*SHU’UMAR MASARAUTA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER’S ASSO…*
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba.
SHAFI NA ƊAYA
Masarautar Zazzau (1953)
Wani irin zafi take ji yana ratsa ta tun daga tafin ƙafarta har zuwa tsakiyar kwanyarta, dalilin haka ya sabbaba mata karkarwar jiki tamkar wacce ta ji kiɗan gangi. Wanda hakan ne ya haifar mata gumin da ke tsatssafowa daga kowacce kafar da ke cikin ilahirin jikinta. Ba yau ne karo na farko da haka ya taɓa faruwa da ita ba, sai dai a wannan ranar ji take tamkar an saka ta a tukunya ana dafa naman jikinta da ruwan zafi. A hankali ta cije baki tana yarfe hannu haɗe da lumshe idanu. Baiwa Maimuna da ke bayanta tana mata fifita cikin ƙwarewa a makirci ta fakaice ta, ta yanki ƙasan jelar gashin kanta ɗan ƙanƙani ta yadda ba za ta fahimci hakan ba. Da sauri ta soke shi a jikinta haɗe da sauke ajiyar zuciya don ko babu komai ta san ta tsira daga siraɗin Fulani Umaima. Ta ɗan numfasa a hankali.
“Ki gafarce ni uwar ɗakina zan ƙarasa sashen Takawa na ce Jakadiya ta karɓo miki magani kamar yadda na ji kin ambata a baya, ranki shi daɗe lamarin ciwon nan na ki ƙara ƙamari yake yi amma tuba nake idan da kuskure a kalamaina uwar ɗakina.”
Ta so musa mata kamar yadda ta yi kafin zafin jikin ya fara galabaitar da ita, dalilinta na yin haka bai wuce yadda take gudun kada Bayin cikin masarautar su fuskanci zaman doya da manjar da ke tsakaninta da Mai martaba ba. Gyaɗa mata kai ta yi haɗe da ruƙo hannunta ta furta, “Idan kin fita Maimuna ki turo mini Baiwa Zainaba.” Cike da girmamawa ta russana, “Allah ya ƙara wa Fulani lafiya, Ubangiji ya buɗi ido lafiya ya kawo mana Yarima mai jiran gado cikin yalwar ariziƙi da ƙoshin lafiya.” Da hanzari ta fice a gaggauce don ko kaɗan ba ta son wargaza shirin ɓoyayyar uwar ɗakinta. Sai da ta turo wa Fulani babba Zainaba sannan ta wuce sashen Fulani Umaima cike da firgici, tana tafe tana waige kamar sabuwar munafukar da ta yi gulma a fada. Da yake Fulani Umaima ta kwana da sanin shirinsu, tun da doshin magriba ta sallami bayinta suka wuce sashensu na bayi. Tamkar wacce aka jefo daga sama haka ta faɗa ɗakin Fulani Umaima da ke tsaye tana kai kawo don gudun samun matsala a shirinsu, duk da tana da yaƙinin Baiwa Maimuna ba za ta iya shallake wa umarninta ba.
A ƙasa ta zube tana sauke numfashi ta furta, “Hutawarki lafiya Fulani mai magajin masarauta, zinariyar Mai martana haskenki bai tsaya iya shi kaɗai ba kin haske lungu da saƙon cikin Masarauta. Ina gwanar wani ga tawa? Kin yi taki kin yi ta kowa, garnaƙaƙin dutse kike kowa ya ja da ke shi zai faɗi…” Fulani Umaima ta katse ta da cewar, “Ina fatan komai ya tafi yadda ya kamata?” Baiwa Maimauna ta saki murmushi, dalilin haka ya sa Fulani Umaima ta sauke ajiyar zuciya duk da ba ta kai ga jin amsar Maimuna ba amma ta fahimci sun yi nasara domin kuwa labarin zuciya a tambayi fuska. “Ranki shi daɗe an gama aiwatar da komai, ga wannan.” Maimuna ta ƙarasa maganar tana kunto gashin kan Fulani Babba ta miƙa wa Fulani Umaima. Wani yalwataccen murmushi Fulani ta saki, Baiwa Maimuna ta ci gaba. “Yanzu haka tana can magashiyan har ta umarce ni da na aika Jakadiya ta karɓo mata ragowar maganinta a wurin Mai martaba.” Wata irin dariya ce ta suɓuce wa Fulani Umaima wacce ba ta tsammace ta ba, tuna wacce take gabanta ya sa ta tsuke fuska haɗe da furta. “Ki jira ni.” Uwar ɗakinta ta shiga can ƙarƙashin gado ta zura hannunta, ta ɗauko wani ƙoƙon kan ƙwarangwal. Wani garin magani ta ɗebo a ciki ta kulle a cikin wata ‘yar busasshiyar ƙaramar fata. Ta fito zuciyarta fes cike da takun isa da ƙasaita. Sai da ta koma kan ƙasaitacciyar kujerarta ta zauna sannan ta miƙa wa Maimuna.
“Ki fara zuwa ki karɓo maganin wurin Mai martaba, amma ki tabbata wannan kika ba ta ta yi amfani da shi, za ki zuba mata a ruwa ko abinci kuma ki tabbatar da ta shafe jikinta da shi. Duk dare ina buƙatar ganinki domin akwai fitar sirrin da nake so mu yi.” Cike da girmamawa Maimuna ta russuna. “An gama ranki shi daɗe, fansar kaina gare ki ya shugabata domin kai da kaya duka mallakar wuyane. Ki sa a ranki na aiwatar da duk abin kika buƙata na gama, Allah ya taimaki giwar Takawa ɗawusu mai yawan ado.” Fulani Umaima ta gyaɗa kai sannan Baiwa Maimuna ta miƙe, har ta je bakin ƙofa Fulani ta furta. “Ki tabbata ba a samu matsala ba, idan aka samu matsala ki kuka da kanki.” Baiwa Maimuna ta russuna. “Godiya nake uwar gijiyata.” Sai da Maimuna ta ɗaure maganin wurin Fulani Umaima sannan ta nufi sashen Mai martaba, Jakadiya ta samu ta sanar da ita saƙon Fulani Babba. Kai tsaye Jakadiya ta tunkari turakar Takawa. Sai da rangaɗa sallama haɗe da kirarin girmamawa sannan ta isar da saƙon Fulani Babba. Kamar ba zai amsa mata sai kuma ya miƙe ya nufi wata jakar fata da ke saƙale a jikin bango ya zura hannunsa, wasu ƙullin magunguna biyu ya ciro ya miƙa wa Jakadiya, ta karɓa tana godiya. Har ta fara tafiya ya furta. “Daga yau a sanar da ita ta riƙa karɓar magani kafin almuru, ba a koyaushe muke da buƙatar hakan ba.” Jakadiya ta amsa sannan ta fice ta damƙa wa Baiwa Maimuna tana jaddada mata saƙon Mai martaba.
Maimuna na shiga sashen Fulani Babba ta same ta kamar yadda ta bar ta, Baiwa Zainaba na gefe tana matsa mata ƙafafuwanta da suka ɗan kumbura. Cike da girmamawa ta miƙa mata maganin da Fulani Umaima ta bata sannan ta furta, “Allah ya ƙara wa Fulani lafiya, Ubangiji ya shiga lamuranki uwar ɗakina. Mai martaba ya ce a jiƙa rabi, rabi kuma a shafe miki jiki da shi.” Idanun Fulani jawur kamar sabon barkono ta buɗe su a hankali ta furta. “A yi yadda ya da ce Maimuna.” Zuciyar Maimuna ƙal ta tashi jiki na rawa ta jiƙa maganin kamar yadda Fulani Umaima ta gaya mata, ta taimaka wa Fulani Babba ta tashi zaune haɗe da kai mata ƙoƙon bakinta. Tas ta shanye shi sannan Maimuna ta shiga shafe mata a jiki gabaɗaya, sannu a hankali ta ji wata sassanyar iska na ratsata. Ta koma ta kwanta sakamakon jin daɗin jikinta da ta fara yi. Ta dubi su Baiwa Maimuna. “Maimuna za ku iya tafiya, Zainaba a tabbata an gyara makwanci su Khadija.” Cikin girmamawa suka zube ƙasa, “An gama ranki shi daɗe, Allah ya ƙara lafiya ya kawo mana Yarima lafiya.” Ba ta iya amsa musu ba sai ma runtse ido da ta yi sakamakon jin wata irin hayaniya da ta yi a tsakar kanta, ga wani irin jiri da ke ɗaukanta. A ɓangare ɗaya kuma wani abu mai tsini ya fara fusgar can cikin ƙasanta. A gurguje Maimuna ta fice haɗe da sake ba wa Zainaba umarnin gyaran ɗakin su Khadija da yake ita ce gaba da ita, ta juya ta fice daga ɓangaren ‘yayan Fulani Babba. A sanyaye Baiwa Zainaba ta bi Maimuna da kallo don haka kawai take jin zuciyarta na wasuwasi a kan Baiwa Maimuna tun da ta taɓa ganinta ta shiga sashen Fulani Umaima sau biyu.
Kai tsaye sashen Fulani Umaima ta faɗa, kuma a wurin da ta tafi a nan ta koma ta same ta. Fulani Umaima na ganin Baiwa Maimuna ta faɗa uwar ɗaki, wani sirrintaccen akwatinta ta ɗauko ta buɗe cikinsa. Kamar kullin idan za ta ziyarce shi haka take saka wannan sihirtacciyar rigar da Boka Bamagujen dutse ya bata, a lokacin ma sai da ta tube kayanta gabaɗaya sannan ta zura rigar mai ɗauke da launin ja, baƙi, ruwan ɗorawa da launin ruwan ƙasa. Rigar ɗinke take da waɗansu ƙananan layu sai kuma wasu ƙananun rubutu da aka yi da larabci, wani ɗan ƙaho ta riƙe a hannunta sannan ta fito wurin da ta bar Baiwa Maimuna. Hannu ta miƙa wa Maimuna babu musu da yake ta san kwanan zancen ta ɗora tafin hannunta a saman na Fulani Umaima, wanda ta tabbata ba don wannan sirrintacciyar tafiyar da suke yi ba babu dalilin da zai kai hannunta jikin Fulani Umaima, musamman yadda take nuna ƙyamar bayi da talakawa ƙarara a fili. Saka hannun Maimuna cikin na Fulani babu jimawa, ta runtse idanunta ta ɗaga hannunta da ta ke riƙe da ƙahon ta busa sau uku sannan ta kira sunan Bamagujen dutse sau uku. Wata irin guguwa ce ta karaɗe cikin ɗakin kamar ƙiftawar ido sai ga su a bakin wani ƙaton farin dutse mai ɗaukar ido, wurin kamar rana tarwai babu abin da ba ka iya gani. Kamar yadda yake bisa al’ada a duk lokacin da suka ziyarce shi, sai da suka saka ƙafarsu ta hagu a tare a kan wani jini da ke malale a gabansu. Sun ɗan ɗauki kamar minti biyu a haka sannan suka ji an bushe da wata irin dariya wacce take alamta musu aikin da ya da ce su yi a gaba. Ƙafarsu suka sake ɗagawa suka ɗora a kan wani kabari da ke gaban wannan jinin sannan suka fara takawa suka haye can sama dutse. Zaune suka hango shi babu ko ɗigon sutura a jikinsa, Maimuna ta kawar da kanta gefe don har cikin zuciyarta ba ta son ziyartar wannan shu’umin bokon don dai ba ta da yadda za ta yi ne. Suna ƙarasawa wurin wata ƙaramar bishiyar kuka Maimuna ta russuna tana faɗin, “Fatan nasara a kodayaushe ya shugabata.” Fulani Umaima ta ci gaba da tafiya don Maimuna ta san ko karen hauka ne ya cije ta ba ta isa ta ƙara koda taku ɗaya ba.
Fulani na zuwa sai da ta fara ɗiban wani jan ruwa a cikin wani ƙoƙon kan ƙwarangwal ta wanke fuskarta, sannan ta nemi wuri ta zauna tana fuskantar Boka Bamagujen dutse.
“Barka da aiki uban gidana.”
Jinjina kai ya yi ya furta. “Barkanki Fulanin Sarki Abdul’aziz.” Shiru ne ya ratsa Fulani Umaima ta kawo ido ta sa wa Bamaguje, ya saki murmushi don ya san wace ce Umaima. Ga tsananin buƙata fal ƙirjinta ga kuma taƙama da izzar mulki, kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci halin da take ciki. “Umaima kin yi ƙoƙari.”
“Sanin haka ya sa na kawo ziyara a ranar da ka buƙata.” Ta amsa masa a taƙaice.
“Kin aiwatar da komai yadda ya kamata, don haka kishiyarki ita da Sarki Abdul’aziz sai kallo sai hange daga nesa. Matuƙar ba asirin nan ne ya karye ba, ba na jin kishiyarki za ta sake ɗaukan ciki a doron ƙasar nan. Ke ba ma ciki ba ina mai tabbatar miki ita da sake yin wata mu’amala da Sarki Abdul’aziz sai dai a lahira idan ana yi. Ina ragowar kayan aikin?” Ya wurga mata tambaya. Jin haka ya sa Umaima ta saki malalacin murmushi ta ɗebo gashin Fulani babba da gashin Sarki Abdul-aziz, haɗe da ƙasar maƙabarta da ta gidan tururuwa ta miƙa masa ba tare da ta tanka masa ba. “Mun sakar mata lalurar fitsarin kwance, kuma mun saka mata lalurar mantuwa da warin jiki.” Bamaguje ya faɗa yana jefa tarkacen da Fulani Umaima ta bashi a cikin wata tunkunya da ke cike da jini tana tafasa. Kusan duk abin da suke tattaunawa Maimuna tana jin su, haka kawai ta ji tausayin uwar ɗakinta ya ɗarsar mata. Musamman da ta tuna zallar cin amanar da take yi mata mai haɗe da zagon ƙasa.
“Ina maganar cikin jikinta ya kwana?” Fulani ta tambaya cike da izza.
Bamaguje ta ɗebi wani jini mai yauƙi ya watsa a jikin wani allon farin ƙarfe. Take waɗansu inuwoyi suka bayyana, yana fara nazartarsu sai gani ya yi ɗuff komai ya ɗauke. Cikin da damuna ya sake ɗiban jinin ya watsa har sai da ya yi haka sau uku sannan ya dubi Umaima cikin damuwa. “Kishiyarki a daren yau za ta haihu!” Dum! Fulani ta ji tsakiyar kanta ya sara kamar wacce aka buga wa guduma. Rai a ɓace ta dube shi. “Wanne irin mugun labari nake ji haka, zancen banza kenan ƙafa ta mutu ta bar takalmi. Cikin jikinta ya fi komai ɗaga mini hankali…” Da sauri ya katse ta.
“Tun fil azal kundunsa rubuce yake da zanen ƙaddararsa, cikin kishiyarki shu’umin ciki ne lulluɓe yake da almara tamkar yadda masarautarku ta kasance SHU’UMAR MASARAUTA. Kamar yadda na gaya miki a yau za ta haihu…” Duk dakiya da ƙarfin zuciya irin ta Fulani Umaima sai da hawaye ya suɓuto mata, Bamaguje ya tsaya yana kallonta haɗe da jinjina kai. “Yau shekarata biyar kenan a cikin masarautar nan ko ɓatan wata ban taɓa yi ba, tun Fulani babba na da goyon fari Takawa ya auro ni. Bamaguje kana son na ƙare rayuwata cikin ƙasƙanci da rashin mamora?” Girgiza kai ya yi, ya sauke ajiyar zuciya.
“Wa ya ce miki ba za ki haihu ba?” Fulani ta zuba masa idanu zuciyarta na bugawa. “Yanzu haka kina ɗauke da juna biyu na tsawon makwanni uku.” Kamar a mafarki haka ta ji kalaman Bamaguje na ratsa majiyar sautinta. “Ki yi imani da ni Umaima matuƙar ina numfashi ba za ki tozarta ba.” Sanyi ta ji har cikin ranta.
“Da kai na dogara Bamaguje na yi imani da kai tun da ba ka kunyata mahaifiyata ba na tabbata ba za ka tozarta ni ba.” Ta yi maganar a raunane.
Wata ƙatuwar kunama ya ɗauko da hannunsa ya ce, “Ba ni hannunki.” A firgice ta wurga masa kallon baka da hankali, ya saki murmushi don ya fahimce ta. “Umaima kenan kura kike ga tsoro ga ban tsoro.” Umaima ta haɗe fuska kamar ba ita ba. “An ya kuwa? Kar fa ka manta ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka, dalilin haka ya sa masallacin kura ba a ba wa kare limanci.” Murmushi Bamaguje ya yi. “Kwantar da hankalinki kamar kin faɗa rijiya. Matso kusa ki ji.” Bamaguje ya furta. Tun bai rufe baki ba Umaima ta matsa kusa da shi, raɗa ya yi mata a cikin kunne lokaci ɗaya ta bushe da wata iriyar dariya cike da farinciki. Ta koma mazauninta na farko tana sauraronsa. “Ki tabbatar da kin aiwatar da abin da na umarce ki, don kuwa kowa rai ya yi wa daɗi ba ya mai shi ba.”
“Bamaguje kenan! Ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba.” Umaima ta furta cike da nishaɗi. Kashe mata ido ɗaya ya yi yana ƙare mata kallo, ganin haka ya sa ta fahimci inda ya dosa. “Tukwina fa?”
“Ka sallame ni kenan?” Ita ma ta wurga masa tambaya. Gyaɗa mata kai ya yi Umaima ta miƙe babu ko kunya ta sauke rigar tsubbun jikinta, Maimuna ta sunne kai ƙasa zuciyarta na bugawa. A fakaice take ƙare wa tsohon kallo cike da ƙyanƙyami don ko ita da take baiwa gani take ba za ta iya haɗa jiki da shi ba. Bamaguje na shirin ɗora hannu a jikinta ta ɗan ja da baya haɗe da sakin murmushin mugunta. “Na sadaukar maka da kishiyata a wannan daren, shi ne tukwicin da zan iya yi maka.” Ba ta jira cewarsa ba ta ɗora rigar a jikinta. Bamaguje ya gyaɗa mata sannan ya furta. “Za ku iya tafiya.” Umaima ta yi masa jinjina da hannu sannan ta sake ɗiban ruwan da ta wanke fuska da shi ta nufi wurin da Maimuna ke zaune hannunta ɗauke da kunamar da Bamaguje ya damƙa mata.
Abin da suka aiwata a farkon zuwansu yanzun ma haka ne ya faru, sai da suka koma daidai wurin da suka buɗe ido suka gan su tun farkon zuwansu sannan, Fulani Umaima ta ɗaga ƙahon ta runtse ido ta busa haɗe da kiran sunan Bamaguje. Ƙamshin ɗakin Fulani ne ya ankarar da Maimuna dawowarsu gida, cike da girmamawa ta zube ƙasa ta furta. “Allah huta gajiya uwar gijiyata.”
“A kullin ina sake jaddada miki bakinki ƙanin ƙafarki Maimuna, duk ranar da kika bari kwaɓarki ta yi ruwa na ji sirrina ya fita za ki bambamce mini tsakanin tsaba da tsakuwa.” Fulani ta yi maganar cikin sigar gargaɗi. “Maimuna ta duƙa kai ƙasa. “Wace ni uwar gijiyata? Kada Allah ya nuna mini ranar da zan aikata miki wannan zunubin ranki shi daɗe.” Fulani ta taɓe baki, “Za ki iya tafiya.” Da sauri Maimuna ta fice ko waige ba ta yi. Har za ta nufi sashen su na bayi sai uwar ɗakinta Fulani babba ta faɗo mata. Haka kawai ta ji sam ba ta kyauta ba. Zuciyarta ta ci gaba da azalzalarta da ta je ta ga halin da take ciki. Cikin sanɗa ta nufi sashen Fulani babba gabanta na faɗuwa. A haka ta ci gaba da tafiya har cikin ɗakin, ras! Ƙirjinta ya buga jikinta ya ɗauki karkarwa sakamkon ganin Fulanin a yashe babu sutura a jikinta. Wani tafkeken maciji ta gani a tsakanin ƙafafuwanta ya kafa kansa a saitin ƙasanta, ga wani irin gurnani da macijin ke yi. Idanun Fulani a rufe amma sai mutsu-mutsu take yi, da alama ma bacci take yi. Daga bayanta ta ji an dafa kafaɗarta, wani abu ne ya tsarga mata ta yi mutuwar tsaye cikin sanyin jiki ta waiwayo. Karaf idanunta suka sauka a kan Fulani Umaima da ta haɗe girar sama da ta ƙasa.
_Ummou Aslam Bint Adam_🌚
07062062624.
*SHU’UMAR MASARAUTA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER’S ASSO…*
Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba.
SHAFI NA BIYU
Ras! Ta ji gabanta ya yi mummunan faɗuwa, lokaci ɗaya ta nemi yawun bakinta ta rasa. Cikin firgici ta buɗe baki za ta yi magana Fulani Umaima ta katse ta. “Me kike yi a nan kuma uban me kike leƙe?” Maimuna ta zube a ƙasa jiki na rawa ta furta. “Ki yi mini aikin gafara uwar gijiyata, na zo na ji ko Fulani nada buƙatar wani abu kafin na tafi.” Da hannu Fulani Umaima ta nuna mata hanya, sum sum sum Maimuna ta fice jiki na karkarwa. Fulani Umaima ta leƙa Fulani babba da ke kwance, ta saki murmushi mai ɗauke da ma’anoni a hankali ta furta. “Mu zuba mu gani idan tusa na hura wuta, in dai ni ce yanzu kika fara gani.” Daga haka ta fice daga ɗakin.
Fulani babba ta jima a haka sannan ta farka, a hankali take sauke ajiyar zuciyata. Duk da a mafarki ta ga Mai martaba yana kusantarta abin ya yi mata daɗi, ta ji farinciki matuƙa saboda idan ba mantawa ta yi ba rabon da wani abu ya shiga tsakaninta da Takawa tun cikin jikinta bai fi wata biyu ba. Danshin da ta ji a jikinta ne ya sa ta kai hannunta, da mamaki take kallon makwancin nata. Da ƙyar ta yunƙura ta tashi nan take fitsarin da ke naɗe da zaninta ya fara ɗiga, da farko ta yi tsammanin ko faya ce ta fashe mata tun da a halin da take ciki tana iya haihuwa a kowane lokaci, musamman da take jin ciwon mara sama-sama. Sai dai zarni-zarnin da ta ji ne ya sa ta shinshina hancinta. A hankali ta furta. “Fitsari? Ni kuma? Kai ina jin dai faya ce ta fashe.” Gudun wasu-wasi ya sa da kanta ta ɗebo ruwa ta sa a katifar ta sauya kayan jikinta amma har lokacin gani take faya ce ta fashe mata. Banɗaki ta shiga ta yi wanka ta fito sannan ta ɗan ci abinci, a hankali ta ji mararta na ci gaba tsikararta daga baya bacci ya sake yin awon gaba da ita.
Fulani Umaima kai tsaye sashenta ta wuce don a ranar ba ta jin sha’awar zuwa wurin Mai martaba. Da shigarta babu jimawa sai ga Jakadiya ta shiga ɓangarenta da saƙon Mai martaba na gayyatarta zuwa turakarsa, ba don ta so ba haka ta amsa mata. Jakadiya har za ta tafi Fulani ta dakatar da ita. “Jakadiya ba na son ki yi nisa da sashen Fulani babba.” Jakadiya ta amsa mata sannan ta fice. Cike da kissa Fulani Umaima ta shirya kanta da sihirtattun turarrukan da Bamaguje yake haɗa mata, ta ƙarasa turakar Mai martaba. Zamanta babu jimawa suka ji wata ƙarar busar sarewa. Da sauri Fulani da leƙa kusurwar turakarsa idonta ya sauka a kan ƙaton shurin da gudajen turuwa suka zagaye da ke cikin ɗakin, gabanta ya yanke ya faɗi don ta san tun da ta ji wannan sarewar a yau mai afkuwa za ta afku. Mai martaba ya saci kallonta, haka kawai yake jin shakkarta a zuciyarsa. Amma ko shakka babu wannan busar sarewar da shuri ya saki na da alaƙa da cikin jikin Fulani babba wanda yana da yaƙini za ta iya haihuwa a cikin daren nan. Ya so ya tanka wa Fulani Umaima amma sai ya fasa, hakan ya sa ta saki murmushi cikin kissa.
“Jikina yana ba ni Fulani babba na gab da kawo mana Yarima, wannan abin farinciki ne. Tun da shuri ya saki sarewa na tabbata a yau za mu iya samun ƙaruwa a gidan nan.” Faɗaɗa murmushinsa ya yi, ya janyo Fulani Umaima jikinsa ya furta. “Wannan haka ne yanzu me kike ganin ya kamata a yi?”
“Ina ganin zai fi kyau a yi dakan ɗaka shiƙar ɗaka… sai a kira Jakadiya ta zauna a wurinta koda ciwon zai tashi tana kusa da ita, a madadin a kira Ungozoma. Amma sai yadda kace ranka shi daɗe farin jakada.” Fulani Umaima ta ƙarasa magana tana sunkuyar da kai ƙasa. Ajiyar zuciya Mai martaba ya yi, “Na baki wuƙa da nama mai farar zuciya Allah ya yi miki albarka.” Fulani Umaima ta amsa sannan hirar tasu ta fara sauya salon faranta ran ma’aurata. Zuciyar Fulani Umaima ƙal ta je ta samu Jakadiya da zancan Takawa, Jakadiya na gama sauraronta ta yi ƙasa da murya tana ɗan waige sannan ta ce. “Wani ma ya yi rawa ma ballantana ɗan makaɗi? Ai wallahi sai mun ga abin da ya ture wa buzu naɗi. Ina mai yi miki albishi tauraruwar Mai martaba gobe war haka Fulani Babba na nan cunkushe da baƙin ciki fal ƙirjinta, idan an isa a yi Yarima ba a ɗakinki ba shegiya nake.” Fulani Umaima ta saki dariyar ƙeta. “Jakadiya tamkar zuma haka kike ga zaƙi ga harbi. Na aminta da ke fiye da haka ma za ki iya aikatawa.”
“Ai shi abin kasuwa na mai ciniki ne, ni ta ki ce Fulani har abada ina bayanki. Fulani kin manta ɗayan kirarin nawa kaska rabi mai jini ki bar shi da gashi.” Fulani Umaima ta jinjina kai alamun gamsuwa. Jakadiya ta sake ƙasa da murya.
“Allah ya taimake ki ni zan ƙarasa zan biya na taso Baiwa Maimuna da zarar haihuwa ta taho gadan-gadan zan turo miki ita.” Murmushi Fulani Umaima ta yi har Jakadiya ta yi gaba ta sha gabanta da sauri ta furta. “Jakadiya a kawo mini kayan Bayi sashena, sannan a tabbatar an bawa Maimuna ta kawo mini cikin hanzari.” Shiru Jakadiya ta yi tana nazaratar Fulani. Cikin zuciyarta tana ayyana ƙwarewarta a mugun makirci da ƙuduri.
Da sauri Jakadiya ta wuce ɓangaren Fulani Babba a lokacin da ta ƙarasa dare ya tsala sosai, sai da ta yi sallama sannan ta shiga har cikin ɗakinta. Shigar Jakadiya ya yi daidai da farkawar Fulani babba, ƙarasawa ta yi gabanta ta ce. “Allah ya taimaki uwar ɗakina ya ƙarawa Fulani lafiya. Yanzu haka Mai martaba ne ya turo ni a kan na kwana da ke saboda yanayin da kike ciki, domin tuni shuri ya saki sarewa.” Murmushi Fulani ta yi don ko ba komai ta ji daɗin yadda Takawa ya ba ta kulawa, hannu ta miƙa wa Jakadiya alamar ta taimaka mata. Wani abu ta ji ya tsira wa mararta haɗe da bayanta. Cije baki ta yi jin ciwon na ƙara tsanani gadan-gadan. A haka ta miƙe ta ƙarasa banɗaki da ƙyar don ta gyara jikinta, a lokacin da ta tashi ta sake lura da fitsarin da ya jiƙe makwancinta sharkaf, na wannan lokacin har ya fi na baya yawa da wari. Fulani na dawowa kafin ta shiga ɗakin ta ci karo da wata mata baƙiƙƙirin a tsaye a dokin ƙofa. Hannu ta miƙa mata cikin wata irin murya ta furta. “Ba ni cikin jikinki!” Da Mamaki Fulani ke kallonta har lokacin ciwo na cin ta, “Wace ce ke? Me ya sa zan baki cikin jikina?” Tana rufe baki ta ga matar ta miƙa hannuwanta masu ɗauke da waɗansu irin baƙaƙen farata da zaƙwa-zaƙwan yatsu, ta miƙa hannun da niyyar shafa saman cikinta, Fulani da sauri ta ja baya haɗe da furta. “A’uzubillahi, Innalillahi…” Da gudu ta ga matar ta shige cikin sashenta, wata uwar ƙara ta ƙwalla nan take sai ga Jakadiya ta nufo wurin da gudu. Jiki na karkarwa Fulani ta ce, “Jakadiya baki ganta ba?” Jakadiya ta waiga hagu da dama ta ce, “Wa kenan ranki shi daɗe?” Dum! Fulani ta ji kanta ya yi nauyi tana son tuna a kan abin da Jakadiya take tambayarta amma ta manta, gumin da ke tsattsafo mata ta share ta ce, “Ba komai mu je Jakadiya marata ciwo take. Wash! Bayana zai ɓalle.” Jakadiya ta taimaka mata suka ƙarasa ciki, kafin fitowar Fulani daga banɗaki tuni Jakadiya ta gyara wurin ta haɗa gabaɗaya kayan karɓar haihuwa. Ganin zaƙi haɗe da jini ya fara bin ƙafar Fulani ya sa Jakadiya ta shimfiɗa mata ƙatuwar leɗa, Fulani da ƙyar ta yunƙura ta hau kai tana jin ƙasanta tamkar ɗa zai faɗo. Fulani Umaima ce ta yi sallama daga bayanta Baiwa Maimuna na biye da ita, yadda Fulani Umaima ta marairaice tana yi wa Fulani babba sannu sai ka rantse zuciyarta cike take fal da tsoron Allah. Wani jan ƙoƙo ta miƙa mata ta furta, “Mai martaba na cikin tsananin damuwa da jin halin da kike ciki, musamman da ya tuna da mutuwar Marigayya Fulani Samira. (Matar Sarki Abdul’aziz ta uku ce da ta rasu wurin haihuwa.) Ya umarci da a kawo miki wannan yanzu na karɓa a hannun Shamaki.” Ɗago kan Fulani babba ta ga Fulani Umaima ta sauya mata a kammani, har take ganin kamar ta taɓa sanin kamannin, sai dai kuma ba ta jin za ta tuna kalar fuskar. Baiwa Maimuna da ke tsaye jikinta ya yi sanyi don ta san garin maganin ba ya wuce na wurin Bamaguje. Fulani Babba ta karɓe za ta kai baki ta ji wani irin nishi ya taso mata, cikin tsananin azaba ta wurgar da ƙwaryar gefe ta riƙe Jakadiya da ke gefenta, take jaririn ya faɗo ya fara mutsu-mutsu yana tsanyarewa da kuka. Wani irin baƙin ciki ya turniƙe ta Jakadiya ta waiga tana kallon Fulani don sanin irin hukuncin da za su yanke, da sauri Fulani Umaima ta fita sakamakon manta kunamar da Bamaguje ya bata. Jakadiya ta tsugunna ta sa reza ta yanke masa cibiya, a tunaninta ko Fulani Umaima ta zubda makamanta ne tun da jaririn ya riga da ya zo duniya. Ta gama yanke masa cibiya kenan Fulani Umaima ta faɗo ɗakin hannunta ɗauke da wata ƙatuwar kunama, a daidai lokacin Fulanin ta sake wani yunƙurin babu jimawa wani jaririn ya faɗo. Kusan mutuwar tsaye gabaɗaya suka yi, fuska babu walwala Fulani Umaima ta ƙarasa ta ɗora kunamar a kan jinin da ke zuba daga ƙasan Fulani Babba, kunamar na fara zuƙar jinin Fulani babba ta yanke jiki ta faɗi jikinta na wani irin karkarwa. Fulani Umaima ta saki shu’umin murmushi, sai dai kuma ganin jariran biyu ya sa ta samu shakkun wanda za ta aiwatar da mugun ƙudurin a kansa, na farkon da jakadiya ta yankewa cibi ta naɗe a zani ta ɗauka, take zuciyarta ta ƙwaɗaita mata wata shawara. Kiran Baiwa Maimuna ta yi ta damƙa mata shi, sannan ta ƙarasa gaban ɗayan jaririn da ko cibiya ba a yanke masa ba. Wutsul-wutsul yake yana kuka ta ɗauki kunamar da ke cikin jinin ta buɗe bakinsa da ƙarfin tsiya ta matse kunamar a cikin bakinsa. Take wani irin ruwa mai yauƙi haɗe da jini ya fara ɗiga a bakinsa. Kamar yadda yaro yake kama mama haka jaririn ya riƙa tsotsar jini da ruwa mai yauƙin. Ya jima yana sha sannan jaririn ya fara wani irin kakari wani farin ruwa mai haɗe da jini na fita daga hanci da bakinsa. Fulani ta waiga wurin Baiwa Maimuna ta furta, “Ina buƙatar ki fita ta ƙofar baya a sirrince, ki samu ƙaton kogi ki jefa shi ko kuma ki samu wani ƙaton ramin ki binne mini shi. Duk rintsi kada ki bar shi da sauran numfashi, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci.” Baiwa Maimuna da jikinta ya gama sanyi ta ce, “An gama ranki shi daɗe.” Har Maimuna ta yi gaba Fulani Umaima ta katse ta, “Iya ruwa fida kai. Kowa ya biya allonsa ya wanke. Ki tabbatar ba a samu matsala ba, wallahi matuƙar asiri ya tonu sai kin gayyaci mutuwarki da bakinki. Ni da kika ganni ba na ƙwaina sai da zakara don haka ki bi sannu, shawara ce na baki don kar ki bari kwaɓarki ta yi ruwa.” Baiwa Maimuna ta russuna rungume da jaririn ta furta, “Tuba nake ragamar damisa a ja ki da nisa. Na yi tsammanin kin fahimci somu-somun hauka zubda yawu. Mai ƙafa ɗaya ma ya yi rawa ballantana mai biyu? Indai ni ce har gaban abadan ba zan taɓa baki matsala ba.” Fulani Umaima ta saki malalacin murmushi ta furta, “Na aminta da ke Maimunatu, idan kin kammala komai ki samu Jakadiya akwai kyakkyawar kyauta. Amma ina buƙatar ganinki da zarar kin kammala.” Cike da girmamawa Baiwa Maimuna ta ce. “Godiya nake giwar Takawa fara mai farar aniya, sikari baki yi farin banza…”
“Ba mu da isasshen lokaci ki hanzarta ki fita.” Fulani Umaima ta katse ta a taƙaice. Daga haka Baiwa Maimuna ta fita daga sashen Fulani ta ƙofar baya, cikin duhu haka ta ci gaba da tafiya tana ratsa bishiyoyi da ƙayoyi har ta samu ta fita ta can bayan Masarauta.
Ganin har lokacin jaririn bai daina kakarin da yake yi ba ya sa Jakadiya ta dubi Fulani Umaima. “Ranki shi daɗe me zai hana mu ƙarasa shi tun da har yanzu bai ƙarasa mutuwa ba?” Da ido Fulani ta kafe jaririn.
“Bamaguje bai ba ni damar haka ba, ki tsaya kawai mu zura wa sarautar Allah ido. Kuma ni kaina ba na son ya mutu yanzu, na fi son na dasa wa Fulani Babba ɓacin ran da har ta mutu ba za ta manta da shi ba.”
Jakadiya ta jinjina kai a daidai lokacin da jaririn ya tsagaita da wannan kakarin, a lokacin Fulani Babba ta farfaɗo. Ta yunƙura a hankali da niyyar tashi da yake jikinta babu ƙwari sai Jakadiya da Fulani ne suka taimaka mata. “Sannu Yaya, barkanmu da arziƙi Allah dai ya kawo mana Yarima lafiya.” Fulani Umaima ta furta tana sakar mata murmushi, wani irin yammm take ji a jikinta kamar tafiyar kiyashi, jiki babu ƙwari ta sakar wa Fulani Umaima murmushi. Idonta ne ya kai kan jaririn da ke kwance ta kafe shi da idanu, wani abu take son tunawa amma kanta ya yi nauyi ta gagara tunawa. Jakadiya ta saki guɗa da ƙarfi tana ɗaukan jaririn da ilahirin jikinsa ya haɗe da gumi, ga wani irin zafi zam a kan fatar jikinsa. Guɗar da Jakadiya ta yi ce ta alamta wa Dogaran da ke kewaye da sashen saukar Fulani babba, kafin wani lokaci tuni labari ya isa wurin Mai martaba. Fulani da Jakadiya tuni suka gyara jariri da mai jego, an turare ɗakin da turaren wuta ko ina sai buga ƙamshi yake yi. Sai dai Fulani babba tana ƙare wa yaron kallo ta fahimci kamar idanunsa ba daidai suke ba, ga yawu da yake ɗan ziraro masa ta gefen bakinsa hancinsa na yoyon majina. Ƙura masa ido ta yi tana son tuna wani abu da ya shafi lokacin da take naƙuda har zuwa haihuwarta, sai dai nauyin da kanta ya yi ne ya haddasa mata ciwon kai ɓari ɗaya take jin kamar zai tarwatse mata. A hankali ta kalli Fulani Umaima cike da murmushi, “Na gode sosai da kulawarki ƙanwata.” Fulani Umaima ta saki murmushin yaƙe don saboda rufewar ido har gani take babu abin da maganin Bamaguje ya yi wa jaririn, amma saboda kissa sai ta furta. “Haba Fulani babba me ye abin godiya ina ce da kai da kaya duka mallakar wuya ne?” Fulani babba ta jinjina kai cike da jin daɗi ta ce. “Amma kuma yaba kyauta tukwici in ji masu iya magana.”
“Ai lamarin tuwona maina aka yi, ni dai bari na wuce Fulani na ji asuba ta fara ƙaratowa.”
Fulani Umaima na zuwa sashenta ta faɗa gado cike da tashin hankali. “Ya zame mini dole na ziyarci Bamaguje kuma a yau ba sai gobe ba sai ya hallaka mini Fulani da abin da ta haifa, idan ba haka ba zuciyata bugawa za ta yi.” Ta ƙarasa maganar tana shiga cikin uwar ɗakinta.
Tafiya mai nisa Baiwa Maimuna ta yi har sai da ta yi nisa da masarauta, ta shiga cikin wani daji mai duhun bishiyoyi. Kuka jaririn ya fara yana wutsul-wutsul, bankaɗa zanin ta yi ta ji tausayinsa ya mamaye zuciyarta. Da yake asuba ta yi haske ya fara mamaye cikin dajin, wani ɗan rami ta hango da ke gefen wata murgujejiyar bishiyar kuka, kallon bishiyar kukar kaɗai ya isa ya tsoratar da gangar jikin mammallakiyar ƙwayar idon. Da sauri ta ƙarasa wurin ta tsugunna sai a lokacin ta lura da zagayyan gidan tururuwar da ke wurin, taku ta fara jiyowa a ɗan nesa da ita da sauri ta saka shi a ciki ta bar wurin ta ɓoye a bayan wata bishiya, amma ga mamakinta sai ta ji shiru babu kowa. Gudun kada asirinta ya tonu ya sa ta fara zabga gudu ta nufi hanyar gida, a yadda take ji ba ta jin za ta iya kashe jaririn da bai ji ba bai gani ba, don rashin imaninta bai kai nan ba. Tana cikin gudun ta ji ta yi karo da wani abu garam! Har sai da ta faɗi ƙasa. Tsoro, firgici da matsanancin tashin hankali ya mamaye ta, take jikinta ya hau karkarwa sakamakon ganin bishiyar kukar da ta kwantar da jaririn a gabanta ta tsaya dass kamar yadda ta baro ta a baya.

Leave a Comment