01
*©Sameena Aleeyou…✍🏾*
_👑Queen Samy Novels Forum….📖📚_
*Dedicated to all Victims of Rape, never give up, fight for your right, this is not something to be ashamed of your self. Make the guilty ones feel ashamed of themselves* 🙌🏾🙌🏾🙌🏾🙌🏾🙌🏾
“Garin Dukku jihar Gombe, gari ne wanda akasarin mutanen dake zaune wajen fulbe ne, ma’ana fulani ne. Ni Sameena tafe nake cikin garin ina bin tsarin garin da kallo yayinda zuciyata ta cika da nishad’i. Can na hangi wata matashiyar budurwa wacce ak’alla bazata gaza shekaru goma sha shida 16 a duniya ba. Daga yanayin halittarta zaka fahimci cewa bafulatana ce ta usul. Bata da matsanancin tsayi snn bata a layin gajeru, farinta irin mai d’auke idon nan ne don saida ta matso kusa sosai na fahimci hakan. Yanayin suturan dake jikinta zai tabbatar maka iyayenta talakawa ne sosai. Silipas din dake k’afufunta kuwa duk ya b’ule yaji jiki.
“Sauri take tamkar mai shirin tashi sama, yanayin tsoro da firgici da ya wanzu a fuskarta zai tabbatar maka cikin matsanancin tashin hankali take. Kaman ta zunduma a guje haka take tafiyar, Yar da d’an karan dake hannunta tayi ta soma sassarfa hadi da gudu gudu sakamakon jiyo muryar dake sata firgici koda a mafarkinta ne tana k’walla mata kira har waje ake jiyowa,. *ZUBAIDAH! ZUBAIDAH, ZUBAIDAH!!!
“Ni kuwa Queen Samy nace ” Bari na bi wann yarinya na rubuto wa d’inbin masoyana labarinta mai cikeda tausayi, Al’ajabi da kuma ban mamaki had’i da darrusa masu girgiza zukata.
“Dan ubanki sai yanzu kika daman dawowa daga karuwancin naki? Macen dake tsaye tsakar gidan rik ‘e da guga ta fad ‘ tana watsa wa Zubaida mugun kallo me nuni da cewa zaki yaba wa aya zak’inta.
“Bakinta na rawa take fad ‘in Yaya Hadiza wllhi ban sami Yayan a kasuwa bane shine na k’arasa bakin tasha….. Ai bata gama cewa tasaha ba Yaya Hadiza ta jefa mata gugan dake hannunta ji kake tum ya fad ‘I a tsakar kanta.
“Durk’usawa Zubaidah tayi tana rik’e da tsakar kanta hawaye na zuba bisa k’uncinta.
Hadiza ta k’araso gamida mak’urota tana fad’in” Dan ubanki ni na aikeki bakin tasha, wani munafurcin ne ya kaiki bakin tasha, auho kice mun karuwanci kika tafi, shegiya Me suffan mayu da aljanai. Rankwashin da ta sake mata a tsakar ka yasa Zubaidah sakin k’ara sabida azaban dataji.
“Hadiza ta shiga janta a k’asa tana fad’in” Au kuka ma zakiyi shegiya munafuka saikace wacce na bugeki toh bari kiga na tapkeki sosai sai kiyi mai dalili.
“Duk kukan da Zubaidah take tana rok ‘on Hadiza tayi hak ‘uri ko gizau bata fasa jibgangta ba kaman Allah ne ya aikota.
“Inna Furera mak’ociyarsu ce ta shigo a guje don ceton Zubaidah dama mak’ota sun saba shigowa kawo mata d’auki, tunda Hadiza ta tsefe ido taci mutuncinsu tsaf suka daina, saiko Inna Furera ce kawai bata fasa ba.
“Da sauri tayi tsalle ta kwace Itacen da Hadiza ke jibgan Zubaidah dashi, dama Jadiza irin ingarman matan nanne.
“Ta shige tsakani tana fad’in” Haba, haba Hadiza, anya kina kuwa tuna mutuwa, kullum sai ki kama wann ‘yar marainiya kita jibga ke ko tsoron kamuwar Allah bakya yi. Cewar Inna Furera .
“Galala take Kallon Inna Fure kafin ta gyara tsayuwa ta soma fad’in” Fure! Fure!! Fure!!? Billahilazim hawainiyarki ta kiyayi ramata, banda munafunci irin taki ina ruwanki da ita, ci kike bata ko sha, cikin biyu babu d’aya. Toh wllhi wllhi ki fice a idanu na.
“Inna Fure tai murmushin takaici kafin tace ” Lokaci ne, da zaran lokacin da Zubaidah zata sami kulawata yazo zata samu kuma ke baki isa kiyi komai ba.
“Shewa Hadiza ta kwashe dashi kafin tace ” Ai dama nasan wajen munafukin wann d’an naki me matse yaran mutane a lungu take zuwa, bacin haka babu abinda zai kaita bakin tasha, Toh wllhi idan ni Hadiza ina numfashi Zubaidah bazata auri Ummaru dreban tanka ba. Ke na tak’sita maki zance Zubaidaha bazata tan’s aure a rayuwarta ba, makarantar data samu na bari tayi ya isheta, amma aure kam saidai tayitaji k’annen bayanta suna tafiya d’akin miji amma banda ita, tunda dama sa ‘anninta Sun k’are k’annenma sun kusa k’arewa. Ta juyo ta narkawa Zubaidah da har lokacin kukan zuci take hawaye na bin k’umcinta tace ” Ke kuma bak’ar munafuka ki tashi ki min wanke wanke kafin ki d’aura sanwa don yau islamiyar ma ba zuwanta zakiyi ba. Daga haka ta wuce d’aki fuuu kamar me shirin tashi sama.
“Inna Fure ta girgiza kai ta k’arasa ga Zibaidah wacce ke faman mik’ewa da k’yar sabida raunin da Hadiza taji mata da itace, tsugunawa Inna Fure tayi tausayin yarinyar ya cika zuciyarta, a hankali tasa hannu ta goge k’wallan da ya zubo mata. Hannu tasa ta shiga sunce d’aurin da Hadiza tai ma Zubaidah da igiyan guga.
“Suna had’a ido Zubaida taji wani sabon kuka na shirin kufce mata, ……..
[1/23, 22:07] +234 803 619 0581: 😭😭😭ZUBAIDAH😭😭😭
02
*©Sameena Aleeyou… ✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum…. 📖📚_
*Dedicated to all victims of rape, never keep silence, keep fighting for your right, this is not something to be ashamed of your self, let the guilty ones feel ashamed of themselves*🙌🏾🙌🏾🙌🏾🙌🏾
“Murya na rawa Zubaidah take fad ‘in” Inna meyasa iyayenmu suka mutu suka barni dagani sai yaya na, meyasa Yaya na ya kasance haka, meyasa bai zama kaman ko wani d’an Adam ba…… ” Tausayin kalamanta sun cika zuciyar Inna Fure, a hankali ta kwance bakin zaninta ta goge wa Zubaidah hawayen dake kwaranya a fuskarta. Hannayenta ta rik ‘e suna fuskantar juna kafin ta soma fad ‘in” Zubaidah kar ki bijire wa ubangijin ki, kar ki bari shedan ya rinjayi zuciyarki, har yake kawo maki ire iren wad’an nan tunani. Mutuwa dole ce kan ko wani mahaluk’i, snn kasancewar yayanki cikin mutane marrasa k’oshin lafiyan k’wak’walwa jarabawace daga Allah, wanda kema jarabawar ya shafeki. Shi kansa Habibu baijin dadin abinda Hadiza ke maki, amma babu yanda ya iya, bazai iya k’watan ‘yancin kansa ba balle naki daga hannun Hadiza, hak’uri shine zakici gaba da yi.
“Goge hawayen tayi kafin ta furta a hankali ” Kenan shikenan ni bazan tab’a jin dad’in rayuwa ba kenn, bazan rayu kaman yanda ko wani d’an adam yake rayuwa cikin ‘yanci ba. ….”Kasa jure saurarenta Inna Fure tayi sabida tausayi, mik ‘ewa tayi kafin tace “Tashi ki soma ayyukanki kafin ta fito ta sameki. Jiki a sanyaye Zubaidah ta mik ‘e daidai lokacin ” Kamalu d’an Yaya Hadiza ya fito cikin shirin tafiya islamiya fuskarsa da alamun bacci ya tashi, yaro d’an shekaru bakwai a duniya. Rungume Zubaidah ya k’araso yayi yana mata magiyan ta shirya su tafi islamiya, itama rungumesa tayi tana k’k’arin lalumo k’aryar da zata shata masa, don tasan yau kam babu ita babu islamiya. Inna Fure ta fice tana sak’sak’en lamarin Zubaidah a zuciyarta.
“Kamalu ya lura da hawayen dake bisa fuskan Zubaidah, Ya kalli gwiwar hannunta yaga jini, shiru yayi kaman bazaice komai ba kafin yace ” Na sani yauma Umma tace ta dakeki ta hanaki zuwa makaranta ko Anty. Kame kame Zubaidah ta soma yi don yaron akwaishi da wayo da kaifin basira, daidai nan Yaya Habibu yayi sallama ya shigo cikin yanayin tafiyarsa na sokaye _Phsycos_ da maganansu.
Kamalu ne kawai ya tafi ya masa oyoyo Zubaidah kam wucewa tayi bakin rijiya don taran ruwan wanke wanke, tabbas tasan Yaya Habibu ya ganta a haka toh fah haka zai wuni yana kuka.
“Inna Fure tana shiga gida ta tarar da Umar dawowarsa kenan. Koda ya gaisheta sama sama ta amsa, Umar ya lura da yanayinta, don ko tambayarsa ko yaci abinci batayi ba, kaman yanda take a kullum. don haka zama yayi bisa gefen tabarman da take zaune ” Sadda murya yayi kafin yace Innata meke faruwa ya tambaya yana kallon Inna Fure. Sauk ‘e ajiyan zuciya tayi kafin ta soma fad’in” Umar shin da gaske kake son Zubaidah.
“Kallon mamaki yayiwa mahaifiyar tasa kafin yace “Haba Inna wann wace irin tambaya ne, Kowa ya sani duk fad ‘in garin nan Zubaidah kadai nake so, nake burin mallaka, bansan meyasa Zubaidah tak’i barina na kai tambaya gidansu ba. Don wllhi Inna na k’agu na rabata da wann muguwar matan yayan nata.
“Inna ta sauk ‘e ajiyan zuciya kafin tace ” A gaskiya Hadiza bata da imani Ummaru……. “Ganin yanayinta yasa mik ‘ewa zuciyarsa na bugawa yake fad’in” Inna ki fad ‘a mun me tayi mata, ta kuma dukanta kaman yanda ta saba ko..
“Gjrgiza kai Inna ta soma tana fad’in a’a Umar don Allah ka zauna, zauna nace ba dukanta tayi ba, kawai dai so nake ayi maganar aurenku, da zaran malam ya dawo zan masa batun insha Allah, take farin ciki ya mamaye zuciyarsa nan ya shagala da zancen……Inna ta bisa da ido yanda yake murna kaman an masa alk’awarin hajji, gwara da ta kawo masa wnn zancen don tasan kalan zuciyar d’anta yanzu sai yaje yayi ma Hadiza kaca kaca.
**********************
*Abuja, Maitama*
“Wasu tagwayen gidaje na hango masu d’an karen kyau, exactly babu abinda ya raba da na gefe, komai iri guda. Wadan nan gidaje gidajen Yaya ne da kuma k’ani, Alhaji Kasim Dasuki shine Babba, yayinda Alhj Jamil Dasuki shine k’ani. Alhj Kasim da k’aninsa sunyi kaurin suna wajen hold’an kasuwanci ta yanda k’asashen duniya da dama suke hold’a dasu, tareda shahararriyar Company dinsu mai suna *Dasuki Holders*, Ko wannensu Allah Ya albarkacesa da yaro namiji k’wara dad’d’daya,.
SALIM KASIM DASUKI, da kuma LABIB KASIM DASUKI, tsakanin Salim da Labib shekara gudane cal, haka nan yaran suka taso cikin sangarci da rashin tarbiya, saboda so da iyayensu ke nuna masu, wanda a nasu tunanin gata ne. Babu mai taba masu ‘Ya’ya Ya zauna lafiya sai sun ga k’arshensa, musamman Alhj Kasim shi yafi k’aninsa bak’in zuciya, wani sa’in Alhj Jamil dinne ke nusar dashi hanya. Haka zai balbalesa tsaf da masifa, uwa uba WA’azin da Alhj Jamil ke masa kan su guje dukiyar haramun cikin kasuwamcinsu, wann dalili Ya soma sakawa Alhj Kasim tsanar Dan’uwarsa har yake tunanin tabbas zasu iya samun sab’ani koma takaisu ga raba dukiyarasu.
[1/23, 22:07] +234 803 619 0581: 😭🙍🏻ZUBAIDAH🙍🏻😭
03
*©Sameena Aleeyou…✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum..📖📚_
*Dedicated to all victims of rape, never keep silence, fight for your right,… This is not something to be ashamed of your self, let the guilty ones feel ashamed of themselves 🙌🏾🙌🏾🙌🏾🙌🏾*
“Salim ne kwance saman coach a bakin pool dake a cikin gidansu, da gani daga ruwan ya fito don daga shi sai gajeren wando. Idonsa manne da bak’in sunshade ya k’ura wa rana ido, gefe dashi k’aramar table ne wanda wayoyinsa ne da kuma Chapman akai.
“A hankali ya kai hannunsa kan table din gamida daukar d’aya daga cikin wayoyin nasa nan ya shiga dialling lambar budurwarsa KAUSAR wacce ake batun saka masu rana. Sosai suke hiran soyayya daga ji kasan suna tsananin son junansu.
“Daga can bayansa yanda Labeeb ke tsaye ya k’urawa cousin d’in nasa ido, shakka babu su duka biyu sunyi tarayya wajen son mace guda, zuciyarsa yaci gaba da tafarfasa, da sauri ya juya ba tareda yayiwa d’an uwan nasa magana ba.
“KAUSAR TAHIR MARAFA, shine asalin sunanta, mahaifin Kausar abokin kasuwancin iyayen Labeeb da Salim ne, musamman Mahaifin Salim Alhj Kasim Dasuki, Shima Alhj Tahir Marafa dan asalin garin Dukku ne, Kausar basu jima da dawowa Nigeria ba daga k’asar Holland dalilin dawowarsu ma sabida neman muk’akin kujeran Shugaban k’asa da mahifinta zai fara ne, farkon dawowarsu sabo mai tsanani ya shiga tsakaninta da Labeeb a lokacin Salim yana can Scotland yana k’arasa wani course dinsa shi, koda Salim ya dawo Labeeb shi yayi masa introducing Kausar, tunda Kausar da Salim suka k’yalla ido akan juna soyayya mai tsanani ta shige tsakaninsu, toh fah run daga wann lokaci Labeeb ya rasa sukuni, a ganinsa cin amana ce wnn k’wace Salim yayi masa.
“Iyayensu gaba d’aya sunyi farin cikin wann Al’amari tun basu hadasu ba gashi sun hada kansu, babu kaman Alhj Kasim Dasuki wanda dama shi Money hungry, baya rab’an mutum sai zai sami alkhairi. Dukda tarin dukiyar da yake dashi baya hanasa hangar na wani. Yasan muddin tilon d’ansa Salim ya auri tilon ‘yar Alhj Marafa wataran zasu mallaki gaba d’aya dukiyar Alhj Marafa.
“JALAL! Na’am Anna ya amsa gamida ajiye takalmimsa da yake faman gogewa, fitowa yayi ya tarar da Annah zaune tana stincen wake
. Kallonsa tayi yanda ya shirya tsaf cikin kaya masu kyau da tsada kaman wani d’an hamshak’i.
“Jalal ina zaka, Jalal farin saurayi dogo mai cikar zati kyakkyawa ya murmusa kafin yace “Annah birthday d’in abokinmu TARIQ zamuje su Salim suna waje suna jira na.
“Fuskar Annah tamau dama tasan zancen bazai wuce haka ba, tasha raba Jalal dasu Salim amma baya ji, yak’i yarda ya tsaya a matsayinsa na talaka bashi da aiki kullum sai k’ok’arin had’a kansa da sangartattun yaran masu kud’i musamman su Labeeb.
“Gyaran murya Annah tayi kafin ta soma fad ‘in” Jalal har yaushe zan maka magana kaji, ka sani kai maraya ne kuma talaka, idan baka tashi ka tsaya ma rayuwarka ba babu wanda zai maka, kai kullum bakada aiki se biyewa su Salim ko, toh ka sani su sunada masu masu, sunada gatansu kaifah, baka dashi , tunda ka gama jami ‘a ka’ki neman aiki ka tsaya kana biye masu, yau kune wancan club din gobe wancan, kune bin ‘yanmata kune shaye shaye…… “Jalal yayi saurin d’ago kai yana kallon Annah, haba Annah shaye shaye fah kikace nasan dai su Salim suna yi amma ni banayi, ina dai da ‘yammata banyi musu ba amma wllhi bana shan komai tunda kika hanani……. “Rufe mun baki Annah, ta dakatar dashi kafin taci gaba da fad’in” Da da kakeyi na maka uzuri don na d’auka yarinta ne zaka daina amma yanzu na gane shashanci ne kawai ke damunka, shekaranka 25 ace bakasan abu me kyau ba toh wllhi ka kiyayeni….. “Sallaman Labeeb ya katsesu.
“Gaisar da Annah Labeeb yayi, ta amsa masa babu yabo babu fallasa, kafin ya d’an daki kafad ‘un Jalal yace Guy let’s get going.. Jalal ya mike yana satan kallon Annah kafin yace Annah sai mun dawo, kallo tabisu dashi har suka fice, girgiza kai tayi kafin tace bazan fasa maka addu’an shiriya ba.
Sameena ce 👌🏾
[1/23, 22:07] +234 803 619 0581: 😭🙍🏻ZUBAIDAH🙍🏻😭
04
*©Sameena Aleeyou..✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum… 📖📚_
*Dedicated to all Victims of rape, never keep silence. Fight for your right, this is not something to be ashamed of your self, let the guilty ones feel ashamed of themselves🙌🏾🙌🏾🙌🏾🙌🏾*
“JALAL, abokin su Saleem ne wanda tun tasowarsu tare suka taso, Jalal maraya ne wanda bashida kowa sai mahaifiyarsa Annah, Annah tayi komai a rayuwarta don ganin ta inganta rayuwar Jalal tun yana yaro, kama daga karatunsa har zuwa girmansa, haka nan ya tashi ba tareda yasan mahaifinsa ba, don Annah ta sanar dashi cewa mahaifinsa ya rasu tun yana k’arami. Annah ta jima tana yiwa matar Alhj Kasim aiki wato mahaifiyar Salim, tun wani lokaci da suka zauna a Gombe, tun yaran gaba d’aya suna k’anana, Annah ita ta rainesu gaba d’aya, Salim Labeeb da kuma Jalal d’inta, wann dalili yasa lokacin da zasu komo Abuja suka taho tareda ita don tun a lokacin bata da miji ya rasu. Ta zauna da d’anta a nan BQ din gidan Alhj Kasim.
“Tunda yaran suka taso iyayen ke k’ok’arin rabasu da Jalal, suna nuna masu cewa shi ba daidai dasu bane, babu yanda basuyi ba don ganin sun rabasu amma abu yaci tura dole suka hak ‘ura suka k’yalesu, amma ko kid’an babu wani abu na arziki da suke masa.
“Shi kuwa Jalal babban abun da ke masa dad’i shine yanda emmata da samaruka yaran masu kud’u suke zaton shima DASUKI’S ne, ma’ana shima dan familyn Dasuki ne, ko ina tare dasu Salim suke zuwa party shisha spot da dai sauransu. Allah ya masa kyaun hallita gabba d’aya yafisu kyau ‘yanmata suna rubibinsa shiko na ja masu class kaman wani d’an hamshak”i ko kad’an bakace Jalal ya had’a jini da talaka ba…wann kenan.
*Gombe, Dukku*
“Huci take kaman wata kububuwa tana watsawa malam Habu mahaifin Umar da abokinsa malam Tanko harara, Malam Habu suka saki baki suna kallon ikon Allah sanda Yaya Habibu ya mik’e ya rusuna gaban Hadiza yana tambayanga shin ta amince a karb ‘I baikon Zubaidah, …. Mikewa Hadiza tayi kafin ta d’ibi ‘yan goron da malam Habu suka shigo dashi ta shiga juye masu a tsakar kansu, tana balbala wutan bala ‘i da masifa, ta yanda take shiga bata nan take fita ba.
“Malam Tanko ya mik’e yana fad’in subuhanallah, Malam Habu ya baka fad ‘a mun haka lamarin yake ba, Malam Habu da kunyar abokinsa mutum mai muhimmaci a gari irin Malam Tanko ya baibayesa, dama yasan haka ka iya faruwa, shiyasa tun farko bai so Ummaru ya nemi Zubaidah ba dukda ya aminta daehankali yarinyar kuma na tausayinta, amma ko kad’an bashi fatan abinda zai hadasa da dilalliya Hadiza,…..
“Zubaidah dake mak ‘ale bayan k’yaure bata san sanda ta sulale gwiwoyinta a k’asa ba tana hawaye sanda ta jiyo irin fatattakan da Yaya Hadiza tayima iyayen Umar, shikenan itakam tasan bazata tab’a aure ba, bazata tab’a jin dad’in rayuwarta ba, mafarkin ta bazai tab’a tabbata ba, takaicin yayanta da tausayin kansu shida ita ya lullub’e zuciyarta. A hankali ta k’arasa kan tabarman da ya kasance makwancinta ta kwanta tana kuka mai tsuma zuciya.
“Malam Habu jiki a sanyaye ya shiga bawa Malam Tanko hak’uri, Malam Tanko yace a’a abokina baza ‘a bar wann magana ba tunda yaran suna son junansu ni nasan yanda za’ayi, ka shige gida zan nemeka zuwa gobe, Malam Habu ya masa godiya sukayi sallama kafin malam Tanko ya hau babur dinsa ya wuce.
*******************
*Abuja*
“Suna isa wajen partyn pili ya dauki shewa da ihu, manyan yara wanda duk gabaki d’aya Abuja sunansu yayi k’auri Sun samu halarta, Tariq ya k’araso yana welcoming nasu sai wani tafe hannaye suke yanda niggas keyi. Tariq shine cikon na hud ‘u a clik d’insu, shima mahaifinsa nada shears a companyn *Dasuki Holdings* kampanin mahaifan Salim da Labib, ..
*Zubaidah, Jalal, Umar, Salim, Labib da kuma Tariq*
*Ku biyo Sameena don jin labarin gumurzumon da wad’annan matasa suka fuskanta………. 👌🏾*
[1/23, 22:08] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
05
*©Sameena Aleeyou…..✍🏾*
_Queen Same Novels Forum…📖📚_
“Alhj Kasim Dasuki, Alhj Jamil Dasuki da kuma Alhj Yusuf Maina mahaifin Tariq sai Barrister Munir Malami lawyer na company ɗinsu *Dasuki Holdings* kuma yaya ga mahaifiyar Salim Haj Farha Dasuki.
“Zaune suke gaba ɗaya a babban parlorn taraban baƙin Alhj Tahir, magana suke na tsaida ranar auren Salim da Kausar, an tsayar sati mai zuwa za a yi bikin saka rana. Daga nan suka ɓuge da hiran kasuwanci da siyayasa. Tunda dama Alhj Tahir na neman tsayawa takaran shugaban ƙasa, nan Barr Munir ya bada shawarin a tafi chan Dukku ayi bikin saka rana hakan ba ƙaramin nasara zai kawo wa neman takaransa ba, gaba ɗaya sukayi na’am da batun Barr Munir snn ƴan garinsu zasu tabbatar shi ɗin mai ƙaunar mahaifarsa ne….. Har farfajiyar gidan Alhj Tahir ya rakosu yanda bodyguards ɗinsu suke… Daga nan ya wuce ɓangaren matarsa uwar ƴarsa Hajiya Raliya don sanar da ita yanda suka tsai da batun auren yaran.
“Kausar da Asmah ya samu a parlorn ƙasa suna playin PSP, gaba ɗaya suka soma gaidashi… Papa sannu da shigowa amsawa yayi da sakin fuska kafin yace ina momman taku, har suna haɗe baki wajen cewa she’s upstirs, ƙarasawa yayi ya nufi stirs ɗin.
“Kausar da Asmah suka ci gaba da game ɗinsu. Asmah cousin ɗin Kausar ce wacce a shekare baifi ta girme wa Kausar da shekera guda ba, tun dawowarsu Nigeria Asmah take gidansu daga zuwa kwana biyu Kausar taƙi barinta ta koma dole Aunty Miemie mahaifiyar Asmah ta haƙura da zancen don tasan halin Kausar da kafiya.
“Momma na zaune gaban dressing mirror tana gyaran fuska as usual don itakam taƙi yarda ta tsufa at her late 40s bats sahun matan nan masu barin gyaran jiki da zaran sunga shekaru ya soma ja masu,… Murmushi Papa yayi gamida rungumota ta baya, murmushi itama ta sakar masa kafin tace” Papa how do i look like, ɗan jan hancinta yayi kafin yace as always my one you look so gorgeous manna mata peck yayi a goshi kafin suka zauna bakin gado ya soma faɗa mata yanda suka tsai da maganan bikin Kausar, nan da nan idon momma yayi raurau Kausar is her only daughter ƙaunar ranar rabuwarsu tazo dukda tasan dole wata rana hakan ta kasance…. Papa yasan kwanan zancen don haka rungumota cikin jikinsa yayi ya soma lallashinta da kalamai masu taushi, “Haba first lady you need to be very strong you know, sooner or later zaki zama mother of the country insha Allah, bama Kausar kawai ba, the whole country will be yours, and for now akwai Asmah though nasan itama tana samu miji zamu aurarta but atleast zata ɗauke mana kewar Kausar…. Jin yanda mijin nata keta faman riritata yana shagwaɓata yasata sakin murmishi gamida goge guntun hawayenta tace” Pappy you ƙnow what made me cry….” Ɗan girgiza kai yayi har lokacin tana cikin jikinsa kafin taci gaba da faɗin” I dont know why, but har raina banjin son auren Kausar da Salim duk da ɗan aminiyata ne, quite alright nasan gidan girma arziki da mutunci zata but…. Kasan yaran zamani kar Salim ya hurting mana baby girl ɗinmu….”Papa yayi murmushi gamida shafa goshinta zuwa gashinta kafin yace” Raliya insha Allah we won’t regret it, bazamuyi danasanin aurar da Kausar wa Salim ba, besides they both love each other wanda kinga hakan akeso ya kasance. Yanzu abunda nake so dake, you shud start preparing we leaving in a couple of days gwara mu mu fara isa tunda mune iyayen bride, I’ll make sure the house is ready from now to tomrrw, ki kira su Kausar ɗin ki sanar dasu su fara shiri, barin ƙarasa parlor inada wasu baƙin.. Gyada kai kawai momma tayi da ƙyar kafin ya manna mata kiss a chick ɗinta ya fice.
“Wann shine rayuwar gidan Alhj Tahir, mutane ne masu Dattako da sanin ya kamata, ko kaɗan basuda ƙyamar talaka kaman Dasuki family, snn abin hannunsu sam bai rufe masu ido ba, da wann dalili yasa akasarin mutane suke mara masa baya a siyaysarsa, yayinda wasu ke ganin The Dasuki family ks iya ja masa cikas a siyasarsa sabida izzan su da ƙyamar talaka ds suke dashi.
“Kausar da Asmah sai murna suke zasu Dukku dukda kakanninsu gaba ɗaya sun rasu amma skwai sauran dangi, Momsy ya maganar kayan gaskiya ki sake masu waya we need them this week, they shud make it possible this week. Momsy ta ɗan sakar mata harara kafin tace” Kausar this is not Holland fah, na faɗa maki ki rage wann rawar kan taki, ba irin auren da kika saba gani bane na turawa, wann auren fulani ne wanda aka san sansu da kunya so be careful,… Momsy tana ficewa Asmah da Kausar suka kalli junah, suna daroya ƙasa ƙasa don suma har sun ɗagota bata son Kausar ta bar gidan ne Asmah ta ɗau waya tace bari kiga na kira *Mamza beauty* (makeup artist) na sanar mata, ke kuma pls ki kira Sarah fashion ( Fashion stylist ne a Dubai wanda zasu ɗinka kayyaykin Kausar da zatayi amfani dasu a events) ɗin ki sanar dasu.
“Rungume pillow tayi gamida lumewa cikin hashaƙin gadon tana tuno farin cikinta Salim, ya kusa zama *Mallakinta* Asmah na mata magana ko saurara batayi ba tayi nisa wata duniyar, girgiza kai kawai Asmah tayi ganida jifar ta da pillow kafin ta fice.
“Tafe suke suna tangaɗi da gani kasan sun bugu da giya, da ƙyar suka iya fitowa daga motan ,Alhj Kasim da har loƙacin idanunsa biyu baiyi barci ba ya dubi agogon bango dake maƙale a ɗakin ya nuna ƙarfe uku na talatainin dare, yasan ba kowa bane zai shigo gidan a yanzu sai Salim, kai tsaye down stirs ya sauƙo ya buɗe ƙofar parlor, chan ya hangesu suna tafe suna tangaɗi gaba ɗayansu, Jalal na riƙe dasu don dama duk randa suka je party suka shawu toh shi ke driving nasu da shike shi bai sha yanda za’a gane sama sama yake kora wine maras bugarwa sosai shide barshi da harƙan bin mata, shiɗinma da yawa ƴan matan ke kawo kansu wasu na zaton shi ɗin ɗan Dasuki Family ne yayinda wasu ke sonsa sabida kyaun da Allah ya masa.
“Wani mugun kallo kawai Alhj Kasim ke binsu dashi musamman Jalal, shikan ya tsana ganin yaransu da sidecake ɗin,….. ”
“ƴan kame kame Jalal ya soma, tuni Alhk Kasim y dakatar dashi da faɗin” meyas baka kai shi gidansu ba ya ƙarashe maganar yana nuni da Labib, Jalal da tuni ya shaƙi kallon ƙasƙancin da Alhj Kasim ke masa, a daƙile yace ” Gani nayi nan ma gidansu ne……”Jar ubancan haka Alhj Kasim yace a zuciyarsa lallai wnn talakan raini na neman shiga tsakaninsu, baiga laifinsa ba lafin su Salim ne,… Securities ne suka ƙaraso suka shiga taimaka wa Jalal, ɗaya security ɗin daga gidansu Labib yake yazo tafiya dashi don hankali mom ɗinsa ba ƙaramin tashi yake ba duk randa yayi dare a waje, duk da hakan ba sabo bane amma she couldnt get used to it har yanzu. Haka aka wuce da Salim da Labib kaman wasu mutattu don tuni bacci yayi awon gabadasu.
“Jalal ya ɗaga gira sama kafin ya dubi Alhj Kasim yace” Have a good evening Sir , daga nan yayi wucewarsa can sashensu. Kallo Alhj Kasim yabisa dashi kafin yayi ƙwafa ya shige cikin gida.
“Washe gari zaune suke gaba ɗaya a babban parlorn Alhj Kasim, Ya kuma duban Hajiya Farha dake zaune gefen Hajiya Nurah mahaifiyar Labib yace” Farha jeki taho min da yaran nan Labib da Salim suna sashen Salim, babu musu Hajiya Farha tabi umarnin mijinta ta fice kiransu.
“Sai ihu suke suna buga game na ƙwallo ko saurarenta basuyi ba, da takaici ya isheta batasan sanda ta fincike socket ɗinba…..”Whatttt!!!!! Suka fadi a tare, Salim yayi jifa path ɗin hannunsa gamida faɗin ” Shitttt, why mum haba haba mum…. Rufe mun baki marassa hankali kawai Mum ta ƙasesu, Labib ya ɗan langɓe kai kana yace” We are sorry favorite Aunty, Kunnens ta janyo kafin tace” Daga yau zaka tashi daga fav son idan baku zama good boys ba, Dad na kiranku bata jira cewarsu ba tayi ficewsrta. Labib yace nasan Uncle ne dama zai sa Fav Aunt ta mana haka he will never change. Salim ya watsa masa mugun kallo kafin ya fice ba tareda yace komai ba.
” Cikin tafiyarsu na samarin da tarbiya bai ishesu ba suka ƙaraso parlorn, gamida tsayuwa ma iyayayen tsegehe akai.
“Alhj Jamil, ya sauƙe ajiyan zuciya kafin yace” Seat down boys, zama suƙayi da ƙyar saman carpet Alhj Kasim kuwa banda hararsu babu abinda yake. Kaman jira yake nan ya soma surfa masu masifa ” When are you boys going to start acting like real Dasuki’s huh?Har yaushene zaku daina alaƙa da wann matsiyacin yaron, he’s not one of you ba daidai ku bane get this to your heads….. ” Alhj Jamil da mamaki yake kallon ɗan uwan nasa ko kaɗan baisan kan hulɗa da Jalal zai masu faɗa ba, a’a ya ɗauka kan ɗabi’u marassa kayu da suke zai masu faɗa, to his gretest surprised sai jin akasin haka yayi, lallai yayansa yayi nisa.
“Labib ne ya ɗago kai yanai ma uncle ɗin nasa mugun kallo ƙafin yace” Pls uncle will give us break, idan dai akan Jalal zaka mana faɗa you can keep on doing it but bazamu taɓa rabuwa dashi ba he’s our childhood friend a brother from another mother…..”Enough Labiiiib! Daddƴnsa ya daka masa tsawa, kafin yaci gaba da faɗin ” Ma ucle ɗin naka kake faɗun magana haka, be careful kana jina, Labib yana wani hure huren hanci yake watsa wa uncle ɗin nasa mugun kallo, Barr Munir ya sako baki da faɗin” Ni kawai a kori ysron da mahaifiyarsa kowa ya huta. Wata harara Labib ya watsa masa kafin yace” Malam ka mana shiru dalla this is family issue who invited you…” Salim ya caƙumo wuyar Labib yana huci yake faɗin ” First kayi rashin kunya wa Dad ɗin second kanayi wa Uncle ɗina, Brothern mahaifiyata how dare you Labib…. Saida aka shiga tsakanin Labib da Salim don kaɗan ya rage basu kaure da faɗa ba.
” Alhj Kasim ya goge zufar data keto masa dukda ac dake busawa a parlorn, iyayensu matan su suka lallashesu kafin suk sanar ɗasu maƙasudin haɗuwarsu.
“Take annuri ya cika fuskat Salim tuni ya mance wani baƙin ciki ya soma farin ciki, Yayinda zuciyar Labib taci gaɓa da tafarfasa, a cikin ransa yake furta ” _no way it can’t be happening, Kausar is mine not yours Salim Dasuki_
“ƙarasawa yayi ya ɗan daki kafaɗan Salim yayi con granulating nasa kafin ya fice cikin sauri.zuciyarsa naci gaba da tafarfasa
*****************************
“Mai anguwa yaci gaba da faɗin’ ni mai anguwa ni na karɓi baikon Zubaidah kina jina ya ƙarashe maganar yana duban Hadiza data sadda kai a gabansa ta cika tayi fam. Ƙiris ya rage bata fashe ba.
“Hamma Habibu kuwa sai wsge baki yake kaman gonar audiga yanai wa mai anguwa godiya, banda hararsa babu abinda Hadiza keyi tanai masa kallon zaka shigi hannu ne. Mai anguwa yaci gaba da faɗin ya ysai da aure nan da wata mai kamawa kowa yaje yaci gaba da shirye shiryensa, kuma uffan Hadiza tayiwa Zubaidah za’a mata hukunci mai tsanani koma ya miƙa case ɗin gaban sarki, daga nan ya sallami Hadiza da Habibu suka wuce.
“Malam Tanko da mlam Habu sukayi godiya sukayiwa mai unguwa suka ɗan tattauna kafin ya sallalmesu.
“Tsakanin Ummaru da Inna an rasa wayafi farin ciki, tuni ya ficr ganin masoyiyarsa, mai shirin kasancewa amaryarsa……
Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:08] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
06
*©Sameena Aleeyou…✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum…📖📚_
“Zubaidah zaune bakin murhu tana kan hura wutan girki, ko kaɗan yau bata jin zafin duk tulin aikin da zatayi, snn ko kusa masifan Yaya Hadiza bai ɗaga mata hankali ba, jinta take tamkar sallah, muddin zata bar wann kurkukun dole taji farin ciki a zuciyarta, uwa uba zata ci gaba da karatunta saidai zatayi kewan Kamalu da Hammanta.
“Wani yaro ne yayi sallama snn yace wai ana sallama da Zubaidah…… “Wulli wulli tai da idanu tana kallon yaya Hadiza dake zaune bakin ƙofar ɗaki ta cika tayi fam ƙiris ya rage ta fashe.
“Meye kike mun kallon ƙurilla mayya jarababbiya, ai shikenan hankalinki ya kwanta za’a maki auren abinda kike so, ƙaramar karuwa kodayake ba laifinki bane kin riga kin san namiji tun a gantalinki na karuwanci…….”ƙwalla suks ciko idanunta kanta na sunkuye a ƙasa, wann mummunar kalma na karuwanci da Hadiza ke jifarta dashi sosai yake ɗaga mata hankali…. Bata gama tunanin da take ba sai ji tayi yaya Hadiza ta janyo wuyarta ta jefata bakin ƙyaure tana faɗin “Wuce kije shegiya mayya kafin ki cinyeni, maza kije yaci gaba da mammatse a lungu yanda ya saba….”
” Ko ɗan kwalliya da ƴammata keyi idan zasu wajen saurayi Hadiza bata bar Zubaidah tayi ba, haka nan yanda ta tashi daga bakin murhu da warin hayaƙin da komai ta turata waje….
“Daga can bakin bishiyar da yake tsaye ya hangeta tana goge hawayen da ya jiƙa mata fuska.. Cikin sauri Umar ya ƙaraso yanda take, tuni ta soma matsawa da baya don bata so yaji ƙaurin hayaƙin da take, gashi shi yayi tsaf ya sha gayu abinsa irin na samari daidai da ajinsa.
” Harɗe hannaye yayi a ƙirjinsa yana kallonta, tausayinta da ƙaunarta na daɗa ratsa ɓargo da tsokarsa,.. Saida ya bari ta gama ƴan goge gogen hawayen kafin ya ɗanyi gyaran murya cikin tattausar murya ya soma faɗi” Zuɓaidah, shiru bata amsa ba har lokacin kanta na kallon ƙasa, kafe ta idanu yayi kafin ya kuma kiran sunan nata, sai snn ta ɗago koɗaɗɗun idanunta ta mar duba guda, Umar yanada ƙwarjini ta yanda duk budurwar da tayi ido huɗu dashi sai ta tsinci kanta da faɗuwar gaba, gashi a yau yafi kullum mata kyau, shi ba fari bane snn ba baƙi can bane, kallo guda zaka masa ka gane asalin bafulatani ne haɗi da kwantattun sumanss da sajensa da suks ƙara masa kyau da ƙwarjini….”Muryarsa ya katseta sanda yayi mata nuni da wani kututturen dabino yace” Mu karasa ki zauna, babu musu tabi umarninsa……” Har sun soma tafiya suka jiyo muryar Hadiza ashe tana laɓe jikin ƙyaure tana saurarensu nan ta soma faɗin “Ku ƙarasa ina, kai wani irin jarabebbe ne, baka jira akai maka ita ba sai kazo har ƙofar gidansu kana matseta, auho ashema kun saba kinji kunya Zubaidah tuna kika zaɓi zama karuwa, toh ni dai kar ki kawo min abin kunya kafin wata gudan da aka ɗiba maku ya cika taƙarashe maganar tana watsa masu mugun kallo.
“Umar yabits da kallon mamaki, ƙarasowa gabanta yayi yanda take tsaye kafin yace” Dillaliya kike ko wa? Galala take dubansa cike da mamaki kodashike tasan Ummaru da wann taurin ran nasa zaiyi fin haka, muryarsa ya katse mata tunaninta yanda yaci gaba da faɗin” Yau ta kasance rana ta ƙarshe da zaki saka masoyita kuka, don wllhi kinji na rantse kika kuma kiranta karuwa kotu zan maka ki sai munyi shari’a daga nan har birnin tarayya, kuma da kike cewa ni jarabebbe, naji na yarda idan dai akan Zubaidah ne sai nafi jaraba ma naci, don nasan bazan taɓa ƙosawa da ita ba, ki kalleta da kyau mana, ke ai kina ganinta kinga mace ba irinki ba, nasan hassada ce tsan tsa kike da ita ba wani abu, yayi wata murmushi mai cike da nishaɗi da gargaɗi kafin yace” This should be the last warning idan kunne yaji toh fah jiki ya tsira, daga haka ya dubi Zubaidah da ƙiris ya rage bata saki fitsari a jikinta ba don tsoro kana yace” Amaryata lets go, dont mind this witch, don yasan Hadiza dai ba turanci take ji ba……”Kallon Yays Hadiza tayi alamun tana jiran umarninta” Haba tuni ta soma bambami tana kunfan baki, yo har ni za’a yi ma turanci, ke Zubaida har kinyi kaurin da zaki biyewa saurayi inji ni nayi ɗawainiyar karatun naki, har shine zaki zaɓi saurayi akaina ya zageni da kalman turanci kina tsaye kina biyesa yayi maki kyau, idan dai namiji ne kije gaki gashi ….. Daga haka tasa kai ta wuce cikin gida fuu zuciyarta naci gaba da tafarfasa….
“Juyowa tayi tana duban Umar, murmushi ya sakar mata kafin suka ƙarasa suka zauna.
“cikin tattausar muryarta ta gaidashi, ya amsa yana wani kasheta da mayen kallo, ita kiwa duk kunyarsa ya rufeta musamman cewa da yayi, idan dai akanta ne sai yafi jaraba naci, wann kalmomi sun matuƙar mata nauyi, kaman yasan hakan kuwa nan yasa hannu ya karɓi ɗan karan da take wasa dashi aiko nan ta ɗago ido suka kalli juna, tai saurin sadda nata idon,
“Zubaidah, ki sani ina sonki ina ƙaunarki sann zanyi komai a sabida ke, nasan kalan rayuwar da kike da wann matar, daga rana mai kaman ta yau ki sani bazan sake barinta taci zarafinki ba.
“Ɗan murmusawa tayi kafin tace” Na gode, cikin muryarta mai daɗin saurare, kaman waccd aka zabura ta miƙe tsaye, ɗan dubanta yayi kafin yace” Yaya dai ko har mun gama hiran ne, ɗan girgiza kai tai kanta na ƙasa kafin tace” A’a gani nayi kaman ƙaurin dake jikina ya dameka.
“Tsuke fuska yayi ya kira sunanta da dakakkiyar murya, ɗago ki kalleni Zubaidah, ta ɗago tana dubansa, Umar yaci gaba da fadin” Nida ke mun zama ɗaya, bana jin ƙauri ajikinki, akasin haka nike ji, ma’ana ƙamshi nake ji, kasancewa taredake yafiye mun komai ina sonki a duk yanda kike. Murmushi tayi harda ɗan rufe fuska alamun taji kunya,.. Dariya ya ɗanyi mai bayyanar da hƙwara kafin yaxe” Oya faɗa mun kina sona… Ware idanu tayi alamun bazata iya ba, Umar yayi murmushi kafin yace” Surbajo na nasan kinayi koh… Kasa cewa komai tayi sai murmushi…. Hira sosai suka sha a wann rana kamsr karsu rabu da juna, basu taɓa hira irin haka ba, kullum saidai su haɗu a bakin rafi taje ɗibo ruws ko kuma ta kai saniyar yaya Hadiza kiwo.
*********************
” Salim ne tafe waya manne a kunnensa yayinda hannunsa ɗaya ke riƙe da coffee cup, “What com’on Tariq pls ka shirya yanzu yanzu, we will fetched you up sai mu wuce airport ɗin… Yeah right , see you soon. Yayi hanging up kafin ya tura ƙofar ɗakin da hannu guda.
“Cak ya tsaya yana kallon Labib dake baccinsa hankali kwance. Kan gadon ya ƙarasa ya ɗauki pillow ya shiga dukan Labib dashi yana faɗin” Will you get your lazy ass out of bed,…
“Labib, yayi miƙa gamida cusa kansa cikin bedcover yana faɗin” Shitt, pls mana Salim, kasan ba’a tashina a bacci i’ll fall sick.
“Salim ya shiga yaye blancket ɗin yana faɗin whatever, You know we cant miss this flight, tun jiya Daddy ya mana bucking flight ɗin Gombe mukayi missing still yauma muyi missing what will u expect, they’ll get mad ai.
“Gajeren tsaki Labib yayi kafin yace” Does it really has to be now, ” Labib ya miƙe yana wangale labulayen tapƙa tapkan windunan ɗakin kafin yace” The flight is 10am and yet is almost 30mins pass 9.. Tsaki Labib ya kumayi babu salati yake hamma kafin yace” waima ina private jet ɗin Dasuki Holdings ne ba sai mu tafi dashi ba, Salim yace gaba ɗaya Jets ukun suna da prob, Daddy yace zaiyi firing masu maintenance ɗinsu, kaga idan mukayi missing wann flight ɗin tofa saidai mu tafi Gombe by road, kai ina I cnat afford to miss this flight ma, i’m dying ti see my Kausar,.. “Galala Labib ke kallonsa kafin yace” Waye ma kake tunanin zaiyi tafiya mai nisa haka by road, haba ba dai ni Labib Dasuki ba.
“Salim yayi dariya kafin yace” Freaking Dude sai ka tashi ka shirya ai na masu Tariq da Jalal magana suna shiryaw Ya ƙarashe maganar yana jifan Labib da towel.
Ba don yaso ba ya miƙe ya nufi bathroom..
“Gaba ɗaya Annah bataso tafiyar Jalal Dukku ba, don tun yana ƙarami data taho dashi Abuja basu kuma leƙawa ba, tana tunanin abinda ka iya zuwa yazo, kar wata rana daɗeɗɗiyar sirrinta data ɓoye masa ya bayyana. Haka tai kusan kwana zullimi……
*Gombe, Dukku*
_Toh fah readers gasu Jalal, Labib, Salim, da kuma Tariq a garin Dukku, shin me zai faru. Shin me Annah take ɓoyewa Jalal tsawon rayuwarsa. Ku biyo Sameena don jin yanda zata kasance_
Sameena ce👌🏾
[1/23, 22:09] +234 803 619 0581: 🌘🌘🌘🌘 *ZUBAIDAH*
07
*©Sameena Aleeyou…. ✍🏾*
_Queen Samy Novels Forum…📖📚_
“Drivers ɗin da suka ɗibo su daga airport suka soma paka luxurious cars ɗin a farfajiyan tangamemen gidan wanda yasha tsari da kayan alatu, idan ka shiga gidan sai ka ranste ba’a Dukku kake ba.
“Kai ysaye cikin gidan suka nufa yayinda gurds suka shiga firfito da luggage ɗinsu.
“Iyayen nasu ne zaune a babban parlorn, ciki harda iyayen Tariq.
“Tun daga nesa Alhj Kasim ya haɗe giran sama da ƙasa sakamakon abinda ya gani, wayo wann tsinannen mayen yaron saida ya biyosu…… Ko saurarensu baiyi ba sanda iyayayen keta faman hugging yaran suna masu sannu da zuwa, rai ɓace ko kulasu baiyi ba yayi ficewarsa, Labib ya rakasa da harara har ya fice. Cikin sauri Barr.Munir ya miƙe yabi bayan uban gidan nasa.
“Da yamma lis hadari ne sosai a garin already dama an idda wani ruwan don haka garin yayi sanyi weather yayi dadɗi. Samarukan guda huɗu suka shirya cikin ƙanan kaya kafin suka shige motarsu mai buɗeɗɗen sama don zagaya gari.
“Mutumina na maka murna fah ka kusa zama ango, cewar Balele dake zaune saman mota a bakin tasha, Umar yayi wani murmushin jin daɗi kafin yace insha Allah abokina, Balele ya kashe masa ido guda kafin yace” Ina tausayin yarinyar nan duk randa aka kulleta a ɗaki daga kai sai ita mutumina nasanka fah babu ɗaga ƙafa ranar…”Wata dariya Umar yayi kafin ya dubi Balele ya soma faɗin” Naji tunda nayi haƙuri ban taɓa bin ko wata mace ba, ban taɓa danne ƴar kowa ba ko ƙanwar kowa, kaga dole duk randa na sami nawa nayi budurina, babban farin cikina shine zan kasance da macen da nake so…..”Balele ya busa sigarinsa a daidai fuskan Umar yana murmushi gamida jinjina kai…. Wani mugun kallo Ummaru ya watsa masa kafin yace waikai baka gajjiya da kayan maye ne? Murmushi Balele yayi kafin yace tuƙa manyan motoci ai saida kayan maye, gaskiya Ummaru ina gani ƙoƙarinka da ko karar sigari baka sha, Umar ya girgiza kai ba tareda yace komai ba ya soma ƙoƙarin miƙewa.
“Ina kuma zaka Balele ya biɗa,
“Bakin Rafi zanje munyi da Zubaidah zamu haɗu can, Balele ya murmusa kafin yace” Zubaidah tsokale idon samarin Dukku, gaskiya kayi sa’a da har ake ƙoƙarin maganar aurenku su Gwatse basu taɓa kai mata hari ba.
“Umar yayu wata murmushi mai cike da ma’anoni kafin yace” Balele kasanni akan abinda nike so, wallhi duk garin nan babu wanda ya isa ya taƙura Zubaidah muddin ina numfashi matar yayanta ma data tashi gabanta ban ragar mata idan dai akan sanyin idaniyana Zubaidah ne balle wasu ƙananun tsageru su Gwaste, wani murmushin ya kuma kafin yace “Shege ka fasa gasu ga ita……”Balele ya bushe da dariya kafin yace” Kai mutumina daɗina da kai akwai zuciya…. “Ba tareda ya kallesa ba yace” Kaga ni zan wuce idan Oga Kabiru ya iso ka basa uzurina dan Allah.
“Aff ai yau bazamuga Oga KB ba cewar Balele.
“Umar ya jiyo gamida mada kallon meyasa.
“Bakada labarin zuwansu Alhj Dasuki da ƙaninsa da kuma Alhj Tahir Marafa na unguwar dutse, mai neman tsayawa takaran shugaban ƙasa….. “Ɗaga kafaɗu Umar yayu kafin yace” Toh ni ina ruwana da zuwansu, Balele ya sake baki yana kallonsa kafin yace” Toh bikin saka ranar auren ƴaƴansu za’ayi jibi jibin nan kuma ƙofa a buɗe take ga dukk mai niyan zuwa kasan dai yanda suke neman muƙamin nan dile suja talakawa jiki. Na tabbata Oga yana can ana yana neman ganin Su.
“Gajerwn tsaki Ummaru yayi kafin ya miƙe gamida ɗaukat hankacip ɗinsa da yake riƙe kan starry dashi idan zai tuƙi musamman mai nisa kafin ya wuce ya bar Balele a nan zaune yana shaƙan kayan mayensa, Balele na masa sallama ko kulasa baiyi ba don baiso ya bar masoyiyarsa tayita jira.
“Wow…. This is so woow I just cant believe it yau gani a mother land ɗina, infact motherland ɗinmu dukanmu cewar Salim dake kwance bayar convertible ɗin shida Tariq yayinda Jalal ke driving Labib ke zaune mazaunin me zamar banza.
“Salim yaci gaba da faɗin” Guys mu ɗan bi ta gefen can rafin I knw it will be awesome…..”Gajeren tsaki Labib yayu sanda Jalal ya karyi kwanan rafin da gudun gaske….. Ihu Tariq da Salim sukayi suna shewa alamun suna cikin farin ciki yayinda Jalal ke tayasu…..”Will shut up for heavens sake, haba… Cewar Labib da gaba ɗaya ransa a jagule yake sabida gani yake shikenan bazai samu Kausar ba ta kufce masa.
“Guy chill up muna celebrating ne, cewar Salim. Tsaki Labib ya kumayi kafin yace” What’s even awesome in this place, this place is sucks dont you see it. Ever since I came to this town nake fama da rashes a jikina for heavens sake i dont even knw who the heck came with the idea a zo nan garin ayi engagement….. Ni idande a nan garin za’ayi ɗaurin aurenka believe me I wont attend your wedding don wllhi na gama zuwa garin nan.
“Tariq yace” Guy chill pills we wunt stay long here, besides nan shine mahaifarku….”Ɗan tsaki Labib yayi kafin yace” Meyasa tuntuni basa zuwa garin sai yanzu sabida suna neman wani abi a wajen ƴan garin sabida a nuna a Network labarun tara cewa Alhj Tahir Marafah yazo garinsu yayi engagement ɗin tilon ƴarsa, people will be thinking sabida Allah yayi hakan amma mu munsan sabida buƙatarsa yayi don yaci takaran shugaban ƙasa…..”Enougj of this Labib, Salim ya dakatar dashi kafin yaci gaba da faɗin” Inlawn nawa kake faɗin horrible things akansa you need to watch your mouth buddy.
“Murmushi Labib yagi a daƙile kafin yace” And who cared if he’s your inlaw, gaskiya ne dole a faɗe ta, nasan Uncle shi ya ya basa wann shawaran don nasan Alhj Tahir is a responsible mutum bai iya ƙaryar ƴan siyasa ba…..” Kan yayi shiru saiji yayi Salim ya cakumu wuyarsa yana faɗin” How dare you say those things to my very own father,….. Kan kace me faɗa na ƙoƙarin kufcewa ysakanin Labib da Salim….. Sai sn Jalal da tun fara cecekucensu bai tofah uffan ba dama sun san miskilancinsa sun san bazai ce dasu komai ba don ya saba, burki yaja ya tsaya tsakiyan hanya ƙiiiiiiiiiiiiiiittttttttt” Gaba ɗaya saida suka jirkita. Juyows yayi yana watsa masu kallo kafin yace” Let me know if u done… Daga haka bai kuma cewa komai ba. Tariq ya fuzar da iska kafin yace” Guys pls lets not ruin our day, besides bai kamata kuna haka ba, this is childishness you’re all matured enough, snn abinda gayika Labib shi yayi Salim, we are all here because of you guys, what will you expect us to feel idan kuna abu makamancin wann a gabanmu nida Jalal, ku tuna we arr all friends and we love each other like brothers, pls lets not ruin this special moment especially you Salim this part of your wedding the beginning of your happiness lts chirrr it pls.
“Murmushi Salim yayi kafin yace” Yeah Buddy you right i shoudnt hve done that, ya kalle Labib kafin yace I knw why my cousin is acting this way sabida nan babu ƴan matansa i’m right…. “Sai snn sukayi murmushi su duka gaba ɗaya harda Labib ɗin ya ɗan daki kfaɗun Salim yace” Sorry Bro for been mean to you….” Its okay Buddy Salim ya faɗi da murmushi saman fuskarsa. Sai snn Jalal yaci gaba da Driving.
“Tsaye take bakin rafi saniyarta tana shan ruwa yayinda ita kuma Zubaidar keta faman tsane rigarta da ya jiƙe shaƙaf da ruwa sakamakon ruwan da aka tsulala, tafiya mai ɗan nisa ne daga wajen rafin zuwa cikin gari shiyasa har ƴanzu Umar bai zo ba, so take ta tafi amma tana tunanin kar ta tafi yazo bai sameta ba ransa ya ɓaci, don ita kanta tsoron ɓacin ransa take sabida zuciya da yake dashi, don haka dole ba don taso ba taci gaba da tsane kayan duk ya kakkame jikinta shape ɗinta ya fito sosai.
“Gama parking ɗinsa keda wuya idanunsa suka sauƙa kanta, baiga fuskarta ba sai bayanta, shi tunda Allah ya haliccess zaice bai taɓa ganin mace mai kyawun sura irin ta wnn yarinya ba, haka kurum yaji ya ƙagu ta juyo yaga fuskarta, Su Labib daketa faman selfie basu ko lura dashi ba, Saida Salim ya taɓosa kafin suka hangi abinda ya hango, sai faman tsane rigarta take ko kaɗan batasan akwai wasu halittu a wajen ba bayan ita da saniyarta……” *God have Mercy* Cewar Labib cikin sandarewar murya yayinda su Salim da Tariq suka kasa furta koda kalma guda,.. Haka kurum Jalal yaji baison kallonta dasuke, dukda shi tantirin ɗan iska ne wajen hulɗa da mata amma ko kaɗan yau ji yayi bai son su kalle wann yarinya da har lokacin bai ga fuskarta ba……

Leave a Comment