COMPILED BY: ABUBAKAR SALEH AL~QUYRAEMEY
WHATSAPP GROUP: TOP HAUSA NOVEL
PHONE NUMBER: 08138873799
FACEBOOK: QURAMI HAUSA NOVEL GROUP
INSTAGRAM: ABUE QUYRAEMEY
For more Novel contact me at low ƴprice
Haske Writer’s Association💡
(Home of Experts and perfect Writer’s)
*SANADIN K’AWA*
NA
*khaleesat Haiydar*
BABI NA GOMA SHA HUDU
1
Tashi tayi daga xaunen da take kan yar katifar dake dakin xata fita da wayarta a hannu, warce ke xaune gefenta ta yi hanxarin rikota tace “Don Allah meye haka Fatima, wlknci ma xa ki min don na xo gidanku” komawa fatimar tayi ta xauna tace “Toh naga haka kawai kina neman xubar mana da aji ne, kuma ni yanxu gun Ammi xan je tun daxu ta kirani fah” kawartata ta hade tace “Kai Fatima ba wani xubar da aji, kema kin san don bani da waya ne ynxu, plss kiyi following dinsa ba don komai ba kawai don mu dinga ganin ko da hotuna ne plsss, ba fa magana xa ki dinga masa ba” Fatima ta wara ido tace “Anya kina da hankali kuwa Husnah, I can’t stoop my self that low inyi following dinsa, you knw I have class” Husnah ta karbe wayar tace “Toh me class naji ni xan yi following din nasa ba ke ba ai” Fatima xata kwace wayar tace “Noo, amma ai Fatima Muhd xai gani ba Husnah Usman ba” Tsaki Husnah ta ja tayi logging Instagram, bbu bata lkci ta yi following wanda take ta nacin su yi following, Fatima dake kallonta tace “Dubi Private account ne fa, Allah ya sa yyi accepting din naki ma tukun” Husnah ta fashe da dariya tace “Ka ji ta, ae dai Fatima xai gani ba Husnah ba” Fatima ta bude baki tace “Au haka ne ma koh? to wllh xan yi canceling yanxun nn” Da sauri Husnah ta boye wayar a bayanta tace “A’a kiyi hakuri plss” Fatima ta turo baki tace “Haka kawai yaje ya raina mu” Husnah tace “Ba xancen raini, xuwa anjima nasan xai yi accepting din request din” Muryar Ammi mahaifiyar Fatima suka ji ta na kwalo mata kira, Fatima ta mike da sauri tace “Kin gani koh…..” fita tayi tsakar gidan Ammi dake tsaye ta gama shanya wankin da tayi tace “Ni xan daura ma yara girki kafin su dawo makaranta kenan” Ta tsuke fuska tace “Ammi wai da fita fa xa mu yi da Husnah tun daxu kuma na gaya maki” Ammi tace “Toh ki fita” daga haka ta koma dakinta, juyawa tayi kamar xata yi kuka ta koma dakinsu, Husnah tace “Wai me?” “Kinji wai in daura ma su Ummi girki, ko wa xai dinga masu idan na bar gidan” Husnah ta kyabe baki tace “Ae sai hakuri nima haka inna ke takura ni a gida wllh, sai naji dama bamu gama secondary ba” Fatima tace “Wllh kuwa ni xaman gidan nn gaba daya ya isheni ma” Husnah ta yi dariya tace “Toh kice Umar ya turo kawai mu sha biki” Fatima ta yatsine fuska tace “Ke ni fa Umar din nn haushi yake ban yanxu, duk naji ma ni na tsane sa” Husnah ta xaro ido tace “Saboda me?” Fatima ta gyara xama tace “Kinga saurayin Sa’adatu kuwa, kinga irin motar da yake xuwa gunta da shi da daddare, hmm baxa ki gane ba, yanxu ba kayanta ba, har takunta ya canxa wllh, i can’t deny envying her, shi yasa ynxu ko magana ma bana mata wllh, ko ta min yi nake kamar ban ji ta ba” Husnah ta yi tagumi tace “Nima wllh ynxu Sa’ad haushi yake ban, ko ya xo bana fita, tun daga farkon layi wnn shegen mashin din nasa da ya rube yake announcing present dinsa, am just bored of him wllh” Dariya sosai Fatima take yi tace “To ba gwara ke yana da mashin din ba, Umar me xuwa min da kafa fa?” Husnah tace “To ba shi yasa nake son mu ma mu faso gari ba, yanxu ace Elbasheer din nan yayi accepting dinmu mu d’an fara masa magana kin ga ai wataran mu ma dawowa kamar Sa’adatu xa mu yi” Fatima ta yi shiru bata ce komai ba, Husnah tace “Allah kuwa Fatima ki duba ki ga” Fatima ta tabe baki tace “Allah yasa ya ma yi accepting din ma dai” Husnah tace “In sha Allah xai yi, idan kinga yyi don Allah ki daure ki d’an ajiye jan ajin nn ki masa sallama” dariya kawai fatima tayi, sai kusan karfe biyu suka fito dakin, ta tarar har Ammi ta kunna coal ta daura sanwan, Tace “Lah Ammi wllh ban ce baxan yi ba” ko kallonta Ammi bata yi, Husnah tayi kasa da murya tace “Toh ba sai kin raka ni ba kar laifin yyi yawa sai mun hadu….” daga haka ta nufi soro tana kallon Ammi tace “Ammi sai gobe xan wuce” ba tare da Ammi ta kalleta ba tace “Toh ki gaida mutan gidan” Husnah tace “Xa su ji” daga haka ta fita, Fatima ta karasa tace “Ammi kiyi hakuri ni ban ce fa baxan yi ba” Ammi tace “Wannan kuma ya rage naki Amira, in dai irin kawayen da xa ki dinga ajiyewa kenan wllh kina tare da wahala, kuma ki bace min da ganin kada raina ya sake baci” Fatima bata ce komai ba ta koma daki tana turo baki. Jin ring din wayarta a karo na kusan uku Ammi dake xaune tabarma suna cin abinci da yaranta biyu tace “Wai Amira ba kiran wayar ki ake yi ba” Fatima dake xaune kan nata tabarmar daga bakin kofar dakinsu da kwanon abincin ta a gaba tace “Ehh Ammi ni baxan iya fita ba ne” Ammi tace “Wa ke kiran ki?” Ta hade rai duk da ba ganinta Ammi take ba saboda duhun tsakar gidan tace “Umar ne” Ammi tace “Shine baxa ki fita ba?” Tace “Ni na gaji Ammi duk kaina ma ciwo yake min shi yasa baxan ma daga ba” Ammi tace “Toh yyi kyau” bata sake ce mata komai ba, Fatima ta gama cin abinda xata ci a abincin ta mike ta shige daki, ta gyara gun kwanciyarta ta kwanta duk ta kagu Ammi ta shiga ciki ta aiki kanwarta ta siyo mata kati don tun daxu da rana sub dinta ya kare, wani littafin hausa ta dauka tana karantawa har kaninta suka shigo dakin, mikewa tayi ta bude jakar kayanta ta fiddo dubu dayan da Umar ya bata da ya xo shekaranjiya tace “Ummi kati xa ki xubo min na dubu daya” Ummi tace “Na dubu daya fa kika ce” Fatima tace “Ba Sajjad idan baxa ki ba malama” fita Ummi tayi dakin ba tare da tace komai ba ba a jima ba ta dawo mata da katin, Tana gama loading dinsa ta yi sub ta bude data, bbu bata lkci WhatsApp messages dinta suka soma shigowa sannan Instagram, bata yi concentrating kan na WhatsApp din ba ta bude IG kawai, tsuru tayi ta na kallon sakon dake nuna mata Elbasheer yyi accepting follow request dinta sai dai bai yi following dinta back ba, ta hade rai sosai, fita tayi a gun nan idonta ya sauka kan hotonsa da yyi uploading 3 days back with more then 6k likes, tsaye yake jikin mota ya Rungume hannayensa ga wani makeken gida dake gefensa kamar a turai, flowers masu kyau ne xagaye gidan ga motoci kusan biyar tana hangowa, he is an epitome of true handsomeness, don yyi kyau har ya gaji a milk geznar dake jikinsa yana kyalli, dogo ne shi ba na wasa ba, don irinsu ake kira da gentlemen, yana da haske amma ba sosai can ba, ga dogon hancinsa da manyan idanuwansa da ya kara fito da ainahin kyawunsa, ta kalli bakinsa me xagaye da millionaires belt ga sajensa dake kwance, lkci daya jikinta yyi sanyi, kawai Husnah so take su yaudari kansu, me wannan handsome din d’an masu kudi xai yi da su ‘ya yan talakawa, ta sauke ajiyar xuciya a hankali ta shiga duba duk hotunansa, kasa ci gaba da kallonsu tayi don gani take xata iya suman kwance, irin wnn kyan da Allah yyi masa haka, cike da courage ta shiga DM dinsa ta tura masa da sallama complete without short cut, yatsine fuska tayi tayi log out, ta koma WhatsApp, tayi replying chats dinta sannan ta kashe data, tunani ta dinga yi na wannan bawan Allah, duk taji ai fa ita gaba daya duniya ta tsani Umar har ranta, daga haka bacci ya dauketa, da asuba da mafarken Elbasheer ta farka kamar ynda ta kwanta da tunaninsa, ta tada kanninta su yi sallah, ita kuma da bata sallahn wanka tayi ta wanke baki ta kintsa kanta ta dawo ta kwanta daki ta jawo wayarta ta kunna data, bata ga alamar ya ga message din nata ba ta mayar da wayar a sanyaye, har karfe sha biyun rana bata da wani kuxari, ta kasa daina tunanin Elbasheer, kunun da Umma ta dama masu ma daxu da safe kadan ta sha, duk bayan wani lkci xata bude data ko xata ga message dinsa amma shiru ko bude msg din bai yi ba har lkcn, sake tura masa Hi tayi ta kashe data, tana xaune bakin coal pot amma bata san shinkafa da waken da take dafawa har ya fara konewa ba, kawai jin tsawar da Ammi tayi mata tayi, ta dawo duniyar tunanin da ta tafi a firgice, Ammi tace “Uwar me kike tunani kike konar min da abinci kan wuta?” Da sauri ta dau tsumma ta sauke abincin tace “Kiyi hakuri Ammi bacci na fara yi” wani mugun kallo Ammi ke mata, ta mike kan kujerar da take ta shiga d’an ginin dake tsakar gidan a matsayin kitchen ta fiddo karamar tukunya ta fito ta shiga dakin Ammi ta dau jarkan mai ta xuba tukunya ta daura man kan wuta ta yanka albasa, yana soyuwa ta sauke ta xubda gawayin ta xuba ruwa ya mutu ta wuce ciki bayan ta juye shinkafa da waken a cooler ta kai dakin Ammi, sannan ta fito ta wuce daki da sauri jin wayarta na ruri, hararan wayar tayi ganin Umar ne don a ranan ya kirata yyi sau hudu tayi silencing wayar tayi Kwanciyarta lkci daya bacci ya dauketa, Sai kusan la’asar ta tashi shi ma kaninta dake shirin islamiyya ne suka tadata da 6uruntunsa, ta ja tsaki ta dau wayarta ta fita tsakar gida, Ammi dake kulla kayan sana’arta na kubewa da Kuka tace “Ke kin yaye xuwa islamiyyar ma ynxu ko Amira, baki da aiki sai bacci da danne dannen waya sai kuma kawayen dake xuwa maki kin mayar da su uwarki da ubanki, kina xaton ni kike ma koh, ae Umar ni ya cuta da ya siya maki wannan shegiyar wayar dake neman kai ki ga halaka” kamar xata yi kuka tace “Ammi wai ni fa ba ko da yaushe nake rike wayar fa…” Tsawa Ammi tayi mata, ta mike hawaye cike idonta tace “Kuma ni na gaya maki malam suraj ya sa min ido a makarantar ne gwara kawai in dinga haddata a gida” daga haka ta shige daki ta kunna data, ga mamakinta taga Elbasheer yyi uploading hotunan wasu mata biyu masu kama da shi Wanda ga dukkan alama kaninsa ne don a caption din ma cewa yyi Blood, ta duba DM da tayi masa taga har lkcn bai bude ba, ranta yyi mugun baci, tayi saurin yi masa typn kamar haka “Toh sannu babba, irin kai wani din nan da baxaka iya replying din message din mutane ba koh, to ni ka san wacece ni da har xaka shareni bawai ka san abinda xan gaya maka ba, plss keep ur girman kai and ji da kai for your family meeting malam” ta hada da emojin jan fuska ta tura masa ta kashe data ta ajiye wayar ta fara shirin xuwa islamiyyar da Ammi tayi mata magana, bata tafiya da waya don haka daga ita sai jakar makarantar ta ta fita gidan bayan tayi ma Ammi sallama, sai kusan shidda da rabi suka dawo gida, ko uniform bata cire ba ta bude data, gabanta yyi mugun faduwa ganin message din Elbasheer.
[9/18, 8:37 AM] Abue Saleh Kurami: KUNDIN HASKE
Haske Writer’s Association💡
(Home of Experts and perfect Writer’s)
*SANADIN K’AWA*
NA
*khaleesat Haiydar*
BABI NA GOMA SHA HUDU
2
Bude IG din tayi ta shiga DM din, “Really” shine reply din da yyi mata, ta mayar masa reply ita ma tace “You reason it….” Xata ajiye wayar sai ga message dinsa yace “Ok then” turo baki tayi ta rubuta masa “Reply my salam now” bayan kusan minti daya ya turo mata message da “Wslm” bata san lkcn da wani murmushi yyi escaping lips dinta ba, sai ta rasa me xata kara ce masa, can dai tace “Good” bai sake mata reply ba, ta mike ta fita xuciyarta fes. Karfe goma ta gama gyara gun kwanciyarta ta dauko wayarta daga caji kasancewar akwai wuta, ta kwanta dai dai nan kiran Umar ya shigo wayarta, tsaki ta yi kawai ta daga kiran, da damuwa yace “Are you okay Fatima, I’ve been calling tun jiya you are nt responding” murya can kasa tace “Bani da lafiya tun jiyan” yace “Subhanallah, what’s wrong, me yake damun ki” yamutse fuska tayi tace “Xaxxabi” yace “Ya salam, kun je asibiti?” Tace “Eh mun je” yace “Amma da sauki yanxu?” Ta tabe baki tace “Shi yasa na daga kiran” yace “Toh Allah ya kara lafiya gobe xan xo da safe” a takaice tace “Toh” yace “Ya su Ammi?” Tace “Lafiya” yace “Toh shkkn ki kwanta my dear, Allah ya sauwake, I will cal tomorrow” tace “Toh” kafin ya kashe wayar ta kashe sannan ta kunna data, ga mugun mamakinta sai ta ga follow request din Elbash don ita ma private ta mayar da account dinta duk da ba ta taba sa hoton ta a IG ba sai hotunan kananun yara masu kyau followers dinta sun kusa dubu takwas, and she is just following few, ta wara ido cike da farin ciki ta yi accept dinsa, tayi ta jira taga ko xai mata magana amma shiru, tana son tayi DM dinsa amma ta kasa don bata ma san abinda xata ce ba, can dai ta daure ta tura masa message kamar haka, “I am Fatima Muhd the daughter of the former minister of Education in Nigeria, am studying pharmacy at Cambridge uni, currently home for holiday, what more….” Bayan kusan minti biyar ya turo mata message kamar haka
“Is there any need of what I didn’t ask?” Xaro ido tayi ganin abinda ya turo mata, ji tayi kamar kasa ya bude ta shige, ta cije lebe gwiwarta a sake ta mayar masa reply “Mtsww na fi karfin ka min wlknci malam don na fi ka nesa ba kusa ba, I pinged you for a purpose…. dat aside da baka kai matsayin inyi following ka ba bare in fara maka introduction, who did you think you are?” ta murguda baki ta tura masa bayan ta gama typing din, ba a dau lkci ya mayar mata reply kamar haka “Really?” tace “Yes” ya bude message din sae dae bai yi reply ba ta yi ta jira amma shiru har ta fara jin bacci, ta kashe data rai ba dadi ta kwanta lkci daya bacci ya dauketa. Washegari da ya kasance laraba har kaninta suka tafi makaranta bacci take, Ammi kuma bata tasheta ba tana ta aikace aikacen gida, sai kusan karfe goma ta tashi ta fito waje ta Debi ruwa a rijiya don yin wanka, sai da ta fara wanke baki sannan ta shiga wankan, ta dau lokaci tana shafe shafenta ta fiddo atamfarta ta saka kasancewar ranan juma’a ce sai a sannan ta fita ta shiga dakin Ammi ta ganta tana karatun al-qur’an, ta bude cooler da ta gani a rufe taga kunu ne sai kosai dake cikin leda, tasan nata ne, ta yamutsa fuska ta juya ta koma dakinsu, wayarta da tayi plug da Asuba a charge ta cire, ta bude data, still tayi tana kallon message din Elbash… “Send your face” Bata san lkcn da ta fashe da wani dariya ba, tana murmushi ta rubuta masa “For what?” Ashe yana kusa sai ga shi ya mayar mata yace “I don’t chat with people i don’t knw facially” wani murmushin tayi tace “I don’t think that bunk policy of urs is true coz u have been chatting with me since yesterday” ya mayar mata da cewa “And What are you insinuating?” Ta fashe da dariya tace “What you are thinking ryt now” yace “Are you calling me a liar?” Ta wara ido tace “Is that what you were thinking, ohk then so be it, that was what I insinuated” Yace “How dare you” ta tura masa emoji din dariya tace “Whatever” yace “Ohk xa ki gane baki da wayo” ta tura masa da cewa “Babu abinda ka isa ka min malam, ni ban ce xaka gane baka da wayo ba sai kai?” Yace “Ohk” ta tura masa da gwalo da dariya, ya bude bai ce komai ba, ring din wayarta ya sa ta tsaida dariyar da take, Umar ne ke kiranta, ta hade rai ta daga, yyi sallama yace “Kin tashi lafiya dear” kamar ana tilasta ta tace “Ina kwana” yace “Lafiya lau ya jikin?” Tace “Na ji sauki” yace “Xan je kasuwa ne na biyo in duba ki am outside yanxu” tace “But is there any need?” A hankali yace “There is pls Fatima” ta tabe baki tace “Gani nan xuwa” daga haka ta katse wayar ta mike ta dau gogaggen Hijab dinta ta saka ta fita xuwa dakin Ammi, durkusawa tayi gefenta tace “Ina kwana Ammi” bbu yabo babu fallasa Ammi ta amsa, tasan laifinta daya bata tashi da asuba ba yau duk da bata sallah, a hankali tace “Ammi Umar ne ya xo yana waje” Ammi tace “Ya rage naki kuma” ta yi shiru kafin ta mike ta fita, yana tsaye jikin bango ta samesa, Sanye yake da shadda fara kal da hula, Umar xa a sa shi a sahun handsome guys, he is handsome, kana ganinsa ka ba bafillatani da tsayinsa, a Kano yyi Bsc dinsa a fannin Biochemistry, yyi masters kuma a medical Biochem, aiki da bai samu ba tukun yasa yake kasuwancinsa a nan Suleja don family house dinsu na nn, sun hadu da shi ne tana ss1 lkcn ma bai gama karatu ba, ita kanta tasan son da Umar ke mata ya wuce misali ita ma a da tana sonsa sosai amma tunda taga kalan motar saurayin sa’adatu taji duk duniya bbu wanda bata so kamar shi, a da bbu wanda ke mata kyau a maxa kamar shi, amma tun da Husnah ta fara nuna mata wayayyun maxajen IG taga ashe ba ma shi da wani kyau, Elbash ya fi sa kyau da wayewa nesa ba kusa ba, ta turo baki ta rungungume hannu tace “Gani” a hankali yace “Ya jikin?” Tace “Na ji sauki” yace “Allah ya sauwake, ya Ammi fa?” Tace “Tana lafiya” yace “Toh ki gaishe min ita, Xan fita kasuwa ne, just want to check on you” tace “Nagode” dubu biyu ya ciro ya mika mata yace “i wanted getting some fruits for you but it’s too early ba su fito ba, gashi ki aiki su Ummi su siyo maki anjima” tace “A’a ka barsa naji sauki ai, thank you” yace “No take it pls dear” ta d’an yi jim kafin ta risina ta karba tace “Nagode” yyi murmushi yace “No thanks baby” juyawa tayi tace “Sai anjima” daga haka ta shiga gida, sakonsa na gaisuwa kadai ta ba Ammi sannan ta wuce dakinsu ta boye kudinta. Bayan an sakko sallar Juma’ah fatima tace ma Ammi xata je gidan wata kawarta da tayi aure Safia, da kyar Ammi ta bari taje kasancewar bata barta taje bikin ba sbda su Husnah, hijab dinta har kasa ne jikinta ta fita gidan sakale da jakarta, ta samu adaidaita ta hau, tana kallon suka wuce hanyar gidan Safia ta turo baki ta kauda kai, sai da ta kai inda xata je ta fito ta basa kudinsa ta shiga gidan, duk da kasancewar gidansu d’an karamin gida da mahaifinsu ya rasu ya bar masu gidan ya fi na su Husnah nesa ba kusa ba, Tsakar gidan kaca kaca ga kwanuka da kaya ta ko ina, Inna mahaifiyar Husnah na xaune tsakar gida tana yankan awara dafaffe, ta duka har kasa ta gaisheta, ta washe baki tace “A’a Fatima daga ina haka” tace “Daga gida Inna” Inna tace “Ikon Allah, Ya su Amina?” Tace “Suna lafiya inna, Husnah na nan?” Tace “Wllh kinga tun safe ta fita ban ma san inda tayi ba, amma nasan baxata wuce anguwar nan ba, ki kira lambarta” nace “Toh” tace “Ki shiga dakinsu ki xauna” mikewa tayi ta nufi dakinsu Husnah na shiga, ita dai tasan a responsible rat will not live in that room don bayan datti, untidiness har da wari yake, ta raba na xauna gefen katifarsu da yyi dukun dukun ta shiga kiran layinta kasancewar tana da sauran bonus, bugu biyu ta dauka tace “Mara kirki sai yau xa ki kirani bayan ko asi bani da shi tun ranan da na bar gidan Ku” Fatima tace “Ke ina fa gidanku ina kika je?” Tace “Kaji ta, ke din ce xa ki xo gidanmu” Fatima tace “Kinga ni ba wani kati me yawa gareni ba, wllh ba wasa nake ba, Inna tace tun safe kika fita” cike da farin ciki Husnah tace “To to Gani nan xuwa ban yi nisa ba” daga haka ta katse wayar, Fatima ta tabe baki, kafin minti goma sai gata ta shigo dakin ta rungume ta tace “Wayyo Ashe da gaske ne, welcome besty” Fatima na kallonta tace “Ina kika je tun safe” Husnah tayi kasa da murya tace “Kinga saurayin Sajida ne yace xai kai mu outing yau, tun safe muke jiransa har yanxu shiru ni har na fidda rai Wllh kilan ma karya ya shirga mata” Fatima tayi dariya tace “Kuna da aiki, ni ba wannan ba, kinsan wnn Elbash din yyi following dina back har mun yi chat” Husnah ta xaro ido tace “Kice Wllh” Fatima ta fashe da dariya tace “Wallahi” wani uban tsalle ta doka tace “Bani in sha kawata, garin yaya” Fatima na murmushi ta bata wayar bayan ta bude IG dinta ta shiga DM dinta da Elbash, Husnah ta nutsu tana karanta messages din, lkci daya ta hade rai tace “My God, to ai tsokanarsa kike ta yi Fatima, dubi fa irin maganganun da kike ta gaya masa marasa dadi” Fatima tace “Uhm ai d’an rainin wayo ne shi yasa nake basa amsa dai dai shi” Husnah ta dafe kai tace “No that was not our plan fa besty, ke da xaki dinga lallabasa” Fatima tace “Tabdi, ya raina ni kenan, ke bari kiji yanda yake jin kansa fa nima haka nake jin nawa kan” Husnah ta fashe da dariya tace “Ke a wa” ta hade rai tace “Ni a mutum” Husnah tace “Yanxu har yace ki basa photo ki ki, haba Fatima you want to spoil d plan kenan” Fatima tace “Ke dadi na da ke baki da jan aji wllh” Husnah ta saki baki tace “Jan aji a wannan xamanin, ai kam xa ki ja har ya tsinke Wllh” Dariya Fatima tayi tace “Koh” Husnah tace “Wllh da gaske, yanxu don Allah ki tura masa hoton” Fatima tace “Tabdi bayan nace masa A’a” Husnah tace “Wllh sai kin tura, to don me dama nasa kika yi following dinsa tun farko” daga haka ta dau waya tace “Bari in duba gallery din muga ko akwai hot pics” tabe baki tayi bayan ta dudduba tace “Ba background me kyau a hotunan, jira akwai wata da muka hadu a IG kusan shekara daya kafin wayata ta lalace, yar masu kudi ce Wllh, idan kika ga gidansu sai kin yi suman tsaye, kinga irin flowers da motocin gidansu kuwa, kusan duk sati sai na je gidan Wllh, amma fa da nisa daga nan don kusan dari uku ne kudin mota xuwa da dawowa, yanxun ma can xa mu je kiyi hoton har kaya ma xata iya ara maki na sani, Allah yasa kin fito da kudi don ni ko taro bani da” Fatima ta saki baki tace “Husnah???” Mikewa Husnah tayi ta dagata tace “Dallah muje kada yamma yyi” daga haka suka fita tace “inna bari mu je gidan wata kawarmu mu dawo yanxu” Inna tace “Toh Allah ya kiyaye hanya, A kula da titi, Fatima kar fa ki wuce daga can ki dawo ki kai ma mamarku awara” Fatima tace “To inna na gode” daga haka Husnah ta ja ta suka fita gidan xuwa inda xa su hau mota.
[9/18, 8:37 AM] Abue Saleh Kurami: KUNDIN HASKE
Haske Writer’s Association💡
(Home of Experts and perfect Writer’s)
*SANADIN K’AWA*
NA
*khaleesat Haiydar*
BABI NA GOMA SHA HUDU
3
Duk yanda Fatima ta so hana Husnah su je gidan warce ta kira da kawarta kin saurarenta tayi haka ta tilastata sai da suka hau mota suka dau hanyar gidan kawarta da suka hadu da a IG me suna Sadiya, Allah ya so ta fito da kudin da Umar ya bata daxu da safe, Tafiyar kusan minti talatin da wani abu suka yi kusa da cikin garin Abuja kafin su iso gidan, sun dade bakin gate don sai da mai gadi yaje ya sanar da xuwansu kafin su shiga gidan, tunda Fatima taga irin kallon da yan gidan ke ma Husnah jikinta yyi sanyi kana gani kasan sun gaji da xuwanta, Sadiyar ma sama sama ta kula su bayan ta fito kafin ta kawo masu ruwa da kayan flour, tuni Husnah ta sauka kasa ta fara cin abubuwan dake gabansu, Fatima ta ki cin komai don duk ranta ya gama baci, Sadiya dai na xaune tana kallo a Tv don duk yan gidan da suka tarar a parlor sun bar parlorn, Husnah ta cika baki da cake ta ce “Kawata mun xo neman wata alfarma ne gun ki don Allah….” Sadiya ta kalleta tace “Toh ina ji” Husnah ta kora cake din da drink ta mike tace “Toh ina xa mu je muyi maganan?” Tashi Sadiya tayi ta fita balcony Husnah ta bi ta tana kashe ma Fatima da ta hade rai ido, bayan sun fita nan ta gaya mata abinda yasa suka xo, har da risinawarta tana roko, Sadiya da ta d’an yi jim tace “Har da kaya?” Husnah tace “Hoto kawai xata yi wallahi” Sadiya tace “Shkkn ba matsala” amma kana jin ynda tayi furucin kasan takaici ne ya isheta, dakin mai aikinsu ta kai su, Husnah na rike da hannun fatima da taki sake fuska tana bin ko ina na dakin da kallo tana cewa maa sha Allah, Allah ka bamu irin haka, suna ta xaune dakin sai ga Sadiyar ta shigo da kaya hannunta da abun kwalliya, nan ta mika ma Fatima kaya na Riga da skirt da kayan kwalliya da mayafi, ta juya xata fita Husnah tace “Ki yi hakuri ki d’an ara mana wayar ki xai fi kyan hoton kuma xa mu yi wasu a nan” Sadiyar ta kalleta sannan ta xauna dakin tace “Toh idan kun gama sai in mata” har Husnah ta gama yi ma Fatima kwalliyar kallonsu Sadiya take, a xuciyarta kuma addu’ar shiriya da Allah ya raba su da karya take barin Fatima da ta yi mata kyau sosai, ba laifi Husnah ta iya make up sosai don ba karamin kyau Fatima tayi ba duk da bata yrda ta cika mata kwalliyar ba, Sai washe baki Husnah take ganin yanda ta fito da kawartata, ta juya ta kalli Sadiya tace “Toh dauketa hoton kawata” nan Sadiya ta mike don daukar Fatima hoton, sosai Fatima tayi mata kyau sai dai taki sakin fuska, kusan biyar ta dauketa a daki, Husnah tace “To ya isa haka mu je waje” tana rike da hannun fatima suka fito compound, nan ma sadiya ta dinga mata hotunan, Husnah na nuna masu background, sae jaraba take wai fatima ta tsaya dososo taki murmushi, Fatima ta galla mata harara tace “Ke kar fa ki dameni wannan din da nake fa, ni na ma gaji ki rabu dani” ba shiri Husnah ta ja bakinta tayi shiru, Sadiya dake ta kallonsu ta d’an yi murmushi tace “Toh wannan na karshen dai ki daure ko dariya kiyi xae yi kyau sosai” Fatima bata san lkcn da tayi dariyar ba a haka Sadiya ta dauketa Wanda duk hotunan babu Wanda ya kai sa kyau, Husnah sae murna take, a nan kuma aka gama daukar hotunan suka koma ciki Sadiya ta tura masu duk hotunan a wayar Fatima, Fatima ta mayar da kayanta ta linke na Sadiya ta ajiye tana kallonta tace “Sister nagode sosai” Sadiya tace “A’a ki tafi da su na bar maki” nan Husnah ta canxa fuska sae dae bata ce komai ba, sai da suka tashi tafiya tace “To ni baki bani kayan ba Sadiya ko na maki wani laifi ne” Sadiya ta yi murmushi tace “Bari in dubo maki to” daga haka ta tafi dakinta ta dauko mata wani kayan ta bata, Husnah ta dinga godiya har da durkusawa tana washe baki, Fatima da takaici ya isheta ta fice daga dakin suna biye da ita, a bakin gate Sadiya ta basu dubu daya kudin mota Fatima ta mata godiya ta fita ta bar Husnah dake ta godiya kamar wata marokiya ta dau hanyar titi, da gudu Husnah ta kamota tace “Kinga masu kirki koh, kuma ace duk sati baxan dinga xuwa nan ba, ko don irin cimarsu ni bbu Wanda ya isa ya hanani xuwa wllh” Fatima dai bata tanka ta ba har suka shiga mota xa su koma Suleja. Sai kusan karfe biyar da rabi suka isa gidansu Husnah, Fatima da duk hankalinta ya gama tashi tace “Kinga baxan shiga ba xan samu adaidaita daga nan in wuce gida nasan Ammi na can tana jirana na dde sosai, sai mun yi waya” Husnah ta rikota tace “Toh amma banda masa bakar magana plss, ki kara editing hotunan ki tura masa masu shegen kyan ciki plsss ki rufa mana asiri mu ma mu faso gari kwanan nan” Fatima tace “Naji ni dai sai mun yi waya” daga haka ta wuce da sauri ba tare da ta damu da dubu dayan da aka basu da Husnah ta boye a jaka tun daxu ba, adaidaita ta samu ya kaita har kofar gida, Ammi dake tuka tuwo tana xaune kan kujera kusa da coal pot bata ko amsa sallamarta ba, a sanyaye ta durkusa nesa da ita tace “Don Allah don annabi Ammi kiyi hakuri nasan na dde sosai, kinga dambu tace in tsaya in koya mata bata iya ba kuma shi xata yi, shine kawai na tsaya na girka mata, kiyi hakuri Ammina” Ammi ta kalleta tace “Toh ni na ce maki wani abu ne Fatima” Fatima tayi shiru bata ce komai ba, Bude ledan da ta shigo da tayi ta fiddo kayan ciki da mayafi tace “Gashi Ammi ta bani, nace ta bari na gode amma ta ki saurarana” Ammi tace “Allah ya saka da alkhairi” Fatima ta sauke ajiyar xuciya a hankali tace “Ameen” sannan ta mike ta shiga cikin dakinsu tana murmushi. Ita ta karasa sauran aikin gidan Ummi na taya ta, suna gamawa ta daura ruwan wanka ta koma daki, sae kusan shidda ta fito tayi wankan ta daura alwala ta shiga daki, Ta gama shafe shafenta ta saka doguwar riga ta dau wayarta ta hau saman gado ta bude data, IG ta shiga ta duba DM dinsu da Elbash taga har lkcn bai ce komai ba, ta d’an yi jim, sai kuma ta tura masa “Are you ready to listen to why I followed you and went ahead to ping you?” Daga haka ta fita ta koma WhatsApp, sai da taji kiran sllh ta kashe data ta mike, tana idar da sllh tayi azkar dinta sannan ta fita xuwa dakin Ammi, Ammi dake xaune Da Ummi da Yusuf suna cin abinci ta kalleta, xaunawa tayi gefen Ummi, Ammi dai bata ce mata komai ba tana jiran ta ji me ya kawota sanin bata shigowa sae idan abu ya kawota, Ita kanta she was uncomfortable can kuma ta mike xatah fita Ammi tace “Kin ci abincin ne?” Fatima ta kalleta tace “Shi xan je in ci ynxu” Ammi dai bata ce mata komai ba har ta fita, ta rasa irin yar tata, bata taba ganin yar da ke kin sakewa da uwarta kamar Fatima ba, Fatima ta debi tuwo kadan da miyar kubewa ta saka cokali ta wuce daki, har ranta ta tsani cin tuwo, ta gama jagwalgwa shi ta tura gefe ta dau wayarta ta bude datan ta, message din Elbash ta gani yace “I am not interested” tsuru tayi tana kallon message din, can tayi murmushi tace “is that so??” ya bude message din yaki cewa komai, bayan kusan minti sha biyar tace “u knw something I already knew about you even before chatting u up?” bayan wani lkci yace “That’s ur cup of tea…”
[9/18, 8:37 AM] Abue Saleh Kurami: KUNDIN HASKE

Leave a Comment