Bismillahir Rahamanir Rahim.
~~~
An ce wai k’addara tana da tarin ma’anoni a duniyar nan.
Ance kamar yadda rayuwarmu take mabanbanciya, haka k’addarar ma take.
Sai dai kamanceceniya a sunanta kawai.
Wani zai fassara maka kaddara da sanadin rasa dukiya ko mulkinsa.
Uwa zata baiyana maka ita da mummunan abinda ya faru ga d’anta.
Uba zai iya d’ora ta kan duk abinda zaiyi hijabi da farin cikin iyalansa.
Wasu kan iya siffanta maka ita da dalilin rasa wani buri na rayuwarsu.
Sannan bayan duk wad’annan, k’addara kan iya d’aukar siffar alkhairi ma.
Misali, wani zai kasance mai nasara a komai na rayuwarsa, sai ace maka ‘k’addararsa kenan.’
Ko kuma idan wani abin alkhairin ya same ka, mutane sai suce ‘Dama hakan na daga cikin kaddarar da Allah ya tsara maka.
Ta riga na san duk wad’annan, kamar kowa abinda bata sani ba shine…
Me cece tata k’addarar?
Yaushe zata fuskance ta?
A wane yanayi zata zo?
Mai kyau? Ko akasin haka?
Wad’annan tambayoyin suke yawo kullum cikin kanta, da su take kwana take tashi, cikin tsumayin lokacin da alk’alami ya bushe akansa, don wata k’addarar tamkar ZANEN DUTSE ce… Babu wani abu da ya isa ya canja ta!
DAYA.
~~~
Ka bud’e zuciyarka ga wanda ba zai tab’a sawa kaji cewa ‘rayuwa tana da wahala’ ba.
🎶’Zani naje gidan ibada…
Ni da masoyi zamu zauna…
Ga wasu zasu kaini d’akin aurena!’🎶
Duk da girma irin na gidan sarautar KIYARI, babu lungu da sak’on da zaka kurd’a sautin wak’ar da ake gudanarwa daga can wajen kamun bikin bai shiga kunnenka ba, sannan ga mutane nan birjik! Tun daga bayi na cikin masarautar har zuwa tarin jama’ar gari da suke d’id’ikowa don gane wa idonsu shahararren bikin da aka fara gudanarwa a yau.
Biki na gimbiya kuma ‘ya mace ta biyu a gurin mai martaba ‘Ahmad Uba Kamsusi’, Haka nan kuma biki na farko da aka fara gudanarwa a gidan sarautar tun bayan zamanin da mai martaba ya gaji mahaifinsa.
Duk inda zaka duba ko ka kalla ado ne na k’awa anyi shi birjik cikin nau’i kala-kala don burge al’umma da kuma dangin ango wanda suma suka kasance jinin sarauta daga garin Sakkwato. Ba wai barin mutane ake su k’arasa can inda ake gudanar da
Kamun ba, amma duk da haka saboda wadata abubuwa kai ba zaka ce ba ko’ina ake bikin ba, don kalolin abinci yawo kawai suke tsakanin mutane kowa na zab’ar ra’ayinsa yaci ya cika cikinsa harda guzurin na gida ma, sannan kuma kid’an daya karad’e ilahirin masarautar ma ya k’ara zirga-zirga da kuma hada-hadar mutane.
A cikin wannan hayaniyar Maijidda na can tsaye ita da Suraj daga bayan hanyar da zata kai ka shamaki inda babu wulgawar mutane sosai. Hannunta rik’e yake da wani kwando mai cike da wasu k’anana abubuwa masu kyalli sai juya shi take cikin yatsunta.
“Dan Allah ki gaya min mana, me Baddon tace da kika gaya mata?”
Muryarsa ta tambayeta a hankali amma cike da zumud’i. Ta d’an cije lebb’enta kad’an tana kallonsa sannan tace.
“Me kake tunanin zata ce?”
“Wallahi ban sani ba tunda kinga ai ba saninta nayi ai sosai ba, kawai ki yanke dogon zancen ki fad’a min ko zuciyata ta nutsu…”
Girarta biyu ta had’e alamun rashin fahimtarsa.
“To meye duk ka wani tashi hankalinka ka san dai ai ba zaginka zata yi ba ko?”
Maganar tasa shi dariyar da bai shirya ba a lokaci guda.
“Zagi kuma Jidda? Wa yake zancensa anan? Kawai fatana Allah yasa ta amince dani ne.”
Jin haka yasa ta juya ga barin kallonsa sannan ta d’anyi murmushi kad’an tace.
“Ai kaima ka san da tace wani abu da ba zan tsaya anan ina sake maka magana ba.”
“Allah da gaske kike? Bata ce miki komai akaina ba?”
Wannan rashin fahimtar ya sake dawowa kan fuskarta, ta juyo ta kalle shi.
“Me kake tunani zata ce? ni fa kawai tace min ne ta san Babanka ya tab’a aiki a b’angaren Fulani kafin ya koma wajen mai martaba, bayan haka bata ce komai ba.”
“Haka ne…” Ya fad’a yana gyada kai.
“… zata sanshi, Baddo ai ta dad’e a masarautar nan, ina jin tun farkon zamanin Sarki Uba take ko?”
Ta d’aga kanta a hankali.
“Na san dai tun mai martaba na yanzu bai yi aure ba suka zo ita da mamanta.”
Ya sake gyad’a kansa sannan yayi shiru kuma, zuciyar Jidda ta d’an matse kad’an, ta zata a lokacin ko zaiyi mata zancen turo iyayensa ko kuma wata maganar auren da zata kaisu ga mataki na gaba kamar yadda ta dad’e tana sak’awa a zuciyarta amma kuma baice komai ba.
Yatsun hannunta na dama na kanannad’e cikin hannun kwandon ta d’an b’ata rai, Allah ya sani zuciyarta tana bashi wata irin yarda tun daga lokacin da ta fara saninsa kafin ma yace yana sonta, amma kwanan nan yanayin mu’amalarsu yana yawan zana mata ayar tambaya a tunaninta… Bata jin kuma zata jure hakan gwara ta fito kiri-kiri ta tambaye shi me yake nufi game da ita, amma zata bashi lokaci dai tukunna.
“Jidda.”
Muryarsa a hankali ta katse tunaninta, ta d’ago da sauri ta kalle shi sannan a lokaci guda tunaninta ya wargaje saboda irin kallon da yake mata, ta san Suraj yana da kyau kuma saboda haka ma take sonsa ko don ace saurayinta na da kyau… Don irin kyan nan da baya cikin k’abilar Hausa-Fulani illa irin jinsinsa na Shuwa-arab, amma me yasa kullum take k’ara ganin kyan nasa ne?
“Kin san me na taho miki dashi?”
Ya tambaya shima yana kallonta, sai ta sake k’ank’ame kwandon hannunta tana murmushi alamun dad’i kafin tace.
“Kace min fura.”
Ya girgiza kansa.
“Tanderi?”
Ya sake girgiza kansa.
“Awara? Dan Allah ya zama Awara?”
Ta fad’a tana langab’ar da kai had’e da k’ank’ance ido, hakan yasa shi dariya mai zurfi yana girgiza kai kafin ya mik’o mata ledar hannunsa.
“Allah ya amsa miki, Awara ce mai zafi ina zuwa gida na tarar Mama tayi.”
Ta karb’a da hannun dama ta bud’e, idanunta suka haska da kyallin murna da godiya sannan ta d’ago ta kalle shi.
“Jidda!”
Muryar Jamila data karyo kwana ta katse abinda shi da ita ke shirin fad’a.
“Yanzu tun dazu kina nan? Hankalin Baddo ya tashi an kusa gama wankan amarya, Jakadiyan Babba sai fad’a take ba’a kawo kyallin ba.”
“Kinga kije kawai ba matsala, Gobe zan shigo ai insha Allah.”
Cewar Suraj sanda Jamilan ta k’araso inda suke tsaye.
“To shikenan, Nagode, Nagoode!”
Ta fad’a da k’aton murmushi tana sake damk’e ledarta.
Shima ya mata murmushin, sannan ya gaida Jamila da ka, kafin ya juya ya tafi.
“Allah zaki ci fad’an Baddo, da kika san wajensa zaki tsaya ba sai ki kawo mata aiken ba tukunna.”
Jin haka yasa ta d’an b’ata rai tace.
“Ni ai bata ce min yanzu za’ayi amfani dashi ba shi yasa da na ganshi na tsaya…”
Sai kuma tayi murmushi, ta nuno mata ledar hannunta game da d’aga gira.
“Kin san me? Awara ya kawo min.”
Jamila ta ja tsakin ta bata shirya masa ba kafin ta fizge kwandon hannunta tayi gaba.
“Wallahi abinda kike baya kyautawa Jidda, nasha gaya miki da ace a wajen wata kike ba Baddo ba da tuni kinsa an dad’e da korar mu daga gidan nan, yanzu in banda sh*g*n kwad’ayi duk abinci da yake yawo a gidan nan me zaki yi da wata awara…”
Tana magana Jiddan na biye da ita, jinta kawai take yi don daga fad’anta har na Baddon ba wanda zai dameta, suna gamawa zata sami waje taci awararta, bata san kuma me ta manta ba bayan hakan.
“… Na rasa waye ya shiga kwakwalwarki ya goge miki sanin cewa a duniyar nan ba kowa ake yarda dashi ba, don wallahi bani ba na san ko ita Baddon ba son wannan Suraj d’in take ba.”
“Wai yaushe za’a daina zancen nan ne? tunda nace ni ina sonshi ba shikenan ba.”
Ta fad’a cikin kunkuni sanda dogarawan dake tsaye suka basu damar shiga babban soron da zai sada ka da kwaryar gidan sarautar inda ake gudanar da bikin. Jamila ta harare ta da gefen ido sannan ta girgiza kanta kawai.
Bayan tarin adon dake wajen idonka zai gano maka taron mutane birjik! Wand’anda ke zazzaune akan wasu tausasan dardumai kashi-kashi da aka tsara maimakon tebura, kowa cikin kwalliya sannan mafi yawansu rik’e da waya suna d’aukar wankan amaryar da ake gudanarwa daga tsakiyarsu, kan wani d’an dandamali da aka fitar masa da rariya musamman saboda bikin.
Amaryar, Gimbiya Aisha Ahmad Kamsusi, na zaune kan wani sabon turmi cikin shigar wata farar doguwar riga da lullubin farin mayafi yayin da tsofaffi dangin iyayenta ke ta kwara mata ruwan farar Humra suna zubo tarin addu’o’insu wanda ya had’e da yanayin wak’ar wajen ta yaren al’adarsu da aka kunna.
Jidda na iya hango fuskar Amaryar ta tsakanin matan dake kanta, ta sunkuyar da kai sai sheshek’ar kuka take, wani zaice ba itace mai d’agawar kan nan da zuba tarin rashin mutunci ga bayin masarautar ba kamar mahaifiyarta, Fulani Hafsatu, hamshakiyar uwargidan Sarki mai cika da izza.!
Allah ya sani tun zuwanta masarautar ranta baya son matar nan, saboda bak’in halinta da kuma bautar da kakarta keyi a k’ark’ashinta, bautar da tun kafin rasuwar mahaifiyarta ba irin k’ok’arin da ba’a yi akan ta bar gidan sarautar ba amma fafur Baddon tak’i, a cewarta yadda mahaifiyarta ta mutu k’ark’ashin kulawar masarautar haka itama zata koma ga Allah anan.
“Jidda tun d’azu muke nemanki, ina kika shiga?”
Muryar Sadiya ta fad’a sanda ta dafo ta daga baya.
“Wallahi Baddo ce ta aike ni can wajen Magajiya na karbo mata sak’o.” Ta bata amsa sanda Sadiyan ta tsaya kusa da ita.
“Taho muje ki zauna tare damu mana, ga inda muke zaune can ana ta hoto a wayoyin su Amina.”
Jidda ta juya ta kalli can inda ta nuno mata, darduma ce guda ta ‘yanmata irinsu ‘ya’ya ko jikokin bayin masarautar har da wadanda bata fiye ganinsu ba, dukkaninsu sun sha ado babu mai babanta su da sauran ‘yan bikin, don haka ne ma duk irin abincin da aka ajiye a kowacce darduma suma akwai a tasu, sai hayaniya suke yi suna d’aukan hotunan kamar yadda Sadiyan ta fad’a, zuciyarta ta d’an had’e kad’an, taji zata so ace itama tana cikinsu ana hirar, amma sanin abinda zai biyo baya yasa ta girgiza kanta.
“Kin san bana son rashin mutuncin k’awayen nan naki Sadiya, don haka kije kawai.”
“Haba Jidda, wai ta yaya ba zaki manta komai bane ba, wallahi yanzu babu me miki ko kallon banza tunda kun riga kun fitar da raini.”
Ta sake girgiza kanta.
“Allah kije kawai, tare da Jamila ma fa nake, ta tafi kaiwa Baddo sak’on yanzu zaki ga ta dawo.”
Daga yanayin Sadiyan bata so haka ba, amma sanin Jiddan ba canja ra’ayi zata yi ba yasa ta gyad’a kai tace.
“Toh shikenan sai mun had’u a cikin gida.”
Bayan ta juya, Jidda ta sake hangar wajen ‘yanmatan a karo na biyu kafin kuma ta
shiga neman Jamila ta cikin tarin hayaniya da kid’an dake tashi a wajen, sai dai duk irin hangen da take yi ba Jamila ba alamarta balle kuma uwa-uba Baddon da sune masu gudanar da tafiyar bikin.
Saboda haka ta juya don neman waje taci awararta, ganin kusan ko’ina da wulgawar mutane yasa ta nufi hanyar fita ta k’ofar yamma inda zata kaika ‘Cikin Gida’ ma’ana b’angaren iyalan Sarki da kuma Turaka da fadarsa ta zaman hutawa, sai dai kafin ta kai ga fita wani daga cikin masu rabon abincin yazo wucewa da katan-katan d’in ruwa don haka ta tsaya rok’arsa ya bata d’aya.
Kafin ya farka katan d’in idonta ya hangi sanda ake zubawa Amaryar wannan kyallin da ta karbo yayin da wani tartsasin wuta daga cikin wasu abubuwa da wasu inyamurai suka zo suka kafa tun safe ya shiga baibaye ilahirin wajen. Gud’a da tarin hayaniya ta sake rud’ewa, wajen yayi kyau sosai taji ya burge ta kuma ta san zata iya ganin Baddon yanzu don a matsayinta na Babbar Jakadiya dole tana wajen amma sai ta yanke shawara fara cin awararta tukunna don haka ta karb’i ruwan ta fita.
A bayan wani gini cikin tamfatsesen tsakar gidan ta samu waje ta zauna, anan d’in ma mutane ne ke ta zirga-zirga daga wajen bikin zuwa cikin b’angaren Fulani (mahaifiyar Amaryar) amma inda ta zauna saman tudun wani tanki ya shiga daga d’an lungu saboda haka ba kowa ne zai ganta ba sai hankali yaje wajen.
Ta bud’e awarar ta fara ci hankalinta a kwance, hannunta d’aya na wasa da ‘Fullo’ dake rataye a wuyanta kamar sark’a. A hankali kamar koyaushe idan ta kad’aita ita kad’ai kalaman mahaifiyarta na k’arshe suka shiga yawo a kwakwalwarta.
‘Bana son ki koma wajen dangin mahaifinki Jidda, nafi son kije ki zauna tare da Baddo, ba wai don ina son zaman inda take ba sai don ko ba komai in kina gabanta na san zaki tashi da irin tarbiyar data bani, watak’il ma wannan halin naki ya gyaru saboda wata k’addarar…’
Ta rufe idonta a hankali tana tauna wadda ke bakinta, amon muryar rad’au yake amsawa a kunnenta kamar yanzu aka yi ta, don tana d’aya daga cikin doguwar magana ta k’arshe da mahaifiyar tata tayi mata kafin ciwo yaci k’arfinta ya zamo harshenta ya nad’e har ta daina iya magana kwata-kwata.
A wannan ranar ne kuma ta bata ‘Fullo’ d’an zagayayyen dunk’ulen zinaren data mallaka daga wajen mahaifinta, tace mata mahaifina ya bata shi ne a ranar da aka saka ranar aurensu, don haka ta sanya masa sunan ‘Fullo’ wanda ma’anarsa shine ‘Baiko’ da fulatanci.
Bata san wace irin k’addara mahaifiyarta take nufi ba, amma Allah ya sani ita kanta ta matsu k’addarar ta k’araso ta canja akalar rayuwarta don ko kad’an ba jin dad’in zaman masarautar take ba, daga Baddo har Jamila hankalinsu yafi karkata ga aikinsu fiye da ita, shi yasa babu wayewar garin Allahn da bata kewar mahaifiyarta da kuma rayuwarta ta baya…
“Kin tabbata nan kuwa tace?”
Muryar wata mata data fito daga d’an nesa da bayan tankin yasa tayi saurin bud’e ido, tunaninta ya katse.
“Wallahi nan gurin tace Ladi, bakina da nata fa tayi min bayani, tace daidai bayan ginin nan malamin daya bada aikin yayi kwatance kuma in ya wuce gobe ba’a binne ba aikin ya lalace, to kema ai kin san kuwa ba zan kuskure ba, duba dai kiga ba kowa ko?”
Ba tare da ta san dalili ba, Jidda ta nad’e k’afafunta zuwa kan tudun sanda k’arar takun matar ya shiga kunnenta, taji alamun tayi ‘yan dube-dube kafin tace.
“Babu kowa, kinga dan Allah muyi sauri mu hak’a mu bar wajen nan, bana son wani ya gan mu.”
“Ki kwantar da hankalinki Ladi, nace miki babu abinda zai faru ba mai ganinmu, kudinki kuma cas! Zaki kwana dasu a hannu don Jakadiya bata da sab’a alk’awari.”
K’arar hak’a ta shiga kunnen Jidda kafin wadda aka kira da Ladin ta sake magana.
“Hankalina ne bai kwanta ba jin yawan kud’in nan da za’a bamu, tunani nake in babu hatsari a cikin aikin nan Fulani ba zata fitar da kudi haka ba.”
D’aya muryar ta ja tsaki.
“Ke fa matsalarki gidadanci, to wallahi Jakadiya ta tabbatar mun in muka bada had’in kai fin haka ma zamu iya samu, don Fulani babu abinda take so illa ganin k’arshen MADAKI, kuma ni kaina shaidace zata iya komai akan hakan don wannan had’in da kike gani tace tun daga can k’asar Gabon aka karb’o mata shi.”
Jidda ta had’iye yawu, jin cewa asiri suke binnewa a wannan lokacin kuma cikin umarnin Fulani da Jakadiya, tukunna ma wacce daga cikin Jakadiyar? Ba dai Baddonta ba? Ta sake had’iye wani yawun tare da ragowar awararta sanda muryarsu ta cigaba da magana k’asa-kasa.
“Kin san jikina na bani Fulani zata sami abinda take so wannan karon, saboda kinga na san tasa anyi masa na kiranye mai k’arfi, don Jakadiya tace dole ne zai dawo gida wannan karon sai dai ba’a san yaushe ba. Sannan wannan kuma tace daya sako k’afarsa cikin gidan nan ba zai sake mararin komawa ba, wanda za’a binne wani satin kuma a cikin lambun bayan turakar mai martaba shi kuma na k’ulle bakinsa ne, tace in har aka same shi, to bai fa isa ya sake mararin komai ba bayan umarnin Fulanin.”
“Cabd’ijam!” Cewar Ladin.
“Wai yanzu duk taurin kai irin na Madaki shine zai sauko har ya dinga biyewa Fulani? Anya kuwa Hadiza? Abinda ba’a same shi tun da ba kina ganin zai yiwu yanzu?”
Hadizan ta sake jan tsaki.
“Me ko zai hana shi yiwuwa? Aikin baya da aka kwantar dashi jinya har ta sami wad’annan kud’ad’en ke kika hana shi yiwuwa? Balle yanzu da aka sami wannan garantin malamin… Ance shekararsa saba’in kenan yana wannan aikin kuma ko sau d’aya bai tab’a bada maganin da bai ci ba.”
Jin Hadizan na neman hasala an tab’a uwargijiyarta yasa Ladin tace.
“To ni dai ta kud’in da za’a bani nake, don haka in kina yiwa Allah muyi mu rufe mu bar wajen nan kan wani ya hange mu.”
Har suka gama tone-tonensu kusan minti goma suka rufe suka bar gurin, Mairo bata motsa daga inda take ba, kuma cikin sa’a babu wadda ta lek’o bayan tankin a cikinsu balle su ganta, suka bi ta d’aya hanyar da suka shigo suka tafi cike da jin dad’in kammala aikinsu.
Ba shiri kuwa ta ture ledar awarar gefe sannan ta sauko ta zagaya ta bayan tankin, da ace bata ji sanda suke kokawar maida wani dutsen interlock ba, babu ta yadda zata iya ganin wajen da suka gama hak’awar don sun mayar da komai tsaf sun rufe sai d’an burbud’in k’asa kawai akansa.
Ta juya kowanne gefenta taga ba mai ganinta, sai kawai zuciyarta ta d’arsa mata da ta tone taga me suka binne, tunda ba abinda zata yi kuma ma ai bata tab’a ganin yaya asiri yake ba, saboda haka ba tare da ta bari zuciyarta ta yanke tunani na biyu ba ta nufi wajen.
Ta tsugunna tasa k’arfi ta d’age dutsen, sannan da saman robar ruwan dake hannunta ta sake hak’o k’asar da bata gama dank’arewa ba, sai da tayi d’an rami mai zurfi sannan idanunta suka ci karo da dank’areriyar layar dake kwance a ciki.
Sai a lokacin kuma gabanta ya d’an fad’i, zuciyarta ta buga, taji kamar wannan lokacin ne da take shekara biyar in tazo d’aukar takalmin sallarta a b’oye don nunawa k’awayenta.
Kar ki jawa kanki bala’i Jidda Babu ruwanki…
Wata zuciyar ta shiga kokarin yi mata gargad’i amma d’aya b’arin zuciyar tata yaja tsaki ya kore hakan, saboda haka ta had’iye yawu kad’an sannan tayi bismillah a fili tasa hannu ta ciro ta.
A take wani irin sassanyan k’amshi kuwa ya sulale zuwa hancinta, tsadadden k’amshi mai dad’i irin wanda ba sai an tsaya tone-tone ba ta san bata tab’a jin irinsa a rayuwarta ba.
“Anya kuwa wannan asiri ne?…” Ta tambayi kanta fili.
“… Na zata ai asiri wari yake.”
Layar ja ce jawur! An nad’e ta da wasu zarurruka kala-kala kusan guda goma, ta sake kallon hanyar da matan suka bi da kuma bayanta kafin hannunta ya shiga warwarewa babu tunanin abinda zai iya samunta.
A ciki farar takarda ce k’al anyi mata rubutu da abinda babu shakka jini ne daga irin bushewarsa, sai dai bata iya karanta komai a cikin dogon rubutun ba, don in ma yare ne to ta tabbata yaren aljanu ne don a duniya bata ga mahaukatan da zasu zauna su kirkiri irin wannan rubutun a matsayin yarensu ba.
Sai dai me? Daga can k’asan rubutun, idonta ya sauka akan sunan da zata iya karantawa, wanda aka yi shi b’aro-b’aro da harafan boko cikin manyan bak’ake.
IBRAHIM AHMAD MADAKI!
BIYU.
~~~~
Ranar da Maijdda ta fara sako k’afarta cikin masarautar KIYARI bayan rasuwar mahaifiyarta da sunan zama ba ziyara irin ta baya ba, kakarta Baddo wadda ta kasance babbar Jakadiya ta sake biya mata bayanin tsarin masarautar wanda a baya bata fiye maida hankali akansa sosai ba don bai shafe ta ba.
Tayi mata bayani dalla-dalla na yanayin gidan sarautar da kuma iyalan dake cikinsa… Wanda har a lokacin bata ga amfaninsa a wajenta ba sai a yanzu da take son sanin waye mutumin data hak’o wani b’ari na k’addararsa jiya.
Mai martaba Ahmad Uba Kamsusi shine d’a na farko a wajen mahaifinsa cikin ‘ya’ya tara wanda cikinsu uku ne kawai maza, ma’ana k’anne biyu ne kawai dashi maza duka sauran mata ne. Bayan rasuwar mahaifinsu sanadiyar wata ‘yar mashashshara, sai ya gaji mulkin a matsayinsa na Babban d’a kamar yadda yake a al’ada da kuma addinance.
K’annensa mata duka sunyi aure kuma bayan su mazan ma duka suna da ‘ya’ya wanda suke sa’anin na mai martaban. Iyalan Sarki guda uku ne, amma banda Fulani wadda ta kasance uwargida, za’a iya cewa sauran guda biyun a suna suke kawai matan sarki amma basu da cikakken iko game da abubuwa da yawa.
Fulani Hafsatu, mace ce wadda kallo d’aya zaka yi mata ka sanya ta cikin jerin manyan mata masu iko, izza, dukiya da kuma ji da kansu. Fara ce k’al mai d’auke da ‘yan k’ananan billen da akewa lak’abi da ‘tsugunna kaci doya’ idanunta na d’auke da wani irin kwarjinin dake sadda gwiwar duk wani na k’asanta, fuskarta kawai ta ishi mutum cikakken bayanin kalmar nan ta ‘isa’.
‘Ya’yanta biyar sune a jere cikin lissafin manya a gidan don sai da ta gama haihuwa tsaf kafin mai martaba ya samu damar fara aure-aurensa. Saifudden ne Babba wanda yake rik’e da sarautar ‘Turaki’ don haka ke kiransa da haka, sai Nadiya mai bi masa, Umarul-Faruk ya biyo baya kafin Aisha (Amaryar da ake biki) da kuma autarta Safina.
Haj. Maimuna, matar Sarki ta biyu tazo ne sanadiyar giftawar rasuwar mijinta wanda yake aboki ga shi Sarkin kafin lokacin da ya karb’i mulki, kwarai Fulani ta tada hankalinta lokacin auren kuma babu irin fafutukar da bata yi ba don canja k’addara amma k’arfin ikon wanzuwar ‘ya’ya uku ya danne duk wata dabararta. Na’ima itace Babba a ‘yayan Haj. Maimuna sai k’annenta Amira da Amina. ‘Ya’yan Haj. Maimuna uku tare da mijinta na farko, maza biyu mace d’aya wanda suke can wajen dangin mahaifinsu, amma a masarautar Allah bai bata namiji ba.
Nene Hadiza, mace ta uku a turakar mai martaba tazo ne a matsayin kyauta ga Sarki daga wani aminin mahaifinsa Hakimin katsina a lokacin da ya hau Sarauta, don haka ita d’a d’aya gareta wanda bai fi shekara goma ba mai sunan Sarkin da kansa Ahmad.
Dukkanin wad’annan matan suna rayuwa ne a cikin gidan masarautar amma babu ruwan kowacce da kowacce, gwara ma tsakanin Maimuna da Nene Hadiza anyi shiri kad’an a baya wanda ya ruguje daga ranar da Nenen ta haifi d’a namiji. Amma Fulani, bata bi ta kan shirgin kowacce balle kuma ‘ya’yansu, ta tattare komai daga ita sai nata kawai, sannan ita ke da iko akan kusan komai da ya shafi cikin gidan sarautar kuma duk yadda kowacce a cikinsu ke ji da kanta haka suke hak’ura subi tsarinta, don in ba Mai martaba da kowa ke shakkarsa ba, Fulani bata saurarawa kowa.
Hakan yasa zamantakewar gidan ta tab’arb’are don idan ba lokuta irin wanda mai martaban kan tara su gabad’aya a rumfarsa ba, za’a iya cewa wani zai shekara ma bai ga d’anuwansa ba saboda hadaniyar komai da shige da fice tana b’angaren Fulani ne inda su ba zuwa suke ba.
Tun kafin zuwan Jidda har kuwa bayan fara rayuwarta a gidan, wannan shine rayuwar gidan sarautar KIYARI kamar yadda kowa ya sani.
Abinda a yanzu bata sani ba shine waye IBRAHIM AHMAD MADAKI? Meye alak’arsa da Fulani da har take b’ata lokacinta wajen binne asiri akansa? Kuma har a irin wannan lokacin da take cikin hayaniyar aurar da ‘ya? Me yasa ma ya samu sunan mai martaba a sunansa amma kuma babu jigon sunan zuri’arsu na ‘Kamsusi’?
“Kinci wannan?”
Muryar Sadiya ta dawo da Jidda daga tunaninta sanda ta d’auko wani abu mai kama da dunk’ulallen nama.
“Sun saka masa tafarnuwa da yawa wallahi ba dad’i.” Ta karasa tana fitar da ragowarsa daga bakinta.
Suna zaune ne kan wani d’an tudu daga can k’arshen tamfatsetsen filin dake cikin gida, ma’ana k’aton filin daya had’a fuskokin ginin kowanne b’angare na matan sarkin da kuma nasa b’angaren hutawar daga tsakiya, b’angaren Fulani shi yafi kowanne girma sai na Maimuna da Nene wanda yake iri d’aya, dogwayen gine-ginen da suka sha k’awa irin na zamani masu d’aukar hankali don ga fitilu nan ko’ina a cikinsu.
Duk girman filin cike yake da hayaniyar d’imbin jama’ar dake ta kai da kawowa a b’angaren Fulanin, don yau rana ta biyu gagarumar walimar dare ce‰ aka had’a a can wani waje ba masarautar ba, don haka daga mata har maza, manyansu da yara na b’angaren ita Fulanin da kuma dangin mai martaba dana k’annensa kowa yayi shigar kece raini sai fitowa ake don wasu har sun fara tafiya can waje inda ake faka motoci.
K’anwar mahaifiyar Sadiya tana da babbar hanya a b’angaren Fulanin, don haka ta hanyarta Sadiya ta samo musu abincin da akayi musamman don bak’in Fulanin, saboda ita tun wayewar garin Allah bata sa Baddonta a ido ba ma balle har ta san me taci, Jamila kuwa ba ta ita take yi ba tana can cikin k’awayenta itama.
Inda suke zaune na fuskantar k’ofar b’angaren Fulanin inda hayaniyar mutane take, don haka sai shilla k’afa suke cikin iskar dake kad’awa saboda ba ga su kad’ai ba lokacin yayi mutuk’ar kyau da dad’i ga duk wanda ke wajen… Ba koyaushe ne ubangiji ke azurta duniya da yanayi irinsa ba.
“Allah naso muma zamu iya zuwa wajen nan, da ba haka ba.” Cewar Sadiya.
“Me zaki je ki musu? Keda ba danginki ba?” Jidda ta tambaya tana k’ok’arin b’are wani alalan ganye.
“Kallo zanyi mana, kema kin san wallahi ba tantama wajen ba k’aramar had’uwa zaiyi ba, kuma za’aci abinci iyakar dad’i.”
Jidda taja d’an guntun tsaki.
“Allah ya sawwak’e miki, wannan da kike ci k’asa ne? Ko yanzu ma fa a k’oshe kike.”
Ta kai alalan bakinta sannan tace.
“Ni kwalliyar Amaryar kawai nake so in gani.”
“Tab! Waya gaya miki tana gidan nan? Ai tun shekaranjiya suka koma wani hotel ita da k’awayenta wai ba zata iya zaman cikin mutanen nan ba.”
Jiddan ta juyo ta kalle ta.
“Da gaske? Amma tayi asara wallahi to meye dad’in bikin? Kawai tazo taga mutane ta koma wani wajen kamar ‘yar gaiya?”
Sadiya ta kai cinyar kaza bakinta.
“Rabu da masu kudin banza ke dai… Kalli waccan yarinyar kiga, ta tsaye a kusa da Namijin nan…”
“Na ganta… Ba mai green kayan can ba?”
“Ita, wallahi tun shekaranjiya ranar k’unshin nan shigarta ke burge ni, ‘yar k’anwar Mai martaba ce a Abuja suke.”
“Ke wai kin san duka zuri’ar gidan nan ne?”
“Kin manta su Hajiya (kakarta) a falon Fulanin suke aiki, shi yasa idan naje nake yawan ganin mutane. Kalli ga yayar Amaryar can ma ta fito, Nadiya.”
Ta fad’a tana nuna wata farar mata ‘yar gayu, sanye cikin wani rantsatsatsen lace da kwalliyar da ba shakka ta canja kammaninta, tana rik’e da hannun wata ‘yar kyakkyawar yarinyar da ta kasance ‘yarta kuma jika ta farko a gurin Fulani da Mai martaba, waya take tana ratsawa ta cikin mutanen da mafi yawancinsu ke gaisheta yayin da wasu maza ke binta rik’e da manyan ledoji nik’-nik’i na kaya.
Jidda ta bisu da kallo har zuwa hanyar da zasu fita harabar motocin, sannan ta sake jan tsaki kad’an, bata jin a duniya zuciyarta zata so wani daga jinin Fulani.
“Ni wallahi haushin bikin nan nake ji, an rik’e su Baddo da aiki tunda aka fara bata zama balle ta huta sosai, kin san jiya har na gaji nayi bacci bata dawo ba, sai Jamila ce kawai ta lek’o wajen sha biyu saura ta sake komawa, sannan ana yin asuba kuma Baddo ko laziminta bata yi ba ta fita.” Ta k’arashe da wani tsakin.
“To ai kinga sune masu bada umarnin abinda za’ayi, shi yasa nace miki kizo muje cikinmu kinga jiya sai wajen sha d’aya fa muka bar wajen nan, damu aka tashi in gaya miki kuma har kusa da amaryar muka je.”
Jidda tayi shiru kawai, don Allah ya sani har cikin zuciyarta tana son komawa cikin sahun ‘yanmatan musamman jiya ma data gama bilinbituwarta ita kad’ai, amma hakan ba zai yiwu bane.
Tun farkon zuwanta masarautar ne Baddo ta had’ata da Sadiya, jikar aminiyarta da suka shafe shekara da shekaru suna aiki a masarautar tare, jininta ya had’u dana Sadiyan sosai suka saba a d’an kankanin lokaci, matsalar shine Sadiya tana da tarin kawayen da suka taso tun yarintarsu tare a cikin masarautar, wanda k’ungiya guda ne sun kai su goma sha takwas.
A cikinsu kuma akwai wasu mutum hud’u da suke ganin sunfi kowa ido da kwalli, su suke juya kowa don sai abinda suka ce ake yi saboda suna da baki, ita kuma Jidda babu wanda yake mata ta kyale balle har yasa tayi abinda bata yi niyya ba, hakan ya janyo banbantar ra’ayinsu, tun daga musun baki kad’an-kad’an har aka fara fad’ar maganganu.
A lokacin bata fi ‘yan watanni da zuwanta ba, daga k’arshe ma ita Jiddan ta haddasa fad’an gaske wanda ta yiwa biyu daga cikinsu dukan tsiya har saida manya suka shigo ciki. To ta yaya kuwa zata iya yarda ta sake komawa cikinsu?
A hankali hannunta ya kai kan ‘Fullo’ dake rataye a wuyanta, bata san adadin yadda take son abin nan ba, don bayan cewar mahaifiyarta ce ta bata shi, shi kad’ai ne kuma abinda baya tab’a barinta a kowanne hali na duniyar nan, koyaushe yana tare da ita kamar mutum da inuwarsa.
A daidai sannan, tunanin data yini tana son ta tambayi Sadiyan ya gifta cikin ranta, ta juyo da sauri ta kalle ta sai faman taune k’ashin hannunta take tace.
“In tambaye ki wani abu?… Idan mutum ya tono asirin da aka binne, wani abu yana samunsa?”
Sadiya ta zare ido.
“Ke kuwa me yazo kanki? Asiri zaki tone?”
Ai na riga ma na tone!
Taji kamar ta fad’a mata hakan amma sanin halinta na mugun tsoro yasa tace.
“Haba dai kawai so nake in sani ne, kwanaki a makarantar dare ba kince min a ajinku anyi muku bayanin tsubbace-tsubbace ba.”
“Eh, to amma ni wallahi a shari’ance ban san wannan ba, a hankalina dai na san ba lallai a rasa abinda zai sami mutum ba, tunda su kansu masu yin asirin zaki ji ance in suka kuskure wajen sakawa wani abin zai iya samunsu.”
Ta d’anyi shiru tana cigaba da kallonta kafin kuma ta juyar da kanta zuwa inda mutanen gabansu ke raguwa saboda tafiya da ake tayi.
“Ki daina irin wannan tunanin Allah Jidda, wani in yaji sai ya kalle ki da wani abun.” Cewar Sadiyan.
Bata ce mata komai ba don hankalinta ya yarda da abinda tace, tunda har ta tone layar jiya ta k’ona ta akan gas d’in kitchen d’insu babu abinda ya same ta, to ta tsallake koma meye kenan sai dai ma taimakon wanda aka yiwa da tayi, don haka hankalinta ya koma kan maganganun matan nan na jiya… Sunce anyi masa asirin Kiranye a baya, wannan ta san ba lallai ta san inda yake ba don k’ila ma ba a cikin masarautar nan suka binne ba, amma kuma kamar sunce akwai wani…
‘…wanda za’a binne wani satin kuma a cikin lambun bayan turakar mai martaba, shi kuma na k’ulle bakinsa ne, tace in har aka same shi, to bai fa isa ya sake mararin komai ba bayan umarnin Fulanin.’
Rad’au tunaninta ya dawo mata da wannan zancen, kuma a take ta yanke shawarar sake tone wadda zasu saka d’in tunda dai babu abinda zai same ta, watak’ila ma Allah yasa taje wajen ne jiya don ta zama silar canja k’addarar ko waye IBRAHIM AHMAD MADAKI.
Matsalar yanzu itace tun farkon zuwanta masarautar nan, ranar da Baddo ta gabatar da ita wajen Fulani bata k’ara taka kafarta cikin b’angaren ba balle har ta san inda wani lambu yake, sannan ma bata san kowa ba balle ta iya gano su waye wad’annan matan har ta san ranar da zasu binne asirin.
“Na manta ban samo mana ruwa ba, kinji cikina kuwa…”
Muryar Sadiya yasa ta juyo ta kalle ta, a lokaci guda tunaninta ya haska mata wani abu… Ta hanyar Sadiya zata iya gano
inda matan nan suke, sannan ita kanta kuma hanya ce tiryan-tiryan da zata kai ta ko’ina a b’angaren masarautar! Ko’ina na nufin har inda zasu bi suje wajen lambun ba tare da an gansu ba!

Leave a Comment