ππππππππ
*NIDA ZUCIYATA*
ππππππππ
*πA heart touching story*π
*IWA*
_(Onward together_)
*Written by*
*Precious girl*β
_In the name of Allah the beneficent the most merciful_
*Page 1n2*
Rabab, “je ki dauko kayan haihuwa suna can sama d’akinta, kiyi sauri don Allah Rabab.
Yanda yake maga sai naji yabani tausayi, na juya na tafi in waigo, sai naga Aunty ta sa hannun ta d’aya tana goge mashi ko gumi ne oho, da rawar jiki ya kama hannunta yana sunbata.
Cikin wata kalar murya naji yana cewa.
“Sannu zuciyata sannu. ”
“ka daina kuka kaga kasa har jikina yayi sanyi. ”
Aunty ke cewa haka.
Ni kuma na tabe baki nayi gaba. A zuciyata nace, naga Romeo and Juliet, wanda har makarantu in za’ayi misalin ‘yan soyayya a darasin English Lectures su ake fada. Na haye da gudu na dauko rio da flask din shayi babba cike da ruwa.
A zuciyata nace. “kilan shi ya cika shi, ina saukowa na iske har sunkai bakin k’ofa yana rike da ita, nabi bayansu bakina a zumbure dan haushi. a zuciyata nace kabar mace tayi tafiya da K’afart ka wani k’ank’ame ta.
Ai sai ga yaya Altab, na doka mani tsawa wai inyi sauri in bude mashi mota, da saurina na bude mota , ina kallo ya kamata suka shiga, nikuma na mik’a mashi flask d’in.
Na zagaya na ajiye rio d’in a gaban mota sannan na zauna mazaunin driver,
Yaya mai fad’an gudu sai gashi yau shike cewa inyi sauri.
Asibitin Dr Hakeem, muka nufa _(Hakeem Specialist Hospital_) dama can Aunty ke awo, nan da nan aka kirashi a waya. Ya iso ina kallon Aunty aka turata d’akin haihuwa, nida yaya a ka bar mu a tsaye.
Na samu damar buga waya, na kira Umma na gaya mata muna abibitin Dr Hakeem, tace to intayin addu’a zatayi waya da gwaggo Hauwa ko zata tsaya wajenta, nace to.
Tun k’arfe 9:30 na safe zuwa 10:00 muke asibitin nan, amma har 12:00 tayi amma shiru,
Na matsa kusa da yaya da yake ta share gumi a fuskarsa, nace mashi zanje in dauko Ilham, daga makaranta amma G.R.A. zan kaita yace “to.
*** *** *** *** *** *** *** *** *** ***
Ina shigowa asibiti na samu Yaya da jariri, a rungume cikin farin shawul, da kayan sanyi a jikinsa,
Na isa da sauri, tareda tambayar mamaki.
“Yaya ta haihu?”
Da sauri yak’araso wajena yana d’an murmushi.
“ta haifi d’aya, saura d’aya ”
“Namiji ne ko mace? ”
“Namiji ne kin ganshi”
Ya miko mani shi yace
“kai wa gwaggo Hauwa shi, kizo mu jira ikon Allah. ”
Na amsa da to, na wuce na kaiwa gwaggo Hauwa shi, na koma inda Yaya yake tsaye. Nace
“Yaya ka zauna dan Allah ”
Ya zaro idanuwan shi gaba d’aya.
“In Zauna? ”
Na tabbata Ikram ba’a zaune take ba, ina zan iya zama? Ai bazan iya tab’a zama ba ita tana a tsaye. In zata kwana, nima zan kwana a haka kedai kije ki zauna ke zama ya gano ni zama bai ganni ba
“Rabab, kin san kuwa yadda yayarki ke cikin zuciyata?”
Na girgiza kaina na wuce wajen gwaggo Hauwa na zauna saboda naga alamar in na tsaya kusa dashi to sai fad’a masa bak’ar magana. tunda ni bana son hirar soyayya
Can baifi zaman minti goma ba aka ce ina Altab yake? ”
Yace “gashi ”
Wata sister ta miko mashi wani jaririn.
Na taso da sauri nace
“Yaya mace ko namiji? ”
Yace “0ho. Sister Mace ce ko namiji? ”
Tace “mace ce wannan. ”
Murna kuwa kamar ya Saki jaririn ya damko bandir d’in kudi ‘yan dubu d’aya ya bata
Duk wanda zai wuce sai ya zari kud’i ya bashi saboda murna, can sai ga Aunty an turota za a kaita d’akin hutawa, yayi sauri ya isa gadon da take ya dafa kanta tare da cemata.
“Sannu zuciyata ”
Nikuwa nadan dafa gadon da take, ta zuro hannu ta kama hannuna.
Hawaye zuka zubo a kuma tunta na rike hannun sosai tare da ce mata.
“Sannu Aunty ”
Ta amsa da. “yawwa”
Muka isa d’akin hutawa, ika kwantar da ita daga gani ba wasa kasan Aunty tasha wahala.
Ni haushi yasa nafita daga d’akin, yanda Yaya ya kankame gadon tamkar ya had’iyeta sai mutane ke nuna shi.nafito waje naci gaba da buga waya, duk wanda nasan yanada hakki a gaya mashi na gaya mashi. Indai da lambar shi a wayata.
Ina nan tsaye ya fito da sauri
“ke jeki wajenta, bani key din mota ”
Yana ta sauri kamar zai ruga bakin shi kuwa yakasa rufuwa. Na mik’a mashi da sauri, ya kar’ba
Nikuma na koma ciki na zauna gefen gado kusa da kafafuwan ta na dafa k’afar ta.
“Sannu Aunty ”
Tace “yawwa kema sannunki na gode. Allah ya yi maki albarka
Nace “Amiin Aunty ”
Duk na fada mata masu gaishe ta, nace “Abba ma gashi nan zuwa ”
“Tayi murmushi, da gani na k’arfin haline. Tace
“ina Abban Yasmeen ya tafi? ”
“wallahi ban sani ba yace dai nabashi key din mota na bashi k’ilan kayan tea, d’in ze d’auko mun manta dasu mai makon yace naje na dauko ”
Tayi murmushi “yanzu haka in don Abban Yasmeen ne ya Manta dake ”
Nima nayi murmushin “zai iya Mantawa.kina ganin yadda yake miki nifa kunya ta kore ni da haushi sai mutane keta kallon ku
“Burge su muke ”
“Kaji Aunty ”
Rabab ki sassauta wa zuciyar ki tsanar aure. ”
Na kawar da fuskata “Aunty, kiyi hakuri, wallahi na daina tsanar Yaya tunda kika gaya mini jiya, ni dai ya daina kama ki cikin mutane kada ace maku yan iska ”
“Rabab kenan………..
[8:50PM, 4/8/2018] βͺ+234 703 488 7604β¬: ππππππππ
*NIDA ZUCIYATA*
ππππππππ
*πA heart touching story*π
*IWA*
_(Onward together_)
*Written by*
*Precious girl*β
_In the name of Allah the beneficent the most merciful_
*page 3n4*
“Rabab kenan, to zan fad’a mashi. ”
K’iri k’iri Yaya yak’i tafiya gida, har k’arfe 12:00 na dare, daga gani daga ita har shi suna buk’atar futawa, ni kaina ina son na huta.
Da k’yar ya yadda can wajen 1:00 na dare, har ya juya zai tafi. ya dawo ya sunbaci goshin ta, sai ta rik’o hannun shi. Yayi saurin juyowa.
“Twin’s din fah? ”
Yadawo ya sunbaci ko wannen su, sannan ya k’ara sunkuya wa ya sunbaceta.
“Dan Allah ka zauna ka huta. gobe zamu tafi gida. ”
“ki daina had’ani da Allah, kin san dai bani iyawa.”
“Altab.”
Ya juyo da sauri cikin wani yanayi na tashin hankali, ko nidai naji gabana ya fad’i saboda ban tab’a jin ta fad’i sunan shi a gaban shi haka ba.
“Lafiya? ” ya tambaya.
“Lafiya k’alau don Allah ka yafe mani koda na sab’a maka a bisa kuskure ko sane ”
“A kullun kalamin amsarki d’aya, na yafe maki kuma ke bakya laifi, ni ko kurkuren ma da wuya ayishi,
sai da safe ko? ”
Ta amsa “Allah ya kaimu ”
Ya lakaci hancin ta.
“Har kin tayar mani da hankali yaushe rabon da ki kira sunana, nima saina rama Ikram ”
Sukayi dariya, nima har suka bani dariya basu tab’a abunda nayi dariya ba sai wannan.
Har ya juya ina dariya. yadaga hannu kamar ze dakeni
“shine kike mana dariya ko ”
“Yafada yana dariya.
“Ga amana nan
“yaya ban Karb’a ba”
“keeee ‘yar k’anwale ”
“Allah yaya zan dai kula dasu kamin kazo ”
“yayi dariya yayi gaba”
Ni kuma na janyo kujera na zauna gaban ta, wajen k’afafunta. Na dinga matsa mata su har tayi bacci. Ita kuwa gwaggo Hauwa dama tuni tayi bacci itada twins d’in a dayan gadon.
A inda nake zaune na kifa kaina, nima sai bacci. Can cikin bacci naji tana salati. Nayi sauri na tashi na rik’ta
“Aunty lafiya? ”
“lafiya kalau k’anwata farkawa kawai nayi ”
“Ko zaki sha shayi Aunty? ”
“Eh to bani insha ”
Na had’a mata tare da mik’a mata tasha abinka da asibiti har dare muka dinga hirar mu.
Na tashi na dauko yaran, ta karbe su ta rungume su tareda fito da na fulanin ta gaba daya kowa ya kama daya yana sha
“Aunty sun kawo ko? ”
Tace “nima yanzun naji sunkawo shine na basu su sha”
Suka sha daidai yanda suka samu, sannan na karbe su na mayar dasu gurin gwaggo Hauwa,
Nadawo na zauna tace inje in kwanta. Nace mata nan ma ya ishe ni Aunty.
Tace “Rabab, nayi addu’a a lokacin da nike nak’uda, Allah yabaki miji na gari, na kuma roki Allah ya cire maki tsanar aure a zuciyar ki.
Da tsanar mijina bana son inga kuna zaune haka tunani kala kala nikeyi don Allah ki sassauta bashida amfani Rabab, gashi yanzu ‘yan biyu na haifa ina buk’atar taimakom ki. Ki ki zauna mani na shekara daya har sud’an yi wayau ”
“Aunty makaranta fa? ”
“Basai ki dinga zuwa daga nan ba ”
“Aunty kwanta ki huta dan Allah ”
“Zan zauna idan har Abban mu ya amince ”
Naci gaba da matsa mata k’afafu har k’arfe 4:00 na asuba nima na kife kaina sai bacci.
Jin anata salati kanmu, yasa na tashi a firgice, Yaya da jama’a akan mu na tashi na ja da baya saboda Dr yazo. Atake haushin sa ya saukar mani daga zuwan shi zai tara mana jama’a
Kamar ance in kalli gadon, sai naga Aunty kwance cikin wani mugun jini cike da gadon ta.
Na Saki wata mahaukaciyar kara. Na gigice. Wata mata ta rik’eni gam.
Ihu nake, cewa nake, sake ni in ganta na kubce na tafi da sauri. Ban isa gadon ba.
“Sai naji dr yace ”
“Allah yayi mata cikawa”
Kamar inyi tunanin mema naji ana cewa? ”
Sai kawai naji yaya ya saka k’ara ya sulale a k’asa mutane suka yo kansa amma ko motsi bayayi
Ni kuma nayi sauri nje na kama gadon ta ina cewa
“Dan Allah Aunty ki tashi
Kar kibar Yaya ya mutu
“Dan Allah ki tashi
Nan aka samu mutane suka kamani inata kiran sunan Aunty. gwaggo goye da d’a d’aya d’aya a kafadar ta tana ta kuka
A nan dr ya karbi wayana ya kira.
Ban fahimce ma me ake cewa ba sai dai naji yana cewa.
Mahaifinta, to yawwa daga asibitin da ta haihu ne Mum kwantar da ita lafiya amma yanzu Allah yayi mata rasuwa.”
Iyakar nan naji nasa k’arar ihu, na na fizge na ruga aguje, do kyar aka kamomi ina ina jin daga nan ban sake sanin Inda nike ba.
Sai dai naji ana cewa
“Sannu Allah sarki, ta farko ”
Nayi saurin tashi zaune “ina Aunty, ina Yaya, ina suke?ku fada mani.
Na Mike zan tashi tsaye aka rikeni gam can daga saman kaina naji anacewa
“Sannu. Tsaya kada ki tashi ki fadi yayan ki yana nan Aunty kuma tana can a falo kwance
Na mike “ku sakeni in gano Aunty
Sai alokacin ansa hannu an d’agoni. hawaye ne masu gudu da sauri ke fira daga idanuwan ta. Bata iya magana ba sai girgiza min kai.nakara fadawa jikin ta jikin ta muka rungune juna gam sai alokacin naji bakin ta yara magana
“Ikram ta tafi ”
Nayi saurin dagowa nace “dan Allah umma karkice min Aunty ta rasu ”
“Rabab duk musul mi dolene yayi imani da k’adda kiyi hak’uri wanda yafimu sonta ya karbi abarsa .babu abunda take bukata illa muyi mata addu’…… Bata karasa ba kuka mai tsanani yarufeta ”
Nadubi Umma nace “Umma da gaske ne Aunty ta rasu…. Nan na k’ara sulalewa ak’asa….
Farkowar da nyi nan naga suma su Aunty K’adra sun iso daga kaduna, na tashi na isa inda take tsaye tana kuka na fada mata.
Muka rungume juna muka dinga kuka,wasu dangin Ummu suka taso suke rik’e mu aka dauko jariran aka bai wa Aunty K’adra.
Za a iya samun mimtuna kamar talatin da zuwan Aunty k’adra, sanna tace intaso inraka ta gurin Yaya Altab, haka muka tafi munkai mu goma, muka shiga wajen Yaya Altab,
Amma mutane ke saman kanshi ana tofa masa addu’oi, da alama bai san abinda sukeyi ba.
Wannan dalilin yasa dole muka koma cikin, ni kuma sai naji hankalina ya k’ara tashi
_”ki d’auki Altab shine na farko a duniya mai k’aunar yayar ki ban da iyayen mu, idan yanzu na rasa Altab, ki d’auka na rasa zuciyata kwata kwata_ _kada mafarkinki ya karanto maki ranar da d’ayan mu zai rasa d’aya wato ranar dani zan rasa Altab, koshi ya rasani_ _wallahi sai kin tausaya duk wanda aka bari a doron duniya, tausayi irin mai bin jinin jiki_ _ina so ki fara addu’a daga yau Allah yasa ki dace da miji kamar Altab_
Maganar da Aunty Ikram kenan tayi min a daren da zata haihu. na kara kudundume kai na cikin hijab a saman gado amma na k’ara sakin kuka. Ina tunanin magan ganun da mukayi da ita
Lallai na yarda da maganar Aunty, yau ga Yaya Altab, a doron duniya ya zama abin tausayi.
“Rabab da zakiyi min wata alfarma da nayi alfahari dake a matsayin na dace da k’anwa mai k’aunata. ”
“Tame Aunty? Ke bakya gajiya, kiyi bacci ki tuna a gadon asibiti kike. Kina buk’atar hutu.”
“Ai dama magar hutu zanyi maki, amma wanda in an kwanta ba a tashi, sai dai yaya zakiyi da yaran nan da Altab. ?”
“Aunty kiyi bacci kawai, in Mum koma gida mayi maganar ”
“Gida? Aini ai ni gidan da zan tafi ba a dawowa balle har a tattauna da d’an uwa, Altab zai shiga wani hali gashi ba mai kula dashi.”
“Aunty dan Allah dan kin haihu sai yaya ya shiga wani hali. Da da kike haihuwa fa ya taba shiga wani hali ?”
“Rabab kina bani tausayi. Duk ranar da kika rasani nida mijina duk da kinada iyaye. ban taba ganin k’anwar da take tsanar mijin ‘yayar ta saboda yana nuna mata soyayya.
“Aunty Allah zan tafi gida inbar ki. na fada maki na daina tsanar mijinki. ”
“K’ilan ko? ”
Na girgiza kaina,

Leave a Comment