✨✨ ZAINABU-ABU ✨✨
Na
ZAINAB A BARDE
🖊️ALƘALAMI YAFI TAKOBI 🗡️ WRITER’S ASSOCIATION
(A.Y.T.W.A)
Free page 1 nd 2
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM, DA SUNAN ALLAH MAI KOWA MAI KOMAI, MAI RAHAMA MAI JINƘAI, TSIRA DA AMINCIN ALLAH SU KARA TABBATA GA FIYAYYAN HALITTA SUGABAN MU ABIN KOYIN MU, SHALELEN UBANGIJI, NA KHADIJA ANGON AISHA, DAN AMINATU RASULILLAHI ANNABI MUHAMMAD S.A.W, YA ALLAH INA ROKON KA, DA SUNAYENKA MASU TSARKI, DAN ANNABIN KA, DA ALKUR’ANIN KA, ALLAH KA JIƘAN MAHAIFINA, (ALHAJI ADAMU BARDE) DA SAURAN IYAYEN MU DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA, IDAN TAMU TAZO ALLAH KASA MU CIKA DA KYAU DA IMANI, AMEEN YA HAYYU YA QAYYUM…
YA ALLAH YADDA KA BANI IKON FARA RUBUTA WANNAN LITTAFI LFY, ALLAH KASA NA GAMA SHI CIKIN NASARA DA KOSHIN LFY.
****
Juyi kawai takeyi, saboda hayaniyar yaran da suka hanata bacci, bargon ta jawo ta tura kanta a ciki wai ko zata daina jiyo hayaniyar yaran, amma ina kamar a cikin dakin suke hayaniyar, dagon tsaki taja tana fitowa daga ciki bargon, fitowa waje tayi inda yaran suke zagaye da wata tsohuwa, “Anna ni ta hamsin za’a bani”,”Anna ni kuma ta ashirin”,”Anna wllhi ni za’a fara bawawa, ai na rigasa zuwa”,”wllhi baku isa ba ni za’a fara sallama”,”duk kuyi hakuri za’a sallami kowa yanzon nan” bayan ta karewa yaron kallo da kowa burinsa a sallame sa, wani takaici ne ya rufeta na tashinta daga daddadan bacin da takeyi, tsaki taja a karo na farko, ai da sauri yaran suka jiyo ganin wacce ta fito yasa sukayi shiru kamar ruwa ya cinye su, lokaci daya suka natsu saboda ganinta, Anna kuwa jin shirun yayi yawa yasata dagowa, murmushi tayi ganin ashai dodonsu ce ta fito, daya daga cikin yaran ne yayi tsuru tsuru, irin na mararsa gaskiya.
Shako masa wuya tayi, “dan buhun ubanka wana kama, dama na gaya maka zaka shigo hannu, wato ranar saboda kaga a gaban uwarka ne harda zagi na ko aiko yau zaka gayawa yan garinku” marinsa tayi aiko yaro ya fashe da kuka, wani marin ta kuma kifa masa, aiko nan yaro ya fadi kasa yana kuka, duk da haka bata kyalesa ba saida ta kuma marinsa, hakan ma ta kyalesa ne saboda maganar da Anna takeyi mata, aiko yana ganin ta kyakesa ya zura a guje yana fadin “Wllhi saina gayaki da mamana” dariya ta barke da ita, “yoo uwar takama in tayi lakada mata na jaki zanyi banlantana kai karankada miya, ku kuma kallon mai kukeyi min” ai dandanan suka sunkuyar da kai kasa, “kuma bari kuji na fada muku wllhi daga yau, in kukazo siyan waina kuka cikamu da surutu, wllhi sai naci uwar mutum kai harda uban ma, ko bakuji mai nace ba” ta daka musu tsawa,
A firgice yaran suka hada baki wajan fadin, “munji”,”karma kuji jikin mutum nai dai zaiyi tsami, ehhe”,”kekam Allah ya shirya min ke, na kula so kike ki korar mun yara, su daina zuwa suna siyan waina ta”,”yoo dan ubansu su daina zuwa mana, suga yadda zanje har gaban uwar yaro inyi kuli kulin kubura dashi” girgiza kai kawai Anna tayi, tama rasa abinda zatace, nan dai ta sallami yaran, hada kwanikan tayi, ta kaisu wajan wanke wanke, daganan ta share gidan sab, wanke wanken tayi, tare da sharo dakunan, saida ta gyara gidan sab sannan tazo ta zauna a kusa da Anna,
“Jikalle ta maza kici abincin in aike ki wajan Hannatu ki karbo min kudina, kusan sati kenn taƙi ta bayar”,”ai Anna bar karyawar nan bari naje na fara karbo miki kudin, yoo mu har akwai wanda zaici mana kudi a kwayen nan ya zauna lafiya ne”,”aa jikalle ki fara karyawa tukunna”,”sai kiyi kuma, saina amso kudin sannan hankalina zai kwanta, kinsan ni fa masifa har cina take in ban samu abokin fada ba” tana gama fadin haka ta zuba sudaddun silifas dinta tayi waje,
“Ya Allah ina mai tawassali da sunayan ka tsarkaka ya Allah, Uban giji ina rokon ka da fiyayyan halitta Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam ya Allah, Allah ka shirya min yarinyar nan” ta daga hannu tana rokon Allah, saboda kullum abubuwan nata gaba gaba suke karayi, saidai shiriyar Allah kawai,
Tun daga naisa yake kwala mata kira, amma ko gaizo batayi ba, ta ci gaba da tafiyar ta, bawai kuma dan bata jisa bane, ta jisa tsarai yan wulakancin ne a kanta, “Zainabu Abu” ya kuma kiran sunanta a ɗai ɗai lokacin da yake karasuwa, “haba masoyiyata Abu, inata kwalla miki kira amma baki jini ba”,”waya gaya maka cewar ban jika ba, najika sarai gadamar tsayawa ne banyi ba, koda akwai wani abu” ta fada tana jijjiga jiki tare da yin fari da ido, “haba masoyiyata Zainabu Abu mai tagwayen suna”,”kaga dakata Bala, kalle ni da kyau” kallonta yayi tundaga sama har kasa, “ka kalle ni ko?”,”ehh na kalle ki”,”nayi maka kala da wacce zata kula ka, ko wani daga cikin kwauyen nan, duk kanku banga sa’ana ba a ciki, dan haka ni kaga tafiyata” tsororo ya tsaya yana kallonta, kamar wani soko, dan dama ba yau ta fara masa rashin M ba, dandai bazai iya rabuwa da ita bane, saboda duk tafi matan kyauyen kyau, Zainabu Abu kenn, ga kyau ga diri, ga rashin mutunci ga rashin kunya, duk ta hada,
“Haba masoyiyata Abu, wai mai yasa kike min hakane?”,”mtwss sai kayi kuma, mutum sai kace maye, ance ba’ayi dashi amma bazai hakura ba, ni kaga tafiyata, kai kuma sai kayi ta tsayuwa a nan tunda bakada aikin yi, nikam ina dashi” tana gama fadin haka ta bugawa bujenta iska, shi kuwa kasa cewa komi yayi, badan soyayyar da yake mata ba, ina zai tsaya tana fada masa bakaken maganganu,
“Assalamu Alaikum, Salamu Alaikun ta fada tana bubbuka kofar langa langar, ko mutan gidan basa nan ne? inma basa nan ina nan babu inda zanje, in kuma sunanan su fito yau yan rashin mutunci ne suka kawo ni, ehhe” hannatu da take kashi a bayi, tunda taji sallamar Zainabu Abu, hantar cikinta ta kada, tasan duk lokacin da akaga Zainabu a waje to ba mutunci ne ya kawo ta ba, ko gama kashi batayi ba, ta wanke ta fito,
“Aa yausu Zainabu Abu ne a gidan namu”,”kinga dakata Hannatu, miko min kawai, kudin Kakata Anna na tafi, dan ba wani dogon zance ne ya kawo ni ba”,”dan Allah Zainabu kice mata tayi hakuri, wllhi zan kawo mata har gida inna samu”,”kutumar uba, ai wllhi baki isa ba, inkinga na bar gidan nan to kin bada kudin nan”,”dan Allah Zainabu, wllhi banida su, dan Allah kiyi hakuri, dana samu zan kawo” Hannatu ta fada tana marairaice fuska ko Zainabu zata tausaya mata ta kyaleta, murmushi Zainabu tayi tana fadin “toh shknn, amma fa ki kawo mata, nace kifa kawo mata kudin ta”,”insha Allah zan kawo” ta fada tana murmushi, ai Zainabu Abu harta kai bakin kofa, ta dawo a guje ta dauke waken dake cikin kwarya, da akalla zaikai kwano daya, “ke a ganinki zanyi zuwan banza ne, to na dauki waken nan a madadin kudin, inkin gadama ki biyoni da kudin gida ki karbi waken ki, inko kika bari yakai gobe wllhi bazan bayar ba” ta fada tana zurawa a guje .
“Na shiga uku ni Hannatu” da gudu itama ta biyo ta kofar gida, amma ina hartayi nisa, “keee! Zainabu dawo ki karbi kudin ki, ki bani wake na, akan dari biyu zaki dauke min waken dubu da dari biyu”,”ba kince bakida kudi ba, to kije ki rike kudin ni kuma in rike waken” ta fada da karfi yadda Hannatun zata iya jiyota”,”ni wai maima yaja min na ciyo bashi a gidansu Zainabu, gashi yanzo ta dauke min waken Alalata.
Koda ta baro gidansu Hannatu bata zarce ko ina ba, sai shagon Dan Liti, tunda ya hangota ya fara mata kirari “kaga Zainabu Abu, jika a wajan Anna, mutum ya tabaki ya tabowa kansa masifa”,”fadi ka kara fara Dan liti mai kwalelen kai” turbune fuska Dan Liti yayi, dan ya tsani ta kirasa da mai kwalelen kai,”wake na kawo maka ka siya”,”yoo banda abinki Zainabu, ai bama siyan wake saide mu siyar”,”aiko dolen mutum ya siya ehhe”,”haba Zainabu ina dole a nan, nida zan siya, lallaba nifa ya kamata kiyi in siya”
“Kan uba, nabi lallabawa da gudu dan ubanta, dan Allah dan Liti karka siya kaji” ta fada tana ajiye kwaryar, dan kwalin kanta ta kwance ta dora shi a kugu, jiki ta fara girgizawa tana fari da ido, “zaka siya, ko kuwa mu raba dan halin”,”kinga Zainabu zan siya, ni banason fitina, ke bakijin kunya wani yazo wucewa yaga kinci damara haka”,”yoo aini abin kunya gaba na basa ba baya ba, kaga nifa banma san maine wani abu waishi kunya ba, danma ka sani”,”niko nafi kowa sani Zainabu, nawa zaki siyar da waken”,”nawa kake siyar da wake?”,”dubu da dari biyu”,”to nima haka zan siyar maka”,”to ai nima zanci riba ko, saide ki siyar min dubu daya” wani banza kallo ta watsa masa, “kaga nayi kala da wacce za’aci riba a wajanta?” ta hayayya ko masa, “naji zan siya a hakan”, “da dai yafi maka” kudin ta ya lissafo mata ya bata, waken ya karba ya juye sannan ya bata kwaryar ta, harta kai bakin kofa sannan ta juyo tayi masa kallon shatara saura kwata, “da baka siya ba ai, da kaga yadda zanyi maka”,”jike dai jarababbiya kawai” harta fara tafiya taji abinda yace ta juyo, “mai kace”,”aa ni bance komi ba” ya fada yana zazzare ido, “daka maimaita ai”.
Shere Fisabilillah
✨✨ ZAINABU ABU ✨✨
Na
ZAINAB A BARDE
🖊️ALƘALAMI YAFI TAKOBI 🗡️ WRITER’S ASSOCIATION
(A.Y.T.W.A)
Free page 3 nd 4
Arewa Book @Zainababarde1
****
Akan hanyarta ta komawa gida ta hadu da Safara’u ta debo ruwa, ita bama ta kula da ita ba, kudin hannunta ta daure a habar zani, sannan ta cakwali gaban rigarta, “ubanwa na kama”,”dan Allah Zainabu kiyi hakuri, kinga inna tace ta aike ni na daibo mata ruwa zata duro girki”,”cha cha cha, dalla rufe min baki kafin in fasa shi a nan wajan, dama gashinan kamar na biri, kinga sai na kara tabar dashi, sauke ruwan kanki”,”dan Allah kiyi hakuri”,”zaki sauke ne ko Aa” ta fada tana kankance ido, sauke ruwan Safara’u tayi, idonta na tara kwalla, ai tana sauke ruwan Zainabu batayi wata wata ba, ta dauki ruwan ta shaika mata shi, tundaga kanta har kasa, kuka Safara’u ta fashe tashi, ganin wannan wulakanci da Zainabu tayi mata, “gobe ma ki kara tsokanata kiga yadda zanyi maki” ta fada tana jefa mata bokitin tare da karawa gaba, durkushewa safara’u tayi ta fashe da kuka.
Tana dab da shiga gida tayi cilli da ƙwaryar tare da shigewa gida, sallama ta rangada tana kwala kiran sunan Anna, “ni wai lafiyan ki kike kwalla min kira haka?”,”lafiya lau Annata, dama kudin ki na karbo maki, gasu ma” ta fada tana ciro su daga habar zani, dari biyu ta bata, “ahh ni Anna yau wace rana Hannatu tayi biyan bashi ta dadin rai” ai bata gama rufe baki ba saiga Hannatu ta fado gidan kamar an jefota daga sama, “Anna ga kudin ki, ki bani wake na”,”wana wake kuma?”,”waken da Zainabu ta kawo maki mana”,”ni bata kawo min wani wake ba, kudine ta kawo min kuma gasu” ta fada tana nuna mata dari biyun,
“Kee! Zainabu ina wake na?”,”ban gane ba wana wake kike magana akai, kin bani wake ne?”,”waken da kika dauka a cikin ƙwarya na alalata”,”kinga malama ni ban daukar maki wani wake ba, kinje chan wani ya daukar maki wake zakizo ki lakabamin, banji ba ban gani ba” ta fada tana murtuke fuska a dole ba ita ta dauka ba, Hannatu zata sake magana Anna ta dakatar da ita, “kinga Hannatu tun muna shaidar juna ki fitar min daga gida, baza kizo har gida kice jikalleta ta daukar maki wake ba, bayan kuma bata dauka ba, dan kinyi biyan bashi, kuma shine harda sharri, to wayace kici bashin?”,”wllhi Anna wake ta daukar min da nace mata banida kudi, kuma Alalar siyarwa fa zanyi”,”kinga ki fitar min daga gida tun muna shaidar juna, kije ki naimi wanda ya daukar maki wake tun lokaci bai kure maki ba”,”Anna dan Allah kisa baki ta fada min inda wakena yake”,”Anna bari na fitar da ita tunda bazata fita ba” nan ta fara tura ta harta kaita kofar gida sannan ta hankadata, “gobe ma ki kara cin bashin Annata, kuma kiƙi biya kiga yadda zan maki” ta fada tana shigewa ciki,
Hannatu kuwa hannu ta dora a ka, tama rasa ihu zatayi ko kuka, a dakeka sannan a hanaka kuka, amma bataga laifinsu ba laifinta ne, da bataci bashin su ba, da duk haka bata faru ba, garama ta tashi tasan inda dare yayi mata, dan tasan kaf garin nan babu wadda ya isa ya karbar mata waken ta, har mai gari da kansa, saboda masifar Anna da jikarta Zainabu, tashi tayi ta kara gaba tana matsar kwalla.
Koda Zainabu ta koma cikin gida abincin ta taci tasha ruwa, ta godewa Allah, “Anna bari naje gidansu siyamah kafin lokacin dora abincin rana yayi, saina dawo na tayaki”,”sha zaman ki jikalle ta, dan nasan ma ba dawowa zakiyi da wuri ba, karki min wani dadin baki, in kuka hadu da ciyama ai baƙu sanin lokaci yayi”,”nace maki Siyamah ake cewa ba ciyama ba, ina gyara maki ne dan kar wataran ki kunyata mu”,”naki na fada yadda kikace din, yadda na iya haka zan fada, yar bantan uba” dariya tayi tana ficewa daga gidan.
Koda taje gidansu Siyama, tararwa tayi innarta batanan, ita kuma tana wanki, “ƙawata ashai dai zakizo”,”kin manta wace Zainabu Abu ashai, bata saba alkawari, tunda nace miki zanzo to zanzo” murmushi Siyamah tayi, nikam ai nafi kowa sanin ƙawata, kinji labarin anjima da daddare za’ayi babban wasa a dandali”,”wasan mai?”,”kin manta gobe ake aurar da yar gidan mai gari” tabe baki tayi “kinsan fa ni abinda ya dame ni nakeyi, ban shiga abinda bai dame ni ba”,”amma dai zamuje ko?”,”gaskiya ba zanje ba, amma in kinga kinason zuwa zaki iya zuwa”,”dan Allah ƙawata ki bari muje” zata sake magana, siyama tace “dan abotar mu fa” girgiza kai Zainabu tayi dan tasan abinda zatace kenn dama, “shknn inkin shirya ki biyo min sai muje”,”yauwa ƙawata ko kefa”,”ina Inna ko batana?”,” eh taje gidansu wasila”,”ki gaishe min da ita in ta dawo”,”zataji sai mun hadu anjima”
Tana fitowa daga gidan ta ga Hansai mai tallar awara, “kee! Hansai a warar ta yauce ko kuwa kwantai zaki siyarwa da mutane?”,”wllhi Aunty Zainabu ta yau ce” ta fada jikinta na mazari, murmushi Zainabu tayi ganin yadda Hansai ta shiga hankalinta, ba zata manta ba tun ranar da hansai tayi mata rashin kunya, ta gudu gida, aiko Zainabu ta bita har gaban uwarta ta lakada mata mugun duka, tun daga ranar in suka hadu take kaffa kaffa kar tayi abinda zataci duka, “ajai bokitin awarar taki kije makarantar Malam Mamman ki kirawo min almajirai mutum goma, saura kuma ki zauna karki dawo da wuri kiga yadda zan maki”,”amma aunt.. bata karasa ba Zainabu ta girgiza mata hannu, ai da sauri ta ruga da gudu dan cika aiki karta sha duka.
Tana nan tsaye Hansai ta dawo da almajirai guda koma kamar yadda ta bukata, layi tasa suka bi, “ki saka ma kowa awara ta naira dari” zuru Hansai tayi, dan karta saka musu Zainabu ta hanata kudin ta, “ko bazaki saka musu bane?”,”zan zann saka” ta fada tana in’ina, haka ta amshi robarsu ta saka musu ta dari dari, kamar yadda Zainabu ta bukata, haka almajiran suka rika murna suna mata godiya, bayan ta sallami almajiran, ta dago tana kallon Zainabu, dubu dayar nan da ta daure a habar zani ta dauko ta mika mata, da sauri Hansai ta karba tana godiya kamar tayi mata sujjada, murnan da take yaudai gashi sun hadu da Zainabu kuma sun rabu lafiya, gashi kuma ta siye mata awara, yau ba saitayi yawon talla ba, haka ta dauki bokitinta ta nufi gida cike da farinciki, “nayi miki sadaka da kudinki, kinga ai kya sami lada, tunda dama bayi kike ba, sai bakar rowar jaraba.
Tana cikin tafiya taga wani mai siyar da lemo, “lemo lemo lemos, ga lemo in ba zaki ba biya”,”masha Allah, Malam mai lemo a bani lemo”,”na nawa za’a baki?”,”fara bani daya in taba” yanka mata lemon yayi, ya mika mata, karba tayi ta fara sha, “kara min wani” saida ta sha lemo biyar, “aikin banza ma, ashai kasan lemon naka babu zaƙi”,”haba yar nan, lemo na kuwa shine mai zaki”,”niko banji wannan zaƙin ba, dan haka bazan biya ba”,”aiko baki isa ba, ni nasan duka lemuka na masu zaƙi ne”,”sai kayi kuma, ni kaga tafiya ta”,”aiko baki isaba” bata kulasa ba ta fara tafiya, binta ya fara yi a baya yana fadin “ki bani kudi na nace” duk inda suka wuce kallon su ake, wasu na fadin Allah ya raba ku lafiya, a haka har tazo gida, tayi shigewarta ciki.
Sallama ya rinka kwalawa, “jikalle ta kamar sallama nakeji ko?”,”bawai kina ji bane, sallama ce Anna”,”bari to naje na gani”,”muje tare mu gani wane” fitowa sukayi, “bawan Allah kaine kayi sallama?”,”nine kudina nazo amsa da ƴarki tasha min lemo taƙi biya”,”to ba nan gidan bane danni banida wata ƴa”,”ga tanan a bayanki” jiyowa tayi ta kalli Zainabu “kinsha masa lemo ne?”,”Anna shine fa yace in ba zaƙi ba biya, ni kuma da nasha naji babu zaƙi”,”to kai kaji, lemon naka babu zaƙi”,”nifa nasan lemo na akwai zaƙi, bari ma kiji” lemo daya ya dauko ya yanka mata, karba tayi ta fara sha, saida ta kusa shanyewa, sannan ta furzo dashi,
“Wannan wana irin lemo kake siyarwa da mutane, abu duk bauri, babu zaƙin yau bare na gobe”,”nide wllhi sai kun biyani kudi na”,”ko sisi bazan baka ba, tunda kai kace in ba zaƙi ba biya”,”ku bani kudina kafin in muku akuya”,”kinga Anna barni dashi” ta fada tana dawowa gaban Anna, “kayi min akuya ni kuma in maka bunsuru, in ka fasa yin akuyar ka raina uwar data haife ka” zaro ido mai lemo yayi jin tana naima ta zage sa, “kinga jikalle ta, taho mu shiga ciki, kai kuma ka kwana a kofar gidan” tana gama fadin haka taja hannunta, jiyowa tayi tana masa gwalo, “wllhi Allah ya isa kudina”
Shere fisabilillah.
✨✨ *ZAINABU ABU* ✨✨
*Na*
*ZAINAB A BARDE*
*ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITER’S ASSOCIATION*
(A.Y.T.W.A)
Free page 5 nd 6
****
Suna komawa ciki ta taya Anna suka karasa abincin rana, ruwan wanka Anna ta dora mata, sanin halinta komin zafi bata iyayin wanka da ruwan sanyi, yana yin zafi Anna ta hada mata, sannan ta kai mata shi bayan gida, “jikalle fito kiyi wankan, ga ruwan chan nakai maki” Zainabu da harta fara bacci, ta fito tana musussuka ido, bandakin ta shiga tayi wankanta, tare da dauro alwalla, da yake har an fara kiran sallar azahar, tana fitowa itama Anna ta shiga tayi wankan, salla sukayi sannan Zainabu ta zubo musu abincin sukaci, suna gama ci ta tattare kwanikan ta kaisu wajan wanke wanke,
“Anna”,”na’am jikata”,”anjima zamuje dandali, kinsan ana wasan bikin yar mai gari”,”hakane, to Allah ya kaiku lfy”,”ameen” hira suka cigaba dayi har aka kira sallar la’asar, salla sukayi, sannan Zainabu ta dauko tsintsiya ta share musu tsakar gidan duk da ba wani datti yayi ba, sannan tayi wanke wanke kwanikan da suka ci abincin rana, tana gamawa ta karbi markadan wainar gobe ta tafi kaiwa, andaici sa’a har taje ta dawo batayi fada da kowa ba.
Haka dai ta taya Anna aiki har magariba ta gabato, saida tayi sallar magariba, sannan ta fara shirin zuwa dandali, wata kudaddiyar atamfa ta dauko, “nide gaskiya Anna kiyi min sabon dinki, jibi fa ki gani gaba daya kayan nawa duk sun kode”,”kiyi hakuri jikata, kinga da yaya ma muke samu muna cin abinci, da sana’ar wainar nan fa kawai muka dogara, kuma nace miki kina fita talla kamar yadda yaran ƙauyan nan sukeyi, kince ke baza kiyi talla ba”,”wllhi ni Anna bazanyi talla ba, kuma wllhi dole ne kiyimin sabon dinki” ta fada tana bubbuga kafarta, tare da marairaice fuska kamar zatayi kuka, “yi shiru kinji jikata, badai dinki kikeso ayi miki ba” daga mata kai tayi tana murza ido, “karki damu insha Allah nayi miki alkawari zanyi miki dinkin”,”nagode sosai Annata, shiyasa nake kara sonki, nayi tsokana yadda nakeso, akawo kara, Anna ta tare min, hoo saini Zainabu Abu”
Sallama Siyama tayi, “ƙawata harkin karaso”,”ehh wllhi kinsan banaso muyi dare, nafiso da munje mu kalli abinda muka kalla mu dawo gida da wuri, Anna ina wuni”,”da ban wuni ba zaki ganni, saida kika gama surutun ki, sannan kika ganni”,”haba Annar mu yi hakuri kinji, haba tawan” nan dai sukayi mata sallama suka fito sai dandali.
Suna zuwa suka tarar har an fara gabatar da wasan, ga amarya nan da ƙawayenta, suma waje suka samu suka zauna suna dan taba hira, “ƙawata gafa mutumin nan yana zuwa” tsaki Zainabu tayi ganin wanda yake zuwa, “Assalamu alaikum gimbiyata” tsaki ta kuma ja a karo na biyu, “nikam Bala na tmby ka mana” washe baki yayi, ya dauka ko ta fara saukowa ne, zata kulasa, “amma dai a cikin dangin ku akwai maye ko?” zaro ido yayi jin wannan cin mutunci, “yoo in ba akwai maye ba irin wannan baƙin naci, soyayyace nace banayi dakai, ko ana dole ne, Bala”,”na’am gimbiyata”,”hohoho Bala, ka fita idona in rufe inajin kunyar ka fa, kada ka bari nayi maka abinda bazaka taba mantawa ba”,”nide indai zaki soni ki fadi koma miye, babu komi”,”kab amma dai Allah yai wadaran naka ya lalace, kinga Siyama tashi mu tafi” haka yasa suka baro wajan ba tare da sun kalli wasan ba, Siyama kuwa sai tsine mai take, yayi sanadiyar da basuga wasan da taci burin gani ba.
******
Durƙushe yake a gaban mahaifinsa, ya sunkuyar da kansa kasa, idanuwansa sun kada sunyi jajir, jijiyoyin kansa duk sun fito, jikinsa har rawa yakeyi tsabar bacin randa yake ciki, “Abee understand me plss, heyy stop I’ve already finished talking is either you choose us or her” yana gama fadin haka ya fice daga falon yana baza babbar riga, dama wajan aiki zaije,
“Mahammad Kareem” mahaifiyar sa ta kira sunan sa, tunda yaji ta kira cikakken sunansa yasan magana mai mahimmaci zatayi, “tunda har mahaifin ka bayason alakar ka da yarinyar nan to kayi hakuri ka rabu da ita” dogo kansa yayi ya kalli mahaifiyar sa, ita kanta saida ta tsorata ganin yadda idonsa ya kada, “Ammi I’m sorry pls it is not that I can’t leave her, indan hkn kuke so I’ll definitely leave her sedai this will be the reason for my passing away, xan mutu kawai Ku huta nima in huta! “Babu abinda zai same ka Muhammad Kareem sai Alkairi, ka cigaba da addu’a, nima zan cigaba dayi maka addu’a, kana tare da addu’ar mahaifiyar ka, a koda yaushe” ta fada tana shafa baƙar sumar kansa, hakan da Ammi ta fada masa yasa zuciyarsa ta danyi sanyi, “tashi kaje ka watsa ruwa, zakaji dadi a jikin ka” daga mata kai yayi ba tare da yayi magana ba,
Bayan ta gama sauraron duk abinda suke cewa, tana jin alamun za’a fito, da sauri tabar wajan tana cike da farin cikin wannan alamari, yau duniya tayi mata dadi, ji take kamar ta zuba ruwa a kasa tasha dan dadi, tashi yayi ya fito daga dakin Mahaifiyar tasa ya shige dakinsa, da kallo ta bisa har ya fice daga dakin, zuciyarta cike da tausayin ɗan nata, ta rasa wannan wace irin bakar gaba ce.
Shere fisabilillah.
✨✨ *ZAINABU ABU* ✨✨
Na
ZAINAB A BARDE
*ALƘALAMI YAFI TAKOBI WRITERS ASSOCIATION*
(A.Y.T.W.A)
Free page 7 nd 8
***
yana shiga dakinsa ya fada kan makeken gadon sa kirar royal, gaba daya duniyar tayi masa zafi, bai kamata Abee ya sako gabar su a cikin neman auran sa ba, ” I will never disappoint you Abee, I will do as you wish, I will leave Shahida even if that will be the end of my last breath, ya Rab i pray with the best name of yours, Rab don’t ever show me the day that I’ll betray to my dad’s command, ya Rab give me the effort to obey him appropriately, ya Rab i pray, ka cire min son yarinyar nan da duk wani abu da zaisa in bijirewa iyaye na” tashi yayi ya fada tiolet,
Ruwa ya sakarwa kansa, wani sanyi ya rigaji yana shigar sa, jin saukar zuwan a jikin sa, yana fitowa ya zura jallabiya, ya kwanta, dan baya jin zai iya zuwa office, saboda a zababban ciwo da kansa yakeyi, kamar zai rabe gida biyu, wayarsa ce ta fara ringing, sunan Nurul Qalb ne ya fito baro baro akan screen din wayar, kasa daukar wayar yayi, coz he couldn’t disobey his dad, ganin bazata daina kira ba, shiyasa ya saka wayar a silent, tunanin yadda zai cigaba da rayuwa ba tare da Nurul Qalb ba yakeyi, a haka har bacci barawo yayi awon gaba dashi, dama yana bukatar yayi baccin, daran jiya kwata kwata baiyi bacci ba saboda tashin hankali, Ammi ce ta shigo dakin, zama tayi a gefen gadon tana kallon sa cike da tausayi, “ka cigaba da hakuri Allah yana tare da masu gaskiya da masu hakuri, soon everything will be alright” fita tayi tare da ja masa kofa.
****
“Umma! Umma! Umma! “ke Shahida what’s wrong kikemin irin wannan kiran?”,”Umma where is Abbana?”,”ya fita office kema kinsan ba’a samun sa a gida a ɗai ɗai wannan lokacin, but are you really okay?”,”Umma I’ve been calling Kareem’s number but he isn’t picking, Umma I’m afraid of his dad kada ya hanamu yin aure”,”Shahida I’ve been telling you earlier to remove his love out of your mind , don’t even let your dad to know this, in kuwa ya sani wllhi ranki zaiyi mummunan baci”,” but Umm… dakatar da ita tayi ta hanyar daga mata hannu, hakan yasa dole tayi shiru, tare da fashewa da kuka, da gudu ta haura sama tana kuka, abin kwanin ban tausayi, dakinta ta shiga ta fada kan gado tana sakin wani marayan kuka, cigaba da kiran wayarsa tayi, amma still no answer, kara fashewa da kuka tayi, a haka har bacci ya dauketa with dried tears on her face.
“Saddiqa wato kece kike daure wa yaron nan kugu ko?”,”Alhaji nifa I don’t even know what you are talking about”,” ohhh dama how would you know? Let me tell you something, dagake harshi, karku kuskura gobe yaƙi zuwa office, lots of work yana can office dinsa yana jiransa saida na tmby akace min baizo ba, wato dan nayi masa fada, shine zaiƙi zuwa aiki, Allah yasa gobe kar yazo, I will show you the true colour of mine, dan Allah Alhaji ka rika sassauta wa yaron nan”,”ohoo wato dai maganata tana kan hanya kece dindai kike hure masa kunne”,”wllhi ba haka ban… ko sauraran ta baiyi ba ya shige bedroom dinsa, ransa na suya, tashi tayi ta fito daga dakin tana sharar kwalla, she don’t exactly know what is wrong with her husband these days gaba daya ya birkice, ya kuma chanza mata, ita dai tasan da ba haka mijin ta yake ba, amma tana kaiwa Allah kukanta komi yayi farko yana da karshe insha Allah.
Mami na ganin fitowar Ammi ta shiga dakin, dama tana labe duk taji abinda suke cewa, shiga dakin tayi, ganin baya dakin kuma taji saukar ruwa, shiyasa ta tabbatar yana toilet, kaya mararsa nauyi ta fito masa dashi, yana fitowa ta tayashi ya shirya, cikin makirci da kisisina tace, “Alhaji are you alright? It seems as if you are a bit angry,”ki bari kawai Maimuna, abubuwan yaron chan sun fara isata, ya rasa wadda zai ce yana so, sai yarinyar nan ƴar wajan Alhaji Bukar, kuma yasan da cewa duk duniya banida makiyi sama da mahaifin yarinyar”,”ai ina ganin Alhaji this is so simple kallon ta yayi jin tana kiran abinda yake bakanta masa rai da abu mai sauƙi, “ni a nawa ganin ka bi duk wata hanya da zaka bi, dan ganin ka toshe duk wata kofa da kasan zata sada shi da yarinyar, sannan shi kuma Alhaji Bukar kaje kaja masa kunne akan ƴarsa ta rabu da danka, idan ba haka ba zaka dau mummunan mataki akan yarinyar”,”wow!! That’s why I always love you , saboda duk lokacin da na shiga damuwa, kinsan hanyar da zaki bi ki faranta min rai”
Murmushi ta saki tana fadin “ba komi it is my priority,”yaran nan sun dawo daga makaranta kuwa?,”ehh sun dawo amma yanzu suna islamiyya,”to in sun dawo kice musu inason ganin su”,”to shknn Alhaji lemme leave you to have some rest, jinjina mata kai yayi, tana fitowa daga bangaran Abba, tana saukowa main falo taga Ammi ta zabga uban tagumi, murmushi tayi, “this is how I always want you to be, I don’t want you to be damn happy “tagumi ma yanzu kika farashi a gidan nan, muddin na haifu a wajan iyaye na” zama tayi a kusa da Ammi tare da marairai ce fuska,
“Saddiqa lfy kuwa kika zabga uban tagumi haka?” firgigit tayi saboda batasan da zaman ta ba awajan, “wllhi Hajiya Maimuna, Alhaji ne ya sako yaron ki a gaba, akan zanchan naiman auransa, yace Kareem will never marry shahida because she is his enemy’s daughter, dan Allah mai zaisa ya sako gabar su, a cikin neman auran yaron nan? hakane take heart dears insha Allah everything will be alright, mu bi komi a sannu, I’ll talk to him insha Allah he might Change his decision,”Allah yasa to, yauwa in yaronki sun dawo yace yana son ganin su” daga mata kai Ammi tayi, saboda duniyar gaba daya tayi mata babu dadi, tashi tayi ta wuce bangaran ta, ranta fal farin ciki.
*******
Boss! Boss!! Boss!!! jiyowa wanda ake kira da Boss yayi, Masha Allah shine abinda na iya furtawa, saboda cikar haiba, da kamala, ta matashin saurayin mai jini a jiki, mai ji da kuruciya, a hankali ya dago da idanuwan sa, da suke fari tar, ya kalli wanda yake kiransa, da Boss, cikin zazzakar muryarsa ya fara magana, “Baabaa lfy kake kwalla min wannan irin wannan kiran?”,”Boss ka kunna labarai, gaba daya garin nan ya dauka akan fashin da mukayi jiya da daddare a Bank din nan” remote ya dauka ya kunna tashar labarai,
“Muna kawo muku labarai da ganan gidan TV A nd Z, to masu sauraran mu kamar yadda kukejin jita jita, akan wannan shaharanran dan fashin, mai suna Boss, wanda har yau babu wanda yasan kamannin sa, yauma ya sakeyin sata a shaharanran Bankin nan, dif ya kashe TV murmushi dauke a fuskar sa, “Baabaa ka bari kawai, garin nan ma bazai gigice ba, sai randa muka kaddamar da nest plan dinmu”

Leave a Comment