Books Reviews & FAQs

Abba Ne Hausa Novel Complete

_*🌻ABBA NE🌻*_

Hakkin Mallakar

_*Sarat Alk’asum ( Maman Nusaiba)*_

 

_*JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION*_

Ina godiya ga rabbis-samawati daya bani ikon rubuta wannan labarin, ina fatan yadda na daura Alk’alami na lafiya na saukeshi lafiya, Allah ka bani ikon rubuta abinda zai anfani Al’ummar Annabin mu Manzo (s.a.w.), Allah ka karemu da karewarka ya rabbi ka bamu zaman lafiya a kasashen mu baki daya, ya rabbi ka k’ara mana ilimi da fasaha da fikira da basira, Allah ka daukaka dukkan wani Marubuci/Marubuciya, ya Rabbi ka k’arawa Marubuta Yan Uwana daukaka da basira.

Wannan littafin na kune akan N 300 only kacal, kada ku bari a baku labari ga masu son labari su tuntubeni ta WhatsApp number na 👉🏻+966577675904 .

بسم الله الرحمن الرحيم

0️⃣1️⃣

*NIGER 🇳🇪*

Tafiya suke cikin mota dukkan su suna hira cikin nishad’i yayin da na hango wani Yaro kyakyawa wanda bazai wuce shekara 13 years ba yayi shuru yana jinsu”Wata kyakyawar Mata ce gefenshi wanda baza ta wuce shekara 30 ba hannunshi cikin nata tana murzawa a hankali lokaci zuwa lokaci tana kallon shi. Cen gaba wanda yake driving d’in ne ya d’an juyo fuskar shi dauke da murmishi shima bazai wuce shekara
40 ba” Yace Khalil ya dai naga ka wani had’e rai? Ko baka son zuwa Nigeria ne? Sake had’e rai Yaron yayi baice komai ba, sai bud’e k’ofar hanci yake. Tsohuwar dake gefen Baban nashi ce tace” Kai Khalilu dan butar Uwaka wajan dangin nawa ne baka son muje? To baka isa ka hana muyi zuminci ba koda yake ai kayo gadon Uwarka Salma shiyasa, nidai ba ruwa yo to in ba kin dangi ba Yaron nan tinda ka shigo motar nan sai wani cin magani kake. Ato nidai baka isa ka hana muje Nigeria ba wajan Yan Uwana ba, wannan idan ka girma an shiga uku a gidan nan, dan na lura mugu za’ayi Babba ma ba karami ba….
Murmishi Khalil yayi yace” Abba wai ni mugu ne inji Inna? Murmishi Abban nashi yayi yace” A’a Khalil tsokanar ka take kaji.. Inna ta rik’e baki tace yau ni naga jaraba ido da ido, kenan kai Umaru baza ka mishi fad’a ba ya rage bak’in hali sai kace wai tsokanar shi nake? To shikenan na dena magana babu ruwana idan D’anku ya zama munafiki, yo in banda rashin son gaskiya irin naka Umaru sai kace tsokanar shi nake, nifa da Bakori naji ance ka fad’i wannan maganar sai nace anyi k’arya.. to sai kuma gashi naji da kunne na, idan mukaje Bakori bazan sake zuwa inda kuke ba…
Abba yayi murmishi yace to yi hak’uri Inna zaneshi zanyi ma tinda har baya so aje Nigeria zuminci. Gyara zama tayi tace Yauwa yanzu naji bayani. Gudu sosai Abba keyi ganin Yamma nayi burinshi kawai subar dajin da suka shiga mai duhuwa. Kiiiiii Abba yaja burkin mota yana fad’in Innalillahi wa’inna ilaihin raju’un, Inna Y’an fashi gasu cen a gaban mu. A matuk’ar razane Inna ta kama hannun Abba tace mu fita kafin suzo mu gudu. Da sauri Abba ya fito Khalil da Maman shi suma suka fito hankali a tashe. Motocin dake gaban nasu wanda Yan fashin suka tsare su suka hana suga fitar da su Abba. Wani rami Abba ya gani guda biyu Y’an madaidaita, kallon Inna yayi yace” Salma kama Inna ku shiga nan, kai kuma Khalil zo mu shiga nan.. da sauri Salma da Inna suka shiga cikin Ramin nan suna k’yarma” Abba da ya dauko wata jaka daga mota ya kwanta ruf da ciki, ganin haka yasa shima Khalil ya kwanta. Cikin azama Abba ya zarge jakar sai ga bindigogi har guda uku gefe guda kuma wata k’aramar jaka ce a ciki. Abba ya kalli Khalil da shima shi yake kallo yace” Khalil ka zauna anan amshi wannan duk wanda kaga yayo nan sai kasa hannun ka anan ka danna to zaka harbeshi.. Khalil ya soma kuka ya rik’e hannun Abba gam yace Abba kada kaje zasu kashe ka kamar yadda suka kashe min Y’an Uwana, kuma waďancen ma k’ila sun kashe su. Rufe mishi baki Abba yayi yace” Kul naga kayi kuka Yarona ka zama Jarumi a duk inda zaka kasance, kada ka bari wani yaga rauninka” San nan ka rik’e bindigar nan nasan ka iya harbawa tinda na koya maka dama saboda halin rayuwa. Girgiza kai Khalil yayi sai kuma yayi saurin goge hawayenshi nan da nan yaji wani kwarin gwiwa yazo mishi” ya gyara kwanciyar shi yace” Abba na dena. Murmushin k’arfin hali Abba yayi yace” Zanje ko ni ko su, nayi alkawari zan kare kasata bazan tab’a zuba idanu ina ganin ana zalinci nayi shuri ba, wannan hakkina ne k’are duk wanda yake dan kasata” Yana fad’in haka ya ciro da waya irin na Police ya soma magana cikin halin damuwa, yace” Hello Bonsoir Sir Shaf ďeta Umar mai Nasara ke magana dajin iyaka tsakanin mu da Nigeria a turo min da Sojoji mota uku. Daga cikin wayar aka amsa mishi da to yanzu yanzun nan za’a tura maka su ko kuma zamu turo maka da Sojojin sama. ABBA ya amsa da to Sir merci beaucoup” Bai tsaya yin komai ba ya nufi inda suka tara mutanen. Cikin sanďa ya shake wani dake kusan shi ya rife mishi baki alburushi ya sakar mishi a cikin shi nan take ya mutu” cikin Azama ya isa ga d’ayan shima ya kashe shi da haka ya kashe mutum hud’u duk basu ankara ba… Yana saita wani ne ya juyo, da sauri yayi baya yana fitar numfashi babu abinda kunnen shi yake juyo mishi sai kara da kururwar mutanen da suka tsare da alama kashe wasun su ne sukeyi. A guje ya koma inda ya bari Khalil yana huci, kallon Khalil yake yace Yarona bazan bari su k’ara kashe kowa ba zan fanshe su, na tabbata ni suke nema. Duk da Khalil Yaro ne amma yana da hankalin gane inda magana ta dosa,cikin kidima yace” Abba to da me zaka fanshe su? Ka bari Sojojin su iso tinda kayi waya dasu. Girgiza kai Abba yayi yace” No kafin suzo sun kashe su kuma har da Yaran goye da tsofaffi bazan iya bari ta dalilina a kashe rayuka ba. Rike shi Khalil yayi yace” A’a nidai don Allah Abba kada kaje. Zame hannun shi yayi ya sake kira Shugaban nasu akan sun tafo ne” Ogan nashi ke sheda mishi ai suna cikin tafiya mai ya k’are amma za’a kawo musu , su kuma Sojojin sama ba’a samu matuki ba saboda yau sunje gida hutu, shima yana d’aya daga cikin matuk’an jirgin. Abba ya k’ara shiga tashin hankali fiye da wanda yake ciki” Yana huci yace” Khalil zan baka umarni zaka bi? Khalil yace eh Abba zanbi…cikin yanayin damuwa da kuna kallon bankana ya shafa kan Khalil yace Allah ya maka albarka” Ameen Abba cewar Khalil da ya kagara yaji umarnin da Abban nashi zai bashi. Bud’e jakar Abba yayi ya fito da wata takarda guda uku ya mik’awa Khalil yace” Wannan ko bayan ba raina ka bari sai ka girma ka mallaki hankalin kanka ka karanta da kyau, kuma duk abinda na rubuta ka aiwatar. Jinjina kai Khalil yayi dan ya ma kasa magana. Abba ya dauko Bom guda uku ya daura a jikin shi, ya kalli Khalil yace maza zo muje. A matuk’ar tsorace Khalil yace Ab…Abba bom ne fa kasa” Had’e rai Abba yayi yace Bana son duguwar magana Khalil. Cen kusa dasu Abba ya tsayar da Khalil ya kalleshi da kyau yace” Khalil ka kula da Maman ka da Mahaifiyata, rai na fansa ne ga k’asa ta zan yaki kowa akan kare hakkin dan Adam” shi dai Khalil kallon Mahaifin nashi yake ba ko k’iftawa. Abba yace” Idan na isa cen zan kirga daga daya zuwa biyar da nace ka harbo to kayi haka kana jina da kyau? Ai tuni Khalil yasaki futsari yace” Abba bazan iya wannan abun ba taya zaka ce na harbe ka,idan nayi haka fa mutuwa zakayi , so kake mu tashi ba kai ne? Wasu zafafan hawaye ne suka zubowa Abba ya maidasu dan karfafawa yaron nashi,yace” Nina saka kuma da kayi ka koma cen wajan Maman ka ka bata du abinda na baka” Matsowa yayi kusan kunnen shi ya soma mishi magana cikin kunnen. Bayan ya gama ne ya juya zai tafi Khalil yace” Abba na zanyi duk abinda kace” Ya fad’a murya a sarke. Murmishi kawai Abba yayi yace Nagode d’ana san nan yayi saurin nufar su.

Abba na isa cikin d’aga murya yace” Ku dakata! Ba dai ni kuke nema ba to gani. Kwashewa da dariya sukayi suna nuna Abba da bindiga sukace, Ashe da gaske kana kishin Al’ummar ka? Cikin rashin tsoro Abba yace Ka tab’a gani Soja yaji tsoro? Ko kaji ance maka Umar yana tsoron irinku? Babban cikin su ne yace” Ai dama da niya muka kama wannan mutanen nasan Y’an k’asar ku ne kuma ko ka b’oye idan kaga muna musu fiďar Rago zaka fito. Abba yace” Ai na san Mutum biyu ne zasu turo ku, idan har raina kuka so to ku saki wannan bayin Allah suyi tafiyarsu ni kuma gani ku kasheni. Dariya suka saka suna nunashi da hannu suna fad’in shege Soja yaga uwar bari. Tuni suka saki wannan mutanen dama Babbar mota ce kowa ya shiga , wanda aka harba suka hada da su a guje direban yabar wajan kowa bin Abba da kallon taysayi yake. Khalil dake cen gefe ya b’oye a cikin wani rami dake kusan su, sai hawaye yake yi, kallon su yake d’aya bayan d’aya. Ji yayi Abba na fad’in” D’aya Biyu Uku had’u biyar wuta! Ya fad’a da karfi. Cikin hanzari Khalil ya harbi bom din da Abba ya d’ago a hannun shi,tuni bom din suka tashi da wuta. A guje Khalil ya nufi ramin da su Inna suke ya fad’a yana k’yarma. Cen yaji takun mutane suna ina Matar tashi take ne? To ku shiga mu duba har Yaron nashi Oga yace mu kashe su” Jin haka yasa Salma ta kunshe bakinta tana kuka kafin suyi wani motsi sai ji sukayi ana fad’in” Maza ku fito yanzun nan.. jiki na rawa suka fito” Babban cikin su yace” Hajiya zabi biyu zamu baki ko mu miki faďe a gaban idanun Uwar Mijinki da D’anki ko kuma mu kashe Danki da Uwar Mijin ki sai ki zabi guda… zazzaro idanu Salma tayi cikin matuk’ar tashin hankali tace” Don Girman Allah kuyi hakuri karku kashe min Yarona, ni na yarda ku kasheni ku barsu su a raye.. wani zazzafan mari taji ya sauka a kan kuncin ta, Khalil daya zaburo d’aya daga cikinsu yasa gindin bindiga ya kwada mishi a kai tuni ya zube a k’asa sumamme” Inna ganin wannan bala’in yasa itama ta suma.. Salma kuka take kamar ranta zai fita sai rokon su take amma sai dariya ma suka mata” d’ayan cikinsu ne ya janye mayafin jikinta yana lashe baki yace” Kai gaskiya dan iskan Sojan nan ashe yana da kayan alatu” dariya suka sa suna janta kiii a k’asa tana kuka.. Babban cikin su ne ya kama rigarta ya keta suka sa dariya, Ita kuma Salma da ta jigata sai kare jikinta take da hannu tana k’yarma. Cikin muryar kuka tace Azzalumai Insha Allah D’ana ne zai kawo karshen ku , kun kashe min Miji.. dariya suka sanya Babban cikin su yace” Yau zaki ga zalinci ganin idanun ki kai ku bankare min ita.. kuka take tana ja da baya tana girgiza kai dan maganar ma ta gagareta. Cikin rashin Imani ko wanne saida ya mata faďe sun kai biyar” suka jata suka jefa a mota. Babban cikinsu yace” Su Babawo sun mutu a hanyar bom din nan ,shi Sojan nan ya dauka mu duka ne. Dariya suka kuma sawa suka ja motar su a guje… Khalil tin lokacin da Maman shi ta kwalla k’ara ya dawo daga sumar da yayi amma rashin karfin ya hana shi tashi, jini ke ta zuba ta kanshi bai san sanda ya kuma sumewa ba, sai farkawa yayi ya ganshi a Asibiti. Kallon gefe yayi yaga Inna ansa mata karin ruwa d’ayan gefen kuma K’anen Abban shi ne da Matar shi tsaye a kanshi. Sannu suke jera mishi amma baice musu komai ba har Doctor yazo. Bayan ya gama auna shi ne yace To alhamdulillahi Kwakwalwar shi bata samu matsalar komai ba zaku iya zuwa gida nan da yamma. K’anen Abba yace mungode Allah yau wata d’aya muna jiran tashin sa sai gashi ya tashi, Allah ya jikan Salma da Yaya Umar.. kallon su yake kamar ya samu TV wata d’aya yake maimaitawa aranshi kenan wata yayi baisan indakanshi yake ba? Wasu zafafan hawayene ke zarya kan kuncin shi. Inna na farkawa ta ringa kuka tana basu labarin abinda ta gani kafin ta suma, suma din kuka suke suna bata hak’uri.
Da yamma Aka basu sallama suka dawo Gida inda aka kai Khalil dakin shi.

_*BAYAN SHEKARA GOMA*_

_*FARCE AÉRIENNE*_ babban Office d’in Sojojin sama wadda take a garin Niamey Niger” Sojoji ne sunfi dari uku jere kowa ya k’ame a inda yake, hannayen su rike yake da manya manyan bindigogi yayinda kafafuwan su sanye yake cikin bak’in takalmi mai tsaki har zuwa kusan gwiwarsu, ko wanne daga gaban rigarshi an sanya sunan shi dana Mahaifin shi.. Ogan su ne ya soma jawabi kamar haka: Alhamdulillah Masha Allah yau ne kuka gama tirenin da ake koya muku, dan haka sakamako ya fito kuma mutum biyu ne suka samu sakamako mai kyau a wannan shekarar. Shuru kowa yayi dan kowa so yake yaji sunan shi. Ogan nasu ya yace Wanda sukaci wannan Jarabawar ba kowa bane sai _*Ibrahim Khalil Umar mai Nasara*_ da kuma _*Abulkareem Yusuf mai Nasara*_ sune wanda suka ci a wannan shekarar congratulations muna tayaku murna. Khalil d’aya lumshe idanun shi tin lokacin da aka soma bayani jin an kira sunan shi ya bud’e idanu da sauri” Abdul dake kusanshi suka rungume juna cikin tsananin farin ciki. Ogan nasu yace su bishi ciki za’a canja musu Kaki, san nan ya sallami kowa su kuma su Khalil suka bishi. Suna zuwa babu bata lokaci aka dauki kake sabo dal aka basu izinin su sanya” wani waje suka shiga inda suka sanya kayan. Ogan nasu na murmushi ya mike ya sanyawa Kahlil taurari guda uku a ko wani kan k’afar shi, ya sanya mishi hular san nan yaja da baya yana murmishi. Sara mishi Khalil yayi ya kame ” Kallon jikin kakin nayi naga an saka *General Khalil Umar mai Nasara*. Shima Abdul sanya mishi nashi akayi inda shi kuma nashi taurari biyu ne wato kenan Khalil ne gaba dashi, shima kasan an sanya sunan shi a jiki. Ogan su ya sara musu ya basu hannu suka zauna ya shiga yi musu bayani akan abinda ya shafi tukin jirgin sama da komai duk da sun iya amma ya kara musu haske akai. Suna tashi a tare shi da Abdul suka nufo gida ranasu fess Abdul sai murna yake, yayinda Khalil ke kissuma abubuwa daban-daban a cikin zuciyarshi, idan ba lura kayi ba baza ka tab’a gane yana cikin farin cikin ba. Suna isowa cikin takunshi na kasaita ya fito sai yanzu na k’are mishi kallo, fari ne amma ba har cen ba, dogo ne kakkarfan gaske fuskarshi dauke da saje wanda ya k’awata fuskartashi, yana da kyau dai-dai misali.. Cikin parlon suka nufa bakin su dauke da sallama” Mamy dake zaune a parlon taci ado na kece reni da fara’ar ta ta amsa musu. Abdul Baki yayi rufuwa yace Mamy munci jarabawar nan fa kuma Khalil shine Oga na. Da sauri Mamy ta mik’e ta rungume Kahlil dake tsaye yana kallon su” Cikin murna tace Alhamdulillah na tayaka murna Yarona duk da bana son aikin nan amma ya zanyi da kai tinda kace zakayi. Murmishi yayi cikin zazzakar muryarshi yace” Merci beaucoup Mamy na. Sakeshi tayi ta rungume Abdul” Bayan sun zauna ne ta kawo musu abinci. Khalil loma uku yayi ya mik’e yana yamutsa” Cike da damuwa Mamy tace Kai fa dad’ina da kai kenan baka son cin abinci. Murmishi yayi sai yace zan sha tea Mamy. Mamy tace OK bari na hado ma san nan ta nufi kitchen. Shi kuwa Abdul sai sunbatu yake yana fad’in, Ai kaji Alkur’an cin abincina zanyi” Sai kuma ya d’ago ganin Khalil ya nufo d’akin shi, yace Kai ina Inna wai take? Ko ci kanka Khalil baice mishi ba ya shige d’akin shi…..

Washe gari Khalil da Abdul suka shirya zuwa Office Mamy nata musu Addu’a, su kuma suna amsawa da Ameen. Koda suka isa tuni an shirya musu komai, Suna isowa jirgi suka shiga Ogansu ya basu wata takarda yace” Khalil wannan da kunje Maradi a babbar Office zaku kai wannan nayi magana dasu . Jinjina kai kawai Khalil yayi dan shi bai saba yin magana dayawa ba. Hannu aka basu nan Suka soma tafiya kafin daga bisani suka lula sararin samaniya. Koda suka isa Maradi sakon suka bada, bayan wani lokaci aka had’a su da wasu Sojojin sai lokacin aka sanar musu da wani daji zasu je inda wasu Y’an ta’adda ke buya sukashe su. Da to suka amsa Suna Sarawa Ogan nasu kafin duk suka shiga jiragen suka lula sararin samaniya. Yak’i sosai akayi da Y’an Ta’addar nan kafin suka samu nasarar kashe su wanda basu kashe ba kuma suka kamo su suna shirin guduwa.. Sai dare kafin suka dawo Garin Niamey a matuk’ar gajiye suka iso gida. Cikin k’ank’anin lokaci A garin Niamey dama sauran karuruwa suka san da general Khalil Umar mai nasara….

Zaune suke a parlo Mamy da Baba Abdul sai Khalil, Sako yaji ya shigo wayarshi, kamar bazai dauka ba sai kuma ya duba” Da sauri ya mik’e yana fad’in Abul maza muje Oga na Kiran gaggawa ankai hari an dauke mutane, kazo muje kafin suyi nisa sun tafi da mutane. A hanzarce Abdul ya mik’e suka nufi d’aki” Masufi minti uku ba sai gasu cikin kayan Sojoji bindigogi a ko wani gefen su. Mamy tuni har ta soma hawaye ta musu Addu’a, Baba na ta ce mata tayi hakuri. Kallonshi Tayi tace Haba don Allah Yaran nan tinda suka samu aikin nan bama zaman minti talatin dasu a gidan nan sai ace zasu je Kasar Ghana gobe ace gasu ce a Agades gaskiya ni inda za’abi ta tawa da sun hak’ura da aikin nan.. Baba yayi murmishi yace Ki bar maganar ma dan Khalil bazai yarda ba. Su Khalil na fita babu inda suka zarce sai dajin dake cen bayan gari da nisa sosai” Computer dake hannun su na nuna musu inda suke Khalil nata sharara gudu. A bakin dajin suka paka motar su, suka kutsa kai ciki dajin sai bishiyoyi sai ka janye zaka ga gaban ka. Gudu sukaji a bayansu, da sauri suka juyo sai sukaga wata mata da ciki tana tunkaro su” Da sauri suka tare ta ganin ta durkushe a kasa ta rik’e cikin dake jikinta. Cikin mawuyacin hali ta d’ago tana kallon su wani mugun ciwo ne ya zo mata ba shiri ta damki Hannun Khalil ta rike gam……

 

 

_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[12/09, 12:03] MAMAN NUSAIBA CE: _*🌻ABBA NE 🌻*_

 

 

Hakkin Mallakar

_*Sarat Alk’asum (Maman Nusaiba)*_

 

_JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION_

_Littafin na kud’i ne only N 300, my WhatsApp number 👉🏻+966577675904 _

 

بسم الله الرحمن الرحيم

0️⃣2️⃣

Ta damki Hannun Khalil ta rike gam sai juya kanta take alamar haihuwa ce zatayi” Cikin Azama Abdul yace Khalil maza kayi lungu da ita haihuwa zatayi ka taimake ta. Khalil da duk ta gama bashi tausayi ya sunkuce ta ya ringa kutsawa cikin dajin dan ya samu inda zai b’oye ta” Gindin wata bishiya ya samu mai inuwa kuma inba lura kayi ba baza ka san akwai mutum a wajan ba, aje ta yayi yana huci ya kama hannayen ta yace Ki daure kinji baiwar Allah zan kaiki gidan ki .D’ago da rinannun idanunta tayi ta zuba su a kanshi tana girgiza mishi kai, cikin sarkewar murya tace” A’a kada ka mayar dani dan ba nan garin muke ba, Mijina sun bishi yayi cikin daji bansan a wani hali yake ba” Zata sake magana taji wani azababben ciwo wanda ya lumka na baya” Sake damkar hannun Khalil tayi tana salati Ganin haka yasa Khalil cire rawanin shi daya naďa a kanshi ya lulluba mata a jikin ta.. idanunshi ya rufe yana jin zuciyarshi na mugun bugawa da sauri sauri” Kamar daga sama yaji kukan Jariri ta sauri ya bud’e idanu yaga Jaririya a k’asa tana tsala kuka. Rasa yanda zaiyi da Babyn yayi shi bai san yadda ake yanke cibiya ba gashi ba wani a kusan shi. Matar ce ta sauke wani wahalallan numfashi ta bud’e idanu duk da ciwon da take ji ta kalli Khalil tace” Kana da reza ko wuka mai kaifi. Cikin rawar murya Khalil yace” Eh akwai reza yasa hannu a aljihunshi ya fito da rezar sabuwa dal ya mika mata… Amsa tayi ta mike daga durkushen da take ta dauki wannan mayafin na Khalil ta aje a gefe” Yankewa Jaririyar cibiya tayi hawaye na zirya kan kuncinta. Daukan Jaririyar tayi ta lullubeta da mayafin ta d’ago kai ta kalli Khalil wanda shima ita yake kallo. Cikin raunatacciyar murya tace Soja ga Y’ata na baka ita halak malak, ka rike min bisa amana idan ta girma kace mata Maman ta na matuk’ar k’aunarta. Na baka ita kyauta har abada ta zama Yarka daga yanzu ka amshe ta mana” Ta fad’a tana murmishi mai had’e da hawaye.. hannun Khalil na rawa ya amshi Jaririyar ya rungume ta tsam a jikin shi, nan da nan yaji k’aunar Jaririyar na ratsashi, cikin damuwa ya kalli Matar yace” Anty na miki Alk’awarin zan rik’e Yarinyar nan da amana, amma ya sunan ki? Kanta k’asa tace” Ni Sunana Zulaihat Don girman Allah ka tafi ni nasan kwanana ya k’are anan zan mutu, kuje kar su kashe min Jaririya ta.. Khalil yace No ki tashi muje duk da ina jin takun tafiyar su amma baza su ganmu ba. A’a kada kace haka Soja karka damu dani kai dai ka tseratar min da Yarinya ta hakan kad’ai zai sanyani farin ciki. Khalil zaiyi magana yaji Harbin bindiga a matuk’ar razane ya juya yaga an same ta a gefen ciki” Dafe wajan tayi tace” Don k’aunar ka da Annabin rahama ka gudu karsu kashe ka, amshi wannan idan ka zauna ka duba” Ta fad’a tana mika mishi handbag d’in ta fara sol. Amsa Khalil yayi tace” Kaje nace komai na rayuwata na ciki kacewa Y’ata ina son… Bata k’arasa ba ta zube anan” A guje Khalil ya nufi wani cikin ciyayi yayi saurin warware mayafin ya saka Jaririyar ya k’ulla a jikinshi da kyau. Sosai yake tausayin Jaririyar da take baccin wahala ya k’ara kutsa kanshi wani waje.. Abdul na cen da sauran Abokan aikin su suna ta masayar wuta da Y’an Ta’adda” Ganin Khalil bai dawo ba hankalinshi yayi matuk’ar tashi, da baya ya soma tafiya sai kuma yajiya na nufi inda Khalil yayi. Waro idanu yayi ganin jini a k’asar bishiyar amma ba kowa a wajan. Sake kutsawa yayi yana wage-waige kwaran baya sukayi da Khalil” A hanzarce kowa ya juyo ya d’ana kunamar bindigarshi sai kuma sukaga sune dai.. sauke Ajiyar zuciya sukayi Abdul yace Ina Matar nan take? Khalil na huci yace” Ta mutu kaga abinda ta haifa zan maka bayanin komai muje kawai. Cikin tashin hankali Abdul yake kallon Jaririyar dake gaban k’irjin Khalil daya Goya ta ta gaba. Juyawa sukayi suka tunkari inda suke jin motsin su. Cikin azama Khalil ya hango wani ya juya musu baya da sanda Abdul ya damkeshi ya bud’e bakinshi ya sakar mishi alburisai.. sakinshi yayi nan Y’an Ta’addan suka ankare da su aka shiga musayar wuta baji ba gani” Sosai suke yaki inda Su Khalil sukaci sa’ar kashe su. Numfashi suke saukewa Khalil zaiyi magana yaji saukar harbi a kafad’arshi ” Rintse idanu yayi cikin azama irin na Sojoji ya juyo ya harbe wanda ya harbeshi nan take ya mutu. Abdul ya tafi a guje cen ya hango Ogan nasu ya harbeshi a hannu da k’afa, nan da nan ya ringa kurma ihu mutanen dake gabanshi suka ringa kallon shi. Cikin tafasar zuciya Abdul ya wanka mishi mari lafiyayye ya damki wuyashi ya shiga dukanshi baji ba gani. Khalil a matuk’ar galabaice yake amma saboda karfi hali irin na Soja ya daure ya iso wajan su Abdul” bakinshi na rawa yace” Maza ku tashi muje kai kuma Abdul tafo mana da wannan dan iskan” Ya fad’a yana yin bol dashi.. da gudu suka ringa bin Khalil har bakin mota shima Abdul ya k’araso ya jefa shugaban Y’an Ta’addar nan a mota yasa mishi ankwa hannu da k’afa duk da a sume yake… Babu inda suka nufa sai Babbar Asibitin cikin Garin dama kafin suzo sun sanar zuwansu. Suna isowa aka ringa daukan wanda suka jikata da waďanda sukayi rauni aka shiga da su ciki dan basu taimakon gaggawa.. Khalil ya shigo ciki da k’yar yana rintse idanunshi shi ya sauke Jaririyar ya kwantar a wani gado zai yi magana yayi baya luuu ya zume anan sumamme. Abdul ya iso a guje ya ringa jijjiga shi yana fad’in” D’an Uwana kada kamin haka ka tashi ga amanar da aka baka. Wani Likita ne ya iso yasa aka daura Khalil akan gadon dake kusan inda ya aje Jaririyar.. tuni suka shiga cire mishi bulat din da yake kafad’arshi , bayan sun gama suka sanya mishi magani suka naďa mishi bandeji a wajan” allura biyu suka mishi san nan suka sanya mishi ruwa… Abdul ya koma gefe ya zauna ranshi na tafasa duk da ya kashe wanda yayiwa Khalil wannan Harbin amma ranshi bai dena suya ba. Wayarshi ya ciro jin tana ringing, ganin daga Office d’in su ne yasa shi D’agawa ya k’ara a kunne amma baice komai ba. D’aga cen b’angaren Ogansu yace” Abdul Khalil baya kusa ne? ina kiran wayar shi bata shiga, gamu nan a Asibitin da kuke ku fito. Iska Abdul ya fuszar mai tsananin zafi ya kalli Khalil dake kwance yana fitar numfashi yace” Ai shima Khalil d’in gashi nan a sume an harbeshi ne.. Cikin tashin hankali yace Subhanallahi ina ne dakin da kuke? Kwatance ya mishi san nan ya kashe kiran. Yana zaune ya dafe kanshi sai kuma ya dauki wayar ya kira Baba ya fad’a mishi halin da ake ciki” Cikin Azama yace gasu nan zuwa. Ogan Sojoji na shigowa a sauri ya isa bakin gadon da Khalil ke kwance, hannu yasa ya shafa fuskarshi yace” Jarumi na sannu Allah ya kare ka. Banko k’ofar akayi da k’arfi hakan yasa Khalil soma bud’e idanunshi. Mamy ce da Baba ta sauri ta isa ga Khalil tana kuka tace” Ka gani ko Yarona dama sai da nace maka bana son aikin nan amma ka nace gashi yanzu ana son kashe ka a banza. Dafata Baba yayi yace” Haba ki nutsu mana don Allah” Bud’e idanunshi ya ringayi tin yana ganin dushi-dushi har ya bud’e idanun shi tar akan fuskar Ogan nasu. Hamdala sukayi kowa nata mishi sannu. Zabura yayi ya sauko daga kan gadon suka rike shi, Baba yace ina zaka je? Numfashi yaja yana jin kanshi na mugun Sara mishi kamar zai rabe gida biyu, yace” Amana ta zan dauka. Kallon shi Mamy tayi da mamaki tace Amanarka kuma Khalil ? Bai bata amsa ba ya isa d’ayan gadon ya dauki Jaririyar ya rungume ta yana lumshe idanu” Sake da baki suke kallonshi, Abdul ya isa ga Khalil yace Khalil ka bawa Mamy Jaririyar a gyara ta mana. Bud’e idanunshi yayi, sai kuma yace ni zan gyara ta da kaina wannan kyautata ce. Mamy da Baba da Shugaban Sojoji na kallon shi. Cen dai Mamy ta isa inda yake tsaye tace” Kawo ta mana Khalil a sanya mata tufafi. Ba dan yaso ba ya mika mata Jaririyar ta masa da sauri. Likitan daya shiga suka bawa Jaririyar Mamy tace A gyara ta” Khalil yace muje tare” Abdul yace kaga ka bari a gyara ta ba fa guduwa za’ayi da ita ba. Ko kala baice ba yabi bayan Nurse d’in data amshi Jaririyar. Koda aka mata wanka anan suka sanya mata wasu kaya masu kyau” Amsar ta yayi ya rungume ta ya mata kiran salla a kunne san nan ya raďa mata suna. Tashi yayi ya dawo wajan su Mamy basu tsaya ba suka wuce gida…..

Suna zuwa gida Mamy ta dauko ruwan zam-zam da dabino ta bata, har yanzu Jaririyar batayi kuka ba, su kansu abun ya basu mamaki. Mamy tace” Na tura Direba ya siyo mata madara da sauran abun anfani. Khalil ya sauke wata Nannauyar ajiyar zuciya yace” Nagode Mamy nawa ne kud’in? Harara ta mishi tace D’an Y’arka ce sai ka nuna sai kai zaka mata hudima” Murmishin gefen baki yayi yana shafa kwancacciyar sumar kanshi. Direba ne ya shiga da kaya a leda manya manya, gaishe da su yayi san nan ya aje kayan ya fita. Mik’awa Khalil Jaririyar tayi ta janyo kayan ta dauko kwankwanin madara babba da komai a ciki” D’akinta ta koma ta dawo da wani kofi dauke da ruwa mai ďumi da cikin. Madarar ta kad’a tace” Kawo ta a bata. Mik’a mata Jaririyar yayi ta masa ta shiga bata, kamar jira Jaririyar take ta shiga sha. Wani sanyi Khalil yaji ganin Jaririyar tashi na shan madarar. Gyara zama yayi ya basu labarin abinda ya faru” Kuka sosai Mamy keyi tana cewa” Allah sarki yanzu shikenan sun kashe mata Uwa? Shima Uban ba tabbas yana raye. Zuciyar Khalil na tafarfasa yace” Eh amma kuma Abdul yace bai ga gawarta a gindin bishiyar ba” Baba yace” Mugaye azzalumai Alhamdulillah tinda har an kamasu , kila ko dauke gawar sukayi su jefar waya sani. Khalil dai bai sake cewa komai ba” Mamy tace” Wani suna kasa mata? Khalil da ya jinginar da kanshi jikin kujera yace” Sunanta Zulaihat amma muke kiranta da Ashma. Murmishi Mamy tayi tace Sunan da nake so Ubangiji ya raya mana Ashma. Ameen suka ce Khalil ya d’ago idanunshi da sukayi jajur kamar an ďasa mishi jini yace” Ina neman wata alfarma a gareku. Baba yace muna jinka” Inason koda Ashma ta girma kada ku tab’a ce mata bani bane na haife ta, kunga Inna bata nan ta koma Nigeria da zama” Dama itace nake tunanin zata bani matsala ta fad’a mata cewa bani bane na haifeta. Dukkansu jinjina kai sukayi Mamy tace Insha Allah babu wanda zai fad’a mata cewa ba kai ka haifeta ba” Inna kuma dama tace wai ka samo mata kaga sai kayi aure ko saboda wannan Y’ar taka. Had’e rai yayi yace” Nifa ban tab’a yin budurwa ba amma saboda Ashma nan da wani lokaci zanyi. Dukkansu dad’i sukaji shi kuma ya amshe Ashma a hannun Mamy ya shige dakinshi da ita” Baba ya bishi da kallo hawaye na zubo mishi… Koda dare yayi Mamy tace Khalil ya kawo Ashma sai yace sam bazai iyaba
, ba yadda Mamy ta iya ta koma ta kawo mishi duk abinda zasu buk’ata ta koma .

Tin daga wannan rana Khalil ne ke kula da Ashma wanka wankie kayanta goyata a baya komai shi ke mata, wani lokacin ma dariya yake basu idan yana mata wasa yake ta magana shi kad’ai. Ashma tayi wayo sosai take gane Abban nata duk wanda ya dauketa indai ba Khalil ko Mamy bane to yanzu za tayi ta tsala kuka tana Abba! Abba, shi kuwa in yana gidan da sauri yake zuwa ya amshe ta su shige daki yayi tamata
Wasa suna ta dariya… samun Ashma a wannan lokacin ba k’aramin ragewa Khalil kewar Iyayenshi yayi ba, ita kad’ai yake sakewa yayi ta dariya da ita, amma inba ita ba babu wanda zaice yana ganin fara’ar shi Koda kuwa anyi abin dariya…

Da gudu ta nufo shi tana kuka, sanye take da kayan makaranta Y’ar k’aramar Jakarta na bayanta a goye” Fitowa yayi da sauri ya tareta suna had’ewa yayi sama ta ita tukun ya rungume ta yace” Ashma na waye ya tab’a min ke? Turo dan bakin ta tayi tace” Abba Malamin mu ne ya dakeni wai nayi rètar kuma har da ce min wai ni aljana ce” Kuma yace wai Abbana mai zuciyar mugaye kuma kasan me Abba wa… Bata k’arasa ba yayi saurin sauke ta ya kama hannun ta yace” Shi d’in ne duk ya fad’a miki haka? Itama tsuke baki tayi kamar yadda taga ya had’e rai, tace” Allah Abba haka yace. Daukan yayi suka nufi ciki yana fad’in” ba dai ke ya zaga ba ya dauko ruwan dafa kanshi….

 

_*😂😂ni kuma ina ganin ran Soja ya b’aci na had’a kan takarduna na arce garin mu😂*_

 

Littafin na kud’i ne only N 300 ne duk mai son karantawa ga number na👉🏻 +966577675904

 

 

_*Taku har kullum Maman Nusaiba*_
[12/09, 12:03] MAMAN NUSAIBA CE: _*🌻ABBA NE 🌻*_

 

 

 

Hakkin Mallakar

_*Sarat Alk’asum (Maman Nusaiba)*_

_JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION_

_*Littafin na kud’i ne only N 300 ne masu son labarin sai ku tuntubeni ta WhatsApp number na 👉🏻+966599791573*_

بسم الله الرحمن الرحيم

0️⃣4️⃣

 

D’ago da rinannun idanunshi yayi ya sauke su akan Abdul yace” Wai an tsinci Gawar Alhaji Buba a bayan Gidanshi tare da Matarshi da D’anshi Y’arshi ita kad’ai ce ta tsira , itama sun bata guba amma tana Asibiti. Cikin razana Abdul ya ringa fad’in” Innalillahi wa inna ilaihin raju’un To waye ya kashe su? Khalil shuru yayi yana kallon Abdul kamar yadda shima yake kallon shi” nisawa yayi yace” Gaskiya ina zargin Abokan shi. Da sauri Abdul ya kalleshi baki na rawa yace Kana ganin a yadda suke har zasu iya cin amanar shi? Guntun murmishi Khalil yayi sai kuma ya tsuke fuska kamar bai tab’a yin dariya ba, cikin kakkausar murya yace” Abdul kaima fa wani lokacin kamar mahaukaci kake, Waye ya gaya maka Aboki baya cin amanar Abokinshi? Girgiza kai Abdul yayi yace” A’a ai abun ne da rudewa Gaskiya indai har su suka kashe shi. Mik’ewa Khalil yayi yace kaje ka shirya yi sauri nima yanzu zan fito” Abdul ya nufi k’ofa yana fad’in Ok zan jiraka a mota, daga haka ya fita… Zama Khalil yayi ya dafe kanshi abubuwa da dama yake ta kissimawa a zuciyarshi, huci yayi ya mik’e ya kaiwa bangon dakin naushi har sai da Y’an yatsun shi sukayi k’ara, yace” No Idan kuka shigo hannuna zaku gwammace dama baku zo Duniya ba” Wallahi saina kashe ku da hannuna kamar yadda kukayi dalilin tarwatsa min farin cikin rayuwata” Wasu zafafan hawaye ne ke zarya kan kuncin Khalil da sauri ya janyo photon Su Abba wanda aka musu su uku” Rungume photon yayi yana kuka mai Zuma zuciyar mai karatu, sai cewa yake” Abbana Umma na zan rama abinda aka muku, nayi Alk’awari sai na kashe wanda sukayi dalilin tafiyarku lahira. Haka yake ta sunbatu yana kuka kamar karamin Yaro. Da sauri ya goge hawayen shi jin Ashma na fad’in” Abba! Abba! Mik’ewa yayi ya dauko ta daga kan gadon ya sauke ta k’asa.. tsura mishi idanu tayi ganin idanunshi sunyi ja tace” Abba ciwon ido kake? Murmishi ya mata yace” Eh zanje na dawo anjima zan kaiki wajan wasa kinji maza jeki wajan Mamy. Da sauri ta fita tana murna jin ance za’a kaita wajan wasa” Yana ganin fitar ta yayi saurin canja kaya ya sanya kakin shi ya dauki duk abinda zai dauka ya fito. Baba ya samu a parlo ya mishi Allah tsare tukun ya fita” Abdul ya watsa mishi harara” Murmishi yayi dan yasan kwanan zancen. Shiga sukayi ba b’ata lokaci suka nufi gidan Alhaji Buba…. Hisham na zaune a bakin gado wata Y’ar k’aramar Yarinyar da baza ta wuce shekara 16 ba ce kwance tana kuka abinta” Murmishi yayi ya kai hannu ya tab’a wiyanta” A razane ta d’ago sai tayi tozali da Hisham, juya mishi baya tayi cikin sautin kuka tace” Ni ba ruwana da kai ma. Dariya yayi ya d’ago ta yana fad’in” Am so sorry my Daughter aikin gaggawa ne ya sameni shiyasa. Dena kukan tayi ta d’ago tana kallon shi, cikin damuwa tace” Abie ko operation kayi ne? Jinjina mata kai yayi alamar eh. Rungume shi tayi tace” Abie kasan me? Dafe kai yayi yace A’a yanzu dai ki bar labarin ki muje kiyi wanka nima nayi sai muci abinci, daga nan sai ki bani labarin” Cike da murna ta sauka a jikinshi ta kama hannun shi suka fito.. Ammi dake zaune baki ta saki tana kallon su , sai kuma ta tab’e baki tace” Aikin banza futsararru ni dama inta nice sai dai ki kwana a haka, ni zaki nunawa Mahaifi nima ba daga sama na fado ba.. Rufaida ta iso gaban Ammi ta mata kiss san nan tace To ai Abie na yazo shikenan ni dama ba ruwana dake” tsaki Ammi taja tace Cen da tsiyar ku karku ma kuskura ku shigo min parlo, inba haka ba nabar muku gidan na fita waje na zauna. Dariya sukayi a tare Hisham yace” Yi hak’uri Ammi na. Kallonta ta maida ga TV ganin photon da ake haskowa yasa tace” Kai Hisham zo kaga mai kama dakai. Hisham yace ki bari na dawo dama kince ai kinga mai kama dani idan mun fito sai ki nuna min…. Khalil har sun kusan zuwa Gidan Alhaji Buba Ogan su ya kira su yace su dawo kes d’in ya koma hannun Y’an Sanda” Rai ba dad’i suka nufi Office d’in.. A office suka samu Ogan nasu yana ta safa da marwar yana ganin su yace” Yauwa dama ku nake jira. Zama sukayi suna kallon Ogan nasu ” Gyara zama yayi yace” Kun ga abinda ya faru duka saura minti nawa aje kamoshi amma sai aka samu wasu suka kashe shi.. cikin tafasar zuciya Khalil yace” Nifa Gaskiya ba wanda nake zargi sai Abokan sana’ar shi, ta yadda zaku yi duba ga yadda suke gudanar da kasuwancin su, shi Alhaji Buba shine Yaron su zai shigo da kaya k’asar nan san nan suzo su amsa ko yakai musu” Abinda nake tunani ko sun samu matsala ne da su ko kun manta binciken da mukayi wannan satin Alhaji Buba ya shigo da kaya” Amma abin mamaki bai siyarwa da su Abokan kasuwancin nashi ba, Tabbas akwai abinda ya faru tsakanin su jiya nayi bincike an Tabbatar min da wani abu ne ya shiga tsakanin.. Jin wayarshi sako ya shigo ne yasa yayi saurin dubawa” Wani k’ayataccen murmishi yayi yace To kunga abinda nake fad’a ko sab’ani suka samu shine yace zai tona musu asiri tinda baza su bashi kud’in shi ba idan sun amshi kaya” Shiyasa cikin dare suka sanya aka kashe shi” Ya karashe maganar yana nunawa Ogan nasu sakon da aka turo mishi… Abdul ya Jinjina kai shi wani lokacin ma Khalil tsoro yake bashi, idan yace abu kazane to hakan ne.. amsa duk sukayi suna karanta sakon” Ajiyar zuciya Ogan su ya sauke yace” To yanzu taya zamu kama su da lefin ne? Kun san dai mutanen nan sun iya takunsu” A fusace Khalil yace” Ko me suke wata rana da kaina zan kamasu, kuma in wuni sukayi suna tafi ni a tafe na kwana Insha Allah sai Alhaji Mati da Alhaji Kabeer da kuma babban dan iskan Shugaban nasu wato Alhaji Sammani duk nine nan zan kashe su da hannuna” Ya fad’a yana dakar k’irjin shi.. dukkansu idanu suka zuba mishi ganin yadda jijiyoyin kanshi suka tashi alamar yakai makura a b’acin rai.. tattaunawa sukayi sosai akan lamarin duk da yanzu kes din baya hannnun su yana hannun Y’an Sanda. Sai kusan la’asar kowa ya shiga Office d’in shi….

Zaune suke a wani tanfatsetsen parlo babba, gaban su an baje musu Abinci kala kala da kayan marmari” Wani daga cikin su ne ya kwashe da dariya yace Su Buba ana cen an bakunci lahira. Wanda yake gefen shi yace ” kwarai kuwa sun dauka mu din wasa ne shi har ya isa ya fallasa sirrin mu ya rayu a Duniya. Dariya suka sanya Alhaji Sammani yace” Nifa baku san abinda yake damuna ba. Duk kallon shi sukayi a tare suka furta” ranka ya dad’e kai yanzu har akwai abinda zai dameka a Duniyar nan? Murmishi yayi yace Eh mana Wannan dan iskan Sojan shine yanzu damuwata, ko kun manta dan gidan Umar mai Nasara ne? Jinjina kai sukayi. Alhaji Mati yace” Ai kawai kabar komai a hannun mu zamu sa a kashe shi daga shi har sauran ahalin nashi da suka rage” Alhaji Kabeer yace Yaro yarone shima ya kusa tafiya inda ba’a dawowa, dariya suka sanya” Alhaji Sammani yace’ Shine fa yasa aka kori Mansoor a wajan aiki wai dan ya zane wannan Y’ar tashi. Waro idanu Alhaji Kabeer yayi yace” Mansoor fa kace Ranka ya dade? Lalle bai san waye Mansoor ba” Hmmm ka rabu da dan iska mana shi fa gani yake ba wani wanda ya isa dashi a k’asar nan tinda ya kai matakin general, ai inya san wata bai san wata ba zamu biyo mishi ta baya gida.
Haka sukaci gaba da hira akan yadda zasu kashe General Khalil Umar mai Nasara da sauran dangin nashi wato su Baba….

Da sauri ta fito tana fad’in”
Abie! Abie!! Ina kake maza fito ka gani Wallahi na ganshi fito ka gani kar a wuce Abie” Ta fad’a tana sanyo kai cikin d’akin shi. Kwance ta sameshi yana bacci da hanzari ta hau kan gadon ta shiga jijjiga shi tana kiran sunan shi” Bud’e idanunshi yayi da suke cike da bacci ya sauke su akan Fuskarta yayinda itama shi take kallo tana dariya. Tashi yayi yana dafe kanshi dake mugun sara mishi yace” Ke wai yaushe zakiyi hankali? Turo baki tayi tana kallon shi, kwafa yayi ya lumshe idanun shi gashi ta katse mishi bacci shi kuma dabi’arshi ce indai ya fara bacci aka tashe shi to bazai sake komawa ba ko da kuwa da dare ne a zaune zai kwana, shiyasa idan ya kwanta Ammi take hana Rufaida zuwa wajanshi. Numfashi yaja yace” Menene ya kawo ki. Gyara zama tayi ta dauko wayarta ta shiga Instagram sai ga photo ya bayyana cikin zakuwa tace” Abie ka ganshi wanda nake fad’a maka kuna kama kuma ma Soja ne ka gani” Ta fad’a tana daura mishi wayar akan cinyarshi. Dauka yayi yana yatsina fuska” Da sauri ya zabura yana bin picture d’in da kallo, Cikin rawar murya yace” Wa… wanene shi wannan d’in? Rufaida tace” A Instagram na ganshi kuma ba dan nan k’asar bane ka ganshi ka shiga ka duba har da wata Y’ar K’aramar Yarinya Y’arshi ce nake tunani.. cikin kaduwa da Al’ajabi Hisham ya gyara zama hannu na rawa ya shiga account d’in shi sai yaga an goge komai a cikin account din sai picture din Yarinyar fuskarta dauke da murmishi, guda d’aya. D’agowa yayi yana kallon ta yace” Ai babu komai amma dan wata k’asa ne shi? Gaskiya Abie ban duba ba wani lokaci ne ina shiga na ga videon shi tare da Yarinyar yana daura mata dan kwali, wayar sai ta rufe to ban kuma gani ba sai yanzu shine nace bari na nuna ma kuna mugun kama ko? Ta fad’a tana daura kanta a kafad’arshi. Hisham dai kurawa pictures d’in ido yayi kamar dai shi yake gani a pictures din, sai kuma yayi screen shot d’in picture d’in ya tura zuwa wayarshi. Mik’a mata wayar yayi yace” Gashi kisa a caji yanzu dai kin hanani nayi bacci ko? Maza je ki shirya mu fita waje” Rungume shi tayi tana fad’in” Wow surprise Abie kamin ko? Murmishi kawai yayi ya cire ta a jikinshi ya shige toilet. Ita kuwa Rufaida sosai take mamakin yadda wannan Sojan yake kama da Abie din ta, mik’ewa tayi ta fita zuwa d’akin ta… Khalil na zaune shida Abdul a wani restaurant hira suke jefi jefi” Abdul yace” Uban Ashma Ikon Allah wai kai nan wata rana Suruki zaka dauka? Dukan wasa yakai mishi ya kauce yana dariya” Khalil yace” Kai yanzu kana ganin abu mai sauki ne rabani da princess? Ai banga ranar ba gaskiya idan har kuwa na ganta to bazan kwana ba a lokacin ina numfashi. Dariya Abdul yayi yace” Mu dai mun shiga uku da kai to idan kayi aure ai zaku dena kwana tare da ita, naga yanzu girma take sai ku raba wajan kwana” Wani kallo ya watsa mishi yana jan tsaki yace” Kai fa mugun dan sa’ido ne ko? To ai sai ka hana muke kwana tare. Abdul ya d’ago zaiyi magana sai yaga wata Mace na tinkaro su” Tana isowa tace Hello. Khalil bai d’ago ba kuma bai amsa ba sai Abdul ne yace Hey, zama tayi fuskarta dauke da murmishi tace” Abban Ashma dama ana ganin kyauta? Da sauri ya d’ago kanshi jin zazzakar muryarta, waro idanu yayi yace” A’a Madam kece sannu fa” Murmishi tayi tace” Yauwa ina Ma chérie take? Oh princess tana gida yau banzo da ita ba” Cewar Khalil yana kallon ta da kyau. Sunkuyar da kanta tayi ta mik’a mishi wata leda baka tace” To akai mata dama ita na siyawa idan taje Ècole na bata, tinda gaku sai akai mata kace ina gaishe ta” Ta fad’a tana murmishi.. Shima Khalil murmishin yayi sosai yaji nutsuwar Yarinyar ta burgeshi” Kallon ta yayi yace” Nace ba ya sunanki? na manta fa.
A sanyaye tace” Sanjina sunana” Abdul ya saki baki yana kallon ta har zata juya sai yayi saurin fad’in baki ji ba. Dawowa tayi ta zauna tana fuskartar Abdul ta d’ago da fararen idanun ta ta sauke su akanshi. Abdul yace” Nace ba ki hak’uri zan miki wata tambaya idan ba damuwa” Girgiza kai tayi tace” ba komai ina jinka. Wai don Allah ke Musulma ce kuwa? Kiyi hak’uri fa naji sunan naki ne kamar bana Musulmai ba” Murmishi tayi tace” A’a ni ba Musulma bace ba. Da sauri Khalil ya kalle ta bakin shi na rawa yace” Ai kuwa ba wanda zai kalle ki yace ke ba Musulma bace yadda kike rufe jikin ki ko wata Musulmar bata yi. Kanta a kasa tace” Ni ba zan iya irin wannan shigar ba gaskiya duk bana jin dad’i shiyasa Nake rufe jikina. Khalil d’aya tsura mata idanu ya saki murmishi yace” Gaskiya hakan shine dai-dai, dan ke ba Musulma bace hakan bazai sa kike bud’e surar jikin ki ga kowa ba, kici gaba da kare mutumcin ki” Jin kai tayi tace” Hakane ranka ya dad’e na gode sosai bari naje gida yamma tayi. Khalil ya mik’e ya dawo kusan ta yace” Bani number ki idan naje gida sai na kira ki kuyi magana da Princess. Cike da matsanancin farin ciki Sanjina ta kalleshi hannun ta na rawa tasa mishi number ta,sai da ta kira taga ta shiga tukun ta musu sallama ta tafi… Abdul ya iso inda yake yace” Kai Oga ko dai ka kyasa? Tsaki Khalil yayi sai kuma yayi murmishi yana shafa kwantaccen sajen shi ya koma ya zauna.. mai kawo abinci ne ya kawo musu lemon guda biyu ya ake musu ” Khalil ya dauki nashi ya shanye tass san nan ya kalli Abdul da yake danna waya yace” Ko baza kasha ba? Girgiza kai yayi yace no na koshi tashi muje gida. Mikewa sukayi a tare sai da Khalil ya biya kud’in abincin da sukayi san nan suka nufi motorsu” Tin kafin suyi nisa Khalil yake jin cikinshi na murdawa, daurewa yayi ya kwantar da kanshi jikin kujera idanun shi a lumshe. Da k’yar Khalil yake gani cikin shi ya tsanan ta ciwo ,da sauri Abdul yayo packing Khalil ya bud’e ya fito da sauri ya nufi ciki numfashin na neman sarkewa, da haka ya shigo falon” Da sauri Mamy ta fito ganin Khalil ne tace” Sannu da zuwa. Jinjina mata kai kawai yayi ya nufi dakinshi, tin kafin ya isa a bakin k’ofar ya yanke jiki ya fad’i” A matuk’ar firgice Mamy tayo kanshi tana salati ta shiga jijjiga shi tana fad’in Kahlil! Khalil!! Ahma data fito da gudu jin ana kiran Abban nata dama shi take jira yazo” A guje ta k’araso inda yake kwance tace ABBA! …

 

Leave a Comment