Batul Mamman
Wednesday, 1 June 2016
Batul Mamman at 03:42
TUN KAFIN AURE
TUN KAFIN AURE💐1
Motsi kadan sai ta daga labule ko zata ga shigowarsa amma shiru. Dawowa tayi falo ta shimfida abin sallah don tana gudun kada ya dawo ya shige daki bata sani ba. Tayi raka’a takwas duk biyu tayi sallama ta sake tashi ta daga leka wajen, wannan karon ruwa akeyi kamar da bakin kwarya tayi ajiyar zuciya…daya daga cikin lokutan amsar addua kenan sai ta koma kan abin sallar ta fara addua. Tana yi tana kuka bukatar tata bata wuce Allah Ya shirya mata Junaid ba. Jin alamar shigowar mota gidan yasa tayi saurin kashe fitilar falon ta koma gefe ta tsaya. Bata dade ba taji ya bude kofar a hankali ya shigo da sanda kamar wani barawo. Mamaki ne ya kamata yadda yake da key din kofar bayan ta rufe ta sannan ta kwashe duka keys din. Yana kokarin hawa sama ne yaji ta haske masa fuska da touch light din wayarta….wane dan kut….maganar ce ta makale a bakinsa ganinta a tsaye fuskar nan kamar bata taba dariya ba. Duk da a buge yake amma sai da gabansa ya fadi.
Saukowa yayi yace Mommy ina wuni…wunin uwarka Junaid? Nace wunin uwarka. Matsowa tayi ta cire hannu ta kwada masa mari har sau uku sannan ta koma ta zauna idanunta cike da hawaye.
Bai iya cewa komai ba don yasan bashi da gaskiya. Yana kallo tana masa kukan nan da ya tsana har cikin zuciyarsa yake jin abin. Mommy ya kira ta a hankali bata ko kulashi ba sai da tayi mai isarta ta tashi ta haska masa agogon bango. Karfe nawa yanzu ta tambayeshi. Hudu da minti ashirin ya bata amsa kansa a kasa. Mu je kayi wanka kawai tace masa. Ba musu ya hau sama tana bayansa yana tangadi amma yana iyaka kokarin dannewa wai kada tace ya sha wani abu. Suna zuwa kofar dakin tace idan kayi wanka kayi alwala ka sauko ina jiranka.
Daki ta wuce ta kalli maigidanta da yake ta uban minshari ta ja dogon tsaki. Ita kam kudi bai zamu musu komai ba sai silar watsewar tarbiyar yaronta. Allah Yasa ma yaran basu da yawa su uku ne. Babbar Nafisa tayi aure itama mai bin Junaid din
Hamida tana gidan mijinta. Shi kadai namiji ya zame mata jarabawa a gidan duniya. Mijinta Senator Rufai Bukar ya rike mukamai da dama har zuwa lokacin da ya fara siyasa yanzu haka karo na biyu kenan da aka sake zabarsa sanata. Ko kadan bashi da lokacin iyalinsa saboda tafiye tafiye idan yana kasar kuwa daga office sai bacci. Baya taba bincikar halin da yaransa ke ciki amma duk karshen wata zasu ji alert mai kauri a account dinsu. Gaba daya lalacewar tarbiyar Junaid bata gabansa. Alwala ta sake sannan ta tashe shi ya sauko suyi sallah a kasa tare da maaikatan gidan tunda ana ruwa.
A falon kasan ta tarar da shi yana nafila tace cikin takaici ko kunya baka ji ka gama aikin sabo ka zo ka tsaya gaban Allah kana neman biyan bukata. Masu aikata laifi bisa kuskure ma suna tsoron haduwa da Allah amma kai naka lamarin kana sane kake takewa. Alhaji dake saukowa daga bene a lokacin yace ni kuwa bana so yaro yana kokarin shiryuwa kina sagar masa da gwiwa… Alhaji kenan ta fada tana shimfida abin sallah wallahi ina dada baku shawara kai da Junaid kuji tsoron Allah. Akwai ranar kin dillaci ranar da dukiya bata da wani amfani. Daga mata hannu yayi to malama naji zan masa fada ince dai shikenan ko.
*********************
Hafsi! Hafsi!! Hafsi!!! Dagewa tayi ta sakar mata duka a baya. A gigice ta dago kai Ummati lafiya kika doke ni. Kujera ta jawo ta zauna kusa da aminiyarta, naga kin zurfafa a tunani ne. Tunda ansa rana ya kamata ki rage tunanin Saif haka. Ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a cikin randa. Ke ko tunanin exams kike? Nima da tawa ‘yar brain din ban tsorata ba sai ke. Ajiyar zuciya Hafsi tayi ta kalli kawarta Ummati wai kinsan ya mukayi da Saif kuwa jiya? Me ya faru ta tambaya cike da zumudi. Ita dai soyayyar Hafsi da Saif tana burge ta. kamar abin arziki ya nuna min hotunan wasu abokansa da sukayi da matan da zasu aura sai daga baya yace ai tunda ansa rana muma yana son muje muyi. Dadina dake sokonci kin manta mun taba hirar dake lokacin da muka ga na Aliya Yunusa duk muka ce muna so. Ke kanki kin yaba da kyan da suka yi. Gara da kika ce yabawa kinsan ko da wasa bazan iya tambayar Mama ba ma balle Baffa. Bazasu taba barina naje ba shiyasa ma na cire abin a raina, amma ina fada masa haka da fushi ya tashi rai a bace.
Ummati ta dafa kafadar Hafsi bari mu fito daga exam dinnan sai muyi shawara. Karatu suka cigaba har malamansu suka shigo ajin aka fara jarabawa.
Suna tsaye a bakin gate din makarantarsu Health Technology dake cikin birnin Kanon dabo. Ummati ta zunguri Hafsi tana waigowa ta danyi murmushin yake. Kana ganinta kasan tana cikin damuwa. Ke na samo mana mafita fa. Nan take hankalinta Hafsi ya kwanta har suka samu adaidaita sahu suka tafi gida.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 2
A tsakar gida ta tarar da mamanta tana dinki. Bayan sun gaisa Mama ta tambayetajarabawa. Alhamdulillah tayi sauki sosai. Hmmm kinji ki wai tayi sauki sosai to a bita da addua dai. In sha Allah ta bata amsa tare da shigewa daki. Tunani kawai take yi na yadda zata gabatar da plan din da suka yi da Ummati idan ba haka ba sai dai Saif yayi hakuri. Amma tasan halinsa sarai na fushi. Gado ta fada tana juyi. Idan akwai abinda ta tsana bai wuce fushin Saif dinta ba. Ina ma dai yayi hakuri har zuwa lokacin aurensu sai ayi kowanne hoto yake so ta fada a ranta.
Sauransu jarabawa uku su gama makarantar gaba daya sai dai har yau ta kasa fadawa Mama. Hafsi ta rasa me yake mata dadi domin kuwa daren jiya da Saif yazo baram baram suka rabu. A cewarsa bai taba tambayarta komai ba sai wannan ta gagara yi masa. Da bacin ransa tayi bacci ‘yar wayar daren ma da suke yi yaki kiranta da ta kira kuma yaki dauka.
Shewar Ummati ta jiyo tare da kannenta Amira da Anisa. Da sauri ta fito ta jawo hannunta suka koma daki. Ummati ta kalle ta to sarauniyar masoya yau kuma me ya faru? Tunda naji muryarki kamar zaki yi min kuka nasan an taba zuciyar. Ba kya ma tausayina wallahi naga abin har dariya yake baki. Plate din abincin da Hafsi ta zuba amma tunani yasa ta kasa ci shi Ummati ta dauka tana ci…bakinta cike da abinci tace bana tausayinki zan zo yau. Ai don nasan Baffa yana gida yau ba aiki ne ba bari zaiyi ki fito ba. Ni fada min me ya faru. Hafsi ta zauna kan dadduma tace akan zuwa daukan hoton nan ne fa. Kwarewa Ummati tayi tana kokarin yin magana. Amma dai ke anyi banza wallahi Hafsi, ina ce tun last week muka rufe zancen nan. Ajiye plate din tayi ta tashi ina zuwa…ganin zata fita Hafsi ta bita da gudu tsaya don Allah ina zaki. Ko sauraronta bata yi ba ta shige kitchen wurin mama. Mama kinga Hafsi ko…dago kanta tayi daga tsintar waken da take yi me tayi miki kuma ku da ba kwa rabo da fada. Wai nace mata ranar da muka gama exams tunda ta safe gare mu ranar tazo muje daukan hoto shine tace wai bazata ba. Mama tun shekaranjiya nake mata magana tana kin bani amsa shine nace bari nazo kawai na fada miki. Kun fiye shirme ke da yar uwar taki meye abin fada a nan. Kinsan halin Baffanku sarai baya son fice fice ba gaira babu dalili nasan abinda take tsoro kenan. Ummati wadda ta zauna a kasa tana taya ta tsintar waken tace Mama dama wai na tarihi nake son muyi ranar tunda kinga ni Bauchi zan….karasa mana bauchi zamu kaiki ko. Tashi tayi zata gudu Mama tace ba komai zan fada masa ranar da ku ka gama din sai kuje kuyi hoton shikenan ko. Nagode nagode nagode abinda ummati take ta fada kenan har ta fita daga kitchen din. Ita kuwa Mama dariya take sai dai bata san me yaran ke kullawa ba.
********************
Kwance yake kan makeken gadonsa yana zukar wata irin taba mai kauri da tsaho, bai ankara ba kawai sai ganinta ya yi a tsaye bakin gadon. Ah sis saukar yaushe…harara ta galla masa kafin ta fizge tabar. A jikin wandonsa ta kashe ta ai kuwa ba shiri yayi ihu tare da mikewa yana kokarin cire dogon wandon. Sis don mugunta sai ki kona ni me nayi miki kuma daga zuwanki. Ko da ya cire wandon saman gwiwarsa ya fara alamun tashi. Ta zauna ai kadan ma ka gani wutar can tafi wannan. Jin yanayin maganarta yasan mommy ta kai shi kara wurinta ne. Daure fuska yayi yace to idan kinzo ganewa idonki ne kinyi sa’ar gani sai ki fita….rayuwa kowa da tasa so please let me be. Duk ranar da na gaji ke zan fara sanarwa. Yana gama magana ya shige toilet tare da banko kofar da kafa daya. Har zuciyarta taji sautin ta mike a sanyaye. Zuwan Junaid America certificate kala kala ya samu banda na school harda na shaye shaye, neman mata da tsabar kin ji. Baya ganin kowa da gashi ciki kuwa harda mahaifin nasu da ya dage sai dansa yayi karatu mai tsada.
Dakin mommy ta shiga ta zauna a gefen gado tayi tagumi tana jira mommyn ta idar da sallah. Ya dai Nafisa kunyi magana da kanin naki. Hmm mommy ai lamarinsa sai addua kawai ta fada tana tabe baki. Nan ta labarta mata yadda suka yi. Mommy tace to ni dai na gaji zan sanar da Hajiyan Dangi halin da ake ciki kafin yaron nan ya dauko mana magana. Zaro idanu Nafisa tayi cikin tsoro tace Hajiyan Dangi….wai .
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 3
Cike da murna Hafsi ta kira Saif ta sanar da shi an bata izini a gida amma sai ta gama exams. Yayi matukar farinciki da jin hakan. Hafsi kyakkyawa ce ga kyan jiki. Tun farkon haduwarsu yayi ta fama da samarin da ke sonta kala kala Allah Ya taimake shi ta zabe shi kuma yayi saa mahaifinta bashi da wasa wurin sa ido akan lamuran ‘ya’yansa. Duk da kasancewarta ba fara ba saboda babanta mutumin maiduguri ne amma yanayin fatarta mai kyau ne kamar ‘yar hutu. Duk wanda ya kalle ta sai ya kara saboda haka Saif yake godewa Allah da wannan tsaleliyar budurwar take sonsa.
‘Yan ajinsu suna ta faman rokonta su tsaya ayi hoton tarihi ciki kuwa harda Ummati amma ita duk hankalinta yayi gaba. Gefe ta jawo kawar tata. Ummati wai kin manta da abinda ke gabanmu ne yau kin tsaya sai hira kike yi. To sarkin azarbabi ko dan jan aji ai kya yi masa yasan kema kina ji da haduwa. Ki bari muyi sallama da mutane cikin mutumci. Da kyar Hafsi ta bari sukayi hotuna sannan suka wuce gida. Cike da doki tayi wanka ta debo kayan sallarta da wasu kaya masu kyau har kala hudu ta zuba a leda. Tana cikin shiryawa Saif ya kirata. Tana dauka ya suma magana.
(Matar baku shirya bane? Na kusa karasowa gidanku fa)
Ji tayi gabanta ya fadi don bata fada masa da yadda aka barta ba. Kashe murya tayi cike da shagwaba.
( Saif kada ka zo please Baffa zaiyi fada. Ka jira mu a bayan layin su Ummati idan ka iso yanzu zan fito nima.)
(Ai duk yadda kika ce haka za’ayi matar. See you soon)
A gaggauce ta fito ta ce Mama zan je gidansu Ummati daga can zamu wuce. To Allah Ya kiyaye amma don Allah banda bude jiki gaban mai hoto. To kawai ta amsa tana sauri ta fita. Hafsa! Taji mama ta kira ta ….a hankali ta juyu tace baki karbi kudin hoton ba da kudin mota ko duk saurin ne. Da gudu gudu ta koma ciki ta karbi kudin tayi godiya sannan ta fita.
Tana zaune gaban motar Saif suna ta hira sai dai gaba daya ta kasa sakin jiki sosai saboda basu gama fita daga unguwarsu ba. Karshe dai fakewa tayi ta duba kasan takalminta ta sunkuyar da kanta har sai da taji sun hau titi sosai. A gaban wani sabon gidan hoto da ake ji dashi a kano Treasures suka tsaya. Zata bude kofa ta fita Saif yace haba matar ai nine mai bude miki kofa daga yau, tunda gashi nayi sa’a kin shiga motata. Ummati da ke baya tayi shewa lallai ma Saif wato ni ko oho. To Allah bazan fito ba sai nima wani cikin ku ya bude min ai nima ina da nawa rabin ran. Dariya duk suka yi sannan suka shige ciki. Zama suka yi a reception ya gama magana da receptionist sannan yayi joining dinsu kafin azo kansu. Wai Saif yau babu aiki ne ka fito yanzu? Matar kenan Lukman na bari ya kama min kafin mu gama. Dayake aikin sa kai ne ba. Da haka nan nace ka zo a wannan lokacin cewa zaka yi aiki aiki. Ledar hanunta ya kala yayi saurin dafe kai kinsan har na manta ba taho da kayan canjawa ba. Bata fuska tayi don Allah da gaske kake? Dariya yayi mata sannan yace ina son shagwabarki matar kinga yadda kika yi kyau kuwa…buga kafa tayi a kasa ni fa da gaske nake yi Saif….nima da gaske nake yi Hafsah ya kwaikwayeta. Zanyu kuka fa dariya yakeyi sosai sanan ya tashi ke wasa nake yi suna mota just give me a minute.
Bayan ya dawo suka shiga aka bar ummati tana jiransu idan an gama na masoya sai ayi na kawaye kamar yadda ta fada.
Suna shiga mai hoton ya ce da Hafsi cikin hausar da bata gama zama a bakinsa ba zaka yi cire wanan veil ko yana nuna mayafinta. Saif ta kalla da alamar tambaya yace ta cire akwai wanda zasuyi nan gaba da mayafin. Nan fa aka rinka hotuna kala kala…babu wanda jikinsu baya taba na juna tun Hafsi tana dan jin kunya har ta saki jikinta. Sunyi kusan kala goma suna canja kaya dama ga ta gwanar kwalliya da daurin dankwali. Mai hoto yace da Saif, Alaji ba zakiyi na english wears ba amarya? Dariya Hafsi tayi tace kaji min mutum baza muyi ba. Saif yace ni nayi tunanin zaki zo dasu fa matar. Juya masa idanu tayi mai hoto yana kallonsu wannan sai bayan biki. To na yarda ya amsa mata sai tana shirin daukan mayafinta sai kawai taji saif ya cire mata dankwali ya kuma fizge mayafin ki dan baza gashinki sai muyi a haka a madadin kananan kayan tunda naga wannan rigar ta kama ki yadda yake maganar wani kasa kasa. Daure fuska tayi sosai Saif meye haka ya zaayi nayi hoto a haka. Ita saboda ma yanayin rigar bata yadda sunyi hoto da kayan ba mayafi ba. Fitted gown ce a jikinta wadda ta bude daga kasa. Saman kuwa ya kama mata kirji sosai gashi gaban yana da dan zurfi ana ganin saman kirjinta.
Shi kanshi Saif ya kadu da ganin surarta banda mai hoto da yake gefe yana ganin bati. Please matar ko daya ne ki bari muyi please, please. Bata son bata masa rai amma ba karamin haushi taji ba. A haka ta bari aka yi guda daya da kyar ta tsaya gabansa bayanta a jikin kirjinsa ya sakalo hannuwansa duka biyu ya ta gaban cikinta. Wani irin yanayi duka suka tsinci kansu shi da kansa yace ya isa guda dayan.
Da rashin fara’ar nan aka dauke su tare da Ummati wanda zasu nuna a gida. Bayan an wanke musu ya bada wayarsa aka tura masa. Ita Hafsi dama tata wayar ba wata mai tsada bace tace bata so. Wanda aka wanke ma cewa tayi ya rike duka a wajensa. Ganin duk ta bata rai bayan sun shiga mota yace Ummati ta bata hakuri. Ko da ummati taga dalilin fushin duka ta kai mata a baya shegiya Hafsi irin wannan pose haka ko ni da Lawal bamuyi irinsa ba. Hawayen da take kokarin boyewa ne suka sakko ba shiri. Saif na gani ya tsaya da ribas din da yake shirin yi da mota…. matar don Allah kiyi hakuri nima sai da nace muyi abin duk ya dameni. Bani da niyar wulakanta ki, ummati ki sa baki mana. Haka suka yi ta bata hakuri har ta dena kukan amma a zuciyarta ba karamin tsanar kanta tayi ba da ta biye masa irin wannan runguma haka kamar an shafa fatiha. Ga wani bakon feelings da takeji tunda ta hada jiki da Saif abinda ko hannunta bai taba rikewa ba. Anya tayi wa kanta adalci kuwa. Da wannan tambayar a ranta suka isa unguwarsu.
Kamar yadda suka tafi yanzu ma a bayan layi suka sauka. Haka ta shiga gida sukuku kannenta suka karbi hotunan da tayi da Ummati suna gani. Baffa ne ya kula da yanayinta Hafsa me ya faru ne duk kinyi wani iri. Kago murmushi tayi Baffa kaina ke ciwo. Daki ya shiga ya samo mata magani Mama tace sannu ai abin ne da yawa ga karatu, kinyi jarabawa sannan kuma baki huta ba kin sake fita. Ai zan baki hutun kwana biyu kafin ki cigaba da tayani dinki kinga sun taro. Baffa ya harareta nifa na gaji duk kin mayar min da yara teloli. Kowa dariya yayi harda Hafsi da ta kakalo ta dole.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 4
A hankali yake tuki kamar yana tausayin kasa. Fitsararrun matasan Abuja ne suka cika wurin maza da mata wanda abin takaici ‘ya’yan musulmi ne mafiya yawan cikinsu. Kallo ne ya koma kan hadaddiyar motar da ya shigo da ita tun kafin a gane waye a ciki. Wuri ya samu yayi parking yana fitowa aka fara ihu da tafi
Juni! Juni!! Juni!!!
Junaid ji yayi kansa ya kara fashewa. Sanye yake da wani matsatstsen jeans baki da bakin takalmi mai kyau. Farar riga ce a jikinsa mai dogon hannu amma bai balle maballi ko daya ba ana ganin bakar singlet din da yayi zanzaro da ita. Hannunsa wani agogo ne mai tsada ga bandana ya daura a kansa wanda ya tara gashi ya aski gefen hagu da dama. Kana ganinsa kaga yaron da ke ji da kudi, kyau da tsabar rashin tarbiya ko rashin sanin ciwon kai.
Junaid Rufai Bukar kenan dan senate president din Nigeria wanda yake fantamawa son ransa saboda kudi da kuruciya da ke cinsa.
Tun shigowarsa harabar club din take kallonsa kamar tsohuwar mayyar da ta kwana da yunwa. Tana son namiji mai kyau a rayuwarta gashi tun da ta fara zuwa club din bata taba ganinsa ba. Yana ta gaisawa da maza da mata tana binsa da ido har ya shige ciki. Itama binsa tayi ta sami wuri a gefe ta zauna don matan da sukayi kansa suna da yawa. Sai da taga an fara rawa ta je kusa da shi suka gaisa. Amma ke bakuwa ce ko ya tambaya yana mika mata cup cike da juice wanda aka sirka da kayan maye. Yes ta bashi amsa. Matar ta hadu don ba ya kirata yarinya ba, yasan da kyar idan bata girme shi ba. My name is Tilly beauty…sunan ya dace da ke kuwa. Ni suna na Junaid. Hmm amma naji ana kiranka Juni. Cire glasses dinsa ya yi kana mata wani shuumin kallo Juni friends dina ke kirana. Nima ina son zama daya daga cikinsu. Then you can call me Juni. Haka hira ta balle tsakaninsu karshe da suka fara buguwa da kyar suka karasa daya daga cikin dakunan da ake bayarwa haya a cikin club din.
Ganin baccinsa yayi nisa ta dauki kayanta ta saka ta kare masa kallo gaskiya Juni yana da kyau ga kudi…just what she needed. Takarda ta samu ta rubuta sunanta da phone number ta ajiye masa sannan ta fita. A waje ta hadu da kawarta Rosie suna haduwa suka tafa. Aiki yayi kyau Rosie sai munji daga gareshi. Shegiya Tilly baki da kyau fa Rosie ta fada tana dariya.
*******************
Da kyar ta samu Baffa ya barta taje gidan yayarta Hadiza kwana uku bayan ta gama exams. Suna kitchen sai hira suke yi Saif ya kira Hafsi a waya. Tashi tayi ta koma daki Hadiza tana ta yi mata tsiyar ta gudu kada aji hirarsu.
Kan gado ta kwanta sannan ta amsa wayar.
(Hello matar kin wuni lafiya?)
(Lafiya kalau ya aiki?)
(Ba dadi gaskiya. Ni missing dinki nake yi sosai yau.)
Yar dariya tayi domin itama kwana ukun da basu hadu ba tun ranar da suka je daukan hoto bata ji dadi ba. Babu abinda yafi damunta kamar yadda ta kwadaitu da son sake jin ya taba ko da hannunta ne. Ya Allah Ka kara tsare mana imaninmu.
(Ina gidan Yaya yanzu amma anjima bayan laasar zan tafi.)
dadi yaji har ransa domin kamar yadda take son kasancewa tare dashi abin yafi daga wurinsa. Karshe dai yace zaizo ya dauketa.
Bayan ta idar da sallah ta zauna gaban mudubi fuskar nan tasha fenti. Hadiza ta kalleta Hafsi amma dai kinsan bai kamata ki fita da irin wannan adon kan titi ba ko. Saurin mikewa tayi to yi hakuri Yaya na yau ne kawai nayi shaawa. Saif na zuwa yayi mata waya tayi sallama da yayarta wadda har kudin mota ta kara mata. Tana rufe gate din gidan ta tsaya ta feshe jikinta da turare mai kamshi abinda bata saba ba domin tasan rashin dacewar mace ta tsaya gaban saurayi tana kamshi irin wannan banda zunubi a addinance. Sai dai ita kanta ta rasa gane dalilinta na yin hakan. Annabi SAW yayi gaskiya da ya fada mana cewa shaidan yana gudu a jikin mutum kamar yadda jini yake gudu. Shi aikin sabo da kadan muke farawa sai a hankali ya zame mana jiki. Mu kiyaye don Allah da yadda muke langabewa jikin maza ayi hoto wai da sunan pre-wedding pictures. ‘Yar uwa idan baki aure shi ba meye makomar rungume rungumen da ku ka yi duk da sunan wayewa?
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐5
A mota Hafsi ta sami Saif yana jiranta. Tana shiga wani kamshi mai dadi ya bakunci hancinta tare da sanyin AC. A kunyace ta zauna tare da gaishe shi. Matar kinyi kyau sosai ga kamshi mai dadi da kike yi. Fari tayi masa da ido har na kai ka kamshi Saif? Har kin fini ya bata amsa yana dariya.
Yana tuki suna hira bata ankara ba taji ya kama mata hannu ya dora akan gear ya hada ya rike. Tana kokarin kwacewa ya matar kina son muyi accident ne kike neman canza min gear? Cikin muryar shagwabar da ta saba magana tace da hannuna fa ka hada Saif. Au hannunki ne ma ba nawa ba. Naka ne mana amma ba’a gama baka ba sai an daura aure. Ku mata komai sai an daura aure ne? Ko kin manta ansa mana rana. Ai yanzu abinda ya rage tsakaninmu kadan ne.
Suna shiga unguwar ta fada masa su bi ta bayan layinsu Ummati sai ta sauka. Ba musu layin suka shiga da yake a tsuke yake ba mutane sosai. A nan Saif ya sami damar kebewa da Hafsi don a gidansu akwai idon jama’a. Rikota yayi ya hanata fita….matar ni fa duk kin rikita min lissafi tun ranar saturday da muka yi hoto. To yanzu me kake so ayi. Wayarsa ya dauko yana nuna mata pictures din. Hafsi ta sami tarbiya daidai gwargwado kuma shima Saif din ya fito ne daga gidan mutumci sai dai koyi da tarbiyar nasara yasa idanunsu ke neman rufewa. Ganin hotunan yasa suka fara shiga wani yanayi. Yadda ya riketa kamar ba zai saketa ba yana kokarin hada bakinsa da nata itama kuma bata yi yunkurin hana shi ba.
Tun shigowarsu layin Mal Aminu ya gane motar sai dai bai gane yarinyar da ke gaba ba saboda yadda take ta kokarin rufe fuskarta. Ganin motar ta shige wata kwanar ba hanyar gidansa ba yasa yayi mamaki kamar ya wuce sai yaga anyi parking dinta a karkashin bishiyar darbejiya shiru ba’a bude kofa ba. Karasawa yayi ya tambayeshi gidan wa yake nema tunda dai a iya saninsa gidansa yake zuwa a unguwar.
Jin ya fara kissing dinta jikinta yayi sanyi hankalinta gaba daya ya tashi. Ashe akwai ranar da zata aikata irin abinda take ji a labari tana ganin bakin masu aikatawa. Wai a zamanin yanzu a haka ne kawai masoya zasu nunawa junansu kauna. Wazu hawaye taji sun zubo mata. Hankalin Saif ya tashi…matar kiyi hakuri wallahi rudin shaidan ne amma bani da mugun nufi a kanki. Yana cikin share mata hawaye suka ji an bude kofar gefen da take zaune…..idanu ta bude a tsorace ganin waye a tsaye cikin rawar murya tace BAFFA!.
*******************
Yau ma a cikin maye ya shigo gidan anyi sa’a ma wurin shabiyu da rabi na dare ya shigo. Fito ya shigo yana yi yana karkada keys din hannunsa. Kamar daga sama yaji kira…Junaidu….ba don namiji bane da gabansa sai ya fado kasa yadda ya mugun tsorata. Cak ya tsaya kamar gunki. Don ubanka juyu ka kalleni. Mommy da ke zaune a gefe shiru tayi. Babu wanda baya tsoron Hajiya Ramatu. A kano take aure a gyadigyadi wurin da aka fi sani da dangi, shiyasa ma ake kiranta da Hajiyan Dangi.
Tsawa ta daka masa bazaka zo ba ne. A hankali ya dawo ya zauna a kan kafet. Hajiyan Dangi doguwar macece kamar mahaifisu ga jiki. Ita kadai ce mace a gidansu kuma ita ce babba. Allah bai bata haihuwa ba sai dai ta rike yara da yawa daga danginta har na mijinta. Cikinsu harda Senator Rufai kaninta. Mace ce mai riko da addini kuma mai sa ido akan tarbiya. Yanzu Junaidu wannan wannan rayuwar ka daukarwa kanka? Tana magana ta soma hawaye gidan malamai manyan mutane muka fito amma saboda giyar kudi na dibanka kana neman lalata rayuwarka. Ta kalli Mommy yanzu sai da lamarin ya baci haka kika sanar dani. Mommy dai hakuri ta ba ta. Bandanan kansa Hajiyan dangi ta fizge. Gobe kaje ka aske wannan shegen kan kuma kazo ka nuna min. Ko ci kanka bai ce mata ba haka ya tashi ya basu wuri. Yana shiga daki tabarsa ya kunna ya fara busa hayaki kai ka ce bakinsa salansar mota ne. A haka Junaid ya tuna bai yi sallar laasar, magriba da isha ba. Tsaki ya ja tare da mikewa ya nufi toilet. Haka ya yi alwala irin yadda kwakwalwarsa ta karanta masa sannan yazo ya fara ramuwar sallolin da bai ma san abinda yake karantawa ba.
A dakin da take sauka kuwa Hajiyan Dangi ce ta yanke shawarar ba zata koma kano ba sai kaninta Rufai ya dawo daga Australia sunyi magana akan Junaid. Babu abinda taki jini kamar yaro yaki ya rinka keta dokokin Allah ba tare da an dauki mataki akansa ba.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐6
Jikinta ne ya hau bari kamar wadda akayiwa wanka da ruwan sanyi a watan december. Iya karfinta ta sa ta fito daga motar har tana ture baffan nata. Da gudu ta tafi gida kafarta ko takalmi babu. Saif kasa motsi yayi a cikin motar ya sunkuyar da kansa. Baffa bai ce masa komai ba ya juya ya nufi gidansa.
Yadda ta shigo a firgice yasa Mama saurin tashi. Hafsa lafiyarki? Me ya faru? Me ya sami yayarki? Ko daya cikin tambayoyin bata amsa ba durkusawa kawai tayi a gabanta tana kuka. Amira ce ta kula da kafarta ta dama tana jini. Mama kinga kafar Hafsi jini take yi. Subhanallahi ke ko hatsari ku ka yi a hanya ne? Ana magana kinyi shiru kamar wata bebiya. Cikin Hafsi har wata kara yayi da jin sallamar Baffa. Bai jira an amsa ba yaja hannun Hafsi zuwa dakinsa. Garammm ya banko kofar har gaban su Mama ya fadi. Ihun Hafsi kawai suka ji tana bawa Baffa hakuri. Tuni Mama ta karasa bakin kofar dakin tana bugawa. Su Amira kuwa sai kuka don tun suna jin kukanta har murya ta dashe. Babu irin magiyar da Mama bata yi masa ba amma yaki budewa.
Baffa ya bude kofa Hafsi na kwance a kasa Mama ta shiga dakin hankali a tashe. Baffan yara me ya faru…ke Hafsa me kika yi? Da kyar Baffa ya iya fada mata tana ta kuka. Ita kam Hafsi hawayenta ba na zafin duka bane kawai. A yau tayi dana sanin abinda ta aikata. Tayi Allah wadarai da maza da matan da basa jin komai lokacin da suke hada jikinsu da juna alhali babu aure a tsakaninsu. Yau ina ranar son zuciya da biyewa shaidan da mukarrabansa wadanda suke tallata irin wannan watsewar da sunan wayewa. Mama da bata zagi yau duk wanda yazo bakinta dankarawa ‘yar tata take yi. Tashi ki bani wuri mara mutumci tasa kafa ta haure ta. Jiki a sanyaye haka ta fita tana share hawaye.
*******************
Yau kwana biyu kenan Junaid yana wasan boya da Hajiyan Dangi da mommyn sa. Tun sallar asuba yake fita sai tsakar dare yake dawowa. Hajiyan Dangi lamarin ba karamin bata mata rai yake ba. Sai da ta cika sati a gidan Senator Rufai ya dawo. Bayan ya huta cikin dare wuraren karfe tara yaje dakin da yayar tasa ta sauka.
Hajiyarmu babbar Hajiya zama da tashi cikin girma. Kirarin da ya saba yi mata kenan yau ma bayan yayi sallama tun kafin ta amsa ya fara. Murmushi tayi tana kallonsa Rufai bazaka girma ba. Ai indai ina ganinki bazan girma ba Hajiya. A kan kafet ya zauna kusa da ita. Bayan sun gaisa tace Rufai kayi min laifi gaskiya. Nasani Hajiya kiyi hakuri don Allah. Lamarin Junaid ba karamin bata min rai yake yi ba amma na rasa yadda zanyi da yaron nan. Dole ka fadi haka mana tunda aiki yafi maka akan rayuwar iyalinka, wannan karon cikin fushi take maganar. Kana gefe kana turowa yara kudin da yafi karfin aljihunsu dama me kake tsammani ga yaro da kudi. Shiru yayi don sam baya iya mata musu kuma ma yasan gaskiya take fada masa. Tace to ni na yanke shawara ayi masa aure kawai. Tun zuwana garin nan yaron nan yake gudu na. Anya zaka iya haduwa da Allah akan yadda kayi wasarairai da amanar da Ya baka na yara? Ni bama wannan ba Rufai kaga Allah Ya baka matsayi a cikin al’ummar kasar nan kuma ni da kai munsan ba iyawarka bace tasa ka samu. Zabi ne kawai na Allah saboda haka ina dada baka shawara kamar kullum ka tsaftace dukiyarka. Ka kiyaye haram don ita kadai zata wargaza duk wani al’amarinka. Kafin ta gama magana idanun senator sun cika da kwalla. Dukiya kam suna kai suna wasa da ita son ransu. Ya Allah Ka bamu ikon gyarawa ya fada a zuci.
Gyara zama yayi to Hajiya wa kike jin za’a aura masa? Sayyada ta bashi amsa a takaice. Sayyada ya maimaita shima ban gane ta ba. Bama ka santa ba. Yar wajen Atika ce kanwar Baba(maigidanta). Tun da ta gama secondary ta dawo hannuna bana ma zata gama Buk. Yarinyar tana da hankali da nutsuwa kuma bata daukar wulakanci shiyasa nake ganin zata taimaka wajen shawo mana kan Junaidu. Har zuciyarsa yayi murna. Yace Allah Ya shige mana gaba kuma don Allah a taya mu addua.
Junaid yasha fada wurin mommy karshe tace yaje ya bawa Hajiyan Dangi hakuri. Yana zuwa bakin kofar dakin yaji maganar da suke yi da babansa. Wata dariya ce taso kubuce masa…wa yaga Junaid da auren dole. Ai ko zai dena holewarsa a waje zancen aure bai ma taso ba. Juyawa yayi a hankali tare da yankewa kansa shawarar barin garin a washegari daidai lokacin da yaji Alhajinsu yana cewa idan Hajiyan Dangi zata koma kano zasu tafi tare.
Batul Mamman
TUN KAFIN AURE💐7
Tamkar mujiya haka iyayenta suka mayar da ita. Babu mai kula ta sai kannenta suma a tsorace don sun fuskanci su Mama fushi suke da ita kada abin ya shafe su.
Zaune take kan abin sallah tana addua bayan ta idar da sallar walha. Idanunta duk sun shige ciki ga ramar da tayi saboda rashin cin abinci. Sallamar Mama taji ta dago kai a hankali ta amsa. Ko kallonta bata yi ba ta shige tana tashin Anisa ta sha magani saboda ta kwana da zazzabi. Mama ina kwana, an tashi lafiya? Kau da kai tayi amma har zuciyarta tana tausayin Hafsi. Ta kuma yarda kaddara babu yadda bata zuwa ga bawa domin duk cikin ‘ya’yanta ita ce mutum ta karshe da zata yi tsammanin zata aikata abinda tayi. Auta tashi ki sha magani kinji ta fada tana shafa kanta…mama baki ji Hafsi tana gaishe ki ba ne. Tsaki tayi naji…karbi ki sha sai ki koma baccin. Ficewa tayi ta koma dakin Baffa ita ma kukan tayi na tausayin halin da yara harma da manya ke fadawa a wannan zamanin.
Fitar mama kenan Amira ta fito daga toilet ta tsugunna gaban Hafsi. Wai ni don Allah me kika yiwa su Baffa ne Hafsi? Anisa dake kwance tace yanzu ko gaisuwarta ma Mama bata amsa ba. Share hawaye tayi babu komai ku dai cigaba da taya ni addua. Tana gama magana ta tashi ta tafi dora girki don yau duty dinta ne. Ko da ta fita kannenta shawara suka yi karshe suka kira yayarsu Hadiza a waya aka sanar da ita abinda ke faruwa.
*******************
Juni ba wayarka bace take ringing tun dazu. Tsaki yayi ya sha giyar dake hannunsa kyale shi Old Man dina ne. Ai tun shekaranjiya dana bar Abuja yake nemana wai ni zaiyi wa aure…what a joke. Chuks ya kalle shi ku fa hausan nan haka kuke sai ku auri yarinya ku sakata a family way at a very young age. Chai, its disgusting. Karshe ta sami VVF wurin haihuwa kuyi mata saki.
Hannu Juni ya daga masa kai Chuks dakata bana son wulakanci. Gara mu aure muke yi da wuri kai at what age ka fara having sex. Wata irin dariya yayi har mutanen dake cikin club din suka fara kallonsu…my friend I was 13 fa. Wata yarinyar neighbour dinmu ce na ma girmeta. Ita ta koya min. Juni yace ka gani ko ashe kune manyan ‘yan iskan. Kun iya bibiyar kananan yara amma idan musulmi sunyi aure sai ku ce child molestation. Hypocrates kawai.
Abeg no insult me Juni…..ai kaine ka fara zagin hausawa nasan karshe kan musulmi zaka koma.
Ha! Kai ai baka son islam Juni you drink like a fish and sleep with every prosti…kafin ya karasa Junaid ya kai masa naushi a baki. Kan kace kwabo bakin Chukwuma ya fara jini nan yan uwansa suka tarar wa Juni ashe akwai ‘ya’yan hausawa. Cikin karamin lokaci sai fada ya kaure tsakanin musulmi da kishiyoyinsu na wani addinin. Ana ta fashe fashen kwalaben giya. Karshe dai sai da police suka shigo cikin lamarin duk aka kama su.
Tilly na kwance akan gado tare da wani hamshakin dan kasuwa taji waya. tayi mamakin ganin sunan Juni ta dauka cike da farinciki. Nan yayi mata bayanin yadda suka yi da police amma jin ko dan waye kuma ya jika su da kudi sun sake shi. Karshe dai yana bukatar account number dinta zai turo mata da kudi ta biyoshi Lagos. Ko sallama bata yiwa mutumin da suke tare ba ta tashi bayan taji alert….lallai Juni na ji da kudi.
*******************
Cikin kuka Mama tayiwa Hadiza bayanin abinda Hafsi tayi. Itama kukan take…wallahi Mama yanzu irin wanan masifar ake fama da ita. Ana zance ana shafar juna karshe inda kaddara ayi ciki. Mama tace abin ne ba kama ba don ni na haifi Hafsa ba amma wallahi nayi mata shaidar alkhairi. Allah Yasa mufi karfin zukatanmu. Amin Mama amma don Allah kuyi hakuri don idan muka nesanta kanmu da ita sai tayi wani abin ma babu wanda ya sani.
Hafsi da Ummati suna ta shawarwari Hafsi tace kinsan har yau babu waya ko text din Saif. Idan na kirashi ba waya a kashe abinda ya kara batawa Baffa rai kenan don shi so yake a sanar dashi a matso da bikin. To aje gidansu mana don bai isa ya jawo mana jangwam ya tsallake ya barmu a ciki. Ke ummati kila a tsoro yaji. Ai ni dadi na dake shegen son saurayi. Ni wallahi daga yau kara kama kaina zanyi har sai anyi aure.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 8
Juni dear….yes Tilly ya amsa mata yana daga kwance. Jin tayi shiru ya taso ya dafa bayanta Tilly ya akayi ne? Ko akwai abinda kike so ne? No tambayarka kawai zanyi. Nawa ne kudin hotel dinnan ne per night? N150,000. Wage baki tayi ko wane kwana daya? Eh menene wai duk kin wani rude. Gani nayi kudin da yawa kuma gashi yau kwanan mu hudu banda abinci da kudin da kake kashewa a club. Wani shekeke ya kalleta kin ma raina ni to ko don ban biya ki naki kudin bane…yana gama magana ya mike daga shi sai gajeren wando ya jefo mata cheque. Ganin kudin dake jiki dubu dari biyar ba shiri ta rungume shi tana ta murna. Hmm kudi a kasar nan yana hannun masu shi suna kashewa kadangarun bariki da kayan maye wani lomar tuwo ta gagare. Masu kudi a rinka cin halal dai.
*******************
Hajara tana kwance tana chatting da kawayenta a group taji shigowar messages. Tana dubawa hotuna ne kamar bazata bude ba don bata da data sosai sai ta bude daya. Zumbur ta mike ta bude sauran. Babu shakka ita ce a duka hotunan biyar. Wadda ta turo cewa tayi ga wani style din pre-wedding pictures. Nan da masu cewa sunyi kyau da masu zaginsu. Wani gumi ne taji yana karyo mata lallai baa shaidar mutum, yarinyar da kullum take shigar mutumci ita ce a haka. Tsam ta tashi ta dauki mayafi ta sauka kasan gidanta wurin makociyarta. A’a Hajara shigo mana ina kitchen…a sanyaye ta karasa dama wani abu zan nuna miki a waya. Maimakon kiyi min forwarding, menene mu gani. Ruwan ruden tuwon da take ne ya fallatso mata a hannu da gefen fuska saboda tsabar rudewa. Na shiga uku ni Hadiza me zan gani haka. Hajara tace a group na gani shiyasa na nuna miki don nasan wace Hafsi. Muciyar ta karba ganin yadda hannun Hadiza ke rawa ta karasa mata tuwon. Daren ranar bata yi baccin kirki ba. Mijinta zai tafi office ya ajiyeta a gida duk da bata fada masa abinda ke faruwa ba yasan babu lafiya.
A falo ta hadu da Baffa zai fita ta gaishe shi. Lafiya dai Hadiza irin wannan sammako ko duk saurin ki taya ni cin kosai ne. Murmushin karfin hali tayi. Baffa akwai wasa sai dai baya sake wa yara suyi yadda suke so. Ganin bata biye mishi ba ya mike muje ciki. Mama na shafa mai suka shigo dakin. Hadiza lafiya kuwa…nan taji tsoron nuna musu hoton sai dai tasan yadda irin hotunan nan ye kawo a social media. Wasu mutanen basu da aiki sai ture turen abinda bai shafesu ba karshe su kunna wuta mai wuyar kashewa. Wayar ta mika wa Mama shima Baffa ya zauna kusa da ita yana gani. Hankalinta bai tashi ba sai da taga ‘yarta babu ko dankwali ta shige jikin namiji sai kace kanin uwarta ko na ubanta. Nan take numfashin Mama ya fara sama sama dama ita haka take idan ranta ya baci. Haka ta fita daga ita sai daurin kirji ta shiga dakin ‘yan matan. Wayar chaja ta fizgo daga jikin bango ta fara tsula mata. Hafsi ji tayi kamar a mafarki ana dukanta tayi saurin tashi. Yaya Hadiza ta gani sai kannenta. Cikin rashin fahimtar laifinta ta fara rokon gafara. Sai a lokacin Baffa ya shigo ya dakatar da dukan. Kyaleta haka ku zauna. Wayar Hadiza ya bata hoto daya ta kalla ta kama kafar Mama tana kuka…don Allah ku yafe min wallahi bazan kara ba. Ki ma kara mana don ubanki…wai ni dame muka kuskure miki ne Hafsa. Lokaci guda kin fara taka rawar gangar shaidan. Wai ma yaushe akayi wannan hoton? Shiru tayi ba amsa. Nace yaushe akayi hoton nan…lokacin…lokacin. Hadiza ce ta katse ta lokacin me? Uhm lokacin da muka ce miki zamu daukar hoto da ummati. Nasan za’a rina cewar Baffa. Dama nasan da taimakon wani a lalacewar da kika soma yi. Amma wallahi ba a gida na ba. Gidansu Saifullahin zani in nunawa mahaifinsa, ki kwana cikin shiri aurar dake zanyi cikin kankanin lokaci mutuniyar banza. Nan dai ya hada duka yaran nasa sun sha fada da nasiha. A dakinsa kowa yace da Mama ta tabbatar ta tuntubi Hafsi ko babu wani abu da ya shiga tsakaninsu domin shi yanzu ya tsorata da halin yaran zamani.
Batul Mam
TUN KAFIN AURE💐 9
Wani irin kuka ne mai tsuma zuciya take yi tunda Mama tayi mata wannan tambayar. Wai ko wani abu ya shiga tsakaninsu??? Lallai ta jawo wa kanta tunda an fara zargin ko lalacewar tata ta kai nan. Gabadaya filon ta gama jika shi da hawaye dadin bakin cikinta ma rashin duriyar Saif. A wannan yanayin Ummati ta shigo itama kukan take yi don a falo Mama da Maman Ummati suka hada su ana ta fada gadon itama ta hau suka jeru kamar masu gasar kuka. Iyayensu sunyi fushi sosai. Tayi nisa da tunani kamar daga sama taji wayarta na ringing. A firgice ta tashi don tasan ko waye me kiran. Ringtone dinsa daban ne….ummati ce ta doke mata hannu da sauri tana kokarin dauka. Ta galla mata harara to banza mara zuciya..duk abinda ya samemu a dalilinsa sai yau zai wani nemeki. Cikin muryar data dashe saboda kuka tace bafa ki san me ya same shi ba. Don Allah ki bani wayar Ummati. Ni wallahi haushi kike bani mtww karbi ni ta dangwara mata wayar ta koma gefe. Ba zancen fita don iyayensu mata suna falo ana ta maida zance.
(Matar ina kika shige ina ta waya.)
Kaji rainin hankali yau fa kwanansu shadaya bata samunsa a waya(kai zan yiwa wannan tambayar. Sai da kaga matsala ka guje ni Saif) kuka ne yaci karfinta.
Shima a hankali yake magana( kiyi hakuri ni kunyar sake haduwa dake da kuma Baffa nayi. Matar ina tsoron zama sirikinsu har abada Baffa bazai dena ganina da wannan tabon ba)
Wani irin faduwar gaba taji (me kake nufi? Baffa fa sun taho gidanku tare da baban ummati)
(Nasani na kuma nayi musu bayani. Tun ranar da ya ganmu na sanar da umma don bana son rufafa a maganar aure. Kunya tasa na guje ki don naci amanar Baffa. Kiyi hakuri muyi rabuwar arziki amma bazan iya aurenki ba.)
Yana kashe wayar wani kuka ya kwace mata har su Mama suka shigo. Ummati suka fara tambaya tace bata san me ya faru ba. Kasa fada musu tayi tana ta kuka. Gajiya suka yi da tambayar aka kyaleta. Sai da Baffa ya dawo ya sanar da Mama yadda sukayi mahaifin Saif yace aure ba fashi tare da basu hakuri shi kuma dan yace bazai iya sake kallonsa ba. Zai fadi haka mana tunda yaso gurbata mana rayuwar yarinya. Suna ta maganganu Hafsi na jinsu daga daki tana kara tsanar kanta da abinda tayi.
******************
Junaid mutum ne mai son jindadi, bashi da magana sosai sai ta zama dole. Ko kadan baya daukar raini wannan kuma hali ne ya tarar da dukiyar da ya taso cikinta. matashi ne dan shekara 30 ga tsaho ga kyau ga fatarsa mai kyau saboda tana shan hutu. Gashin kansa da saje kuwa a kwance yake don kudin da ake ajiyewa don gyara shi daban ne. Yana son kula da gashin kansa ko kadan baya son abinda zai bata shi.
Yana kwance kan kujera kansa a cinyar Tilly tana fara shafa masa kai. Doke mata hannu yayi yana magana kasa kasa ki dena taba min kai I hate it. Dan tabe baki tayi to yi hakuri naga ko wanka baka yi ba meye abin bacin rai don na taba? Tashi yayi ya bude fridge ya dauko lemon gwangwani ya fara sha. Ki shirya muje party amma bana son wannan faratan naki kamar mayya ya juya mata baya ji yadda kika kusa kwashe min baya. Yi hakuri Juni ta fada tana murmushi bari na cire su nayi wanka.
Lallai ma yarinyar nan wallahi kinyi kadan abinda ya fada kenan lokacin da ya fito daga wanka ya kama Tilly tana satar masa kudi. A fusace ya karaso gabanta tasha mari hagu da dama. An fada miki bani da hankali ne? Kumatu ta rike tana kuka ni ka mar Juni? Ke ‘yar waye da bazan mareki ba? Barauniya kawai get out of my room. Kafa yasa yana kai mata duka tana ta ihu. Da kyar ta rarrafa ta fita ya jefo mata jakarta waje ta ce zaka san ni kayiwa haka Juni sai na bata maka rayuwa. Ta mike da kyar tana dingisawa mugu ko kudina bai bani ba duk kwanakin nan dana yi.
*******************
Dai dai yake kallon mutane kowa da budurwarsa ana ta sha’ani. Shegiya Tilly da nasan haka take ai da tun wuri na nemi me rako ni nan. Kai da wa kake magana Juni? Shafa kansa yayi zancen zuci ne ya fito fili birthday boy…Imi dan wani gwamna ne abokin Junaid ne tun suna secondary duk watsewarsu tare sukeyi. Ina babe din da na ganku tare ne jiya? Tilly barauniya? Ai na bata takardar sallama dazu….sata fa tayi min don rainin hankali. Imi da buduwarsa suka fashe da dariya ai abokina ka fiye kwashe kwashe ne. Ya rungumo yarinyarsa ya Simy akwai wata a kasa ne kada yayi kwanan kadaici yau. Kai kyale ni kawai. Maybe na tafi portharcout gobe. Dont worry I will pay bana son ganinka so quite. Wayarta ta dauko ta mika masa ga hotunan wasu nan duk kawayena ne idan ka zaba kayi min magana. Bakin ruwan suka koma ana ta wasa da raye raye shi kuma yana kallon ‘yan mata kala kala a wayar. Tsaki yayi zai kira Simy ta karbi wayarta sai kawai yaci karo da hoton da ya daga masa hankali. Zuciyarsa ce take bugu da sauri da sauri…he wants this girl at all cost abinda kawai yake fada a ransa kenan.
Batul Mamman
TUN KAFIN AURE💐 10
Jikinsa har tsuma yake bai taba ganin macen da ta sace masa zuciya ba kamar wannan. Fatansa daya wannan saurayin daya rungumeta ba mijinta bane. Tura hotunan yariyar yayi daya gani a wayar ya tashi da sauri ya je wurin da Imi da Simy suke ta rawa yana mata liki da dubu daya. Janyo hannunta yayi suka fito daga wurin rawar Imi ya jawo wata suka cigaba. A irin wannan rayuwar ana tafka kazanta da tsabar rashin kishi. Muna mantawa akwai ranar da zamuyi accounting for every second da muka rayu a duniya.
Rawar ta cigaba da yi a gabansa ganin hakan ya sake janta suka kara nisa da mutane. Yarinyar nan nake son duk wani information a kanta. Ta dan nutsu ta kara kallon hoton wai wannan kake nufi? Eh mana are you blind? No…sai tayi dariya sorry. Gaskiya Juni bansan….katse mata magana yayi kada kice baki santa ba. Kudi ya dumbuzo daga aljihunsa ya damka mata a hannu. Ki nemo min duk abinda ya dace …ya sake kallon hoton…my God she is so pretty. Kallonsa tayi Juni wannan fa pre-wedding pictures ne. Maybe ma anyi auren don na kusa wata da ganinsu. A wani group aka saka na ma manta wadda tayi sending. Ai sai ki sake sending ki tambaya. Look Simy bani account number dinki. Washe baki tayi yanzu kayi magana. Zan nemo ta ko tana gidan miji ne sai tazo ta kashe maka kishi…kanne masa ido tayi ta tafi. Simy ‘yar shekaru goma sha tara karamar yarinya ce da iyayenta suka kyaleta take irin rayuwar da take so saboda yanayin aikinsu. Tana abinda taga dama babu me tsawatar mata a cewar su kuruciya ce ke damunta. Wai kuma yar musulmi kenan babu ko tsoron mutuwa.
******************
Kallon ‘yan uwanta take ana ta hayaniya. Kanta har wani sarawa yake don ciwo. Wai nan lefenta aka kawo shine har yanzu mutane basu gama tafiya ba. Dakinsu ta nufa kai tsaye wata kakarta tace ai tunda kika dawo bamu watse ba ki tsaya ki kalli abin arziki. Ai ni kam wannan miji yayi ina ma ina da sauran kuruciya. Dariya duk aka sa Hafsi ko sai hawaye. Auren da zaayi ba dadin rai. Abinda komai Baban Saif ne yayi don yace shi ba karamin mutum bane aure ya zama dole. Shi kuma Saif kamar bai taba cewa yana sonta ba alaqar tasu yanzu ba yabo ba fallasa. Da gaske yayi nadamar abinda ya aikata sai dai kunyar iyalin Baffa yasa har ransa baya son ayi auren. Allah Yaso shaidan baici galaba a kansu ba da da wane ido zai tsaya a gaban mahaliccinsa? Ko matasa nawa ne ke tuna irin wannan a lokacin da suke matse ‘ya’yan mutane suna aikata haramun?
Ita kanta Hafsi tana tsoron rayuwar da zasuyi. Da wane ido zasu rinka kallon juna. Ba don zuwan Baffa ba da kila shikenan. Rayuwa kenan wasu na nadama wasu kuwa zuciya ta gama bushewa a aikin sabo. Tir da wannan rayuwa ta shaye shaye da zinace zinace. Ya Allah Ka kara shiryamu Ka bamu wadatar zuci.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 11
Da gaske Simy ta shiga neman yarinyar hoto don Juni dubu dari da hamsin ya saka mata a account yace cikon sai bukata ya biya. Hoton ta fara turawa groups uku da take tsammanin daga nan aka turo don ta manta inda ya fito. Sai bayan kwana hudu ya kebbi tayi magana tace ai saurayin yayan kawarta ne a kano suke. Jin haka Simy tayi saurin cewa ai yarinyar da makotansu ne sun dade basu hadu ba tana neman address dinta ne. Nan dai ba wani dogon bincike yar kebbi ta turo da number din Zainab. Mata mu rage tallata sirrinmu a social media don Allah.
Kamar akan kaya yake a lagos din sai dai kuma dole ya tsaya don Imi yana nan Simy ba tafiya zata yi ba. Yana cikin restaurant din hotel din da yayi masauki tayi masa waya ta shigo. Nan yayi mata kwatance suka hadu. Sai da ta cika cikinta da abinci wanda ya kasa ci don dokin jin abinda zata fada masa. ta sanar dashi yadda suka yi da yar kebbi cikin tsananin farinciki ya kankameta sannan ta bashi number din Zainab. Tana ta dariya Juni lallai yarinyar nan ta tafi da imaninka idan akwai saura. Ke me kike nufi? Ya daure fuska…ni duk iskanci na bana hadawa da izgilanci ga addini fa. Ga wayarki ya mika mata..zan ciko miki kudinki anjima. It was nice doing business with you Juni. The pleasure was all mine ya bata amsa.
Dakinsa ya koma ya hada kayansa. Bayan ya gama ya kira number din Zainab. Kamar gaske sallama ya fara yi mata ta amsa duk da taji bakuwar murya.
Dan gyaran murya yayi( Zainab ce ko)
(Eh, wa ke magana)
Shiru yayi yana tunanin karyar da zaiyi ( ina yayanki ango to be?)
( ya Saif ya fita)ta bashi amsa.
( suna ta shirye shiryen biki ko)
Mamaki ta fara yi dai amma tayi shiru (eh amma fa still bangane ka ba)
( ina printing din cards na biki ne a nan kusa da unguwarku shine nake son nuna masa sample don kiran kasuwa).
Sai a lokacin ta dan saki rai tayi masa kwatancen gisansu kamar yadda ya bukata ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Yarinyar kamar mara wayo ya fada shi kadai, ba wani bincike ta turo da address.
Scrolling waya yayi ya nemi sunan Oldman ya kira. Senator Rufai yayi mamakin ganin sunan Junaid yaron da number dinsa da suke da ita gaba daya basa samu sama da sati biyu. Hakuri Junaid ya bashi tare da sanar dashi zai tafi kano wurin Hajiyan Dangi itama ya bata hakuri. Senator Rufai murna yayi sosai. Yana matukar son dansa lalacewar yaron kawai ke damunsa.
******************
Kano ta dabo tumbin giwa yau tayi babban bako. Junaid Rufai Bukar ne yake tafiya cikin nutsuwa don yau manyan kaya ya saka tare da aski wanda gashin na zuba zuciyarsa na kuna. Hatta faratansa yaje wani salon a lagos ‘yan mata sun gyare shi. Shadda yasa light blue anyi mata dinki mai kyau kansa harda hula. Idan ka ganshi sai kasa shi cikin mazan kwarai sai dai abin ba a fuska yake ba.
Yana tafiya maaikatan airport na binsa a baya ganin sunansa yan maula sun rude. Motar da babansa ya turo ce ta karaso gabansa aka saka masa kayansa a cikin booth. Kudin ya basu masu yawa tunda bai san zafin nema ba. Kowa sai murna…Tilly dake bayansa wadda baisan ma jirgi daya suka biyo ba tayi murmushi tasan ba a banza yayi wannan shigar yazo kano ba. Sai ta rama wulakancin da yayi mata a lagos. Wayar Rosie ta nema ta sanar da ita ta shigo gari.
Gyadi gyadi yace da driver din ya kaishi . Dreba ya shafa kai yallabai ai Alhaji ya gina ma Hajiyar gida a hotoro ai kusan shekararta biyu a can. Shima Juni kai ya shafa don yaji kunya. Rabonsa da zuwa sada zumunci ‘yan uwansu na kano ya kwana biyu.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐 12
Tun kafin ya iso Hajiyan Dangi tasa su Sayyada yi masa abinci. Kusan tafi iyayensa murnar zuwansa ma tunda mommy tayi mata waya ta sanar da ita yana hanya. Alkawari ta daukarwa kanta da yardar Allah yaron nan sai ya shiryu. Ita da kaninta kawai iyayensu suka haifa,tunda bata da nata ‘ya’yan nasa sune natan. Idan ta bar dan uwanta ya cigaba da sangarta danshi lallai taci amanar mahaifiyarsu.
A falo ya risketa tana karatun Al-Qurani cikin murya maidadi take karanta suratul Sajda. Wata irin nutsuwa da kwanciyar hankali yaji yana ratsa masa zuciya ya kasa karasawa cikin falon. Sai da ta kai karshen aya ta ajiye tare da yi masa nuni da ya karaso ya zauna. Bayan tayi addua tace Junaidu dan gudun hijra ka dawo? Murmushi yayi tare da sosa keya. Yi hakuri Hajiyana bazan kara ba. Kallonsa kawai take yi hatta tafiyarsa irin ta babansu ce. Kamar su ta baci. Inama ace yayi koyi da halayen Malam na kwarai.
Haka ta kira ‘yan matan gidan nata suna gaisawa dashi. Wai Hajiyan Dangi ta iya kiwo ya fada a ransa. Ba don yunwar yarinyar hoton nan bace kawai a ransa ai da yasan yadda yayi a sami ‘yar rage dare ko da daya ce. Wani shegen murmushi yayi, Hajiyan Dangi dake gafe tana kallonsa tayi tana murmushin…sai na gyara maka zama yaro.
*******************
Ko kafar gida Hafsi bata zuwa yanzu Saif dinma Baffa ya hanashi zuwa a cewarsa sa hadu idan an daura aure. Duk abin duniya ya isheta gashi dai zata auri wanda take so amma babu wannan farincikin ko kadan a ranta. Duk surutunta yanzu ta zama wata abar tausayi. Yan uwanta kuwa sai shirye shirye suke yi hankali kwance.
*******************
Ya kusa awa biyu a gefen gidan sannan yaga fitowar wanda yake jira. Tabar hannunsa yayi saurin kashewa ya tada mota ya bishi a baya. Yinin ranar duk inda Saif yayi Junaid na binsa a baya ba tare da ya sani ba. Takaici ne ya isheshi don kuwa baiga alamun anzo gidan da yake nema ba. Karamin tsaki yayi ganin sun kusa karasawa gidansu Saif din. Horn ya rinka matsa masa kamar hauka dole Saif ya tsaya yayi parking. Wannan takun kasaitar ya dinga ya har ya isa kusa da motar Saif. Ganin bai sanshi ba sai ya mika masa hannu su gaisa. Kin karbar hannun Juni yayi daya tuna yadda suka kankame abar sonsa…..abar sona??? Ya tambayi zuciyarsa. Sannu dai, Saif ko? Eh ya amsa masa fuska a sake…Saif akwai fara’a. Shiru yayi don bashi da abin fada abin har ya fara isar Saif. Ban fa gane ka ba wa kake nema ne? Hoton cikin wayar ya nuna masa idanun Saif har wani kankancewa suka yi don tsabar bacin rai. Yayi imani ko mutum daya bai turawa hotunan ba kuma Hafsi ko wayar kirki bata da ita shiyasa ma bai tura mata ba. Juni ya katse masa tunani I want her kuma zan iya biyanka ko nawa ne ka kaini wurinta. Ikon Allah….kai kuma daga ina? Kana ma da hankali kuwa? ba ko kunya balle tsoro kake fada min hakan. To bari kaji na fada maka this coming saturday zata zama mallakina. Kasa karasa magana Saif yayi saboda tsabar takaici ya tsaya yana magana da kwancen hauka. Shafa kai Juni yayi plan dinsa is working. Sai kuma ya yamutsa fuska tunda baka jin lallami kasani cewa nan da ….sai ya dubi agogonsa kamar 20 minutes yarana zasu dauko min ita su kai min ita hotel. Wani mari yaji a kuncinsa kamar wuta kafin ya dawo hayyacinsa kuwa Saif ya shiga mota ya tayar. Shege ya fada yana shafa kunci amma fa marin da zafi…kodayake its worth it.
Bayan Saif yabi har kofar gidansu Hafsi. Yana tsaye a can gefe ya hango wani dattijo mai cike da kamala ya fito sunyi magana da Saif. Yasan bai wuce barazanar karyar da yayi ba Saif din yake fada shi kuwa bukata ta biya dama plan dinsa yaga gidan kuma ya gani. Sauransa jin sunanta duk da a zuciyarsa ya rada mata suna pretty.
Batul Mamman💖
TUN KAFIN AURE💐13
Wallahi Baffa kamar mahaukaci fa yake magana kuma nayi tunanin da gaske yake. Gyara tsayuwa yayi to Saifullahi ai kadan ma kuka gani. Illar irin wannan abin dama ba na lokaci daya bane. Me zaku fadawa yaranku idan suka ci karo da hoton nan gaba? Shin kuna da bakin tsawatar musu bayan sun san borin kunya kawai kuke yi. Allah Ya kyauta ka tafi gida kawai in Allah Ya yarda babu abinda zai faru. Saif kallon Baffa kawai yake yi don yaga kamar bai yarda da abinda ya fada ba. Shi kadai yasan abinda ya gani a idon yaron nan. Jiki a sabule ya juya ya tafi.
********************
Wannan tafiyar kasaitar yake yi har ya shigo gida yana dan fito don yau zuciyarsa fes take. Tunda yazo kano bai sha giya ba sai taba da shisha suma duk a waje saboda sa ido irin na Hajiyan Dangi. Tsohuwar nan akwai hana ruwa gudu. Turus yayi da ya ganta zaune a kan gadonsa. Fuskar nan babu fara’a koma waje kayi sallama ka shigo kamar dan arna kana min fito kamar mai kiwon kare. Haba Hajiya ai dakina ne kuma nasan babu kowa a ciki meye na sallama kuma. Ashe baka san cewa akwai aljanu da malaikun Allah a ko ina ba. Don baka ganinsu hakan ba yana nufin babu su ba. A duk lokacin da zaka shiga wurin da babu kowa sai ka ce Assalamu alaina wa ala ibadullahis salihin. Ai na iya Hajiya bafa complete jahili bane ni. Naji koma dai kayi. Fita yayi yayi mata kyakkyawar sallama ta amsa sannan ya shigo. Cire kaya ya fara yi yana wurgi dasu tace maza ka gama ka tsince min su ga tsintsiya nan ka share dakin. Me??? Ni din Hajiya? Kai mana Junaidu ko kana jin saurayi kamar ka zan bari a share masa daki. Ni wallahi bacci nake ji duba fa ki gani na dawo da wuri shadaya bata yi ba. Ta mike Allah sai ka gyara dakin nan idan ba haka ba zaka ga yadda zanyi da kai. Tana fita ya fada gado sai dai bai gama gyara kwanciya ba ta dawo. Yauwa kayi sallah kuwa?… .au kwanciya kayi ko to tashi ta fada tana dukansa da slipas din kafarta. Dole ya mike Hajiya bana so fa. Sallah kuma nayi don nasan ina da ayyuka a gabana shiyasa ma tun da Baba yazo muka je muka yi sallar asuba ina dawowa nayi duka sallolina ya kare maganar da murmushi. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun shi kawai take fada. Junaidu lalacewar taka har ta kai haka? Shiyasa ka gagara shiryuwa mana. Ta share wasu zazzafan hawaye dake sauko mata. Ashe baka san cewa wutar masu barin sallah daban take ba? No Hajiya nifa nayi ko bakiji abinda na fada bane. Bakin gado ta zauna Junaidu babu wata sallah da zaka yi ba a lokacinta ba da gangan Allah Ya karba. Harma gara lokacin ya wuce maka bisa kuskure sai ka rama. Ita fa sallah kariya ce daga aikin sabo da alfasha. Rayuwa da mutuwa gaskiya ne Junaidu, azaba ko rahmar kabari gaskiya ne, wuta da aljanna ma gaskiya ne. Maganar Hajiyan Dangi da hawayenta sun taba masa zuciya har bai san lokacin daya dora kansa a cinyarta ba yana bata hakuri. Junaidu ka kiyayi Allah sai Allah Ya kiyaye ka. A yau alkawari daya nake nema a wurinka shine na tsayar da sallah. Nayi miki bazan kara bari naji kiran sallah na kasa tashi ba. Ta shafa kansa Allah Yayi maka albarka. Amin
******************
Ummati ana ta rawar kai biki ya gama matsowa da kyar aka barsu zuwa salon don ko gyaran jiki Hafsi bata yi ba. Wannan kuma duk yana cikin punishment din da aka tanadar musu a gida saboda laifin da sukayi don a cewar Maman Ummati itama haka zaayi mata tunda bakinsu daya.
Sai da Saif yayi jan ido sosai sannan kanwarsa Zainab ta fada masa gaskiya ita ce garin binciken waya taga wadannan hotunan a wayarsa ta tura wayarta, daga nan kuma ta tura wa kawayenta. Da belt ya zane ta tana ihu tana bashi hakuri. Ko da mamansu taji dalilin dukan Allah Ya kara tace musu duk su biyun. Ke banda gulma me ya kaiki bincika masa waya….bayan zainab ta koma daki da kuka Maman tace gobe ma ka sake daukan yar mutane kuje yin hoton rashin kunya….istigfar ya rinka yi a zuci. Allah Yasa daga wannan bazasu fuskanci azabar Allah ba. Don kam shi da Hafsi sunyi nadama sosai.
Batul Mamm
TUN KAFIN AURE💐 14
Duk abinda yayi niyyar yiwa Pretty kamar yadda ya saka mata suna maganganun da Hajiyan Dangi tayi masa yasa duk jikinsa yayi sanyi. Washegari bai bari ya makara sallar asuba ba domin kafin lokaci ma yayi setting alarm. Suna dawowa ya shiga dakin Hajiyan Dangi. Har ka manta yadda ake sallama ne? Ba shiri ya fita yayi sallamar ya jira tayi masa izini ya shigo. A kasa ya zauna cike da ladabi tace yau dannan nawa akwai magana a bakinka. Fadi inji Allah Yasa alkhairi ne. Shafa kai yayi alkhairi ne Hajiya. To ina jinka. Wai yau shine da jin kunya abin ya bashi mamaki… dama yarinya na gani ina son aura kuma idan da hali da wuri nake son auren. Allah mai girma da daukaka ta daga hannu sama ta yabi Allah SWT sannan ta kalle shi. A ina take kuma ya sunanta? Nan fa daya yace a ransa, sai kuma dabara ta fado masa. Nasan gidansu dai amma banyi mata magana ba domin mafi son ki fara nema min izini. A’a wai kuwa Junaidun da ta sani ne wannan? Yau komai a hankalce yake yi. Allah Yasa bata yi masa zancen Sayyada ba itama yarinyar bata sani ba da yazo ya bata kunya. Kwantar da hankalinka bari na fadawa Baba sai musan abinyi zuwa karshen sati. Sanin cewa nan da kwana uku zaa daura mata aure Junaid ya fittike mata shi lallai yau yake son taje. To naji bari dai na fada masa tunda da kanka ka zo da maganar. Tana fita yayi ajiyar zuciya yarinyar da har yanzu baiga zahirinta ba yake tunanin aura….sai dai kuma irin yadda yake jinta a ransa yasan da gaske yake burin rayuwa da ita, baya jin zai taba iya yarda wani ya shiga tsakaninsu.
Sai bayan laasar Hajiyan Dangi ta shirya tare da wata yar uwarsu Gwaggo Mairo suka nufi unguwar sabontiti inda Junaid yayi musu kwatance a matsayin gidansu Pretty. Karba ta mutumci da karramawa Mama tayi musu bayan sun gama gaisawa ne Hajiyan Dangi ta gabatar da kanta tare da fadin dalilin zuwansu. Mama tace kuma nan gidan yaron ya fada muku? Nan ne domin ya kwatanta min gidan ta waje sosai Hajiya ta bada amsa. To Hajiya ni dai banda yaran nan biyu da suka gaisheku bani da wata ‘yar sai Hafsa wadda asabar dinnan zaa daura mata aure. Babbar kuwa shekararta uku ma da yin aure. Shiru Hajiyan Dangi tayi sai Gwaggo mairo ce take ta basu hakuri tace nasan yaronnan kam ba kananan yake nufi ba zamu sanar dashi yayi hakuri. Hajiyan Dangi ta fiddo kudi a jakarta tace gashi a bawa amarya. Allah Ya sanya alkhairi. Mama taki karba itama hakurin ta basu. Hajiya sai ta ajiye kudin a kan tebur. Suna kofar fita Hafsi ta dawo daga salon duk a gajiye. Har kasa ta durkusa ta gaishesu. Ko baa fada ba Hajiya tasan wannan ce Hafsar da danta ya gano. Lallai ya rude don yarinyar tana da kyau. A sabule suka fito don ba haka aka so ba. A tunaninta indai yayi aure wasu daga cikin ayyukan barnar da yake aikatawa zasu ragu ko ma ya bari gaba daya.
Tun a mota ta kira shi domin taga missed calls dinsa da yawa sai dai bai dauka ba. Suna isa gida Sayyada ta sanar da ita ai ya tafi masallaci ne. Dadi ne ya cika mata zuciya sannan ta shige daki. Cike da doki ya shiga dakin yana ta washe baki. Har zuciyarta take tausayinsa… junaidu yarinyar nan ashe ranar asabar za’a daura mata aure. Kayi hakuri ka nemi wata. Mikewa yayi hakuri fa kika ce Hajiya. To ma baki basu kudi bane? Ai wallahi da sunga kudi magana zata chanja. Murmushi tayi zauna Junaidu. Ina so ka sani ba fada ta bace Annabi SAW yace babu kyau wani ya shiga cikin cinikin wani ma balle harkar neman aure. Ai ba’a hada nema akan nema. Abu daya zaisa ka iya nemanta sai dai indan wancan yace ya fasa. Wani irin bacin rai yaji a ransa idanunsa sun kada sunyi ja. Fita yayi fuuu ya buga mata kofar daki har sai da ya tsorata ta. Allah Ka shirya mana ta fada a fili.
Jan mota yake a guje kamar zai tashi sama. Baya ganin gabansa ma da kyau. Club ya shiga ya tayar da kura kafin ya tsayar da motar. Idanu duk a kansa ya shiga. Waiter na shirin zuba masa giya ya sunkuce kwalbar yana kafa kai. Sai da ya bugu sosai ya jawo hannun wata yarinya suka fita tare yana tangadi. A waje ya dauko wayarsa ya bata yana lumshe idanu kira min oldman. Waye kuma oldman? Ki dduba za zaki gani a wayar. Ringing biyu ya dauka sai yayi mamakin jin muryar mace ta sanar dashi wurin da dan nasa yake ya daga masa hankali. Yana ajiye wayar ya kira Hajiyan Dangi ya fada mata. Nan tayi masa bayanin abinda ya faru sannan ta sanar da maigidanta inda Junaid yake. A can abuja kuwa Mommy Senator Rufai ya tasa yace mata gobe zamu kano.
Batul Mamman

Leave a Comment