hausa novel blog
‹ › Home
View web version
Thursday, 5 January 2017
aisha ummi at 03:48
KWARYA TABI KWARYA 1-End
, 8:04 AM] Ummi A’isha: [1/12, 7:52 AM] Ummi A’isha:
KWARYA TABI KWARYA! 1⃣
Na UMMI A’ISHA
JAN KUNNE duk wanda ya canja wannan labari ko yayi editing dinsa, ko kuma ya cire sunan marubuciyar ko ya canja sunan taurarin ciki Allah ya isa ban yafeba!.
CANAL AWWAB MANSUR ADAM shine sunan dake manne agaban rigar dake jikin kyakkyawan sojan wanda ke fitowa daga cikin babban bankin Nigeria wato CBN acikin garin abuja dogone kyakkyawa wankan tarwada yanada matsakaicin jiki, sanye yake cikin uniform din sojoji wanda suka dace dashi yana rike da waya kirar BlackBerry bold 2 baka hannunsa daure da agogon azurfa na Rolex, yar karamar bindiga ce rataye agefen aljihun wandonsa kansa babu hula shekarunsa bazasu gaza 29 zuwa 30 ba, kai tsaye inda yayi packing din motarsa ya hara, motar tasa yar yayi ce kirar zamani wanda sai wane da wane ne ke iya hawanta, BMW New modern itace motar da ya bude yashiga blue colour, fita yayi daga cikin harabar bankin ya nufi unguwar wuse kansa tsaye ya tasamma wani babban gida mai yalwar shuke shuke kamar akasar India kasancewar unguwar unguwace ta manyan mutane kuma unguwace tamasu kudi, yawancin ministers da mukarraban gwamnatin tarayya ne acikin unguwar, hon yayi mai gadi ya bude masa yashiga ya Adana motarsa yafito yana rike da wayarsa ya shiga cikin gidan tunda ma’aikatan gidan suka hangoshi suka fara russunawa suna diban gaisuwa shi kuwa canal sai shan kamshi yake dahaka yakarasa wani wawakeken falo ginin zamani wanda ya kayatu da kayan alatu, yar karamar bindigar dake jikin wandonsa yazaro.
[10/8, 16:52] Admin Aysha:
KWARYA TABI KWARYA2⃣
Na UMMI A’ISHA
Bindigarsa ya zaro daga gefen aljihunsa ya ajiye akan dan karamin stool din dake ajiye acikin falon, benen dazai kaishi falon hajiyarsa yabi har zuwa cikin kawataccen falon nata tana zaune cikin shiga ta alfarma da Kamala ta zubawa makekiyar tv din dake manne ajikin bangon falon ido, wata drama take kallo a channel din CTV, ahankali yashiga cikin falon bakinsa dauke da sallama cikin fara’a ta dago ta dubeshi tana faman murmushi, Awwab barka da zuwa, yawwa umma sannu da hutawa kusa da ita yaje ya zauna yafara gaida ta cikeda sakin fuska ta amsa masa gaisuwar da yake mata, cikin muryar shagwaba yace umma dan Allah ki samo min yarinya wadda zata rinka gyara min bedroom dina domin kullum idan nazo acikin datti nake ganinsa nikuma banida time din da zan zauna na gyarashi, murmushi tayi to awwab akwai wata yarinya da zata zo ta zauna awurina inyaso ko ita sai ta rinka gyara maka dakin, yawwa thank you umma, bari naje nayi wanka saboda ina son na dan kwanta na huta, gobe da sassafe zan koma ibadan jirgin 6 nake son bi, kallonsa tayi soja kenan Allah ya kaika lfy ya tsareka maza aje a huta kafin abbanka yadawo daga office, yayi min waya cewa 3 zai dawo gida kaga yanzu kuma 2:20 tayi, to umma sai nafito, saukowa kasa yayi ya dauki bindigarsa ya nufi side dinsa wanda yake da dan tazara kafin kaje, yana shiga dakinsa ya tube kakinsa ya shiga toilet yayi wanka yafito sallah yayi sannan ya kwanta akan luntsumemen gadonsa wanda yasha shinfidu da kaya masu laushin gaske, bai jima da kwanciya ba bacci ya daukeshi, acikin baccin nasa yafara mafarki da wata kyakkyawar budurwa tabiyoshi da wuka tana cewa sai ta rama abinda yayi mata, gudu yake itama binsa take daf dazata kamashi ya farka a firgice, firgigit yatashi.
KWARYA TABI KWARYA3⃣
Na UMMI A’ISHA
Yana tashi yafara kiran sunayen Allah tareda yin addu’a Allahuma inni a’uzubika min sharri fi manami an yadurruni fi dini wa dunniyaya, tunani yafara yi wannan mafarkin shine na 3 da yayi wannan budurwar tana bibiyarsa da wuka, to wacece? Tambayar da yayiwa kansa kenan amma sai dai bashida amsar wannan tambayar, tashi yayi ya shiga toilet yayi brush yafito, side din mahaifinsa yanufa ya tarar dashi akishingide acikin tamfatsetsen falonsa wanda ya tasaru mutuka gabansa yaje ya durkusa ya gaidashi,cikin jin dadi mahaifinsa yadafa kansa yace son kazo lfy? Lfy lau abba nasameku lfy? Lfy son ya aiki? Alhamdulillah abba, amma dai zakayi 1 week ko? Girgiza kai yayi no abbba gobe zan koma dan akwai wani training da zamuyi har na tsawon 2 weeks kuma daga gobe zamu fara shiyasa zan koma goben, murmushin mahaifin nasa yayi dakyau Soja Allah ya tsare amin Abba, hira suka zauna yi shida mahaifinsa sai daf da magriba yafito daga falon mahaifinsa ya dauki wata sabuwar motarshi Prado one door mai bakin glass yafita daga gidan, wani babban hotel mai tashe yanufa yana zuwa ya faka motarsa yashiga cikin club, yanmata da samarine kawai awurin yaran masu kudi sai sheke ayarsu sukeyi kowacce ka kalla acikin maye take, kansa tsaye ya nufi inda ake zuba giya yaje ya karbo kwalba daya wata kujera ya nufa yaje ya zauna, yana kurbar giya yana kallon yanmatan dake chashewa kamar akasar turai, ji yayi an dafashi ahankali ya waiwaya, wata kyakkyawar budurwa baka ya gani ta tsuke cikin riga da wando acikin maye tafara yi masa magana, kazo…. Muje ka… Kaini… gida luu yaji tafado kansa cikin sauri ya tureta yatashi yafito daga cikin club din,cikin motarsa yashiga ya zauna yanata kallon mutanen daketa kaiwa da komowa acikin harabar hotel din anan ya raba dare sai wurin 12 sannan yanufo gidansu.
KWARYA TABI KWARYA4⃣
Na UMMI A’ISHA
Acikin maye sama sama yake driving din har ya iso unguwarsu yashiga gidansu cikin maye yafito daga cikin motarsa yana tafiya yana hada hanya har ya isa dakinsa, mahaifinsa yana tsaye yana kallonsa ta saman benen dakinsa sai dayaga yashiga dakinsa sannan yasaki labulen dakin yana ajiyar zuciya shi dai yarasa a ina awwab ya dauko wannan dabi’a ta shan giya da neman mata alhalin da bahaka yakeba, amma tun lokacin da yazama soja yatare a bariki shikenan yadauki dabi’u munana bayan shikuma yasan yabashi dukkan tarbiya wacce uba yakamata yabawa dansa, runtse ido yayi tareda yi masa addu’ar shiriya. Awwab yana shiga daki yafada kan gadonsa yakwanta nan wani irin nannuyan bacci yayi awun gaba dashi sai karfe 5 na asubha yasamu ya iya farkawa, cikin rashin kwarin jiki yashiga toilet ya watsa ruwa yafito yatafi masallaci, bayan sun fito daga masallaci ne mahaifinsa yakirashi suka shiga falonsa cikin damuwa uban ya furta son meyasa kake haka? Yaushe zaka canja saga mutumin banza zuwa na kirki? Son sam baka iyo halina ba kuma baka iyo halin mahaifiyar kaba, tunda kazama soja kazama dan iska, cikin sauri yadago ya kalli mahaifin nasa, yes kazama dan iska awwab baka tsoron haduwarka da Allah ko kadan domin zuciyarka tagama bushewa, sunkuyar da kansa yayi yayi shiru batare da yace komai ba sai da akayi yan mintuna sannan yace kayi hakuri abba insha Allahu zan daina, cikin alamun damuwa uban yace to my son Allah yanufeka da dainawa amin abba, yanzu zanje nashirya natafi Ibadan domin jirgin 6 nake son bi, to son Allah yakaika lfy sai munyi magana amin abba nagode.
KWARYA TABI KWARYA5⃣
Na UMMI A’ISHA
Jikinsa a sabule yafito yashiga side dinsa yayi wanka yashirya yasaka kakinsa wanda sukayi mutukar yimasa kyau yadauki yar karamar bindigarsa ya soketa a muhallinta kamar kullum, dakin ummansa yaje yasameta zaune akan sallaya tana jan carbi zama yayi ya gaisheta sannan yayi mata sallama yafito kai tsaye airport driver ya kaishi yashiga jirgin kabo air line ko minti 10 ba ayiba jirginsu yatashi zuwa Ibadan tafiyar data daukesu 15 minutes, yana sauka wasu sojoji guda 4 suka zo suka sara masa tareda kamewa kai kawai yadaga musu yashiga cikin motar da aka gindaya agabansa, gidan baya yashiga sauran sojojin sukuma suka shiga tasu suka nufi barikin sojoji, suna zuwa aka bude musu gate suka shiga kofar wani gida sukaje suka tsaya anan dagudu sukazo suka bude masa kofar motar yafito batare da yayi musu magana ba cikin gidan ya shiga har wani dan madaidaicin falo inda wani babban mutum yake zaune hannunsa rikeda jarida yana karantawa, sallama yayi tareda sarawa mutumin yace Weldon sir! Dagowa mutumin yayi welcome canal awwab, atsaye ya zauna batare da ya zauna ba, sir nakaraso, ayimin afuwa banzo da wuriba, no problem canal, zo ka karbi wannan taswirar kagani, wani map ya mika masa kaduba kagani wannan dan kauyen natsakiya ana fama da tarzomar yan tada kayar baya so yanzu yanzun nan ina so kaje kahorar da sojoji guda 40 katurasu suje su kwantar da tarzomar tunda ina ganin 40 ai zasu isa saboda kauyen bashida wani girma, yes sir yafada tareda fita daga cikin falon kai tsaye wajen dandazon sojoji yanufa inda ya cika umarnin da aka bashi daga nan yatafi wani babban fili wanda iya masu irin uniform dinsa ne kawai awajen sai wani guda daya nasa daban da alama yafisu mukami, nan suka fara wani training irin nasu na sojoji sai yamma likis suka tashi, gidansa yanufa wanda yake cikin barikin sojojin yana shiga kiran basma yashigo cikin wayarsa basma itace budurwar sa wacce zai aura yanzu haka tana can a babban birnin london a Oxford university tana karantar mass com, cike da kasala da aji ya dauka hello basma daga daya bangaren ta amsa hy Darling yakake am fine basma yanzu haka daga wani training nake duk nagaji shigowana gida kenan, sonake nayi wanka nahuta, ayya to shikenan bari nabarka sai kajini bye, kashe wayar yayi tareda ajiyeta agefe yashiga wanka bayan yafito ne wani kiran yashigo wayarsa yadauka hello canal yakub ya akayi? Canal awwab ga yanmmata fa ansamo shine nace ko zakazo kaduba? No yau wlh babu abinda zan iya kawai kubarsu ni kasan bana son yan hannu nafi son virgin, ok to ba damuwa, wayar tasa yakashe domin baya son adameshi, salla yayi yaje falonsa ya bude fridge din dake ajiye giyace kala kala aciki ba don kar ummi A’isha tayi karya ba to danace muku babu lemo ko daya duk giyane aciki,kwalbar guilder ya dauko da cup yazo yasamu kujera ya zauna yafara tsiyaya yana sha.
[1/12, 8:20 AM] Ummi A’isha: KWARYA TABI KWARYA6⃣
Na UMMI A’ISHA
Sai da ya shanye kwalbar giya 2 sannan yatashi yana hada hanya yana tangadi yashige dakinsa yana zuwa ya fada akan gado nan bacci yayi gaba dashi bashi ya tashi ba sai karfe 3 nadare. Asubha tanayi yayi salla kasancewar barikice babu masallaci ko church aciki, yana idarwa ya fita motsa jiki bai dawo ba sai 7 koda yadawo wanka kawai yayi ya sanya uniform dinsa wanda yadace dashi yafita zuwa office, office din nasa ya tsaru sosai komai najin dadi an tanadar masa sai 5 yabaro office yadawo gida, nan ya zauna yakira basma suka fara hirar soyayya sai da aka kira sallar magriba sannan sukayi sallama. Salla yayi yayi wanka ya saka dark blue din t shirt wadda aka rubuta i can i will ajiki yasa blue din jeans yadauki bindigarsa yasoke ajikin wandonsa yafito yadauki motarsa sai wani club wanda ya kasance matattarace ta yan iska. Yana zuwa yayi parking din motarsa yafito ya nufi inda ya hango abokansa zazzaune kowannensu da kwalbar giya a hannunsa wasu kuma taba sigari suke busawa gefe daya kuma yan matan bariki ne kowacce taci ado tayi kwalliya cikin kaya matsattsu. Karasawa yayi ya basu hannu suka gaggaisa sannan yakoma gefe ya zauna yayi order giya kwalba 2 masu tsada, ana kawo masa yafara tuttulawa cikinsa sai da ya shanye tas sannan ya ajiye kwalbar namfa tafara aikinta jin jikinsa yayi ya mutu murus dakyar ya tashi yashiga motarsa yarufe amma bai baro wurinba sai karfe 3 nadare yana tafe yana hada hanya abinka da mai kaki babu jami’in tsaron da ya iya tareshi dahaka ya karaso cikin barikin yabude gidansa ya shiga, yana zuwa ya zube acikin kujera sai barci.
KWARYA TABI KWARYA7⃣
Na UMMI A’ISHA
Barci yake kamar wanda ya mutu sai da asuba tayi sannan ya iya tashi yagabatar da dukkan abubuwan da ya saba gabatarwa abisa al’adarsa sannan yafita office. Kwanansa 6 agarin ibadan ya shirya tafiya zuwa garin abuja, jirgin karfe 7 na dare yabi 7:30 ya isa gida yana zuwa side dinsa ya wuce yana shiga dakinsa ya ganshi tsaftsaf an gyarashi yadda ya kamata komai an ajiyeshi a muhallinsa ga wani kamshin dadi da dakin yake yi, bathroom yashiga nanma kalkal an wankeshi tas, wanka yayi yafito yayi salla ya saka wata riga karama dark brown yasaka wando baki iya gwiwa ya nufi dakin ummansa yana shiga yasameta kishingide akasan carpet tana kallon wata drama atashar CTV kusa da ita yaje ya zauna tareda gaisheta ta amsa cikin kulawa kallonta yayi umma naga an gyaramin dakina ko har kin samo min mai gyaran ne? Murmushi tayi awwab kenan dama ai nace maka kanwarka zatazo ko? To itace tagyara maka, ras yaji gabansa yafadi, mikewa yayi umma bari naje wajen abba dan bai ma san nazo ba, fitowa yayi daga dakin umman adai dai kofar fita yahadu da ita farace doguwa yar siririya kamar baturiya amma tafi kamada yan kasar indiya kallon ta tayi gabansa yaji yayi mummunar faduwa take yaji ya tsaneta tsana marar misaltuwa, ina wuni tafada cikin zazzakar muryarta, bai amsa ba yawuceta yashige side din abbanshi yana shiga yasameshi zaune yana signing ajikin wasu takardu idonsa sanye cikin medical glass, gabansa yaje ya zauna abba barka da dare, cikin fara’a ya amsa masa gaisuwar tareda rufe takardun dake gabansa ya cire gilashin fuskarsa, yajuyo ga dan nasa awwab agaskiya nagaji da ganinka haka yanzu kayi girman da yakamata ace ka ajiye iyali, yakamata ace yanzu kanada mata, ni yanzu banida wani buri illa inga ka ajiye iyali dan hakane ma yasa na zaba maka matar aure NIHAL arazane ya kalli abbansa haba abba wacece kuma nihal? Kanwarkace awwab tagama karatun secondary sch dinta kuma mahaddaciyar alqur’ani ce, cikin faduwar gaba yace kayi hakuri abba bazan iya aurenta ba akwai yarinyar dazan aura next week zata dawo Nigeria tagama karatunta kuma tana dawowa maganar aurenmu za ayi, kuma abba auren yanzu ai ba haka ake yinsa ba kamar ni ace na auri yar secondary? Gaskiya nafi karfin haka danni wlh abba matar da zan aura mai cikakken ilmi ce wadda takeda degree, dan yanzu a harkar aure ma ana duba bright future, amma me secondary me tasani na rayuwa? Auren yanzu abba aurene nazamani kuma na aurene nakowa da muhallinsa shiyasa ma bahushe yace KWARYA TABI KWARYA!.
KWARYA TABI KWARYA8⃣
Na UMMI A’ISHA
Tunda yafara maganarsa mahaifin nasa kawai kallonsa yakeyi har yagama, amma acikin zuciyarsa fadi yake yaro yarone yaro man kaza, gyaran murya yayi shikenan awwab naji abinda kace kuma naji duk bayanin da kayi to amma ita yarinyar yar inace? Abba yan kanone amma acikin garin nan suke da zama yanzu haka tagama karatunta a London dawowa kawai zatayi, to Allah yadawo da ita lfy, amin abba, tashi yayi yafito yanata cika yana batsewa haka kawai wata yar secondary akan me? Yanzu duk ajin nan nawa ace wai kamar ni na auri yar secondary wlh bazai yiyuba ni yarinyar da zan aura me class ce sannan kuma mai degree ce amma ba illiterate ba da wannan zancen zucin yakarasa falon umma tana zaune wannan yarinyar tana zuba mata abinci, barshi haka NIHAL yaji umma tafada cikin sauri yabi yarinyar da kallo au dama wannan ce da yarinyar da abba yake so ya aura? Mts shikuwa me zaiyi da wannan yar mitsitsiyar yarinyar? Wuce nan wannan ai sai abokansa ma suyi masa dariya. Wata irin harara ya wurga mata da mamakinsa sai yaga itama ta harareshi gamida murguda masa baki,idonsa yabude cikeda mamaki ya kalleta a haife bazata fi shekaru 20 ba aduniya makewa yayi yaje kusa da umma ya zauna yana babbata rai, kallonsa tayi awwab ya akayi? Kai da waye? Umma nida abba ne wai wata yarinya ya zaba min bayan kuma ni inada yarinyar da zan aura, murmushi umman tayi kar ka damu awwab abinda kake so shi mahaifinka yake so nasan bazai taba matsa maka ka auri yarinyar da baka soba, sai alokacin yayi murmushi hakane umma amma kema ki kara fada masa yanda nake din nan ba kowacce kuchakar yarinya zan aura ba kallon wannan yarinyar yasake yi saboda dama dan ita yafada harar sa ta sakeyi akaro na biyu tsaki yaja umma ni yanzu bana burin nayi auren jahila sam sam nafi son wayayyiya yar makaranta
KWARYA TABI KWARYA9⃣
Na UMMI A’ISHA
Murmushi umman sa tayi wannan haka yake awwab Allah yabaka wacce kakeso, me zaka ci nihal ta zuba maka? Yatsina fuska yayi babu abinda zanci kuma idanma inaso to da kaina zan zuba basai an zuba min ba, kallonsa yarinyar tayi tare mikewa ta fice daga falon, shima mikewar yayi tareda bin bayanta da harara fita yayi yaje dakinsa ya dauko key din motar sa yafice daga gidan sai Rossy Guest villa yana zuwa yasamu anata chasu mata da maza sai rawa suke masu shan giya suna sha, masu rawa sunayi masu rungume rungume suma sunayi can gefe yakoma ya zauna yana kallon masu shige da fice kafin daga bisani yayi order kwalbar giya guda daya Ana kawo masa ya shanye amma bata bugar dashi ba agogon hannunsa ya kalla karfe 10:30 gida ya hara saboda washe gari yake son komawa yana zuwa yashige dakinsa yaja birki a falo yazauna akan kujera yana kallon silin, bacci ne yadauke shi mafarkin wannan yarinyar yafara ta biyo shi aguje, gudu yake iya karfinsa amma sai da ta kamashi wukar hannunta tadaga sai sheki take alamar kaifi cikin karaji tace yau zan kasheka,zan rama abinda kayi min wukar tadaga zata luma masa firgit ya farka cikeda firgita amma dayake soja ne bai wani damuba kawai dai duniyar tunani ya shiga yana son gano wacce yarinya ce wannan kuma shin meyayi mata da har take son rayuwarsa wannan shine karo na 3 dayayi mafarkinta gashi kuma yanzu tayi nasarar kamashi, daga kansa yayi ya kalli agogon dake manne acikin falon karfe 3:30 nadare mikewa yayi tare da lalubar bindigarsa yawuce cikin dakinsa.
KWARYA TABI KWARYA1⃣0⃣
Na UMMI A’ISHA
Yana shiga yacire kayan jikinsa yazauna iskar a.c tana shigarsa yana nan zaune yana nazari har 4 tayi wanka yashiga yayi yafito lokacin anata kiran salla a massalaci, salla yayi yatafi dakin mahaifinsa yayi masa sallama yafito yashiga wurin umma itama sallamar yayi mata yatafi garin ibadan lokacin dayaje karfe 7 tayi agurguje ya shiga gidansa ya dauko wasu takardu yafita zuwa office dinsa. Sai la’asar yadawo yashiga gidansa yayi wanka ya ahirya tsaf yafito gidan yakub abokinsa yatafi yana shiga ya sameshi zaune da wasu yan mata sun sakashi a tsakiya sai masha’a suke aikatawa tsaki awwab yayi yasamu kujera yazauna, kallonsa yakub yayi canal yau zamuje club ne? Yeah hakan dai zai fi kazo muje ka kyale wadannan yaran, kana ta bata lokacinka akan wadannan matan marassa aji kallonsa yakub yayi yace sorry canal bari nazo mutafi fita waje yayi yazauna cikin motarsa yana jiran fitowar yakub, bai jimaba yafito suka tafi akan hanyarsu ne yakub yadubi anwar yace canal wai me yafaru ne naga kamar yanzu baka fiya kula yan mataba? Wani dan karamin tsaki awwab yayi wlh yakub ni kaina ban san menene dalili ba, amma kuma ina ji ajikina cewa akwai gagarumin abunda yake tunkaro rayuwata akwai wani abu wanda zai faru dani nan bada jimawa ba but ban san yaushe ne ba, kallonsa yakub yayi cike da mamaki taya kasan haka? Wlh yakub akwai wasu mafarkai dana jima inayi kuma har yau ban daina ba sannan akwanakin baya akwai wani abu da yataba faruwa wanda bai yiyuwa na iya fada maka domin sirrine wanda ya shafi rayuwata,yanzu gaba daya jina nakeyi a wani irin yanayi, sanin kanka ne ina son mata kuma ina nemansu aduk inda nasan zan samesu to yanzun ma dai ba dainawa nayi ba amma inajin wani irin abune a tare dani, ahalin yanzu nafi son nasha giya akan nakula mata sai dai zan kulasu suma nan da wani dan lokaci dai dai lokacin suka karasa club din, nidai ummi A’isha nakosa naji wannan labarin na awwab masu karatu nasan kuma kun kosa ko? Ko baku kosa ba.
[1/12, 8:28 AM] Ummi A’isha: [1/12, 8:21 AM] Ummi A’isha: KWARYA TABI KWARYA1⃣1⃣
Na UMMI A’ISHA
Suna isa awwab yayi packing adai dai inda aka tanada domin packing din motoci, kashe motar yayi suka firfito suka shiga cikin club din, nanfa suka fara gwangwajewa sai da dare yayi sosai sannan suka dawo gida. Ranar juma’a da misalin karfe 4 na yamma awwab yabar ibadan ya nufi abuja karfe 4:30 ya isa gida falon ummansa ya fara zuwa suka gaisa sannan yafito yashiga dakinsa, wanka yayi yafito yashirya cikin wani dafaffen boyel baki yasa hula zannabukar itama baka agogon azurfa na Gucci ya daura a hannunsa yafesa turaren ice hot yasa bakin takalmi harp cover yafito hakika yayi kyau na daukar hankali gashi yanada kwarjini sosai, side din umma yakoma lokacin da yashiga ita kuma tana kokarin fita ganinsa da tayi yasa taja da baya tareda komawa kusa da umma ta zauna, shigowa ciki yayi take falon ya gauraye da daddadan kamshin turarensa, umma ya kalla yace umma zanje gidansu basma,au basman ta dawo ne? Eh umma tadawo tun shekaran jiya saboda itama nazo garin yau, to kagaisheta, zataji umma yafada yana dan murmushi, ta gefen idonta ta kalleshi yayi kyau mutuka taba baki tayi acikin zuciyarta tace danma dai adon iya najiki ne daki kaca kaca yake, shiko awwab ko kallonta bai yiba yafice daga falon yaje yadauki wata motarshi black yafita yanufi zone 2 unguwar su basma. Gidansu basma gidane babba kuma iyayenta yan boko ne nakarshe asalima su rayuwar turai sukeyi agidansu, yana zuwa aka bude masa yashiga yaje ya ajiye motarsa a inda aka tanada, yafito ya shiga gidan wanda yayi mutukar tsaruwa a falon manyan baki ya zauna yana jiran isowarta, sai da yashafe samada minti 20 sannan tafito taci uwar kwalliya cikin wata bakar doguwar riga ga uban gashin kanti har gadon bayanta ayangance take takunta bakace sosai marar tsayi kuma bata da hanci, oh ikon Allah masu karatu nazata basma zatafi haka haduwa amma sai naga abin ba haka yake ba, tana zuwa inda yake ta zauna ajikinsa tana fadin welcome my man! Kallon so awwab ya jefa mata sannan yace thank you my dear! murmushi basma tayi sannan tace yakake? Lfy my dear ya sch dafatan an gama lfy? Lfy tafada kamar wadda bakinta yayi mata nauyi.
KWARYA TABI KWARYA1⃣2⃣
Na UMMI A’ISHA
Kallonta awwab yayi gashi yanzu kin gama sch saura me? Murmushi tayi saura aurenmu kuma, yawwa my dear haka nake son ji so yanzu zan sanar da dad dina cewar yazo suyi magana da dad dinku ko? Eh hakan yayi, ammafa inada wani uzuri,name? Ya tambayeta agaskiya awwab ina son zanyi aiki kuma sannan duk lokacin dana samu admission zan koma sch nayi masters dina, to ai duk wannan ba problem bane ni awajena, babu matsala zakiyi aikinki kuma zakiyi karatu ai duk mai saukine ni dama babban burina shine na auri mace mai class kamar ke domin ke ta dabance, wani malalacin murmushi tayi thanks my canal, bari naje nadawo tafada tareda mikewa ta shige gidan tana cike da farin ciki domin samun miji kamar awwab tasan sai mace mai sa’ar gaske, kuma yana da fuskar mutanen kirki dan idan basani kayiba baka taba cewa yana shan giya balle har kayi tunanin zai nemi matan banza, shigowa tayi hannunta rikeda tiren silva ta zubo masa kayan motsa baki kamar ba acikinsa shi daya zai zuba ba, agabansa tazo ta dire farantin tana murmushin jin dadi, tana farin cikin zata auri awwab duk da cewa ita tasan yana shan giya da neman mata amma hakan bai sa taji tsanarsa a ranta ba asalima itace taganshi tana so,kusa dashi tazauna my man amma idan munyi aure a anan zaka barni na zauna ko inyaso Kai sai ka rinka zuwa? Yes haka nake tunani my dear saboda akwai gidan da dad dina yabani kyauta a nan kusa da gidanmu so i think anan zamu zauna saboda dad baya so nayi nisa dashi, kai amma fa naji dadi sosai, mikewa yayi bari nawuce gida sai munyi waya ko, tashi tayi tabi bayansa har zuwa compound din gidan.
KWARYA TABI KWARYA1⃣3⃣
Na UMMI A’ISHA
Tsayawa tayi ta zuba masa idanu komai na shi burgeta yakeyi domin ya hadu iya haduwa ita kanta tasan awwab ba ajinta bane yafi karfin level dinta kawai dai Allah ne yadorata akansa har ya amince da soyayyarta yake sonta, kofar motar ya bude yashiga yayi mata sallama tafara daga masa hannu har yafice daga cikin gidan sai da taga fitarsa sannan tayi ajiyar zuciya tareda furta awwab kenan nida kai aurene zamuyi irin na KWARYA TABI KWARYA tana gama fadin haka ta shige gida. Shi kuwa awwab gida yakoma yana zuwa yashiga wajen umma ya tarar da ita zaune tana cin apple gefe daya kuma nihal ce take mammatsa mata kafafuwanta wanda ta dorasu asaman tumtum, kusa da umma yaje ya zauna tareda cire hular kansa juice din dake gaban umman ya dauka ya balle murfin yafara sha amma sai yaji dandanon baiyi masa dadi ba, dan shi yanzu giya ce take yimasa dadi abaki amma komai dadin juice idan yasha sai yaji babu dadi, ajiyewa yayi umma ta kalleshi awwab kasha juice din mana, no umma ya isheni inada juice adakina idan naje zansha, kallonsa nihal tayi ta taba baki, kamar hadin baki shima ita ya kalla gabansa yaji ya fadi, to shi wai meyake faruwa ne? Duk tun lokacin dayafara ganin yarinyar nan yaji gabansa yana faduwa.
KWARYA TABI KWARYA1⃣4⃣
Na UMMI A’ISHA
Kallonta yasakeyi sosai kamar dai yasan ta awani wuri amma ya kasa tuna ko a inane, hakama muryarta kamar yatabaji sai dai ya manta a inda yaji hararta yayi aransa yana fadin yarinya karama sai iyayin tsiya da kwainane, dagowa dara daran idanuwanta tayi ta wurga masa harara, hararta shima yayi yana daddanna wayarsa chtn yake da basma ta palm chat, kallonta yasakeyi baki yaga ta murguda shi abin nata ma dariya kuma yake neman bashi yarinya sai kace tababbiya baiyi mata komai ba ta ringa harararsa? Remote din tv ya dauka ya kamo MBC Action yafara kallon wrestling ita kuma nihal tanata aikin daddannawa umma kafafunta yana nan zaune yana kallo har 9 tayi umma ya kalla umma kira talatu ta zubo min tuwo dan kadan,a’a ga nihal ta zuba maka mana, a’a umma kira talatu dan Allah kira umma ta kwallawa talatun sai gata dasaurinta tazo ta durkusa, talatu zubawa awwab tuwo sai dai kin san cin abincinsa dan kadan zaki zuba masa, to ranki yadade da saurinta ta tashi zubo masa ta kawo masa yakarba da cokali yake cin tuwon yanaci yana kallo, jifa jifa kuma yana duba sakonnin daketa shigowa cikin wayarsa, dahaka har ya gama cin abincin ya tashi, dakinsa yashiga yacire kayan jikinsa domin shi bai cika mu’amula da manyan kayaba sai dai idan ranar Friday ne abbansa yayi fadan har yagaji bashida kaya sai jeans da t.shirt ko kuma boxer, wanka yashiga yayi yafito yayi salla yaje yabude fridge dinsa zai dauko giya amma wayam babu ita babu alamunta tsaki yaja yasan wannan figigiyar yarinyar ce ta kwashe masa to amma me zatayi da ita? Wata zuciyar tace babu abinda zatayi da ita kawai tsabar mugunta ne yasata kwashe maka, zama yayi afalon zuciyarsa cikeda kunci, tsaki yayi taja gashi yau baya son fita club domin so yake yayi bacci ya huta, dakinsa yashiga ya kwanta dakyar bacci ya kwasheshi. Washe gari basma tayi masa waya ta sanar dashi cewa zatazo ta gaisheda ummansa, tashi yayi yashiga cikin gidan dakin umma lokacin 11 dai dai yasameta suna yin breakfast itada abbansa, tsugunnawa yayi yagaishesu sannan yahau kan dining din shima yahada tea yafara sha, kallon abbansa umma tayi tace Alhaji dama ina son fada maka ka shirya kaje gidansu yarinyar da awwab yake so ka tambayo masa aurenta saboda iyayenta sun bashi dama.
KWARYA TABI KWARYA1⃣5⃣
Na UMMI A’ISHA
Dan haka yanzu abin yi yarage garemu sai mu nemo masa aurenta, kallonsa abba yayi wai hakane my son? Yes abba hakane murmushi abbansa yayi ato alhamdulillah insha Allahu zanje gidansu yarinyar in Allah ya yarda, mikewa abban yayi to ni zan tafi office hajiya Sadiya babu wani abu ko? Mikewa tayi tabishi tana cewa babu komai abba, kallo awwab yabisu dashi har suka fice, dai dai lokacin nihal tashigo falon tana sanye da doguwar riga ta shadda, ke ina abinda kika dauka min acikin fridge?? Wani mugun kallo ta watsa masa mai nuna alamun baka isaba, ke nifa ba sa’anki bane kin gane? Bana son raini idan kin saba rashin kunya kisan a inda zakiyita amma ba anan ba, dankwalin kanta ta turo gaban goshinta ma’ana gayawa keya dan kwali yabaka amsa, nan da nan ya sake kuluwa dan dai kawai shi baya dukan matane amma da babu abinda zai hanashi babballata tashi yayi yabar falon yakoma dakinsa, sai waya ya yiwa umma ya sanar mata da zuwan basma anjima. Yamma tanayi basma tazo gidansu awwab cikin shiga tasu ta yayan manya, an bazo gashin kanti awwab ne yafito yayi mata jagora har cikin falon suna shiga umma tana zaune akan sallaya da alama salla takeyi ita kuma nihal tana lallatsa wayar umma sallama basma tayi tanemi wuri ta zauna kamar ba zata amsa ba ta amsa sallamar tareda dagowa kanta ta kallesu, tsaki taja acikin zuciyarta wai dama wannan ce basman? Lallai ashe jinta yafi ganinta tab su awwab angamu da aiki akan wannan yake wani rawar kafa? Harara ta watsa musu daga shi har basman, itama basman sai faman harare harare take tayi kamar wacce aka zaga, maganar umma ce ta katsesu sannu da zuwa basma cikeda yanga tace yawwa sannu umma ina wuni? Lfy lau umma ta amsa cikin fara’a ta dubi nihal wacce taketa faman yatsina fuska da harare harare tace nihal kawo mata ruwa da lemo, to umma tafada batare da ta tashi ba sai da tagama jan ajinta sannan ta tashi hakan ba karamin batawa basma da awwab rai yayi ba, ruwa roba daya ta dauko da lemo gwangwani daya sai tsurar cup guda daya ko a faranti bata doro ba tazo gabansu ta ajiye akan center table takoma mazauninta wato kujerar datake kallonsu ta zauna ta dauki wayar umma taci gaba da lallatsawa awwab ya kulu ya kulu, ita kuwa basma haushin nihal ne ya cika ranta kamar taje ta shaketa takeji, kuma ita a iya saninta awwab bashida kanwa su 2 ne kadai awurin iyayensu daga shi sai yayarsa Anty jamila to a ina suka samo wannan yarinyar mai kama da aljana? Wani kishi taji ya turnuketa marar misaltuwa kara daga idonta tayi takalli awwab wanda shi kuma nihal yake kallo cikeda tsana da jin haushinta itama nihal din su duka biyun haushin su takeji in banda harara babu abinda datake aika musu, to meye dalili? Nidai ummi A’isha banida amsa.
[1/12, 8:36 AM] Ummi A’isha: [1/12, 8:29 AM] Ummi A’isha: KWARYA TABI KWARYA1⃣6⃣
Na UMMI A’ISHA
Daure fuska awwab yayi yayin da itama basma ta daure tata fuskar, umma ce tayi magana tace basma kisha ruwa, to umma nagode tafada tana mai cigaba da hararar nihal ita kuwa nihal basu ma isheta kallo ba daga basman har awwab din gani take bata da lokacinsu amma haka kawai taji basman nan bata burgeta ba kamar yadda itama basman taji sam nihal bata yi mata ba shirune ya dan gitta afalon kafin umma tace basma ashe kuma an kammala karatu ko? Washe baki tayi wlh kuwa umma nagama yanzu sai maganar aiki kuma, kallonta nihal tayi tareda taba baki daidai lokacin awwab ya kalleta ya harareta bata kyaleshi ba itama ta watsa masa harara, ganin abin yayi yawa yasa basma mikewa umma ni zan tafi tashi umma tayi to jirani ina zuwa dakinta tashiga ita kuma nihal ta dubesu ta kara tabe baki azuciyarta tana cewa wlh sam baku wani dace da juna ba, umma ce tafito hannunta rikeda leda wadda tasako turarrurruka da man shafawa aciki tabawa basma, gashi basma nagode kigaida mutanen gida Allah yayi albarka, amin nadawo tafada tana murmushi wucewa tayi awwab yana binta abaya sai da sukaje daf da kofa nihal tace agaida gida bakuwa, ko waiwayowa basuyi ba bare su tanka mata ita dinma dama tafada ne domin ta tsokane su to kuma sai akayi sa’a basu kulata ba. Suna fitowa harabar gidan basma ta dubi awwab my man wacce yarinya ce waccan? Meye alakarku da ita? Kai ya girgiza wlh yadda kika ganta haka nima naganta ban san wacece ba, sai dai ina son nasan meye alakarmu da ita amma jinina bai hadu da ita ba saboda bata da kunya fitsararriya ce ta karshe, baki basma ta taba ai naga alamar marar kunya ce sai wani kallon banza take yimana sai kace wasu sa’anninta, wlh dan kawai nice nazo ne badan haka ba da sai na tsinka mata mari murmushi awwab yayi babu ruwanki da ita ki barni da ita ni zan koya mata hankali,kallonsa basma tayi ina fata dai baka sakar mata fuska? Haba ina ruwana da ita nifa sau 2 kawai nataba yimata magana tun zuwanta gidan nan tsakanina da ita harara ce.
KWARYA TABI KWARYA1⃣7⃣
Na UMMI A’ISHA
Yawwa my man haka nakeso saboda dama bana so kabata fuska ko kadan domin idan taga fuska zata iya cewa tana sonka, no no kima daina wannan tunanin mezanyi da wannan karamar yarinyar, yarinyar da har yanzu bata gama cika mace ba murmushin farin ciki basma tayi shiyasa ko yaushe sonka karawa yake acikin zuciyata domin kai acikin maza na dabanne you are special one, kanada class da iya taku ba irin sauran maza bane murmushi yayi to yanzu sai yaushe ni kinga gobe nake son komawa Ibadan, ok to shikenan Allah ya kaika lfy zamuyi waya later, motarta ta bude tashiga ta tadata tadaga masa hannu ta fita daga gidan, juyawa yayi yakoma side din umma, zaune ya hango nihal tana yankewa umma farcenta tsaki yaja yaje kan kujera ya zauna yakalli umma,umma wai me aka dafa agidan nan ne? Awwab dashishi akayi, to ai umma ni bana son wannan abin dan Allah sa talatu ta dafa min indomie duk da ba lallai ne ma in iya ciba ni kin sanni da tsantsami, to bari nihal ta dafa maka shiru yayi yadauki remote ya kunna tv, nihal bar min yankan farcen kije kitchen dina ki dafawa awwab indomie inji umma, tashi tayi har zata fita umma tace nihal kar kisa yaji dayawa saboda awwab bai son yaji, to umma tafita ta shiga kitchen, acikin mintunan da bazasu fi 5 ba ta shigo da plate a hannunta da spoon tazo ta ajiye agabansa ko kallonta bai yiba itama bata kalleshi ba, kusa da umma takoma ta zauna lokacin umman har tagama yanke farcen, kamar kada yaci amma ganin yana jin yunwa yasa yadauki cokalin yadebi indomien yafara ci jin harshensa yayi kamar zai cire saboda yadda tasha attaruhu, ajiye spoon din yayi yatashi yabude fridge ya dauko juice din gwangwani ya dan kurba ya ajiye dakyar ya iya magana umma bari naje naci abinci a restaurant daga can zan wuce nasha lemo harararsa nihal tayi aranta tace zakaje kasha giya dai ba lemo ba, to awwab adawo lfy inji umma.
KWARYA TABI KWARYA1⃣8⃣
Na UMMI A’ISHA
Sai da ya harari nihal sannan yafita cikeda da jin haushin nihal yanufi dakinsa yayi wanka ya sake kaya, dark purple din riga mai dogon hannu da bakin wando jeans yafesa turarensa na ice hot tadauki gun dinsa yanufi motarsa BMW blue wadda takasance mai dark black din glass, yana shiga yadaga kujerarsa ya ajiye bindigar sannan yatasheta ya fita,nihal kuwa lokacin da awwab yafita ta kalli umma tace umma bafa Lemo zaije yasha ba, wlh.. Umma ce ta katseta hanyar cewa bana son surutu nihal kar nakarajin wannan maganar a bakinki, shiru nihal tayi tareda tashi ta wuce dakin umma. Yana fita ya saki kida a motarsa wakar d banj ya kunna cikin before in love, a hankali kidan yake tashi har ya isa wani katafaren wurin cin abinci hot pot restaurant and catering services, a kan titin mai tama,a waje yayi packing din motarsa yafito yashiga,shinkafa da miya yayi order sai dan salad aka kawo masa yaci ya biya, yana shirin fitane yaci karo da zaituna, zaituna yarinyarsa tunda dadewa, kallonta yayi cikin mamaki zaituna kece? Murmushin jan hankali tayi nice ranka ya dade, yakake? Normal yagida, gida lfy, yanzu ina zakije? Zanje gidane ko kana so ne narakaka?. Yes idan kikayi haka zanji dadi, ok to muje,jerawa sukayi har inda ya ajiye motarsa suka shiga bai zame da su ako ina ba sai Dan Musa guest lodge,suna zuwa yakarbi mukullin daki suka shiga dubansa zaituna tayi canal dama bakayi aure ba? Ke yakamata nayiwa wannan tambayar dan tuntuni nayi zaton kinyi aure, gefen fuskarsa ta shafa no ina tareda kai tayaya zan iya auren wani, ai duk maza ganinsu nake kamar mata yan uwana kai kadaine kawai namiji a wurina, murmushi yayi tareda riko kugunta kar fa ki yaudareni zaituna idonta ta fara sannan tace babu yaudara tsakanina dakai ka yarda da abinda na fada, janta yayi suka fada gado. Sai wurin karfe 5 sannan suka dawo hayyacinsu alokacin awwab bacci kawai yake ita kuma zaituna tazuba masa ido cikeda so inama ace awwab mijin tane haka kawai take rayawa acikin zuciyarta motsi yayi yafarka daga dan baccin da yayi yatashi yashiga toilet yayi wanka yafito tareda fara tashin zaituna hannunsa tariko tareda kara jawoshi jikinta nanfa suka koma ruwa
KWARYA TABI KWARYA1⃣9⃣
Na UMMI A’ISHA
Sai da suka dada shafe awanni suna shedancinsu sannan suka shirya suka fito, abakin wani titi yayi dropping din zaituna tare da rubuta mata cheque na wasu makudan kudi masu yawan gaske. Wani gidan saida giya ya zarce yasiyi wata yar karamar robar giya yafito yashiga motarsa yadan kurbi giyar kadan sannan ya rufe ya boye sauran akasan kujera, gidansu ya wuce lokacin karfe 8 nadare yana shiga ya wuce wurin abbansa yagaisheshi anan ne abban yake yi masa albishir da cewa yaje gidansu basma sun ganada mahaifinta, dadi awwab yaji domin shidai yana son basma saboda iya jan ajinta, mikewa yayi yafito zuwa sashen umma nan ya taradda ita zaune da fitsararriyar yarinyar nan nihal yana shiga suka hada ido da nihal take ya dalla mata harara itama ta rama kujerar da umma take kai yaje ya zauna kamar wanda zai shige cikinta, awwab kadawo? Eh umma yanzu daga wurin abba nake yace min yaje gidansu basma dazu harma sun gama magana da mahaifinta murmushi umma tayi eh haka yagaya min ai yanzun nan yafita daga cikin falon nan, komai ya daidaita saura yanke ranar aure kawai kansa ya kwantar ajikin kujera, oh nima nakusa zama mai gida kenan, dariya umma tayi dadina dakai rashin kunya, yanzu agabana kake fadar zaka zama maigida? Dariya awwab yayi sorry ummana ai gani nayi kece abokiyar shawarata kuma abokiyar zancena shiyasa kikaji na fadi haka, to ai shikenan awwab Allah yakaimu lokacin, amin umma wayar hannun nihal ce tayi kara taduba tareda dagawa cikeda yanga tafara magana hello hamid, ok bari zan kiraka anjima, awwab ne yaji gabansa yafadi kallonta yasakeyi tana sanye da leshi fari mai ratsin baki ajiki, ta turo dan kwalinta gaban goshi hakan yabashi damar hango tulin gashin kanta data tufke,harara ya jefata mata sannan acikin zuciyarsa yace wannan yarinyar yar duniyace da alama, ita kuwa nihal sam bata ma san yanayi ba domin hankalinta yana ga wayar umma datake hannunta sai lallatsawa takeyi, ko hararta da yayi bata gani ba domin da tagani shikansa yasan sai ta rama.
KWARYA TABI KWARYA2⃣0⃣
Na UMMI A’ISHA
Kallonta yaci gaba dayi ita kuma tanata daddana wayar dake hannunta da alama sakon txt massage take turawa, she’s very cute and beautiful yafada acikin zuciyarsa wata zuciyar tace yes is true ammafa muguwa ce da alama saboda dazu taji umma tace bakason yaji shine tacika attaruhu a girkin dan kar kaci dai dai lokacin ta dago dakanta ta kalleshi harara ta cilla masa amma shi sai yayi murmushi karo na farko dataji ya burgeta domin tun farkon ranar data fara ganinsa bai taba yimata murmushi ba sai dai aikin harara amma yau gashi abin mamaki itace ta harareshi bai ramaba a maimakon ya rama ma sai ya aika mata da sakon murmushi mai tausasa zuciya, hararsa takara yi aranta tace good naji dadi tunda yanzu ka gane nima ba kanwar lasa bace da alama kagane cewa u are d one that loose d game shiyasa kafara sakkowa but naso ace munci gaba da buga wasan so that sai agane waye winner, maganarsa mai dadi tajiyo yana yiwa umma magana, umma wai ni kwana 2 ina baba mai gadine? Tunda nazo ban ganshi ba, eh wlh awwab yazo yayi min sallama cewa zaije gida dansa bashida lafiya, ayya umma inane kauyen nasu? Wlh awwab sai dai ka tambayi idi mai gadi ni ban san garinsu ba, ok to idan idin yasani sai kawai na aikeshi ma ya kai masa sako, murmushi umma tayi Allah yasaka da alkhairi Allah yayi maka albarka Allah ya biya bukata, amin ummana kinyi min babbar addu’a domin inada wani babban buri arayuwata kuma inada muhimmiyar bukata awurin ubangijina, kallonsa nihal tayi ta taba baki ta dauke kanta,murmushi yayi acikin zuciyarsa yace yarinya zanyi maganinki ni banida time din da zan tsaya ina musayar harara dake,umma ya kalla umma zan sha tea da sauri ta kalli nihal, nihal tashi ki hadowa awwab tea, mikewa tayi tana cikeda takaici kinga kisa min lemon tsami aciki kuma iya sugar da Lipton kawai zakisa bata kulashi ba tafita tashiga kitchen, lallai gayen nan dan rainin hankaline nifa ba yar aikin gidansu bace da zai rinka sani bauta amma zanyi maganinsa dariyar mugunta tayi dai dai lokacin data gama hada tea din tadauka acikin glass cup takai masa yana nan zaune a inda tabarshi amma umma bata wurin ta tashi, akan stool din dake gabansa ta dire tea din takoma ta zauna tazubawa tv idanu tana kallon drama sahrul asmar a tashar MBC Bollywood sai da awwab yagama jan ajinsa sannan ya dauki tea din yakai bakinsa kurba daya yayi yadawo dashi saboda gafin gishiri da yaji kamar zaiyi magana dariya nihal tafara kamar me sannan tace yadai? Murmushi yayi yafara kwalawa umma kira umma! Umma!.
[1/12, 8:47 AM] Ummi A’isha: [1/12, 8:40 AM] Ummi A’isha: KWARYA TABI KWARYA
2⃣6⃣

Leave a Comment