Books Reviews & FAQs

Yarima Fudhal Hausa Novel Complete

07/07, 16:12] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

*YARIMA FUDHAL*

 

*©FIDDAUSI S.A*
(QURRATUL-AYN)

01

 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM…….!

 

 

DUKKAN YABO DA GODIYA SUN TABBATA GA ALLAH MAD’AUKA KIN SARKI MAI KOWA MAI KOMAI.

INA ROK’O AGARESHI YANDA YA BANI IKON FARA LITTAFIN NAN LAFIYA, YA BANI IKON KAMMALA SHI LAFIYA AMIN.

TSOKACI

WANNAN LITTAFIN K’AGAGGEN LABARI NE BANYI SHI DANCIN FUSKAR WANI KO WATA BA, FATANA KAWAI AL’UMMA SU AMFANA DA DARASIN DAYAKE CIKIN SA.

BANYAR DA WANI KO WATA YA JUYAMIN LITTAFINA TA KO WACCE SIGA BA DUK WANDA YA JUYAMIN LITTAFI KO YA CIRE SUNANA ZAN BARSHI DA ALLAH KAWAI.

**********************************

**

 

 

 

Gida ne tamfatsetse mai dogayen katangu da suka sha zane mai d’aukan hankalin wanda yake kallo, hakanne zai baka tabbacin cewa gidan sarauta ne.

Haka kuma girman gidan zai baka mamaki kai kace gari ne guda.

Gidan na d’auke da b’angare guda bakwai, banda filin shamaki da k’afa bata iya kaiwa k’arshen sa.

Soron fada shine soro na biyu a cikin gidan, sai kuma soraye uku da za ka sake wuce wa da zai sa da ka da farfajiyar gidan, a nan ne za ka ga b’angare har guda shida. B’angaren Mai Martaba sai b’angaren Mai Babban d’aki, sannan wajen Matan sarki guda biyu, sannan b’angaren yaransa, sai can ciki kuma b’angaren bayi ne tare da ma’aikatan gidan.

Sai kuma b’angaren kwara-kwaren sarki daban sannan kicin a can k’arshen gidan, sai shamakin doki da shamakin tsakar gida.

°°°°

Gidan ya hargitse baki d’aya, jama’ar gidan sai kai kawo suke daga tsakar gida zuwa sauran sassa na gidan.

Hakan ne zai tabbatar maka da wani muhimmin abu ne yake shirin faruwa a cikin gidan.

“Allah ya taimaki sarki ina mik’o gaisuwa, Yarima Fudhal na kan hanya duk kan jama’ar gari kowa na marhabin da dawowar sa”.

Murmushi sarki ya yi wanda ba’a iya ganin sa sabida rawaninsa daya rufe rabin fuskarsa, amma duk wanda ya kalli fuskarsa zai san ya yi farin ciki da jin wannan maganar.

Fadawa suka hau fad’in’ “Sarki ya amsa gaisuwa kuma ya yi farinciki da kyakkyawan albishir d’in ka”.

Waziri Salmanu ya d’an rusuna gaban sarkin shi ma yana mik’a tasa gaisuwar tare da fad’in’ “dole kowa yayi farin ciki ya mai Martaba, domin yau kimanin shekaru goma sha biyar kenan rabon Yarima Fudhal da k’asar nan, gashi kuma yau zai dawo k’asarsa cikin k’oshin lafiya tare da nasarori masu tarin yawa”.

Shi ma Fadawa suka amsa masa da’ “Sarki ya amshi gaisuwarka ya kai babban waziri “.

Haka dai kowa ya dinga kawo gaisuwarsa Fadawan sarki na amsa masa.

Sarki ya cika da murna da farin ciki ji yake kamar yajawo goben yaga Yarima kuma d’a mafi soyuwa a gareshi.

 

Mai Martaba Sarki Ubaiyd kenan, ya gaji sarautan a wajen mahaifinsa sarki Salmanu. Shi kad’ai ne d’a a wajen mahaifin nasa bashi da wa ba shi da k’ani. Shiyasa yakeji da iyalinsa sosai musamman Yarima Fudhal wanda yake ganin shi ne magaji a bayan sa.

Sai dai wani abu dake b’atawa mutane rai da Sarkin kuma basu da ikon magana akai shine.

Sarki Ubaiyd ya tsani a fad’i laifin yaransa, shi a ganin sa komai sukayi dai-dai ne.

Domin ‘ya’yan sarki ne kuma jikokin sarki ‘ya’yan masu fad’a aji a cikin k’asar, a ganinsa kome suke so suyi kuma komai sukai dai-dai ne.

Abin da mutane suka kasa fahimta kenan rashin ‘ya’ya da yawane ya sa shi yin hakan, ko kuwa son nunawa duniya yaransa sunfi kowa ne?.

••••••••••••••

Mai Babban d’aki Hajiya Marka mahaifiya ce ga mai martaba sunanta na gaskiya Hauwa’u.

Mace ce kamila mai son addini ga faram-faram da son jama’a, ga kuma uwa uba fad’a aji in dai taja layi a gidan ko sarkin k’aryarsa ya tsallaka balle kuma sauran al’ummar gidan.

Fulani Bingel itace uwar gida a cikin gidan mace mai alkunya da addini da son mutane, tana girmama dukkan mutumin daya girmama ta ba tada wulak’anci ko kad’an gata da son ado. Yaran ta uku, mata biyu an aurar dasu Sadiya da Sa’idah sai autan su Yarima Fudhal.

Sai Fulani Sokoto mace ce fara doguwa mafad’aciya ce tak’in k’arawa. Gata makira tasan luggar tuggu kala-kala, duk bayin gidan suna tsoron ta ainun, domin sarki yana yarda da maganarta d’ari bisa d’ari.

Tana da yara biyu Mace da Namiji Jalil da Jalilah su kad’ai ne yaranta a gidan.

 

Sai uwar Soro babar kwarkawara ce ta sarki, Sauran kwara-kwaran sarki guda biyu duk babu wadda ta tab’a haihuwa a cikinsu.

************

Kishingid’e take bisa kushin tasha ado kamar babu gobe sark’ar gwal ce dank’areriya a wuyanta hatta warwaro da ‘yankunne zuwa zobuna duk na gwal ne. Tana sanye da wani dank’areren less fari da ta d’ora alkyabba bak’a akai.

Gefe guda farantin kayan marmari ne ajiye sai bayi uku mata zaune a gabanta suna mata hira jefi-jefi.

Jakadiyya ce ta shigo da sallamarta ta zub’e bisa carpet tana gaishe ta.

 

Fulani bingel ta amsa fuskarta cike da annuri tana duban jakadiyya da kanta yake k’asa.

Jakadiyya ta cigaba da magana ba tare da ta d’ago kanta ba’

 

“Gani Gare ki, naji ance kina nemana ?”.

Fulani ta sake fad’ad’a murmushinta, kafin ta bud’e baki ta fara magana’ “Inaso a shirya dukkan abinda ya dace domin tarbar Auta na, sannan a canja masa bayi wad’anda ki ka amince dasu”.

“Angama ya shugaba ta”.

Daga haka Jakadiyya tamik’e ta fice, ta nufi b’angaren bayi domin cika umarnin Fulani Bingel.

Nan da nan ta gama bawa kowa aikin sa, an gyare b’angaren su Yarima tsaf.

An kuma gyare masa d’akinsa duk da cewar baya nan amma d’akin fes domin kullum ne sai an share an goge shi.

“Yanzu Mama wannan Yayan namu na dawowa Sarki zai daina bi takanmu fa, baya nan ma ya aka cika bare kuma ya dawo”.

Cewar Jalil kenan yana kishingid’e a gefan mahaifiyarsu.

Yaro d’an kwalisa kenan mai shekara ashirin da bakwai a duniya. Jalila dake kwance kan cinyarta taci gaba da fad’in’ “ai ina jin ma mance zai yi muma ‘ya’yansa ne, gaskiya Fulani ta cuce mu wallahi da take k’ok’arin rabamu da mahafinmu”.

 

Fulani sokoto ta d’an tab’e baki tare da murmushi tana shafa kan d’iyar ta ta.

“Haba dai ita d’in me?, ai ko tana yawo da guraye k’aryarta ta rabaku da mahaifinku ku dai ku zuba ido ba ga ni ba?”.

Sallamar d’aya daga cikin bayin gidan ne ya katse su daga tattaunawar da suke.

Baiwar ta fad’i gaban Fulani sokoto tayi gasuwa tana fad’in’
“Da girman kujerar ki uwar magajin gobe, hak’ika na jiyo wani batu mafi girma!”.

Fulani sokoto ta mik’ar da Jalila da ke kwance bisa cinyarta tana duban Baiwar ta ta domin jin batun da tazo mata dashi.

“Ina jinki Ladidi”.

“A gafarce ni Uwar Magajin gobe, albishir mafi muni ne ke tafe da ni, Fulani Bingel ta saka Jakadiyya ta canjawa Yarima Fudhal bayi,
bayan duk mun gama shirin mu a kan tsofaffin bayin nasa”.

Fulani Sokoto rik’e kai kawai tayi ba tare da ta iya cewa komai ba tsabar takaici, ta yiwa Ladidi nuni da hannu akan ta tashi tafita, nan da nan Ladidi ta mik’e ta fice jiki na b’ari.

“Yanzu Mama meye abin yi?”.

Jalila ke tambayar Fulani Sokoto da k’yar ta iya bud’e baki ta ba ta amsar.

“Zan yi tunani akan haka”.

Ta mik’e tayi cikin d’akinta ta barsu nan cikin falon na ta.

*****

Jakadiyya ta sa aka jere mata ‘yan matan bayin gidan kaf ta gama duba su duk ciki ba su yi mata ba kuma bata amince dasu ba, hakan yasa tace musu kawai su cigaba da aikinsu, ita kuma ta koma b’angaren Fulani Bingel.

Da shigarta ta fad’i a gabanta tana fad’in.

“Ayi hak’uri a gafarce ni na duba duk kan bayin babu wanda su ka yi, da za’a bani dama zuwa gobe da k’arfe bakwai sai a sake d’iban sabbin Bayi kafin zuwan Yarima”.

“An baki dama, kiyi duk kan abinda ya dace”.

“Nagode kwarai da gaske”. Jakadiyya ta mik’e ta fice.

*UNGUWAR KWARI*

 

Unguwace da mutane da dama su ke mata ik’irari da unguwar talakawa.
Domin a ganin su babu unguwar da ta kai yawan miskinai da gajiyayyu a cikin fad’in garin kamar Unguwar Kwari.

Unguwace mara tsarin gidaje ga tarkacen bola kala-kala a cikin unguwar layi-layi, gidajen duk na k’asa mara sa kyan gani.

Amma duk da katutun talaucin da ya yiwa unguwar yawa hakan bai hana a samu wad’anda suke neman nakansu da guminsu ba. Duk da wasu jama’a nawa unguwar lak’ani da unguwar k’azamai hakan bai sa an rasa masu tsafta cikin su ba sabida ba duka aka taru aka zama d’aya ba.

Gidane na k’asa wanda katangarsa iya rabi ce kana iya hango dukkan abinda mutanan gidan suke yi a tsakar gidan.

Gidan na d’auke da d’akuna biyu kacal, sai kicin da wani kwarab’abb’an band’aki da yasha tsimmokara kala-laka domin kariya.

Gidan tsaf dashi an share shi tas ko ba tabarma sai mutum ya zauna duk da turb’ayace a k’asan.

Wata ‘yar dattijuwar mata ce zaune bisa ledar buhu a tsakar gidan da sanda a gefanta.

Idanuwanta a rufe wanda shine zai baka tabbacin makauniya ce, magana take yi cikin d’aga murya’
“Aynu! Ke Aynu!! wai mai kike yi a cikin d’akin ne haka?”.

Dattijuwar ke ta b’ab’atu bakin k’ofar d’akin da take zaune.

Gidan shiru kai kace sambatu take babu kowa a gidan, can aka d’ago yagaggen zaninda a ke rufe k’ofar d’akin da shi da sunan labule.

Wata ‘yar budurwa ce da shekarunta ba zasu wuce goma sha biyar zuwa da shida ba ta fito da ga cikin d’akin. Tana sanye da wata kod’add’iyar atamfa da ba za ka iya tan-tance kalar taba bare ganin zananta, hijabin jikinta bak’ine amma ya zama ja tsabar dad’ewa da gajiyar wanki da rana.

Fuskarta watsai bak’ace amma ba can ba, tana da manyan idanuwa da gashin ido dana gira zara-zara, sumarta har kusan girarta hakan ne zai saka kasan tanada yawan gashi sai pink lips d’inta, duk da bak’ace. Amma leb’anta pink a tak’aice dai kallo d’aya ba zai sa ka fahimci kyawunta ba.

Wato dai tana da wani sihirtaccen kyawu na ban mamaki da ba kowa ke iya sanin hakan ba.

“Gani Ummata ina shiryawa ne fa, mai zan siyo miki?”. Tayi maganar cike da shagwab’a.

Murmushi Umman tata tayi, tana mai mik’o mata wata duk’unk’unanniyar Naira hamsin “Ungo Aynu maza je ki kisiyo mana garin kwaki da sugar musha, nasan baki karya ba ko?”.

“Ehh Ummana bari in je in dawo to”.

“To ki dawo lafiya akula da hanya”.

“Amin”. Aynu ta amsa tana mai sanya wani talitsattsan silifas da k’iris ya rage ya hudo k’asa ta sanya ta fice tana ‘yan wak’e-wak’enta.

Awaje taci karo da wani mutum dake jingine jikin wani icen dalbejiya, bai da k’afa d’aya sai guda d’aya yana
dogarawa da sanda.

Durk’usawa tayi har k’asa na ji tana fad’in’ “ina kwana Baba?”.

“Lafiya k’alau Aynu, kin tashi lafiya?”.

“Lafiya k’alau Baba, Ummata ta aikeni ne”.

“Ki dawo lafiya a kula da hanya”. Cewar Baban nata kenan. Ta mik’e ta ci gaba da tafiya abinta.
[07/07, 16:13] Nana Sales Aliyu Fbk Mai Quratu Group: *YARIMA FUDHAL*

 

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION®

 

 

©FIDDAUSI S.A (QURRATUL-AYN)

02

Mintuna kad’an da fitar ta sai gata ta dawo hannunta rik’e da leda bak’a k’arama, da sallamarta ta shigo cikin gidan Ummanta dake zaune bakin k’ofa kamar yanda ta fita ta barta ita ce ta amsa mata sallamar tana fad’in.

“Har kin dawo Aynu ?”.

“Ehh Ummata kinsan shagon Malami babu nisa ai”.

“To dauko kwano ki jik’a sai ki d’ibarwa Babanki ki d’ibi naki”.

“To Ummata”.

Ta amsa tana mai shiga cikin d’akin na su, sai gata ta dawo hannunta rik’e da babban kwano da kofuna guda uku.

Ta juye garin a cikin kwanon taje ta zuba ruwan da ta d’ebo tun asuba dake basu da ruwa sai asuba famfon unguwarsu yake zuwa.

Ta d’auraye garin sannan ta sake zuba ruwa ta dawo ta zauna ta dauki sugar ta sanya a ciki ta juya, ta zubawa Ummanta ta mik’a mata sannan ta sake zuba wani ta d’auka ta kaiwa Babanta d’akinsa yana kwance ta shiga da sallamarta yamik’e ya zauna yana amsa mata sallama.

Durk’usawa tayi ta ajiye masa kofin garin tana fad’in.

“Baba gashi inji Umma”.

“To sannun ki nagode sosai Allah muku Albarka !”.

“Amin”.

Ta amsa tare da mik’ewa ta dawo tsakar gidan inda Ummanta take ta zauna gefan ta tare da janyo ragowar garin ta hau sha.

YAMMACIN RANAR

Da yamma sai da ta kammala komai da zatayi a gidan, sannan tayi shirin islamiyya tayiwa Ummanta sallama ta tafi.

“Assalamu alaikum mutana nan gidan nan?”.

Wata mata ‘yar dattijuwa take ta kwad’a sallama cikin gida.

“Amin wa’alaikissalam Tasalla kece a gidan namu?, Bismillah shigo”.

Umma ta amsawa matar sallama tana daga cikin d’aki.

Matar ta shiga d’akin ta zauna bisa ‘yar guntuwar katifar dake yashe tsakar d’akin da bata da maraba da tabarma.

Suka gaisa da Umma tamik’awa Umma bak’ar ledar da ta shigo da ita tana fad’in.

“Gashi Umman Aynu dama abinci ne na kawo muku”.

“Amma kuwa mungode Allah ya saka da alkhairi kamar kinsan tun safe Aynu ba taci komai ba wallahi, yarinyar nabani tausayi sosai k’arama da ita amma tana fuskantar gararin rayuwa !?”.

“Haba Umman Aynu !, kada kice haka mana !, ko wanne bawa da irin jarabtarsa arayuwa, barema yau ina tafe da kyaky-kyawan albishir gareku ina kyauta ta zaton wasu matsololin naku zasu kau”.

“To Allah yasa Tasallah wanne albishir ne haka?”.

“Wato gidan Sarkin da Zainabu tawa take aiki zasu d’auki sababbin ma’aikata shine nake ganin mai zai hana Aynu taje ko Allah zai saka a dace”.

Umman tad’an jin jina kai kafin tace.

“Anya kuma?, nifa kin san bana son abin da zai saka inyi nesa da Aynu ko kad’an”.

“Ki yarje mata tayi aikin nan domin zaku samu alkhairi aciki, duk wannan abincin da ki kaga ina kawo muku daga gidan Zainabu ke zuwa dashi, bayan haka kuma ga kud’in da ake biya duk wata”.

“To zan duba ingani Allah yasa a dace”.

Cewar Umma kenan, Tasallah ta dubeta karo na biyu.

“Bawai zaki duba ba amincewa zakiyi domin nasan Babanta bashi da matsala akan hakan !, nazo miki da wannan maganar ne sabida ina da yak’inin zaku samu sauk’in rayuwar data tsananta a gare ku ne”.

Tayi shiru domin taji ko Umma za tace wani abu, jin da tayi ba tace komai ba yasa ta cigaba da magana.

“Sannan aiki a gidan ya dan ganta da b’an garen da kake aiki, kinga Zainabu Fulani Bingel takewa aiki albashinta dubu goma sha biyar ne, wad’anda ke aiki b’angaren Fulani Sokoto suna d’aukan Dubu goma, to kinga ko dubu goman ne ina laifi a wajen wanda baya dashi?”.

“Kinsan Jakadiyyar gidan Yayar Babar muce, shi ya sa ban ji komai ba nakai Zainabu aiki gidan sabida tana da kirki wallahi baza tab’a bari wata b’araka ta b’ullo ta gefen suba”.

“Hakane Tasallah !, bari Aynu tazo sai muyi maganar, mu ko b’angaren dubu goman ta samu Allah yasa masu albarka”.

“Amin, haka ya kamata kice ai”.

Nan suka cigaba da tattau nawa kafin Tasallah tayiwa Umma sallama tana fad’in.

“Idan ta amince zatayi ki turota da safe kamar shida da rabi domin anaso bakwai tayi musu acan”.

“Insha Allah zatazo kin san Aynu akwai himmar sammako ai”.

Suka sanya dariya ta fice daga gidan, tabar Umma nan zaune tana tunani.

Batafi mintuna talatin da tafiya ba Aynu tayi sallama da sauri ta shigo gidan ta ajiye jakarta tayi maza tad’auki buta ta shig e band’aki mintuna biyar tafito ta shiga cikin d’akin ta tadda Ummanta zaune tana lazimi, Aynu ta zauna gefanta tana fad’in.

“Sannu da gida Ummata”.

“Yauwa Aynu kin dawo lafiya ko?, fatan anyi karatu da yawa?”.

“Lafiya k’alau Ummata, nayi karatu sosai kuwa”.

“Masha Allah a dage sosai”.

“Insha Allahu Ummata”.

“Duba cikin kwanun da ke can rufe akwai abinci ki d’auka kici”.

“To Ummata”.

Tamik’e ta dauko ta zauna har tasa hannu zata fara ci sai kuma ta dubi Ummanta ta da tambayar.

“Umma kinci abincin kuwa?”.

“Ehh naci ‘yar gidan Umma, har Babanki shima yaci wannan nakine kici abinki”.

Aynu tasa hannu ta ci gaba da cin abincin ta.

“Ummata waye da aikin ladan nan haka?”.

“Kema ko ba’a fad’ab ba kinsan wace ai, Tasallah ce Babar Zainabu ta kawo mana d’azu”.

“Amma Umma babu abinda zamuce da Maman Zainab sai dai Allah yasaka mata kawai”.

“Amin dai, yauwa inkin gama inason magana da ke”.

“To Ummata nagama ai, bari in wanko hannuna”.

Leave a Comment