in an kyautata dakuma in ba’a kyautata min ba.
Daga ta dukeni akan silly things se ta zageni,ban isa inyi wasa da kayan wasan da Baba yasiyomin ba haka zata dukeni tace zanbata mata guri bayan tayi gyare gyare,kallo ma ban isa inyiba,fita gurin yan uwana yara muyi wasa ma ban isa inyi ba setace zanje inbata jikina waje in ja mata wanki. Kullum cikin tsangwama,abinci ma seta ga dama zata bani wani sa’in se inyi kwana biyu ba’amin wanka ba,innayi fitsari a bandaki nakirata tazo tamin tsarki setaki kula ni haka ko kashi ne setace inyi dakaina ai yarinya kamar ni yakamata ace nasan irin abubuwan nan,inbanayi tayaya zankoya? haka zan dulmiya bandakin da kazantata wurin kokarin yin tsarki inkuma tazo tagani shima yazama laifi. Duk wannan wainar da ake toyawa mahaifina baisani ba dan agabansa kulawa take nuna min na musamman wanda nikuma tsoronta yake hanani faɗa masa sannan shima Mama bawai yabani wannan fuskar baneba tunda aganinshi ana kula dani dari bisa dari. Gradually suka fara sabawa da matan Kawunai na wanda suka dinga hada mata karya da gaskiya game da mahaifiyata,wai ta asirce mahaifina se abunda tace yakeyi,wai tayi ahankali dani yanda taga mahafina yana sona ɗin nan ma wayasani ko asirin har akaina tayi masa. wannan yasake sa takara takuramin akan wanda takeyi da sekuma yazamanto kullum tana gurin su suna hira toh Inna fita danzuwa gun yan uwana muyi wasa sesu sakani gaba suna zagi,daga mecemin ina warin kashi seme min korar kare,i was 5years then and nafara gane komai sede infashe da kuka inkoma sashin mu,haka nadinga hakuri har Allah yasa wataran Baba yadawo yasamu tana dukana,jikina duk yayi radau radau dashi tana kuma zagina. Bakaramin mamaki yayiba sabida for almost three years betaba ganin this side of her ba,dayayi mata magana don neman ba’asi setakasa controlling emotions dinta tafidda halinta atake which left him in dismal. Take yajani jikinshi yana tambayata abubuwan dasuka faru hakanan banboyemai komai ba dan gani nake inhar nabar chance dinnan tatafi bazan sake samun wataba,he was beyond shock dahar seda yayi hawaye akuma take yasaki Yadikko Basira yace duk abubuwan datayimin don muzgunamin Allah zaisakamin takuma sani itama tabar Ƴaƴanta awasu gidan,she never know yaza’ayi treating ɗin su? Inka wulakanta ɗan wani kai wazai daraja taka? And what will she gain by bullying an innocent child like me fisabillahi?.
Tundaganan Baba yace bazai sake aureba indai banyi wayau ba besides,shidaman sabida inzama ina da mai kula dani din shiyasa yayi auren. haka yazame min uwa yazame min uba,kullum shizaiyi min wanka,yadafamin abinci yakuma gyara ko’ina agidan kafin yafita kasuwa hakanan duk inda yake hankalinshi nakaina,in time din lunch yayi dole zaidawo gida yakawomin dan yawanci akasuwa yake saya nasafe nedai yake mana dakanshi.
Kawu Adamu ne yafara noticing wahalar da Baba na yakeyi wanda hakan yasa yakirashi yamishi magana kan why not inzai fita yana barina a sashin su,anan za’ayimin komai tareda sauran Yan uwana abincima kuma bawani matsala baneba. Haka ya amince da shawarar wan nashi bawai don yaso ba sedan karyace yayi rejecting offer ɗin shi,duk safe senaci abinci kafin natafi sashin su hakanan inzai dawo da dare zaitahomin da kayan makulashe sede fah rayuwata takoma gidan jiya dan yini nake cikin damuwa.
Wurin yan uwana ma banasamun sauki dan they make mockery of me all the time tunda daman sunsaba,iyayensu sun koya musu wannan dalilin yasama banason fita wasa dasu namafi enjoying ayyukan da ake tiƙa min acikin gidan,haka nakoma kaman machine daga wannan matar takirani zata aikeni se wancan tace inyi mata kaza dan Kawu Adamu yazo yakara aure kawu Sani kam daman tunbayan auren sa bada jimawa ba yasake auren. I never complained to Baba dan ni mutum ce daban iya kai labarin abunda akayimin ba inbawai antambayeni ba. Ni Babu abunda yafi damuna ma irin yanda suke involving dina a harkan kishinsu,wannan tace tariga kirana wancan tace kaza hakadai.
Wani abokin Baba a layin mu dayaga ana yawan aikena kuma kullum cikin kuka yake kallona yasa yayi calling attention dinsa,yafaɗa mai halin da akeciki wanda Baba dakanshi yafara dawowa gida darana yana observing komai and anan yayanke shawarar barin gidan kawai,yacema su Kawu Idrissa zainemi gida kusa da kasuwa yafi,dan anan ɗin yana kashe Kuɗi sosai akan Transport kullum tunda haryau besayi abun hawaba,basu ji dadin decision dinshi ba hakanan basukuma hanashiba.
Haka Baba yasama mana gida akusa da kasuwa muka koma can nidashi,akuma take yasayi machine dinsa roba roba,yasamamin makaranta both islamiyya da boko dede karfin shi nafara zuwa daukan darasi,seya zamanto banama yawan zaman gidan dagani harshi. Dasafe tare zamu fita yakaini makaranta haka darana zezo ya ɗauke ni muje gida muci abinci nayi wanka nasauya kaya semu sake fita tare,inya ajiyeni a islamiyya seya koma bakin aikinsa.
Daman kuma 6 ake tashi,daya daukeni zamu koma gida inda zaibar sana’arsa gurin yaransa dake tayashi.
Haka rayuwar mu takasance cikin jin ɗadi da walwala,banida wanda nashaku da irin mahaifina,dan shine komaina arayuwa. In anyi hutun makaranta kuwa banayinshi agida,dan inwannan hutun yakaini Giyaɗe to next hutun kuwa Babban Buli zaikaini wurin dangin mahaifiyata wanda se alokacin nasan mahaifiyata tarasu.
Gidansu kawu Idrissa ma yakan kaini inmusu wuni,kamar a weekend haka hakanan duksanda naje sundinga jin haushin yanda nayi bulbul dani,haka zasuyita gulmace gulmacen su.
Tun sanda nashiga primary five mahaifina yafara fama da yawan jinyace jinyace.
Littafin *QADR* na kudi ne don samun damar shiga paid group Amin magana tawannan number for payment details
08147722806.
Vote
Comment
Share!
🌹 _*QADR*_ 🌹
( _The story of Rukayya_ )
Written by *Zeeneert* 💞
*Zeeneert*@wattpad
*Two*
Free page
Jinyar kuma regularly dankuwa baya wata daya bekwanta ciwo ba,gashi kullum cikin shan magani yakeyi,yarage fita kasuwa yaransa dake tayashi suke kulamai da kasuwancinsa yanzu.
Haka zansaka Baba agaba ina kuka in naga bayida lafiya because shine kadai abunda nake kallo inji dadi araina inkuma ji cewa nima mutum ce,I was 11years then ina neman 12 dan nama kusa shiga. nafara wayau nakuma fara sanin ciwon kaina dakuma sanin abubuwan da akayimin abaya. muna third term a makaranta wanda gap muke da fara jarabawar shiga aji shida da bakowa keyinta ba sai ɗai ɗaiku kuma ina kyautata zaton ina ɗaya daga cikinsu dan koda aka faɗa mana ana saida forms na common entrance na exams ɗin shiga boarding schools like federal colleges dakuma Turkish international Schools kin faɗa ma Baba nayi,acewata na gwammace inyi primary six ɗin incigaba da day than inje boarding school inbar Baba shikadai. babu kuma abunda yakara tunzurani da ƙin makarantar kwana irin yanda kawayena dakeda yayu a boarding school suke bani labarin muguntar da akeyi acan.
*September,2007*
Sanda muka gama exams mukayi hutu daman kauyen *Babban Buli* garinsu mahaifiyata yakamata inje hutu anma ganin rashin lafiyar mahaifina ya tsananta kwanan nan yasa nace masa ni babu inda zani zanzauna muyi hutunmu agida tare.
Atake Baba yacemin “A’a injeni kawai,babu daɗi tunda sunsaka ran ganina”. duk yanda naso yin rigimar bazani ba seda yaki dolena nafara shiri anmafa na qudiri niyar zanna zuwa ganinshi bayan kwana bibbiyu tunda daga kauyen *Babban Buli* zuwa cikin garin Bauchi babu wani nisa.
Washegari dasafe yakaini yayini tareda Bappanaina kafin yadawo gida da yanma. dukda babban Buli kauyene kutub anma inajin daɗin zuwa garin sabida sonda yan uwan mahaifiyata kenuna min,duksanda naje nan nan sukeyi dani hakanan duk abunda nakeso za’ayimin barinma Kakata da ake kiranta da *Gogode*,sona take tamkar ƙwai gashi kullum cikin pampering ɗina takeyi wanda hakan kaɗai zainuna maka irin sonda takema mahaifiyata.
Sa’anni na kuma ƙawaye na su Hari,Mairo,Bulo da Kwaiɗum duk sunada samarin su dan har ansaka ranar auren Bulo wanda hakan bakaramin mamaki yakebani ba tunda cikin mu ma banga wanda yafara irgen dangi ba bare sauran signs na nuna cewa mun balaga,innaji zasuje hira dariya abun yake bani tunda ga yarinta karara afuskar mu duka sannan cikin birni naga bahaka akeyiba.
Yau kwanana biyu agarin natashi daniyar dubo Baba inda already nagama hada plans ɗina. Tun sassafe nasamu Gogode na kalallameta da maganganu masu daɗi dukwai don tabarni inbi su Hari ciki gari tallen Nono daganan in sulale gida ganin Baba na anma fir taƙi dafari seda nasaka mata kukan shagwaba sannan tabari. Haka muka kama hanya muka tafi kasuwar Bauchi,daman ranar cin kasuwa su suke kaiwa inda yayunsu kekaiwa kullum. koda naje rumfar Baba na saida kayan miya yaran aikinshi cemin sukayi yanzun nan yatafi gida zaidawo anjima wanda kalamansu yasa naji dadi sosai tunda har yasamu yafito ranar sede fa harmuka tashi tafiya baidawo ba dole nabisu Hari muka koma Babban Buli bayan nabar sallahun sugaidaminshi.
Washegari kuwa segashi yazo Babban Buli,da gudu naje na rungume shi yana shafa kaina yace *Mamana* (sunan dayake ƙira na dashi kenan kasancewar ni ɗin maisunan mahaifiyarsa *INNANI* ce) akacemin kinje nemana? gyaɗa kaina nayi ahankali still banbar jikin nasaba,Baba yace “karki ƙara fita ke kaɗai kinji? inanan lafiyata lau inkuma bakiyarda ba ni zanna zuwa dubaki kullum anma banason yawo Mamana”
Washare baki nayi sannan nace “nayarda Baba,nayi tunanin rashin lafiyarka zai iya tashine shiyasa naje intabbatar anma tunda babu komai bazan sake fitaba harsai ranarda hutu yakare kazo daukana” murmushi yayi bayan yacireni daga jikinsa,yashafa fuskata cikeda sona yace “Yauwa Mamana, Allah yayimiki albarka” nace “Amin” kafin yakama hannuna muka karasa cikin gida yagaida su Gogode ya ajiye tsarabar daya kawo mana kafin yatafi.
Washegari talata itace ranar dabazan taba mantawa acikin tarihin rayuwata ba,rana ta goma sha ɗaya ga watan september,ranar da wani namiji apart from my Father yashigo cikin rayuwata and wannan shine mafarin dukwani abu dake kunshe cikin tarihin rayuwata dake cikeda abubuwan al’ajabi kala kala. Lol,I don’t know where you all first meet your soulmate but inna faɗa muku nawa zakusha dariya.
Daman a al’ardar garin Babban Buli duk safiya yara kaman mu sukan fita karkashin wata bishiyar kuka suyi surfen hatsin da iyayensu zasuyi abinci dashi ranan kafin akai injin nika. Toyau haka ta kasance,ni,Hari, Bulo,Mairo,Kwaiɗum dakuma Ƴar kanwar mamana Indo data tashi gaban Gogede duk muna nan karkashin wannan bishiyar kukar harma dawasu Ƴan matan ana surfe,except ni daban iyaba Indo ce keyimana namu.
Kowa da turmin sa da tabaryarsa yayinda suke surfen atare suna waƙa cikin yaren fillanci,inkaga yanda suke ɗaga tabaryan atare suna mayarwa cikin turmin sesun baka sha’awa inda nikuma nake zaune kan wani dutsi dabayida tsayi sosai se faɗi ina kallonsu ina dariya tareda tayasu yin wakar cikeda nishaɗi. Bamu ankara ba kawai mukaga Kwaiɗum ta zare idanu tareda sakin ihun *Gujjjoh!(Barayi!!!)* ta fillanci kafin tasaki tabaryar hannunta taruga aguje tayi hanyar gida,sauran ma dasuka ga mutanen dake tahowan suka kwasa da gudu suna ihun “Gujjo gujjo! Gujjo en(ga bayari ga barayi! ga barayi!)” dafari bakaramin tsorata nayiba nima anma dana juya naga mutanen dasuke kira da barayin sena saki dariya harda kwanciya ina riƙe cikina dankuwa abun da su Harin sukayi bakaramin dariya yabani ba ahaka har waɗanda ake ƙira da barayin suka karaso inda nake,sunkai su takwas wanda duk maza ne se mace daya kyakyawa da’ita dukda kuwa ba musulma baceba.
Dukansu suna sanye da riga da wando na jeans sekuma rigar leda koriya da’akayimata ratsin kalan ruwan toka dake sanye saman T-shirt ɗin kowannensu(Reflective jacket) yayinda kawunansu kesanye da irin hulunan kwanon nan(helmet) danake yawan ganin masu aikin kwalta nasakawa hakanan kafafunsu nasanye da irin canvas ɗin da muke amfani dashi amakaranta duk ranar sports dukdama na kafarsu dana gani yamin kyau alokacin sosai bansani ba kodan suɗin sunsa different colours da designs ne? Inda mukuma a makaranta simple white canvas kawai ake bari musaka.
Dukkaninsu akwai wata igiya dake makale awuyansu wanda igiyan naɗauke da wani farin abu mekaman shape ɗin agogon bango dan harcikin abun akwai rubutu irin wanda nake gani a agogon parlourn gidan mu. kowa naɗauke da school bag abayansa sekuma wasunsu dake riƙe da guduma,wani first aid box,wani tape dadai sauransu.
A iya sanina masu sharan titi kowani farkon wata da masu aikin kwalta dakuma masuyi ma yara allurar polio kaɗai nasan suna saka irin waɗannan riga da hulan amma sauran abubuwan danike gani tattare dasu bana tunanin nasansu,first aid box ɗin da nagani hannun ɗaya daga cikinsu ne yasa lokaci guda nayanke shawarar cewa suɗin masu allurar polio ne,dariya nakuma saki ina tuno yanda su Hari suka kwasa aguje.
Ɗaya daga cikinsu ne yazo ya tsuguna gabana tareda zubamin idanu yana mamakin yanda nike dariya kamar wata tababbiya yayinda macen dake tareda su tazo tazauna gefena tana sauke ajiyar zuciya inda naji wani daga cikin wadanda ke tsayen yana cemata “Zamafa baikamasu ba they’ve a long way to go” anma hakan baisa tatashi ba.
Dakyar na tsagaita dariyar danakeyi ganin yanda suka zubamin idanu dukansu, barinma wanda ke tsugune gabana. As soon as danabar dariyar nagaban nawa yace “meya hanaki guduwa? ko ke sharifiyace baki tsoron musace ki?” se kawai nasake kwashewa da dariya inda fararen hakwarana tas suka bayyana cikeda yarinta nace “guduwa kuma? niba baƙauya bace ba ai nasanku” kallona yatsaya yi daga sama har kasa wanda inada tabbacin kayan jikina sun tabbatar masa maganar danayi yanzu donkuwa riga da skirt na English wears da Baba yasayamin kwanakine jikina.
Seda yagama karemin kallo sannan yace “Lord. This’s interesting” yakarashe maganar ayayinda yake cire class bag ɗin dake bayanshi ya ajiye by my right yakwanta yayi pillow da jakarshi inda yashiga karema sararin samaniya kallo,da mamaki abokanan shi ke kallon shi inda me rikeda first aid box ɗin yace “Haba *Lamiɗo* yaza ka kwanta kuma?” dariya yasaki sannan yadubi wanda yamai maganar a ɗai ɗai ce yadaga hannu sama sannan yace “nifah Uztaz kadaina shigamin hanci ta kudundune. tayayama bazan kwanta ba bayan nahaduda Yar birni kamar ni” yakarashe maganar yana kashemin ido daya teasingly wanda tunda yafara magana nazuba mai idanu jin ascent dinsa irin na fulani ne and when I look at him na tabbatar da zargi na dankuwa kallo ɗaya zakayi masa kagane bafulatani ne usul because dukwasu features na fuskarsa da jikinsa sunnuna dukda kuwa ba fari bane shi.
Maganar dayayi ne yasani fita daga duniyar tunanin dana shiga yacemin “Amma ke ba Yar kauyen nan bane koh?” Ina dariya na gyada masakai sannan nace “garinsu Mamana ne nan nazo hutu gun kakanni na anma acikin Bauchi muke zama” yace “No wonder. shiyasa naganki Yar kyas kyas dake kaman ni” yakarashe maganar yana ɗaɗɗaga Reflective jacket ɗinsa irin shiɗin nan,yanda yayi maganar seda yasake sani dariya dan yanda yake magana ma kaɗai bazai barni in riƙe dariyar tawa ba.
Wanda ya ƙira da Uztaz ɗin ne yasake magana akaro na biyu yace “Haba *Lamiɗo* kai akodayaushe seka jamana delay newai kai?,katashi mutafi mana dan Allah kuma kamata yayi musamu yan kauyen nan muyi musu bayanin abun da yakawo mu semu wuce bawai mutsaya bata lokaci ba. kanadai gani jiya haka akayita mana faɗa damuka koma late” daganan Uztaz yadubi macen dake zaune ta dayan gefena yace “Faith let’s go please” inda sauran samarin ma suka fara ma *Lamiɗo* mita,jin sun dameshi yasa yatashi zaune yace “kunfa isheni wallahi tallahi. kuma daɗin abunma niban cema kowa yajirani ba daman. tare Ummana ta haifoni dakune ko tare aka turo mu makarantar dazanyita bin abinda raina bayaso kamar wani ɗan taure? kuyi tafiyarku kawai” daga cikinsu wani yace “Anma dai kasan bazai yuyu mutafi mubarka bako?firstly you’re the group leader and secondly ance muna tafiya as a team kada muyarda muraba kanmu. Inmuka tafi muka barka mezamuce ma malaman namu kuma?”
Shrugging shoulder ɗinsa yayi yana dariyan shakiyanci yace “wannan ku ya dama koni nace abani group leader ɗin?”
Dukansu inka ga fuskarsu zaka tabbatar ransu abace yake ga abunda yayi ɗin, ɗaya daga cikinsu ne yazo yaja hannunshi yana rokonshi daya tashi sutafi wabce hannun yayi sannan yajuyo yakalleni yace “Yar birni kiraba mana gardaman nan dan Allah” senayi shiru ina kallonshi dukda kuwa sunan da yakirani dashi yabani dariya.
Ya gyara zamansa sannan yashiga zayyanomin yanda suka fara aiki as a team jiya yace “Yar birni dukkaninsunnan babu wanda baisan halina ba,babu wanda baisan kalulana da unseriousness ɗina ba amma dan wulakanci da aka tambayesu wasuke son abama group leader sukace ni” ya ware hannunsa yana kallona sannan yacigaba da magana “toh ni mema nasani a geologyn da har zasu sa abani group leader inbanda zagi?” Saurayin danaji yana kira da Uztaz yace “that’s past Lamiɗo, group leader anriga anbaka sekayi hakuri awuce gun” Yar dariya yasaki sannan yace “dabanyi hakuri ba koh ganina bazakuyi ba aradun Allah” Uztaz yamatso inda yake yana dafa kafadunshi yace “Toh yi hakuri katashi mutafi, we’ve a long way to go” sake cire hannun Uztaz din daga kafadunshi yayi sannan yace “Naqi. sena gama bama ‘Yar birni labari” yajuyo yacigaba da kallona sannan yace “kinajiba?” na gyada masakai ahankali bawai don inagane kan labarin nashi baneba sedan kawai yanason bani ne kuma babu dadi in sace mai gwiwa.
Yace “nayi hakuri nakarbi group leader dinda suka kakaba min,jiya muka fara field work dinnan. haka muka yini muna nausawa cikin daji kamar wasu mahaukata,ko mafarauta iyakaci batareda naga wani abu mai mahimmanci dasuketa ikirari ba” yarinyar dasuka kira da Faith tace “haba *Lamiɗo* duk rocks dinda kagani basu isheka kalloba? and we discovered alot of things after that” hararanta yayi sannan yace “Dallahhh! Inbanda duwatsu uku da aka nuna muku tun zuwan mu kinsake ganin wani kala daban kuma?” Faith dariya tayi sannan tace “Kai baka gani ba kenan?” Yace “Ahap! anma kema dai akwai ki da tambayar rainin wayau wallahi. Yoni Ina ruwana da haukan ku? kawai binkufah nakeyi don babu yanda na’iya ne” Faith na dariya haryanzu tace “toh kayi hakuri kacigaba da binmun Lamiɗo” yace “naji. anmafa yausaina huta gaskiya” yakarashe maganar yana shirin sake kwanciya da alama ma yamanta ni yakebama labari.
Uztaz yayi saurin rikoshi yana fadin “Don Allah karka kwanta” yayinda wani daga cikinsu yace “inbanda Lamiɗo ma a aikin jiya kawai harzakayi jumping into conclusion? bayan zamuyi sati biyu muna abu daya besides, mapping fah akace muyi so don Allah katashi muyi abunda yakawo mu bakatsaya kana bama yarinyar unnecessary labarin dabama ganewa takeyiba” *Lamiɗo* yamaimaita kalmar “Yarinya” kafin yakwashe da dariyar yana kallona sannan yace “Naji. Kuma inma jariri naje inabama labari babu ruwanka
dani Mallam. kuma komadai menene nisai na huta gaskiya” yakarashe maganar yana kara shirin kwanciya, Uztaz yayi saurin sake rikoshi.
Nikuwa dana zuba musu idanu inajin zancen su tun ɗazu cikeda curiosity nace “Daman ku ba ƴan polio baneba?” wani irin zabura Lamiɗo yayi yana zare idanu wanda har hakan yakusan bani tsoro,yakama salati yana tafa hannu yace “laha ila ha ilallahu Muhammada rasulullahi” yatashi tsaye yafara tafiya yana musu alama da hannu yace “Kuzo! kuzo! Kuzo maza mutafi. ashema duk kanwar jaaa ce natsaya inabata labari” yacigaba da tafi yana salati “kukodai akwai bakin jini aradu. Yan birnin ma kansu basugama saninku ba bare Yan kauye” yayi maganar yana nunnusu da yan yatsunshi kafin yakwashe da dariyar mugunta kuma,bin bayanshi sukayi suna dariya dukda kuwa bata musu randa yayi yayinda nikuma nabisu da idanu ina mamakin reaction ɗinsa.
Can nahangosu tsaitsaye tareda Bappanaina dasu Kwaiɗum da alama su Kwaiɗum ɗin ne sukaje suka sanar dasu Barayi sunshigo musu ruga shiyasa suka ɗungumo suka taho don gani da idanunsu. tashi nayi dagudu nakarasa inda suke tsatsaiye inda naji suna gaiggaisawa da juna kafin Uztaz yashiga yimasu Bappanaina na bayani yace “Daman mu ɗalibai ne daga jami’ar Gombe munzo duba yanayin duwatsun dake yankin nanne dakuma albarkatun kasa” take Kawunai na suka sakar musu fuska yayinda Kawu Idiii yace “Allah sarki. yara suntsorata dasuka ganku ai shiyasa suka shiga gida da gudu don sanar damu,kunsan barayi sukanzo su sashe mana dabbobi da yara shiyasa sukayi tunanin ko kuna daya daga shicinsu ne” murmushi dukansu sukayi kafin sukace “A’a ba abunda yakawo muba kenan kuma insha Allahu kullum zamuzo muna wuce wa tanan dan inda aka yankar mana mu duba gaba da kauyen nanne sannan nanne kaɗai hanyar da zata sadamu da bakin titi mukoma gida shiyasa komunshiga dajin dayanma tanan zamuna fitowa” Kawu Idi yace “yayi kyau. bakomai Allah yabaku sa’a” dukkansu suka amsa da “Amin” kafin sukayi musu sallama suka tafi sunacewa “sesun dawo” inda naji Lamiɗo kuma nacewa “Aradun Allah innaje naga yauma duk duwatsun irin ta dace bankara binku sede kowa yayi takansa. haka kawai,azauna anata tsara mana karyayyaki da bamu wahala sannan ace karatu mukazo yi? toh bazai yuyu ba”
Littafin *QADR* na kudi ne don samun damar shiga paid group amin magana tawannan laying for payment details
08147722806.

Leave a Comment