ZUBAR RUWAN NONO ALHALIN BABU CIKIN BABU GOYO (HYPERPROLACTINEMIA)
Nayi wannan rubutun a matsayin bayarda amsa ga tambayar wata member. Amma naga ya dace in fitarda shi a matsayin post, kamar haka:
Hakika matsalar zubar ruwan nono alhalin babu ciki kuma babu goyo tana matukar damun matanmu a yau. Babban abinda wannan matsalar take haifarwa shine hana mace samun juna biyu. Na tabbata mata da yawa a cikin group dinnan wadanda suke da matsalar rashin haihuwa, wacce ta shafi lafiyarsu, sunada wannan matsalar.
Idan mace taga ruwan nono yana zubo mata kuma babu ciki ko goyo, to, tana da matsalar hauhawar sinadarin prolactin ne a jikinta, wanda ake kira “hyperprolactinemia” a likitance. Akwai matsalolin lafiya masu yawa wadanda suke haddasa shi, kamar:
1. Ciwon sankara na jakar pituitary (prolactinoma). Jakar a karkashin kwakwalwa take kuma ita ce take samarda muhimman sinadaran sarrafa ayyukan jiki.
2. Rashin yin ayyukan jakar hypothalamus yadda ya kamata (hypothalamic dysfunction). Ita jakar tana cikin kwakwalwa ne, kuma ita be cibiyar daidaita ayyukan jiki (body functions coordinating center).
3. Karancin sinadarin thyroid a cikin jiki (hypothyroidism). Shima wannan sinadarin yana da muhimmanci wajen sarrafa ayyukan jiki da girman jiki.
4. Laulayin amfani da magunguna (medication side effects).
5. Ciwon koda na lokaci mai tsawo (chronic kidney disease).
Ana magance matsalar zubar ruwan nono ne bisa la’akari da abubuwan da suke haddasa shi. Idan ciwon sankarar jakar pituitary ce, to, babban maganinsa shine yin amfani da rukunin magungunan ciwon laka wadanda ake kiransu a jimlace “dopamine”. Bromicriptine da cabergoline suna cikinsu, domin tasirinsu wajen motse sankarar da kuma tsayar da zubar ruwan nonon.
Mai yiwuwa ne idan likita ya dora mace akan magungunan tsayar da zubar ruwan nono yaga an dauki tsawon lokaci bai tsaya ba. To, sai tayi hakuri ta cigaba da bin umurnin likitan. Amma idan duk magungunan da aka dorata akansu basuyi tasirin da ake bukata ba, zabin da ya rage ga likita yayi amfani dasu sune:
1. Kara yawan magungunan da ya dorata akansu (dosage adjustment). Misali, idan da yace tasha 2.5 mg (kwaya daya) na bromicriptine ne, to yanzu yana iya cewa tasha 5 mg (kwaya biyu). Dalili shine yana yiwuwa kwayoyin cuta (pathogens) wadanda suka haddasa ciwon 2.5 mg bazai iya yin tasiri akansu ba sai an kara zuwa 5 mg. Ko kuma ya kara mata adadin lokacin shan maganin. Misali, idan da yace tasha sau daya ne a rana, to, yanzu yana iya cewa tasha sau biyu a rana.
2. Canza mata maganin (switching medications). Akwai magunguna masu yawa wadanda akeyin amfani dasu wajen magance matsalar zubar ruwan nono, kuma tsarin aikinsu (line of action) yana bambanta. Domin haka, likitan zai iya canzawa mace maganin wanda yake da tsarin aiki na daman. Zai yiwu a dace.
3. Yin hadakar magunguna (combining drugs), ta hanyar gwamutsa magunguna wadanda tsarin aikinsu daban. Misali, likita yana iya hadawa da magungunan ciwon nono na matan da suka kai shekarun daina al’ada (menopause) wadanda ake kira “aromatase inhibitors”, kamar letrozol.
4. Yin tiyata (surgery) domin cire karin da ya haddasa cutar zubar ruwan nonon. Amma wannan shine matakin karshe, domin ba’a yinsa sai dukkan magunguna sun gagara.
5. Yin amfani da haske (radiosurgery) a haska kwayoyin cutar da suke haddasa ciwon domin a kashe su.
6. Likita ya shawarci mace da ta canza tsarin rayuwarta, ta hanyar daina yawan motsa kan nononta (nipple stimulation) ko dai ita dakanta ko kuma lokacin mu’amalar aure. Sa’annan ta kaucewa cin kayayyakin da zasu sanya ta kiba kamar kayan zaki, da maiko, da kayan gwangwani, da sauransu.

Leave a Comment