Books Reviews & FAQs

Wasa Farin Girki Hausa Novel Complete

(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)*

💎°•° *WASA FARIN GIRKI* °•°💎 {cigaban gidan gandu}

 

💎1~2💎

 

 

💎*sameemah point of view*💎

Inajin duk abinda baba umaru yake fada akan wai na maida komai ba komai ba, kuma nayi tawakkali,saidai da yasan abinda nakeji a cikin raina a lokaci da bayyi gangancin yin wannan furucinba,dan ji nake kaman na sha’keshi yah daina motsi dan haushi.
Duk da gargadin danayi masa amma bai jiba sai ma cigaba da yayi da cewar,
“Nasan Har yanzu kina jin haushi da kuma shiga yanayin damuwa saidai ina so nasanar dake cewa,hakan yah kasance a zanen kaddararki yahke,sannan ni nacika alkawarine na matata hajara dana dauka,wanda tah bani kafin tah koma ga gidan gaskiya”
Saurin juyowa nayi na kalleshi jin yace wai wasiyyar ummah tah ce da ta bashi kafin ta rasu,kenan dama abinda ta fadawa baba umaru kenan ranar da ta ce mu fita tana shirin mutuwa,wannan tambayar ni kadai nayiwa kaina amma kuma banida amsarta.
Tashi nayi domin fita a dakinnasa dan a halin yanzu bana bukatar abinda zai hadani da wani ma tukunna,dan na gano duk tsawon shekarun danayi a rayuwata a cikin duhu kai da jahilcin rashin sanin mai yake faruwa nayi ta dukka.
Dakinmu na nufah koba komai naji dadin rashin ganin mutane a gidan domim kowa yah watse bayan kwana uku da biki.
Wanka nafarayi badan nasoba dai dan yanda naji jikina yana hamami,rabona da wanka tun kwana uku da suka wuce.
Kayan inna rabi nagani a gefen nawa kayan da alamun anan take zaune kenan tunda aka daura auren,kallon dakin nakeyi wani kululun bakin ciki yana cina a zuciyah,nayi niyyar gyarashi na zauna ni kadai ashe nima so suke su fitar dani a cikin gidan.
Duk da cewa yanzu ba wannan ne a gabana ba,burina shine na san mai yake faruwa tsakanina da sameer dan yamzu nasan shidin ba jinina bane tunda aka daura min aure dashi.
Kuma na dau alwashin nima bazanyi musu yanda suke so ba matukar basu fadamin mai yake faruwa ba.
Dukkan gidaje guda ukun na amare babu wanda yayi wani doki da zuwan amaryar tasa,saboda duk abinda yake mararin zai samu daga wajen ta daren farko dama ya riga da ya karba a waje tun da dadewa,daya kuwa ma bazawara ce dan haka baya bukatar yin wani rawar kafah.
Zainab ce tah kalli yunusa wanda yah ke kokarin saka kayan aikinsa na yansanda zai fita.
“Yanzu dan tsabar rashin mutunci irinna maza,daga kawoni koh satin amarci banyiba kace min zaka fita wani aiki,kuma itama waccar uwartaka hadda cewa yau nice dayin tuwon gidannan?,,t
Duk maganar da takeyi ta rike wani dan karamin kunkuminta mai kama da muciyah tana jijjiga shi,amma yunusa bai kukataba kaman tana magana da dutsi,sai ma cigaba da gyaran takalminsa da yayi.
“Yanzu yunusa inaa magaan amma kaaman ka bawa banza ajiyata,toh wallahi tun wuri kaje ka fadamusu ba zaman yi musu tuwo nazo yiba,toh in ma tuwonne haka kawai daga zuwana koh sati banyiba har za’a dameni da nazo nayi aiki,saikace an kawomusu jaka koh?,toh wallahi bazan yiba nikam”
“Ashe kuwa kema bazaki ciba,kuma ninan da kika ganni aradun Allah yau bazan sayo miki gurasaba,dan tah jiyama saida nayi bashi na sayo,kuma tunda na rakaki kwanan uku ai yah isheki koh,dan haka koh ki dafa su baki naki,ko kuma kice bazaki dafaba ki zauan haka kalass,danni kam bazanje nace musu ke ba jaka bace,amma tunda kina ganin sudin jakunai ne basu da iyaye koh kuma suma basuyi amarcin ba sai kije ki fada musu”
Yana gama kawo nan a zancen sa yah dauki hukarsa yayi gaba kaman ba shine mai daukin auren ba kwana uku da suka wuce.
Ajiyar zuciyah zainab tasake mai cike da takaicin abinda angonnata ya fadamata,dafe hannunta tayi akan goshinta dayan kuma ta rike kunkumi,abin duniyah duk yah fara isarta tun ba aje ko ina ba.
Ganin ba sarki sai allah ne yasata fitowa daga dakinnata ta nufi sashen surukar tata domin gaisheta.
Sun daga nesa take jiyo masifarta da babbar surukarta wanda duk cikin su tafi yi mata rashin mutunci saboda halinta na sanyi da rashin magana,
“Dallah can ta shi Kuban waje,dan mijinnaki yakawo kudi sai akace kuma a baki kiyi yanda kika dama dasu,wato dan baku kuke nemowa ba kuma zaune saidai kici kusha sai kuma kashi a masai,toh bazan bada jaka biyun ba,wazobiyah (hamsin)ga tanan ki sayo masa ja da yalo(tetracycline),yasha,ba duk ku kuke jawo gudawar ba,ko ina mutum yah wice banda kukdaje da wari babu komai,duk kun cika gida da kazanta”
Daga kai tayi tana kallon zainab wanda ta iso wajen ta zuba mata idanu sai masifah rakeyi babu full stop bare kuma comma,
“Ke kuma miye kikayimin shekeke akai kaman wata wanda tasaka wandon karfe iyee”
Saurin tsugunnawa zainab tayi tana jinjina masifa irin ta,inna laraba.
“Inna Ina kwana”
Saida ta yahtsina fuska kaman bazata amsaba kafin tace,
“Lafiyah,nikuwa kawuna(yunusa),yah fadamiki zancen yau zaki dora tuwon dareko,dan in bai fadamikiba toh bari ba nanata miki,yau kece da ciga magirka,dan kowacce yarknyah idan aka aurotah toh kwana uku takeyi saikuma tashiga layin dafa abinci,dafatan kin fahimta”
Saurin daga kai zainab tayi kirjinta yana bada lugufen duka,bata tsammaci abin haka yakeba sai gashi duk masifarta da raininta ta kasa yiwa inna laraba musu,sai ma wata karkarwa da jijinta yah debi yi………hmm muje zuwa.

Kwass kwass kwass kakejin karar takalimi mai tsini yana sakkowa daga kan beni.
Hajiyah mairoce ta sha wasu arnan kaya ga kuma sarkar gold a wuyanta,tun daga bakin kofa salma ta kafeta da ido ganin irin shigar da matar tayi da kuma itah kanta tsadar suturar.
Wannan shine kallonta na farko da hajiyah mairon,dan tunda yan gidansu suka kawota suka tafi koh wata halittar bata sake gani tah shiga sashenta ba sai mai kai mata abinci kawai,bare kuka uwa iba mijinnata rabinta dashi tun hirar dasukayi lokacin ana gobe daurin aure,sai kuma aikan da akayi mata akan maigidan yana kiranta sashen uwar gidan.
Saida tah gama jijjuyawar ta kafin tah dawo kujerar da take facing salma tah zauna,wani kallo ta ke zifanta dashi na zaki sani yarinyah,tun kafin wani a cikinsu yah yi magana sallamar su sameerah da umaruje ya jiyarci dodon kunnesu.
Ba laifi kam sameerah tayi shar da itah na kyallin amare,sai murmushi takeyi,a kasan kujera suka zauna,sameerah har wani sunne kai takeyi itah ga mai suruka.
Dauke kanta daga kallon salma tayi ta miyar kan sanyi zuviyar tata da kuma matar da suka shigo tare,
“Ina kwana mom”
“Lafiyah son yakk”
“Normal mom,yah abokiyar zamanki?”
“Hmm gata gaka ai,saika tambayeni itah,ko duk aurenne yasaka ka haka”
“Ahah kawai na tambaya ne”
Itama sameerah ganin sun gama gaisawa ne yasakata cewa,
“Ina kwana mom(uhmm a dole anji wani yah fada,duk da halin bakin cikin da salma take ciki saida taji kaman tah tuntsire da dariya)”
“Lafiyah”
Daga haka hajiyah mairo bata sake kallon inda sameerah take ba bare kuma salma wanda dama tunda suka zo wajen bata kulata ba,sai cigaba da magana da sukayi da danta.
“Lah my son nikuwa yah tafiyah Dubai dinanan ne,yakamata kaje karisa karatunka sananan idan ka dawo maganata tana nan”
“Mommy amma da sameerah zamu tafi koh,tumda wata shida zanyi acan bandawo ba”
Wani sihirtaccen dadine ya jiyarci zuciyar sameerah jin inda zasuje ita da mijinnata,har ta fara hasasowa irin rayuwar dazasuyi acan din,bazama ta yarda su dawoba idan suka tafi can,maganar hajiyah mairoce tah katseta daga hasken tunanin da takeyi zuwa na duhun bakin ciki.
“Bada it ah zaku tafiba kai kadai zakaje,so kake ka takura kanka ka kasa more jin dadinka,da budurwace ma ko kuma irin matanann na nuna wa sa’a sai ku tafi,amma banda wanda bata san komai ba kam tayi ta baka kunyah.
Sannan maganar mu na auren ku da Suhaila yana nan sannan itama ta dawo Nigeria lokacin dazaka dawo,nariga na yanke hukunci nan da sati daya zaka tafi”
Emotions guda uku ne yake yawo a cikin falon,umaruje kunyah ce ta kamashi,dan baiso mamar tasa tayu maganar auren da zayyi a wajen ba,itah kuwa sameerah tunda uwarta ta haifeta,da kuma duk irin tujarar da suke yiwa kansu a gida,bata taba jin disgawar da akayimata mai ciwo kaman wannan.
Yayinda salma a bangarenta kuwa dadi yah kaman yah kasheta jin yanda kishiyar tata take cakawa sameerah magana mai zafi.
Kowa dawowa yayi cikin hankalin lokacin ma har ummaruje yayi musu sallama yah tafi wajen abokanansa.
Suma tashi sukayi zasu tafi hajiyah mairo tah tsaida su tareda cewa,
“Bangama dakuba ai,inaso na sanar daku cewa na sallami dukkan yan aikin gidannan,daga yau kune zaku dunga yin komai na gidannan,na abincin mu da kuma na wanda ake fita dashi sadaka,ke zaki iyah tafiyah saboda ina da iko dake,ke kuma ki jira wanda yah kawoki yah tabbatar miki kiji da kunnenki,duk kuma wacce taga bazata iyaba toh yau basai gobeba zata koma gidan tsofi”
Har salma tayi niyyar juyawa tayi mata musu sai taga tamkar zakine a gabanta yake bata umarni,hakan yasa jikinta yayi sanyi tah koma ta zauna,duk da bata ce komaiba.
Itakuwa sameerah rarrashin zuciyar ta tayi ta bar sashen,zuciyarta sai bugawa takeyi tsoronta dayah kar asirin da take dan takama da shi ya karye ta,shiga uku gashi yamzu da gaske ta fara son umaruje aranta tun daren farkonsu yah kama zuciyarta.
Basu fi minti uku a zaune ba bayan tafiyar sameerah alhaji bala ya fito daga dakinsa yana gyara hannun rigarsa,wajen hajiyah mairo yaje yah zauna yana wani yake hakorah.
“Afuwan uwar gida sarautar mata,na barki a zaune kina ta jirana koh”
Saida hajiyah mairo tayi wani rausaya da kuma kallon salma ta gefen ido wacce tah zama tamkar kungi ganin koh inda take alhaji bala yayi bare kuma yayi mata magana,”anya kuma shine koh kuma wani ne daban”tah fada aranta.
“Babu komai honey kawai dai kasaka ni zamane har nakusan awa guda,nayi zaton koh kaki wankanne irin jiyah,ina shirin tashi naje na tayaka kuma sai gashi ka fitoma”
Dad’i kasheni haka alhaji bala yaji kaman an saka shi a cikin lambun soyayya.
“Ahah ahah karki damu gimbiyah mai tafiyah da ragamar rayuwata ,ina na isah nasakaki aiki bayan jiyah na saka ki,menene yake faruwa?”
“Sakonna na umarnin daka kafa gidanna nake so kasanar da matarka dan taji da kyau,karma ta daukeshi da wasa”
Kallonta alhaji yayi rai a bace kaman yaga kashi mai wari,
“Toh ma saina sake fada mata,ai duk abinda kika zartar dadai ne kawai yin biyayyane aikinta idan tanason zaman gidan”
Baki salma tasake tana kallonsu,musamman ma yanda alhaji yake wani cuccusuwa a jikin hajiya mairon,kaman wani mai shirin shan nono koh kuma mai kokarin komawa cikinta,koh kunyah basaji sai ka ce wasu yara.
Cikin dashashshiyar muryah irin ta wanda yashaki bakin cikinnan salma tace,
“Toh idan kun gama bani aikin dazanyi zan iyah tafiyah”
“Eh kina iyah tafiyah,kaima alhaji yah kamata ka tafi aiki haka,nima fita zanyi yamzu”
“Angama Ranki yadade”
Dukkansu kowa barin falon yayi farinciki kal zuciyar hajiya mairo,burinta yana cika.Kiran hajiyah laila tayi tana fada mata aiki yayi kyau sosai,dan yanzu kaff mutanen gidan itace take da iko dasu.
Inna rabice tah shigo dakin tah samu sameemah tah daga kayan aikinta tana shirin sakawa,aikuwa abinda bata sone yah faru dan kwaredede tah hada mata ganin abinda take shirin aikatawa.
“Tabdijan lallai ma kam,ina kike kokarin zuwa haka da aurenki da komai,kina da hankali kuwa ? Toh idam baki tambayi baba karamiba(sameer) ba inda zakije a gidannan,dan shike da iko dake a yanzu ha………….”
“Wallahi karki sake kicigaba da cewa shike da iko dani,babi wanda ya isa yayi iko dani,nice nan nake iko da kaina,kuma zuwa aiki ba bashi ya dad’e bai bani izinin ba ina ga kuma wanda zai hanani fitah daga gidannan idan yah isa”
Duk maganar nan da takeyi saida tah jiyo tah kalli inna eabi tukunna ta fada,dan ma tasan da gaske takeyi ba karyah ba.
Saurin fita daga dakin inna rabi tayi da sauri dan gani takeyi kaman sameemah dukanta zatayi.
Cigaba tayi da shiryawarta hankali kwance har ta gama tsaff kafin tah fito daga dakin,karo suka ci da baba umaru da kuma sameer wanda shima fuskarsa babu alamun walwala a cikinta,saidai hakan bai dameta ba dan shidinma haushinsa takeji kaman tah sha’keshi.
“Yah isa haka wannan boye boyen, inna rabi tah fadamin cewa wai kin ce saikin fita,toh babu wannan zancen,indai akam abinda yah farune shekarun baya inshaallah yanzu zan sanar daku basai gobe ba,saidai daga lokacin zaki bi mijinki ku tafi wannan shine burin ummanki idan har kin dauketa da daraja kaman yanda kika fada.

*fitowar farko kenan daga littafin WASA FARIN GIRKI(cigaban gidan gandu)*
Sannan littafin zai dunga zuwa da,MADUBIN GANI (point of view),wato duk wanda aka sakawa shine zai dunga bada labarin mai yake faruwa,da abinda yake ransa da kuma abinda yake gani.

Nashiryah fah tsaff domin kayatar daku fiyaeda littafin farko. Domin saida nayi nutso kana nayi linkaya kafin na fito muku da zakinsa coii.

Amma ba’a bawa wanda bashida jaka guda a wajensa(200),dan haka saikuyi harama domin mallakar naku a hannu.

Domin samun shigaban labarin dakuma yanda zata cigaba da kayawa toh ku biyoni tahanyar biyan kudinku nairah 200 kacal,ta wannan hanyar.
Masu turowa ta asusun banki:
3131951977
Masu biya ta katin wayah kuma:
09035784150

Muna jiran isowarku domin cigaba dulmiyawa cikin cakwakiyar da take shirin kunnowa kai,ina yimuku tabbacin baku biyha kudinku a banza ba.
Domin komai kuke bukata mun tanadar muku a littafinnan.
Tun daga kan rashin mutumci, artabu, cakwakiyah, sarkakiyah, soyayya tausayi, harma da saka ku kuka,duk na shiryah.

💎Sadi-Sakhna💎_______✍🏼

 

*(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)*

💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}

 

💎3~4💎

Kowa samun waje yayi yah Zauna a tsakar dakin harda sameemah wanda koh kayan aikinnata bata cireba,da alamun har yanzu bata hakura da zuwa aikinba.
Numfasawa baba umaru yayi kaman bayason fadin abinda yake sirrinne,saidai dolene yah budeshi yunda bukatar hakan tah taso.

 

💎*Baba umaru,a Madubin Gani*💎

 

Shekara talatin da biyar suka wuce,lokacin ina matashin saurayi mai neman na kansa,duk da yayuna da kuma babana suna iyah kokarin su akan komai naci da sha, har ma da aure idan mutum yaso niyyar yi.
Saidai ni ban yadda da hakanba don nafison nakasance ina neman abin kaina bawai na dogara da abin wani ba.
Hakan yasa na yanke shawara inda na fara bin babbaan yayanmu mai suna ABDULLAHI,ana ce masa malam Audu,wato shine kawunku kawu audu wanda yah rasu tun kuna kanana,sanadiyyar ciwon koda.
Shikuma sana’arsa shine saida kayan fulani a garin bauchi a kasuwar wunti. Bayan wani dawowarsane nace nima zan bishi mutafi koh taimaka masa saina dunga yi,baiyi musu ba kuwa saima dadi da abin yabashi.
Lokacin da muka tafi saida nayi shekara d’aya kafin na zo gida,inda anan ne na hadu da innarku hajara tana kawowa fura daga kauyensu zuwa garin mu,da farko nasha wahalar shawo kanta saboda macece itah mai kunyah dakuma sanin yah kamata.
Lokacin da muka daidaita kanmune muka sanar da manyam suka shiga zancen,da yake aurene ba irin na yanzu ba sai an ja lokaci,wata d’aya mukayi sai gashi mun tare a dakin Da’aka yimana da kuma dan zagaye.
Zaman aminci da ganin darajar kowa mukayi har tsawon shakera biyu kafin hajara tah samu ciki,
DA take ni ba anan nake ba ina wajen Audu bansan me ake cikiba,ashe hajara wahala yake ji a wajen mahaifiyar mu kasancewar bata sonta,tafi son na auri y’ar kawarta aminyarta wato Ramatu,saidai duk abinda yake faruwa hajara tah toshe duk wata kofah da zansan abinda yake faruwa,har saida tazo haihuwa ne lokacin nazo akace bazata iyah haihuwa lafiyah ba saboda karancin jini da kuma rashin samun ishashshen abinci mai gina jiki.
Abinne yaban mamaki ganin babu abinda aka fi karfinsa ,tun daga sannan na fara zargin ba lafiyah na musamma yanda naga tah rame tayi baki,mata fara da itah amma tah koma haka.
Allah cikin ikonsa dayah dubemu sai hajara ta haifi d’anta na miji wata ranar juma’a bayan doguwar nakuda da kuma jin jiki da tayi,har masu karbar haihuwar suka ce bazata sake haihuwa ba ma saboda yanayin laushi da mahaifarta tayi.
Ranar suna aka sakawa d’a suna SAMEER,bayan an yanka masa rago.
Kasancewar ina nan nazo gidan saboda haihuwar matata,sai hajara taji dadi har tayi wankan arba’in dinta cikin walwala da kwanciyar hankali,duk da bata fadaminba amma nasan taji dadin jama danayi a tareda itah batareda na tafiba.
Tun da IYAH taji cewar hajara bazata haihuba sai zakaminta nasan na auro inna ramatu yah tashi,aikuwa tun kafin haajara tayi arba’in tashiga ta fitah saida tah kawo ramatu gidannan,duk da bana son auren amma nayi na’am da cewar hakan yana cikin kaddarata.
A zama na da ramatu babu inda na banbanta ta da matata hajara saidai sha’nin mata dakuma in sun samu daurin gindi daga wajen uwar miji,sai hakan yakara hura wutar tsiyar ramatu a cikin gidan.
Tun kafin hajara tayi arba’in ramatu da samu ciki,wanda itah bansamu damar ganin haihuwar ramatuba sai saƙon haihuwarta daya sameni kawai.
Ban tashi dawowa gidaba saida sameer yayi wata shida yayinda shikuma dan inna ramatu (manjo )yake da wata huɗu.
Aikimmu kam alhamdulillahi yana karbuwa sosai,dan yanzu shagonmu yah cika da kaya,har na samu hayar daki ɗaya wanda zan iyah tafiyah da matata daya muzauna.
Nan ma wani artabun aka buga ina na yanke shawarar yin wata shida da kowacce sai kuma tah koma wata tazo.
Bayan shekara goma muna kasuwanci sai ciwo yah kama mallam Audu inda ya barmin kasuwamcin nakeyi,saidai nima banyi wata biyu ba akayi godabara kaya suka ce ɗibemu a hankali.
Hakan yasa nayi niyyar komawa gida saboda komai yah kare,wannan zuwan da ramatu mukaje sai masifah takeyi wai an koma yin abinci marar daɗi,nida jinta kawai nakeyi dan banida amsar dazan bata a lokacin.
Da muka isa gidanma wani tashin hankalinne yasameni, domin a kwance na samu hajara a ɗakinta rai a hannun allah,wai laulayin ciki takeyi tun wata uku da tafiyarmu,gashi bayason abinci barkatai sai wanda tah zaba tukunna.
Nan nafara jinyarta gashi kuɗin hannuna bashida yawa sosai,ana cikin hakanne wata hajiyah ta turo saƙo akam idan inaso naje zata bani aiki na gadi a gidansu,kuma ta yaba da hankalina saboda ina yawan sayar mata da kaya,mun saba a wajen cinikayyah.
Abinda nayi tunani shine aikin gadi sai an zauna a gidan,sannan indai za’a zauna toh fah wata rana za’a bata,idan kuwa na kuskura na tafi da ramatu toh a ranar za’a koromu,sannan kuma bazan iyah tafiyah na bar hajara a wannan halin ba,kuma halin da take ciki tana bujatar taimako sosai.
Hakan yasa na yanke shawara babu wanda yahsani na cewa ramatu aikin dako zan tafi yi a wani ƙauye,kuma bazan iyah tafiyah da hajara ba bata da lafiyah,tsalle tayi ta dire akan bazata je wajen wahala ba saidai na tafi da hajara kk kuka nasan yanda zanyi,lokacin kuwa ta yaye ƴarta sameerah.
Baƙaramin daɗi najiba dana samu nakashe wannan wutar.
A ranar na fara yimana shirye shiryen kayan ita dai hajara kallona kawai takeyi,dan nasan idan zanyi shekara ina abu indai ba faɗamata nayiba bazata tambayeni ba.
Ranar tafiyarne na kaiwa iyah kayan sameer saboda yana zuwa makaranta shi,kuma ma yayi girma a tafi dashi gashi bamusan wajen ba muma tukunna.
Mun daɗe muna tafiyah a mota sai gamu a garin bauchin yakubu,hajara kam duk tah galabaita saboda jijjigar mota ,gashi dama koba mota amai takeyi inaga ta samu dalili.
Mai adaidaitah sahu muka ɗauka zuwa anguwar rail way inda tayi mana kwatancen gidan.
Shima kansa mai adaidaitan baisha wahala ba saboda gidan ba a lungu yake ba,kan hanyane inda kowa zai gane.
Kuɗin na bashi kafin na ranƙwafo da hajara zuwa jikina muka fitah zuwa bakin gidan.
Duba takardar ta take hannuna nakeyi sannan kuma ina sake duba gidan,”anya kuwa shine?” nafaɗa a raina,dan gaskiyah giraman gidan bayyi kama da wanda za’a gayyaci kamanni cikinsaba.
Ganin ba sarki sai allah ga kuma matata tana bukatar taimako ne yasa kawai nayi shahada da tunkari kofar gidan,saboda mun riga mun zo kuma ai babu batu komawa.
Wasu inyamuraine masu kayan sojoji suka buɗe mana kofar gidan,saboda tsabar tsoro bansan lokacin dana mika masa takardar hannu na ba,saboda dama tace idan nazo nabawa ɗayah daga cikinsu,zasu barni na shiga.
Hakan kuwa akayi ina mika masa yabani hanya wuce ina mamakin toh wane irin aiki kuma zanyi,danni a iyah tunanin gadi nakawo da tace zata ban aiki a cikin gida kuka zan iyah zuwa da iyalina,toh kodai ba nan bane,dan nan kam suna da mai gadi,wanda koh kare bazai nuna masa gadin ba ,dan ga ganinsa a fuska ma zaka tantance.
Nidai ban sare ba muka cigaba da tafiya a hankali saboda yanayin tafiyar hajara da bata sauri saboda rashin karfin jiki.
A bakin wata kofah muka tsaya saidai itah karamace amma dai tafi kofar shiga ɗaki girma,da wata yarinyah muka,haɗu tah yimana iso zuwa ga matar gidan.
Shiga mukayi tareda itah bayan tah dawo tacemana mu shiga.
Tabbbb danƙari wani kayan sai amale aradu,ai ina arba da inda aka shigo damu na saddaƙar da cewa ba’a Nigeria nake ba kawai,dan wajen badai ado ba kam.
A ƙasan wajen muka samu waje muka zauna inda mai aikin tacemana mu tsaya.
Bata daɗe ba kuwa sai gata ta shigo bakaman sauran masu kuɗiba da zasu iyah barka a zaune har awa guda.
Sallama tayi mana tareda nuna mana kujera akan mu zauna,nidai duk hankalina bai kwanta da zaman kujerar ba saboda kar mu bata musu,amma kasancewar ƙasan da sanyi ga kuma yananyin jikin hajara sai muka koma kan kujerar.
Har ta gyara zama zata fara magana sai kuma tayi saurin kiran wata a cikin gidan,saida ta bayyana naga ashe wacce ta rakomu ce,
“Yawwa blessing kawo musu abin sha da abinci mana,kinga har na fara cikasu da surutu kafin na bansu wani abu(juyar da kanta zuwa ga inda muke sannan tah cigaba da cewa).
Afuwan malam umaru,naga mai ɗakinnka ma kaman batajin daɗi sainaga kaman ma ƙaruwa zamu samu,yamzudai bari na saka akaiku ɗakin dazaku zauna kuci abinci ku huta daga baya sai muyi magana koh?”
“Toh shikennan babu matsala duk yanda kika ce ranki yah daɗe”
“Kacemin madam kawai,itah kuwa tah kirani da sunana Maryam,allah bamu ikon zama na fahimatar juna”
Daga haka ta tashi tayi hanyar wan beni,itah kuwa hajara tun gaisawa da sukayi bata ce komai ba sai murmushi da take kawai,duk wanda yaganta yasan akwai alamun gajiyah a tareda itah.
Ɗakine mai matsakaicin girma amma yah ƙawatu kam matuƙa,gashi an shareshi tasss sai ƙamshi yake fitarwa mai daɗi da kuma sheƙi.
Wacce hajiyah maryam ɗin takira da blessing ce tasake dawowa ɗauke da kayam abinci,godiyah nayi mata na ɗawainiyha damu kafin tah fita a ɗakin.
Kallon hajara nayi wadda samu bakin gado tah zauna tana ɗan riƙe ciki.
“Ciwo cikin yakeyi ne”
Batayi magana ba sai jijjiga kai da tayi,nima bansake tambayarta ba nayi hanyar banɗaki domin ganin menene babu,saidai da mamakina naga komai yana inda yake gashi na zamani,dan ma allah ya taimakeni nasan yanda ake amfani da banɗakin zamani da hakan sai yaban wuyah.
Ruwan mai ɗan zafi na haɗa mata a bahon wanka,wajen cin abine dai saida aka kai ruwa rana tukunna.
Muna cikin hakanne kuwa blessing ta sake dawowa,ɗauke da magani inji hajiyah maryam na masu ciki,dayake itama cikinne da itha kuma bai girma sosai,dan zayyi wata ɗayah dana hajaran.
Ina bata maganin kuwa tah fara baccin farin ciki wanda rabonta dashi har tah manta ma.
Kwanan mu uku a gidan kafin hajiyah maryam ta nemi ganina a falon baƙi.
Gaisheta nayi tah amsa batareda dogon jawabi ba tah shaidamin cewar aikina shine bayin fulawa safe da yamma da kuma kula dasu akai akai.
Mamaki abin yabani jin ɗan karamin aikin da zanyi kuma aka bani muhalli da kuma albashi ga uwa uba abinci mai rai da lafiyah,dan kwanan mu uku har mun murmure daga ni har hajara,wanda yanzu tah koma kaman ba itab saboda. Magananin da ta ke sha da kuma samun abinci mai gina jiki.
“Nasan zakayi mamakin ganin karamin aikin dana baka,amma bakomai bane dama nayi niyyar taimaka maka,kuma bai kamata mutane masu amana da rike mutuncin alƙawari su ƙare ba,kayimin abinda bazan mantaba nima,inshaallahu dama ina da niyyar buɗe shago toh zan baka ka riƙemin nan gaba,amma a halin yanzu wannna shine kaɗai hanyar dazan tsimaka maka”
Farin cikine haɗi da jin daɗi suka kamani har na rasama da wanne irin baki zan gode mata irin kyautar da tyimin haka.
Itama ganin na diriricene yasakata saurin barin falon tana murmushi,da alamun bata son godiyar tawa kenan.
Nikuwa hakan bai wuceba dan dana koma ma na faɗawa hajara tun kafin na rufe baki tace zatayi mata godiyah tsakanin itah da itah.

Tun daga fita godiyah ba itah hajara ta,dawoba sai wajen karfe tara ba dare,abinne ya ɗauremin kai inda na tamabayeta mai yah faru,nan take cemin wai hira suke tayi irinna mata ,musammaan ma akan ciki da kuladashi,da kuma tsabtar jiki da tah muhalli.
Sannan tace mata idan cikin yakai wata biyar zasu dunga zuwa awo tare.
Tun daga lokacin daga na fita sai hajara ta tafi sashen hajiyah maryam tanan tayata ɗan ayyuka ita kuma tana koyamata abubuwa,musamman da yake karatun nursing tayi saidai bata aiki a kan hakan.
Nima bana hanata zuwa tunda ina ganin sanji a abubuwa da dama a game da zamanta da hajiyah maryam ɗin,kuma bata zama cikin kaɗaici sai ma wani haske da ta ƙara saboda kyakykyawar kulawa da take samu a wajen hajiyah maryam ɗin,matar da ba abinda zan iyah saka mata dashi sai alkhairi.
Wani muhimmin shirye shiye aka fara a gidan na tarbar dawowar mai gidan wanda yake aiki a kasar India,mukan mu ganin hajiya mairo tana murnar tarar masoyinta yasa muma muka fara tayata murnat duk da bamusan shiba bare jin labarinsa,hajara kamma a can ta yini suna ta aiki.
Can wajen la’asar misalin karfe uku ji karar shigowar motoci,tab nan fah abin yazama abun kallo,dan kuwa inaga duk girma da faɗi irinna farfajiyar gidan saida suka cika da motoci kaff,babu koh masakar tsinke.
Mudai muna tsaye daga bakin ɗakinmu wanda yake ɗan gefe da inda motocin suke fakawa ,mun zubawa sarautar allah ido.
Can bayan sun gama shigowane kuma sai dukkan sauran motocin suka baɗe suka fito.
Samarine da mata farare kall ba irin na kasar nan ba,duk da akwai masu surkin bakin fata a cikinsu,sanye suke kkwannensu da kaya baƙiƙƙirin kaman zunubi.
Dukkan layi sukayi a jikin jar motar da take tsakiyah wanda itah ce kaɗai mai banbancin kala a cikinsu,dan duk sauran baƙaƙene.
Na gaban motarne yah fito kafin yazo yah buɗe bayan motar. A ɗan jima kafin mamallakin motar yah jefo ƙafarsa waje,kafin yah fito da dukkan sauran jikinnasa.
Kyakykyawane na fitar hankali,dan koni dana ke na miji naga kyawunsa bare kuma mace,.
Kayane a jikinsa farar shadda ƙal,da kuma baƙar hula da takalmi shima baƙi siɗik, taku yake cikin kwanciyar hankali har yazo yah wuce falon hajiya mairon,yayinda sukuma sauran naga duk sun koma motarsu sun bar gidan,sai jar motarce kawai take nan da kuma wanda yah tuƙota.

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

💎Sadi-Sakhna________✍🏼💎

 

 

*(¯’*•.¸,¤°’✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿’°¤,¸.•*’¯)*

💎•°• *WASA FARIN GIRKI* •°•💎 {cigaban gidan gandu}

 

💎5~6💎

Tun lokacin daya dawo aka ɗauko wasu masu aikin daban ana biyansu ,saboda abincin da’ke dorawa gidan yah fi na mutum ɗari ƙartin samari,duk kuma na sadaka ne,da farko hajara taso tashiga cikin masu girkin ta tayasu amma hajiyah maryam ta hanata,a son ranta tah huta ba’ason mace mai ciki tanayin aikin wahala mai tsanani.
Har aka shafe kwana uku da zuwan alhaji ABDULWAHAB kullum gidannan a cike yake da mutane masu neman taimako,kuma duk wanda yah shigo toh baya fita hannu rabbaan saida kayan abinci koh na sutura,gwargwadon abinda yazo nema dai.
Masu karbar abinci kuwa har dare ake kaiwa ana karbar abinci a kofar gida,dan masu rabawa da ban masu dafawa daban haka masu sakawa a cikin robobi.
Muma kanmu kayan da hajiyah maryam ta bani har kuka nayi saboda ganin yawansa.
Tunda muka kalli alhaji abdulwahab lokacin da yah zo gidan zuwan farko bamu sake sakashi a idonmu ba saboda yawan zirga zirga dayake tayi na,meeting halarta wurare da sauransu.
A kwana na huɗu kuwa yah koma inda yah fito wato ƙasar India da sassafe ma yata fi koh tashi bamuyi daga bacciba.
Shima saida rana nakejin zancen a wajen hajara ta dawo daga wajen hajiyah maryam,wai ƙiran gaggawane yah sameshi daga can akwai abinda zayyi.
Kwanci tashi har muka shafe wata guda ciff a garin bauchi gidan alhaji abdul wahab,shahararren mai kuɗi da duniyah take damawa dashi.
Zuwa sannan hajara tah daina wani laulayi saboda cikinta yayi wata biyar,duk bayan sati biyu yanzu suke zuwa awu ita da hajiyah maryam,inda direba yake kaisu yah ɗakkosu.
Kowa yah kalli hajara sayya yayi mamakin canjawarta tayi luwai da itah.
Nikuwa a cikin wata biyunnan zuwana gida uku,kuma kowanne sainayi sati guda nake dawowa,hankalin ramatu bai zo kaina ba saboda tah samu sana’a tanayi ,gashi kuɗi yana shiga mata,idan nace tazo mutafima nasan bazata biniba tunda bata san wainar da ake toyawa a canɗin ba.
Da haka rayuwa ta cigaba da garamana har watan haihuwar hajara yakama.
Naƙuda tah fara gadandan inda hajiyah maryam ta zauna a wajenta tana taimakata,amma ganin abin yana son yah fi ƙarfin saninta gashi itama da tsohon ciki,sai ta ɗakko mota domin mu tafi asibiti,musamman dana faɗamata yanda tayi a cikin fari,da kuma matsalar da mahaifarta take dashi.
Can asibitinma saida muka kwana tukunnan a washagarine tah samu damar haihuwa.
Munyi farin cikin samun kanta duk da tah galabaita amma saidai yarinyar tana jin jiki ga kuma tare ta fito duk da mahaifar gabaɗaya,wannan labarin yaui mana babu daɗi amma babu yadda zamuyi sai rungumar ƙaddara.
Kasancewar yarinyar bata da lafiyah saida muka zauna a asibitin na tsawon kwana biyu tana karbar magani,ga tsada amma hajiyha maryam tace koh godiya kar muyi mata,itace da godiyah ma zaman da muke da itah,saboda bata da kowa a garin bauchi aurene kawai yakawotah.
Ranar suna iyah yan uwan hajara ne guda dayah tazo,wanda itah ma shekararta biyune da aure dama tana da niyyar zuwa,wato inna rabi.
Yarinya taci sunan hajiyah MARYAM,ana kiranta da sunan tah,kar kuga murna a wajen hajiyah maryam kaman ta cinye yarinyar dan murna,dan ma bata da lafiyah ko yaushe tana ɗaki,ba a fiye futowa da itah ba,saboda cutar sanyi da take ɗauke da shi.
Bayan sati biyu da haihuwar hajara itama hajiyah maryam tah haihu,inda tasamu ƴa mace,saidai ita a gida ta haihu,kawai ma’ikaciyar lafiyar aka turomata domin tah taimaka mata.

Cikin koshin kafiyah kuwa suka samu kansu daga itah har y’arta ba’a samu wata matalaba,itah ce ma aka ɗan yi mata ɗinki saboda ɗan ƙaruwa da tayi.
Tun kafin suna mutane suka fara cika da mutane,mutanen arziƙi da kuma ƴan uwa wanda dama haihuwarta suke jira.
Lallai munga mutane kam kuma manyan mutane ba mutane haka ba.
Duk da haihuwa tah farko da alhaji abdul wahab yasamu amma bai zo ƙasar nigeria ba,hakan yabawa mutane da dama mamaki kan cewa wane irin aikine ya riƙeshi haka,dan tun farkon samun cikinma bai wani murna ba,saidai tambayar lafiyar uwar kawai yakeyi,ga shi shekararsu huɗu da aure sai yanzu allah yabasu arziƙin samun haihuwa.
Da sati yah zagayone yarinyah taci suna SAMEEMAH,suna kawai taci,kasancewar hajiyah maryam tanason sunan.
Biki akayi a lokacin sunan kaman na yin auren wata mace,saboda dumbin mutane da taro yah tara, banda abin duniyah a da akayi ta rabawa.
Tun daga sannan hajiyah maryam ta cigaba da rainon ƴar ta ciki kwanciyar hankali.
Maryam kuwa tun bayan haihuwarta kowane sati sai ankaita asibiti domin gwajij numfashinta,amma koda da sau ɗayah hajiyah maryam bata taba gajiyawa ba akan hakan,mukan ma har mun fara cire rai da rayuwarta,musamman ma mahaifiyarta wanda cikin dare idan na farka saina ganta tana zaune tah zuba mata ido,soyayyar ɗa da mahaifi duk sainaji nima wani iri.
Dahaka muna cikin yanayinnan har maryam tayi wata huɗu,amma kaman ƴar wata biyu haka take.
Wata ranane jikinnata yayi tsanani muka tafi asibiti kwananmu biyar acan tace ga garinku nan.
Ko mukanmu iyayenta bamu yi damuwar da hajiyah mairo tayiba,dan saida nazo ina basu baki itah da hajara.
Dawowa gida mukayi gida saboda ayi mata sallah da kuma kaita gidanta na gaskiyah,inda kowa zaman jiran nasa yake yi.
Bayan sadakar uku har mun fara manatawa da itah,dan dama itah ba lafiyayya bace.
Zuwa yanzu sameemah tayi wayo dan kullum nan muke yini da itah,saboda hajiyah mairo tah koma aikinta na asibiti,duk da alhaji Abdul wahab baya so amma haka ta lallameshi ta,koma aikinta a cewarta taimakon mutanene zai kaita ba neman kuɗiba.
Shaƙuwa sosai tah shiga tsakaninmu da sameemah,dan wani lokacin da ƙyar mamarta take ɗaukarta idan tah dawo daga aiki,dayake akwai abincinta na yara shi ake bata.
Itah ma hajara daga bayah aiki hajiyah maryam ta,sama mata a asibitin suke na shara da gogen daƙin masu jinyah,sai yazamana tare suke tafiya a motarta,idan hajiyah maryam ta shiga aiki sai hajara tah riƙeta,kusan ko yaushema tana wajen hajaran idan dai ba dutynta bane.
Haka har muka samu shekara biyu kyawawa a gidan,yamzu ansaba kowa yasan da wa yake zaune,dagani har hajara munyi sabo da mutanen wajen sosai da sosai.
Sameemah kyakykyawar yarinyahce dan kallo ɗaya mutum zai tabbatar da hakan,saidai bata da son mutane irin na uwarta,dan idan ka ɗauke mu da mahaifiyarta toh babu wanda take sakewa dashi,da farko hakan kaman abin ƙiwa ne yarinta sai kuma hakan yajuye kaman halinta ne,amma duk da haka yarinyah ce mai shiga rai da kuma farin jini a wajen mutane.
Kwatsam da tsakar rana saiga alhaji abudul wahab yadawo saidai wannan zuwam babu manyan motoci kaman na farko,ita kanta hajiyah maryam tayi mamakin rashin zuwannasa da kuma zuwan bazatan dayayyi,dan daga kallon irin kallon da take jifansa dashi mutum yasan tana jin haushin rashin zuwannasa.
Sameemah da take hannunta yah miƙo hanu zai karba,aikuwa dama badai kiwuyah ba,da sauri tah maida hannun gefe tareda juya kai.
“Kagani koh,ko ƴar ka ma tana ƙin zuwa wajenka tunda bata sanka ba”
Dariyah kawai yayi tareda karbar yarinyar duk da bata so yayi hanyar kofar tasu.
Itah binsa tayi a baya,ni ma kuma muka bar wajen har sannan muna mamakin irin zuwan bazatan da babban mutum kaman alhaji abdul wahab yayi.

Lokacin da kwana uku yah cika munyi zaton zai koma,sai muka ga har anyi sati guda bai tafiba,hakan yasa mukayi tunanin koh hutu yah samu a wajen aiki yasa yazo domin yayi su da iyalansa,kuma ya kyauta hakan,dan itah kanta hajiyah maryam taji daɗin hakan.
Sannan sameemah har ta fara sabawa dashi dan koyaushe yana tare da itah,kuma duk sanda yah fita sai yah siyo mata abin wasa da kayan ciye ciye,wani abin ma bata iyah amfani da shi,kawai siyah yake irinna iyaye masu ɗokin irin na ƴaƴan fari.
Mukuma a namu bangaren muna tah shirye shiyen tafiyah zuwa gida,saboda iyayen hajara suna so taje ganin dangi,nima kuma inason zuwa ganin yah yanayin gidan yake tafiyah. Mun yanke shawarar nan da sati ɗaya zamu tafi,kuma zamu kai wata guda bamu dawoba.
A ranar da daddare kowa yayi bacci kasancewar daren yayi sosai,ba abinda mutum yakeji sai shirun duniyah kawai,kowa yan kwance yana hutawa.
Ban daɗe da zagawa bayi ba naji bugun ƙofar ɗakinmu,saida na kalli hajara wanda take kwance kafin na isa bakin kofar ina wasiwasin na buɗe ko kuma na barta,ina cikin hakane naji muryar hajiyah maryam da alamun tashin hankali a cikin muryarta tana cewa,
“Malam umaru kabuɗe ni ce,kayi sauri banida lokaci sosai”
Cikin sauri har jikina yana rawa na zare sakatar dakin da sauri.
Haɗa ido mukayi da itah jikinta sai rawa yakeyi lokaci zuwa lokaci tana waigawa baya kozata ga wani yana biyota.
Sameemah ce a hannunta wacce take ta bacci abinta,saurin mikomin itah tayi da sauri,zuwa lokacin hajara tah tashi,sai na miƙa mata yarinyar,tun kafim na tambayeta ta fara magana cikim sauri muryar tana rawa,
“Na roƙeku dan darajar allah,ku fitah daga gidannan a yanzu basai gari yah waye ba ku bar gariannan ma idan san samu ne,bazan iya yimuku bayanim abinda yake faruwa ba,saidai inaso ku riƙemin ƴata da amana a wajen ku,duk da nasan zakuyi hakan tunda nafi kkwa sanin halinku na mutunci,sannan ku kumin alkawari zaku riƙeta a matsayin ƴar da kuka haifa a cikinku,kar wani yasan gaskiyar iyayenta,na baku itah halak malak burina kawai tasamu gata da kuma rayuwa mai kyau koda bana cikin rayuwarta,kartayi maraicina ko kuma rashina”,
Tana gama faɗan hakan tah ciro wani ƙullin kuɗi a jikin rigarta ta miƙamin kafin ta cigaba da cewa,
“Ga wannan kuɗin,na aikina ne danayi na tsawon shekara kuda,wannan zai isheku hawa motah,wannan katin kuma na asusun bankine mabuɗin cirewar sunan sameemah ne,nabaku zaku iyha amfani dashi wajen inganta rayuwarta,amma idan kunga bazaku iyah amfani dashi ba saboda nasan halinku toh,ku ajiyemata idan ta girma ku bata a matsayin kyautata tace a gareta kuma ina rokonta,da tayi muku biyayya tamkar mahaifanta”
“Kuyi sauri ku fito yanzu nan kafin lokaci yah kure mana,kuma dan allah karku bari sameemah tah tako garin bauchi lo da wass”
Tana gama faɗan hakan tah fara haɗamana kayanmu da sauri,akwati ɗayah muka ɗauka ta rako mu bakin get ɗin gidan,hajara tana rungume da sameema a jikinta,duk da bamusan menene ba amma munsan abinda zai raba ɗiya da mahaifiyarta na kaɗan bane ba.
Hajara ce tayi karfin halin cewa
,”amma hajiyah maryam bazaki iyah guduwa keda itah ba ko kuma boye ta?”
“Dazan iyah hakan danayi tuntuni,ku tafi kawai wannan shine iyah abinda zan iyah,zanyi mata alkhairi daga inda nake ma”
Tana gama faɗamana hakan tah juya cikin gidan da sauri,hawaye yana zuba a idonta amma sai ƙoƙarin hanasu zuba takeyi,saidai ko daga ganinta tah ɗan aamu nutsuwa data raba ƴarta da koma menene yake tunkarowa.

A daren muka fara tafiyah har da gudu gudu,domin muma babu abinda yake cikin ranmu sai ƙoƙarin ƙubutar da rayuwar baiwar allah da take bacci a bayan hajara,batasan ma me akeyi a duniyarba.
Kafin gari yah waye har mun kai wani kauye dayake kusa da bauchin a hanyar gidanmu,tsaywa mukayi domin hajara ta huta saboda gajiya ga kuma goyon yarinyah ƴar shekara biyu.
Anan muka tsaya muka sayi ƙosai muka ci,kafin muka tsaya jiran motar garinmu a wajen.
Cikin sa’a kuwa saiga mota bata cikaba muka shiga sai gida.
Da tsakar rana sai gsnimmu akayi babu tsammani,sai tambaya suke mai yasa muka taho yau bayan sai wani satin,cawa muka kamawa takeyi kawai,sauran mutan gida sai tambayar hajara suke akan suga ƴartata,ba musu kuwa ta sakko da sameemmah wanda take tah bacci abinta,jin hayaniyane yasata farkawa,aikuwa tana ganin inna Hauwa matar mumkaila wanda amaryace a lokacin zata ɗauketa tayi saurin maƙalrewa a jikin hajara,tana kukan rikici.
Kowa mamaki yakeyi da kyau irin na sameemah har ma kyau na kayan jikinta,marasa haƙuri kam ma har saida suka yi magana irin su inna ramatu.
Nidai daga ni har hajara babu wanda yace wani abu,sai sunane muka ce musu an samu sabani ne sunan ta sameema ba maryam ba kaman yamda aka faɗamusu,dan haka bamu sha wahala ba wajen boye ainihin tarihin sameemah a wajensu.
Tun daga lokacin sameemah ta ware tamkar ƴar gida,dan dama ta saba damu sosai musamman ma hajara.
Shekarar sameemah huɗu hajara tah dara ciwon ƙafa,wasa wasa ana tah magani amma ciwo sai gaba yake yi,sannan nikuma kulawar danake bawa sameema sai yah fara zuwa idon mutanen gida,hakan yasa dana ga za’a samu matsala na fara ja baya da lamarinta ba kaman da farko ba.
Haka na shigaba da kulada itah,har zuwa wasu shekaru inda tace itama ga garinmu.

Wannan shine iyah abinda nasani a game da abinda yake faruwa,
Ina mahaifin sameemah bansaniba kawai nasan yana aiki a india sannan kuma mahaifiyarta bansan koh tana rayeba,dan maganar da take yi mana kaman wasiyyah haka take yinta.
In kuma tana raye bansaniba,dan nasan danginta amma ban san a wane gari suke ba,abinda nasani shine itah ba ƴar garin bauchi bace kawai.
Amma tabbas tah kargaɗeni akan kar na sake na barki kije garin bauchi.

💎~~~💎

Yana kawo nan a labarin sa saida kowa ya zubar da kwallah na tausayin hajiyah maryam da kuma tunowa da mutuwar inna hajara musamman ma inna rabi an taso mata da tsohon mikin mutuwar ƴar uwarta mai sonta,banda sameemah wanda fuskarta babu alamar rauni a cikinta,saima kallon gefe da tayi kawai.
Tashi baba umaru yayi ya ɗauko wani ɗan akwati ƙarami ja.
Buɗeshi yayi da wasu lambobi yah ciro wani kati a ciki,na shaidar sumun asusu a banki.
Miƙawa sameemah yayi tareda cewa,
“Wannan shine abinda mahaifiyar ki ta bamu akan cewa mu baki idan kin girma ko kuma muyi amfani dashi,saidai bamu taba ba dan aduniya babu abinda bazamu yiwa jinin hajiyah maryam ba,dan tayi mana abinda bazamu taba mantawa dashiba.

Lambar asusu:3131951977
Lambar waya:09035784150

Dan allah karki karanta koh karka karanta baka biyah kuɗin ba,domin akwai hakkina na naira jaka ɗaya(200) a kaknka koh akanki idan baki biyaba kike koh kake karantawa.

Leave a Comment