Books Reviews & FAQs

Wani Jinkiri Hausa Novel Complete

7/11, 11:08 PM] tannee Alkalancy: 🍃🍃🌹🌹
🍃🍃🌹🌹

🌹🌹🍃🍃 🌹🌹🍃🍃

_*WANI JINKIRI…*_

*Written by* ✍🏻

*Sa’adat Alkali D/tsafe*

*🌈KAINUWA WRITES ASSOCIATION*🤝🏻📚📚

_*Da sunan Allah mai rahama mai jinkai*_

*“`Dikkan godiya ta tabbata ga Allah (S. W. A) da yanuna man wannan rana, masoya littafe na gani nasake dawo muku da wani sabun littafin wanda bashi kuke tsimaye ba, ina mai baku haquri narashin ganin cigaban littafina da bansamu damar yin cigaban sa ba, wanda yake da suna KASAITACCE hakan yafaru ne sakamakon wasu ‘yan dalilai amma karku damu zanci Gaba dashi insha Allah nagode*“`

🍃🍃 _*Dedicated-*

_*Nasadaukar da wannan page nawa gaduk wata Mace dake cikin duniyar nan, wacce take da sunan Aysha, ya Allah yakara daukaka wannan sunan aduniya, da dik masu sunan gaba daya ameen…*_😘 🌹🌹

*(1)*

Kwance take kan dan wani qaramin gado tayi nisa sosai cikin tunanin kadarar ta da Allah ya qadarto mata cikin rayuwar ta,

Yanzu Allah kadai yasan erin samarin da take samu suna tafiyar su wasu ma da zaran anfara musu zancin suturu magabatan su suke tafiyar su, wace erin rayuwace wannan? dika sa’annin ta sunyi aure wasu ma Harsun Haihu amma eta shiru kakeji.

tunawa tayi da wata rana har gore wata maqociyar su da sukayi fada da ita tamata wanda ranar kwana tayi tana kuka har kukan da tayi ya haddasar mata da ciyon kai,

tadade tsaye a kanta tana karantar ta kokadan batasun ganin ‘yar uwar ta cikin wannan hali na quncin da take ciki,

jitayi ana share mata hawayin ta dake zubowa daga idanun ta, wanda ita kanta batasan iya adadin wanda ta zubar ba, ko ba’a fada mata ba tasan qanwar tace Dijah, lumshi idanun ta tayi a hankali kafin tayi qarfin halin miqewa zaune tana duban ‘yar uwar ta.

cikin qarfin Hali ta qaqalo murmushin dole tace sister yau she kika shigo dakin nan har bansani ba?

tafada tana tsare Dijah da kyakyawan idanun ta tare da murmushi dauke a fuskarta wanda saida gefin kuncinta yalotsa.

inako zakisan nashigo Adda?Dija tafada tana mai kallon ta, kafin taci gaba da cewa “bayan kinyi nisa cikin tunanin da kika sabayi a kullum wanda kokadan bai da wani amfani agareki, sai kinje kinjefa kanki cikin wani hali da mu kanmu baki daya, Haba adda kiyi tawakali mana komai fa na duniya mai wucewa ne wllh wataran sai labari batun yau ba nake cemiki *WANI JINKIRI* fa Alkhaire ne amma kinqi yarda da hakan sai kice ke maganganun mutane ke damunki toh shi zaisa Allah ya canza miki jarabawar daya rubutu akanki kome?

kosu mutanin su zasu kawo miki mijin?

bari kiji ingaya miki adda indai kikace zaki biye tamutane toh ko zaki kashe kanki a banza wllh,

yanzu wake ta mutane bakayi ba ma ance kayi bare to ka aikata, ay qiris kawai suke jira asaka abakin duniya,

ni abinda nakeso gareki yanzu “kifidda komai aranki kidibi abunda kafishsheki, kidage da addu’a wanda nasan kinayi muma muna iyakar qoqarin mu gurin roqon Allah, fatanmu kawai dai Allah ya za’ba miki miji nagari shine kawai fatan mu.

shiru tayi tana nazarin dik maganganun ‘yar uwar ta, tabbas tasan dik abunda tafada Gaskiya ne kuma tayi alkawarin yanzu zata cire komai aranta, zata kuma toshe kunnen ta daga saurarin dik zantukan mutane na banza, zata koma yin rayuwar ta tamkar ta da insha Allah.

kallon Dija tayi cikin kulawa da so tace haqiqa dikkan maganganunki Gaskiya ne kuma insha Allah yau komai yazo qarshe bazan qara damar da kaina ba bare na zubda kwallah har nabata muka rai keda umma ba, tabbas dik abunda kaga Allah yayi akanka shine dai dai mai yuwa idan nayi aure da wure ba Alkairi bane gareni shiyasa hakan ta kasance, tohhh Allah dai yasa mudace.

Ameen Adda *SAFFEAH* abunda nakeson kigane kenan”wllh namatuqar jin dadi da jin wa’annan kalaman da suka fito daga bakin ki, kuma nasan matuqar kikayi hakan Umman mu ba qaramin dadi zataji ba,

Yanzu bari natashi naje naqarasa aykin da nake kafin Umma tadawo.

Au..daman wai umma tafita ne?

Safeena ta tambaya, ehh tafita tindazu Dija tabata amsa.

Allah yamai data lapiya, mekike dafa manane yau?

Wllh Alalen gwangwani ce nake da mai da yaji kinsan fa yau juma’ah

sosai safeena tayi murmushi harsai da kyakyawan haqoranta masu matuqar haske suka bayyana cike da jin dadi tace kai amma wllh sister naji dadin wannan alalen da akayi yau ina matuqar son ta Allah,

Itama Dijah cikin dariya tace sanin hakan da nariga da nayine, yasa nazage dantse nashirya ta, yanda zakiji dadin ta sosai.

Rugume junasu sukayi cike da kaunar juna suna murmushi, kafin Dija tazare jikin ta tafita,

Etama safeena meqewar tayi tafara cire kayan jikin ta dan shiga gurin wanka.

Wannan Kenan…
[7/11, 11:08 PM] tannee Alkalancy: 🍃🍃🌹🌹
🍃🍃🌹🌹

🌹🌹🍃🍃 🌹🌹🍃🍃

_*WANI JINKIRI…*_

*Written by* ✍🏻

*Sa’adat Alkali D/tsafe*

*🌈KAINUWA WRITES ASSOCIATION*🤝🏻📚📚

*K̉ẻ t̉ảw̉ảc̉ẻ t̉ả h̉ảr̉ Ả̉b̉ảd̉a, ̉ Ảỷs̉h̉ả h̉ủm̉ảỉr̉a, ̉ Ảl̉l̉ảh̉ ỷảd̉ảủk̉ảk̉ả d̉ảr̉ảj̉ảr̉ s̉ủn̉ản̉ ảỉs̉h̉ả f̉ẻỷẻ d̉ản̉ả k̉ỏw̉ản̉ẻ s̉ủn̉ản̉ m̉ảc̉ẻ ả d̉ủn̉ỉỷả, h̉ảk̉ả n̉ảk̉ẻ r̉ỏq̉ỏn̉ ảl̉l̉ảh̉ ỷảd̉ảủk̉ảk̉ả d̉ảr̉ảj̉ảr̉ t̉ảw̉ả ảỉs̉h̉ả ả d̉ủn̉ỉỷả f̉ẻỷẻ d̉ả d̉ảủk̉ảk̉ảr̉ d̉ả ỷảỷỉw̉ả s̉ảủr̉ản̉ m̉ảt̉ả,* I͎N͎A͎ M͎A͎T͎U͎K͎’A͎R͎ S͎O͎N͎K͎I💘😔

💞 *MིRིSི MིAིKིAིMིA*ི💞 🌹🌹

🍀☺🍀☺🍀☺
I LOVE♥ YOUR
╔╗╔╦╗╦ ╦  ╦═╗
╚╗║║║║ ║  ╠╣
╚╝╝╝╝╩ ╩╝╩═╝
😄🎀😄🎀😄🎀

 

*(3)*

Wani tsaddadin guy ne nahango yana saukowa a hankali kan matattakala zuwa qasa, hannusa riqe da wani haddadin cup hannusa daya kuma yanaga kunnesa alamar waya yake amsawa sanye yake cikin wasu qananin kaya da sushi m matuqar karbar lallausar fatar jikinshi,

Yayinda security’s biyu ke dafama bayansa cike da aji yake takowa har allah yasa dashi da shiga cikin wani tangamemen parlor daya amsa sunansa,

har yasamu guri ya zauna vai daina wayar da yake ba, qafarsa ya daura kan d’aya yana kur6an lemon dake riqe a hannusa,

Manyan mutanene kusan su biyar suke zaman jiransa kowaninsa kallo daya zaka masa idanunka zai tabbatar maka naira ta zauna ajikin su.

Shiru kakeji parlou yayi hatta da wanda ke wayar bakajin abunda yake fada.

Saida yashare kusan 10mnt sannan can na iya jiyo kalmarsa ta qarshe da yake cewa me too my sweet mom😘 sannan naga ya dauke wayar a kunnesa

ahanali wani dayan security yamatso kusa dashi tare da ranqufawa gurin dai-dai saitin kunnesa yayi masa mgn wanda koni banji me yake fada ba,

Dai bayan daya naga wannnan security yaje gurin mutaninnan yana karba files dinsu kafin yakoma daya gefe yatsaya.

can dai daga cikinsu yayi gyaran murya cikin girmamawa yace” muna neman alfarma ranka yadade dan Allah da ataimaka mana abamu kwangilar nan dan allah👏🏻

gefe daya yamaida kansa kafin yakoma jiyo kansa gurinsu cikin taushin murya yace musu insha allah karku damu, kuna iya tafiya, daga haka yamiqe yanufe sama cike da takonsa.

 

*AིྀDིྀAིྀMིྀAིྀWིྀAིྀ*

Su safeena sun isa garin adamawa lafiya sun sauka gidan waning babansu mallam sule, mallan sule babban malamine danshi ke bada sallah anan cikin unguwarsu yanada mata biyu kuma kowaccin ta tanada yara uwar gida fadima tanada yara takwas biyar maza hudu mata, lubabatu kuwa tanada yara shida biyu maza mata hudu, gidane babban gida wanda dika iyalin gidan nacikin gidan annan suka ajiye iyalinsu,

Gidan gwanin shawa da birgewa zamane wanda babu kissa acikinsa daga uwayin har ‘ya’yan koda su safeena suka sauka gidan baqaramar tarba aka musu ba, saboda sosai akaji dadin xuwansu, dan kwananan ma aka yanki shawarar zuwa kaimusu ziyara sai gasu sunzo da kansu.

Su jidda kam da zalifa da ikram da najwa. ba wanda yakaisu jin dadin zuwan su safeena

Saboda jidda da zalifa sune tsaran safeena, ikram kuma da najwa sune tsaran Dija shiyasa kusan kansu yaxo daya, wannan kenan…

 

*WྂAྂNྂEྂNྂEྂ SྂAྂIྂFྂ…?*
***********

Saif dane ga shahararin dan kwangilar nan kuma d’an kasuwa Alhaji Ahamad Baseera,

Alhaji Ahamad Nazeer yayi suna matuqa aduniy fiye da yanda ake tunani, Alhaji Ahmad yanada mata daya Hajiya Asma’u macce mai gadara da nuna isa tana matuqar son jin dadi a rayuwar ta, Saif shine danta na ukku aduniya kafinshi akwai mata biyu aunty sadiya da aunty meena dik sunyi aure harda ma yaransu kuma dik manyan jigajigan masu kudin Nigeria ne suke aure, sannan shi SAIF bayanshi sai qanisa mai binsa uzaif bayan uzaif akwai mata biyu nadiya da nafisat” nafeeaat itace auta dik cikinsu ba wanda ya gado halin mamy su sai Nadiya, nadeeya sosai halinsu daya da mamy, na qyamar talaka kokadan basasun yara6esu akwai son nuna qarya da nuna cewa su wasu ne.

Saif tsaddadin yaro matashi mai aji yanada kyau naban mamaki baya da hayaniya kokadan kuma baya da buqatar amasa, miskiline shi sosai wanda saikaji jiki kafin kasamu irinsa

baya da ra’ayin ko wace mace a yanzu, yafi maida hankalinsa gurin harkokinsa dana mahifinsa kwatakwata shi bama zaunin qasarmu bane Nigeria, yafi buqatar kullum yana waje rashin son hayaniya kumq bayason takura da yawan surutu mutunne shi d’an hutu

Ko yanzu mahaifiyarshi ce takirash suke magana akan lallai yadawo dan zasuyi tafiya adamawa ita dashi dan tanason yaje yaga ‘yar governor adawama ‘yar qawarta dansu dai dai ta, bayanda zaiyi ne kawai shi yasa yakar6a mata saboda shi yarone mai matuqar biyayya ga iyayin sa…

 

“`Yanzu labarin zai fara… “`

love u💋 all my fans💕😘
[7/11, 11:08 PM] tannee Alkalancy: 🍃🍃🌹🌹
🍃🍃🌹🌹

🌹🌹🍃🍃 🌹🌹🍃🍃

_*WANI JINKIRI…*_

*Written by* ✍🏻

*Sa’adat Alkali D/tsafe*

*🌈KAINUWA WRITES ASSOCIATION*🤝🏻📚📚

 

SAKO GAREKI MARUBUCIYR WANI JINKIRIN

*Naga saqonki na kumaji amma dauka bai zaman man dole ba, nasani dik abunda kake sai kaga wani qalubale aciki abinda kika fada dubunki sunfada akan marubuta, toh kisani bazan canja sunan book dina akanki ba kuma bazan daina yinsa ba, wannan tatsuniyar munsha jinta amma kisani ninasan kaina dan haka banda wannan time yanzu inada abubuwanyi agabana kema kiji danaki*
🤝🏻😊

 

*(4)*

Tafiya suke cike da nishadi suna raha kai daga ganin su suna cikin farin ciki su shida ne dukan su, tafiyarsu suke cikin wani layi na masu kudi kasancewar unguwar shiru shiru ne yasasu tafiya yanda sukaga dama dik wannan rakiyar ta Zalifa ce tazone gurin wata qawarta da sukayi scol daya suka kawo mata ziyara yau gaba dayan su,

a kullum cikin yiwa zalifa qorafin qin zuwa gidansu summy take, ita kuma zalifa bawai batason zuwa bane a.. a sai dan batason shige matane dan gudun wulaqanci dikda tasan summy ba haka take ba,

sallama sukeyi da su summy wacce tarako su tare da musu godiya da nuna jin dadin ta, ta wannan ziyarar da suka kawo mata.

Can suka fara jiyo jiniya tashigo cikin layin🚔🚔🚔

Tsayawa sukayi dan ganin masu wucewa ikram ce tace cikin saure munbani koxo mutafi kada ‘yan sanda nan sutafi damu, dik da kowace hankalinta nakan kwana da motocin zasu bullo bai hanasu darawa ba,

summy ce tace lallai sis ikram a kwaiki da abun dariya tohh kuma aka cemiki shikenan da ‘yan sanda sunga mutun sai suhau kame ko?😅

Kwantar da hankalinki wannan abun da kikeji bai wuce ‘yar gwamna garin nan ce tazo kawo ziyara gidan qanwar mahaifiyar ta daman tana zuwa, saboda ‘yan uwanta, amma wllh abunda nakeso daku karku kuskura ku kusance layin kubari tafara wucewa ko motoncin kada kukallah dik da ido ba’a masu shamaki, amma ku daure kudaukesu daga motocin da zasu shigowanan dan wlh mamallakiyar su batada mutunci kokadan tanada gadara da isa da nuna ubanta governor ne,

Najwa ce tace ay wllh aunty summy ba abunda bamu sani gameda marar kunyar……. Mgnr ta talaqene sakamakon danniwar motocin cikin layin da suke tsaye, adai dai lokacin da sunka kusanto su, akuma dai dai lokacin da wata mage tafito daga cikin wani gida tabiyo kan titi zata wuce,

Safeeena batayi wata wata ba ganin za’a taka wannan magen ana gani tayi saurin zuwa ceton ranta.

Qoooo….. Take motocin sukaja wani erin Brake. Qutttttttttt..

Sai da kan Hanifa yayi gaba yayi baya gaba daya drink din da take riqe dashi ya6ata mata wankan da tayi,

Kutt tashin hankali wanda ba’asa masa rana🤢

Gaba daya securities din dake cikin mota suka fito kankace me sunke waye Safeena suna huci ko wannin su fuskarsa tamkar baqin kumurci, rasa tayi yazatayi gata riqe da mage kawai sai tasake mage jikin safeena yahau rawa muryar ta narawa tace dan Allah kuyi haquri wllh bada gangan nayi ba.

Wace ‘yar iska jaka ce taso kasheni kwanana basu qare ba, safeena ta tsinkayo muryar Hanifa wacce qanqanin lokaci suka buda mata hanya ta bayyana gaba gareta

ke dabbace koke sakarya ce da kina ganin motoci zasu wuce zaki karawa mutane a hanya kesan kowacece ni agarin nan da har kika za6e ki halaka rayuwata akan ki cece ta mace wllh natsaneki banza sakarya wacce batasan menene muhimmanci rai ba.

cikin qanqanin lokaci idanun safeena suka qanqanci jin erin zagin da ake surfa mata nafitar arziki, wani wulaqantaccin kallo ne tafara jifan Haneefa dashi kafin tace…

**********

Wani mahaukacin gidane naga ‘yan wangale get dinsa nan take wasu shahararrun motoci suka fara dannawa cikin gidan, gidane wanda bayada ko lissafi sunyi tafiya mai dan nisa kafin su shiga get din dazai sadasu da harabar filin gidan wanda cike yake da shuke shuke na alfarma abin ba’a cewa komai qaryane na iya lissafa muku abunda ke cikin gidan amma ku kwatanta da kanku zaifi. 😇

Mamy ce nafara hangowa tadosu motocin bayan sunsame guri sunyi parking sai faman murmushi take tamkar anmata bushara da Aljanna, suma su huzaif bayanta sukabi suna mai farin cikin dawowar dan uwan su.

tinkafin yafito mamy ta sanya kanta cikin mota tare da riqo hannun sa suka fito tare, nan take wani sansanyar qamshi yamamayi gurin mai taba zuciya😜

A hankali suke tafiya shida mamyn sa har suka isa cikin wani babban parlou

Numfasawa Nafeesat tayi kafin tace a gaskiya sis nadeeya brother Saif yanada matuqar kyau kinga fatarsa har wani yellow tayi gawani sihirtaccin kyau da allah yazu bamasa, uwa uba gashi dan gayu komai nasa mai kyaune wllh dik maccen da tasamu tsadaddin mutun kamar bro a gaskiya ita kam tagama sa’ar miji anan duniya☺

Cikin jin dadi nadeeya tayi wata dariya kafin tace gaskiya ne kam sis masha Allah, yaya saif kam Allah yabashi komai shi yasa qawaye na ke damuna da zancin sa,

Allah nima haka nafisat tace.

Wai gulmar me kuke kunbar mutane da yunwa Uzaif ne ke wannan mgnr yana daga bakin qofar parlou.

Cikin sauri suka qarasa suna dariya qasa qasa.
[7/11, 11:08 PM] tannee Alkalancy: [6/22, 7:53 AM] tannee Alkalancy: 🍃🍃🌹🌹
🍃🍃🌹🌹

🌹🌹🍃🍃 🌹🌹🍃🍃

_*WANI JINKIRI…*_

*Written by* ✍🏻

*Sa’adat Alkali D/tsafe*

*🌈KAINUWA WRITES ASSOCIATION*🤝🏻📚📚

🍃🍃🌹🌹

😅😅😅😅 _*wayyo a gaskiya kaina zai fashe,😇 wannan erin comment haka tinkafin ayi Nisa, tohhh ina godiya fa sosai🤝🏻*_

~______________________~

*(2)*

*WACECE SAFEENAH?*

Safeena ‘yace ga malam Lirwanu, itace ‘yarsu ta farko a duniya sannan Deja, tsakanin ta da Deja shekara biyu ne ba wata tsera atsakanin su dan kusan ma tsayinsu daya saboda Deja nada dan tsayi sosai kasancewar safeena gajiruwace yasa nan take Deja takai tsayin safeena,

sai qannin su tagwaye mace da namiji saleem da saleemat baza su wuce 10 years ba,

dik wannan maganganun da mutane suke yawanyi akan safeena ba wani girmane sosai tayi a gida ba dan duka duka bata wuce 22 years ba, Kawai tsabar sa ido ne da rashin aykin yi saboda sunga Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa, shekara biyar da suka wuce sakamakon hatsarin mota da yasamu daga Kano zuwa Kaduna,

ba wani qrfine malam lirwanu yake dashi ba, ‘yar sana’ar sai da gwanjo ce yake da itace Allah yarufa masa asiri yake daukar dawainiyar iyalinsa, cinsu shansu tufarsu har zuwa kan kudin makarantar su har suka kammala secondary scol dinsu, yana fafutukar sama musu kudin cigaba da karatunsu zuwa Jami’a Allah yayi mishi rasuwa.

Haka rayuwa ta canzawa su safeena yau dadi gobe akasin haka abubuwa suka taru suka musu yawa, gashi bamai taimaka musu kowa takansa yake, abinda zasuci ma wuya yake musu, sauqin ta dai gidan da suke ciki mallakin su ne,

a haka har Allah yakawo musu mafita suka sai da wata tinkiya da umman su ta siya, da dadewa suka dauke ta da ‘ya’yan ta Duka aka sai da.

tohh fa da kudin ne suke ‘yar sana’arsu ta hannu suke samun abunda sukaci.

Cikin taimakon ubangiji Allah yasama abunda suke sai dawa Albarka har umma taga bari takama sana’ar mijin ta ko Allah zai sa adace, haka kuwa akayi takama saro kayan gwanjo masu kyau tana sai dawa da haka suke rufawa junasu asiri ba wanda yasan halin da suke ciki…

*CIGABAN LABARI*

shirye shirye kawai su safeena suke ita da Deja da Alama tafiya zasuyi edan ka kalle fuskokin su qunshi suke da farin ciki, sungama shirya komai Deja ta shiga gurin wanka safeena na fitar musu kayan da zasu saka, umma ce tayi sallama tashigo cikin dakin gefen gado tasamu ta zauna kafin tacewa safeena harkun shirya Kenan?

cikin murmushi safeena tacewa umman su ehh wllh umma har mun shirya tintini ni harma nayi wankan Deja ce tashiga yanzu, wllh umma kokadan banaso muyi tafiyar dare ne shiyasa gara mutafi da wuri Adamawa akwai nisa sosai.

Hakane umma tafada ahankali kafin tace tohh ni har yanzu baku sanar dani ko yaushe Zaku dawo ba, ko ba rana?

wata kyakyawar dariya safeena tayi cikin ‘yar tsokana tace tohh umma mutun yaje garin mahaifinsa kam aysai yaga dama zai dawo gaskiya ba rana dan so muke mugana da ‘yanuwan mu sosai suganmu,mugansu kedai kawai sai kin gammu.

baki umma tariqe cikin mamaki tace ehhhh lallai sannuku masu dangi yo ay naga da mahaifin naku yarasu ba wanda yataimaka mana dako tsinke, kuma sunsan muna buqatar taimakonsu shine zaki wani cikani da zancin ‘yanwanku banaso cika baki, umma takai qarshin maganr ta murmushi dauke a fuskarta dan ko ita cikin tsokana tayi wannan maganar,

tabbb ayko wllh umma kiyi shirunki kawai dan koni gaskiya banji dadin abunda sukai mana ba, kawai dai dan kada muyada zumunci ne da bazanma koma taka qafata garinnan ba,

Deja ke wannan maganar wadda shigowarta daki kenan taji ana wannan chapter shine tayi saurin karbewa.

Ke waya sakaki kinsan fa banason haka ko? safeena tafada cikin dan shan mur” Allah yabaki haquri sarkin son dangi yi haquri tuba nake.

haka dai suka gama dik abunda suke suka fito tare da yiwa umman su sallama, tana mai musu fatan isa lapiya har suka bar layin gidansu suka same mai napep ya daukar musu kayansu sai tasha,
Acan tashar kuwa basu wani dadi ba dan bayan su mutun biyune kawai yarage ba kuma dade ba, motar tacika, suka dauke hanya sai dai muce su safeena Allah yasa a sauka lapiya..

***************

*NEW DELHI*🏢

Babban birnin dake cikin garin India, wani tamfatsetsen gida ne wanda bazai fadu na lissafa iya tsarin kyansa ba, gidane wanda ya amsa sunan sa gida,

Tako wace kusurwa da lungu securities ke tsaye a gurin kai daga ganin hakan kasan wanda ke cikin gidan ba qarami bane,

Kut-melesy wannan aljarnan Duniya haka abun ba’a cewa komai, masu karatu zansu ku biyune dan ganin shin wayene wanda ke cikin wanna gida haka…

Leave a Comment