❄❄❄❄❄❄❄
*YAYA NANE KO MIJINA 2020*
❄❄❄❄❄❄❄❄
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*🌞
( _WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ 💪)
https://www.facebook.com/100452275039839/photos/a.100452311706502/100452611706472/?type=3
*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
0⃣1⃣
*Itafa waiwaye akoda yaushe tana zama adon tafiya ne…*💃💃
*Bismillahi rahamanir rahim*
,,,,,, Cikin sauri take har haɗa littattafan dake zube akasan ɗakin, cikin mintina ƙalilan, duk ta gama harhaɗawa ,ta ije kowanne a ma’adanar shi, tana fitowa suka hada ido lokaci daya suka sakarwa junan su murmushi.
Tace”aunty kingani Sai yanzu nagama.
“Alhamdulillah dama ALLAH ALLAH nake naji kin gama, domin yanzun duk inda yake ina da tabbacin yana kan hanya,saiki shiga ciki kiyi wanka kizo kici abinci.
“To aunty bani minti goma IN SHA ALLAH.
“Jeki nabaki minti talatin.
Aikuwa bata jira ta karasa maganar ta ba, tanufi ɗakin ta, ta sakar wa kanta ruwa tana lumshe ido zuciyar ta cike da fargaban abinda zata tarar agun Yayan nata…
cikin mintina goma harta gama shiri.
Bawani kwaliya tayi ba, Amma tayi kyau ta sa riga da zani na atamfa sannan ta dauko hijabin ta, harkasa ta saka sannan tafito.
Tana fitowa suka hada ido da ya’yan nata, Yana cin abinci.” ta durkusa harkasa ta gaishe shi , sannan ta nufi kitchin ta debo abinci ta zauna tana ci.
Babu wanda yayiwa wani magana acikin su harsuka gama, ta kwashe kayan abincin tashiga dashi kichin.
Harzata buɗe kofar dakin ta, taji ankira sunan ta Wanda ko amafarki taji, muryan Nan tasan ma’mallakin ta
Cikin natsuwa take tafiya har takai inda yake zaune tunshigowar shi tace”ya’ya gani.
Saida suka kusa mintina uku zuwa biyar baice mata kumai ba,daga bisani yadago Kai, Yana kallon ta sannan yace”wai saboda ALLAH maryam sai yaushe zakiyi hankali, ki daina wawta?
Cikin rashin fahimtar inda yadosa take kallon shi, Dan itah a’iya saninta babu abinda ya haɗasu bata yi komai ba… Tsawar daya daka mata shiya dawo da itah daga duniyar tunanin da tashilla….
Zaki bace min dagani ko saina rufe ki da duka kije ki dauko han out ɗin nagani.
Jikin ta har kerma yake tanufi dakin tana shiga ta fashe da matsanan cin kuka,cikin kukan tace,O Ni maryam na shiga uku wanan wani irin ya’ya ne? dakayi abin fada dawan da bana faɗa ba sai ya hau ka da masifa.
Nan dai tashare hawaye ta fita dantasan,ko giyar wake take sha bazata fita da hawaye afuskar ta ba.
Yanda ta barshi haka ta dawo tasame shi,ta mika mishi Yana karba,ta sunkuyar dakan ta babu abinda takeyi aranta sai addu’ar ALLAH yasa ta rubuta daidai yanda yace.
Cikin tsawa taji ya kira sunan ta,saboda tsora ta har saida tayi fitsari a’inda take zaune.
“Na’am
“abinda nace ki rubuto min kenan?
Kayi hakuri, ya’ya zan sake rubuto maka wani IN SHA ALLAH.
“Tashi kibani guri sakarya kawai.
Cikin sauri take tafiya,harta shiga dakinta tana shiga tafaɗa kan gado tana kuka Mai tsuma zuciyar duk wani mai sauraro ahaka dai harbarci barawo ya dauke ta.
Sai misalin karfe shida ta farka tana farkawa ta nufi toilet tayi alwala tayi sallah tana gamawa tanufi kitchen Dan taya auntin ta,aiki Dan tana da lecture karfe 8am.
Tana sauka tanufi kitchen jinkarar ruwa shi ya tabbatar mata auntin nata tana ciki, “good morning aunty
“Good morning my beautiful sister,kin tashi lafiya?
Lafiya kalau.
Cikin sauri suke aiki basufi awa daya ba suka gama kammala duk abinda suke da bukata.
Suna gamawa ta nufi dakin ta tayi wanka ta danyi make up Dan kukan datayi jiya yasa duk idon ta sun shige ciki, doguwar rigar jallabiya ta dauko ruwan madara ta saka, sannan tadauko veil baka ta daura ta ɗauko flat shoo baka ta saka aƙafarta.
Haka dai taji zuciyar ta na bugawa batasan dalili ba saikawai tayi addu’a ta nufi falo.
Tafiya take cikin natsuwa har’ta’iso falon tana Isa taga harsun Fara cin abincin.”inah kwana ya’ya.
Lafiya Lau.
Nandanan tadauki plet ta zuba iya abinda zata iya ci, tana gamawa ta mike tsaye tace”aunty saina dawo.yaya sai… tunkafin takarasa ya daga mata hannu.
Koda takai makaranta jiki asanyaye ta Isa aji tana shiga lectural Yana shigowa ,ahaka dai har akagama lecture Bata fahimci komai ba.
Tana fitowa daga ajin,ta nufi hanyar da zata sadata da gindin bishiyar, da ta saba Zama akoda yaushe.
tana zaune tayi zurfi cikin tunani taji anata kwalla mata kira,ɗagowar da zatayi ta hangi Yusuf mutumin da ya takurawa rayuwar ta.
Yana isowa inda take ya zauna suna fuskantar juna yace”
Haba Maryam kina ji inata kiranki kikayi banza Dani,kodai nayi miki laifi ne?
girgiza Kai tayi tace,” a a wallahi babu abinda kamin kawai kai nane keɗan min ciwo.
“Ok babu matsala Amma dai kinsha magani ko?
Cikin kosawa da maganar shi tace”Yusuf bara natafi gida sai mun haɗu gobe….
Bata jira jin abinda zaice ba ta miƙe tana tafiya kamar ance ta juya baya kawai Sai ganin mutum atsaye tayi yana kallon ta….
nandanan ta tsaya cak ko ɗaga kafarta bazata iya ba, saboda tsanani tsora ta.
Ganin haka yasa yanufe ta, gadan gadan Yana isowa inda take ya kalle ta cikin bacin rai.
“yace Daman Maryam abinda kike Yi kenan ko? to kisa aranki,, Inda annabi yabar duniya haka kema kinbar makarantar Nan Kenan har’abadan.
Yana gama faɗan mata haka yajuya yanufi motarsa yana shiga ya fizgi motar…
ganin fitar shi yasa ,itama ta nufi motar ta tayi hanyan gida cikin tashin hakali.
***
Hashim tunda yabar harabar makarantar tuki kawai yake kamar zai tashi sama ,kirjinsa kuwa tafasa take kamar zata faso kirjinsa,ikon ALLAH ne kawai yakai shi gida.
Yana shiga yasamu guri yayi parking.
Yana sauko wa yashiga cikin gidan ko sallama babu…. zainab tana zaune a fallon Yana shigowa tanufe shi tana
Mishi sannu da zuwa.
Ko kallon inda take baiyi ba ganin haka yasa Tani me guri ta zauna,, domin tasan idan Yana cikin fushi irin haka bayaso ana mishi magana.
Ba’afi mintina biyar ba,tashigo gidan cikin kuka tafaɗa jikin aunty zainab tana cewa, “aunty ki taimakeni, ki ceci rayuwa ta,wallahi babu abinda ke tsakani na dashi.
Cikin Rashin fahimtar inda maganar t ta dosa “tace wai meya faru ne?
Cikin kuka ta faɗa mata duk abinda ya faru.
“To ki daina kukan,Nan Kar ki sakarwa kanki zazzabi Kinga yanzu Yana cikin fushi,amma nayi miki alkawari zanbashi hakuri ke kuma ki kiyaye.
“IN SHA ALLAH.
Suna cikin haka kawai sai ganin shi ta yi yanufo gurin su hannun sa rike da bulala.
aikuwa tana ganin haka ta tashi da sauri ta boye abayan aunty zainab.
, “Dan ALLAH kayi hakuri wallahi ta faɗa min babu abinda ke tsakanin su.
wallahi idan baki matsaba zan hada dake.
Sanin hali irin nashi yasa ta zame jikin ta
aikuwa tunda yafara dukan ta babu sa sauci tuntana ihun niman agaji,har ta sadakar ganin haka yasa zainab tanufo shi cikin kuka tace.
“Hashim kasheta kakeson yine?
Jin haka yasa yadawo cikin haiyacin shi yanuna ta da Dan yatsar hannun shi Yana cewa” kadan kinan.
Aikuwa tunkan yakarasa magana tayi kasa sumammiya.
Ganin haka yasa aunty zainab kwalla kara atare suka nufo gurin ta ko motsi batayi…..
*Komai yasa Hashim fusata haka Dan yaga Maryam da yusuf?*
*hy guys am back again with another blood Booster hope you will like it* .
*Pls comment*🍭🍭🍭🍭🍭❄❄❄❄❄❄❄❄
*YA’YA NANE KO MIJINA 2020*
❄❄❄❄❄❄❄
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION*🌞
( _WE AIN’T PERFECT BUT WE’RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS_ 💪)
https://www.facebook.com/100452275039839/photos/a.100452311706502/100452611706472/?type=3
*P.W.A*✍️
*STORY*
*&*
*WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
*Bismillahi rahamanir rahim*
0⃣2⃣
“`Prayer is the key that opens your day to every blessing. It also is a lock that closes the night to keep you safe while sleeping. So what you have to do is “use your key all the time.“`
,,, Cikin sauri yanufi motarsa da ita…. gudu yake Yana isa yafita da gudu Yana Kiran dr,Yana kallo akashiga da ita cikin.
“meyasa nakasa jurewa? meyasa meyasa?hakadai yarinka jerowa kansa tambayuyi,,, Har dr ya fito…
“Ka kwantar da hankali ka,ta farraɗo,, saidai Naga duk jikin ta shatin bulala,
Matar kace ko kanwar ka ?
Tambayar tazo mishi, abazata shiyasa yarasa amsar da zai bashi….
Kwanan su biyu a asibitin aka sallame su.
Cikin kwana biyun kuwa, duk wanda yakalli Hashim yasan cewa Yana cikin tashin hankali…..
Ranar da aka sallamesu,suna
Isa gida duk kansu suka zauna afalon gida….
Hashim juyowa yayi Yana fuskantar Maryam yace..
“Maryam.
“Na’am ya’ya.
“Dama bawani abu yasa na bukaci idan muka dawo nayi miki magana da keba,, saidan inbaki damar ki..
Cikin sauri ta ɗago Kai ta kalle shi sannan ta maida Kai kasa.
“Shin Maryam aure kikeso ko karatu?
Saida tayi shiru nadan mintina biyu zuwa uku,,, sannan ta ɗago Kai tace”ya’ya wallahi karatu nakeso,wan…
Tunkafin takarasa ya dakatar da ita.
“To wancan Dana ganku tare wanene shi?
“Ya’ya Department dinmu ne daya,bani da wata alaka dashi.
Hashim saida yayi wata buyayyiyar ajiyar zuciya yace” to shikenan tunda shi wancan ba saurayin ki bane to wanene saurayin ki?
Cikin razana ta ɗago Kai tana kallon sa tace,”wallahi (ALLAH) ya’ya banda saurayi Kuma ,bazan auri kuwa ba sai wanda kazabar min, Dan inada tabbacin banida wanda yake so dabkauna ta irin ka,duk fadin duniyar Nan, Dan haka nake da tabbacin bazaka zabamin wanda zai cutar da niba.
Hashim baisan lokacin da ya miƙe tsaye ba Yana murmushi yace,”(ALLAH)yayi miki albarka,dayar Dar (ALLAH) zanzabar Miki, miji na gari IN SHA (ALLAH).
Haka dai suka watse kuwa yanufi shashinsa.
Hashim Yana shiga daki yafaɗa kan katifar sa Yana murmushi…. shidai yana ma’makin sanyin hali irin na Maryam, gashi dai shine ya daki ta, Amma Kuma itace ke bashi hakuri da haka haryayi barci.
Washa garin ranar aunty zainab ta tashi da matsanan cin zazabi, sai kuka take jikin ta yayi zafi ganin haka yasa Hashim ya kaita asibiti gojin farko aka tabbatar musu da tana dauke da juna biyu.
Farin ciki agurin Hashim baxai misaltu ba,domin kuwa kudi yarinka rabawa Yan asibiti….
Farin ciki da Maryam tayi harya wuce wanda Hashim yayi…
Haka dai suka cigaba da rainun cikin aunty zainab… hargashi yau tana cikin wata na tara,tun kafin lokacin haihuwar tazo, duk lokacin da Maryam tashiga kasuwa saita sayawa jaririyar da aunty zainab zata haifa kaya tana buye wa.
Ranar juma’a aunty zainab ta haifo ƙyakyawar ɗiyar ta mace,murna agurin Maryam bazai kwatantu ba….
kayan da ta dade tana tarawa, tafitar aka sakawa yarinyar.
ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Hashim Khadija,,,, Amma suna kiran ta, da ikram.
Tunbayan da sukayi arba’in ikram takoma ahannun Maryam, tsakanin ta, da aunty zainab saidai, Tasha nono ta koma hannun Maryam.
Ahaka hartakai shekara daya aduniya, zuwa lokacin babu Wanda tasani sai Maryam, idan Maryam tafita ta rinka kuka kenan har’sai tayi barci.
Tunbayan faruwan wanna lamarin,
Maryam bata Kuma zuwa makaranta ba,,, , hakan ba ƙaramar damin Yusuf
yake ba,, ,gashi baisan gidan suba,
kullum da maganar ta yake kwana
Yake tashi.
Kana ganin shi,saika tausaya mishi duk yafita daga haiyacin sa,ganin haka yasa mahaifin shi ya zaunar dashi Yana tambayar sa.
“Aiya sanina Yusuf bakataɓa niman wani Abu agurin mu karasa ba,
Idan Kuma akwai kafaɗa min.
Shiru kamar bazai bada amsa ba,ya Dan ɗago Kai yace”a a Abba babu duk abinda nake so Kuna min.
“To menene damuwar ka, kaga duk yanda karami.
Cikin kuka umman shi take magana”Yusuf kasan cewa duk duniya bamu da wani sauran Jin dadi daya wuce ganin ka cikin walwala da annashuwa,.,,, bayan Kai wa muke dashi?
” kai kafada mana damuwar ka,ko wace iri ce zamu yi maka;maganim ta.
Shiɗinma kuka yake, saidai mara sauti yace”wallahi umma nasani kuma ina alfahari da kasancewar ku iyaye agare ni.
Nandai ya labarta musu labarin Maryam ,da rashin sanin inda zaiganta.
Duk kansu sun jajanta mishi da alkawari duk inda maryam take saisun nemeta.
Hakan bakaramar dadi yayiwa Yusuf ba.
Haka dai iyayan yusuf suka cigaba da niman gidan su Maryam,har suka samu ta hannun ƙawar ta ikram.
Tun bayan wannan Rikicin daya faru tsakanin Maryam da Hashim,basu sake samun sabani ba Dan dama shi matsalar shi daya ne,bayaso yaga Maryam da saurayi….
to dama Kuma itah wannan ma baya gabanta.
Hashim Yana kwance a falon gidan Mai gadi yazo yace,”yallabai wasu mutane ne suke sallama dakai.
“DAGA inah?
“Ban tanbaye suba… Amma daga gani mutanan kirkine.
“Niban tambaye ka ko mutanan kirki bane ko na banza,daɗi na dakai saurin yarda da mutani kaje kashigo dasu.
bayan sunshigo ne
Hashim ya miƙa musu hannu sukayi musabaha,…… sannan yasa Maryam takawo musu ruwa.
Tana zuwa ta gaishe su,suka amsa mahaifin yusuf yace,”mun gode Maryam.
Cike da ma’maki afuskar ta, tace bakomai…. saidai kallon mutumin datayi kamar ta sanshi idan kuwa bashi bane to ita dai ta taba ganin irin fuskar nan,,,, haka dai ta haura sama cike da mamaki.
Hashim Jin ankira sunan Maryam yasa gabaki daya yarikice,,,, cikin ranshi kuwa addu’a yake ALLAH yasa ba niman auran ta suka zoba.
maganar da mahaifin yusuf yayine yadawo dashi daga duniyar tunanin da ya shillah.
“Da farko dai sunana alhaji bala jawabi dankasuwa ne ni,wayannan Kuma kannena ne….
“Ok ALLAH sarki Ni sunana Hashim abubakar sadiq,,, saidai bangane kuba…. abinda ya iya faɗa kenan,,, domin shi akage yake yaji abinda yakawo su.
“Ok dama bawani abubane Dan waje nane yaga ƙanwan ka Yana so,shine yace muzo Nima masa izini.
“Cikin ma’maki yace ƙanwata ainah? “ni banda ƙanwa agarin nan.
“A a bawata bace illah Maryam.
“Wacce Maryam?
“Wacce takawo Mana ruwa idan banyi kuskure ba .
Tsananin fusata Hashim baisan lokacin daya tashi tsaye ba yace,”Dan ALLAH ku tashi kufita tunkan Raina yabaci.
“Mahaifin yusuf yace”malam Hashim niman aure muka zo ba tashin hankali ba.
“Niman auran matar tawa?
Jin haka yasa gabaki ɗaya suka rikice…. suka bashi hakuri dacewa,”wallahi Hashim ba musan cewa matar aure bace,ai iya sanin mu cemana akayi , gidan ya’yan tane Nan ,kayi hakuri.
Da haka harsuka fita agidan suna Kara bashi hakuri….
Shikuwa mahaifin yusuf duk inda ranshi yayi dubu to yabace….. shi dama shi kaɗaine abin bazai dameshi ba,hakan Nan yaje ya dauko mahaifin yarinyan nan yumna wacce akabawa yusuf yace baya so,shikuwa yace babu maibyiwa ɗan shi auran dole….. haka dai suka hakura da magana auran.
Wanda haryanzu tana Nan Batayi aure ba,,, saboda tsananin son da takewa Yusuf….
To gashi yaje yajawowa kanshi abin gori.
***
Shikuwa Yusuf tun bayan tafiyar su gidan su Maryam yake ta Addu’a ALLAH yasa kar’asamu wata matsala,,,, haka kawai yaji zuciyar sa tana bugawa.
Mahaifiyar sa tana lura da yadda yake ta kaiwa da komuwa tace,”Yusuf ka kwantar da hankalin ka,da yardar ALLAH babu abinda zaifaru sai alkairi…..
“ALLAH yasa haka.
“Amin.
Ba”afi mintuna biyar ba yashigo gidan kana ganin sa kasan ransa aɓace yake…. yusuf naganin shi yatashi yanufi gurin shi Abba Kun….Marin da yajine yasashi kasa karasa maganar…
Kallon abban nashi yake cike da ma’maki,Dan shi a iya sanin shi tunda yake mahaifin shi baitaba zaginshi ba bare akai ga mari.
hajiya Fatima ma haka tsaya tana ma’makin abinda zaisa alhaji ya mari Yusuf,,, saidai tasan koma menene to bakaramar abubane .
Cike da bacin rai ya kalli Yusuf Yana cewa,”ni zaka maida karamin mutum? ni zaka sa ayimin rashin mutun ci? nizaka sa ayimin gori agari?
” to bara kaji,duk abinda kake so ina kukarin Naga namaka,,, Amma kasani,hakan bazaisa na tsalake iyakokin ALLAH ba ,Don haka daga rana mai kamar ta yau bana son sake jin zancan maryam acikin gidan nan.
“ALLAH yawuci zuciyar ka alhaji wani abinne yafaru?
“Wannan yarinyar ashe matar aure ce Yusuf yasa muje Nima masa auran ta hargidan mijin ta? “inbadan ALLAH yasa mijin Mai hankali bane da wayasan irin cin mutun cin dazai Mana?
, “sannan nanriga na yanke shawaran zan aurawa Yusuf yarinyar Nan yumna…. “har na biya sadaki Nan da wata ɗaya, Don haka kuje kufara shirye shirye.
Yusuf wanda tunda mahaifin shi yafara magana yake daskare aguri ɗaya, ko ƙwaƙƙorar motsi bai iya ba… sai asannan yaga wata farar haske ta gift ta idon shi,harya kusa shigewa cikin dakin shi.
juyuwar da mahaifin yusuf zaiyi kawai sai ganin Yusuf yayi yazuɓe kasa babu alamun Rai atare dashi,dagudu ya nufi gurin shi,batare da bata lokaci ba suka nufi asbiti dashi Rai ahannun ALLAH.
****
Shikuwa Hashim Yana raka su ya dawo cikin gida inbanda zufa babu abinda yake yi ,axuciyarsa Yana tunanin ta inah zai bullowa lamarin nan, haka dai yarinka tufka da warwara har yasamarwa kansa mafita…
Cikin sauri yaja motar sa yafita ,gudu kawai yakeyi ikon ALLAH ne kawai yakai shi kaduna. Yana Isa maigadi yabude mishi gate yanemi guri yayi parking.
Da sauri maigadin yanufo shi Yana Mai sannu dazuwa,”alhaji ba’ba Yana gida? abinda ya iya tambayar sa kenan batare daya amsa gaisuwar Saba.
Cikin sauri ya amsa da “eh Amma saidai akwai baki acikin gidan.
Da sallama yashigo gidan,suka amsa alhaji ba’ba cike da ma’maki yace,”Hashim lafiya naganka awannan lokacin?
“Lafiya kalau abba .
“To Naga ɗazu mukayi waya baka faɗamin zaka zo ba.
Cike da murmushi afuskar sa yace,”kawai dai ina zaune naji inaso naganka shiyasa nazo
…. Amma gobe zan koma IN SHA ALLAH .
Sosai maganar sa ta faranta ran mahaifinsa yace,”To ALLAH ya kaimu,samu guri ka zauna garama da kazo,,,, domin kuwa waƴannan da kake gani sunzo niman auran ƙanwar kane safnah.
Zama sukayi gabaki ɗayan su aka tattauna zancan auran,,, ,cikin ikon ALLAH aka saka ranar auran Nanda wata daya mai zuwa,,, Dan angon zaitafi karatu India Kuma so yake yatafi da matar sa.
Bayan tafiyar su alhaji ba’ba yake tambayar Hashim dalilin zuwan shi kaduna da yamma haka…. Don kuwa yasan tabbas haka kawai bazai taso yabar aiyukan Saba .
Cike da natsuwa yace “dama bawani abu bane alkawarin da akayi shekara goma Sha tara nakeson atayar dashi inaga lokacin yayi.
Saukar da ajiyar zuciya Alhji ba’ba yayi yace,”Hashim kana ganin babu wata matsala?
“cikin ladabi yace, “IN SHA ALLAH.
“Babu damuwa ALLAH ya taimaka…. zanyi magana da Usman naji yanda za’ayi, Danni tunani nake kamar ahada da na safnah aiyi lokaci daya koya kagani?
“Sunkuyar da Kainsa yayi yace “to abba duk yanda kace.
Godiya Hashim yayi sannan yatashi yashige gida,danufin gobe da asuba zai koma Kano.❄❄❄❄❄❄❄
*YA’YA NANE KO MIJINA*
❄❄❄❄❄❄❄

Leave a Comment