Books Reviews & FAQs

Tsohuwar Soyayya Hausa Novel

Gargaɗi
ban yarda wani ko wata su juyamin wannan labari ta kowani siga ba, ko kuma a karantashi a youtube channel. Labarin Tsohuwar Soyayya hakkin mallakar Azizat Hamza ne.

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__

*TSOHUWAR💖 SOYAYYA*

*©Azizat*
Wattpad @000Azee

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Free page

*Shimfiɗa*

A duk lokacin da soyayya ta zamo tsakani da Allah to haƙiƙa ta na nan har ƙarshen rayuwa. Yanayi zai iya chanjawa, mutane za su iya chanjawa amma soyayya ta na nan a zuciya.
Soyayyan da ake yanzu yawanci soyayya ce da ke zuwa da buri da ado da ƙyale-ƙyale. Kuɗi,kyau, su suka fi zama jagora a soyayyar yanzu.

Ɗan maikuɗi sai ‘yar maikuɗi. Ɗan mai mulki sai ‘yar mulki shi ne abinda mu ka samu tun zamanin kaka da kakanni. Bature shi ne wanda ya fara watsar da wannan al’ada ta yanda indai soyayyace ta asali to ba ruwansa da kuɗi ko sarauta. Misalai na nan da dama kamar auren Prince William da Kathrine, prince Harry da Meghan. Ku duba auren Mark Zuckerberge da Priscilla chan, Bill Gates da Melinda.  Aure ne da su ke yi saboda soyayyar asali. Amma idan ka garzayo ƙasar mu Nigeria maimakon abin ya ragu to abin ƙaruwa ya ke. Duk min kyan ki/ka idan zuri’ar ku ba naira to fa sai dai ki auri mutum mai dama-dama amma asalin ƙusosin ƙasa masu kuɗin kuɗi, sai dai ki gansu ko ka gansu a talabijin ko jarida da kuma yanar gizo. Haka nan masu dama-dama ɗin ma ba son raɓan talaka su ke ba kowa ya na son upgrade.
Wannan labari ƙagagge ne idan yai kama da rayuwar wani/wata/wasu to anyi shi dan a faɗakar. Ba wanda ya fi ƙarfin ƙaddara da kuma hukuncin Allah. So whatever happens it’s destined already.

I promised you, this story will make you smile,laugh, cry but most importantly it will make you ponder. And you wont regret investing your time, strenght and money in to this journey.

*Follow me as i take you on a journey, a journey of true love…..*

0️⃣1️⃣ It’s 2018

Wajen liyafar ya cika da mutane musamman ma’aikatan BBC Hausa harda ma na sashen BBC English. Familyn Bulama su na nan a wajen ‘ya’ya da jikoki. Musamman wanda dama su na London a wannan lokaci ko kusa da London ɗin. Wanda su ke nesa ma sun zo, saboda Mom Aaliyah ta kowa ce.

Ta na zaune aka kira sunan ta *Aaliyah Badamasi Bulama* ta taso ta na murmushi wanda ya ke ƙara sanyawa fiskarta alhini. Ta je wajen podium ɗin ta ƙarɓi award da aka bata sannan ta amsa mic ta yi jawabin godiya da Hausa sannan cikin turancin ta na ƙwarewa ta ɗaga award ɗin ta ce “this is for my husband Ahmad may his soul rest in Jannah Amin”

Hawaye ne su ka ciko a idon ta ta yi saurin sa hannu ta goge tareda barin wajen, tana saukowa aka sa tafi.

Da sauri Zaid ya nufo ta ya rungumeta yayinda sauran ‘yan uwa su ka fara zuwa ɗaya bayan ɗaya su na ma ta congratulations…

Wata budurwace da ba za ta fi shekara ashirin ba ta ƙaraso wajen da Aaliyah ke magana da wasu turawa.
“Excuse me, can i take a picture with you ma’am?”
Aaliyah ta yi murmushi  ta ce “sure”  selfie ta mu su kusan guda uku sannan ta ce “thank you”
Kai tsaye wajen da Zaid ke zaune ya na magana da wasu ‘yan uwan sa ta je. Neman izinin magana ta yi da Zaid wanda ko kallo ba ta ishe shi ba.

A hankali ta ce “plz Zaid ka taimaka ka bani minti ɗaya naka, abinda zan gaya ma ka is very important”

“Zaid ka saurareta ma na” inji Hafiz.

Ko ɗagowa bai yi ba balle ya amsa ya cigaba da danna waya.

Ta fito da wayarta daga cikin purse ta danna kira. Sai ga wayar Zaid ta na ringing, ganin baƙuwar number ya sa shi yin tsaƙi sannan ya ɗauka
” Hello”
“Hello Aaliyah ce”
Sai a lokacin ya ɗago ya kalleta. Kallon a ina ki ka samu special number na.

Murmushi ta ma sa sannan ta ce ” na san za kuje Nigeria cikin satin nan so i will be waiting for you there” ta wuce ta barshi da mamaki.
“And who the hell is she?” ya faɗa da ƙarfi

Hafiz ya ce “kai zamu tambaya ai”

Tsaki yai dan ya san irin matan nan ne ma su bibiyar sa.

“Kai amma fa tanada kyau” inji Rabi’u da ke gefen su.

Yarinyar na fitowa daga ɗakin taron kai tsaye taxi ta shiga sai airport. Tun acikin taxi ɗin ta kira Abban ta ta sanar ma sa jirgin su ƙarfe goma sha biyu na dare zai tashi, ya ma ta addu’an Allah ya kawosu lafiya.
Tana cikin jirgin ma selfie da su ka ɗauka da Aaliyah Badamasi ta ke kallo. A hankali ta furta ‘ its now or never’ ….

 

Wanka ta yi sannan ta gabatar da shafa’i da wutri, da ta idar ta na jan carbi aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin.
“Come in” ta bashi umurni. Sanye ya ke da silk pyjamas baƙi. Murmushi ta yi ganin ƙwan na ta ɗaya a duniya.
“Ba ka yi bacci ba?”
Zama yai gefen ta ya riƙe ɗaya hannun da babu carbin ya ce “are you Ok Mom?”
Ta ajiye carbin ta sa hannu ta na shafa gashin kan sa mai tsantsi da yalwa.
“I’m Ok son, thank you”

“Kin missing Daddy ko?”

Ta ɗaga kai alamar eh.

“I miss him too”

ya jima a ɗakin kafin daga baya ya ma ta sai da safe.
Ta jima ta na addu’o’i kafin daga bisani ta je ta kwanta.

Kwantawanta ke da wuya maganganun Ahmad ya fara dawo ma ta, daren rasuwar shi.

*”Na zalinceki Aaliyah, na hukunta ki da horo mafi tsanani ta hanyar rabaki da ɗan ki na tsawon lokaci, ki yafemin. Dont be lonely after my death ki…”*

Ta yi saurin toshe kunnuwanta saboda yadda maganar ke tuno ma ta da abin da ta daɗe da binnewa a zuciyarta.

“Na yafe ma ka Ahmad, haka ƙaddara ta ta zo” ta faɗi a hankali…

………………………………

Bayan yai waya da Aaliyah ya ci gaba da kallon program ɗin har sai da aka gama. Ta rame ma sa, haka nan kaman ba ta da lafiya ya ke gani. Zulumin rashin ta da zai yi ya ke. Shekara ashirin da biyar bai taɓa fashin jin shirye-shiryen ta ba tun ta na yi a BBC english har ta koma na Hausa haka nan kuwa a duk lokacin da kewarta ya addabeshi toh programs ɗin ta su ke ɗebe ma sa kewa ya na da record na programs ɗin ta tun daga 1993 zuwa last program da ta yi a farkon shekaran 2018.

“I pray you have peace idan ki ka dawo Nigeria Aaliyah”

………………………………….

“Abba, Abba….”

Muryar ‘yar ta sa ya doki kunnen sa. Yanzu ya ke shirin fita ya je ya ɗauko ta. Ya fito daga ɗaki da sauri, a stairs su ka haɗu saboda yadda ta shigo gidan da gudu. Ta rungumeshi ta na faɗin “i miss you Abba nah”
“Yanzu ke da na ke shirin zuwa na ɗauko ki, sai ga ki”
Ta kissing goshin sa ta ce
“what’s important is that im home now”
Ya ɗan ja kunnen ta ya ce  “na hanaki gudun nan ba kya ji ko”

“Sorry Abba” ta faɗi ta na murmushi.

Kai tsaye ɗaki ta shiga ta yi wanka sannan ta fito a dining ta ga ƙannenta na breakfast sai a lokacin su ka ganta saboda Lokacin da ta shigo gidan ba su tashi a barci ba. Ta joining ɗin su su ka karya tare, su na ci ta na basu labarin bikin da ta je a London…

Gaba ɗaya ta gama haɗa kayan ta tun jiya, ita da London yanzu kam sai dai ziyara wanda ba ta tunanin za ta yi shi nan kusa, amma ba dai zama ba. Ta yi murmushi lokacin da ta tuna farkon zuwanta gidan nan. Rayuwa kenan komai yai farko zai yi ƙarshe. Gashi yanzu ƙarshen zaman ta a London ya zo ƙarshen kasancewarta matar Ahmad ya zo.

“Mom an gama fitar da kayan?” Zaid da ya leƙo ɗakin ya ke tambaya.

“Yes son nima ina saukowa yanzu”

Ok ya faɗi sannan ya tafi.

A hankali ta ƙarasa wajen  dressing mirror ɗin ta, ta ɗan tura shi ƙasa sai ga wani safe a jikin bango. Ta danna number kamar haka 0108 sai gashi safe ɗin ya buɗe. Wata ƙaramar jaka ce acikin safe ɗin. Ta fito da jakar tareda rungumeta ta na hawaye. Muryan Zaid da ta jiyo ya na bawa ma su aikin gidan umarni ya sa ta yi saurin ɗaukan jakar ta sa acikin handbag ɗin ta, da shi ke handbag ɗin babba ne sannan ba komai a ciki, ya sa jakar da ta cusa ciki ya zauna daɓas. Ta yi saurin goge hawayen ta sannan ta ɗau jakar ta fito.

Har su ka isa airport zuciyar ta bai bar bugawa da ƙarfi ba. Haka kawai gaban ta ke faɗuwa. Tun rasuwan Ahmad rabonta da Nigeria wannan kaɗai ya isa ya sa ma ta fargaba musamman idan ta tuno rabuwar ta da Hajiya Inna.

Hannunta saƙale da na ɗan ta Lokacin da su ke fitowa daga jirgin. Da mamakin su har lokacin ba su ga wani ya zo tarban su ba. Cikin ɓacin rai Zaid ya fara kiran ‘yan gidan na su  saboda rashin mutunci bayan ya riga ya shaida mu su yau zasu taho amma ba wanda ya zo ɗaukan su bayan har Lokacin da za su sauka ya faɗa.

“Zaid Ahmad Wamako” ya ji wata siririyar murya ta kirashi
Murmushi ta ke mu su har ta iso. Kamar dai ya taɓa ganin ta amma ba zai iya tunawa ba dan ‘yan matan da ya gani cikin satin nan kaɗai sun fi ashirin.

Ta ƙaraso ta rungume mom, “i’m so happy na same ku da ban san ya zan yi ba.”

“And who are you?” Zaid ya tambaya da ƙarfi. Ta maida kallon ta ga mom ta ce ” mom ni die hard Fan ɗin ki ce, saboda ke na je bikin retirement na ki a london” ta fito da wayarta ta na nuna ma ta selfie da su ka yi ranan.

“Ayya, ‘yata ya sunan ki?” mommy ta tambaya.
“Aaliyah”

“Ashe ke takwarata ce,na gode”

” mom da alama ma su zuwa ɗaukan ku ba su ƙaraso ba, ki min alfarma na kaiku gida”

“Kar ki damu ‘yata za su ƙaraso nan ba da jimawa ba”

“Plz mom do this for me, ko dan son da na ke mi ki”

Mom ta ce ” Ok dear” ta kalli Zaid ta ce “mu tafi”
“But mom you dont even know h………..” ya katse maganar lokacin da ya ga mom ta fara tafiya da Aaliyah, Aaliyar ce ma ta ke jan akwatin ta. Bayadda ya iya dole dai bin bayansu yai.  Wata haɗaɗɗiyar mota su ka nufa wanda driver ke tsaye a wajen ya na jiran su. Sai da ya ƙaraso wajen ya hango motar gidan su na shirin tsayawa ya cewa Mom da ke shirin shiga motar Aaliyah “Mom ga driver ya zo, barin bi shi”
Ta ɗaga masa kai.
Har su Aaliyah su ka bar airport ɗin bai shiga motan ba yana tsaye yana zubawa driver masifa.

Sun yi nisa da tafiya Aaliyah ta ce “Mom bari ki ji wani surprise” ta bawa driver wayarta ya haɗa da radio ta fara playing wasu recordings.

Muryan ta Mom taji a cikin recording ɗin, ba za ta iya tuna shekarar da ta yi wannan program ɗin ba amma ta san ya jima ƙila tun farkon shekaran da ta fara aiki a sashen BBC Hausa ne. Ta sake tabbatar da hasashen ta lokacin da ta ji muryarta na kiran *”shiri ne wanda ni Aaliyah Badamasi Bulama zan gabatar”*
Aaliyah ta katse record ɗin ta kalli Mom da idon ta ya cicciko da hawaye ta ce “you are surprised ko?”

“A ina kika sami wannan?, inada tabbacin sanda na ke gabatar da shirin nan ba a haifeki ba”

Aaliyah ta yi dariya. “Gaskiya ne Mom, sai dai kamar yadda na faɗa mi ki ni  Fan ɗin ki ce tun ina ƙarama. Na taso da soyayyar ki da son sanin ke ɗin wace ce”

Mom ta zaro ido
“Dont be surprise mom idan na ce mi ki inada records na duka shirye-shiryen ki tun lokacin da ki ka fara aiki har zuwa ƙarshen program ɗin ki a gidan radio”
ta yi wani ƙayataccen murmushi ta ci gaba ” ku masu aikin gidan radio ai farin jini gareku. Zazzaƙar muryarki mai sanyaya zuciya. Kar ki sha mamaki idan na ce mi ki takanas saboda ke aka sa min suna Aaliyah”

“Wow! I’m speechless dear”

Aaliyah ta cigaba da kunna ma ta records ɗin  wanda Mom ce ta buƙaci hakan. Ta na ji ta na tuna Lokacin ƙuruciyar ta a wajen aiki da kuma girman ta. Muryar dai idan ba ka lura ba ka iya cewa bai chanja ba iya waɗannan shekaru sai dai fa ita ma’abociyar muryar ta chanja sosai girma ya kamata, shekaru ashirin da biyar ba wasa ba ne, shekaru biyar a sashen Turanci sai shekaru ishirin a sashen Hausa.

*Tsohuwar soyayya labari ne mai ɗaukan hankali cike da darussa na rayuwa. Labari ne da ba za ku so ya wuce ku ba. It’s a different journey entirely, different from mutum mugu ne, duk kyan namiji da sauransu. Labari ne da ya zo da salo na daban wanda sai wanda ya karanta zai san the journey is worth investing in.*

*ga mai son cigaban labarin zai biya #200 kacal ta wannan account ɗin 3099546325 Azizat Hamza, firstbank. Idan kuma credit card ne to MTN card na 200 za a turo wa wannan numbar 08137311900. Sannan za turo shaidar biya (screenshot) na kuɗin zuwa numbar nan still 08137311900. Ko kuma ka biya #300 ka samu labarai guda biyu wato tsohuwar soyayya da sakatariya ta*

 

 

 

*TSOHUWAR💖SOYAYYA*

*©Azizat*

Wattpad @000Azee

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Free page

0️⃣2️⃣ find the diary

Har su ka iso tangamemen gidan, Aaliyah ba ta bar yiwa Mom magana akan aikin ta ba tareda ba ta wasu bayanai a kan ta, wanda ba kowa bane ya sani. Like makarantan da ta yi tun daga primary har masters na ta. Like exact date and day da ta yi aure har kalar kayan da ta sa ranar da aka yi wushe-wushen ta a Maiduguri thirty years ago.

“Who are you Aaliyah?” Mom ta faɗi lokacin da motar ta tsaya a farfajiyan gidan.

“Kamar yadda na gaya mi ki i’m your biggest fan Mom. Ina son ki, ina son komai na ki. Infact idan kin bani dama i want to be a daughter to you”

“Ina ganin dole mu zauna mu yi magana” Mom ta faɗa sannan ta fita daga motar.

Ganin Aaliyah ba ta fito ba ya sa ta ce ” ‘yata ki shigo ma na”

Aaliyah ta yi murmushi ta ce ” na san da gajiya a jikin ki, zan zo gobe idan kin huta”

“Thank you dear” ta faɗi tareda maida duban ta ga gate saboda buɗewa da akayi. Motar da ta ɗauko Zaid ne dan haka ta tsaya saboda su shiga gidan tare. Sai da Zaid ya fito daga motar sannan Aaliyah ta fito da sauri ta ce “Mom idan ba za ki damu ba barin yi magana da Wamako”
“No problem dear”
Ta ƙarasa wajen Zaid da ya haɗe rai ganin ta nufo shi.
“Plz Wamako give me two minutes”
“Na san maganar ba za ta wuce barar soyayyata ba. Kar ki ɓata bakin ki dan ba za ki samu ba”

“You guessed wrong, Zaid ka taimaka ka bani lokaci mu yi magana, there’s something you need to know about your mother”

” rubbish”  ya faɗi tareda barin wurin.

Murmushi Aaliyah ta yi sannan ta wuce wajen motar ta saboda Mom ta bar wajen.

“My prince mi daughter ke ce ma ka ne na ga ka haɗa rai?”

” she’s just like the rest, she’s crushing on me”

“Amma kamar ba haka na ke gani ba”
Ya kama hannun Mom ya haɗa da na shi ya ce ” manta da zancen ta, she’s a nobody”…

Kamar yadda ta tsammanta hakan ne ta faru kallon kirki ba ta samu a wajen Hajiya Fatimah ba balle ta samu tarba mai kyau.
Sashen Hajiya Inna da su ka shiga ma abu ɗaya ne nan kam maimakon shiru Inna sai da ta zageta tatas kamar yadda ta saba. Zaid da ya ke ƙoƙarin kare Mom ɗin ne ya sa abin yai sauƙi.

Ɓangarenta na nan yadda ya ke ba abinda aka chanja. Gyara shi kawai aka yi saboda ƙura. Ta zauna gefen gado maganganun Hajiya Inna na ma ta yawo a ka.
*” ashe za ki iya takowa gidan nan, ai na ɗauka daga chan gidan ku za ki wuce tunda Ahmad ya rasu, alaƙa ta yanke. Tsabar sheɗanci yaushe Ahmad ya rasu amma za ki gama aiki wai har wani dinner ki ka haɗa ki na wani bubbuɗa haƙora irin ga ki bazawara ko. To wallahi indai zawarci za ki yi ba anan gidan ba kije chan cikin dangin ki ki yi….”*

“Mom are you Ok?” Muryan Zaid ya dawo da ita.
Murmushi ta ma sa. Ya ƙaraso ya durƙusa a gabanta ya riƙe hannunta biyu. “Mom kar ki damu da maganganun Inna. She’s old and crazy”

“Kakar ta kan” ta faɗi tana dariya.

“Yeah she’s crazy”

Dukkan su biyu su ka sa dariya…

……………………………..

Aaliyah na komawa gida ta turawa Zaid text kamar haka:

*dan Allah ka bani dama mu haɗu gobe, we really need to talk. Aaliyah*

Ta na gama tura text ɗin Abba ya leƙo ya ce “princess zan fita, ba zan dawo da wuri ba kar a yi lunch da ni”

“Ok Abba”

Ta na tsammanin reply ɗin Zaid amma har yamma shiru. Ta sake tura ma sa wani text ɗin amma still bai yi reply ba. Ta kirashi ya ƙi ɗauka.

Ta na zaune ta na karatun ƙur’ani Nusrat ta shigo ɗakin da gudu.
Ta na zuwa ta faɗa jikin Mom.
“My Mom ashe kin dawo, mun kalle ki a Tv ni da su Inna da Mummy ranan. I miss you”

“Oh I miss you too dear”

Kallon yarinyar ta ke yi wanda kamannin Ahmad gareta.

“Mom ina Yaya?”

“Ina ga yana part ɗin sa ki duba shi acan”

“Mom kar ki gayawa Mummy na gaya mi ki, ranan Inna ta ce kar kowa ya shigo wajen ki, wai idan ki ka gaji za ki tafi. Mom ina ba za ki tafi ba ko?”

Ta girgiza ma ta kai.

Sai da Nusrat ta fita sannan ta sauke nannauyan ajiyar zuciya.
Abin ya kai haka ta faɗi a zuciyar ta.
Saboda Zaid za ta zauna anan, saboda shi za ta shanye ko me za a ma ta…

Sai da ta shirya za ta kwanta text ya shigo wayarta ta duba baƙuwar number ce ta karanta text ɗin, saƙon bangajiya ne sai daga ƙarshe aka rubuta yours Aaliyah. Ta yi murmushi sannan ta kira numbar su ka sake gaisawa da Aaliyar. Ta rasa dalilin da ya sa lokaci guda yarinyar ta shiga ran ta…

*”a duk inda ki ke, a ko wani lokaci, a ko wani hali, duk min rintsi, ina son ki Aaliyah, har ƙarshen rayuwa ta, har ƙarshen numfashi na a doron ƙasa. I will forever love you Aaliyah”*

Waɗannan kalmomi su ne abu na ƙarshe da ta tuna kafin ta yi bacci.

Washe gari ba abinda ya chanja ba wanda ya zo wajen ta ita ce dai ta je ta gaida Inna sannan ta duba Zaid a part ɗin sa wanda bai jima da tashi daga bacci ba. Gaisawa su ka yi sannan ta wuce ɓangarenta. Kitchen ta shiga dan ta nemi abinda za ta ci saboda jiya haka ta wuni da yunwa sai dai ba kayan abinci a store ba komai a kitchen ɗin sai kitchen utensils.
Ta fito ta zauna a falo ta na tunani.
Wayar ta ya shiga ringing a ɗaki ta yi sauri ta je ta ɗauko ta ga numbar Aaliyah ce kafin ta ɗauka wayar ta katse. Ta yi saurin kiran ta
“Hello Mom ina cikin gidan ku ki aiko a shigar da ni”

” tsaya zan zo da kai na”  ta faɗi sannan ta shiga ta sa hijab ta fito.
Motar jiya ne ta kawota. Aaliyah na ganin mom ta fito ta yi saurin fitowa daga motar ta na murmushi. Ta ɗauko basket a cikin mota sannan ta nufi wajen Mom. Da murna ta tareta su ka shige cikin gidan. Kai tsaye falo su ka zauna.

“Sai ga ki da safe na ɗauka sai yamma za ki zo ai”

“Mom wallahi Abba ne yai ma na breakfast shi ne na ce dole sai na kawo kin ci kin ji girkin Abban mu”

“Kai kai Aaliyah da rigima, shine tun daga gida ki ka taho da shi”

“Yes Mom i have to. Kin san Abba na shi ne number one fan ɗin ki in this whole world”

“Kayya, to na gode”

“Hope ba dai kin karya ba dan dayawa na kawo saboda mu ci mu ƙoshi”

Mom ta yi murmushi.

“Mom ina ne kitchen na ɗauko ma na plate da cups”

Mom ta tashi ta ce “barin ɗauko”

A falon su ka baza kolin sinasir da miyar taushe da su ke ci wanda miyan ya ji nama. Sai da Mom ta kurɓi shayin da Aaliyah ta kawo ta ji wani abu ya tokareta.

Aaliyah ta ce “you dont like it?”

“No, shayin nan kamar…” sai kuma ta yi shiru

“Abba ya iya haɗa shayi, this is his favourite recipe, he calls it Aaliyah’s tea. He’d being making it for more than 30yrs now”

“Aaliyah mi ye sunan Abban ki?” Mom ta tambaya.

Aaliyah ta san anzo wajen but this is not the right time dan haka ta ce ” Sani, Aaliyah Sani suna na”

Ajiyar zuciya ta yi sannan ta ce “Oh that’s nice, ki ce wa Abba ya iya haɗa shayi”

Su na cikin cin abinci ya shigo falon da sallama.
Mom ce ta amsa ma sa yayinda Aaliyah ta shagala da kallon sa. Sanye ya ke da baƙin jeans three quarter da farar vest, gashin kan sa a kwance lub-lub sai sheƙi ya ke yi.

“And what are you doing here? Ba dai a nan gidan ki ka kwana ba?”

Sai a lokacin Aaliyah ta yi firgigit da kallon sa.

“Mom i dont like this, daga haɗuwa da yarinya kin shigo da ita gida har kuna cin abinci tare. What if she’s a spy”

Mom murmushi ta yi ta ce ” kai da za ka tayani murna na samu daughter sai ka hau fishi, haka ake yi”

Ya harari Aaliyah ya ce “yarinya ƙarama da ke sai shegen shige-shige”

“Eliza,Eliza” ya fara kira da ƙarfi.

Mom ta kalleshi ta ce ” Son lafiyar ka kuwa, wace Elizan kuma ka ke nema?”

“Mai aikin ki ma na, ko ta fita ne?”

Hmmm kawai Mom ta ce ta ci gaba da ƙurɓan shayin ta.

Aaliyah ta kalli Zaid da ke rarraba ido ya na kallon Mom ta ce ” ni da Mom ne kawai a wajen nan tun ɗazu ba wadda ta shigo”

“This people are trying my patience abi” ya faɗi tareda yin hanyar waje.
Aaliyah na jin shi ya na kiran sunan ma’aikatan gidan.

A tsakiyar main parlour ya tsaya ya na masifa.
“Dan Ubanki Eliza jiya ban ce ke za ki dinga kula da ɓangaren Mom ba. What the hell are you still doing here?”

“Oga….” sai kuma ta yi shiru

“Talk” ya daka ma ta tsawa.

“Ni ne nan na ce kar wanda ya shiga wajen Aaliyah” muryan Inna ya doki kunnen sa.

Ya juyo a fusace ya ce “Inna mi hakan ke nufi?”

” hakan na nufin idan ta na son mai aiki, ta kawo na ta, amma wanda su ke nan ba wanda zai yi ma ta bauta”

” interesting” ya kalli Eliza ya ce ” je ki ɗakin Inna ki haɗa ma ta kayan ta she’s leaving this house”

“Zaid kana da hankali kuwa” Hajiya Fatima da fitowar ta kenan ta faɗi.

” listen old woman, gidan mijin ki ya na Sokoto Idan bai mi ki ba akwai wani gidan sa a Wamako ki je chan ki zauna ki yi iko yadda ki ke so. But this house is my fathers and he built it for my Mom so ba ki da hurumin aiwatar da doka a gidan nan. Idan ba tsofin zamani ba ma da shegen son duniya ke da ɗanki ya mutu mi ya kamata ki yi banda ki koma ƙuryar ɗaki ki na nema ma sa gafara tareda ke kan ki amma banda tada fitina ba abin da ki ke yi a nan. Look ni Zaid ba zan lamunci cin mutunci daga wajen kowa ba, duk wanda ba zai kyautatawa mahaifiyata ba to zai iya tattara kayan sa ya bar gidan nan. And that includes you Anty” yai maganar ya na kallon Hajiya Fatima.

“Innalillahi, yanzu ni Zaidu za ka ciwa mutunci. Abinda Aaliyah ta ce ka ma na kenan?” ta ƙarasa maganar tana goge hawaye.

Zaid ya ƙaraso wajen ta ya ce ” ki yi kuka yadda ki ke so ɗanki ya mutu. Ni tawa uwar ta na nan da ran ta and i will always protect her. Idan wani ya yi ƙoƙarin ƙuntata ma ta i promise, ko waye sai na yi maganin sa”

” ka san dai ba kai kaɗai ke da dukiyar ba, na ga da shi ka ke taƙama” Anty ta faɗi

Dariyar rainin hankali yai sannan ya ce ” to waye matsiyaci anan. Aaliyah Badamasi Bulama dai ko da ba ta auri Ahmad Wamako ba ta gaji arziƙi idan ba ki san tarihi ba Inna ta sanar da ke”

“Zaid ni ka ke cewa matsiyaciya, kai Allah ya jiƙan rai” ta fashe da kuka.

Kallon ma su aikin da su ka tsaya cirko-cirko a wajen yai ya ce “Eliza ke da wannan ku wuce wajen Mom and, idan ku ka ƙara barin wajen ta. I will deal with you mercilessly. Now get the hell out of here!” Gaba ɗaya su ka fita da gudu.

Ya kalli Anty ya ce ” na yadda ba ni kaɗai ke da dukiya ba, amma ki sani this particular house is my mothers, infact zaman alfarma ku ke yi domin a ko wani lokaci tana da ikon koran ku. You can ask Dad’s lawyer if you want” ya na faɗin haka ya haye sama.

Kwalin taba ya ɗauka ya ciro ɗaya ya sa ta a baki ya ɗau lighter ya kunna. Sai da ya zuƙeta sau uku sannan ya ɗau wayar sa da ke ringing. Yawan kira da kuma text da ta ke mi shi ya sa ya gane numbar. Kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya ɗauka ya na furzar da iskan taban.
Shiru yai ya na sauraron mi za ta ce sai dai kuma kafin ma ta ce wani abu ya jiyo muryan Inna ta na faɗa.
“Wamako plz come, Mom is crying….” da sauri ya cillar da wayar sannan ya jefa tabar a ƙasa ya take ta ya fita daga ɗakin da gudu…

Aaliyah kam yau ta tabbatar da maganar da ake cewa *’the rich also cry’* sai yaushe Mom za ta samu farin ciki, Ahmad Wamako ya rasu amma kuma iyalen sa ba su bar tozarta Mom ba sai yaushe za ta bar wannan ahali wanda ba su san darajar ta ba.

” har Zaid zai ce nan ba gida na bane na koma Wamako ko Sokoto. Gidan Ahmad ɗin, gidan ɗa na!. To ki sani, wallahi wani batun Ahmad ya mi ki kyautan gida duk shirme ne. Ke ce za ki bar gidan nan ba mu ba”

Kamar wani Mahaukacin zaki haka ya shigo falon. Kallon Mom yai da hawaye ke zirya a idonta. Bai yi wani tunani ba ya kaiwa Inna mari wanda Aaliyah ta yi saurin riƙe hannunsa.

Mamaki ƙarara a fiskar Inna da Anty.

“Zaid plz dont” Mom ta faɗi a hankali.

“Mare ni Zaidu, mare ni, sai na san ka cika tantagaryan ɗan iska”

Huci ya ke yi kamar wani mayunwacin Zaki da kakkausar murya ya ce ” i swear Inna if you ever insult my Mom again, i will forget the fact ke Kaka ta ce.  Zan mi ki abinda har ki mutu ba za ki manta ba”

Ya kalli Anty ya ce ” duk ranan da ki ka shigo wannan waje ba tareda izinin Mom ba wallahi a ranan za ki bar gidan nan. Now get out!”

“Zaid please, iyayen ka ne”

” Ahmad ma kin shanye shi kin juya shi yadda ki ke so balle kuma ɗan da ki ka haifa. Mu na nan da ke Aaliyah” Inna ta faɗi sannan ta juya su ka fita.

Mom ta dafe ƙirjin ta da ke ma ta zafi.

Mom ya faɗi tareda ƙarasawa wajen ta da sauri. “Mom are you Ok?”
Murmushin ƙarfin hali ta yi sannan ta ce ” Zaid dan Allah ka dena ɗaga mu su hankali, they deserve your respect. Bai kamata ka treating na su kamar wasu yaran ka ba”

” kafin su samu respect ɗi na sai sun fara respecting na ki Mom”

“Ba rin shiga ɗaki i’m having headache”  shi da kan shi ya taimaka ma ta ta shiga ɗaki sai da ta kwanta ya ja ma ta bargo sannan ya fito bayan ya kissing goshin ta.

Ya na fitowa ya ga su Eliza su na shiga da kayan abinci kitchen ɗin. Wato tsabar mugunta kayan abincin wajen ma kwashe su a kayi.

Kujera ya samu ya zauna ya miƙar da ƙafar sa ya na kallon ceiling. Maganganun Daddy na yawo a ƙwaƙwalwarsa.

” Zaid take care of your mother. Iya rayuwar auren mu ban kula da ita ba. I hurted her so much not only me even my family too, ni na raba ta da kai for my own selfish gain. Plz dont let her ever cry again……”

“Wamako, Wamako” muryar Aaliyah ya dawo da shi a hankali ya saukar da idon sa a kan ta. Tsugunne ta ke kusa da shi.

“Plz ka bani 10 minutes na ka mu yi wata magana mai muhimmanci. Its about Mom”

“Minene?” Ya faɗi a hankali

“Can we go to somewhere private plz”

Ido ya ƙura ma ta wanda ya sanya ta yi saurin janye idon ta daga kallon sa da ta ke saboda tasirin da kallon sa ke yi ajikin ta.

” it better be important” ya faɗi tareda tashi tsaye ya ce ” follow me”

Ba mu su ta tashi ta bi bayan sa.

Wajen swimming pool ɗin gidan su ka je. Sai da ya kunna taba ya zuƙa sannan ya ce ” i’m listening”

Ta fito da wani envelop mai ɗan girma ta miƙa ma sa.

“Miye wannan?”
“Just look at it”  ta faɗi.
Ya buɗe envelop ɗin ya fito da hotunan da ke ciki.
hotunan Mom da Dad ne lokacin bikin su wani a wajen dinner wani a wajen wushe-wushe. Shi wasu hotunan ma bai taɓa kallon su ba sai yanzu.

“What does this mean?” Ya tambaya ya na kallon ta.

Ta miƙa ma sa wani envelop ɗin. Ya karɓa tareda buɗewa hotuna huɗu ne a ciki. Still hotunan Mom ne ta na budurwa amma ta ɗau hoton da wani saurayi wanda da gani kasan hoton masoya ne.
Zaid ya ɗago ido ya kalli Aaliyah ya ce ” explain”

Aaliyah ta nisa ta ce ” idan ka lura da hotunan farko za ka ga babu murmushi a fiskar Mom idan ma akwai ba genuine smile ba ne. Amma ɗaya hoton she’s completely happy.”

“And so?”

“Zaid, i need to know the complete story, i need to know if Mom still loves that man”

“This is bullshit, abinda ya sa ki ke damina da kira ke nan?”

“Zaid, ina son ka min wata alfarma. Your Mom has a diary plz find it”

“You must be crazy. Personal diary na Mom zan ɗauka in baki saboda kin sha ƙwaya. See, duk wani stupid idea da ki ke da shi you better drop it. Infact kar ki sake shigowa gidan nan”

“Zaid, na rantse da Allah akwai babban al’amari da ba ka sani ba a rayuwar Mom, and you really need to know. Ba zan iya gaya ma ka komai ba yanzu saboda ba ni da cikakkan labari amma with the diary we’ll know everything”

“Aaliyah ki ke ko waye. Tashi ki bar nan”

“Plz Wamako find the diary” ta faɗi sannan ta ɗau jakar ta ta bar wajen ba tareda ta ƙarɓi hotunan a wajen shi ba…

*Tsohuwar soyayya labari ne mai ɗaukan hankali cike da darussa na rayuwa. Labari ne da ba za ku so ya wuce ku ba. It’s a different journey entirely, different from mutum mugu ne, duk kyan namiji da sauransu. Labari ne da ya zo da salo na daban wanda sai wanda ya karanta zai san the journey is worth investing in.*

*ga mai son cigaban labarin zai biya #200 kacal ta wannan account ɗin 3099546325 Azizat Hamza, firstbank. Idan kuma credit card ne to MTN card na 200 za a turo wa wannan numbar 08137311900. Sannan za turo shaidar biya (screenshot) na kuɗin zuwa numbar nan still 08137311900. Ko kuma mutum ya biya #300 ya samu labarai biyu wato Tsohuwar soyayya da kuma sakatariya ta*

 

 

 

*TSOHUWAR💖SOYAYYA*

*©Azizat*

Wattpad @000Azee

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Free page

0️⃣3️⃣ Aaliyah and Saeed’s diary

Tun tafiyar Aaliyah ya ke kallon hotunan, yana yi ya na zuƙar tabar sa. Tabbas ya san Mom da Dad arrange marriage a ka mu su. To dama haka ake yi ai, rich girl for a rich boy. But for thirty years Mom would’ve fall inlove with Dad ai. Zuciyar sa ya raya ma sa. Amma kuma idan ya tuna maganganun Dad sai ya ga kamar har ya rasu babu soyayya tsakanin su. Anya kuwa? Good 30yrs fah.

Ya maida hotunan tareda cigaba da tuno rayuwar su kafin Dad ya ɗauke shi a London. Duk da yana da ƙarancin shekaru amma yana iya tuno wasu events da su ka faru. Ƙarar wayar sa ne ya fargar da shi. Ya amsa kiran ganin wanda ya bugo.
“Zaid mi ya faru ne, Fatima ta kira ni tana kuka wai dole a raba gado. What is happening?”

Sai da ya zuƙi taba wanda itace ta uku da ya ke sha ya ce ” Uncle, abinda ta ga ya fi ma ta kenan. And i’m Ok with it”

“A’a Zaid, Ahmad ba zai so haka ba, ka san yaran Fatima mata ne kai ne Ubansu yanzu. Responsibilities na su na hannunka har su yi aure.  Zan zo ranan Friday sai mu zauna a tattauna matsalar”

“Ok Uncle”

Sai daya ajiye wayar sannan ya tuna ko breakfast bai yi ba. Dama breakfast ɗin zai je yi a wajen Mom ya tarar da badaƙalar da su Inna su ka shiryawa Mom…

…………………………….

Kwana biyu da tafiyan Aaliyah amma kuma ya kasa cire maganganunta a ran shi, musamman idan ya kalli Mom sai ya ga kamar tana cikin damuwa. Idan ya tambayeta kuma ta ce ma sa ba matsala.

Yau ma su na cin abincin dare tare amma ya lura a takure ta ke kamar ba ta jin daɗin abincin duk da kuwa ita da kanta ta bada order abinda su Eliza za su girka.

“Mom is there something you are hiding from me?”

“Ofcourse not son, mi ka gani?”

“Mom kamar akwai abinda ke damunki, you always look disturbed. Like you are hiding something very important….”

“Zaid” ta katse shi
“I’m fine son, yes i look worried saboda yanzu ba da bane, but nothing else”

“Mom that night, twenty years ago….”

“Zaid!”  Ta faɗa da ƙarfi.

“Shikenan tunda bakyason maganan”

Ajiye cokali ta yi ta ce ” I’ve lost my appetite”

Sai da ta shige ɗaki ya sauke ajiyar zuciya. Ba zai manta abinda ya faru shekara ashirin da su ka wuce ba. He was only eight amma ya na iya tuno komai. Lokacin da Dad ya ɗauke shi daga London kullum sai ya tuna kukan Mom a daren ranar. The screaming, the cries, everything.
Maganan Aaliyah ya tuno da ta ce akwai babban al’amari a rayuwar Mom that he needs to know about. “Could it be related to what happened 20yrs ago?” Ya tambayi kan sa.

He was only eight years lokacin da ya rabu da Mom and ba ta taɓa neman sa ba.  She stays in London all the while. Ya tuna lokacin da ta zo Nigeria ya ƙi ya je wajen ta. How she kneel and cried.  Hawaye su ka gangaro ma sa. Lallai ne dole ya nemo diary ɗin Mom atleast he will find some answers there…

Ta ya Zaid zai tuno ma ta da abinda ta ke ƙoƙarin ɓoyewa iya tsawon rayuwar ta. This is too much for her.

Ta sa key ta buɗe drawer, ta fidda jakar da ta jima tana adanawa.
“If only you came Saeed, if only you came that day”  ta faɗi hawaye na zirya a idon ta.

*”Ke ce zuciya ta Aaliyah, idan na rasa ki na rasa zuciya ta gaba ɗaya” *  ta tuna maganganun sa lokacin da ya sanya ma ta zobe a hannun ta. Ta kalli yatsarta da ke ɗauke da tabon ƙuna. Ko ba zoben a wajen akwai shaidar zaman zoben a yatsar.
Gani ta ke kamar yau ne komai ya faru. Da saka zoben da kuma cire shi.

“Makhtub” abinda mai duban ya faɗa kenan lokacin da ta tambayeshi.

“Zan auri Saeed?” Tambayar da ba za ta taɓa mantawa ba kenan.

“Makhtub yarinya, rubutacce ne, ko sama da ƙasa za su haɗu sai kunyi aure. Sai dai…..”

Ƙaran wayarta ya fargar da ita ta yi murmushi lokacin da ta ga Aaliyah ce.

Ta ɗauka wayar ta na murmushi, lokaci guda Allah ya haɗata da yarinyar nan amma ba ƙaramin shiga ranta ta yi ba.

………………………

Mom ba ta wajen aka yi zaman saboda Zaid bai ma sanar da ita ba. Idon Hajiya Fatima yai zuru-zuru lokacin da lawyer ya gama bayanin sa. “Wannan gidan da ku ke ciki na Aaliyah ce. Aaliyah, Ahmad ya bawa gidan nan”

Gidan da Aaliyah ba ta zauna a ciki na cikakken shekara ba. Ta ya Ahmad zai ma ta haka? Fatima ta tambayi kanta

“Hajiya Fatima, ina so ku daure ku yi zaman lafiya tsakanin ku. Idan ki ka cire wannan gida da Ahmad yai wa Aaliyah kyautar sa Aaliyah ta yafe gadon Ahmad. Daga ke, ‘ya’yan ki sai Zaid ku kuke da wannan dukiya, kuma idan aka ce a raba kowa yai na sa waje ba za ku ji daɗi ba. Zaid shi kaɗai ne ɗa namiji dan haka ki bashi haɗin kai ya kula da ƙannen sa”  lawyer ya faɗi ya na harhaɗa takardun da ya nunawa su Hajiyar.

Da Hajiya Fatima da Inna duk ba wanda ya ce wani abu har Zaid da lawyer su ka fita a falon.

………………………

Sai da aka yi sati biyu da dawowar su sannan Mom ta shirya ta tafi Maiduguri. A wannan lokacin Zaid ya samu damar bincika ɗakin Mom. Ya jima ya na dube-dube a ɗakin amma shiru bai ga diary ba.
Ya zauna akan gadon ta ya na haki.
“Kodai Mom ta tafi da shi Maiduguri ne ko kuma Mom ba ta da diary?”
Zuciyar sa ne ya tuno ma sa ɗaya daga cikin drawers ɗin a kulle ya ke da key. Ya tashi da sauri. Ya nemi key ɗin wajen bai gani ba. It’s obvious duk sauran wajen ba a sa key ba sai last drawer ɗin definitely akwai abu mai muhimmanci a ciki.

Ganin neman key ɗin zai ɓata ma sa lokaci ya sa ya fita dan ya nemo guduma ya kwaɗe, ya san duk rintsi kafin Mom ta dawo zai sa a gyara ba za ta ma ganeba…

To his surprise wata jaka ya gani a cikin drawer ɗin. Tsohuwar jaka ce wanda aka yi yayinsu a irin 80’s ɗin nan. Ya sa hannu ya ɗau ko jakar tsaftsaf ta ke ba ƙura ko dauɗa a jiki. Sai da ya zauna da kyau a tsakiyar ɗakin sannan ya buɗe jakar. Diary guda biyu ne a ciki sai album. Album ɗin ya fara buɗewa yana ganin hotunan da ke ciki. Hoton farko na Mom ne lokacin tana jaririya sai da ya jima yana kallon hoton kafin ya cigaba da kallon sauran, cikin hotunan da ya ke dubawa ya ga harda wanda Aaliyah ta bashi. Sai daya gama kallon hotunan sannan ya jawo ɗaya daga cikin diary ɗin ya buɗe date ya gani a sama sannan aka rubuta *The beginning*
Rufe diary ɗin yai ya kwashe komai ya maida cikin jakan sannan ya ɗau jakar ya fita daga ɗakin…

Tana kitchen tareda Abba su na girki ƙaninta Abdul ya shigo ɗauke da wayarta da ke ringing.

“Z Wamako na kiran ki Anty”

“Abdul ka maida wayar ka ga aiki mu ke zan kira daga baya” ta faɗi tana ƙoƙarin saita nitsuwarta.

“Tun ɗazu fa ake kira” Abdul ya faɗi yana miƙa ma ta wayar. Tana amsar wayar kiran ya kuma shigowa. Abba ya ce ” ki je ki amsa wayar ki”
Haɗiye miyau ta yi ta amsa wayar tareda ficewa daga kitchen ɗin da sauri.

Minti biyar sai ga ta ta dawo fiskarta ɗauke da farin ciki. Abba ya kalleta ya ce ” waye *Z Wamako*?”

“Ehm. Abba ƙawata ce da mukayi makaranta ɗaya. Zainab….Zainab Wamako sunan ta”

Kamar faɗin Wamako ya tsikareshi lokaci guda ya furta *Wamako*

“Abba ka san wani mai irin sunan ne?”

Ya jima bai ce komai ba, hankalinsa ma ba ya wajenta. Sunan Wamako ya taɓo ma sa wani tabo da ke zuciyansa tsawon shekaru.

“Abba are you Ok?”‘
Yai firgigit ya ce ” yes, yes princess”…

…………………………

Ba ta sha mamaki ba da Abba ya amince da tafiyarta amma da sharaɗin  za ta dawo kafin ƙarfe shida na yamma. Ko ba komai za ta samu ta yi abinda za ta yi kafin nan.

Driver ne ya kaita har gidan su Nawal. Kamar yadda ta tsara. Da dreban su ya tafi sai ta kira Nawal ta fito da motar ta su ka fita. Har cikin compound ɗin gidan su Zaid Wamako ta shiga da ita, su ka rabu akan za ta kirata.

Kiran Zaid ta yi akan ta iso ya ce ta shigo ɓangaren Mom.

A zaune ta sameshi yana karanta jarida.

“Wamako da gaske ka samu diary ɗin?”

Hararanta yai ya ce “idan ban samu ba zan kira ki ne”

“Oh. Ina diary ɗin? Ka karanta?”

“Aaliyah ki ke ko wace, I dont trust you. Ki faɗamin miyasa ki ke bibiyar Mom ɗina”

Ba ta bashi amsa ba sai ta buɗe jakarta ta fitar da wani diary daga ciki ta ce “wannan diary ɗin shi ya sa na san wacece Mom kuma shine dalilin da ya sa na ke bibiyarta”

Kallonta yai na wasu daƙiƙai sannan ya ce biyoni.

Ɗakin Mom su ka shiga inda ya fito da jakar da ya gani a drawer.
Lokacin da ya fitar da abinda ke ciki Aaliyah harda ɗan ihunta.

Zaid ya ce “lafiyar ki kuwa”

Aaliyah ta ɗan yi gyaran murya ta ce “duk farin ciki ne ya jawo haka”…

A ƙasa su ka zauna bayansu na jingine da gado. Nan su ka fara karanta diary ɗin Mom…

 

 

Leave a Comment