Books Reviews & FAQs

Ummu Waheedah Hausa Novel

🎀🎀🎀🎀🎀 *UMMU WAHEEDAH*🎀🎀🎀🎀🎀
Paid Book #200

“`LABARINE DA YA SHAFE KALUBALEN RAYUWA, KUNCI, SOYYAYA, NADAMA, DA KUMA DARASIN RAYUWA“`

*Dan Allah idan kin san don ki fitar min da littafi zaki siya, toh ki bar kudinki, ki tuntube ni ta wannan number domin jin yanda zakiyi payment*

Daga Alkalamin✍️
MARYAM YUSUF UMMU JUWAIRIYYAH *{Sahibar Royal Star🪄}*

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

“`MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA’AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER’S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP“`

_🍂”ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU”🍂_

YAR FULANI, INA TAYI MURNAR KAMALLA WANNAN KATSAITACEN NOVEL DINKI MAI SUNA NDAIGOL AM (HAIHUWATA), UBANJIGI ALLAH YA KARA MIKI BASIRA DA HAZAKA, ALLAH YA CIGABA DA DAFA MIKI A DUKKAN LAMURANKI, AGASKIYA WANNAN LITTAFI NAKI, YA FADAKANTARWA, NAJI DADIN NOVEL DIN SOSAI FIYEDA TUNANIN MAI TUNANI, TABBAS YA CI SUNAN SHI, *NDAIGOL AM {HAIHUWA TA}* AGASKIYA HAIHUWA BAI YIWA MOMMY AMFANI BA😭 KASHHH! *SADEEY* ALLAH YA KARA DAUKAKA ALKALAMIN KI, ALLAH YA YI MIKI KAGANTAR KARFE TSAKANIN KI DA MAKIYAN KI, DA FATAN ZAKI NISHADANTAR DAMU A WANNAN SABON NOVEL DINKI MAI TAKEN *LAULAM {KISHIYATA}* FATAN ALKHAIRI YAR’UWA, KUMA ABBOKIYAR FADA A EDITING ROOM😝😂

The Experience Writer’s of:-
Amfanin Zumunci
Kaine Silah
Makauniyar Soyyaya
Amatu-Rahman Yar Baiwa
Illar Bakin iyaye
A Dalilin Kishi
Munaifatullah
Yar Commissioner
Prince Sapwan
Rayuwar makaranta {private school}
Doctor Rumaysa loading…..
And now UMMU WAHEEDAH

*Bismillahi Rahmani Raheem*

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai amincin Allah su kara tabbata ga fiyyayen hallita Annabin rahama, ya ALLAH yanda ka bani ikon fara wannan littafi nawa lpy, Allah kasa nagama lpy, ya ar-rahman kayi hani da hannu na wajen rubuta abunda bazai amfane al-umma ba, kuma ina rokon ka da ka bani ikon isar da abunda nakeson isarwa,

Typing📲
Free page
Episode 1to5

 

*NNAMDI AZIKIWE AIRPORT*
________________✍️Wata kyakyawar yarinya ce na hango tana saukowa daga mattatakalan jirgin da saukar su ke nan, ko minti biyu ba su yi ba,

Cikin shigar abaya red colour wace akayiwa ado da black stones ya yin da veil din abayan kuma black colour ne, sai da na kare mata kallo ta’s,

Subhanaka lahuma fatabarakallahu ahsanul khalkin shi ne kalmar da na furta a ya yin da nayi ido biyu da ita,

Waton yarinyar kyakyawa ce sosai ajin farko, fara ce ta’s hasken fatar ta har wani glowing ya ke,

Gata da ɗan siririn hanci circle face din ta mai dauƙe da ɗan ƙaramin pink lip, oily eye din ta kuwa dauƙe da zara-zaran gashin ido,

 

Ƙirjinta cike suke dam tamkar zasu fasa rigar abayar dake sanye a jikinta, gata da manya-mayan hips OMG, wannan idan aka kirata da Queen of beauty ba a yi ƙarya ba, domin kuwa kamar ma ta fi hakan,

 

Na tabbatar da koda ita ce ta yi kan ta, ba na jin za ta iya yiwa kanta irin wannan kyau da take da shi ba, ba namiji ba ko mace ta kalle ta,

 

To sai ta kara kalla domin kuwa kallo guda ba zai ishe ka ba, har sai ka kara kallon ta, da sauri wata kyakyawar ƙaramar yarinya mai ƙama da ita sak taje ta rungume ta,

 

Tana fadin “Oyoyo Aunty *WAHEEDA* barka da dawowa gida Nigeria da fatan kin sauka lafiya” zata kara magana ke nan wata matashiyar mata wace ba za ta haura shekara Ashrin da biyar ba aduniya ta dakatar da ita ta hanyar cewa,

 

“Haba Waleedah ki barta haka nan mana, ba ki ga duk ta kwaso gajiya bane? Bari idan muka koma gida sai ki cigaba daga inda kika tsaya, Waleedah dariya tayi ba tare da ta sake furta komai ba,

 

“Aunty shine Daddy bai zo dauka na ba daga ke sai Waleeda? Kuma me ya sa shima Yaya bai zo ba, ba cin duk sun san yau ne zan dawo, gaskiya ni banji dadi ba” ce war *UMMU WAHEEDA* tamkar zatayi kuka,

 

“Kiyi haƙuri ƴar gaban goshin Daddy ai kin san Daddy ba zai fasa zuwa tarɓon ki ba, sai da dalili, kawai kiyi haƙuri Daddy baya agarin su na da vital meeting a Gwarinfa yana can, shi yasa bai zo ba,

 

“To shi kuma Yaya Faruk fa?” “A’a WAHEEDAH stop questioning me like that, haba” WAHEEDAH murmurshi tayi tare da ce wa “Aunty yi haƙuri” ta manta da cewa Yayar ta ta ba ta da son surutu ko kaɗan,

 

A dai-dai wani babban gida mai matukar ƙyan gaske driver ya shiga danna horn, gidan ya haɗu iya haɗuwa, ƙai koda ganin gidan toh kasan gidan wani babban attajiri ne, wanda kudi sun zauna masa iya zaunuwa,

 

 

Wangale musu gate mai gadi yayi, gate din ka ɗai ma abin ƙallo ne, saboda haɗuwar gate din, idan ƴaran unguwa za su yi misali da giɗan, har cewa suke gida mai gate din zinari,

 

Ƙallon kalo suka shiga yi daga shi har ita, ya yin da tunani da take daban haka shima tunanin da yake daɓan, “ƙar dai ace gidan su ne nan, Allah ya sa ba yarinyar nan ne Alhaji yake masa maganar ta ba,

 

 

“Tabb! ashe ko akwai aiki babba, duk maganar zuci ne yake tayi, ya yin da itama ta lula duniyar tunani, “me wannan dan iskan yake agidanmu, da alama ma kamar gate man ne shi din” hanya kuwa wannan MUBASHIR ɗin da na sani ne kuwa, no impossible”

 

 

Wani irin wawan harara ta maka masa, kafin daga bisani tayi gaba abinta, Aunty Zahra kuwa tuni har ta shiga ciki, itama WAHEEDAH shiga parlourn tayi dauke da sallama a ɓakinta, wata ƙyaƙyawar mace na hango zaune saman lumtsuma-lumtsuman royal chair daƙe cikin ƙawataccen parlourn,

 

Da sauri *UMMU WAHEEDAH* taje ta rungume ta, tana “Fadin shi ke nan Mommy ke ba ki yi missing ɗina ba ko?” “Mommy murmurshi tayi tare da ce wa “Ni na isa na ce banyi missing din gudan-gudan auta na ba”

 

 

“Nayi missing dinki my dear da fatan kin sauka lafiya?” “Lafiya qlau Mom alhamdulillah, ashe Daddy baya a garin?” cewar WAHEEDAH, “E yana wajen meeting a Gwarinfa, cewar Mommy,

 

“E haka Aunty Zahra tace mun, “Mommy wai an canza muna gateman ne? Ina Ya Faruk? Shima bai zo airport ba, why? WAHEEDAH ta sake fada “Kin ga don Allah Auta ki tashi ki je ki yi wanka sai ki zo mu ci abinci kin ji?

 

 

“Karki damu da rashin zuwan Faruk airport, idan kuma kina son sanin me ya hana shi zuwa, to idan ya dawo kya tambaye shi, maza tashi kije kiyi abinda nace, cewar Mommy, “toh shikenan” WAHEEDAH ta fada tareda haura sama,

 

 

Wani karamin daki na ga ta shiga mai matukar kyan gaske, komai na dakin da pink color akayi ado dashi, kasancewar shi ne favorite color ɗinta, towel ta ɗauko ta shiga cire kayan jikinta, toilet ta shiga, wanka ta yi, ya yin da ta dauro alwala, kasancewar lokacin sallar azuhur ya yi,

 

Sai da ta bada farrilah sa’anan ta sauko kasa, abinci suka ci, daga bisani Waleedah ta fara magana, “Aunty WAHEEDA ai yanzu ba za ki koma London ba ko? Tunda kin riga da kin kammala karatun ki”

 

 

 

“E my daughter insha Allah na riga da na kammala karatuna, koda zan koma to ba yanzu ba, oh Walee kin zama big girl fa, sai shegen son surutu, dukkan su dariya su ka yi, ya yin da Aunty Zahra ta zuba musu ido ta na kallonsu, domin kuwa ita bata fiye son yawan magana ba, tun rasuwar mijin ta, ta koma wata kalar tausayi, ko kadan ba ta son yawan surutu.

 

 

“Mommy an jima fita zanyi” cewar WAHEEDA “zuwa ina kuma? Kin san dai Daddynku baya son yawon nan ko?” cewar Mommy tana jefe mata kallon kwarilla, “Mommy ba fa wajen yawo zan je ba, kawai shopping ne na ke son na yi,

 

 

“Kayana duk ba atamfa, shi ne na ke son na je na siya da kuma wasu abubuwan da ba ni da su, “Okay to, ai shi ke nan, Allah ya ƙai mu an jiman lafiya” cewar Mommy, “To ameen” cewar UMMU WAHEEDA,

 

 

“Ƙai! Mommy ta ce ka yi ka kai ni zuwa stop and shop, zan je na yi siyyaya a plaza ɗin, WAHEEDA ta faɗa ba tare da ta ƙalle shi ba, saboda wani irin mugun haushin sa ta ke ji, magana fa na ke, ko kuma kai din kurma ne? baka jin magana, iyeeee, kuma wallahi sai ka gaya min uban me ka ke a gidanmu, da kai na ke MUBASHIR, WAHEEDA ta fada ta na mai nu na shi da yatsa .

 

 

 

*UMMU WAHEEDA* is not for free, don Allah sis kar ki shiga hakkina👏, ki siya, sai ki sha karatun ki hankali kwance🥰 I promise ba zan yi disappointing dinku ba, ba za ki yi, dana sanin siyen book dina ba, insha Allah,

 

*Comment and Share Fisabilillah, Maryam Yusuf Ummu Juwairiyyah, SAHIBAR ROYAL STAR🪄 CE*

🎀🎀🎀🎀🎀 *UMMU WAHEEDAH*🎀🎀🎀🎀🎀
Paid Book #200

“`LABARINE DA YA SHAFE KALUBALEN RAYUWA, KUNCI, SOYYAYA, NADAMA, DA KUMA DARASIN RAYUWA“`

*Dan Allah idan kin san don ki fitar min da littafi zaki siya, toh ki bar kudinki, ki tuntube ni ta wannan number domin jin yanda zakiyi payment*

Daga Alkalamin✍️
MARYAM YUSUF UMMU JUWAIRIYYAH *{Sahibar Royal Star🪄}*

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

“`MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA’AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER’S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪
UP-UP-UP“`

_🍂”ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU”🍂_

The Experience Writer’s of:-
Amfanin Zumunci
Kaine Silah
Makauniyar Soyyaya
Amatu-Rahman Yar Baiwa
Illar Bakin iyaye
A Dalilin Kishi
Munaifatullah
Yar Commissioner
Prince Sapwan
Rayuwar makaranta {private school}
Doctor Rumaysa loading…..
And now UMMU WAHEEDAH

*Bismillahi Rahmani Raheem*

Typing📲
Free page
Episode 6to10

_____________”Kin ga Malama dakata, ni wallahi ba hauka zaki mun ba, kar ki ga lokacin da muna a school kina min rainin wayo ina kyale ki, idan kika min rashin mutunci anan zan shayar dake mamaki ne,

 

“Kar ki yi tunanin kina a gidanku, ki so ki min yanda ranki ke so, ki dinga gaya min magana yanda kika ga dama, ” cewar wanda naga ta kira da Mubashir,

 

“Kai! dan iska ya isa haka, idan…. “dakata wallahi idan ki ka kara kirana da dan iska, to zan nuna miki zallar iskanci anan kuma yanzun nan” cewar Mubashir,

 

“UMMU WAHEEDA fashewa ta yi da kuka, tareda ficcewa daga wurin, hanyar parlour ta nufa, Mommy ce zaune ta na kallon wani series film a mbc action, kawai ji tayi mutum ya fada saman jikin ta,

 

 

“Mommy wallahi ki yi wa wacan dan iskan magana, na rantse ya fita a idona na rufe, wai cewa ya yi zai yi iskanci da ni, tsabar ya na dan iska” ni gaskiya Mommy sai ya bar muna gidanmu, tunda dai ba na Ubansa bane ba, naga dai ba bu naira daya na Ubansa a ginin gidan nan,

 

 

Don haka ya zama dole ya bar min gidan Ubana, cewar WAHEEDA afusace “WAHEEDA me ya faru? ke da wa kuma? kin san dai bana son rashin kunya ko? kuma kar ki sake kiran kowa da dan iska, kin ji na gaya miki, wallahi last warning ke nan,

 

 

UMMU WAHEEDA kara fashewa ta yi da kuka, ya yin da ta nufe dakin ta, kuka ta shiga yi sosai mai cin rai, ita dai a tarihin rayuwa ta sha jin ana cewa ko wace yar auta a gidan su ana ji da ita, amma ita kam ba haka bane a nasu gidan, domin kuwa ko kadan Mommy bata ji da ita,

 

 

Gwanda ma shi Daddy a koda yaushe farin cikin ta ya ke so, sam baya kaunar abunda zai bata mata rai, amma awajen Mommy akasin haka ne, sai da ta yi kuka mai isarta, Waleeda tayi ta buga kofar dakin ta har ta gaji, amma UMMU WAHEEDA taki ta bude mata.

 

 

 

Mommy ma haka, amma bata bude mata ba, sai gab da isha ta bude kofar dakin nata, kuma hayaniyar mutane da ta dinga jiyowa a parlour ne yasa ta bude, don da dukkan alamu Daddy ne ya dawo, lekawa tayi ta window ai kuwa hashashen ta ya tabbata, domin kuwa Daddyn nata ne ya dowa daga Gwarinfa.

 

Saukowa ta yi kasa don su gaisa da Daddynta, dukkan ilahirin mutanen dakin ko kallo basu ishe ta ba, su Aunty Zahra ne zaune da Faruk sai Mubashir da ya shigo gaida Daddy sai Waleeda tana kwance saman kujerar mai zaman mutum biyu, sai Mommy tana gyara dining area,

 

 

 

Daddy kuwa zaune saman kujerar mai zaman mutum daya, da sauri UMMU WAHEEDA ta je ta rungume Daddyn nata, ta na kuka ta na fadin “Daddy don girman Allah kace ya bar muna gidan mu, wallahi! wallahi!! Daddy dan iska ne,

 

 

Na tsane shi, Daddy tun mu na school na san shi, Allah shi din ba mutumin arziki ba ne, wallahi Daddy dan shaye-shaye ne, yawo yake da matan banza, ba ya da mutumcin, ba ya da tarbiya ba shi da…..

 

 

 

Ai bata ida zancen ta ba, Mommy ta dauke ta da wani irin wawan mari har sai da ta daina ganin kowa na dakin, “Yanzu WAHEEDA ni zaki nuna wa duniya ban isa dake ba, ni zaki zubawa kasa a ido, ban hana ki cewa wani dan iska ba, cewar Mommy afusace, daman tun dazu take da takaicin ta.

 

 

 

Gaba dai Faruk ran shi ya yi bala’in baci, yana matukar son kanwar shi sosai da sosai, da sauri taje ta rungume shi, tana fadin “Ya Faruk na shiga uku na, Mommy ba ta so na, Allah da gaske nake shi din dan iska ne…….. Mommy sake daukan ta tayi da wani irin mahaukacin mari, na yanzu ya ma fi na dazu, don kuwa WAHEEDA kasa ta fadi sumamiya,

 

 

 

Babu ko alamar numfashi tattare da ita, Daddy wani irin wawan kallo ya dinga jefa wa Mommy tare da cewa “wallahi Asma’u idan wani abu ya faru da Mamana sai nayi shari’a da ke na rantse da wanda ya raina ya ke a hannunsa, Daddy ya fada tareda nuna ta da dan yatsa,

 

 

 

 

Aunty Zahra sosai ta dinga dizgar kuka tana ba wa Daddy hakuri, domin ita dai a rayuwar ta bata son hayaniya ko kadan, ta tsane duk wani abun tashin hankali, da sauri Ya Faruk ya je ya dauko goran ruwan faro a firijin watsa mata su ya yi a fuska, wani irin dogon ajiyar zuciya ta sauke, nan ta ke ta cigaba da rera kukan ta mara sauti,

 

 

 

Daddy ne ya ja ta zuwa dakin sa, shi kuwa Mubashir tun farkon marin da Mommy ta yi wa WAHEEDA ya ficce daga cikin dakin, Aunty Zahra kuwa hakuri ta dinga ba wa Mommy, ita dai tsawon zaman ta agidan bata taba ga bacin ran Mommy ba,

 

 

Sosai Daddy ya dinga bawa WAHEEDA hakuri, har ya samu ta dawo hayyancin ta, “Mamana me ya hada ki da Mubashir, tun da na dawo Mommynki ta dinga kawo min korafi akan wulakancin da ki ke masa, kin san ba dabiar gidan nan bane wulakanta dan Adam belle kuma talaka,

 

 

 

Sam kai ki fara, don ba daukan miki zan yi ba, talaka shi ma mutum ne kamar mu, sa bo da haka don Allah kar ki kasance mai wulakanta dan Adam ko shi waye, cewar Daddy, “To shi ke nan Daddy insha Allah zan kiyaye, amma ni ba wulakanta shi nayi ba, cewar UMMU WAHEEDA, “To haka nake son ji, kiyi hakuri zan yi wa Mommynki magana, kar ta sake dukan ki, je ki zuwa an jima akwai maganar da nake son nayi dake.

 

 

 

“To shi ke nan Daddy Allah ya kara nisan kwana” cewar WAHEEDA, “Ameen Mamana, an jima zan baki tsarabarki, kar ki bawa kowa, cewar Daddy, “To Daddy nagode” WAHEEDA ta fada dauke da murmurshi abakinta,

 

Leave a Comment