1
✍MMN YAZEED
07014197556
Santalelan saurayi ne mai kimanin shekara 35 yafaka mutarsa a kofar gidan su ya ziro kafafuwan shi farare tas kamar ka taba jini ya futo,
yafara taku d’aid’ai ya doshi hanyar da zata sadashi da d’an d’ashe shen gidan nasu, yana taku dai dai irin na manyan sojoji yayi sallama abakin falon,
can daga cikin falon aka amsa mai, sallama dattijo ne mai kimani shekara 60 yana zaune tare da matansa guda uku duk suka waigo da murmushi akan fuskan su sabanin guda 1 data had’a rai daga cikin matan, ya karaso cinkin murmushi ya zauna yace sannunku da hutawa. duk suka amsa yace Abba ina wuni yace lfy lau, babana daga ina ka futo yace naje gidan babane. ka kyauta yaka same su. lfy lau, sunce agaishe ku yace muna amsawa wani kyakyawan yaro ne, ya rugo da gudu ya fada jikinsa yana fadin abba faruk kaga momy zata zaneni ko, ya rungumo shi yana fadi mekayi mata, yace waitace na dameta da surutu. Faruk ya fara fada bawa da bakinsa za’a hana shi magana ne. hjy safyya tace to masu da ai wannan mijin namu bayajin mgn hjy aisha wadda suke kira da momy tace rabo da shi dan allah aishi banzai gane ba in banda yawon bin kasashe me ya sani. shedai faruk ko sauraron su beyiba yanacen ya duka satin yaron yana cemai my son ka kwantar da hkln ka baxan bari ta dakekaba, zo muje dakina bama zaka koma dakin ba bare tace ka dameta.
yaron yace abba faruk idan dady ya dawo be ganiba zaimin bulala. Waye dadyn naka, ya taba ka yagani saina zane shi .yaron ya zaro ido ya ce zaka iya zane shine faruk yace sosai makuwa yaron ya kalkale da dariya yace idan ya dakeni saina kiraka ko. yauwa may son ashe ka gane, toh tashi muje.
nan suka mike yadauke shi suka nufe dakin faruk suko su hjy safyya da Anty amarya suna ta tattaunawa akan shakuwar faruk da yaron itako hjy Aisha wato momy banda hararar faruk ba Abun da take har alhaji ya lora da haka yace Aisha lfy kuwa. lfy lau alhaji meka gani. yace a,a Amman dai ni abinda nakeson kigane kirage nunawa yaron nan halin ko in kola, kirinka janshi ajikin ki. mikiwa tayi tare da fadin alhaji kenan saikace wani dan karami yaro, toh goyashi zanyi ne koko mezan mai, sa annin shifah daga mai yaya 3 sai mai 4.
tayi daki tabar alhaji yana fadi Allah ya shiryeki Aisha sudai su hajiya suna ta darawa.
TUSHEN LABARI
Malam faruku matawale babban malami ne kuma sananne agarin kano yana da matarsa 1 Wanda suke kira da inna sun haifi yara uku dukka ninsu maza ne Ahmad shine babba, sai mai binshi yusuf sai karamin su wato usman kasan cewan malam faruku bai samo karatun boko mai zurfe ba saiya ci alwashin in Allah ya yarda yayan shi zasuyi, dan haka ya jajirce da taimakon mahaifiyar su wacce suke kira inna kuma Allah yacika masu burin su wada dukkan ninsu suna aikin gwamnati yusuf wadda kasance da na 2 acin yayan malam faruku sai ya kasance ya fesu daukaka da tarin dokiya kasan cewan malam faruku malami ne da yasan abinda yake bai nunawa yayan shi ban banciba suka taso da matukar San junan su ayanzun haka alhj ahmad yanada mata 2 da yara 7 shikuma alhj yusuf matan shi 3 yara 6 alhj yusuf shine mahaifin faruk wadda yaci sunan mahaifin su wato malam faruku sai karamin su alhj usman yana da mata 1 da yara 3
gidan alhj yusuf gidane da ya ginu akan tarbiya, yara da manya kowa na girmama kowa hjy safyya itace uwargidan alhj yusuf tana da yara 2 Sulaiman shine babba yana da mata 1 da yara 2 sai hafsat itama tayi aure yaranta 3
hjy aisha itace ta 2 yaran ta 3 faruk shine babba maibin shi aminu shi aminu yayi aure da dan shi 1wannan dalilin yasa mahaifiyar su hjy aisha take matukar jin haushin faruk sabuda yaki yin aure acewarshi shi har yanzon baiga wacce tamai ba duk da yawace yawacen kasashe da yayi adalilin karatun shi ayanzun haka dai ya kammala karatun shi ya zama cikakken soja Aminu kuwa yana zaune da matarsa anan cikin gida mahaifin su haka kuma akwai shakuwa tsakanin faruk da abdallah yaron kaninshi aminu sai karamar su mena yanzu tana shekara17 .
anty amarya ita takasace amaryar alhj yusuf data 1 aliyu tundaga shi bata kara haihuwa ba yana shekara10
faruk tunda ya dauki abdallah suka shiga daki basu suka futo ba saida aka kira sallahn mangariba sannan suka futo lokacin falon bakowa sai meena zaune tana kallo. ke mekike har yanzon kinanan, tashi kije kiyi sallah dan ubanki. afurgece tamike ta nufi daki dan balakin tsoron shi sukeji saboda masifan faruk ko aminu dake binshi be bariba. faruk narike da hannun abdallah suka doshi kofar fita domin zuwa masallaci, nan sukaci karo da aminu yafuto shima zashi masallahci. a’a yaya dama yaron nan yana wajenka ne. eh menene a’a bakomai nadauka yana wajen su momy ne.
ka hanashi zuwa gun sun ne . yaya naga ida yaje saiya wuni yana sasu surutu dama shiyasa nace yana maganar yana sosa keya. dakata aminu kaga daga yau karku sake dukan shi akan surutu, lfy ce da beda lfy da be yiba, kuma kace ma maman shi, nace karta kara dokan shi. yace angama ranka ya dade. da haka suka isa masallaci saida akayi ishai su kadawo bayan sunci abinci sunkare yace toh my son tashi kaje ka kwanta kaga gobe akwai makaranta ko. ni banajin banci fah abba a’a maza katashi karka makara . nandai ya tashi bada sanran shiba yanufi dakin maman shi shiko faruk daga nan falo alhj yawoce haka al adan gidan alhj yusuf take da daddare suna zama hira da iyalan shi yatarar da sunata hirar su suna dariya ya nemi wori ya zauna akasa bayan sun sha hirarsu sai alhj ya waigo gun faruk babana waikai baka sha,awan kayi aure ne? maganar tazowa faruk abazata dan haka ya dirirece yarasa mema zaicewa Abba ne .a da idan zaimai magana makaman cigar wannan baya mai acikin mutane kamar haka.
waibada kai nake magana bane, ko Baka jine? inaji alhj ya hausan kanaji amma kiyimin shiru. furuk ya dukar dakai zanyi ne abba, ka kwantar da hankalin ka . kamar yaya nakwatar da hankalina karka bari fah raina yabaci, nagaji da ganinka ahaka indai Baka da lfy ne kafada anemar ma magani, amma ninafara gajiya da ganinka haka. hjy aisha ce tasa baki ai alhj asamu ko wacece ahada shi da ita .hjy babba tace a’a baza ayi haka ba adai karamai lokaci.
tun yaushe nake samai lokaci, alhj ne yake fadin haka cinkin fada harcewa nayi yaje gidan yaya ahmad yazaba acikin yaran gidan amman ko kala baice minba.tokai faruk meyasa baka jeba? alhj yace ba magana ake maka bane, karka maidamu en iska. yace abbba aibasai najeba nariga ai nasansu. yace au toh waceka zaba acikin su ukun?
ban zaba ba abba. baka zaba ba? alhj ne yayi tambayan ciki bacin rai toh meye dalili ? faruk ya dada dukar dakai yace abba ai sun tsofa. duk falon suka kwashe da dariya banda hjy aisha faruk ya dada kulewa yana ganin ansa shi atsakiyar kannan shi suna mai dariya faruk yace kai kutashi kubar nan. alhj yace baza su tashiba, idan kayi zuciya kayi aure .zuciyar faruk kamar ta faso ta fito dan bakin ciki 🏇🏻
[6:34PM, 11/6/2016] +234 701 419 7556: 💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞
2
✍MMN YAZEED
07014197556
Alhj yace toh yanzun me kake nufe, kana nufin sunma tsofa kenan?
yace kuma dai ai da kunsani kunyimusu aure tuntuni, yanzun xfah duk sun wani yamushe.
suka kara kwashewa da dariya bandan aminu da ya wjuyar da kai yana dariya babu sauti dan gudun kar yaya faruk yagan shi meena kuwa tasa kanta acikin hijjabi tana dariya
hjy aisha ce tace kuje ikon Allah wai talle keyiwa audi gori.alhj yace tunda kadawo ai sai ka aurar da dasu.
kai faruk kaji tson Allah yanzo dan wulakanci su Hafsat dinne suka tsofa kana ganin yan mata masu ji da kansu.anty amarya ce ke fadi haka tare da murmushi akan fuskarta.
dan Allah abba kabar maganar su zan nemi wata nan bada dadewa ba kansa aduke.
nagaji da sama lokaci gidan babanku usman ma ai akwai yan mata, kaje cen ka duba .
abba ai duk kalansu daya. toh shike nan amma inason kasini tun ina kebeka yau har nayi maka maganar cikin yan uwanka ka kiyayi ranar da zanma mai gaba daya.
in Allah ya yarda ma haka bazai faruba inji hjy babba.
da haka hirar tasu ta tashi.
bayan kwana biyu faruk tafe cikin shirin shi na zuwa warin aiki yayi sallama dakin momy daga ciki aka amsa yashiga ya zauna ya gaisheta ta amsa ba yabo ba fallasa momy zatafi. adawo lfy tace atakai ce.
momy waike saiki rinka cemin adawo lfy bazakiyi min ardu,a ba.
ai ita nama .
wlh wannan ba ardu,a bane.
toh me kake son nace maka .
cewa zakiyi Allah yatsare ya kuma bada sa,a.
toh Allah ya tsare ya bada sa,a.
ameen ameen,yau bazan dawo da wuriba zan wuce gidan baba.
au ka canza shawara kenan da kuma kace sun tsofa.
a,a niba gunsu zanjeba wajen nura zani. kaidai kasani.
ya juya yatafi yana tunani azuciyar shi waisu dasuka dage sainayi aure saikace natare masu wani abun hard a momy ita da ada ko gaishe ta nayi dakar take amsawa saboda wai kuya ta yayan fari amma ayanzun ta ware har tana min maganar aure, Allah ya hadani da irin matar da ke mafarkin samu na huta da surutu.
wuraran karfe biyar faruk ya baro wurin aiki ya doshi gidan wan mahaifin shi yashiga gidan sai ga hafsat anata karairaya ansa matsatson kaya da dan gyale azuciyar shi yace ji wadda ake tunanin ni zan aure ta Allah ya kyauta
ke zo nan.
takara so atsora ce dan baza ta mance yaya faruk ba,
dan ba imani gareshi ba
ina zaki haka?
zanje bikin kawata ne.
kice zaki fatty.
a,a yaya wlh ba faty zani ba.
ya kai mata duka ni kike karyatawa wuce gida ki canza kaya.
ta wuce tana kuka yabi bayanta
alhaji ahmad yana zaune a falo saiga hafsat tana kuka ke lfy kuwa.
yaya faruk ne ya dakeni wai daga yaganni zanfita yace wai zani faty
bata rufe baki ba saiga faruk yashigo tare da sallama alhj ya amsa masa tare da murmushi maraba da babanmu faruk ya zauna tare da gaishe shi ya amsa ya mutanen gidan naku. lfy lau, baba wadannan yaran baza ayi musu aure bane alhj yayi murmushi yace babana kenan kadai gaji me sunan naka sosai shima jiya da naje harna tashi maganar shi kenan xkuma kaga sunada tsayayyu can ma gidan babanku duk xsuturo mana yaran da suke son aure kuma mungama binkece amma na dakatar da maganan ne dan yusuf yazo min dawata magana, ban saniba ko ya sanar maka? a,a baba wacce magana ce?
wai da yana tunanin ko zayi yar gida.
eh yafada min .
toh wani shawara ka yanke, nasan dai ba kunyata kakeji ba dan bamu fara haka dakaiba kuma banason mufara.
baba yaran ne duk kunbar su sun girma agida. alhj yayi dariya sosai yace inna fahimta kana nufin sunma tsofa,
yayi murmushi irin nasu na manya yace babana kaima fah ka tsofa. furuk yayi dariya yace baba aini namiji ne . toh kodai yar secondary zamu samo maka? dai dai nan nura ya futo yana fadin kai dan rainin wayo ne tundazon nake jiranka. nura yaron alhj ahmad ne shine na 3 yayyin shi guda buyu mata ne suyi aure sai sai mai binshi salisu da kannan su mata su uku shima nura yayi aure yaran shi 2 yana zaune agidan mahaifin shi kafin ya karasa ginin shi ya tare furuk da nura tare suka taso kowa yasan sirri kowa basa boyewa juna komai. alhj yace yauwa nura zo ka zauna.bayan nura ya zauna. dama akwai tam bayan da zanma.
toh baba yafada tare da gyara zama. wai wace irin mata zaku aure ne ?
nura ya fahimci inda alhj yasa gaba.
yayi dariya ya dukar da kai yana dan sosa keya abba wai da muna neman wadda zamu karashe rainon ta ne, ko yar secondary ce.
toh toh na fahimta kuma kana da gaskiya babana,amma abinda nake so dakai karku ja mana lokaci kaga su hafsat suna da tsayayyu baza asa lokaci mai tsowo ba kuma baza atabayi baka ba rana daya za ayi, dan na fahimci kasa wasa a al amarin ka.
nura ne yayi magana baba insha Allahu wannan karo ba wasa. toh ai muna son haka, baba yanzun ina zaku, faruk ne ya dago kanshi domin tunda nura ya fara wa alhj magana faruk ya dukar da kanshi . dama cen gida zamu .
toh adawa lfy
suna fita faruk yafara hararar nura suka nufi motar faruk bayan sun hau titi nura ya waigo yaga faruk sai shan kamshi yake yace gafara malam dan kasamu na rufa ma asiri kake fushi.
ai da nagaya maka ra,ayi na bance kagaya ma baba.
aida kasani ka kar yata ni kawai agaban shi kace karya nakeyi, kaga sai subaka wacce suka ga dama komai tsofan ta.
faruk ya waigo ya kalle nura fuskar shi da murmushi toh saime, ina ruwanka,
kaini nama samu matar da zan aura.
karya kake wlh,kai zaka iya tunkaran budurwa kace kana so.
lallai nura ka raina min wayau, ko nakaika kaganta? eh kakaini makaryacin banza kawai .
toh shikenan bari mujuya,zanga waye makaryaci ni ko kai nan faruk ya dauke hanya nura dai nabinshi da ido.
yaga ya shiga layin gidan kakannin su.
anan kasamu matar ? eh yace atakaice ya faka motar akofar gidan malam faruku suka futo.
nura ya waiga ya kalli faru dake raraba ido yana neman dan aike.yayi murmueshi yace idan baka da number ta aikeni nakira maka ita mana.
a,a yace tare da kiran wani almajir
shiga nan gidan gidan kace ana sallama da inna. nura yayi dariya yace wlh faruk kai dan iskane🏇🏻
[6:34PM, 11/6/2016] +234 701 419 7556: 💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞
3
✍MMN YAZEED
Lokacin da yaron yashiga gidan inna na zaune atsakar gida akan kujera yar tsugune .alhj usman da yazo kawo ma iyayen shi ziyara yana zaune akan tabarma suna ta hirar su saiga yaro yayi sallama inna ta amsa .yaron yace wai ana sallama da inna. inna tadanyi jim tace kai yaro injiwa ? wasu samari ne a mota. alhj usman ne yayi magana koma dai su wanene ce dasu su shigo .
yaron ya koma ya same su jikin mota .
wai tace ku shigo.
faruk yace, kace mata saurayin tane yazo zance .yaron ya juya, nura ya wai go, kai zomu shiga kana bata mana lokaci.
su inna na zaune yaro ya dawo ,ya fada sako.
inna takwashi da dariya .alhj usman ne ya mike, muje naga wanne dan iskan ne.
inna tace ai bawanda zayi haka sai faruk alhj yakama hanya yana fada,
yana futowa ko ya hango su faruk jikin
mota , nan suka fara raba ido dan basusan yana gidan ba. kai kunci kaniyar ku ashe baku da kuya.
nura yace baba ni baruwana faruk ne.
yayi mai dakuwa kaniyar ka. ku wuce kuba matane waje,
su ka wuce suka shiga ciki alhj kuwa bai koma ba yace idan kunshiga kuce na tafi.
faruk nashiga yafara fadin ke kuma madam ace ana kiranki saki toro mana baba, wlh sai na ce nafasa.
tosai me, mexanyi da tuzuru, ai kama ci sa,a uwarka bata nan da ita zanturo maka. yace ZAKIN GANE KURENKI
kai ne dai zaka gane, kuran naka, badai kaki aure ba kuma ko bakayiba za,a maka.au haka kika kitsa musu kenan?nura ne yace inna,rabu dashi dan Allah baki da cabin mutsa Baki ne .ko da yake nasa duk kikai ma wancen tsohon. toh acici, kazo kenan, bilkisu dai tana fama wlh.
ina ruwanki kincika sa ido wlh, faruk tashi muje mugaida tsoho mu wuce kar a rufe min kofa.
faruk yayi murmushi, aikaji irinta tsoronta kakeji kenan.
sunshiga sashin malam basu jumaba suka futo sukayi musu sallama
4
bayan wasu kwanaki faruk ne a dakinsa yana kokari shiryawa Dan tafiya office daga falo ya fara, juyau wata magana da tasa gabasa faduwa, muryan Aminu yaji yana cewa hjy antsaida ranar ne, eh nan da sati uku masu zuwa . lallai Ashe zamu sha biki.Aminu yasake cewa. harda yaya faruk ne ? hjy tace haka sukace, ni safyya naga yadda za ayi wan,nan abu kaga yaran nan kowaccen su maneman ta sunkawo komai angama magana, yaya za,a hada da faruk da ko budurwa baya da ita. anty amarya tace kudai baku sani ba ko yana da ita, kila tanacan wani garin. faruk dake tsaye sai yaji kafafuwan shi duk sun sage ya koma bakin gado yazauna yace zuciyar shi me suke nufi ? suna nufi ni zasu mawa auren dole, aikuwa duk yarinyar da akayi gangacin aura min zata gane kuran ta.
kwan kwasa kofar da akayi ne yafarkar dashi daga tunanin da ya keyi, tare da fadin wanene, meena dake tsaye bakin kofar tace nice, momy na kiran ka ,
gaban faru yafadi dan Indai momy takira shi toh akwai wani important abu, yace menene ? tace nima bansani ba. yace kice ina zuwa. faruk ya mike yauki jakarsa yamufi dakin momy, yayi sallama bakin kofar yaji shiru ,ya tura kofar yashiga nan ya hango momy zaune bakin gado tana share hawaye, yakarasa ciki ya zauna a kasa yace momy, lfy kuwa ? batace komaiba saida tagama share hawayen ta, ta waigo tace waikai me kake nufi kana nufen kafi karfin kowane ko kuwa, toh wai bari na tambaye ka, baka da lfy ne , ko kuwa Neman mata kakeyi. wai saiku dinga cewa bani da lfy nace muku lfy ta lau,momy ta katse shi, karya kakeyi inkuwa flyr ka lau toh lallai kana neman mata.
momy kidena min irin wan,nan zargen wlh ba abin da nakeyi, kawai lokaci ne beyiba.
momy ta daka mashi tsawa, karka kuskura kagaya min maganar banza dan kaga ina daga ma kafa ,wai kai katashi dan rashin mutunci kaje har gidan alhj ka gaya mai bakason y’ay’an shi, har da cewa sunma tsofa saboda kai baka da kunya, toh ai barasa manema suyi ba daman dole za,a musu.
faruk fah hankalin shi yatashi dan tunda yake da momy betaba ganinta tana fada haka ba, yace momy Allah ya huci zuciyar ki, kuma in Allah ya yarda zan kawo matar da zan aura kafin lokacin, dan Allah gafara can katon baza kawai,momy dai ta inda take shiga bata nan take fitaba,
hjy babba ce tajuwo fadan momy tashigo tana fadi, haba aisha ki mishi hakuri mana wannan fada haka, hjy nagaji da halinshi wlh zaka gane kuran ka,hjy takali faruk daya takure, idon nan jawor tace yanzon dai tukuna ba office zaka ba ? murya adashe, yace, eh. tace tashi ka tafi
momy ta daga murya takira aminu.yamsa tace kana da number nura ? eh
kace ina kiran shi
[6:34PM, 11/6/2016] +234 701 419 7556: 💞💞
ZAKI GANE KURENKI💞💞
5 to 7
✍MMN YAZEED
07014197556
Hjy safyya ta nemi wuri ta zauna, tace aisha bafa haka akeyi ba ke da zakiyi mai nasiha kuma saiki zauna kinamai fada.
wlh raina ya baci hjy, yanzun kinga alhj laifina yake gani, fadan da alhj yake min na tabbata baya mai irinshi.tace haka dai za aitamai nasiha.
4:15
faruk ne tafe ya tashi aiki ya rasa ina zai nufa , ya daga waya yakira nura, daga can, furuk najin an daga, yafara fadin akwai matsala.
yace
Allah ya rabamu da ita ,me yafaru ?
bakaji wata magana bane agidan ? kamar ta me ? maganar bikin su hafsat. eh naji
tare da naka bah.
toh ni wazan aura ? ina nasani kuma aikai zan tambaya faruk yaja tsaki, yace muhadu mana yanzon.
ni dama yanzun ina kofar gidan ku, katashi aiki ne .eh mekaje yi gidan bayan kasan bana,nan.
au saikana gidan zanje . ai nasan indai banan nan ba zuwa kakeyi ba.
hmmm aminu ne yayi min waya dazun wai momy tana kirana.
gaban faruk ya fadi azuciyar shi yace lallai momy da gaske take yi. nura ne yace najira ka mushiga tare.
a,a shiga kawai inkungama ka same ni a daki.
nura ya sauka ya rufe motarsa ya nufi ciki yaci karo da meena zata fita, yace meena ina zuwa haka tace . wlh yaya nura ban ganka ba, gidan inna zani . kice yau inna tana da babban bakuwa, sai dare kenan.
a,a bayau zan dawo ba zam mata kwana buyu, amman karka gayawa yaya, dan yace wai adaina barina kwana agidan .toh karki damu bazan gaya maiba kicema malam duk abinda yaci ya ragemin
ina, nan zuwa. tace toh
bayan nura yashiga gidan tare da sallama yasa kai ababban falon gidan anty amarya dake zaune ita da samira matar aminu suka amsa masa sallama, abdallah dake gefen su yana wasa ,ya rutumo aguje ya d’ane aminu , yana fadi ina abba furuk?
yace abdallah kenan kuna gida daya kuma zaka rinka tambaya na shi. yace toh ai yau bangan shi ba. toh yanzun nan zaka ganshi ,yana hanya.
samira ce takatse musu hirar daga shigowan shi kasashi gaba da surutu. yagaida Anty amarya kazauna mana.
a,a zan shiga gun momy ne samira tace inawuni yaya.lfy lau samira ya megidan.tace lfy lau. yasakai dakin momy ,ya kwan kwasa kofar ,tace shigo nura . bayan yashiga ya zauna ya gaida momy tace rike gaisuwar ka banason momy me yayi zafi ? dakai da Dan,uwanka nakusa dai amsa gaisuwar ku .
dan Allah momy karkiyi haka, inkikai fushi haka ai bazamu ga albarkan abin ba, nasan banzai wuce maganar auran faruk ba, dakata nura, nasan duk halin da dan uwan ka yake ciki kasani. yace haka ne momy ya fada a takaice .
toh naji, inaso na tambaye ka, amma kamin alkawarin zaka gayamin gaskiya .
insha allahu zanfadi abida na sani.
nura dan uwanka yana neman matan banza ne ?yace
toh nidai a iya sanina faruk baya ta ammali da mata, gaskiya.
momy ta dukar da kai tai shiru, nawasu mitina sannan ta dago tace, toh ko dai baya da lfy ne?nura yadukar dakai yace
wlh lafiyar sa lau kuma daina tunanin nan.
nura tunani ya zama dole , yanzun baban ku laifena yake gani yace kila baida lfy,banja shi ajikina ba bare ya fada min, kuma innayi tunani sainaga kamar haka ne ,
ni tunda nake ban taba jin ance you ga budurwar sa ba,, koko ace ya taba cewa yana son wance, kaga ko abin akwai kulle kai.
yace gaskiya ne momy, nima din bantaba gani ba, amman dai lfyr sa lau wlh , aure kuma yanason yayi Amman shi anashi ra,ayin yafi son karama kuma
yana so ya zaba da kansa.
waya hana shi ya zaba, yanzun kanin shi tun yana secondary za,ace yace yana son wacce ,amman wannan shiru fah. yanzun dai momy dan Allah kikwatar da hakalin komai zai wuce insha allahu, barinje wajan faruk din .
toh shekenan kunadai rike da ranar ko? eh yace da ita yana kokarin fita daga dakin
nura ya tura kofar dakin faruk ya shiga, yasame shi zaune akasa yace, meye haka kuma ? faruk yace wlh hankali na atashe yake. toh ai kai ka zabi haka .
bahaka bane, nura,bazaka gane ba, yanzon acikin yan kwanakin nan, za,ace nasamu matar aure saikace yar tsana.
gaskiya faruk nagaji da halinka , kai wai wani irin buri kaci ne haka.
ba haka bane nura, niyanzun ma tsaya, tukuna dai ,momy har yanzun kuka takeyi ? a,a batayi kuka ba, amman dai ranta abace yake, kuma bai kamata ace kamar ka kana batawa iyayenka rai ba, faruk kafa girma ya kamata ace anwuce wannan worin.
na sani nura, dazun fah momy kuka na sameta ta tanayi.
toh ina amfanin irin wan nan ,haka dai nura yayi taba faruk shawarwari
akwana atashi kwanaki nata tafiya abubawa nata faruwa gashi yau har saura kwana biyu biki gidajen ya,uwa duk ya kaceme faruk kuwa antura su abuja daga office dinsu anasa ran dawo wan shi ayau
kuma ayau ne iyayansu suka shirya zama domin tattauna agidan mahaifin su wato malam
bayan sun bude taro da ar,dua ne suka fara tattaunawa akan matsalan da faruk yakeso kawo musu acikin dangi wannan zama kuwa anyishi harda yaya sulaiman da anty hafsat yayyen faruk wada hjy safyya ta haifa
malam faruku ne yafara magana, yanzun dai takwarana banda shi kenan awannan biki. alhj usman yace to baya ga anbarshi yana abinda yaga dama ba saikace yafi karfin mu, ai yaka mata mununa mishi mune iyayen shi, saimu zauna yaro karami yana juya mu ,wlh tllh be isaba.
alhj ahmad yace saurara usman yaran zamani yanzun lallaba su akeyi, inhar akace za,ayi musu da karfin tsiya toba inda abin zaije.
hmm ku kuke sa yaran nan nama na tsayayya wlh dole sai anbi abinda yake so kenan.
sulaiman ya dukar da kai yana son yayi magana amman yajin tsoro baba usman karya dawo kanshi alhj yusuf yace nidai idai nine anemi koma wacece a aura masa kwai, malam yace haka yadace amai, ina nura? alhj usman yace bezoba ai dukkan su muna fukai ne.
alhj ahmad ne yace nidai inhar zakubi zawara ta malam aban dama ta karshe, ayi bikin nan abar faruk ni nasan yadda zanyi masa
[6:34PM, 11/6/2016] +234 701 419 7556: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞
7 to 10
✍MMN YAZEED
Alhj usman ne yace nidai gaskiya ban amince da wannan shawara ba.
alhj ahmad ne yace ,yusuf kai me ka gani . yace duk yadda kuka yanke daidai ne
alhj ahmad ya dukar da kanshi kasa yayi shiru yana tunani falon yayi shiru can alhj ahmad ya dago kai yace usman ina da hujjujin dayasa nace abar nasa sai daga baya,
kaga nafarko faruk baida yarinyar da zai aura sannan lokaci ya kure balle muce zamu nemar mai wata inkuma mun samu yariyar ma toh bawani kwakwaran bunkece zamuyi ba saboda lokaci yariga ya kure, dan haka nakeson abarmin komai ahannuna nanda wasu yan sati faruk zaiyi aure ko yaki ko yaso.
malam ne yace nayarda da dalilan ka dan haka kubar maganan ahanun sa alhj usman badan ransa yaso ba .
haka akayi bikin akabar furuk
faruk dai yaga andaura aure shiko bawan da yamai wata magana nandai yafara tunanin kila zaman da sukayi sunyi shawaran abarshi sai sanda yaga dama, dan haka ya sake ranshi yanata harkan gaban shi, bayan anyi biki amare su biyar kowacce tana dakinta .
faruk ne zaune a haraban gidan su yan shan iska da waya ahannu sa yana dan dadda nawa, saiga motar alhj ahmad ta sawo kai nura ne ke jan motar faruk ya mike da sauri yaje wurin ya budewa alhj murfen motar yafuto nan yafara gaida shi ya amsa da murmushi , nura ya zagayo ya mikawa faruk hannu suka tafah , alhj yayi gaba yabarsu anan yana fadi inkugama kusame ni aciki, sundade tsaye suna cabtar su sannan faruk yaga kira daga maihaifin sa, yadaga yana fadi gamunan zuwa, ahanyan su nashiga ciki faruk yake tambayan nura wai lfy kuwa ?
yace ai kasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki . dahaka suka isa falon.
alhj ne yace babana manyan kasa, kagama buyar kenan ko ?
baba dama ba boyewa nayi ba aikine yayi mana yawa.
toh ai shikenan, yanzo a ina muka kwana.
faruk yayi shiru ya dukar da kai kasa . alhj yusuf ne ya kalle shi yace bada kai ake magana bane .faruk yadago ya nama nura alama da hanu, kace wani abu mana.
nura ya make kafada. faruk dai daya ga ba sarki sai Allah ,sai yace baba wlh ban samu bane . yanzun kana nufi baka samu wace kakeso ba? eh
shikenan babana yanzo umarni zanbaka, bana neman amincewan ka ,ko zabin ka , kuma yanzun ne zamu gane kafi karfinmu ne ko kuwa, yadda kuwa zamu gane kafi karfinmu shine bijerewa umarnin mu.
dan haka nake sanar dakai kashirya karban angoci nanda wasu kwanaki zamu zabama mata, ya kalli faruk da nura yace kunji ko bakuji ba ?
suka hada baki sukace munji. yace kutashi kutafi .suka tashi sukayi cikin gida. bayan fitasu ne Alhj yusuf ya kalli yayan shi yace gobe inson zanyi tafiya zanje katsena gidan alhj nasuru babban dansa yarasu gobe ne bakwai zanmai gaisuwa . au haka ne fah naji sanarwa aredio enkaje kamai gaisuwa.
yace zaiji insha allahu
alhj nasiru aminin alhj yusuf ne tare suka taso da zumunc
mai karfi tunsuna yara kanana. bayan suyi sallama alhj ya tafi. sai alhj yusuf ya mike yanufi dakin hjy aisha , momy taji mamakin ganin alhj dan baifaye zuwa dakinsu ba.n yace jeki kiramin faruk. tace yau kuma ba baban saika kira sunan gatsal haka. eh ba zance mai baba ba dan banana ba haka yake ba, d’a da mahaifi sai Allah momy bataji dadin maganar nan ba. ko .kuma ma barshi ,ki gaya mishi nace inhar alhj ya kawo mai mata yace mai baya so ,Allah ya isa ban yafemai ba, bejira mezata ce ba ya fita. wa shegari anayin sallah subahi alhj yatafi katsina bayan yayi sallama da iyalan shi. 8:00 faruk ya fito domin tafiya office ya leka dakin momy yace natafi .tace yauwa zo nan dama babanka yace nafada ma inhar baban ku yakawo maka yariyar dazaka aura, kace a,a beyafe makaba. faruk besan lokacin da yazauna ba yace momy me yayi zafi haka? oho kaika sani . momy dan Allah kibashi hakuri dan Allah. nidai sako yabani kuma nasanar ma tashi ka fitanmin adaki.
KATSINA
Bayan alhj ya isa gidan alhj nusiru yatarar da shi yata karban gaisuwa,
alhj nasiru yaji dadin zuwan shi kwarai da gaske, bayan mutane sun watse yarage daga alhj nasiru sai alhj yusuf sai kuma hirar bayan rabowa ta barke inda alhj ya tambaye shi wai faruk yayi aure kuwa?. yace inafah har yanzun baiyi aure ba , ko kunya bayaji d’an aminu fah shekar shi uku da wani abu. yace ai lefin ku ne me yasa baku bashiba acin yaran ku ba. nima naso haka amman kasan halin alhj ahmad memakon muyi sharawara atsakanin mu sai yace sai annemi zabin yara, toh shi kuma faruk anashi haukan wai shi yar secondary yake so.alhj nasiru yayi dariya lalai faruk, toh balaifi idai wan,nan ne takwana gida sauki , aini inada kananan yara badai ni da niyar aurer dasu yanzun , amma tunda dana ne na bashi ko nan da sati daya ne sai ayi alhj yaji dadi sosai yarasa wane irin godiya zaiyiwa alhaji nasiru. bayan sun shiga cikin gidan yayima matan shi gaisuwa yarako shi har gon motarsa yashiga yace gobe su yaya ahmad zasuzo. yace allah yakawo su lfy .
alhj nasiru da bai naimi shawaran kowaba ya yanke hukunci ya shiga gida ya kira matan sa guda biyu , yace dama wata magana ce ta taso ya kwashe yadda sukayi da alhj ya gaya musu .hjy rabi uwargidan alhj ce ta daka talle tace wacce yar taka kabashi, badai zainab ba. yace ita. nan tamike tafara fadin wlh wlh bazai yuwuba yama zayyi haka dandai ni baka sona kowanne tarkace ka zubomin ingaskiya ne kabashi humaira mana ko dan ita yar gaban goshin kace.alhj ya kalli ta yace kingama ta murguda baki tace eh.yace shikenan dama abinda yasa nace zainab naga humaira tayi kankata da yawa ne kinga fah zainab wannan shekarar zata gama secondary humaira fah sheranta17 ne kuma ss1take tace alhj gaskiya nifa bazan taba yarda da wannan zalincin ba alhj yamike yana fadi baki isa kihanani iko da yata ba hjy fatima wadda suke kira da anty tace alhj dan Allah kubari tunda dai kariga da kayi musu alkawari nina amence abashi humaira amman dan allah alhj kagaya masu zata cigaba da karatu.
alhj yaji dadi sosai yace nagode fatima dama ai zata cigaba da karatun ta wannan dalilin yasa nakejinki araina fiye da yadda baki zato. hjy tamike tawuce tana fadin kukusani alhj yace bari naje can gidan yaya nasanar mai tace toh yana fita tashiige daki tafashe da kuka tana tausayin yarta yayanta kenan guda biyu daga yayan humaira auwal sai ita humairan
bayan alhj yusuf ya koma kano bai sauka ko inaba saigidan yayansa bayan ya gaya mishi yadda sukayi da alhj nasiru yaji dadi sosai dan haka suka shirya tafiya washe gari basu gawa kowaba acikin matan su
nura ne yaja su kuma shima besan meye zasuyi ba , nura nata kasa kune ko zaije suna fadin inda zasu sukasha manyan kaya haka su uku ne ciki alhj ahmad sai alhj usman saikuma kanin malam sun isa gidan alhj nasiru karfe 2:24 bayan sun huta sunci abinci saiya hada su da auwal ya kaisu gidan wanshi malam buba
bayan sun shiga gidan ankarbe su da mutunci suji dadin tarbar da aka musu sanan sukafara maganar akan abinda ya kawo su alhj ahmad ne yayi magana , malam nawa zamu bada sadakin yar tamu yayi dariya yace sadaki ai baya kadan ku bada dubu talati Allah yasa su zauna lfy .alhj Ahmed ne ya mike yace ina zuwa yana fita ya daga waya yakra kaninsa yusuf ya fada masa . yace a,a ni amatsayina uban yar ,ban yarda ba dubu dari zaku bada, alhj ya koma ciki yace uban yar yace be yarda ba, yace wai dubu darine sadakin ta malam buba ya gane wasuke nufi yace a,a dari yayi yawa dakyar dai ya karbi dubu dari buyu harda kayan sarana suka tsaida rana sati daya.
suka futo suka samu nura a motar
sun kawo kano fly saida suka tsaya ahanya suka sayi dabino alewa sanan nura yakara tabatar da zargin sa azuciyar shi yace yau faruk akwai tashin hakali kenan.
gidan malam faruku suka yada zango suna shiga inna ta rangala gula nura ne ya fakaici idonsu ya harari ta.
nandai aka raba kowan ne ya wuce gida da kulin nashi nan da nan lbr ya karade dangi kowa na murna shikuwa faruk besan dawan garin ba dan tun safe ya tafi gidan kakan shi maifiyar Maman shi

Leave a Comment