WATA KISHIYAR ๐ฅฐ๐น
(Alkhairi CE KO SHARRI)
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
Na Maryamah_Mrs AM
Page 1
Lagos Nigeria
Cikin sauri nake har hada takaddun ina qara duba agogon hannuna dukda nasan dakyar idan bazan makara, qarfe Tara jirginmu ze tashi zuwa Kano dan halartar wani conference meeting da aka turani daga office din mu. Gaba daya befi saura 45 mins Taran tayi ba inda na dan samu kwanciyar hankali babu nisan tazara tsakanin unguwar tamu zuwa Airport din. Buda qofar dakina da akayi da dan qarfi ya sani cewa ” not now please” azatona daya daga cikin yara nane sedai shirun da naji yasani waiwayawa, megidan ne da kansa wato ENGINEER BASHIR AHMAD da nake Kira da Baban Ali Yara kuma suna ce masa Abbi, Aliyu sunan babban Dana wanda Sunan Amininsa ne ya saka masa da ya rasu sati biyu kafin na haifi Aliyun.
Fuskar sa a hade duk da kasancewarsa dama ba mutum bane me fara’a amma dai ai yanayimun nidai. Kallona yake kamar yanda nima nake kallonsa fuskata dauke da gajeran murmushi nace “Baban Ali ka ganni har yanzu ko? Wallahi Amna ce tayi mun shirme tun jiya da dare nace ta zubamun papers din nan a jaka ashe batayi ba (Amna Qanwata ce kuma Autar mu danake ruqo bayan rasuwar Mahaifin mu da Mahaifiyarmu ta sake aure).
“Uhm” kawai yace mun yana nufar gaban mirror na, ban damuba na qarasa zuge jakata tareda ratayata na dauki wayata dake gefe kafin na nufi qofa da niyyar fita
“Idan kin dawo zuwa end of the month ku fara shirya zaku koma Gombe” muryarsa ta doki kunnena,
“To meya faru kuma? Bari dai in na dawo se muyi maganar a nutse” na sa kai na fice daga dakin. Already Emmanuel Driver office dinmu na waje yana jirana dan haka da sauri na fita ina amsa a dawo lafiyan da yara suka biyo ni suna yimun.
Bayan na nutsu a bayan motar zuciyata ta tafi tunanin me zamujeyi a Gombe kodai wani abune ya faru a bangaren sa? To bangarensa mana dan nidai ko da safiyar nan nayi waya da yan uwana kuma ba abinda akacemun ya faru to ko Matar tasa ta haihu ne? Aa in haihuwa tayi ai kaitsaye zece Amira ta haihu bawai kawai zakuje Gombe ba. Haka dai naita tunane tunane har zuwa Sanda Jirgin mu ya tashi.
A matuqar gajiye na shigo gida kusan qarfe 9 na dare, se yanzu nai dana sanin qin bari na kwana a Kanon dan jirgin 6 na biyo na dawo saboda ban gayawa yarana zan kwana ba nasan bazasuji dadi ba musamman da yake Gobe Saturday ne munsaba zama a gida. Bayan nayi sallar Magriba da Isha naci abincin da Aliyu ya kawo min, ina zaune tsakiyarsu kowa da hirar da yakeyi mun wani irin farin ciki yana cikamun zuciya. Tabbas yaya rahma ne, a duk sanda na kalli yara na ina jin tamkar bani da sauran wani damuwa a rayuwa se fatan Allah ya rayamun su.
Amna qanwata dake matsayin babbar Yata a yanzu nada shekaru 15 tana SS2 se Aliyu shekaru 13 ya shiga SS1 saboda Jumping da makarantarsu suka masa dan Yaro Masha Allah yana da qoqari tamkar Mahaifinsa. Jafar ke bi masa se Farida, Abdallah, se yan biyu na masu shekaru 5 Ahamd da Muhammad su Shidan nan sune rayuwata ban kuma hadasu da komai ba.
Har qarfe 11 muna zaune duk da irin gajiyar da nayi dan har wani ciwo kaina yakeyi, sauqin dana samu tun a kano na aika da report din komai Office dan haka Weekend din nan bacci zan shaqa. Sallamar Baban Ali ce ta katse ni na dago ina kallonsa da mamaki dan Duk hirar da muke a zatona yana Dakinsa dan shi dama be fiya zama ayi irin dogon hirar nan dashi ba, gaba daya muka masa sannu da zuwa ya Amsa yana nufar dakinsa. Se a sannan na tuna ko kirana beyi ba yaji ya na sauka, Se na miqe nima ganin kamar baya cikin yana yi me dadi dan in lafiya seya dan tsaya damu ko ze shige dakin ga kuma fita da yayi da daren nan, tashina yasa suma duk suka miqe mukayi exchanging Hugs kafin Mazan suka nufi dakinsu matan ma haka.
A tsaye na same shi yana cire rigarsa na qara sa taya shi ina cewa “Ashe baka nan, na tambayi yara sukace kamar Zoom meeting kukeyi kana daki”
“Uhm” ya kuma amsa mun. Nan da nan naji raina ya baci dan gaskiya ina da saurin Hasala amma fa ina da sauqin kai rainin hankali ne bana so, to rainin hankali mana ace wani inje kano in dawo a ranar ai ya tambayeni ya hanya koda yake dama duk satin nan tunda ya dawo Weekend naga yana wani fuzga ban kula shi ba nasan qiris yake jira ya sauke abinda ita yar Gwal din baze iya mata ba. A raina naja tsaki tareda cewa “Dan rainin hankali wato ga bolarka can Yarinya ta bato maka rai kazo ka juyemun to bazan tanka ba”. Ganin ya shiga Toilet yasa na fita, dakinan yaran na shiga can na tarar da Ahmad da Moh suna kwasar Dambe abun haushi wai Jafar na musu waqa Su Casu bame rabasu, haka suke kamar Kaji kullum fada kamar ko yaushe kuma akan Gado ne saboda Bunk ne dasu Aliyu da Jafar se nasu Muhammad, Ahmad da Abdallah Babban gado suke kwana su ukun to wai se ace A gadon Yah Jafar za’a kwanta shine a sama dan haka yau in wannan ya kwana gobe wannan amma rigima irin ta Ahmad se yace sedai dan uwan ya bashi kwanansa. fada na musu kafin kwantar dasu dukka a gadonsu muka karanta Azkar din bacci naja musu qofa tareda kashe fitila.
Amna da Farida tuni sunyi bacci suma Adduar na qarayi musu ma ja musu qofar na shiga dakina, jikina na qara gyarawa tareda daukar wayata na ja qofar na fita. Har Baban Ali ya kwanta ganin rigima yake nema yasakani kashe fitilar da ya bari a kunne nima na nemi wuri nesa dashi na aje muqamiqina wata gajiya na sake saukar mun.
“Kufa fara Shiryawa Next week zaku koma Gombe” ya sake fada, sena gyara kwanciyata ina cewa “Allah ya kaimu dan wallahi na gaji bacci nake so inyi kuma na biye masa surutu zamuyi tayi dan dai yasan abinda yake fada bame yiwuwa bane tunda na fara aiki ai bama zuwa Gombe se lokacin hutu shima ba kowanne ba se yayi corresponding hutun Yara da nawa ko kuma da wani babban dalili amma rana tsaka ana tsakiyar Term yace wani tafiya ko yar Gwal din ce ta haihu wlh bazan bar aikina na tafi ba duk sanda nai hutu naje mata Barka. Ina wannan mitar bacci yai awon gaba dani da ban farka ba se Qarfe 7 harda Rabi na safe.
Yau Baban Ali halin fulani ya motsa kenan ko ya tashe ni sallah dan gajiya ce ta danne ni banajin ko juyi nayi a baccin nan. A gurguje na dauro Alwala nai sallah bayanna idar da azkar dakyar na miqe dan bawai baccin ya sake ni bane na fito palour, Amna da Farida na zaune Se Ahmad dake bacci a kan Three sitter. A tare suka gaida ni na amsa ina tambayan ina Su Jafar Amna ce tace sun fita Jogging da Abbi
“Kunyi karatun Asuba ne” na tambayesu suka amsamin da eh
Mamaki ya qara kamani amma na dake na shiga kitchen Tea nake so nasha kafin na koma bacci. Kafin na fito sun koma dakin su har Ahmad sun dauke shi daga wurin dan haka na zauna kan Dining ina shan Tea ina tunanin meya ke damun Eng ne haka. Haka na qarasa na koma baccina wanda koda na sake farkawa 12 harta gota na rana.
A dakin nai wanka na shirya kafin na fito ina jin gajiyar ta sake ni. Palour kamar Gidan biki saboda hayaniya Farida da Jafar na musu akan wani film da suka kalla. Da gudu Ahmad da Moh suka nufoni har suna neman kadani na riqe hannayensu muka qarasa cikin palour.
“Ina Abbi” na tambayesu dan koda na farka ban ganshi a dakin ba kuma dai nasan Saturday Sunday yana gida seda babban Dalili yake fita kafin su bani amsa ya shigo da sallama ciki ciki, kallo daya yamun ya dauke kai tareda nufar kan Dining ya aje abunda ya shigo dashi, jin an fara kiran sallah yace su tashi suyi Alwala suka wuce masallaci da Mazan mu kuma muka tayar da tamu a Gida.
Abun mamaki bayan sun dawo kuma se gashi ya zauna a palour tareda yaransa suna hira dan nidai kitchen na shiga na fara qoqarin dora mana abincin rana dan na dare a waje zamu je muci in yaga dama kenan. Da wuri na gama dan Garnished spaghetti na mana se na dumama Grill Fish din daya shigo dashi ko a ina ya samo da safen oho. Farida da Amna na kira suka jera komai akan Dining kafin muka zauna gaba daya banda Abbi dake amsa waya sena dakata har ya gama sannan na masa maganar Abincin.
“Kifin kawai zaki kawomun da juice” ya fada. Ban kawo komai ba dan nasan spaghetti bata wani dame shi ba amma dai yana ci musamman irin wadda nayin, na hada abinda ya buqata na kai masa sannan na koma muka ci gaba da cin abincinmu. Koda muka gama wurinsa Twins suka koma da Abdallah Jafar da Aliyu suka kwashe kwanuka zuwa kitchen tareda wanke wa Amna da Farida kuma daki suka shiga Farida zata yiwa Amna tsifa. Nima palour na koma muka hadu muna yar hira sedai abinda na fahimta Baban Ali yaransa kadai yake amsawa dana saka baki se naji yayi shiru tsam na miqe Ahmad ya tashi shima ze bini dan haka yake indai muna gida da na dauke qafa ze aje tasa nace masa “koma ka zauna aiki zanyi” ban ma shiga dakinsa ba na shige nawa.
Kwanciya nayi kan gadona ina replying whatsapp messages daga nan muka shiga hira da yayata Alawiyya da muke Uba daya, tamu tazo daya nan na shiga bata labarin abinda Baban Ali ya tsiro dashi kuma. Dariya tayi tana cewa “kedai da Engineer Miskili kafi mahaukaci ban haushi” nan muka ci gaba da firar mu ban san lokaci ya tafi ba seda naji ana kiran La’asar.
A dakin nayi sallata ina idarwa na shiga wanka, daidai na fito naji Knocking nasan yaran ne basa shigomun daki sena basu izini koda kuwa Ahmad da Muhammmad da suke qanana. Bayan na amsa Abdallah ya shigo, sak kamanninsa da yanayin Miskilancinsa irin na Bashir ne sedai duk cikin yarana ya fisu haquri wannan kuma halin takwaransa wato mahaifina ya gado. Cikin sanyinsa Yace “Mami Wai Abbi yace kiyi masa text na abinda zamu taho miki dashi”.
Se naji wani dus kamar yaya na masa text? Ba tare zamu tafi ba? Har na bude baki da niyyar tambayarsa se kuma na fasa nace masa ” Kacewa Abbi ya leqo ina son magana dashi”. Da toh ya amsamin kafin ya fita ya barni da mamakin wannan sabon rainin hankalin.
Abbi
Lokacin da yaron ya gaya masa saqon har sun shiga mota ya ma kunnata, ganin idon su ya sahe cewa yana zuwa ya fito yana qara daure fuskar sa. Tana shafa wa santala santalan cinyoyinta mai ya sameta, yaso ya shagala da binta da kallo dan a duniya ASMA’U takai duk inda mace ake so takai, Asma’u mace ce guda harda Rabi wallahi ta ko ina ta hadu bakuma ze taba manta halaccinta a rayuwarsa ba shikansa ya kasa gane dalilin da yasa yake mata wasu abubuwan. Waiwayowan da tayi tana qoqarin sakin towel din jikinta dan sam bata ji motsinsa ba yau saurin juya fuskarsa dan a wannan bangaren baya taba iya tsallake tarkonta. Jikinta tamkar Magnet yake ga idonsa, a kullum gani yake kamar qara mata kyau da sura akeyi Ma’u bata tsufa.
“Au Abbi ka shigo ashe, Ban gane me Babana yake fada ba yau kuma danwaken zagaye zakumin kenan” na fada ina cigaba da zura rigata dan nayi sauri na shirya nasan Bashir baya son jira sam a zatona ma dalilin daya sa zasu fita su barni kenan.
“Nop banyi niyyar fita dake bane, kiyimun text din abinda zaki ci mu taho miki dashi in kuma beyi miki ba shikenan” kawai yasa kai ya fita.
Se na raka bayan sa da kallo kawai kamar wata doluwa, ” tofa Baban Ali kodai gamo yai da Aljanu ne” na tambayi kaina ina qara cika da tsabar mamaki.
Share
Share
Share
https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
WATA KISHIYAR ๐ฅฐ๐น
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
Na Maryamah_Mrs AM
Page 2
WATA KISHIYA(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
Ni kadai tsuru kamar mayya a gida har qarfe 10pm ga gyangyadi inayi amma na kasa shiga daki na kwanta saboda tsoro gashi har sannan basu dawo ba. Tsayuwar motarsa da naji ta sani miqewa daidai lokacin da Ahmad ya kwaso da gudu yana kwallamun kira “Mami Mami”
“Na’am Ahmad meya faru” na fada ina tare shi, labarin inda sukaje ya fara bani, gurin wasan da ya kaisu, Favorite restaurant dina sukaje suka ci abinci daga nan suka tsaya Cinema sukayi kallo abinda ya saka su yin dare kenan.
Saboda gajiya kowa dakinsu suka nufa, dakaina nayiwa Twins wanka na shirya su kafin 11pm gida yayi tsit duk sunyi bacci sannan na shiga dakina raina yana suya,
Tsabar bacin rai ko takan take away din da sukamun ban bi ba nima wankan na shiga ina sake danne zuciyata na shirya na nufi dakin Baban Ali.
A kan gado na sameshi yayi daidai yana amsa waya fuskarsa dauke da wani shegen murmushin da bazan iya tuna rabonda yayi mun shi ba ko ba’a fada ba nasan da Amira yake waya dan Baban Ali bashida kwashe kwashen yammata, Ada ni kadai ce a rayuwarsa kafin ya kwaso min Alaqaqai.
Wayar dana tarar yana yi ita ta qara bata mun rai saboda wannan ai wulaqanci ne ko? Nasan matar sa ce amma ya kamata nima ya mutuntani idan zeyi wayarsa se ya nemi kebantaccen wuri bawai cikin dakina akan Gado na ba, wannan sabuwar ta’asar da ya samu ta fara kaini bango dan haka ban san sanda na saki wani wawan tsaki ba ina janye ido na daga kansa bayan mun hada ido.
“Ke dawa kike tsaki?” Ya tambayeni still wayar na kunnensa.
“Ni da waye a dakin” na fada raina na qara quna.
“Anty ce ko” na jiyo muryar Amira na tambayar sa daidai sanda na duqa kusa dashi dan na dauke Safar daya ajiye akan gadon sena daga sauti yanda nasan zata jiyo nace “Nice din yar iya ko kina da magana ne”
“A ko yaushe ina gaya miki ki ringa jan girmanki ko? Amma shikenan” ya fada yana miqewa daga kan gadon ya nufi qofa. Wani baqin ciki ya tokare mun wuya, kawai na haye gadon na kwanta tareda fashe wa da kuka.
Duk yanda nake daurewa se Bashir ya qure ni tunda ya auri yarinyar nan ban sakeyin sati ba tare da nayi kukan baqin ciki ba shikenan ni a haka zan qare? Bansan sandaya dawo dakin ba na dai farka cikin dare naji mutum ya kwaqumeni aiko na ingizashi da qarfi har seda ya farka na tashi daga gadon na shige toilet. Fitsari nayi na dauro Alwala, hijabina na zura na fara jero Salloli tare da dogayen Addua.
Kamar kullum a duk sanda muka samu sabani na fara sallar dare nan haka ze zabga tagumi yana kallona in ya gaji shima ya to Alwalar ya tada Sallah (bawai dan banayi ba Aa nafi tsawaita Idan mun yi fada dan karna kwanta kusa dashi dan duk bala’i bama raba gado ๐๐) nasan me yake tunani qila qarar sa nake kaiwa gurin Allah ko ๐๐ wallahi ko daya duk abinda Bashir yake mun ban taba yi masa Allah ya isa ba sedai ma in roqi Allah daya yafe masa ya kuma bashi ikon Yin Adalci a tsakanin mu ya ci gaba da bashi yanda zeyi ya kula damu. Ko ba komai nasan Bashir yana sona nima kuma ina sonsa to ban rabu dashi a lokacin Matsi ba se yanzu da dadi ya samu se in tafi in barwa yar taka haye?? ina ba wannan magana.
Ban sallame ba har seda aka kira sallar Asuba, ina kallonsa ya fita masallaci kafin nima na tashi nayi Raka’atanul fajir sannan na bada Farillah. Rashin samun bacci cikin dare yasa ina idarwa ko Azkar ban samu yi ba na koma bacci, sanda na farka goma harta gota dan haka anan dakin nayi wanka na shirya kafin na fito palour.
Ko ina qalqal sun gyara dan ko kadan banyi wasa wurin koyawa yarana aikin gida ba komai nidasu mukeyi bani da me aiki tunda har kuma yanzu dana ke fita aiki da safe kafin mu fita mukeyin komai tunda kuma ba wuni muke a gidanba baya yin datti. Babu kowa a palor se Baban Ali yana aiki a system dinsa ya dago yai mun kallo daya tareda mai da kai ya cigaba se na qarasa kusa dashi ciki ciki nace masa ina kwana dan har yanzu haushin sa nake ji, se ya amsa ba tareda ya kalleni ba.
A dakin Boys najiyo hayaniya da alama PS sukeyi tunda suna da Tv a dakin nan suke yin Game dukda lokaci da yawa yana dauketa saboda karsu shagala da wasa a qi karatu amma Weekend dama aikin kenan wani sa’in hardashi zasu hada anan palour suyi.
Kitchen na nufa dan naga sun kwashe kayan kan dining, a roba na tarar da dankali ciki ruwa an yanka su, nasan Amnace ta ajiyemun tunda tasan nafison dankali da an kwashe daga wuta nan da nan na maida man da sukayi suya na zuba kafin na debo kwai guda uku na fasa tareda zuba abubuwan da nake da buqata a ciki, ina kwashe dankalin na maida wani pan din na soya kwai, scramble nayi dan ban fiya son me fefe ba na juye akan plate din chips na zuba Ketchup a gefe na fito. Ta gabansa na wuya ina juya jiki tareda baza masa qanshin turarukan dana fesa aikuwa naji yanda yaja numfashi da ajiyar zuciya ina kuma jin idanunsa akaina har na zauna a dining amma kafin na juyo ya dauke idonsa, girgiza kai nayi ina sake cika da mamakin Bashir a raina haka naja kayan tea na hada ina ci ina dan kallon drama da akeyi a Tv.
Har na gama ci babu wanda ya leqo a yaran Gogan ma anata latsa laptop kamar besan Anyi digona a palour ba sena taso na dawo cikin palour na nemi 1 sitter dake facing nashi na karkace ina latsa wayata nima. Whatsapp na shiga group dinmu na Secondary na bude aikuwa na tarar da chats bila adadin, ban samu damar bi ba saboda wasu ne suke qara shigowa se kawai na fara bi daga nan. Ban karanta message din mutum hudu ba na fuskanci dalilin ubannin messages din dana gani ashe Labor zaayiwa kishiya (Labor prefect dinmu da muna school kuma abin dadin qanwar daya daga cikin yan ajin namu qawarta ta hannun dama zaa auro mata, tasan mijin zeyi aure amma bata san yarinyar ba se yau da taje karban lefen Qanwar Qawarta taga dangin Mijinta ne yan kawo lefen ๐คฃ๐คฃ๐๐๐คฃ๐คฃ๐)
Wata muguwar dariya na sheqe da ita har ina kwarewa da ta saka Baban Ali dagowa ya zubamun ido, yasan Ma’u sarai tabbas mugunta ta gano shine dalilin wannan Dariyar. Be gama tunanin kuwa ba na fara voice note still ina dariyata nace “Alhamdulillahi layi ya fara ja ashe? To Allah ya qarawa mazajenmu budi suyi ta auran mana qannemu” na tura ina sake sheqewa da wata dariyar ganin yanda Safiya Sani Labor keta kumfar baki da daukan Alwashi kala da kala ita ma yayar Amarya Zulaiha Balarabe tana aiko da nata.
Masifar da Safiya takeyi seta tunamun da lokacin da za’ayimun tawa kishiyar mun hadu gurin gate together dabanyi niyyar zuwa ba saboda a lokacin bana cikin nutsuwata. A kallo daya zaa gane damuwar da nake ciki duk na hargitse, na tuna yanda ta sakani a loko tana mun wa’azi.
“Wallahi Asma’u kin bani mamaki kin kuma bata wayonki kamar wadda bata san Allah ba, duk ina karatun islamiyyar da kikayi? Kin karanta Alqur’ani tsaf kin haddace da fassara amma kina nema ki kasa aiki dashi. Karin auran nan kinsan umarnine na Ubangiji in har Namiji nada hali da biyu akace ya fara sedai ko in baze iya adalci ba ko kina so kice Bashir ba Adali bane?? Sannan ma ke ai kiji dadi koba komai kinsan wadda za’a auro miki ciki da bai baki da fargabar azo a tarwatsa miki gida tunda Ai Amirah kusan tarbiyyarki ce ma. Haka matar nan ta dage tanamun wa’azi har na sauketa kan layin gidanta mukayi sallama na wuce a raina ina Addu’ar insha Allahu itama se an mata taji in da dadi (Ni fa alokacin duk wanda ya bani haquri se na masa Addu’a Allah yasa shima a masa kuma Alhamdulillah gashi tana karbuwa kuwa ๐คฃ๐คฃ).
Wani mulmulen ashar ta dannomun bayan taji voice dina nan kuwa na samu nayi na ci gaba da kunnata kafin kace me fada yabar kan Yayar Amarya ya dawo kaina harta na jcewa qila dani aka hada baki nace oho dai aikin gama ya gama biki saura 2 weeks , wannan nishadi ya mantar dani wanzuwar Baban Ali a gurin har wurin 12 sannan yara suka fito muka ci gaba da sabgogin mu. Gaba daya dai haka muka cinye weekend din ba dadi tsakanin mu Monday muka koma aiki. Office dinsa yafi kusa da makarantar yara dan haka kullum shi yake fita dasu ni kuma tunda ina rigashi tashi sena biya na debo su amma yau bayan mun fito gaba daya har Ahmad ya kama handle ze bude gaban mota ya dakatar dashu da cewa “kuje Maminku ce zata kaiku”
Sororo nayi ina kallonsa araina nace meye haka toh sukuwa yara suka dauki Murna dan dama mitarsu kullum yawanci Friends dinsu Momys dinsu ke kawo su school dalilin ma daya sa na dawo ina dakkosu ke nan dan da duk shiyake hadawa. Tafiya ta qaru haka nayita sauri gudun makara na samu na ajiyesu amma dukda haka ni seda nayi latti dan school din tana gaba da office dina innaje sena dawo baya while shi kuma yana gaba da school din dole seya wuceta zeje nasa office din.
Wuni nayi ina mamaki wato duk sati da sabon salon da ze bullo dashi? Allah dai ya kyauta.
A daddafe muka cinye satin kullum kuwa sena makara dan kafin na kaisu na juyo traffic ya fara haduwa, abun takaicin wani sa’in zamu hadu a hanya har Horn ze mun in na tsaya ajiyesu ya wuce ni abin na qona mun rai ni kuma nayi alqawarin bazan masa magana ko na tambayi dalilin dayasa yake hakan ba nasan dai duk sare sarin neman fitina ne in tanka su samu nayi dani a dangi to an dena (Dangin fulani dangin magana ๐).
Muna haka Weekend ya zagayo wannan karon ma yaransa ya diba suka fita yawonsu, abunda ya ragemun haushi ranar Saturday wuni nayi rama baccin gajiyar sati daban samu nayi ba danayi sannan Sunday fita mukayi nima da Matan layin mu dama muna haka once in a month zamu hada picnic muje beach a dan warware takaicin Namiji ๐๐ mu shaqi iskar duniya to wannan Lahadin ma can muka wuni dan a gida na fita na barsu ma muka dawo kusan lokaci daya.
Yanda Bashir ya tsume haka nima na tsume na fita a sabgarsa sam tunda haka yake da buqata ina jinsa ze raba dare yana waya da Amaryarsa har inji yana ce mata tayi haquri ta kusa dawowa kusada shi ai, wani lokacin naji haushi wani sa’in nayi mamaki kai Namiji dai a barshi kawai.
A da idan aka cemun Bashir ze sake kallon wata mace da sunan soyayya zance qarya ne amma daga sanda ya koyamun hankali ko ji nayi mace na shan Alwashi akan Namiji zan dakatar da ita dan tabbas Akan Bashir na sake yarda da akace Namiji Badan goyo bane (Inji Asma’u fa ๐).
Ranar Laraba na tashi da ciwon kai da ya saukar mun da zazzabi, ina nade akan gado har Bashir ya fita masallaci, a zaune na iyayin sallah ina idarwa na koma kan gado na nade har ya dawo ya fara shirye shiryen fita office. Dukda ya ganni akwance which is unusual hakan be saka ya tambaye ni dalili ba abinda yai matuqar qona mun rai ace har mun kai matsayin haka kamar wasu maqiya to wai duk me yayi zafi ne?
Seda ya gama shirinsa tsaf sannan ya kalleni
“Yau bazaki je aiki ba kenan? Se ki tashi ki miqasu karsu makara” yasa kai ya fice daga dakin. Wasu hawayen baqin ciki ne suka fara tsere a fuskata, idan Bashir ya gaji da zama dani gara ya fito ya fada mun yafi wannan Kisan mummuqen da yakeyimun ai, shigowar Jafar ta sakani share hawayena, ya matso kusa da ni yana cewa
“Mami mun shirya fa ko Abbi ne ze kaimu yau?” Cikin muryata da kuka ya fara dishewa nace mace
“Kuje maza ku bishi Jafar bani da lafiya”
Nan da nan fuskar yaron ta chanza zuwa tausayi yace “sorry Mami kinsha magani toh?
Bari na hado miki breakfast to Abbi baze kaiki Asibiti ba?”
Dole na qirqiro murmushin dole nace “it is not that serious Jafar Kaina ne yake ciwo nasan stress ne dana qara hutawa ze dena, maza kuje ku tafi and don’t tell your brothers ku wuce Makaranta kawai Allah yai muku Albarka ya bada Ilimi me amfani” na qarasa ina dafa kansa se ya amsa da “Amin Mami Allah ya baki lafiya, Bye love you” ya mun peck a goshi ya fita da sauri dan su kansu kwana biyu ba wani gane kan Abbin suke ba.
Yana fita na miqe dakyar na tsaya bakin window ina hangensu,
Shiya gaya musu Abbi ne ze kaisu dan haka suka fita da sauri dan har ya gama Shan Tea ya fita yama kunna mota. Da ido ya bisu ganin sun jere masa a gaba, cike da baqin miskilancinsa yace ” yadai kunzo kun mun layi a gaba?”
“Abbi Mami ce tace kai zaka kaimu bata da lafiya” cewar Jafar.
Seda gabansa ya fadi jin bata da lafiya dan ciwon Asma’u ba abune me sauqi ba, irin mutanen nan ce da suke dadewa basuyi ciwo ba amma in ya kwanatar dasu kamar bazasuyi ba. Harya niyyata daya koma yaji me yake damunta se wata zuciyar tace masa qila dan taja attention dinsa ne ya sakata kwanciya tace musu bata da lafiya dan Asma’u can pretend yasanta sarai dan haka ya qara gintse fuska tareda bude qofar sa ya shiga yana cewa “kuje ku ce mata tazo ta kaiku you are getting late”
“Abbi kana jifa yace bata da lafiya base ka kaimu ba tunda hanyar zaka bi” Farida ta fada dan ita yar gaba gaba ce daman, be amsata ba yai wa motarsa key ya qara gaba se suka rakashi da idanu gaba daya kamar yanda nima Mamakin sa ya nemi kashe ni a tsaye BASHIR dai shine haka? BASHIR dana sani me jarabar son yaya da tattalinsu kamar kwai, to kodai shiga tsakanin mu akayi da BASHIR ne?????
https://chat.whatsapp.com/IcgqoNAQ9V612x1JRXBMVS
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
WATA KISHIYAR ๐ฅฐ๐น
(Alkhairi CE KO SHARRI)
๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐๐
Na Maryamah_Mrs AM
Page 3
A salube suka shigo gidan gaba daya suka zauna A palour banda Abdallah daya zarto dakin da nake, yana ganina ya wullar da school bag dinsa ya taho da gudu jikina se ya sa kuka, nasan kukan me yake Abdallah akwai son karatu indai ba ciwon gaske ba baya Missing school.
Bubbuga bayansa nake da sigar rarrashi ina qoqarin hana nawa hawayen fitowa.
โMami kinga Abbi ya tafi ya barmu kuma Yah Jafar ya gaya masa bakida lafiya amma ya tafiโ ya fada in between tears, se na jashi zuwa gefen gadon dan jin kaina yana dada sarawa ga zazzabin na sake ruruwa.
โKa dena kuka, sauri yakeyi yana da meeting ne shiyasaโ
โMami bafa yanzu bane se 10 naji yana waya da Uncle Samuel aiโ
โAbdallah bana hana ka ba, idan babba ya fada maka magana ka dena jayayyaโ
โAmma Mami…โ
โShiii ya isa kirawo mun Amna se na kira muku Uber ya kaikuโ na katse shi dan bana son aja maganar, fita yayi ba jimawa Amna ta shigo itama fuskarta da damuwa.
โKi dauko wayata kiyi muku order Uber bazan iya driving ba bana jin dadiโ na fada mata ina kaiwa Kwance jin jiri na dibana.
โMami ko mun tafi ma kafin muje mun makara bazaa bude mana get ba sedai kiyi waya ki fada bazamu zo baโ.
Agogo na kalla tabbas kafin a samu uber su tafi lokaci ya qure dan haka na miqa mata hannu ta bani wayar, Number da suka tanada dan wani uzuri nayi dialing dakyar ina ringing kadan suka amsa, cikin muryata dake nuna halin da nake ciki nayiwa receptionist din bayanin Bazasau samu zuwa ba bani da lafiya Abbinsu kuma yayi tafiya, fatan samun sauqi tayimun tareda cewa idan gobe ma babu me kawo ayi musu Registration na school bus tunda tana zuwa har nan estate din namu, shaf na manta da zancen ma school bus se yanzu dan haka ba bata lokaci nace tayi kawai.
Har na gama Amna na tsaye bayan na aje wayar tace โMami in kawo miki ko tea kisha se kisha Paracetamol kafin Abbi ya dawo kuje Asibiti?โ
Kai na daga mata ta fita ba dadewa se gata da try ta doro tea se toast bread da kuma paracetamol da ruwan roba. Da daddaya suka shigo suka mun sannu har sannan Amna na tsaye seda na shanye ta ballomun maganin nasha nakwanta sannan ta fita.
Koda na farka bayan Azahar na danji dadin jikina dan zazzabin ya sauka sefa ciwon kan da sauran jiri da nake ji, wanka na lallaba nayi na dauro Alwala a raina ina qara mamakin Baban Ali da haryanzu ko waya beyo yaji sun tafi ko basu tafi ba. Agunda nai sallah na zauna naji anyi knocking, izinin shigowa na bada Aliyu ya shigo da Sallama hannunsa dauke da Babban try da suka dora abinci.
โMami kin tashi tun dazu muke leqowa kina bacciโ
โNa tashi Yaya (haka nake kiransa saboda qannensa su saba) ina su Ahmad naji shiru?โ Na tambaye shi
โBacci suka kwanta bayan mun dawo daga masallaci, Maman Ruth ta shigo muka ce mata kina bacci(Maman Ruth maqociyarmu ce)โ
โLallai an samu yanda ake so bacci yanzu, me kuka dafa neโ na fada ina jawo try din gabana.
โIrish porridge Yah Amna ta miki mu kuma Rice and Beans muka ci da fishโ.
Kwanon na bude faten se tururi yake da qamshi kai kace Wata babbar chef ce tayi girkin. A plate na zuba wanda zanci muna dan hira da Aliyu har na gama ya kwashe kayan ya fita se nima na fito palour dukda dauriya kawai nakeyi amma kaina yana ciwo sosai, ban idasa zama akan kujera ba wani irin jiri ya kwashe ni daga nan ban sake gane komai ba nidai na farka kawai Na ganni kwance a gadon dana tabbata na Asibiti.
BASHIR
Tunda ya bar gidan hankalinsa ya kasa kwanciya, har ya kai get din estate din ya juyo da niyar daukansu se kuma Shedaniyar zuciyar da take ingizashi ta sake yi masa fanfo. Har ya kai office yana tunanin sun taho ko basu taho ba lokaci lokaci yana duba Mirrow koda ze hango su a bayansa amma shiru harya wuce makarantar tasu. Yana shiga Office be zauna ba ya kira layin makarantar ya tambaya ko sunzo nan matar ta sanar dashi Madam ta kira ta bada excuse ai haka ya aje wayar jiki a sanyaye jin dagaske dai ashe bata da lafiyar ba lambo tayi ba kaman yanda yayi tunani, duk haka ya shiga aiki sukuku babu kuzari har sanda ya shiga Meeting kafin su shigama yana Kallon kiran Amira amma yaqi dagawa dan se yaji yana jin haushin ta ita ce ummul Abaโisin ta komai da yake faruwa ai.
Tun yana sallar Azahar da be samu yi ba se qarfe uku bayan sun fito daga dogon meeting din da suka share awoyi sunayi wayar sa take ta qara dan ya manta be sakata a silent ba, yana sallamewa wani kiran ya sake shigo wa ya zarota a fusace dan ya ayyana Amira ce kadai zata iya masa irin wannan kiran mahaukatan sedai ya cika da mamaki ganin Number Asmaโu da yayi saving da MAโUNA akan screen. Be kai ga dagawa ba ta yanke kafin ya yi wani abu aka sake kira se yai saurin dannawa dan tabbas yasan ba lafiya ba.
Muryar Aliyu ce cikin kuka yake ce masa โAbbi kazo Mami ta yanke jiki ta fadi tun dazu bata motsiโ ai se yaji tamkar a saka guduma an bugi kwakwalwarsa Asmaโu ta fadi meya sameta? Innalillahi.
Ikon Allah ne ya kawo shi gidan kawai yana shiga ya tarar dasu a zagaye da ita suna kuka kamar wadanda aka cewa ta mutu se ya matsa da sauri ya dagota yana jijjigata โAsmaโu Asmaโu ya shiga kiran sunanta. Danshin da yaji a hannunsa daya tallafo qasan ta ya saka shi duba wurin Jini ya gani wanda duk basu lura ba se yanzu ai kuwa yaran suka sake rudewa da Kuka kamar me shikansa dauriya yayi ya dagata tareda cewa Amna da Aliyu su fito suje Asibitin sauran Yaran kuma yace su Shiga gidan Maman Ruth kafin su dawo dan Anty(Amaryar Ogan sa ta take flat din dake kallon nasu) ta tafi Zamfara garinsu bikin qanwarta.
Bashi da Nutsuwar da ze ja mota dan haka yau Amna da kullum yaga Asmaโu ta bata driving se yayi balaโi to gashi yau ta masa rana, ita kanta jikinta rawa yake cikin ikon Allah dai suka qarasa asibitin dan basu da nisa sosai.
Emergency a ka karbe ta, bayan kusan Hour daya Dr Bolaji ya fito daga dakin da suka shiga da Asmaโun. Alama yayi wa Bashir daya biyo shi office
Se ya kalli Amna da Aliyu da fuskokinsu suka kode saboda kukan da suka sha,
โKu jirani a nan ina zuwaโ ya fada tareda bin bayan Dr Bolaji.
Bayan ya nutsu a office din Dr Bolaji ya kalle shi tareda turo masa takardar daya gama rubutu.
โStrees da damuwa suka hadar mata har ya jawo jininta ya hau sosai shine kuma yai sanadiyyar fitar cikin jikinta, ga wannan kaje ka kai Pharmacy zasu baka bill na kayan da akayi amfani dasu se ka karbo wadannan magungunan kuma, Allah ya taqaita abun amma ku kiyaye faduwa irin wannan ko a gaba ze iya jawo mata Paralyze bama dai fatan hakanโ Dr Bolaji ya fada cikin harsheb turanci yana maida kai ga takaddun dake gabansa, kamar kazar data sha ruwan zafi haka Bashir ya miqe ya nufi Pharmacy din dan karbo magunguna.
Sanda ya dawo ya tarar da Nurse ta fito daga dakin da Bedsheet a hannunta daya baci da jini da kuma kayan jikin Asmaโu da suka kawota dasu. Tambayan ta yanda zaayi da maganin yayi tace ya shiga dasu ya ajiye zata dawo yanzu seya tura qofar dakin a hankali ya shiga.
A ciki ya tarar da Aliyu da Amna kowannensu na share hawaye nan da nan yaji shima hawaye da be zata ba sun sakko masa, shikenan ya rasa Babyn da be masan dashi ba. Allah ya dorawa Bashir jarabar son Yara a rayuwarsa, ya kance shi beqi ya haifi yara Ashirin bama in ya fadi haka Asmaโu se tayi dariya tace
โHaba se kace Akuya in dai ba kuma mata hudu zakayi baโ. A lokacin ya kan ce mata ke zaki zama Akuyar kuwa kiyi ta zubo su dan kinsan nidai babu gurbin wata mace bayan ke a cikin rayuwata. ko bayan data haifi Yan biyu Asmaโun taso tayi planing acewarta yaran sun isa haka amma ya fitittike yace idan tayi koda be sani ba be yafe ba dan shi yana son yaga ya tara zuriโa masu yawa kuma Alhamdulillah yanzu Allah ya hore masa yana da yanda zeyi ya kula dasu, yasan bazatayi ba shi yasa dadewar da tayi bayan Yan biyu be dame shi ba yasan daga Allah ne bayan haka dama ance in shekaru suka fara ja haihuwar na ja baya ita ma kuma Asmaโun na kusan shekaru 33 ne yanzu.
A hankali ya ajiye ledar kan drawer dan Nurse tace karsuyi motsi me girma daze farkar da ita ya qarasa gefen gadon yana kallonta tayi wani fresh tana bacci kaman bame ciwo ba se ya rankwafa kanta tareda kissing goshinta, under his breath yace โget well soon my Maโu, Iโm sorry for hurting youโ.
Zaman kurame sukayi shida yaran kowa na tunanin abinda ya dame shi basu Ankara ba se jin kiran sallar Magriba sukayi se a sannan ya tuna ai ko Laโasar beyi ba. Shida Aliyu suka tafi masallaci har suka dawo kuma bata farka ba dan haka cikin damuwa ya koma gurin likita yana gaya masa.
โBabu damuwa mun mata Alluran bacci ne dan ta samu ta huta sosai jinin ya sauka zata farka amma se zuwa cikin dare, kaje kawai kayi settling bills babu buqatan me jinya Nurses din mu zasu kula da itaโ.
Jiki a sabule ya koma dakin, Gurin da Su Aliyu suke ya kalla yace su tashi su tafi gida
โAbbi ni zan kwana a nanโ cewar Amna
โAa baa barin me jinya mu tafi da safe kafin ku tafi school se mu biyo ku dubataโ. Dakyar suka tafi har shi kansa ji yake kaman ya sake zama sedai tuna sun bar sauran yaran yasa dole suka tafi bayan ya biya kudin duk abinda ya kamata ace ya biya din.
ASMAโU
Basufi awa uku da tafiya ba na bude ido lokacin qarfe tara na dare harta dan gota, jinina yana da qarfi sosai ba kasafai Allurar bacci take daukata na dade ba. Sakayau na tashi kaman an zare mun qaya dukda bansan ainihin abinda ya same ni ba amma babu ciwon kan babu jiri se kawai kasala da nake ji da kuma bakina da sam ba dadi. Ina qoqarin miqewa Nurse ta shigo tana ganina ido biyu ta fada da faraโa tana cewa โSannu patient har kin farka lallai kina da qarfin jini muda muke tunanin se kin kai gobe maโ
โMurmushin na mayar mata cikin muryar marasa lafiya nace โgashi har na tashi kam amma naji dadin jikin ma sosai aiโ
โKarki tashi Bari na sake duba Bp na ganiโ ta fada ganin ina qoqarin miqewa daga gadon, zama na koma nayi ita kuma ta dauko Abun auna BP, seda ta gama ta kalleni still tana murmushin tace โkinga kuwa yayi normal bari na hada miki ruwa to ki wanke jikinki dukda naga bakiyi staining bama se kici abinciโ
Kallon rashin fahimta na bita dashi fahimtar haka ya sakata Dafani tace โIโm sorry kin samu miscarriage saboda faduwan da kikayiโ
โMiscarriage kuma? Cikine dani daman?โ
โEh almost 3 months ma baki sani ba?โ Ta jefin tata tambayan, se lokacin na gane a fili nayi magana. Sena qaqalo murmushin dole to ban ma san me zance ba dadi zanji ko rashin dadi ma oho nan ta barni ta shiga toilet din, mintina kadan ta fito bayan ta tara mun ruwan. Ita ta rakani har toilet din kafin ta baroni na fara wankan.
Sosai naji dadin ruwan bayan na gama nayi brush da sabon tooth brush din data ajiye mun na saka pant da pad da duk a nan na gansu sannan na daura sabon towel babba na rufo kaina da qarami na fito ina jina wata sakayau a raina ina yaba tsarin Asibitin komai nasu tsaf kamar A Turai.
Turus na tsaya kofar toilet din ganin Mutum a zaune bakin gadon dana tashi wanda da alama an kuma chanza bedsheet din kai, haka kawai na tsinci kaina da daure fuska abinda yai ma yara da safe yana dawomun se kawai na juya da niyyar komawa cikin toilet din yai zuruf ya miqe tare da biyo ni kafin na samu damar rufe qofar ya turo ta ya shigo ciki bani da zabi kawai na durqushe a qasa na fashe masa da kukan da ban san nima na menene ba.

Leave a Comment