Hausa Novels

Mata Jigon Al-Ummah Hausa Novel

[7/5, 4:59 PM] Nabila Lady: πŸ‘©β€πŸ‘©β€πŸ‘§ *MATA JIGON AL,UMMAπŸ‘©β€πŸ‘©β€πŸ‘§*

πŸ‘‡πŸ½
*4 STAR’S WRITERS*πŸ–ŠπŸ“š

 

*NABILA RABI’U ZANGO* (Nabeelert Lady)
&
*NABILANCY LUV*πŸ’˜
(Auntyn S&S)
&
*NABILA DIKKO*
&
*NABILA MAMAN KHALIL*

 

*Page* 1⃣2⃣

*Nabilancy Luv* πŸ’˜
(Auntyn S&S)
πŸ‘‡πŸ»

Humaira ta Rungume yaran ajikinta taringa rarrashinsu dayi musu dabaru dan suyi hakuri su zauna agidan tare da ita domin tuburewa sosai Amal din tayi taringa kuka wai itakam bazata kwana awannan gidanba saidai gidan Abbanta

Dakyar tasamu suka lallabu tace musu Abban nasune yace su dawo wannan gidan wancan yasiyar wanda yafishi zaisiya musu inya dawo daga tafiyar da yayi takara dace musu bakuga wanda suka sayi gidan sunzo amota sun koremu sun fito mana da kayanmu waje ba?

Twins da sukafi wayo suka gyada kai afahimtarsu dai sun yarda

Da hakan tasamu Suka saki jikinsu agidan

Da dare tashiga kicin zata dora girki kenan saiga makwabciyar Zee din tashigo musu da Abinci a babbar cooler

Tariski humaira a kicin din tace mata ” a,a “yar uwarmu kada dai kinyi girki ga abinci nakawo muku.

Humaira da fara.arta tace “to aiko godiya muke don yanzun da zan dora mana.

Maimuna tace “haba dai ana tare aibama hakan a unguwar nan muko mace tafiya tayi tadawo aranar bazatayi girkiba zamu dora mata wanda zai isheta itada yaranta da mijinta hakama intayi bakuwa to balle ke da kike da nauyi kuma bakuwar makwabciyata ai bana bari ki wahalaba zee macece me kirki tana mana hakan muma dole murama mata.

Humaira tace “kai amma kunkyauta tsarinku na unguwar nan yayi Walh kunburgeni kunada hadin kai da kirki nagode Allah yasaka da Alkairi.

Maimuna tayi dariya tace “bakomai aiyiwa kaine.

Humaira tazuba abincin a babban flet sukaci su dukansu tuwon semo ne miyar yauki

Da safe ta kunna gas ta dumama musu tuwon daya rage sannan ta dafa musu shayi sukashe taga kayan shayi komai akan daining table ba abinda babu zee yar hutu ce tanajin dadi ba abinda ta nema ta rasa akwai zawarawa masu shi sannan tana daukar salary me tsoka

Tunda iyayanta suka rasu take zaune abinta agidan ita kadai bayan rabuwarta da mijinta

******
Karfe goma akano tayiwa Zee dayake da wurwuri tabaro KDn

Koda tazo taji damuwar da humaira tashiga

Ranta yai matuqar baci ta ringa masifa ita kadai humaira tayi shiru tanajinta

Taringa surfawa humaira masifa akan meyasa bazata kwaci “yancinta agun khamal ba da ace tun wuri bata bashi fuskar komaiba da bazai mata wannan sharrin ba

Takira Ashanty tana gaya mata

Itama Ashantyn ranta inyai dubu yabaci tace “ina humairan kuma.?

Zee tace” gata agidana da yaran

Ashanty ta kurma ashar “dan abu takazan ubansa saki nawa yai mata? Domin inba uku yayi mataba bazamu bari takoma ba abun ya isa haka dan yaga tana sonsa dan kut…

zee takatseta da sauri “aibasaikin kai ga hakanbama kawata ita kanta tace tabar zama dashi har abada ta hakura ammafa bai furta mata saki ba.

“au baiyi sakiba?lallai nizan karbo mata takardar sakin kuwa innadawo duk inda yake saina nemoshi bari jibi naji Ahmad yana cewa aikin nasa damukazo yakeyi din zaikare may be mutaho ajibin ko mukara one day mudawo.

zee tace “to Allah yadawo daku lfy.

sukai sallama ta kashe

zee tahau rabawa yaran tsarabar datazo musu dashi alawowi da biscuit da choculet ne

aiko dai sukaita murna abinka da yaro sai sukaita shige mata itako tanata jansu ajiki itama don yaran suna burgeta very cute dasu gasu kyawawa abinso

Humaira ta kwantar da hankalinta agidan Zee tana samun cima mekyau indai Zee taje store siyayya itada wani to komai na zee da iyalanta yafi yawa duk wanda yazo gunta ce masa takeyi yr,uwar tace tazo dayake ackn gidan take zance a farfajiya ko a falo

Kwana biyu atsakani saiga Ashanty ta dawo Ahmad ne yakawota har kofar gidan Zee din tashiga tayi masa sallama da Humairan

Humaira tasako hijabinta tafito suka gaisa

Yace “naji abinda yafaru tsakaninku da abokina kiyi hkr kidauki hakan ajarabar da ubangiji keyi miki kiyita Addu,a akan lamuranki Allah yasaukeki lfy Allah yaraya miki yaran ki insha Allahu zanringa taimaka miki akan harkar yaran bazan bari susha wahalar rayuwa ba duk abinda kike da bukata akansu kikirani kai tsaye ki gayamin nayi alqawarin zan musu komai na rayuwa domin abinda duk yayo khamal shiyayoni tare muka taso abokinane na yarinta shine baida halin da za.aso tunda har zaka juyawa iyali baya ka wulakantasu kibarshi wataran zaigane hanyar daya dauko bame bullewa bace kedai kirumgumi yaranki kibasu kyakykyawar tarbiya kinji.

Tashare hawaye tace “naji nagode Allah yasaka da Alkairi.

Yace “amin. Yakawo dubu ashirin yabata.

Takarba tana godiya takoma ciki tabarshi da Ashantyn ackn motar.

*****

Watanta biyu agidan Zee Allah yasauketa lfy ta zankado “yarta mace kyakkyawa me kama da ita futuk

Zee tagyare “yar fes dama ita takira wata metron takarbi haihuwar humairan agida

Ranar lahadi ce ranar hutu ashanty tace da humairan kyanta kisakawa yarinyar nan sunanki yanda kukai kama dinnan kinga saimuce mata little humaira damun ganta munganki.

Humaira tayi dariya tace “hhhmmm nikuwa kinga da sunan mahaifiyata nakeso nasaka sbd inajin kaunar mamana nasan tana sona sbd babana kawai bata nunawa walh ina lura ranar karshe danaje har hawaye ta goge dana fito kuma naga ta biyo bayana ta labe axaure kinsan da cewar ita tasan me takeji aranta kuma kinga ya cancanta inyiwa wani ciki takwara wataqila halan yasaka susoni agaba

Zee tace “humaira kenan walh kisani komai zakiyi musu baxaki burgesuba kawai dai zanbaki goyan bayane nima akan kisaka din domin cancanta bawai don burgewaba fatanmu dai har kullum Allah yakawo ranar da zaku shirya atsakaninku.

Ashanty tace “Amin. Duk sharrin shaidanne da sharrin tsinannnan can daya zamo sila ai da yardarr Allah saikin koma gabansu kundawo dai.dai

Humaira tagoge hawaye tace “Allah yasa. Nadade dayin nadamar abinda nayi musu tun aranar dana fara haihuwa nahaifo mace naringa ayyanawa araina shin intaimin hakan yazanji tabbas zanji ba dadi zanji daci ackn raina lallai iyaye abin bine.kuma dukkan abinda mukai inhar bamu tuba ba munbi Allah to musaka ran za.a kwatanta mana akanmu

Nan dai sukaita tattaunawa suna bata kyakykyawar shawara akan iyayanta tinda su masu sontane

Haka kuwa akai ranar suna akasakawa jaririya suna Nana Khadija

sunan Innartata saisuke kiranta da Deejah

Ahmad shine yayi yanka yai kayan jarirai

Yaringa mata hidima tamkar uban “yayan

Matarsa saida taji haushinsa da taji labari dan dai tana shakkarsa bata tsaurara ba abinba

Suko manyan kawaye har walima suka hada agidan aka kafa rumfa akofar gida sukasha shagalin suna “yan gun aikin Zee sunzo matan kaf dinsu “yan gayu domin tace musu sis dintace ta haihu tazo gidanta daga nesa

Harda gudummawarsu haka yan unguwar sunyi bajinta da kara

Anko sukai su ukun na less dan 20k

Zee ce tayiwa humaira ita kuma ashanty tasaiwa yaran “yan kanti dukansu

Bayan suna Ahmad yaringa kawo kafa gidan

Duk kwana biyu sai yazo wani zubin ma Ashanty bata sanin zuwansa zaikawo wa maijego kayan shayi da kudi

Kokuma yace gun yara yazo har dibansu yakeyi suje shan ice cream tuni sukai sabo dashi kuwa

Dayake zee naficewarta tun sassafe aiki batasan Anayiba

Saida tayi arba,in sannan Ahmad yazauna da ita yace mata zaisaka yaran amakaranta amma me tsada mekyau yakeso suyi

Ta amince taringa masa godiya

Yace mata “kiyi shiru ai yiwa kaine nasani ko inci gajiyar hakan agaba innazama sabon ubansu.

Humaira bata gano nufinsa ba domin shi har ransa sonta yakeyi tunda yagano ita din me kwayayen haihuwa ce yo dama shi uwar “ya”ya yake nema rashin haihuwar daga matarsane neman Aure yake Ashanty ba Aurenta zaiyi ba watsewa kawai akeyi ayanzu kuwa tunda yasamu agida ab’agas aishikenan

Yo Ahmad ai abokin naka baiyi saki ba…..πŸ˜ƒ

*fans kugaya masa yajira akarbo takardar saki daga hannun Khamal mana,To akwai tabbacin Khamal Din Zaibayar kuwa*?_

******* *******

*Alk’alaminπŸ–‹*
*Marubuciyar Zamani*
*Nabila Rabi’u Zango*
*Nabeelert Lady*
πŸ‘‡πŸ»

 

Hannu Malan Bukar yasa ya share zufar data zubo mashi, kada dai ace Alhaji ya samu labarin auren dole zai yima Hamrah? Gyaran murya Alhaji yayi yana fad’in Malan Bukar ko akwai matsala ne? Murmushi Malan Bukar ya saki yana gyara zama yace bakomai Alhaji kawai ka tuna mani da Mahaifiyar Hamrah ne baiwar Allah mace mai kirki.

 

Alhaji yace Hamrah itace d’iyarta kenan? Malan Bukar yace kwarai kuwa, domin ita kad’ai ta haifa Allah ya mashi abunsa, sai dai ko sau d’aya Hamrah bata tab’a kukan mutuwar Mahaifiyarta ba saboda Kubra ta had’ata da d’iyarta Hibbah ta rik’esu tamkar itace ta haifesu, saboda son da take ma Hamrah ne yasa lokacin da Hibbah ta samu miji Kubra tace dole tajira itama Hamrah ta samu sai ahad’a tare, ganin shiru bata samu ba yasa na yanke shawarar baka aurenta domin nasan zaka riketa amana, hakan da nayi sosai yayi ma Kubra dad’i, shiyasa da taga an kawo kayan sa ranar Hibbah ba’a kawo na Hamrah ba ta shiga damuwa, shine nace zanzo nayi maka magana sai gashi ma ka kirani.

 

Alhaji yace Allah sarki, gaskiya samun irin su Kubra a wannan zamanin sai an tona, Allah ya bata ladar rikon marainiyarsa da tayi. Malan Bukar yace amin. Alhaji yace dama akan wannan maganar ne yasa na kira ka, insha Allah zuwa gobe zan aiko da kayan sa rana sai a bama Hamrah hakuri dan bazan samu zuwa ba idan aka kawota gidana sai muga juna.

 

Malan Bukar yace haba Alhaji ai bakomai nima nafiso idan aka kawota kuga junan domin Hamrah yarinyar kirki ce, kuma tana na’am da wannan auren sosai. Alhaji yace maganar kayan lefe kuma zan bada wasu kaya da zatayi amfani dasu wajen bikin sai a d’inka mata, sauran lefen ba’a k’asarnan nakeso a had’o mata ba idan yaso bayan an kawota sai na bata lefen da hannuna.

 

Saurin kallonshi Malan Bukar yayi jin abinda yace, sam ba haka yaso ba, domin Kubra tace idan aka kawo lefen Hamrah sai su rage wasu kayan su sayar tunda sunsan lefen Hibbah dole zaiyi tsada.

 

Muryar Alhaji yaji yana fad’in ina fatan akwai telan da zai mata d’inki kamar kala goma a cikin sati hud’u? Murmushi Malan Bukar yayi yace sosai ma. Alhaji yace shikenan a goben za’a had’o da kayan insha Allah, kuma ba mata bane zasu kawo zan aiko da babban yarona mai kular mani da shaguna shine zai kawo, Bilal dan yana shirin tafiya waje da shi zan aiko amatsayinsa na babban ‘Dah na namiji. Malan Bukar yace ai ba damuwa mungode sosai Allah ya k’ara girma. Dubu goma Alhaji ya bama Malan Bukar yana fad’in ga wannan kayi cefane. Godiya yayi masa ya tafi cike da farin ciki.

 

***

Sosai Umma taji dad’in kud’in da Alhaji ya bama Malan Bukar, sai dai bataji dad’in rashin kawo lefen da zasuyi ba, sosai taci buri akan lefen saboda tasan dole Alhaji ya saki kud’i yayima Hamrah kaya masu tsada, amma bakomai ko bayan ya bata ne zataje ta d’auko abinda takeso idan ma hada zinari duk sai ta karb’o su.

Malan Bukar yace yanzu Kubrah zanje nasiyo ko zabbi ne guda biyu a soya ma yaron Alhaji da zai zo kawo kaya kinga kada aka gazawar mu ko? Umma tace wannan haka yake, dole sai munyi badda sahu akan wannan bikin na Hamrah saboda kada Alhaji da mutanan sa su fahimci wani abu, bakomai zanyi komai amma dole na fanshe wahalata.

 

Malan Bukar yace yauwa kinga bayan biki sai kije ki samo mana abinda ya bata, domin yace lefen ma a waje za’a had’o mata, gaskiya ba dan Hibbah ta samu miji ba da ita ya kamata ace ta auri Alhaji.

 

Saurin tashi Umma tayi tana fad’in haba Malan, taya zaka had’a Hibbah da wancan tsohon da yakusa yin jika da ita, ai wallahi koda Muftahu ba mai kud’i bane Hibbah bazata auri tsoho kamar Alhaji ba, ita dai wancan marar galihun banza taje tayi ta fama, amma Hibbah sai sardidin saurayi matashi mai arziki Miftahu.

 

Jiki a sanyaye Malan Bukar yake kallon Umma, jiyayi wani kululun abu ya tsaya masa azuciya, idanuwanshi ne suka ciko da ruwa, nan take kanshi ya sara, yana so yayima Umma masifa amma ya kasa domin asiri yana aiki akansa, acan k’asar zuciyarsa yanaji bai kyauta ma Hamrah da Mahaifiyarta ba, amma kuma baya iya magana.

 

Ganin yayi shiru ne yasa jikinta yayi sanyi, kada dai ace asirin jikinsa ya fara sanyi, dan tunda ta zagi Hamrah taga yanayinsa ya canza, k’arfin hali tayi ta sake d’aure fuska tana fad’in ashe Malan yanzu ka daina sona ko? Shikenan nagode. Da sauri Malan Bukar ya tashi yana fad’in haba ni na isa, kiyi hakuri idan na b’ata maki rai, duk abinda kikace haka za’ayi. Murmushin jin dad’i ta saki jin maganinta har yanzu yana aiki, sai dai dole taje a k’ara mata wani idan zata kai sunan Muftahu wajen boka domin yasa Hibbah ta mallakeshi. Kallonshi tayi tana fad’in shikenan ya wuce.

*****

Washe gari haka yaron Alhaji ya kawo kayan sa rana da suturar da zatayi amfani dasu wajen biki, sosai aka kawo kayan sa rana masu yawa, haka suka zuba mashi zabbin a takarda suka kulle tare da lemuna aka saka aleda Malan ya kaiasa har mota.

 

Bayan da suka gama rabawa aka bama Malan nashi itama ta d’auki nata aka fitar dana ‘yan uwan Hamrah sai itama aka bata kad’an ko zatayi rabo.

 

Bayan sun gama Malan Bukar ya kalli Umma yana fad’in dama wata alfarma nake nema awajenki, bana so naje garin iyayen Hamrah, shine nace ko zaki barta taje ta kai masu tayo ko kwana biyu ne domin tayi masu sallama? Tab’e baki Umma tayi tana fad’in dama ai bazan tab’a barinka kaje da kan ka ba, bakomai tunda zuwan k’arshe ne zata iya zuwa, na bata tayo sati d’aya ma, nima ina buk’atar sirri nida Hibbah agidan, idan ta tafi zamufi sakewa.

 

Washe baki Malan Bukar yayi yana fad’in nagode sosai Uwargidata. Murya ya bud’e yana kwalama Hamrah kira…. Bayan tashigo ya fad’a mata abinda Kubra tace, da sauri ta d’ago kai tana murmushi, godiya tashiga yima Umma. Tab’e baki tayi tana fad’in kamar wacce akace zataje wani birnin tarayya, keda zakije kauye ma, kuma wallahi idan kika wuce sati d’aya nida ke ne, sannan duk munafurcin da kika had’a zansa Ubanki ya tsine maki, dan haka kaja mata kunne agabana naji, kuma ka fad’a mata matuk’ar ta had’ani da ‘Yan uwanta babu kai babu ita, a yanzu nakeso ka fad’a.

 

Da sauri suka kalleta kowa gabanshi yana fad’uwa. Umma tace abinda kukaji shi nake nufi, kuma idan baka fad’i haka ba ina mai tabbatar maka da babu inda zataje, dan haka ina sauraron ka……..

 

***** ******

*Rubutawa Nabila (maman Kalil)*
πŸ‘‡πŸ»

_In the memory of my late father Alhaji Hudu mai Agogo my his soul rest in peace amen_

Cikin rawar baki Mufida ta amsa masa sallamar da yayi mata, amma amai makon ta fada dalilin kiran nata, sai kawai tai shiru ta kasa cewa komai,gaba daya kwarjin sa da tsoransa ya gama rikitata,sai kace wadda take tsaye a gabansa,jin shirun nata yana so ya cinye masa lokacinsa ,sakamakon wani taron gagawa da zasu shiga, hakan yasa ya katse shirun da cewa

“Wacece kuma daga ina?”

Cike da fargaba Mufida ta gyara zamanta saa’nnan ta hadiyi wani kakauran yawu da kyar ta daure ta ce masa

“Yallabai sunana Mufida, kuma nima a nan garin nake,
Ya kuma tambayar ta da

” aina kika sami wannan Lambar tawa yan mata?dan ni in banda mutane masu muhimmanci a rayuwata babu mai wannan lambar, ”

jin wannan tambayar daya watso mata yasa gaba daya ta gigice ta cire wayar ma daga kunnenta, ta kuma rasa mai ma zata ce masa,ga banta neya dinga dukan uku uku,ita dai daga nan batasan mai ya faru ba sai gani tai wayar ta kawo haske,take kua wani zafafan hawaye masu dumi suka ciko mata idanu taf, ba tare da tayi auneba suka dunga zuba ba kakautawa daga idanunta,hakika ko a iya haka mufida da fahimci matsayinta a wajensa,musamman ma ga yadda yake amsa mata magana a wani gagauce, tabbas shawo kansa ba Abu bane mai sauki.

Share hawaye tayi,kana ta lalubi lambar Alawiya ,tayi saa dan kua a lokacin har tayi shirin shiga wanka,bata boye mata komai ba dan ta fada mata dukkan abinda da ya faru,shiru itanma tayi na wasu yan lokaci saanna tace ,

“agaskiya kawata irin wadannan mutanen fa sunada wuyar shaani, na fiskanci dole bafa hk ya kamata ki tunkareshi kai tsaye da wannan maganar ba,dole kidanyi yan dabaru,”

“Kamar yaya fa?”

Cewar Mufida,

“Ina nufin naiman taimako,kinga a yadda kike bani labarin matar nan tashi to ina mai tabbatar miki da cewa bazata taba yadda mijinta ya hadata da wataba amatsayi kishia ba,idan kinga wata ta shiga gidannan sai dai kuwa yar wanke wanke,ina jin kawa baki san yadda yan Sudan suke da mugun asiri bane?ay gaba daya suke dauke idanun mazajen zu akan mata,mutum bazai kalli kowacce mace ba ballantana yayi shaawar karin aure,don haka mu hadu dake gobe karfe goma sha daya na safe akawai inda zan kaiki,saura kuma kike min bazakiba dan nasan halinki akan muguwar akidarki ta kin naiman taimako,amma fa ba dole ko ya kika gani?”

Itadai Mufida gaba daya da jin wannan zance jikinta yayi sanyi,tabbas a magan ganun da Alawiyya tayi biri yayi kama da mutum ,ace ko wajen aiki zata sai yayi mata rakiya? A idanun jama’a ma kenan wa yasan a gida kuma me yake mata?.dan haka ba tare da wani dogon musu ba ta amince da shawarar kawar tata.

Tsabar lungun da garin kedashi ko keke nape baya shiga, ala dole tasa sukai goyon biyu akan mashin saboda karancin sa awannan hanyar,tafiya ce sosai akeyin ta akan rairayi,dan idan dan acaba bai saba bin irin hayarba tuni zai zubar daku,inda tsautsayi ma kaji ciwo,itadai mufida duk tagaji ta kosa matuka su karasa inda zasu,dan mai mashin din ta fiskanci akwai rawar kai ,gudu yake sosai kamar akan kwalta yake

Bayanda malam Dattijo ya gama zane zanen shi akan kasa hade da dan jijiga kansa ,ya dago ya dubi mufida, wadda dama tun bayan zuwansa Alawiyya ta zaiyana masa komai yace

“Mufida ko?”

Da sauri ta bashi amsa da a malam,saannan ya cigaba da cewa

Tabbas taurarin ki da nashi masu haske ne,akwai kuma fa’ida game da hakan,amma fa husulin dake shirin dusashe wadannan taurarin mai girman gaske ne,ya zama dole a tashi da rokon Allah dan magance faruwar hakan,domin kowa matukar hakan ta kasance bazai wa kowa kyauba,”.

Da sauri Alawiyya ta tabbayeshi da cewa

“Malam kuma menene husuli,?”

Jin haka yasa yadan saki murmushi kana ya bata amsa da cewa

“Wani shamaki ne mai girman gaske da zai katange kawarki daga aurar wannan mutumi,akwai aiki mai karfin gaske akansa game da mata ,dan haka kada ki kara kuskurar sake masa magana ko kice zaki fada masa bukatarki,da kanshi zaizo gareki,ya kuma bukaci ki yadda ya aureki ,ammafa husulin babbane yan mata,zaa’yi rubutu akan allon karfe,akuma wankeshi da ruwan zamzam,ya zaayi ki bashi wannan ruwan yasha?”

Idanu Mufida suka hada ita da Alawiyya ,dan dukkansu sun san alamarin bamai yiwuwa bane,mlm ya katse musu shirun su ta hanyar cewa

Nasan bazaki iya ba yan mata, dan idan irin haka ta faru turawa mukeyi a aywatar mana da duk abinda mukeso,zan gama komai daga nan zansa wata mai siffaraki taje masa cikin mafarki ta bashi,zai kuma sha,kuma bukata zata biya da izinin Allah, kedai kawai kibi duk kaidodin dana fada miki,”

.murmushi Mufida ta saki kana tayi ajiyar zuciya,dan haka ba tare da wani bata lokaciba ta zaro dami yan dubu daya daya ta ajiye gaban malam,ita kanta batasan ko nawa bane,nan dai ya bata wasu kullin magunguna na wanka dana sha sukai mai sallam suka fita,tare da alkawarin dawowa bayan komai ya kammala,basu sami matsala wajen fita daga garinba,kasan cewar motar diban itace ta shigo dan haka da sauri suka hau kan itace suka zauna kyam sai tafiya, *mata kenan* *JIGON AL’UMA*

Bayan kwana uku tsakani kamar yadda malam ya fada ma Mufida kuwa hakan ta kasance ,Tabbas idanunta ba karya suke mataba DC Anas ne a kofar gidansu,tasha mamaki matuka ace abinda kake nema ido rufe yau gashi har gida.

Karasawa tayi suka gaisa sannan tace masa ya karaso daga zaure, bayan ta dakko shimfida tayi masa ,ta kuma ce mishi zauna,shidai ba abinda yake face zumudin ganinta,ya kura mata idanu kur, ko kiftawa bayayi,ita dai ta kasa cewa komai dan tsabar murna

Cikin tsanani so da kulawa yace

Mufida agaskiya da maganar aure nazo gareki bada wasa ba,duk da dai yau daya kika fara ganina ,nasan zaki dau maganar tawa kamar wasa,hakikanin gaskiya Allah ya doramin tsananin kaunarki a zuciyata ,kuma ni ayadda nake jinki a raina banson auren mu ya wuce sati buyu ma,”

Fadin hakan yasa Mufida taji wani mugun sanyi aranta ,take cikin zuciyarta tace lallai malamin nan ya iya aiki sosai,rausayar da idanu tayi sannan tace

” nagode da furta kana sona da yayi,kuma zanyi shawara game da kalamanka a kaina,”

“Kamar zuwa yaushe ?”
ya katseta da tambaya,

“Nanda sati daya”

Da sauri ya kuma katse yana cewa

“Haba mufida kada ki azabtar da zuciyata mana da yawa, wlh sati daya yayimin yawa,nandai da dare zan kiraki donjin shawarar ki”

Zata ce wani Abu yace mata” shrrrrt” hade da kashe mata idanun sa masu kyan gaske,ay bata San sanda tai difba,dazai tafi cheque a ajiye mata na 500k bai jira tace wani abuba ya fice abunsa……..

 

****** *******

 

*Alqalamin Nabeela Dikko..* ✍🏻

πŸ‘‡πŸ»

“Da sallama Aliyu ya shiga gidan…”Inna shatu ce ta amsa masa yayinda take kokarin fitowa daga makewayi.”Hannunta rike da buta.”

“Inna barkah da asuba Aliyu ya ce “da ita cikin ladabi.”

“Barka kadai gadanga antashi lafiya ya hakuri!?”Inna ta ce da shi.”

 

“Da godia inna….Baba fah?”

“Mallam yana nan shiga daga ciki bari naje na sama maka abin Karin kumallo naja ta tafi islamiyya.”

 

“Yawwa Inna nagode….”Dakin mallam ya nufa inna ko abin kari taje ta daukowa Aleeyu a kitchen Wanda daman an ajiye masa.”

 

“Da fargaba ya shiga dakin cikin sanyi da tsoron me zai biyo baya ya gaida Baba.”

“Amsawa yayi fuskarsa a daure! sannan ya ce “Aleeyu naji dukkan abinda ya faru! kuma saleema bata kyauta ba! kuma kaima baka kyauta ba! da ka yanke wannan danyen hukunci! a gaskiya banji dadi ba!”Ba yadda zanyi qaddara ta riga fata!Amma ina horonka da babbar murya karka qara kuskuren saki irin wanda ka aikata!Fatana Allah yayi maka wani zabi na alheri amma adinga sara ana duban bakin gatari!Kar ka manta *MATA* sune *JIGON AL’UMMAH* wulaqanta su ko cin zarafinsu ba abine mai kyau ba!Dan su ne JIGON AL’UMMAH kuma hasken Al’ummah,ko ba komai iyayen yarinyar nan suna da kirki da mutunci!”Hakan da ka aikata kamar bamuyi masu adalci ba!”Shiyasa nayiwa tufkar hanci nayi saurin sanarda mahaifinta…”Kuma ranshi ya baci matuka yabani tausayi wallahi Allah dai ya shirya mana.”

 

“Ameen Baba,”Aleeyu ya ce “wanda tun fara zancen ya suke kansa aqasa cikin ladabi yana sauraren mahaifinsa.”Duk sai yaji wani iri ba dadi!Tabbas awani gefen bai kyautah ba dan idan an ciza hurawa akeyi.”Nan dai ya cigaba da bawa baban nasa hakury har ya dan huce.”Inna shatou kamun gero da yaji gyada da kosain wake takawo masa domin kari.”Batare da bata lokaci ba ya fara ci suna taba fira har ya cinye tatas saboda yunwa ta azabtar da shi sosai.”

 

 

“Kai malammai meye haka kunyi sallama an amsa muku kunki ku qaraso!”Idan bazaku shigo ba!”Ai sai ku koma inda kuka fito!”IInna luba ta ce da su saleema “A hasale!”

“Ba saleema ba har lailah taji tsoro da sauri suka qarasa gurin gurfanawa sukayi dukkan su suna gaida inna da Baba.”

 

“Wani kallo banza baba yabi saleema da shi mai cike da tsana…..kan kace me!”Inna luba ta rarumo tabarya a gefen kitchen ta makawa saleema aka……”Wayyo na shiga uku lailah….!”Saleema tace a firgice saboda zafin goshinta da ke zubda jini!Inna ko jibgar saleema takeyi ta ko’ina tana zaginta tana kukan takaici!”Saleema kuka take ita da lailah suna ba inna hakuri!”Lailah kokarin jaye inna takeyi a jikin saleema kamar daga sama taji saukar mari a bakinta wanda inna ta yanka mata saboda takaichi nan ta hade har ita ta dinga jibgar su iya karfinta ga inna luba da jiki barkallah…Ko damutsanta kadai abin kallo ne!Nan take suntum bakin lailah ya qabe!”Da kyar Malam ya samu kan inna yana bata hakuri da lallami kan ta kyalesu hkn!”Wanda tuni tayiwa saleema targade a kafa!”Nan ma mallam ya dinga zubawa saleema fada da zagi cikin masifa!kuma dukkan abinda tayiwa Aleeyu sai dai ya sanar mata komai!…..”Lailah da bakinta ya kumbure sai kuka takeyi bare saleema da tasha dukan kawo wuqa…!”Hakuri suke bashi saboda shima da sun matsa dukan su zaiyi.”

“Mallam yace yanzu ki tashi ki wuce kibar min gidanah ki koma gidan ubanda kika kwana jiya Wanda ya fiye maki nan!Kibi duk Wanda kika zaba da yafimu daraja!Kije duniya makaranta ce saleem…..tun bai isuwa zancen ba inna da jikinta ya dauki rawa!”Kuma ya mutu mututus domin saukar Abu taji kmr mashi azuciyarta!shiyasa taji wata irin fargabar saleema ta darsu azuciyarta…”Ta ce cikin sanyin murya haba mallam ina zataje to!?”Dan Allah abar zancen nan ayi hakuri saleema kiyi hakuri bacin raine yasani nayi maki hakan lailah kuyi hakuri…!”

 

“Haba Luba hakurin me kike vasu!? ai abokin barawo ma barawo ne ita da qawarta halinsu daya!” Dan haka ni ba uban da zan ba hakuri ku tashi ku fice min daga gida….!”

“Haba mallam ba za’ayi haka ba!Hakuri zamuyi da fatan shiriya agareta!”

“To nidai……Innnalillahi wa’inna ilaihi raju’un!!!Inji Baba tare da dafe kansa da yayi muguwar sarawa ga jiri da ke yawo da shi asararin samaniya!”A hankalin ya kai kasa ya zauna!”Da sauri ta kama shi sannu mallam ga ruwa!”Dan Allah kayi hakuri ka debe zancen nan aranka kar wani ciwo ya kama ka!”Wannan abin ya riga ya faru kuma ruwa baya tsami banza da saleema har Aleeyu dukkan sunada laifi!”Fatanmu Allah yayi mata wani zabi mafi alheri!”

“Ameen luba ba yanda zanyi da ikon Allah.”

“Yawwa,mallam kaje ka kwanta ka huta!”

“Hakan zanyi saboda banajin dadin jikina duk yayi sanyi!”saleema kuyi hakuri komai ya wuce Allah yayi mana jagora!”

“Ameen,Sukace dukkan su kana baba ya shiga dakin!”Inna ko jikinta har mazari yake,tuni takawo masu abinci da abin sha,tana basu hakury!”

“Saleema dadi ne aranta saboda komai yazo mata da sauki!”A wani gefen ko duk jikinta ciwo yake mata!”Amma dai Alhamdulillah tunda ayanzu tagane aikin mallam yayi daidai.”

“Abinci suka Dan tsakura lailah ta ce ”Saleema ni natashi zanje aduba lafiyata na samu maganin da zan sha!”Wallahi abinda akayi min yau har na manta da yaushe rabon ayi min irinsa!”Ba Dan Inna bace kowace yau sai ta kwana agidan mari!”Haka kawai mtwsss ni kinga wucewata zanyi tun ba shigo ta hanani tafiya ba!”

 

“Haba lailah kiyi hakuri lokacin da muka zo aikin bai kama jikinsu ba,Ina ga tsarin da ke jikinsu ne yayi yawa,kinsan su da yawan karatu da addu’ah, ai kinga yanzu sunyi sanyi sosai!”

“To nidai ki gayamata na wuce idan ta fito daga toilet din,Ni har yanzun Wallahi Ina ji haushin abin nan!!”

“Haba lailah!”Kibar zancen ya wuce!Kiyi hakuri!”Kuma nagode sosai sai gobe zan zo kinga yanzu bana fara fita ba!”Amma goben zance masu asibiti zanje aduba ni!”

“Owk sai kin zo!!”Amma karki kara sakewa ana dukan ki kamar jaka!”Lailah ta ce sannan ta wuce bakinta a kumbure!”

“Inna na fitowa taga lailah ta wuce!”Saleema ta ce inna daman mijinta ne ya kirata ta dawo gida tayi baqi!”

“To ba laifi ni kunyarta ma nikeyi!”Ki kara bata hakuryi kinji saleema!”Yanzu ni zanje gidan tanko mai dauri yazo ya gyara maki targadan nan kar yayi tsami!”Kiyi hakury bacin zuciya ne ya kawo hakan!”Akan dan wani na nemi halaka tawa ‘yah!.”

“Haba inna!Ai kin shafa min mantileta ynzu hkn INA jin zafynsa! kibar shi kawai da sauki!”

“A’ah bazan yadda nayi wasa da lafiyarki ba,kedai sai nadawo inna tace”Sannan ta wuce.”

“Shagon sayarda magani lailah ta nufa aka duba bakin sai magungunna da aka bata!”Gida ta wuce tana tsaki!”Yanzu me zancewa Abba yara!zance ana fada naje rabon fadan akasamu sabani aka dakeni abaki!”Kai gaskiya matar nan ta cutar da ni!!!”Da zancen zucin har ta isa gidanta,fatty tasamu ta na haramar komawa gidanta Dan tagaji da zaman jiran lailah…!”

“Da mamaki ta kalleta lafiya lailah had’ari kikayi ne!?”Kai!fatty Dan Allah Barni da abin haushi kedai Maman saleema ce ta jibge mu duk ita taji min ciwon nan wallahi fatty aini bazan qara karambanin shiga tsakanin masu fada ba… ”

“To garin yaya! Hakan tafaru!?Na kira ku duk baku daga ba!?Ina ita saleemar ne!?

“Nan dai lailah ta labartawa fatty komai tun farko har karshe dangane da auren saleema!”

“Fatty bataji dadin al amarin ba,Amma mai faruwa ta faru!”Ta nisa tace”yanzu lailah shi ne Baku sanarda da ni duk abinda ya faru ba!?Ko mun fara yar boye boye atsakanin mu ne!?”

“Ba haka bane fatty yanzu nan muka ce gobe gidanki. Zamuje asanar maki!”Kiyi hakuri!”

“Ba damuwa ni zan koma gidan Dan na dade anan!”Allah ya sauwaqa ya baku lafiya.”

“Ameen nagode sai munzo goben “Inji lailah.”

“To yayi kyau sai na ganku akwai labari mai dadi shi ne nakosa na ganku na sanar maku!”Masha Allah inji lailah….”Da Har
Parking place ta raka fatty suna cigaba da tattaunawa, in da motar ta nufa taja yayinda get man din da sauri ya wangale mata get!”Ta fice daga gidan aranta tana jimamin hali irin saleema .”

 

Leave a Comment