Books Reviews & FAQs

Sai A Lahira Hausa Novel Complete

Sai A Lahira Hausa Novel Complete

 

 

Muje zuwa gidan iko

*NA*
*HADIZA BARA’U GIDAN IKO*

*🅿️age 1*

 

*_Wanan litafin malakin gidan iko ne ban yarda a juyamin shi tako wace fuska ba batare da izinina ba Dan haka a kiyaye_*

*_Kamar yanda na nishadan tarda ku a litafina na ZAN FASA KWAI yau ma gani da sabo mai saban salo Mai taken SAI A LAHIRA daga ji sunan shi basai nace komai ba labari ne Wanda duk ya karanta Sai yayaba Dan haka kubiyoni Dan jin yanda zata Kaya da a na kudi nai niyar sakin shi saboda soyayyar da kukemin da addu’ar ku yasa na sakeshi free da fatan zaku bani goyan baya duk da hakan Dan dai in Kara faran ta muku da akwai book dina Mai taken HAWAYE wannan na kudi ne akan 300 kacal zaki sha karatu HAWAYE bansan ya Zan kwatanta muku Shiba Aman duk wace ta cire 300 ta karantashi zatasan akwai abubuwan karuwa sosai a ciki da ban Al ajabi ga siradin rayuwa abin ba acewa komai Mai bukata zai iya tuntubata akan wanan number Dan in sata group din in tabiya 300 dinta kacal Sai a nunamin soyayya ta hanyar siyan book din akan farashi kalilan_*

_ga hanyar da za’a bi Dan siyan book dina HAWAYE 1780003378 Eco bank ko katin MTN ta wanan layin 07064551049 Sai najiku masoya na hakika_

_In kinsan Dan kifitar zaki siya Dan Allah karki siya Amana daya ce wace taci ita da Allah_

 

 

*K* ayataccen wuri ne irin holl din Nan me girma Wanda ake gabatar da party irin na bikin Aure. Wurin ya kayatu da kyakkyawan tsari kasancewar angon babban kicima ne. Hasken fitulu ya haske tarwai ga kwalliyar docration me burgewa inda wakar nasara ke tashi tare da wani haske me sauya launi da Dole ya burgeka Yana ta canza launi.

Wata katuwar mota me numfashi ta faka inda jerin gwanon motocin suka faka Wanda kallo daya zakayi musu ka Gane sunci sun tada Kai lallai bikin na manyan gwaskaye ne. Kyauren motar ya bude inda amarya da ango suka fito Atare tamkar dai antsara yadda fitowar tasu zata kasance .
Amarya cikin shigar doguwar Riga irin ta bikin aure kalar fara tana Kuma lullube da mayafi me kama da net kafarta sanye da dogon takalmi kalar silver hade da Yar jakar shi silver colour fuskarta da make up me kayatarwa sai dai fuskarta amurtuke Babu annuri ko kadan inda angon ke ta washe Baki alamar Yana murna da wannan Rana akasin amarya. Ya lura da Amaryar Bata saki ranta ba akan abinda ya fada Mata.
Don haka ya rungumo ta Yana Kara Bata hakuri Amma dai Bata saki fuskar ta ba.
Suka Isa holl din yayinda abokan ango suka taho tarba inda wani bakin ciki ya Kara turnuke amarya saboda ganin Babu wata kawa Tata awurin wannan party Wanda aka Hana kawayen ta da Yan uwanta zuwa . Bata taba Jin irin wannan party ba na Hana Mata zuwa bayan amarya kawai. Ta dubi abokan angon Wanda suka zamo kamar angon nata wato masu abin hannun su kowane yanayin shi ya nuna yayi hannun Riga da talauci sai dai abinda ya Bata tsoro shine kowanen su ido jajir tamkar sun Sha wani abun maybe . Kuma Wai sunyi anko na jar shadda da bakar hula Dara. Ta lura da wani Jan zobe me girma da tagani wurin Bashir angon nata Wanda Bata taba kawowa ranta wani Abu akan zoben ba sai yanzu da taga abokan Bashir din kowane Yana sanye da shi a yatsan shi na tsakiya.
Kaf wurin party maza ne sai wata mace guda Daya da ta taho ta tarbeta cikin murna da farin ciki.ta kamo hannunta har Kan high table ta zaunar da ita.
Tabi matar da kallo inda taga matar tayi Mata Kama da Yar duniya farace tas irin farin Nan na bilicin fuskarta da tsagen kalangu bakin ta dauke da hakorin makka guda biyu sama da kasa. Ta sake maida hankalin ta Kan abokan angon Wanda suka zubo Mata idanu da jajayen idanunsu inda taji wani matsiyacin faduwar gaba me tsanani ya risketa ta sunkuyar da kanta tanajin wani Abu me kama da nadama na son sauko Mata. DJ ya soma sauya kida yayin da mc ke ta babatu Amma Sam amarya zainab Bata fahimta saboda zuciyar ta ta SHIGA binciken shin waye angon nata Bashir? Kuma suwaye abokan shi masu jajayen idanu da jar shaddar su da Jan zobe?
Bata gama hada lissafin 4+4 ya Bata 8 ba taji an dafata akafada ta dago da kanta inda ta ga matar Nan me kama da Yar duniya tana Mata murmushi. “Kiyi fa hakuri amarya da abubuwan da Zaki gani kin San ko yaushe ilimin yawa yake karawa mu namu salon ya Sha bambam da sauran. So kar kiyi mamaki komai Kika gani kiyi hakuri kar ki nemi ba asi ko sanin Yaya abin yake? Kafin tasamu abin cewa don tambayoyi ne fal bakin ta inda taga matar Nan ta fito da wasu kwalabe Wanda bakin kwalbar bai Bata damar ganin abinda ke ciki ba.

Ta zubawa kwalbar ido zuciyar ta na fada Mata wannan kwalbar giyace! Matar ta kware ledar da aka nade bakin kwalbar da bincine marfin wani shegen tsami ya dira Kan hancin zainab wacce ta tabbatar da zaton ta na giyace a yau idon ta ke gani abinda Bata taba gani ba ko acikin mafarki sai gashi Wai giya abikin AUREN ta to meye hadin Bashir da abokanshi da giya?
Kafin ta samo amsar ta soma jiyo tsamin na sauka a kafatanin jikinta

Ta dago afusace tana kallon matar dake jifar ta da murmushi ta Kuma dubu Bashir da son ganin irin matakin da zai dauka sai taga Babu alamar zai yi wani Abu sai ma murmushi da ta karanto a fuskar shi
Zuciya ta zo Mata wuya ta Mike da son sharawa matar Mari akan yafa Mata ruwan giya Amma sai Bashir da ya lura da abinda take nufi yayi maza ya damke hannunta ya na kyar Mata idanu.
Haka matar Nan ta juye musu kwalbar giya biyu ajikkunan su kafin ta dire kwalaben
Inda bakin ciki ya saka Amarya kuka saboda tunda uwar ta ta haifeta ba ta taba ganin giya da idonta ba bare ace ta taba ta sai yau da ake Mata wanka da ruwan giya giyar da ta tabbatar babu abinda Hime da malam suka tsana Arayuwa irin ta.
Kanta na kasa tana shakar kuka kukan takaici da bakin ciki inda take Jun nadamar auren Bashir.
Sai Kuma ta Kuma ganin wani kayan bakin ciki inda aka soma dire musu abin tabawa Wanda ba abun tabawar ba hatta ita kanta kyamar kanta take.
Duk yadda matar Nan ke rarrashin ta da Bata hakuri akan taci wani Abu Amma Bata ko dubeta ba bare taci saboda bakin cikin dake damfare a ranta.
Abokan ango da mc me magana da salon ban dariya sai taji duk haushin kowa take ji mussamman Bashir da ya biye Mata ko waye shi Wanda a yanzu ita da kanta ta gama fassara ko waye shi abinda take Jin ba zata dauka ba.

Abokan ango suka taso suna bawa ango hannu suna gaisawa inda itama Daya daga cikin su ya Miko Mata hannu Wai suyi musabihar inda taji wani takaici na naushin zuciyar ta inda taso fashewa dama ta so ta amayar da abinda ke ranta akan wankan giyar da akayi Mata….

*I* donta taf da hawaye take kallon Bashir ganin gardin abokin shi ya Miko Mata hannu Wai su gaisa abinda Bata Saba gani ba. Ta zuba mishi ido da son ganin abinda zaiyi don asanin ta dai duk namiji me kishi ba zai taba Bari hakan ta faru ga matar da yake neman AUREN ta bare wadda aure ya zarga igiyoyin Sunnah. Sai taga yayi Mata alamar ta Mika hannun nata su gaisa da abokin nashi.

 

Hawayen ta ya silalo akan dakalin fuskarta cikin Rawar murya tace

“Bashir dama ka shirya wulakanta Ni ne akan tsinannun abokan ka da kace min sun fiye maka kowa da komai a DUNIYA?

“Dama don ka tozar tani ne yasa ka Hana kawaye na da Yan uwana zuwa don kar suje su bada labarin muguwar dabi ar ka da abokan ka? “Nayi nadamar sanin ka a Rayuwa ta nayi nadamar AUREN ka fiye da yawan shekaruna. Ayau na tabbatar da Ubangiji baya barin hakkin wani akan wani Kuma shi din me gaggawar Sakayya ne. “Na rantse maka da Allah Bashir na fasa AUREN ka idan har Kai kadai kayi saura a DUNIYA sai dai in mutu babu mijin aure…..

Ya tareta Yana me ruko hannuwan ta.

“Cool down my beby yi hakuri me ya Bata Miki Rai ne haka?

“Idan Kika fasa aure na in mutu kenan kike so? Indon na Hana Yan uwanki da kawayen ki zuwa Nan ne ai nace Zan shirya Miki wani kayataccen party agida na Wanda Zaki gayyato Yan uwanki da kawayen ki ko? Nan abokai na NE suka shirya Mana shi Kuma bama bukatar kowa sai amarya tuni na fada Miki Ina girmama abokai na duk abinda suke so zanyi musu shi koda Ni din bana ra ayin shi Raina ma zai iya Zama fansa agare su indai sun bukaci hakan So kar ki damu da duk abinda zasuyi Miki da yardata da amincewa ta hakan ta tabbata…….

Tayi saurin katse shi

“Kaji matsalar farko da zamu fara samu da Kai tunda har ka bawa abokai damar da Ubangiji bai Basu ba.”Ina tsoron yadda abokan ka zasu saka abinda ba zaka Musa masu ba akaina tunda har kake fada min ranka ma fansa ne garesu ina ga Ni da Zan kasance karkashin ikon ka? Zamana da Kai da su ba zaiyuwu ba wallahi don Kai da su nayi muku wata irin tsana wanda ban taba jin irin ta ba saboda giyar da nagani a muhallan ku da Jan idon ku ya Kara jefani cikin shakku karshe Kuma yadda ka Hana Yan uwana da kawaye na zuwa don kar su Dora ayar tambaya akan ku……

Wayar ta dake ta Kara tun dazu ta isheta da Kara ta jawo pos din ta fito da wayar inda ta iske kiran da ta rasa missed call kusan arba in da biyar na Yan uwan ta da kawayen ta.

Ta daga Kiran humaira dake shigowa

“Sannu Yar duniya shine Kika shanya mu kikayi tafiyar ki ke Yar Dadi miji ana ta Kira kin share mutane ai da Baki gayyato mu ba tunda kunyi nufin watsa mu……

“Kiyi hakuri humaira wallahi ban San haka ba nima……

“A a na bar Miki hakurin don ni har na zo gida ma a tashi taro lafiya ta tsinke wayar ta. Ranta ya Kuma baci inda matar Nan ta Kuma zuwa tana Bata hakuri akan haka suke nasu Sha anin . Abokan ango suka soma yiwa amarya kyautar girma inda kowanen su ya bawa amarya kyautar rafar dollars su goma Sha biyu haka suka dire Mata Rafa goma Sha biyu sai dai ta karanto wani babban alamari a fuskokin su da zuciyar su al amarin da ta tabbatar ba ALHERI bane

DJ da mc suka soma hada Kayan su saboda dare ya soma har Sha biyu da kusan rabi inda abokan ango suka soma ficewa matar Nan Yar duniya wadda taji sunanta Wai karisha ta dubi abokan da cewa tana Nan zuwa su saurareta bayan ta tambaye su hotel din da suka sauka suka fada Mata barewa suka sauka.

 

Karisha ta tattare Mata kudin da aka Tara Mata ta zuba Mata cikin wata Yar jaka ta Mika Mata ta dubeta ta dubi kudin

“Allah ya tsareni kar bar kudin mutanen can da Raina da hankalinki na Bai kwanta dasu.

Ta Mike tana Shirin barin wurin inda karisha ta kyalkyale da dariya

“Kai bash amaryar mu fa ta Shaka dayawa Ina ga Kuma Taji aikin dake jiranta? “Aikin da Kuma ya zamar Mata Dole tunda taci abin hannunmu

Suka biyo bayan zainab wadda ta tsaya abakin motar Bashir tana jiran yazo ya mayar da ita gida

 

Suka karaso shida karisha wadda zainab ke musu kallon Yan bariki wadanda Babu Allah a zuciyar su da ayukansu

 

“Zee kirawo gida ki fada musu mun wuce dake abawa Yan rakiya amarya hakuri tunda Kinga dare yayi….

Ta juyo arude

“Banji abinda kace ba Bashir? Da wane bakin Zan sanar da Hime hakan?

“Ba zaka Jamin abin kunya da abin fada ba kamaida Ni gidanmu gobe Yan uwa suyi min rakiya Amma ba Zan bika Ni kadai tsinken ragi ba . Karisha tace

“Bash Bari in kaita gida goben sai muje mu dauketa.

Karisha ta bude motar ta inda Bashir yace suje shi zai wuce gida.

Wani kololon bakin ciki ya turnuke zainab bisa Dole ta SHIGA motar karisha suka dauki hanya sai dai maimakon taga sunbi hanyar gidan su sai taga akasin hakan

 

Inda taga karishi ta dauki titin by pas inda ta dubi karisha a kule

“Kin fa baro hanyar haj sai mun koma baya.

Karisha tayi murmushi

“Ina sane amarya Sha guda zamu biya Nan ne in bada sako.

Bata Ankara ba taga motar taci burki bakin kofar SHIGA hotel din barewa

Abinda ya haddasa Mata sarawar Kai me tafe da bugun zuciya………

 

 

To Bari mugani ko wace irin waina za a Toya

Ta wake CE ko ta masara

 

 

Leave a Comment