TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*BOOK 1*
*Wannan Labarin tundaga farkon sa har karshensa Tukwaici ne kuma Sadaukarwa ne zuwa ga HALIMA YUSUF GWARZO(Besty) Amincin Allah su tabbata a gareki Allahu ya iya miki Halima Allah ya jibanci Lamuranki Duniya da Lahira Ameen*
_Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai_
*Intelligent Writer’s asso*
*🅿️01*
*GUMEL:Jigawa_Dutse*
_Area:Zango Street_
Friday 5:30pm
Ta jikin get din ta fara lekawa so take tagani ko da wani a Haraban gidan duk da tasan ba lalle ta samu gilmawar wani ba yau jumma”a kuma adaidai wannan Lokacin Duka mazan yara da manya suna masallaci inda Baba Mallam ke musu karatun yammah Matan kuma Kowacce tana cikin gida a irin wannan ranakun na Alhamis da jumma”a suke samun Damar Taimakama iyayen nasu Tunda Ranakun makaranta basa samun Lokaci da sun dawo makarantar Boko abinci kadai suke ci sai sallah da Haraman tafiya islamiya in suka dawo kuma Dare yayi sai Sallar mangariba sai zama yin karatun Tsakani mangariba da Isha”i,sannan in an gama sallar Isha”i kowa zai yi aikin makarantarsa,ko kuma wankin kayan makaranta ko Guga da Sauran aikin karfe 10na Dare kowa yake neman makwanci Saboda Kada a makara Sallar asuba da Shirin makaranta ba atashin mutum sau Biyu sau Daya na biyun kuma Da Duka ne zai sa ya tashi wannan Dokace ga Duk wanda yasan Daya Daga Cikin Dokokin gidan BABA MALLAM da BABA SA”IDU.!
Hankalinta ta Dawo dashi tana kare ma anguwan nasu kallo Shuru ba wani Hayaniya ta Mutane yara duk suna gida Manya kuma suna wajen aikinsu Kofar wani masallaci take Hanga Daga inda take tsaye Fuska ta yamutsa ganin Takalma nan Birjit a kofar Hadadden masallacin mai kama da aljannar Duniya.
Daman tasan yau Dole ne akwai karatun yammah shiyasa bata yarda ta Biyo ta gaban masallacin ba ta yanko Hanya duk da nisanta ta gwammace nisan da Haduwa da Zaluman dake cikin masallacin nan yau suyi bandashenta kamar yadda suka Saba..
Karamin tsuka taja tana gyara zaman Bakar Jakar bayan Dake makale a bayanta wacce ta Sagala Hannu Daya Hannun Daya kuma ta sakeshi.
Yarinya ce wacce ashekaru akallah bazata gaza shekaru sha biyar aduniya ba Doguwace wankan Tarwada mai Dauke da wasu manyan Idanuwa da Doguwar Fuska,kallon Farko Zaka mata ayadda take Motsa baki zakasan tana da Surutu da Tsiwa Sanye take da kayan makaranta na Wando mai Ruwan kuka da Farar riga sai Farin Hijabi da Farin Dankwali kafarta Cikin Takalmin makaranta na Combas samfarin na mata da Safa.
Akallon Farko in kayi mata zaka Fahimci yadda ta jigata,Tun daga yadda Fuskarta Duk ta Kode bakinta ya Bushe yadda kuma take tsaye bakin karamin get din gidansu mai kalan brown zakasan tana tantantaman Shiga gidan ne ko kuma tana Tsorom ta tarar da wani da bataso acikin gida.
Ita Kadai taja tsaki kamar Tsaka afili ta Furta”Ni ba tsoron shiga gidan nake ba..Ni AMINA Aminene tsoron Uban wa zan ji..?kwakwazo ne bana so da Hayaniya uwa uba bana son Yaya ta fito ta ganni ita Kadai ce nake gujema Rigimata..!
Tafada Lokaci Daya tana sosa giranta acikin Ranta tana Tunanin ko taje gidansu HANNE ne..?
Da sauri tace”Kai bama zani ba..Saboda wannan uwar yar saka Idon Yaya Abida..!
Tafada Lokaci daya tana Kallon Wani Makeken get din Daga gaba da Gidansu kadan wanda Jikin Gininsa Daya yake da wannan Kayattacen masallacin da na daga kaina naga ansakamai suna da wani Launin Fenti da larabci Cikin Sha”awa da Burgewa.
*SHEIK YUNUS ABDURRAHAMAN BAZANGA MOSQUE..*
Sannan abun mamaki Gabadaya Daga gidan datake tsaye har wanda take kallo mai hade da masallacin Duka suna Layi dayane juna jikin juna Fenti Daya Komai iri haka get dim ma da kofofi kamar duka gidan gidan mutum Daya ne saboda babu abunda ya bambamtasu illah mai jikin masallaci yafi girma da kawatuwa Sabanin da wanda Amina ke Tsaye awajen yake karami sannan bai kai wanchan abubuwan More rayuwa Daga Ginin ba ammh bayanan komai da komai iri Dayane babu abunda ya bambamtasu.
Tagama Tunanin bata da wata manufa yanzu banda tayi shahada ta kutsa kai cikin gida haka kuwa akayi Da karfin gwiwanta ta Tura kofar get din ta Shiga gidan maimakon na Hangi wanchan gidan sai na Fahimci Daga ciki katanga ta raba Tsakanin Gidajen.
Mota Dayace aharaban gidan wata Siyana ce,Motar da ake kai su makaranta ce wani Lokacin in waccan babbar Macapoli din bata da lafiya ko kuma wani abu ya faru daman ko ABA bai cika Parking din motarsa anan ba yawanci yafi ijiyeta a haraban Gidan Baba mallam Saboda yawancin Saukarsa sai ya fara isa chan kafin ya iso anan Ko Yaya JA”AFAR bai cika ijiyar Mota anan ba Komai su sun saba gudanar dashi Bangaran Baba Malam din Daya zame musu tamkar wani bango abun Jigina da alhafarinsu.
Wani kofa naga ta shiga mai Dauke da Dogon Koridin Dayaji Interlock ko”ina,Sannan yana Dauke da Dakuna Hudu ajere suna Kulle da Kofofi
Daga gani Dakuna ne na mazan gidan ko baki indan hakan ta kama,
Kafin inga ta kara ganin wata Kofa Da karfin gwiwanta ta Tura kofar ta shiga sallamar ma acikinta tayi ta Ba kowa a tsakar gidan nasu wanda ba mai Fadi bane Sosai Daga gefenta kuma Ta hangi HAMIDA tana Gaban Famfo botiki ne a Gabanta tana wanke Kayan makarantar.
Dagachan yammh kuma Kitchen ne Babba Daga ganin yanayinsa zaka Fahimci haka sai daga chan Hannun Hagunta kuma Tiolet ne guda Hudu na Waje Biyu na Wanka Biyu na Lalura sannan Daga gabas dinta kuma Jerin Dakuna ne Guda Hudu,Daya yana nesa da ukun wanda ke Rufe Dakin Aba kenan mai Dauke da Ciki da Falo,Sai Dayan kuma Katon Dakin su ne mai Dauke da Falo kadai ammh babba ne Tun zamanin su Yaya Jalila adakin kowa ke cin yayinsa kafin Aure ya Dagasu har zuwa yanzu da suma suka taso suna cin nasu Lokaci.
Sannan Daki na gaba kuma Dakin MAMANMU CE mai Dauke da Ciki da Falo da bayi sai Dakin kurya kuma Dakin YAYA ce shima kamar na Mamanmu haka yake Daga bakin Dakunan anyi Rumfa Babba wanda ya bada inuwa sosai Daga gaban Rufar kuma akwai katuwar Bishiyar Umbroller
Ko”ina agidan yana Tsabtacene duk da Interlock ne aduka Tsakar gidan ammh bai hana ka gansa kal ba ta tabbata Hamida tayi aikinta kenan Saura ita Daga chan kuma wajen bayika igiyace Doguwa Cike da Shanyan irin kayan makarantar Dake Jikinta.
Cikin Lokaci kadan tagama Nazarin Tsakar gidan ajiyar rai ta sauke Yaya bata Tsakar gida tana Dakinta bari ta Lallaba ta shige Dakinsu ta Sauke gajiyarta kafin ta fara amsan Korafin da kwakwason yan gidan nan akanta da Kullim baya karewa kara Hade ranta Tayi saboda bataso wani ya mata mgana ma ayanayin Datake ciki.
Ita Zainab isa zata rainama Hankali..?tasan ta bata shiri da makaryaci mara Cika alkawarin Bata da Mutumcin in aka Shiga harkanta Tasan bata da kudi Ranar ita yau a makaranta ta ari kudin Break dinta..?ranar haka ta Dawo makaranta ko Biyar bata kashe ba Tana ganin Hamida na kashe kudinta itama ko oho haka take duk da karancin Shekarunta bataso ka Roketa abunda take dashi bata baka ba Zainab isa kudin Mashin dinsu na Ranar da zasu koma gida aka Sace acikin aji,ita da kannenta suke zuwa makarantar wata Unity school dake Cikin gari ne taji Tsausayinta yasa ta ara mata kudin Hannunta naira Hamsin ta Hada dana Hannunta da Niyyar Ranar jumma”a zata kawo mata kudinta,Amina tana girmama alkawari mai Saba shi kuma bata shiri dashi yau Zainab isa batazo makaranta ba ita kuma ana tashi Tana ganin Direban su Mallam Idi yazo Daukansu ta Boye tana ganinsu Hamida da jawaad suna ta Nemanta Ya Shamsu nata Muzarai ta Sulale tayi amfani da kudin Breakdinta da bata kashe ba ta hau mashin taje gidan su Zainab isa ai tasan gidan Saboda sun Taba zuwa gaisheta ida yan ajinsu Lokacin data kone da ruwan zafi.
Sai dai kash tana zuwa ta iske gidansu a kulle wani yaro ta hadu dashi nan waje shi yake fadamata Zainab basa nan sun tafi garinsu Zaria yau da Safe.
Ranta ya baci ta Cizi yatsa ta kudira aranta sai ta Gumdumama Zainab rashin Mutumci bata da ko asi ahannunta yasa ta tako a kafarta Tunda anguwan su Zainab Hadeja Road har anguwansu Zango Street.
Ga yunwa ga kishi ga ba sallah ba Salati iya wannan kadai ya isheta batason kuma adameta da wata mgana.
Ko barayin da Hamida take bata kallah ba Duk da tun shigowarta ta Saki abunda take yi ta mike tana kallonta Cikin mamakin karfin Halin Amina.
Sai da taga ta wuceta zata shiga Dakinsu yasa tace”Ke kam Amina ina kikaje an tashi makaranta muna ta nemanki bamu ganki ba..?Anya Amina baki gudun mgana kullum Aba da Yaya mgana suke akanki naga hakan ma kara miki Dadi yake yi..?
Amina tana jinta bataso ta waigo ba, Saboda bazata mata kyau ba Daga ita har Hamidan Tsakaninta da ita Wata Uku Cur..Kamar bata girmeta ba in Na samanta sun mata mgana ta Ragamusu Hamidan bata isa ba
Ganin in ta tsaya tankata zata kara bata Lokaci yasa ta kara Sauri ta saka Hannu kenan ta Daga Labulen Dakinsu Taji Hamidan na Fadin”Tukunna ma ina kike je..?
Ranta ya kara baci ga gajiya ga yunwa ga kuma wani banzan kallon da Ya Zulaihat da ya Zeenatu Dake Cikin Dakin kowacce kan gadonta na katako kamar na yan bording suke jifanta Dashi ta kasa gaba ta kasa baya.
Kamar Daga sama taji Ya Zulaihat na Fadin”Shigo ki fadamana Gidan Uban wa kike je bayan an tashi makaranta..!?
Bata gama Rufe baki ba Yaya Zeenatu ta Dauka da Fadin”Kema kinsan bazata taba fada ba wannan mai Taurin kan tsiya..Duka ne kadai yaran data sani kuma yau sai kin Daku..Domin ba Dadewa Ya Jafar yazo ya Tambaye ki muka Fadamai gaskiya shida Ya Nasir suka shigo kuma yadda suka Fita yau in s suka kama Dukanki sai na Lahira yafi ki jin Dadin Sakarya mara Tunani..!
Ta karishe Fada tana Hararanta kafin ta saki tsaki ta Cigaba da Duba Littafin Turancin dake gabanta Fuskarta Kaf irin na Hamida ne sai dai Amina tafi su haske ammh har Zulaihat din suna kama ta jini ita Amina manyan Ido ta Fisu da rashin jiki.
Har Duhu Amina take gani Saboda yunwa da gajiya ga bacin rai bataso ta shiga Cikin Dakin suna Cigaba da yaba mata mgana tasan sai ta tankasu kuma basu da imani Taruwa zasu yi suce zasu Daketa tasan bmai Centonta sai Mamanmu in ta Yaya ne su kasheta ita kuma bata iya Shuru da bakinta wanda ya fadamata goma sai ta Fadamai ashirin.
Shawaran canza Daki tayi da Niyar Shigewa Dakin Mamanmu ta Saki Labulan Dakinsu tana Fadin”Duka ai baya kisa..Dayana kisa da ko Burbushin Amina ba”a samu ba..Kuma ni ba Sakarya bace Ehe..!
Tafada tana kunkuni Zulaihat Dake Dakin tace”Eh me kike cewa ne..?
Zeenatu Wlh Zaginki tayi..!
Tafada Cikin takaichin yadda Amina take so ta zame musu ciwon kai acikin gidan ko Aba bata ce Amina na jin tsoronsa ba.
Zenatu tayi Falati da Zanen datakeyi wanda Bilogy teacher dinsu ya basu Doguwar rigace ajikinta ta Fice tana Fadin”ki barta bakinta zan fasa wlh..Zatasan wa take ma rashin kunya..!
Tana daga kwancen tace”Uhm..Ki Dirji bakin gudun Reni ammh nasan ko kin gama bakin Amina bazai taba mutuwa ba..!
Tafada Lokaci daya tana girgiza kai aranta take fadin Allah ya shirya Amina
Zeenatu ta fito Daga Dakin Daidai Lokacin da Hamida take fadin”Mgana fa nakeyi Amina..?gwara ki fara fadamin Inda kika Tsaya na samu yadda zan kare ki agaban Ya jafafar yau.!
Azafafe Amina ta Dago Daga Nufar Dakin Mamanmu datayi niyya Jakarta ta Sauke Saboda Jidalin Dake kanta bazata iyasa da wannan nauyin ba,Manyan idanuwanta ta Sauke kan Hamida tana Fadin”Hamida…Hamida..Hamida Sau nawa na kiraki..?
Hamida na yar dariya tace”Kamar sau uku..!
Amina ta tareta da”ba kama bace..Sau uku na kiraki saboda ki gane girman Warning din da zan miki..Hamida ki Fita Daga Rayuwata Wlh..Ina ruwanki da inda naje inace ke bagaki kin Dawo gidan ba..!da kike fadin ki kareni gaban ya Jafar na sakaki ne..?ke kika saka kanki kina kokarin kare abunda bazai taba karuwa ba Hamida Ni Amina wake sona..?Aba kullum Amina mai Laifin ce awajensa Hakama Yaya kowa baya fadamin abun Alheri akaina Daga Mamanmu sai Baba Mallan ke sona..Sai Hajiya Baba da Hanneta bandasu fadamin me yabon Amina..?kinga kuwa ko Icce aka sakama baki haka Lalacewa yake yi ballatana Mutum kamar ni to bari kiji na Fadamiki ni AMINA SA”IDU GUSAU kainuwa ce dashen Allah baki ko Duka baisa yaga karshena ba, ballatana ganin baya na saboda haka ki adana kalaman bakin ki kuma Rufemin Dattin bakin ki in kuma ba Haka ba ki jirani na ci na koshi in Jidali kike nema na Rantse da wanda Raina ke hannunsa kin Tare ni kin sam.u..!
Tafada Lokaci Daya tana Girgiza kugunta kamar wacce take Shirin Dambe,Zeenatu Data fito tsayawa tayi tana kallonta Hamida kuwa cigaba da wankinta tayi tana Fadin”Allah baki Hakuri..Kya yi bayani in kika shiga Hannun Ya Jafar..!
Wani Tsaki taja kafin ta Duka tana Daukan Jakar makarantar tana Fadin”In yazo kada ya bar Amina da Rai..Yau aka saba ko yau za”a kareta Hamida..?da duka na kisa da yanzu Amina ta Dade a kushe..!
Dauummmm…!
Taji Saukar Dunkullen Dumdu abayanta kafin ta karisa mganarta Dumdum dayasa sai da ta Duke kasa kan Jakarta tana bankare baya saboda taji Saukan Dumdum a bazata.
Zeenatu tace”Yauwa Yaya..Don Allah Daketa bari na karyo Iccen Bishiyar Nan ki Daketa da ita tunda tace Duka baya mata komai..!
Tafada tana Nufar Bishiyan Dake Haraban wajen ai ko ba”a Fada ba,Tasan Hannu Dayake ke da wannan Dumdum ba tun yau ba Tun tasowarta bata iya Haddace dukan kowa ba, da an Dageta taji zafi ya Huce shikenan ta manta ammh Duka Daya Duka Daya daga Hannu Dayane bazata taba manta yanayin ba bata Cika Duka ba mai Hakuri ce sai dai In ta saka hannu ta Duma maka Dukanta Har Ka kwana bazaka manta dashi ba Hannu Dayane mai kama da goma
YAYA CE..ita kadai ce Amina bata saba da Dukanta ba kuma Dukanta ne kadai ke saka Fitar Hawaye a Duka Idanuwanta Aba bai duka sai dai Fada Ko su Ya jafar sai dai su gaji su kyaleta zatayi ihu ammh in ka Duba ba Fitar Hawaye ko Daya Amina akwai Taurin rai da kafiya kamar kafuran Farko..!
Dagowa tayi Idanuwanta na Cikowa da Hawaye ta Sauke kan Fuskar Yaya kamar an Tsaga kara yadda kukasan yan Biyu sai dai bambamcin Amina yarinya ce Yaya kuma Shekarun sunja akallah 49 aduniya ammh Hatta Shape din Fuskarsu iri Daya ne tafi Amina Haske sosai ita din Fara ce ammh ba Tar ba.
Cikim bacin rai take kallon Amina rai Daya..Rai kwara Daya da Tunda ta Haifeta bata Huta ba Amina..Amina ta Addabi kowa acikin gida da waje ba inda ta bari ita kadai take so ta jazamusi hawan jini da Ciwon zuciya ita kadai TA FITA ZAKKA..cikin Ya”ya goma sha Biyu Dake gidan kowa ya gama lafiya banda Amina kowa Amina tagaji takai makura ga kauda kanta kan Lamarin Amina.
Tana Kitchen Sanda Amina ta shigo Taje Duba Wani mganin Ciwon Ciki ne Ararrabi Data ijiye Cikinta ke Juyamata take so tasha..Tun Sanda yaran suka Dawo suna Fadin basu ga Amina ba takasa mgana to me zatace…?wannan ai ba karon Farko bane da Amina tataba batan Dabo a makaramta ba,akwai Lokacin da har an baza Cigiya agidan Radio sai gata ta Dawo wai taje Birthday din yar a Jinsu kaninta ake ma Birthday Bakimciki yasa Aba dinsu ya kamata yayi mata Duka ammh baisa ta Daina ba Amina kanta Tsaye take aikata Duk Abunda taga Dama,a kananun SheKarunta Duka ya Zame mata sabo eh mana Gaskiya ta fada Da Duka na Kisa da an kasheta ita kam Tin tana Daukan Amina aljanu gareta har ta yarda ma kanta Lafiyanta Kalau Amina Zakka take so ta zame musu Cikin gidan nan da Zuru”a gabadaya.
Koda ta Haifesu kaf ya”yanta Ba ita take Renansu ba BALARABA ce Mammansu banda Jafar duka ya”yanta ita take Renonsu ta yayesu in ba Fadamaka akayi ba bazaka Taba Cewa Yaya ta Haihu ba Duka yaran Gidan komai nasu Mamanmu Mamanmu Kowa mamammu In kaji Yaya sai in Mamanmu ta sakota Cikin Shirginsu komai na Tarbiyan yaran da komai na Rayuwarsu na Hannunta ne sai In ma ta musu wani abun take sani Daga baya ba ita kadai kaf Dangin Sa”idu suna girmama Balaraba Kuma sun saka mata suna ita mai karamci ce Taci wannan sunan Domin ita Maman kowa ce.
Bazata kyale Amina ta zautataba kullum Kokenta kan kare ma Amina ne,Mganar Rauninta kan Amina ne Koda yaushe Cikin nema mata Taimako take gani take Aminar ba ita kadai bace kullum kalamanta kenan
“Yaya ku daina Ganin Laifin Amina..Adaina Dukar min Ya’a yaya ba Laifinta bane.. ku lura kamar Amina ba ita kadai bane ni dai ina Zargin Aljanu suka taba Amina Tun tana ciki..Yaya bazan taba barci ba sai naga Amina ta dawo kamar kowacce y’a acikin gidan da watarana Zaku yi alfahari da ita..!
Lokacin datake Fadar haka kukane acikin Ranta da Zuciyarta tasha kuka Har da majina kan Amina in ana Dukanta haka zata zo ta tare har ana Samunta tana Fadin”Jafar ka bari..Kada ka sake taba ta nace..!
“Mamanmu ki barni..Ki bari na Illata wannan rayuwar kafin ta kashe mana Uba da Bakaken Hallayarta..!
Rike Amina take ajikinta ta Fashe da kuka tana Fadin”To in bazaka bari ba sai dai ka Hadamu duka ka Dakemu..Ammh bazan bari ku illatamin yata ba..!
Ita ta Haifi Amina ammh wannan Raunin Maman Amina ke Daukansa bata Cika maida kai kan lamarin Amimar ba Tunda bata wata shakuwa Tsakaninsu,ammh yau taji tana so ta Nuna ma Amima ta bar wasu Zukata su Huta ta Duba Raunin Mamarta akanta ko Saboda ita ta sauya wannan Bakin Halin nata.
Kallon Datake mata Da kuma Tuna wasu abubuwan yasa Hawaye suka Cika kwarmim idonta.
Amina na Dafe da baya ta Bude tace”Yaya..ki ts
Bata kai ayaba Yaya ta kaimata mari wannan karon ya Sameta da Karfi Har sai da ya fito da Zulaihat Daga Daki da Gudu Hamida ma ta bar wankin da Sauri ta karisa tana Fadin”Yaya kiyi hakuri..!
Har Zeenatu Dataje Karyo Icce sai gata ta dawo Wlh bada gaske take ba Bata Dauka Yaya zatayi Duka ba,Duk da Rashin jin Amina yarinyace mai Shiga rai sannan Kaunar junansu ajininsu yake koyaya wni abu ya samu Daya Dukkansu sai sun ji wani iri.
Amina na musu rashin kunya kunkuni da Sauransu suna zugawa in za”a Daketa ammh akazo ana Dukanta sun Rika bada Hakuri kenan Hamida mai Saurin kuka Harda kuka take sai an gama Dukan tazo tana Daga Aminan sai ta Kalleta tayi Dariyan dauriya da yaki da Abunda take ji tace”Wai Kuka kike Hamida..?kuka fa..Kima Daina kuka Amina ce Aminene ce badai mutum ba sai ta Allah..!
Hamida na sharan kwallah takan Dungure mata kai tana Fadin”To kidaina wasu abubuwan don Allah Amina..Ba domin kowa ba domin Aba da kuma yadda muka zama Zuru”ar gidan bazanga..!
Amina alokacin sai dai ta kalleta tana Fadin”A”ah fa..Ni bansan laifin da ake yawan Fadin Amina nayi ba. abunda dai nasani shine Amina..AMINA SA”IDU Haka Allah yayita..Ko ta Sauya shi Hali ai zanen Dutse komai zai Sauya da Mutum banda Halinsa..!
Yaya ce ta katse ma Hamida Tunaninta Cikin Fitan Bacin rai da wani bakinciki Yaya ta Rufe Amina da Duka kota ko”ina tana Fadin
AMINA Yanzu abunda kika Zabama rayuwarki kenan..?So kike kamar yadda kika saka ma ABA dinku Hawan jini nima ki sakamin ko..?Gidan Uban wa kika je bayan an tashi makaranta..?Duka Sauran yan”uwanki sun gaji da nemanki sun dawo..Saboda ke kin FITA ZAKKA agidan nan sai abunda kika dama kike yi ko Amina..?Bin Maza kika fara..?Nace bin Maza kika fara..?Wlh ina Tsausayinki Ranar da Bakinciki zai kai Alhaji kasa Nima kin Sakani kuka ba sau daya ba sau Biyu ba, Amina ki kashemu ki Huta nace ki kashe mu ki huta..!
Amina bakinta bai yi Shuru ba Fadi take”Ni bana bin maza..Wlh Allah Amina bata bin maza ki yarda dani Yaya..!
Take fada tana Tsiyayan Hawaye,Hawayen da Dukan Yaya ne kadai da kalamanta kan saka aga Fitarsu daga Idanuwan Amina.
Bakinta ta Bike sai da ya fashe cikin Takaoci tace”Kina Kara batamin rai in ina mgana kina mgana..Amina Bakin ki na Daya Daga Cikin Nakasunki bakin ki baya iya mutuwa koda girman Laifinki yafi girman Duniya ne..!
Amina ta sharce jinin bakinta tana Fadin”Yi hakuri Yaya..!
Haka kawai take fada tana kuka sosai abu Daya yafi Tsaya mata arai Cewar da yaya tayi tana bin maza tasan Tana da kafar yawo da Bin Gidajen kawaye gayyar ko ba”a gayyaceta ba Amina sai taje tasan tana da rashin kunya da Kafiya da Taurin kai da Tsokana tasan bata da Kirki wani Lokaci ammh Wlh maza basa gabanta Tsakaninta dasu sai goge reni Domin har ayanzu Amina bata jin kunyar zagewa ta Chasa wanda yayi mata shiyasa kaf ajinsu na Boko da islamiya suke shakkarta bata Duba Jinsu ita wanda yace mata kole ne zatace mai cas ammh bata bin maza ita ba yar iska bace!
Gabadaya jikinsu Hamida yayi sanyi Amina na kuka tana Fadin”Kiyi hakuri yaya..!
Ita uwa Dabam take acikin Ranta tanajin kamar Amina ta koma Ruwan sanyi da Yaya zata Daina damuwa akanta Mamanmu zata Daina kuka akamta ammh ko ta Dauki alwashin abanza da ta gama Damuwarta za taji kamar kara mata wasu abubuwan akeyi wani Lokacin ita kanta Har mamakin irin Taurin zuciyarta take ko na wani kato albarka.
Dukkansu Hakuri suke bama Yaya batace komai sai kwallah Data ke sharewa Zeenatu ne ta Ruga Dakin Mamanmu ta taso ta wacce take kurya tadan kwanta Sama Sama taji Zeenatu na Fadin”Mamanmu..Mamanmu..!
Bude ido tayi tana Fadin”Zennatu meyasa kika tasheni..?nasan barcin yammah bai da dakyau..Kaina ke Saramin..!
Da sauri Zeenatu tace”Daman nasan baki ji ba.Yaya yau ranta ya baci gashi chan tana kuka tana Dukan Amina..!
Ai bata gama ba ta ingize Zeenatu ta Diro Daga kan gado Dankwali a Hannunta Zaninta na neman Faduwa ta Fice da gudu Zeenatu ta Bita da kallo ta Girgiza kai.
Tana fitowa ta isa ga Amina ta Rumgumeta tana ganinta ta riketa tana kuka take fadin”Mamanmu don Allah ki fadama Yaya bana bin maza Wlh ban bi maza gidan su yar Ajinmu naje Zainab isa kudina naje amsowa na iske sun yi tafiya ba kudi a hannunsa saina tako akafa mamanmu ammh kiji fa abunda yaya ke..!
Bata karisa ba ta Rufe mata baki Cikin Rauni tace”Basai kin fada ba..Nasanki Amineene..bazaki fara Halin da bana ki ba..
Share Hawayen Daina kuka matukar mamanki na Raye baki ba hawaye har Abada..!
Tafada tana share mata kwallah Cikin kauna Yaya kada kai tayi ta bi hanyar Dakinta tana Fadin”ki Rika samun waje acikin ranki kina fadama Amina gaskiya..Ko tana so ko bata so Ta fita zakka acikin gidan nan..!
Daga haka ta bankade labule ta shige Dakinta Mamanmu bata Damu ba mikewa tayi tana Dago Aminan Lokaci Daya tana Fadin”Hamida Dauki Jakar Amina ki kaimata Wajen Dirowarta..Ke Zeena zubo mata abincinta a filet ki hado mata da Ruwa da Zobo yanzu adakina..!
Zulaihat dake gabanta ta kallah kafin tace”Matsa ki bani waje..!
Zulaihat ta kalleta kafin tace”Mamanmu..!
Rai bace ta balla mata Harara tana Fadin”Ki yi wanke wanke..Gobe Aminan tayi..ku kuma kuyi abunda na sakaku..!
Daga haka ta shige Dakinta Dauke da Amina Dake kuka kamar ta maidata Ciki Hamida ta ja Jakar makarantar Amina zuwa Dakinsu Dirowansu kusa da juna ne Domin gadon su ma ahade yake ita tana Sama ne Amina na kasa saman gadonta ta ijiye mata ta Fice ta koma bakin Famfom ta Cigaba da wankinta ita kuma Zeenatu ta shiga Kitchen ta Bude Cooler ta Dibo Taliyar da Kifin Dake ciki ta Bude Fridge ta Dauko Ruwa da Zobo ta Fito zuwa Dakin Mamanmu.
Ita kuma Zulaihat ranta bace ta Fara Fito da kwanukan da aka bata akichen Zuwa bakin Famfo.
Hamida Dake Dauraye kayanta Tace”ki barshi Anty Zulaihat in na gama shanya zan wanke!
Kai tsaye tace”Yauwa.Daman duk Ranar da Amina ta kwaso jidalinta yafi Shafarki..!
Daga haka ta wuce Bata bi takan Hamidan Dake Dariya ba tana Fadin”Amina ce Anty Zulai..Wlh ko Aba baya iyawa da jidalinta ko Ya Jafar gajiya yake..!
Take fada tana Dariya shanyan kayanta tayi tazo ta fara Jika kwanukan sai ga Amina ta fito Daga dakin mamanmu kallonta tayi itama ta kalleta kai tsaye tace”Gobe da Safe har zuwa rana zan yi wanke wanke..Zan rama miki kada kice kin Dauki Jidalin Amina..!
Tafada tana Share bakinta Daya kumbura Hamida kai kawai ta kada Amina ce sai tayi mgana.
Ta fara wanke wanke sai gata tafito jikinta Riga ce doguwa na Atamfa sai Hular Dake kanta Kayan makarantarta ne ke Hannun ta Zata wanke saboda gobe Asabar suna Hadda Tun Safe sai yammah,haddar tasu daya take da islamiyan shiyasa ana tashi Uku da Rabi ayi sallah aci abinci a shiga islamiya itama Madaratul Umar Bin kallab din mallakin Baba mallam ce snnan gabadaya malaman makarantar ya”yansa ne da Dalibansa har ya jafar yana koyawar ajin manya Wato Jss1 da ajin matan aure ya Nasir da ya Uzairu da ya Nazim Duka suna koyarwa anan,Sai dai yanzu Ya Nazim da ya Uzairu suna Makarantar jami”a sai sun dawo Hutu suke zuwa Yaya shamsu ne shima Dukka da kananun shekarunsu Kansa na ja yayi Sauka da Hadda ga Sauran Littafai kai duk ya”yan mallam haka suke akwai kwanya kuma ance duk Kwanyarsu basu kai Babban DA’N MALAM ba dake jami”ar madina yana koyawar chan yake zaune da iyalansa sai karshen shekara suke zuwa gida sai dai Sakonsa akai akai yana zuwa ga mahaifansa.
Har ta fara wankinta ta gama bata cema Hamida komai ba itama batace mata ba Tana idar wa kenan tana Shanya Sallamarsu Ya Jafar da da Ya Nasir ta karade gidan da Sauri Amina ta juya tana kallonsu Fes suka Hada ido hudu da Ya Jafar wata uwar Harara ya Zuba mata yana fadin”Gama Shanya..Ki Tsaya a inda kike ki kama kunninki..!
Nasir Dake gefensa yace”in kin gama kama kunnin ki hada da Tsallon Kwado..Yau zaki gane iskancinki kadan ne Amina..!
Daga haka suka wuce lokacin suna amsa gaisuwan Hamida Jawaad dake bayansu ta kallah yana mata Gwalo yaro dan shekaru goma.!
Amina Rai ta bata a fili ta Furta..”Azzalumai Biyu kenan..Allah ya Hadasu abota kamar yadda Muguntarsu tazo Daya..!
Hamida ta kallah wacce ta zuba mata ido Hararanta tayi da karfi Tana Fadin”Bana son gulma Hamida..!
Kanta ta kauda tana Dariya gama Shanyar tayi ta koma bakin kofar gida ta Coge taki yin abunda akace sai taji motsi sai ta yi kamar ta Duka ta kama kunni sai taga basu bane sai ta Mike Dakin yaya suka fara shiga.
Tana chan tana Hararan Hamida suka Fito Da sauri ta Duka ta Daga hannunta Sama Jafar ya kalleta Cikin wani yanayi kafin yace”Kada kiyi..Kiga yadda zan yi dake agidan nan..!
Nasir kuwa wayarsa yake latsawa hannanunsa Daya Dauke da Littafan Karatu na addini Dakin mamanmu sukayi sallama suka shige Amina ta bisu da Harara afili ta Furta”Duka ai baya kisa..!
*Janafty*
*15/07/2022*
*TA FITA ZAKKA..!*
_(Aminene)_
*BOOK 1*
*Wattpad:JamilaUmar351*
*Mallakar:Janafty❤️*
*SADAUKARWA:ga Halima yusuf gwarzo (Besty) Alherin Allah ya kai miki a dukkan inda kike*
_Wannan Labarin Jinjina ce gareki *SUMAIYYA ABDULKADIR TAKORI*(Takorinmu) Allah ya raya miki zuru”a ya tabbatar da aminci da zaman Lafiya agidan auranki_
*🅿️02*
Hamida na wanke wankenta Ammh Rabin Hankalinta na kan Amina ganin yadda ta koma ta zauna Dirshan a kasa Tana wani cin mgani kamar babu abunda ma ya Dameta yadda take zaune kamar tana zaune acikin Daki ne cikin Natsuwarta.
Abu daya ke bama Hamida mamaki bama ita ba kowa da kowa Dake gidan nan yana mamakin yadda Amina bata jin tsoron Ya Jafar da Ya Nasir wadanda kaf gidajen sune manya kuma su ke hukunci da kuma Daidatuwar Tarbiyansu bama su ba na Sama dasu su ya Zeena suna Tsoronsu da basu girmansu banda Amina Har yau har gobe bata taba ganin Wannan Tsoron da Shakkarta acikin Idanuwanta ba.
Tagama wanke wanken kenan taji an fara kiran sallah Daga masallacin gidan Mallam Daidai da fitowar Zeena Daga Dakinsu kanta ba Dankwali sai akayi rashin Sa”a Lokacin Ya Jafar da Ya Nasir suka fito Daga Dakin Mamanmu tana Biye dasu abaya.
Bata da yadda zatayi sun riga sun ganta Ya Jafar ya Duka yana Saka Takalminsa mai igiya Hamida Ta kalli Amina Dake zaunenta tace cikin Rada..’Ke Amina ga su nan fa sun fito..!
Daga ido tayi ta kallesu kafin ta mike Tsugunne ta daga hannunta sama kamar gaske.
Ya Nasir ne ya kalli Zeena Dake kokarin komawa Daki Cikin Muryansa mai Cike da Iko yace”Wacece nan take yawo ba Dankwali..?
Ba yadda Zeena zatayi Dole ta juyo tana Fadin”Nice ina yini Ya Nasir..!
Harara yayi mata kafin yace”Dillah wuce ki saka Dankwalin ki..Kuna manya kuda su Hamida zasu yi ku musu Fada..!
Bata ko kara mgana ba ta shigo Dakinsu Daman Dakin Mamanmu zata shiga ta Dauko littafinta jiya ta manta Dashi,bata zata har alokacin basu tafi ba Shiyasa ta fito haka.
Tana Shiga Dakin Zulaihat data mike Tana Tatattara Littafanta tace”Kema kin samu Rabonki kenan..!
Zeena bata iya mgana ba Umh kawai tace ta Dauki Damkwalin Abaya ta saka lokaci Daya tana Tura kofar Bandakin Dake Daknsu ta shige Tare da Rufowa Zulaihat ta Bita da kallo Lokaci Daya.
Achan waje kuma Nasir ne ya kalli Hamida yana Fadin”wai sau nawa zan ce kudaina zama bakin Famfo nan da mangariba..?baku gujema Lafiyarku ko .?
Kanta na kasa tace”Ai nama gama yanzu zan tashi ina wanke wajen ne..!
Mamanmu ta kalleta tana Fadin”Wato Zulaihat ke ta bar ma aikin kenan..?gobe kuwa sai tayi shi..!
Tafada Daidai Lokacin Data hango Amina da Sauri tace”Amina wa ya sakaki kama kunni da mangariban nan…?
Jafar kai tsaye yace”Nine mamanmu..Zata fadamin inda ta Biya bayan an tashe su daga makaranta..!
Mamanmu ta Bude baki zatayi mgana ya Rigata da Fadin”Don Allah Mamanmu kada ki saka baki..Bazan Daketa ba in har ta bani amsar Tambayana..!
Mamanmu tace”Kada ku maida Amina Jaka mana..Jikinta fa ya Saba Da dukanku..!
Bai Saurareta ba ya Nufi Aminar Nasir ne ya tsaya yana Fadin”Wake ja Mamanmu..?yarinya Daya Tal zata zame ma kowa ciwon kai..!
Mamanmu tace”Sai addu”a..nidai kada ku tabamin D’iya..Nasan ku da Duka kamar kun Hada kauna..!
Yana jinta yar Dariya kawai yayi Hamida kam data gama kwashe komai ta maida Kitchen Dakin Yaya ta shige ta sameta Har ta Kabbarta Sallah Cikin kurya ta shige ta samu Jawaad na saka Jallabiya da Sauri yana Fadin”Ya Hamida Don Allah su Ya jafar na nan..?
Hararansa tayi kafin tace”Bansani ba..Sai ka fita kagani..!
Dariya yake yi kafin ya Fice ta bishi da kwafa tana Fadin”Zaka Dawo zakasan wanda kake ma Dariya..!
Daga haka ta shige Tiolet din Dake Cikin kuryan Dakin na Yaya.
Jafar gaban Amina ya Tsaya yana kallonta kamar yadda itama take kallonsa abun na bashi mamaki ba kowa ke iya Hada ido dashi ba Saboda kwarjininsa da yadda kannensa ke tsoronsa ko Jadwa Datake Daga shi sai ita bai jin tana kallonso ido Cikin Ido.
Kai Tsaye Cikin Kakkausar Muryansa yace”Da aka tashe ku makaranta ina kika Tsaya..?ko nace ina kikaje..?
Amina kai tsaye tace”Gidan yar ajinmu Zainab isa..!
Da mamaki yace”Yaya ta aikeki ko mamanmu..?ko Aba..?
Itama Cikin dan mamakin ta Waro Idanuwanta kafin tace”Kudina naje amsowa..!
Tafada tana Dan Tura baki Hannu yasa ba tsammani ya bige bakin yana Fadin”Watarana sai na rabaki da Hakoranki na gaba..!
Nasir Dake bayansa yace”An fa Tada sallah Jafar..!
Jin haka yasa ya ja kunnenta Har sai da tayi kara Cikin Fada yace”Kije kiyi sallah ki jirani kafin na wuce zan dawo ban yarda da mganarki ba..!
Sannan ya saketa gefe ta koma tana Sosa kunnenta Nasir ma sai da ya bata Rankwashi mai Zafi sannan suka Fice Sai ga Jawaad ya Fito ya Bisu abaya da Gudu yana ma Amina gwalo,Tana Dafe da kanta Dataji zafin har Tsakar kanta tace”Yaro in na kama ka sai na Lahira yafi ka jin Dadi..Na fika Jidali da Fitina..!
Tafada kafin ta mike tana Kakkabe Jikinta nan bakin famfon ta karisa ta Bude ta fara alwala sai da ta gama kana ta shige Dakin Mamanmu ta isketa kan Darduma tana Lazimi..!
Kai Tsaye Amina ta wuce uwar Dakinta tana Fadin”Mamanmu na Dauki Hijabinki Cikin Wardrope dinki..nawa suna Dakinmu kuma bana son shiga..!
Tafada Muryanta Cikin yar shagwaba Tana Daga zaunen kan Darduma ta Daga mata kai Ciki ta shige ta Bude makeken Wardrope din ta Bude barayin Gogaggun Hijaban Mamanmu ta Dauko guda Daya ta fito tana zuwa Mamanmu ta matsa gefen Darduman Datayi sallar duk da Shinfidadden Cafet din italiyan din Daya malalen Falon
Tana cikin Sallar mamanmu ta Fice kuma Tana da tabbacin Dakin Yaya zataje domin duk bayan mgariba da isha”i adakin take yinsa suna Hira da Tattauna wasu abubuwa Kamar ba Kishiyoyi ba..
Tana Idar da Sallar ko dan addu”a bata Tsaya yi ba ta mike Zaraf kamar an tsunguleta mganar Ya Jafar take Tunawa Dayace zai dawo duk da tasan da Wahala ya dawo yau sai gobe saboda akwai wa”azin da Baba mallam ke yi kowani bayan Sallar mangriba zuwa Isha”i sannan in an gama zasu Rufe da Sallar Isha”i kuma Tana da Tabbacin Aba ma ya dawo suna masallacin Tare in ma sun fito daga waje zasu gaisa ya wuce gidansa ina ma wannan mayyar matar tasa zata barsa ita Har mamakinta take yadda take mutuwar son Ya Jafar ko ina abun so a wajen wanda ya maida mugunta Dabi”arsa.
Baki ta Tabe bata tsaya Cire Hijabin Jikinta ba ta Fice Takalmin mamanmu na Yawom Tsakar gida ta Zura ya ma mata yawa sosai karamar kafarta ta Zurma aciki batason shiga Dakin su ne Saboda hamida tasan su Ya zeenatu ba lalle su bi ta kanta ba ammu Hamida gani taake tafi kowa Shigar mata Hanci da Dunkunkune in ta koma Dakin Hamida tayi mgana sai ta tankata kuma Hakan kamar wani Lasisi ne ta siyo ma kanta Fada Wajen Aba Shiyasa ta zabi Tafiya gidansu Hanna tayi zamanta sai Dare yayi Lokacin Hamidan ta kwanta sai ta Dawo.
Batare data Fadama kowa ba,kamar yadda ta Saba yin komai gaban kanta ta saka kai ta fice Daga gidan kuma Har ta fice bata Hadu da kowa ba,Awajen ma ba kowa Saboda an shiga masallaci Wajen yayi Haske Saboda an kunna Generator massllaci ba wuta suma ana Dawowa sallah su Ya shamsu zasu tada na cikin gidan Mallam babba ne mai bama Duka gidan da gidansu wuta taji dai ana ta Fada D’an malam Dake madina ya aiko da kudi aka siya har ma gyaran gidajen da aka sabunta musu wattanin baya duk shi yake turo ma dasu Ya Jafar kudi su kuma suna aiwatar da umarninsa.
Tasamu nasaran shiga gidan kanta Tsaye saboda Buba megadi shima yana masallaci wannan Dokar Baba Malam ne,ba hujja kana jin ana Kiran Sallah ka fake da wani aiki ya zama Dole kowa ya bar komai ya tafi kiran Allah
Gidan Baba Malam ya wuce yadda zan kwakwatanta muku Babban gida ne mai Dauke da Haraba mai girma Dauke da Motoci guda biyar hudu suna Bayyane Daya kuma an Lullubeta da Tamfol Tadade ahaka in ba mai mallakin Motan ya Diro garin ba bamai da ikon hawanta Duk da bai Saka Dokar haka ba,Sai Dayar bakar prado din ta mallam ce in fita ta kamasa Dayar 306 iri daya guda Biyu Daya ta Ya Jafar ce Daya ta Nasir,Sai wata benz baka ta Aba ce,Sai babbar Macapolo ta Jigilan makaranta ne.
Haraban gidan na Zagaye da Fulawowi masu kyau da yarari.
Daga Cikin gidan kuma Flat Biyar ne ajere na Farkon na Baba Malam ne grefensa akwai Dakuna kamar guda Biyar saboda mazan gidan Falt din Dake bayansa kuma Shashen Hajiya Babba ce Uwargidan Mallam sai shashen mai bi mata Hajiya uwa Daga nata sai na Anty Nasara na Anty Amarya shine na karshen wanda Daga gefensa kuma wani katon Kitchen ne da Store mai Dauke da Kimai na Bukatar mace na girki Kowacce tana da nata ashashenta ammh Gudun Fitina yasa aka Fitar da na waje inda duk wacce keda girki Zata Fita ita da yara da masu aiki suyi komai Tare Dokar gidan ce da Tsarin komai Bisa Tarbiya da Sunna Baba mallam Sharahararran malami ne Daba iya Nigeria ko Gumel ba Har Kasheshen Larabawa an san dashi.
A Babban Falon Dake shashensa ake Taruwa Matan da yaran maza da mata aci abinci sannan Ashashen sa ne kadai akwai Talabijin shima kuma In suna wajen sai Tashar Karatu sai wa”azi in ba kaga an Sauya sai in Dare ya Tsala yana so ya kalli Labarai Sun saba ya Zame musu jiki Duk wanda ya kwana da tashi agidan Mallam ina ka Fito karatu ina zaka ne..Me kace Aya ce mai na maida maka Hadisine ba iya Iyalan gidan ba Har damu da muka Hade dasu muma Dokarsa muke bi Domin har yau har Gobe in ba”a Fada maka ba Mutanen gari Dauka Suke mu jikokin Mallam ne BABA SA”IDU ne babban yaron Malam..!
Kai tsaye shashen Hajiya Babba ta wuce Domin nan ne Dakin su Hanne Auta take ga Hajiya,Bata Tsaya sallama ba ta Tura kofar shashen da Karfi Tana Kiran sunan Hannan.
“Hanne…Hanne..Hanne..!
Take Fada lokaci Daya tana Wulka manya Idanuwanta Cikin kayattacen Falon na Hajiya Dayaji komai na More Rayuwa.
Sai dai mamaikon taga Hanne sai taci karo da Hararan Ya Aisha Dake Zaune kan Darduma tana karatun pass Q domin suna gabda fara WAEC da NECO, Bata katse Karatun nata ba ammh Amina tasan Hararan ko ta macece Yasa ta Daga Hannunta tana Fadin”Yi Hakutri Ya Aisha..sallamu Alaikum..!
Tafada kai Tsaye tana kara Wurga ido wajen neman Hanne.
Abida Dake zaune kan kujera Tana Karatun Qur’ani
Wacce Tunda taji Bangazan kofa Da kira tasan sai Amina itace kadai bata da natsuwa Kaf acikin ya”yan gidansu da gidan Baba Sa”idun.
Itama Hararan ta jefa mata kafin tace”A tsakiyar falon ake sallama Amina..?
Sai alokacin Amina ta ganta aranta ta Furta”Uwar sa’ido..!
Afili kuma sai ta Dan Rasauya ido kafin tace”Sallama fa sunanta sallama Ya Abida..!
Abida daman ai tasan bazata koma ba Kafiya ce da ita kamar kafura.
Bude mata ido tayi tana Fadin”Au bazaki koma bakin kofa ki sake wata ba kenan..?
Amina ta Bude baki tace”Ah gaskiya..!
Cikin kunkuni tace”Haka kurum..Tab…
Abida tace”Me kikace..?
Kallonta tayi da manya Idanuwanta kafin tace”Nifa ban ce komai ba..!
Abida Kai ta Rausaya a cikin Idanuwan Amina akwai wani kaifin da indan ta kalleka sai kaji gwiwanka yayi sanyi..!
Da hannu ta nuna mata tana Fadin”Hanne tana Dakinmu tana Guga..!
Ai bata gama Rufe baki ba Amina ta Kwashi gudu tana kara kiran sunan Hanne Wacce sai Lokacin taji kiran da Sauri ta kashe Iron din Daman Hijabin haddarsu na gobe take gogewa ko mafarki take yi tasan Sautin Kiran Amina Dabam yake kuma akowa da Hannatu yake Kiranta Aminene ce kadai ke kiranta da Hanne.
Akofar Dakin sukaci karo Dakin Dake kusa da Bedroom din Hajiya sai wani Wanda suke Saukar baki Dangin Hajiya in sun zo nesa dana Hajiya.
Kusan karo sukayi da juna Wanda yasa Hanne tayi baya tana Fadin”AMINA gani nan fa..!
Tsayawa sukayi suna kallon Juna kafin Amina Taja hannunta su koma Cikin Dakin Tana Fadin”Hajiya fa..!?
Hanne tace”Tana Dakinta..!
Amina tabi Dakin da kallo ta Sauke ganinta kan Hijabin da Hanne ke gogewa tace”Dadina Dake kina da Zafin Nama Hanne..ni fa ban ji ma Hijabin nawa awanke yake ballatana akai ga gugansa..!
Hanne Dukawa tayi ta kunna Soket ta Cigaba da Guganta ita kuma Amina kan Karamin gadon Hanne ta Zauna Babban na Ya Abida da ya Aisha ne
Hanne bata damu ba tace”ai ke babba ce..Amina kike ni kuma Hannatu..!
Amina Tayi dariya tana Fadin”dillar Sarkin Tsoro..Ki Saki jiki ki amsa sunanki Hannatu Yusus Abdurraham Bazanga kowa shakkarki zai yi..!
Hanne na Guganta bata Dago ba tace”Uhmm..Meya fito dake Daga gida da Daran nan..?nasan da Dalili..!
Amina ta Tabe baki tana Kwabe Hijabin Jikinta Lokaci Daya tana Fadin'”Ke da kika sani..Yau fa Har Yaya sai da ta Dakeni Hanne su Ya Zeenatu suka min gami wajen su ya Jafar harda fadamin in ya Dawo sai na Sani..!
Hanne na Duken ta Dago kanta tana kallon Amina Kafin tace”Kan Tafiyarki yawon da kika saba in an tashi makaranta ko..?nima fa ana tashi nazo ajinku bakya nan..!
Gajiya akayi da jiranki Ya shamsu yace mu taho gida..!
Amina ta Zabga mata Harara tana Fadin”Ni daman bance ku jirani ba..Nasan Hanya..!
Hanne tace’Koma miye dai baki kyauta ba..Amina don Allah ki daina Wasu abubuwan kai tsaye ko ni in kika fadama zakije wani wajen.ko Hamida haka zata faru..?
Amina ta Juya idanuwanta kafin tace”Hanne..Hanne..Ki kyaleni don Allah kada ki batamin rai bazaki iya da Jidali na ba..!
Hanne bata Kara mgana ba itama Aminan haka Sai da ta juya taja Littafin Data gani kan gadon Hanne Ta Fara Budewa kafin ta Dago Tana Fadin”Hanne akwai Kwazo..Kin yi aikin Malamin Lissafin nan..!
Hanne na Nimken karshe a Hijabinta tace”Ba Dole ba kada ma na manta kinsan mugu ne wlh ya Rantse Bulala goma ga duk wanda bai yi ba..!
Amina ta tabe baki kafin tace”Kan bala”i..Wai haka yace..?
Hanne ta kashe Soket din ta Mike Dauke da Hijabin tana Fadin”Ajinmu ba..Bansani ba ko ku bai Fada muku ba..Ammh nasan komai tare yake mana ba bambamci..!
Amina tace”Oho ni fa sanda ya shigo ina chan ina Karatun littafin da Ziyada ta daukomim adakin Antyta Garin Kallon Ruwa kin ji Dadinsa Hanne..!
Hanne ta tsaya kyam tana kallon Amina kafin tace”Amina Daman baki Daina wannan karance karancen nan ba..?kinsan fa in aka sani bazaki ji Dadi ba..!
Amina tayi tsaki tana Fadin”To sai me..?ke zaki fada..?ke ni kyaleni Sai fa nayi kema zan koya miki Allah da dadi..!
Hanne tace”Allah ya Tsareni..!
Amina ta tsuntsire da Dariya tana ganin Hanne ta Bude babban Wadrope din Dake Dakin gefen inda kayanta yake ta sakashi Kana ta Rufo Tana kallon Amina kafin tace”ki Tafi da littafin gida ki kwafe kada muje Ranar Monday Uncle Gaddafi ya Dakeki kinsan Halinsa..!
Amina tace”Dillah Rabu dashi..Duka na Kisa ne..?da yana Kisa da babu Burbushin Amina aduniya kuma ya Dade bai yi Dukan ba Alqur”an bazan yi ba..!
Hanne ta kada kafin tace”Ammh in kika kiyye taba Lafiyarki fa Amina..?
Amina tayi kamar bataji ta ba ganin Haka yasa Hanne ta karisa gabanta Tana Fadin”In ya jafar ya dawo fa..?
Amina na Dariya tace”Ke bazai dawo ba kema kinsani..Yaushe mai wannan Dakalin bakin zata barsa..!
Hanne na Rufe baki tana Fadin”Ke Amina Anty Shamsiyan ne mai Dakalin baki..?
Amina na Dariya Harda Buga Kafa tace”Eh mana baki taba Lura ba..Sai ma in tana mgana..Sweetheart..!
Amina ta fada tana kwaikwayonta Dayasa sai da Hanne ta Duka saboda Dariya Kafin ta Dago ji kake Tas sun Kashe da juna Cikin Nishadi Tare suke Zube kan gadon Amina nama Hanne Rada akunne dayasa ta kara Saka Dariya tana Tureta Lokaci Daya Tana Fadin”Ba ruwana..Ba ruwana Amina..Bazan iya Da jidalinki ba kinsani..!
Amina bata Damu ba Chanza Fuska tayi tana Fadin”Kin Tuna sadda Muna aji uku a islamiya kullum Karatunta Dayane..Anjadada.Kalli Leben nata jadaddaad..!
Dariya sai da tasaka Hanne Hawaye Saboda yadda Amina ke yi da baki kamar Tsohuwa zatace isuhu..!
Cikinta ta Dafe tana Fadin”Ki barni haka Amina kada ki kullarmin da ciki da Dariya..!
Dariyan suke gabadayansu Basu san da shigowar Hajiya ba sai dai sukaji mganarta Daga sama.
“Dariyan me kukeyi haka ne..?
Da Sauri suka jiyo suna kallonta Hajiya Babba tana sanye da Doguwar rigar Shadda ajikinta Mace ce Doguwa ga kiba,Akallah ta bama Shekaru hamsin baya sai dai Hutu sun Lullube shekarunta Da ka ganta Kaga su Hanne da Ya Aisha Saboda suna Kama da ita sosai.
Amina ce ta mike zaune tana Fadin”Hajiya ina yini..?
Hajiya na Daga kofar Dakin tace”Lafiya lau Mamah..Sai yau nake ganinki..?
Amina na Dariya batace komai ba Bata iya maidama Hajiya mgana Saboda Kirkinta,Mamah take ce mata Saboda sunan Mahaifiyar Baba Malam Amina kec dashi basa Kiran Sunanta ita tace Mamah shi yace Mamana..!
Hanne ce tayi zaraf tace”Yau ma Laifi Tayi Hajiya..!
Hajiya ta kada kai tana Fadin”Ohh maamah duk baki ji nasihata ba ko..?Don Allah ki natau ki dinga jin mgana Bana son wannan Korafin Kowa yace ke Babanki Sa”idu kullum Mganarki yake yi hakama iyayenki mata Don Allah Mamah ki rika jin mgana ki zama kamar kowacce y”a acikin Gidanan..!
Zaku Dauka yadda Amina tayi shuru Tana jin Fadan ne nan kuwa bata ma Fahimta Domin indai wannan Nasihan ne ta Haddacesu Daga bakin Hajiya da Baba Malam
Ammh Cikin Dan kada ido tace”Shikenan Hajiya..!
Kallon Hanne tayi kafin tace”Ku tashi kuyi sallar isha”i gashi chan ana Kira..Ku fito muje falon Malam mu ci Abinci..!
Da Sauri Amina tace”Hajiya zamu ci namu anan..!
Saboda in akwai abunda ta Tsana wannan al”adar ta gidan mallam Akwai Wadanda bata son Haduwa Dasu acikin gidan nan.
Hajiya ta juyawa tana Ficewa Lokaci Daya tana Fadin”Ba ruwana ku da Babanku..!
Sai da Hajiya ta fice ne Hanne tace”Meyasa indai kikazo gidanan bakya son zuwa Falon Baba cin Abinci..?
Amina tace”Ba wani dalili..Kawai bana son ganin matar nan ne..!
Hanne tace”Wai Anty Amarya..?
Amina ta tabe baki kafin tace”Itafa Bata da Mutumci Ni tun Ranar da Fada ya hadani da Sa’adatu ta Shigar mata Har tana Fadin meyasa ta Hada kashi da irin Tsiya kamata..?na tsaneta Daga ita har ya”yanta kinsan ko a makaranta bana mgana Dasu..kuma ina jiran Watarana yarinya ta shigar min Harka na Sauke mata Hayakin kaina..!
Hanne ta mike tana Fadin”Amina baki da mantuwa..!
Amina tace”Bana manta wanda yayimin Alheri..Da wanda yayimin Sharri..Kina wani abu kamar kuma jin Dadin zama da ita kuke..Saboda Baba malan ne take Rage wasu abubuwan ammh da badomin haka ba Allah kadai yasan iskancin da zatayi..!
Hanne tace”Ni ina ruwana da ita..Iyaka in mun hadu na gaisheta ko Shashenta bana zuwa sai ta kama..Sa”adatu ma ta Dade batamin mgana kinsani Saboda ke..!
Amina tace”Share banza..Itace akasa mu muyin gaba badai ta Mutum ba sai Allah..!
Hanne na Dariya tace”Kinsan fa Diyar yayarta Ya Dan mallam ke aure ko..?
Amina ta yamutsa Fuska tace”Haka naji shiko Duk yanmatan Duniya sai ita .?
Hanne tace”Kowa haka yake fadi..in kinga ya”yan masu Sarauta da masu kudi da malamai yadda suka rika kawo ya”yansu wajen Baba ammh Duk yaki sai kawai Rana Tsaka yace Anty Sakina yake so..Kinsan tare tatashi wajenta dasu ya Jidda !
Amina tace”Eh mana na Tuna lokacin duk da bamu da wayau tafi kowa iskanci kamar gidan Ubanta..Nifa inaga Tun da akayi auran ban kara ganinta ba Duk zuwan da sukeyi har su tafi bama Haduwa har shi Ya D’anmalam din bazan iya Tuna kamaninsa ba gaskiya..!
Hanne tace”Kinsan bai cika yawan zuwa ba..?in yazo ma shi kadai kwana Biyu yake ya koma in kuma Zai zo da ita sai karshen shekara kuma suna Gidansu Dake nan Kano Road sai dai in sunzo gaida su Hajiya kuma Har gidanku yana shiga gaida Yaya Hajiya tace Dan Dakinta ne sosai..!
Amina ta mike itama tana Fadin”Ke ni ban taba ganinsa ba..Kina da Hotonsa .?
Hanne tayi Dariya tana Fadin”Sha Kurumimki naji Hajiya na Fadin nan da wata Daya suna na nan zuwa Saboda Mganar auran su ya Aisha..!
Amina ta kwalalo ido kafin tace”Kice muna da shan Biki..!
Hanne tace”Wlh kuma har dasu ya Sadiya ma za”a Hada fa…kilama Har dasu Ya Zeenatu..!
Amina tayi wata Dariya kafin tace”Allah yasa hardasu..su tafi su barmana Gidan dagani sai Hamida muci uban juna..!
Dariya suka saka Gabadaya Harta Tafawa suna cigaba da Hiransu Salla sukayi Tunda suna da alwala Sai da suka idar kana suka fita Falo ba kowa suna Falon Baba Malam Kichen din Hajiya Hanne ta shigo ta Dibo musu Doya da miyar Stew nan falo suka Fito suna ci suna Hira da Dariya Daga ganinsu kasan kaunar da suke ma juna Daga Allah ne.
Sai wajen 9:30am na Dare su Ya Aisha da Ya Abida suka shigo Ya Aisha Daki ta wuce ita bata cika mgana ba Ya Abida ce ta kallesu tana Fadin”Meyasa baku je Dinner ba..!
Amina ce tace”Mun yi namu mu kadai..!
Kai ta kada kafin tace”Sannu Shafaffu da mai..To Baba na kiranku..!
Amina Rada take ma Hanne tana Fadin”Mijin Ya Abida zai sha Gulma..!
Hanne na Matse Dariyanta Ya Abida ta Zaro ido tana Fadin”Amina me kike cemata akunne gulmata ko..?
Da Sauri Amina tace”Labarin wata yarinya mai Bala”in saka ido nake bata..yar ajinmu a islamiya..ko Hanne..?
Hanne ta Daga kai da Sauri Abida Wucewa tayi tana Fadin”Sai na Daki bakin yarinya yanzu nan..!
Amina ta Rakata da Daga Lefe tana Shigewa suka kyakyalce da Dariya
Saida suka gama Hanne ta kwashe komai takai Kitchen Amina tace”Dauko Hijabina na tafi gida Hanne..!
Hanne tace”Kiran baban fa..?
Tace”In mun fito sai na shige gida..!
Hanne tace”Nazata nan zaki kwana..!
Kafada Amina ta Daga kafin tace”Anki din..Ina fa Kirge nice na kwana Na karshe..Malama kece fa da kwana..!
Hanne tace”Dillah zan kwana nima gobe..!
Amina tace”Yauwa sai na baki ma Labarin wannan litaffin..!
Da Sauri Hanne ta Danne bakinta tana Nuna mata Dakin dasu Ya Abida suke Amina Tayi Dariya Kafin tace”Sai me..?Allah yasa ma suji..!
Hanne dai wucewa tayi ta barta Tasan wacece Amina bata da tsoro komai zai Faru sai da ya faru ita zata saka a uku.
Hijabinta ta Dauko mata itama ta Dauko nata tana Fadin”Muje na Rakaki..!
Fita sukayi Daga Dakin suna Tafe suna Hira Amina na Zagin malamar hausansu har tana kwaikwayon mganarta Dukkansu Jss3 suke sai dai Amina Ita da Sa”adatu suna A ne yayinda Hamida da Hanne ke ajin B.
Suna tafe har Shashen Baba Maallan Amina tasan inda suka zo yasa ta Bude baki Daga Kofar Falon ta kwarara Sallama.
Hajiya Dake Cikin Falon gefen Baba Mallam Dake zaune kan kujera yana Duba wani Littafi tace”Ga Mamar taka nan ta iso..Kaji Doguwar sallama kamar ta Kirki..!
Tafada Cikin Zolaya yana Duken yace”Ta kirkin ce mana Zainabu…Mamana Harda yarinta ajikinta da ta kara girma ta mallaki Hankalinta sai dai Labari..!
Kai kawai ta Kada tana Hangen abunda ba Haka ba kan Aminar ita ta amsa Sallamar ta Amina Hanne na Shirin Shiga ta riketa tana Fadin”mu shigo baba cikin harshen larabci
Shi kanshi sai da ya Murmusa ya Dago Fuskarsa Daya cika da Farin gemu Cikin Dattakonsa yace”Na”am…!
Baisan meyasa ba Ko Muryan yarinya yaji sai yaji wani Dadi yana mata kauna wanda ko cikin ya”yansa sai an Tona Amina haka Allah yayi ta mai Farinjini ne Malam yana sonta Saboda Allah da kwazonta Duk da take bata maida hankali Kokari gareta yana ganin makamceceniyar kwakwalwarta Data D’an malam awajensa da itace kadai yake Dogon Mgana da Larabci bata kakare ba Tana Jin Labarci Fiye da yadda kowa ke Tunani kuma Bayan Baba Malam ko Baba Sa”idu baisan wannan baiwar nata ba..
Sannan ko makaranta sun sani tana da Jawo Jidali ammh itace Over roll acikin ajinsu har mamaki ake yi masu Hassada da ita na Fadin Cuta akeyi Amina jidalinta baya barinta gane Karatu shiyasa Sa”adatu ke Kishi da ita matuka basa Shiri ko a islamiya da hadda Itace Zakka kamar yadda ta Fita Zakka acikin gida Daga waje ba,sannan Amina Zakka ce sai kowa Tunani yake sa”a take ci Saboda ba”a Taba ganin tabama karatu Muhimmanci ba nan kuwa basu sani ba Tana da baiwa sau Da

Leave a Comment