12/15, 1:59 PM] Abu~ammar: *🕊️RAINON SOJA…!🕊️*
*#Through the gate of love a Valiant, fearless heroical and Sympathetic Story.*
Free Page 1
*Labari da Rubutawa daga:©Ayshatou Maman-teddy*
*December 02-12-2023 …..7:30am*
#Rainon soja#whispering of love💔#Book 1#chapter 1#hand salute 💃🏻#travelling .
Wata moto ce ke guda a tsakiyar ƙwalta inda babu gida gaba babu baya sai Falfalan dajin ALLAH.
Mota ce irin ta haya wanda yake dauke da mutane sun kai Goma zuwa goma sha biyu , kallo ɗaya zaka yi masu ka fahimci matafiya ne wanda suka fito daga cikin garin Zaria zasu iso Garin Abuja . Kowa hankalin sa yana akan hanya banda Mace Ɗaya wacce tun da suka shigo moton idanun ta ke tsiyayar da Ƙwallah, daga saman jikin ta kuma yarinya ce Wacce a shekaru ba zata Haura Ɗaya ba zuwa ɗaya da Rabi a Duniya . Tausayin yarinyar nata take jin yana ratsa ta haka zuciyar ta na kuka mata . Juyawa tayi tana kallon mai gidan nata wanda shima jimami ne da kuma tsoro fal a zuciyar sa. Hajara kina ganin idan muka je Muka koma a halin yanzu Ƴan uwan ki zasu amshe mu? Zasu amince da Auren namu a yanzu kuwa? Hajara ko zamu koma ne…..Ɗaga masa hannu tayi tana saurin riƙo hannun shi kamin cike da Raunanniyar murya ta fara cewa ” A’a Salihu ” kar ka ƙara furta hakan , yanda muka ƙudurci kawo Zahra dangina Don taga iyayen ta da kakanni a yau babu abun da zai fasu daga yin hakan sai kuma idan ƙaddara ta Gifta .
Ka janye Tsoro ka manta da komai nasan su ma a yanzu sun manta kuma kowa zai yafe mun inshallah. Fatan mu a yanzu shine Allah yasa mu sauka lafiya .
“Hummm” .
Sauke Ajiyar zuciya Salihu yayi kana yakai hannun shi yana ɗaukar ƙaramar yarinyar tasu yana daura ta bisa jikin sa . Ƙurrrr yayi mata da ido kamin yace ” Wai Haihuwar ki ce aka ce mun ba alheri a rayuwa ta Zahra , Ni nasan Allah shine mai yin komai shine wanda yasan ƙaddara ba ɗan Adam ba. Ko ina raye ko ina a mace ina rokon ALLAH ya kare mun ke da kariyar sa. Shiru Hajara tayi tana kallon uba da ƴar wanda yake ji tamkar ya haɗa ta da jikin sa ya zamana babu wani abun cutarwar da zai iso gareta . Murmushi take bin su dashi kamin ta juya tana kallon dajikan da suke wucewa.
Kaman wanda aka ɗaga moton suka ji tayi sama tayar gaban ta yana fita fittttttt ji kake kwaltan da tayar suna fidda wani irin ƙugi ƙuuuuuuiiiiiiii nan take moton ta ɗaga tare da kifowa kif kaman wanda aka dirkake su . A dai dai kuma wannan sa’ilin da babu gida gaba babu gida baya ,sai falfalan dajin ALLAH . Yanda moton tayi ƙwatsa ƙwatsa jini na malala a tsakiyar titin ga hayaƙi dake tashi tamkar an kunna Masu fetur da ashana wurin yayi baƙiƙirin kai daga Ni kasan babu mutum ɗaya daga cikin moton nan da ya shura sai dai muce Allah yajiƙan wanda suka rigamu gidan Gaskiya 😢 .
**
Nigerian defence academy ( NDA)
#Nd 1 .
Yaran sojoji ne birjik a ƙame rana na dukan tsakiyar kan su , amma yanda wurin yayi shiru da yanda sukya a ƙame tamkar wanda ruwa yaci yacinye su . Mutumin dake daga nesa ba zai taɓa kawowa da akwai mutum ko ɗaya a wurin ba,bare kuma sojoji da sun haura 100 ɗari duka a layi . Kasancewar su Nd 1 yasa duka yawancin su yara ne matasa wanda daga secondary ne suka shigo , duk girman yaron dake wannan wuri babu guda ɗaya da ya haura 18 . Duka ƙasa da haka ne sai kuma 18 din , ciki har da masu 15 years yayan manyan kenan masu faɗa aji a ƙasa . Sune suke kawo yaran su tun da yarinta .
Cike da Wani irin ƙaraji tamkar zai tashi wurin da yaƙi Muryar Major ɗin su ya katse su yana furta ” Hand salute! Daram dam dam….kaji takon su duka ya sauya suna juyawa ga Major ɗin a lokaci guda suna ɗaga yatsunsu tare da ƙamewa da ƙafafun su . Bin su da kallo yayi dukan su Sanye suke cikin t.shirt na sojoji sai wandon su mai ratsin tambarin su na soja.
Idanun Major Jibril ne ya sauka akan Wani kyaƙyƙyawan yaron dake daga can tsakiyar layi , su duka a ƙame suke amma shi a wannan lokacin Wayar hannun sa yake latsawa cike da kula murya ƙasa-ƙasa yake furta ” Mami…Hello .
Wani irin Tsawa Major Jibril ya daka masa Wanda sai da Hantar cikin Duka yaran ya kaɗa yana bada amon ƙulululu… Mamaki ne ya kama su Ganin Yanda Aliyou Haidar bai Girgiza ko ya saki wayar tasa tayi ƙasa ba ,sai ma ƙara mannata da yayi da kunnen sa yana furta ” Mami I’m in trouble Major Jibril ya na mun magana bye bye .kamin ya jira jin mene Zata furta ya datse kiran da Sauri yana maida Wayar cikin Aljihun sa .
Cike da shouting da ɗaga murya irin na Sojoji Major ya furta ” Who are you ? ….kamin ya rufe baki cike da Ƙwarin gwiwa tare da gigiwa irin na Aliyu ya furta” ALI HAIDAR “. yana furta zancen tare da ƙamewa kaman yanda suka saba yi don respect. Kallon shi Major Jibril yayi kana ya bashi umarnin ya fito wajen layin . Cike da kuzari da Sauri ya fito yana gyara tsayuwar sa , kallo Ɗaya Major yayi masa yaga tsayayyen namiji ne a gaban sa tun kan ya girma a yanzu ma zaka fahimci hakan , ƙwayar idanun sa ya kalla ganin rashin tsoron sa yasa shi Furta ” Waye Soja a tare da kai ? .
Sorry sir
Fa furta yana kame ma Major ɗin , Tambayar ya kara nanata masa karo na biyu wato a dangin sa Waye soja? Wanda a wannan karon kai tsaye Ali haidar ya basa amsa da my Dad…! Ya furta da ƙarfi yana Ƙara ƙame ma Major Jibril . Meye sunan Mahaifin ka ? General Saleh Yelwa . Girgiza kai Major Jibril yayi tamkar General ne a gaban sa , don yasan Waye General Yelwa babban sune shine ya basu horo a lokacin tasowar su .
Kallon Aliyou Haidar yayi kana ya cigaba da cewa ” Ya ake yin Hand salute?
Ok sir . Ya furta yana Sara masa tare da hade ƙafafun sa .
Kallon Sauran sojojin abokanan sa yayi shigowan yanzu Nd 1 kana cike da Arrogant voice ɗin sa ya fara cewa Hand salute!
“You raise the right hand smartly in the most direct manner a kuma lokaci guda extending and joining the fingers …keep the falm plat and facing the body.
“Yana maganan tare da nuna masu yanda ya kamata suyi don haka Majorn ya sanar dasu a jiya . ”
Komai dai dai ya faɗa , Wannan yasa Major kallon sa yana basa horo da ya fita can Rana ya fara tsallen kwaɗo shine punishment ɗin sa na yau , Gobe ba zai ƙara kuskuren da yayi irin na yau ba.
Ficewa Ali haidar yayi yana nufar inda Major yace yayi tsallan kwaɗon , Ɗan waigawa naga yayi yana kallon wani direction yana murmushi .
Gani nayi wani Matashin yaro wanda ba zai haura 17 ba yana kallon Aliyu idanun shi sunyi ja na damuwa ga gumin dake karyo masa , damuwa duka sun bayyana ƙarara a fuskar shi . Haɗa ido suka yi da ƙanin nasa yana jifan sa da harara tare da cewa a zuciyar sa ” Yaushe Haidar zai daina rashin ji ne? Yau sai ya sani bari ya gama mu koma . Murmushi Aliyu haidar yayi yana furta to menene na dumuwa Yaya Khaleel bafa wuya ne dashi ba . Yanzun xanyi na gama .
Tsallan ƙwadon ya fara yi su kuma sauran sojojin suna fara fareti . Fiye da Awa ɗaya yake aikin tsallan ƙwaɗon amma babu alamar gajiya a tare da shi , don shi jin sa yake tamkar training din da suka saba yi ne a gida yake yin sa a yanzu. Ni Ko nace yo ba dole ba , Mahaifin su soja mahaifiyar su babban Ƴar sanda ce , Wanda a yanzu take da matsayin mataimakiyar Commissioner of police. Hajiya Nafisat Yelwa kenan . Ƙaramar ƙanwar su kuma jidderh itace take makarantar yara na karatun architecture . Sauran labari zamuji shi a gaba inshallah ku dai ku cigaba da biyo wannan Golden pen din don wannan tafiyar ta musammance .
Ali Are You not tired ? Baka gaji ba Haidar? Muryar Areef ya katse shi wanda yake fareti dai dai inda Aliyou Haidar yake . Cike da hade gira tamkar wani bad boss yace ” Na riga da na saba da ko wani horo na soja tun kamin nazo nan. Ɗan wannan tsallen kwaɗon ba zai gajiyar Dani ba .
Da kyau!
Muryar Major Jibril ya katse su wanda basu san yana tsaye da a bayan su ba. Tabbas wannan yaron yana da jan rai da zuciya kangararriya , haka ake son soja ya kasance , Major yayi maganan a zuciyar sa yana juyawa tare da kallon Manyan sojojin dake bayan sa. Ina so ku bi mun bayan Ali haidar Yelwa yayi gudu tun daga nan Kaduna jaji har zuwa Zaria ya dawo a ƙasa ba tsayawa ko Hutawa yanzu . Ok sir ……! Suka yi maganan cike da amsa kuwa . Juyawa Ali haidar yayi yana kai hannun sa tare da miƙa yana miƙewa tsaye . Da sauri ya furta ” Major idan ba damuwa zan iya ɗaukar Helmet da Armor idan ba damuwa da ruwa ma . Wani irin kallo duka suka bi shi dashi , yayin da Major Jibril cikin Tsawa yace ” Kai ba yaƙi aka ce zaka tafi ba , You Are under punishment now , shine har kake tambayar Helmet da Armor rigar kariyar harbi me zai maka ? Ruwa kuma ba zaka sha shi ba har kuje ku dawo …………………..!
*Ina kuke masoyana💃🏻 nasan yawan ku kun haura irin billions ɗin nan😹 kuyi mun share page ɗin nan ga mutanen ku nasan ƙaranci yanda nake da jama’a billions haka kuma ƙaranci 1 million people😹. Ga masu buƙatar na tallah masu hajar su ƙofa a buɗe take zaki zanzare kuɗin aljihun ki ayi Miki tallah don samun customers sai ki tuntuɓeni ta WhatsApp ga nombibina nan a daga ƙasa*
*Labarin RAINON SOJA na kudi ne kar ki fara karantawa tun fari idan kin san baki da kuɗin saya don Allah… Book 1 free ne shine wannan ,idan mun gama shi book 2 na kuɗi ne kar azo ana ayi haƙuri da sauran su , Sannan group din littafin guda uku ne 3 , muna da na ƙasa shine ₦500 (regular group) sannan aƙwai yan tsakiya shine ₦1000 (Vip group)sannan aƙwai na sama shine ₦1500 (Special payment)…Zaki iya payment din ki ta wannan account number 6037312299 Mohammed A’isha keystone bank shaidar biya ko katin MTN ta wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne ga MTN numbern da zaki tura tanan 09061466409 zaku iya fara payment naku tun yanzu don na samu damar sakaki group da wuri kamin mutane suyi yawa kunsan hidimomin da yawa …to hajiya ta wannan salon tafiyar ta daban ce kar ki bari ayi babu ke a barki a baya .labari ne mai ɗauke da darussa 😹💃🏻✨yanda yazo a ƙarshen shekara haka daɗin sa ya kasance na musamman kun san alƙalamin mmnteddy baya rubuta labari mara ma’ana ato.*
*Anty Aysha Mamanteddy*
[12/15, 1:59 PM] Abu~ammar: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and sympathetic story.*
_Book 1_
_Free page 2_
*Littafin rainon soja book 1 free ne , book 2 na kuɗi ne regular group ₦500 Vip group ₦1000 special payment ₦1500 .*
*Zaki turo da kuɗin ki ta wannan account number 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932. Idan Vtu transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409 ku fara payment da wuri a page 10 Free page zai ƙare*
Maman Teddy.
Marubuciyar
My Lady boss
Yar tsakar gida
Bafullatanan Ruga
Walijaam
The sexy Boss
Gidan Ƙwarata
Siyasata
The virgin maid
Habibi da’iman
Mr romantic
Duniyar shahara x world
Yar Aiki
Dijama yar Fulani
Zuma da maɗaci
Kwarton manya
Da sauran su .
Yayin da Major Jibril cikin Tsawa yace ” Kai ba yaƙi aka ce zaka tafi ba , You Are under punishment…shine har kake tambayar Helmet da Armor rigar kariyar harbi? , Amfanin mene Helmet zai maka ? Ruwa kuma ba zaka sha shi ba har kuje ku dawo ban yarda ko Hutawa kayi ba . Cike da ɗaga murya tamkar saukar Aradu Aliyu ya ƙame tare da furta ” Yessss sir “. Yana furta hakan ya fara cika umarnin Major Jibril yayin da Wani soja dake gaba dasu ɗan ND 3 yake bin bayan Aliyu haidar da ya fara gudun sassarfa kaman yanda Major yace dashi . Tun daga jaji yake gudu a wani irin tartsatsin rana gashi ba hulan su ta soja wanda yake tare dukan Rana ,ko ruwa kuma ba’a yarda mishi yasha ba .
**
A hankali take bin bord ɗin da kallo , tana sakin Murmushi tare da kai laɓɓanta tana kissing ɗin zanen fuskar Aliyuu Haidar . I love You Booo mie. Ta furta tana shafan giran sa wanda yake a tattare ya haɗe kaman hadari. Ƙamshin turaren da taji ne yasa ta saurin juyowa tana kallon inda Mami ke saukowa cas-cas-cas cikin shigar suit ƙafarta tasa cover irin na mata , Fuskar ta cikin baƙar gilashi da gani kasan no respect ba zaka taɓa cewa itace ke da yara uku maza biyu mace ɗaya ba wato jidderh, Khaleel da kuma iyayen kafiya da naci wato Aliyu haidar. Mami….! Ƙaramin Muryar Jidderh ya katse Ni cike da yarinta tana sakin mawa Mahaifiyar nata fara’a . Cikin sauri Mami ta nufo inda take tana rage tsawon ta tare da hugging ɗin jidderh tana cewa ” Morning my baby love”. Ana nan kina kallon Khaleel da Aliyu ? . Yes mami i really miss Booo mie da kuma Ya Khaleel . “Hummmmmm” Hajiya Nafisat ta sauke Sanyayyar ajiyar zuciya kana ta kai hannun ta tana shafa kan Jidderh cikin sanyi da Muryar rarrashi ta furta ” Sorry my lav zasu dawo nan kusa bada jimawa ba ‘.
Gyaɗa ma Mami kai jidderh tayi tana sakin Murmushi haƙoranta da wawulo na bayyana wannan yasa Mami dariya tana cewa”Alright muje kiyi breakfast sai na kai ki school daga nan Ni na wuce Office . Hannunta ta kama suna nufar Dinning room…..yanda Mami ke tafiya kadai zaka fahimci zaman gidan Na sojoji ne masu kaki komai oya-oya ake yin shi babu shauƙi irin na mata , tun tasowar yaran nasu a haka cikin gidan ya kasance, Daddy Soja Mami Police yar sanda 🫡 . Haka suka taso basu san suga iyayen su kullum a tare ba ,idan yau Daddy yana hutu to gobe Mami zakaji an sauya mata wurin aiki ko bata gari , dukan su yaran sun taso cikin horan sojoji ne ,don gidan baki ɗaya har ta masu girki cook sojoji ne , masu kulawa dasu sojoji masu kai su school sojoji Wannan yasa duk horo suke shan baƙar wahala , gashi General Saleh Yelwa ya ƙudurci son ganin yaran nashi sun zama tamkar shi Wato Sojoji . Wanda a yanzu a lokaci guda Duka su biyun suka fara NDA . A yanzu Aliyuu Haidar shekarunsa sha shida ne Bama ce ya cika ba ,sai Khaleel babba shine gaba da Haidar shi kuma shekarun sa 17-18 don tazaran su ba nesa bane shiyasa kan su yake daya ,sau tari wanda basu sani ba ma kiran tagwaye suke yi masu .
Sai dai Khaleel na fama da shan Wahalar Aliyu saboda Neman magana irin nasa ga kafiya da fusata ga saurin ƙufula da zuciya, a haka kuma yake zafin son Ƙanin nasa . Wannan shine taƙaitaccen labarin Gidan General Saleh Yelwa da iyalan sa . Bari mu Jah gaba muji wani hali Aliyu yake ciki a yanzu .
**
Tafiya ce suka yi ta mai dogon zango yayin da Ali ya haɗa gumi iya gumi a wannan lokacin har sun kai wuraren Gwargwaje sannan suka kuma juyowa zuwa jeji. A tsakiyar wani ƙaramar jeji ne kan hanya idanun Aliyu da Yaron Captain Lawal suka sauka kan Wata moto da tayi ƙwatsa ƙwatsa a titin wuta na tashi ta sama da ƙasanta . Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un kalmar da Lawal yayi kenan yayin da Haidar ya cigaba da Gudun sassarfa yana ƙoƙarin wuce moton . Amma kai baka da Hankali Wani irin mara imani ne kai Ali ? Wucewa zaka yi kana ganin halin da Mutanen moton ke ciki . Tsayawa Haidar yayi yana ƙamewa tare da seniority ya furta ” I’m under punishment Sir “.
Kama kai Lawal yayi kana yace ” Mu ceci mutanen nan ka dakata da Wannan Gudun da kake yi haka nan ,idan mun koma xanyi ma Major bayani . Ok sir . Aliyu ya furta yana saurin ƙarikowa inda moton yake hannun sa yasa duk da ƙarfen da tayi zafi ga moto ba karama ba . Tura moton suka yi da ƙarfin na sojoji suna ɗaga ta , Saurin rufe ido Ali yayi don wannan shine karon shi na farko da ya fara ganin gawa ido da ido a rayuwar sa . A takaice gaba ɗaya moton babu wanda ya shura dukan su sun zama gawa, gashi mutuwar wahala abun ba dadin faɗi da gani sai ka zubda masu da Hawaye jini ne kawai ke malala…..Hu’uhhhhmmmmmmm Suka ji wani jan iska da karfi anyi tare da fara tsala ihu irin na yara jarirai . Hasbunallahu wani’imal wakeel “. Lawal ya furta da sauri yana kai hannun sa yana fuzgo yarinyar da take maƙale jikin mahaifiyar ta , har ta fara sanƙarewa.
Aliyu Ruwa ruwa Aliyu Ruwa kawo ruwa .! Yana maganan hankalin sa a tashe da kuma yanda yarinyar ke ihu iya ƙarfin ta numfashin ta na kokarin ɗaukewa.
Kallon Sa Aliyu yayi kana yace ” Ai Major yace ba zan taho da ruwa ba ko ka manta ne ? .
Ba tare da ya tsaya ba Aliyu amsa ba ya fara gudu da yarinyar a hannun sa ,hakan yasa Aliyu shima bin bayan sa don su nemi ruwa su bata a wannan falfalan hanyar jejin da babu gida babu gida baya ,itako yarinya ƙiwuya ne yayi mata yawa ganin bata san fuskokin ba. Wannan yasa ta take kuka har da shirin riɗewa . Sir Lawal ka daka ta gudun nan , wannan ihun yarinyar yayi yawa kaman mun sato ta? . Cak Lawal ya dakata da gudun yana kallon Aliyu kamin ya juya yana kallon kyaƙyƙyawar fuskar yar lukutar yarinyar wanda nan take ya furta ” Laaa Aliyu kalla? Kai take kallo tayi shiru Aliyuu kalli dariya ma take yi maka yanzu . Ɗaga gira Aliyu yayi yana zuba ma yarinyar Manyan idanun sa da suke warwaje na rashin tsoro , Ganin yanda take Wangale masa baki kaman ba itace mai kukan ba ko kuma ta san shi yasa shima jin wani irin yanayi lokaci ɗaya na shigar sa gami da yarinyar . Amshe ta Ali zata yi shiru a hannun ka yanzu . Ba musu Aliyuu ya miƙa hannun sa yana amsan Yarinyar da take ta Wangale bakin nata tana dariya tare da miƙa masa hannayen ta duka na yara . Lawal ne ya bude baki zai masa magana da nuna masa yanda zai riƙe yarinyar don ya lura bai ma iya daukar yara ba , Kawai caraf yaga ya ɗaga yarinyar yana ɗaura ta bisa wuyan sa tare da riƙe hannayen ta a sama . Zamu iya tafiya Yallaɓai.! Yayi mganan cike da amsa kuwa da ƙamewa , cikin sauri Lawal yace ” Kai Ali mu aje wannan duk abin a gyefe yanzu ina zamu kai yarinyar nan. ?
Shiru Aliyu yayi masa yayin da Lawal ya cigaba da cewa ” mu tafi Barack da ita. Mu sanar mawa Major.
A’a gidan General Saleh Yelwa zan kaita yanzu. Ko mun dare zan dawo barack . A’a kana fa bisa laifi ne ,idan ka tafi zaka iya samun wata matsalar, sannan kuma dole mu nemi abun hawa don yarinyar a gajiye take . Gudu Haidar ya fara yi mai sassarfa kana ya yi gaba tare da daga murya yana cewa ” Sai na dawo Yallaɓai”.
*
Ali Meye haka nake gani? Wacece wannan a saman wuyar ka ka ɗauro? . Muryar Mami ya katse shi cike da amsa kuwa take maganan cikin ɗaga murya don kallo ɗaya tayi masa jikin ta sam bai bata ba .
Mami abani ruwa na bata . Meye sunan ta ? Kuma Meye na kawo mana ita cikin gidan nan? .
Ban san sunan ta ba , Amma na kawo ta gare ki ne , domin ki sanya mata sunan da ya dace . Ki kuma raine ta. Yanda yake maganan idanun sa kafe akan Mami yasa ta Fahimtar bafa wasa yake yi ba ,don dama shi ba ma’abocin yin shirme bane sam baya wasa . You’re very stupid Ali..! Baka da hankali . Ka dauko yarinya nayi mata raino , ko ku kan ku a haka kuka taso ban raine ku ba ,kuma har yau kulawa da ku ake yi , shine ka dauko yarinya wai na raine ta? Har na sa mata sun …..Kai Ali talk to me openly about this child, a ina ka same ta Wacece ita? .
Wannan shine tambayar da ya kamata ki fara yi mun tun farko Mami , duk da bani a mood din zan baki amsan yanzu , i need massage. Where’s Jamima? . Yanda yake maganan kaman House boss din gidan yasa ta , cewa sannu Mai gida General Saleh Yelwa, ina magana kana maganan a kira maka wacce zata matsa maka jiki ? Aliyu zan cire duk wata Sangarta da soyayyar da nake maka na aje ta a gyefe a yanzu faɗa mun Wacece wannan Yarinyar……? Mami idan na faɗa Miki Wacece ita , zaki raine ta ki kula da ita tamkar yanda kike yi mana koma fiye da namu so nake ki raine da hannun ki akasin mu da sojoji suka raine mu , ki ake wannan aikin naki ki zama cikakkiyar House wife matar gida don ki kula da Ma’eesha sunan dana sanya mata kenan Mami…..Kai yi mun shiru Ali , bana son Shashanci tambayar da nake maka daban amsan da kake bani da ban , to Bara kaji Wannan yarinyar ba zan raine ta ba , ba kuma zata zauna a cikin gidan nan ba . Ka dauko yarinya kaman Aljana ji ta fa tana wuru² da ido kai Ali fice mun da yarinyar nan yanzu. A’a mami zan zauna da ita , zan fasa cika duk wani mafarki na har ta girma .
Kallon sa Mami tayi cike da rashin fahimta ta furta ” Ban fahimce ka ba ban gane inda ka nufa ba Aliyu.
Takowa yayi yana Fuskantar Mami da itama shi take kallo yana ƙara gyara zaman yarinyar dake bisa wuyan sa , Yes Mami zan Aje aikin soja na naɗan wani lokaci, zan raini Ma’eesha har ta girma , zata taso ne a hannu na Wato RAINON SOJA……………….!
*Har yanzu muna sharan fage ne ba’a fara chakwakiyar ba a cikin littafin rainon soja kudai ku cigaba biyo alkalamin nawa wannan salon sa na daban ne . Kar kuman ta wurin yi mun sharing zuwa masoya na na duniya baki daya.*
*Littafin kuma na fa kuɗi ne ₦500 regular group vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 call number or Vtu transfer number 09061466409*
[12/15, 1:59 PM] Abu~ammar: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story .*
Free page 3
________________________
MAMAN TEDDY
Marubuciyar
My Lady boss
Walijaam
Siyasata
Yar maula
Kwaryar sama
The virgin maid
Gidan Ƙwarata
The Sexy Boss
Yar aiki
Bafullatanan Ruga
X world duniyar shahara
Mr romantic
Dijama
Kwarton manya
Yar tsakar gida
Zuma da maɗaci
Sadaka yalla
Yar waye
Taɓarah
________________________
“Da sauran su💃🏻 a yanzu kuma gata ɗauke muku da sabo mai ɗauke da sabon Salo na musamman wato Rainon soja , niko da kaina nace za’a sha duka😹soja da raino ai abun ba’a magana 🤣labarin sai wanda y karanta shi kar ki bari ayi babu ke Hajjaju…labari ne mai tafe da rikirkirteccen Al’amura wanda da fari sai kunce ya abun yake , Gaban yafi farkon🕊️dadi tun a yanzu ina sauraren comments din ku da masu fatan alheri na gode sosai . Sannan masu buƙatar daga farko don Allah kuna rinƙa tambaya ne a wasu groups da kuke ciki , idan kuka biyo Ni ayyukan da hidimomin nawa suna da yawa , bana samun damar turawa ta private 🙏🏻. Gare ku masu buƙatar fara payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake ; Regular group ₦500
Vip group ₦1000
SPC payment ₦1500
Via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 Vtu transfer number 09061466409 Yan Niger zaku turo da katin Airtel 500f .
Duk wanda nayi ma tallah a shafi na ku bishi kuyi kasuwanci dasu ina da cikakken Aminci dasu da ba babu cuta inshallah. Sannan masu buƙatar na tallah masu hajar su ƙofa a buɗe take 💃🏻 .
•••••
Takowa yayi yana Fuskantar Mami da itama shi take kallo yana ƙara gyara zaman yarinyar dake bisa wuyan sa , Yes Mami zan Aje aikin soja na naɗan wani lokaci, zan raini Ma’eesha har ta girma , zata taso ne a hannu na Wato RAINON SOJA……………….!
Rainon soja ”!
Tabbas ya tabbata Aliyu baka da Hankali , ko ka tarkata ka fitar mun da yarinyar nan daga cikin gida ko kuma yanzu kaga ɗanyar hukunci daga gare Ni . Tayi maganan tana rufe idanun ta babu alamar rahama a tare da ita , don ta lura sai tayi masa zafi-zafi sannan zata iya tanƙwara zuciyar sa . Muryar Daddy ne ya katse su wanda tun da suka fara maganganun nasu tun da fari yana daga Saman up stairs da yake saukowa yana sauraren su ” Cikin Muryar sa ta manya General Saleh Yelwa ya fara da cewa ” Haidar ”! Ali Haidar har yanzu kafiyar nan naka bata rabu da kai ba ko? Duk da ita ce ai ka biyo, yayi maganan yana kallon Mami da take zabga mawa Aliyu Harara, Yanzu ba zamu hanaka abun da kayi niyya ba Haidar, tun tasowar ku nan gidan Daddyn ku gida ne mai cike da yanci kowa abun da yake so yake yin sa . Amma ka sani muna da iko da kai da dole idan munce abu sai kayi shi koda bai maka ba , ai mu muka kawo ka duniya baka kai ka haifo mu ba .
“Daddy…”!
“Saurara mun ,yi mun shiru sau na gama magana ta sannan kayi naka , General ya katse yaron nasa yana takowa zuwa tsakiyar falon. Baka da hankali har yanzu kan ka Rawa yake yi Haidar ka fara mantawa da Waye Ni , Saboda tsaban sarganci kawai kaga yarinya a jeji kasa hannu ka ɗauko ta ,kuma kana maganan zaka bar aikin soja? Naga dalilin da zai dakatar da kai daga aikin nan. Ni bai dame mu ba ka riƙe ƴa ko ka kaita duk inda zaka kai ta,amma mu dai ka sani Soja kaman kayi shi kuma yanda ka fara babu tsayawa . Sannan fitowa daga Barack da kayi yau sai ka fuskanci hukuncin daga gare Ni”.
Kallon Daddy Mami tayi don ita har ga Allah bata son duk abin da zai ɓata ran Aliyu , Sannan kuma tasan Genaral Saleh Yelwa da magana ɗaya idan yayi ta sai anyi shi. Cikin sauri ta kalli Daddy tana furta“A’a janar ka rabu dashi kasan idan ya koma can ma horon da zai fuskanta sai yafi ta nan. Aliyu maza koma ka mayar da wannan yarinyar ko ka bani ita na miƙa mawa police a shigar da case akan lamarin ta ” .
“No mami”. Wannan ba abu bane wanda zai yiwu, nace Miki duka moton fa sun ƙone itama Allah……. Alright na Fahimta. Mami tayi maganan a ƙufule cike da jin Haushin taurin kai irin na yaron nata , Daddy na wuce Office shi zan turo Babba yazo ya fara amsan hukuncin sa ” . Tana gama faɗin haka ta juya tana ficewa daga falon,yayin da General Saleh Yelwa shima ya fara ficewa daga falon ne Muryar Aliyu ya katse sa. “Daddy na shirya amsan ko wacce hukunci daga gare ku , amma ban shirya amincewa a rabani da wannan yarinyar ba , a gaban idona naga gawan iyayen ta , bata da kowa ,ko gidan marayu aka kai ta baxasu bata kulawa ba . Meye amfanin arziƙin mu da ba zamu iya daukar nauyin wannan yarinyar ba? Mu zamu iya kulawa da ita….Eh ƙwarai zata samu kular soja”! Daddy ya furta yana katse Haidar tare da cigaba da cewa “ ban damu ba don ka raine ta amma ka sani Soja shine cikar burina akan ka , So nake ku zama kamar Ni, koma nace fiye da Ni. A yanzu ina da matsayin Genaral kai kuma so nake naga ka zama Marshal a kaf Nigeria mutane uku ne suka taɓa iya riƙe matsayin Marshal a aikin soja don haka haidar ko kai ko Yayan ka Khaleel dole ina buƙatar ganin wanin ku ya zama Marshal, ba General nake so ku kai ba ”.
Jub-jub-jub-jub . Babba ya shigo falon wani irin ƙaton basamuden soja ne , ɓaki ƙirin har bula yake yi na baƙi fuskar sa a murtiƙe wannan ko a hanya ka gan shi sai ka face ba zaka tsaya ba🤣 . Ka hora mun shi ta hanyar bashi training exercise mai wahala daga nan sai ya koma NDA . Ok general. Babba ya furta yana ƙame mawa Daddy . Yayin da shi kuma ya juya yana barin falon .
Kallon babba Aliyu yayi kana yace “Babba please Bara na ba Ma’eesha wani abun da zata ci , kaga bata ci komai ba kuma alamu sun….cike da murya ta Basawa Babba yace “Yi sauri”. Nufar fridge Ali yayi cikin sauri yana Buɗewa tare da fiddo da nutri mulki yasan wannan don jidderh ake ajiyewa, Saurin Ɗaukar Glass cup yayi yana cewa “ Mu tafi ” . Bayan gidan suka nufa can ƙarshe inda aka saba hora su duk idan sunyi laifi. A hankali ya sauke ma’eesha yana kallon kyaƙyƙyawar fuskar ta,kana ya fara kokarin aje ta ƙasan wani bishiya mai ƙasa ƙasa don wurin kaman gerdina yake . Buɗe baki Ma’eesha tayi tana fara tsala ihu tare da riƙo hannun Ali haidar tana juyar da kan ta tare da kokarin riko hannun shi irin na yara . Don duka kallon baƙi take yi ma sauran Sojojin. Ganin yanda Aliyu ya ruɗe yasa Babba dan tsagaitawa yana jiran ya rarrashe ta sannan ya bashi horon kaman yanda General yace dashi. Ɗaukar Ma’eesha yayi yana Girgiza ta tare da Buɗe nutri milk din yana fara bata ba bu magana don shi ba gwanin surutu bane ,sai dai yayi mamakin yanda ya iya kula da yarinyar ma haka. Shiru kaji tayi tana amsan madaran tana sha , kusan mintuna Goma kana ta ture bakin ta da kan ta alamun ya ishe ta . Farin hankie yasa yana goge mata bakin ta ,kana ya kalli babba yana cewa ” ina jiran ka. Sauke yarinyar ka aje ta can gyefe.
Wani irin kallo Aliyu yayi masa kana cike da haɗe gira ya furta ” Naka ka bani horo inda zan aje yarinya wannan Ni ya shafa Yallaɓai “.
Girgiza kai Babba yayi kana ya kalli ma’eesha wanda tausayin yarinyar ya kama shi ,duk da bangare ɗaya na Zuciyar sa yaji zafin kalaman Aliyu. Kallon sa yayi yana cewa “Sit-up zaka yi na awanni biyu daganan sai ka koma Barack . Ɗauke kai Ali yayi yana Maida Ma’eesha wuyan sa tare da fara yin Sit-up ɗin wanda hakan yayi mugun ba da yawa sojojin wurin mamaki . Shi fa yanzu ne ya fara Aikin sojan amma a haka yake sit up da yarinya a wuyar sa babu alamun ya gaji sai dai kawai gumi da sauko masa. Kusan mintuna arba’in ya ɗauka bai huta ko ya tsaya ba ,don yasan yana tsayawa to farko zai dawo , sannan ƙila ma ya amshi wani horon da yafi wannan wuya. Idanun sa sun yi jaaah don yanzu ƙafafun sa sunyi zafi kaman basa jikin sa haka yake jin su ,amma da yake yaro ne namiji sam bai yi yunƙurin dakatawa ba. Hannun Ma’eesha yaji tana wasa da suman kan shi tana gwalon gwalon gwarancin ta na yara , Wannan yasa shi ɗago kai yana zuba mata Lulun idanun sa tare da sakin mata murmushi . Itako sai ta sake Wangale masa baki . A haka ya kammala bai ma san lokacin yayi ba sai da babba ya dakatar dashi sannan . Saɓa Ma’eesha yayi yana ficewa daga cikin gidan tare da komawa NDA a ƙasa .
**
Kai tsaye wurin ƙwanan su ya nufa inda kowa yake da gadon sa kaman zaman hostel . Areef ne cikin sauri ya dirko daga gadon sa yana aje littafin hannun sa tare da bin Ali haidar da kallo yana kuma kallon Ma’eesha da a halin yanzu idanun ta a rufe suke alamu tayi barci. Haidar Wacece Wannan?. Miƙa masa Ma’eesha yayi cike da rashin son magana Aliyu yace “ Ƙwantar da ita Bara naje wurin Major Jibril na sanar masa da dawo wa ta ” . Aliyu kana cikin matsala Major a fusace yake me yasa baka dawo tare da Lawal ba?. Banza Aliyu yayi ma Areef yana ƙoƙarin raɓa sa don ya kwantar da Ma’eesha ne Areef ya kuma riƙo hannun sa yana ƙoƙarin yi masa magana ne Aliyu ya harzuƙa wani irin asharrrr ya danna masa da sai da Sauran mates din nasu dake wurin suka kakkale su . Juyawa Aliyu yayi idanun sa sunyi jah cike da masifa da jaraba ya furta ” Ya akayi ne ? Da me wani magana ne ,munafukan banza”! Shiru babu wanda ya tanka sa don sun lura a fusace yake , duk da Wasu dariya suke yi ma Areef ƙasa ƙasa , don yana wulaƙantuwa wurin Aliyu amma kullum yana nan nace dashi. A gadon Areef ya kwantar da ma’eesha yana juyawa tare da ficewa daga Wurin .
“Kaman yanda Areef ya faɗa masa hakan ya faru don ya wahala da horo iri² a wurin Major tun yanayi yana dauriya sai da idanun shi suka fara zubda ƙwallah duk ƙarfin zuciyar sa sannan Major yasa akayi masa ligi-ligi ƙafafun sa sun sha duka da sanda . Da kyar yake iya tafiya don yanzu har 8:pm yayi .
Tun da ya shiga inda suke yake jin sauti kaman na kiɗa tare da ɗan kukan Yarinyar, Muryoyin abokanan sa sojojin yara yana tashi a hankali kaman masu bitan karatu wai nan waƙa suke yi ma ma’eesha😹 . Yana jan ƙafan sa da suka kumbura ga nauyi da jikin sa yayi ya isa inda suke . Gani yayi su kusan shida duka sun zagaye Yarinyar kowa nayi mata Wasa ,Areef na riƙe da ita , Sai Ibrahim dake aikin ƙarƙada Wani roba wai duka don tayi shiru , Sai wasu sun su dake mata waƙar baby girl . Ganin yanda ya shigo yasa su duka jikin su sanyi . Gadon sa ya nufa yana faɗawa ta rigingine kansa na kallon sama . Tun da ya shigo ma’eesha ta gan shi sai ta dakata da ƙananan kukan nata tana gwalon gwalon gwarancin ta . Murmushi Areef yayi yana kallon ta tare da nuna mata inda Aliyu ke kwance yana furta “ Uncle” . Uncle ya dawo. Hannu Ibrahim yasa yana amsan ma’eesha kana ya nufo inda Aliyu ke kwance. Da gudu ta saki zullo tana kuɓcewa daga hannun Ibrahim tare da faɗawa jikin Aliyu tana kwanciya bisa ƙirjin sa tana yin lamo . Sauke Ajiyar zuciya Aliyu yayi tare da ɗaura hannun sa bisa suman kan ta yana shafa mata a………………!
*Littafin Rainon soja na kudine regular group ₦500 vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 .*
*Ga masu buƙatar a tallah masu hajar su zasu iya mun magana sannan kar ku manta wurin yi mun share zuwa masoya baki ɗaya ngd*
[12/15, 1:59 PM] Abu~ammar: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story .*
Free page 4
________________________
MAMAN TEDDY
Marubuciyar
My Lady boss
Walijaam
Siyasata
Yar maula
Kwaryar sama
The virgin maid
Gidan Ƙwarata
The Sexy Boss
Yar aiki
Bafullatanan Ruga
X world duniyar shahara
Mr romantic
Dijama
Kwarton manya
Yar tsakar gida
Zuma da maɗaci
Sadaka yalla
Yar waye
Taɓarah
________________________
“Da sauran su💃🏻 a yanzu kuma gata ɗauke muku da sabo mai ɗauke da sabon Salo na musamman wato Rainon soja , niko da kaina nace za’a sha duka😹soja da raino ai abun ba’a magana 🤣labarin sai wanda y karanta shi kar ki bari ayi babu ke Hajjaju…labari ne mai tafe da rikirkirteccen Al’amura wanda da fari sai kunce ya abun yake , Gaban yafi farkon🕊️dadi tun a yanzu ina sauraren comments din ku da masu fatan alheri na gode sosai . Sannan masu buƙatar daga farko don Allah kuna rinƙa tambaya ne a wasu groups da kuke ciki , idan kuka biyo Ni ayyukan da hidimomin nawa suna da yawa , bana samun damar turawa ta private 🙏🏻. Gare ku masu buƙatar fara payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake ; Regular group ₦500
Vip group ₦1000
SPC payment ₦1500
Via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 Vtu transfer number 09061466409 Yan Niger zaku turo da katin Airtel 500f .
•••••
Tun da ya shigo ma’eesha ta gan shi sai ta dakata da ƙananan kukan nata tana gwalon gwalon gwarancin ta . Murmushi Areef yayi yana kallon ta tare da nuna mata inda Aliyu ke kwance yana furta “ Uncle” . Uncle ya dawo. Hannu Ibrahim yasa yana amsan ma’eesha kana ya nufo inda Aliyu ke kwance. Da gudu ta saki zullo tana kuɓcewa daga hannun Ibrahim tare da faɗawa jikin Aliyu tana kwanciya bisa ƙirjin sa tana yin lamo . Sauke Ajiyar zuciya Aliyu yayi tare da ɗaura hannun sa bisa suman kan ta yana shafa mata a Hankali. Girgiza ta yake yana ɗan jijjigata da jikin sa , kana ya lumshe Lulun idanun sa ba tare da yace da sauran abokanan nasa komai ba .
Kallon Ibrahim Areef yayi kana ya maida kallon sa ga Aliyu da har a wannan lokacin idanun sa suke a lumshe tamkar mai tunanin wani Abu koma muce babu shakka wani abun yake tunanawa . Sauke Ajiyar zuciya Ibrahim yayi yana zama Gyefen mattress din Aliyu , “Haidar”! Ya ambaci sunan shi tare da mai da kallon sa sosai bisa kan Fuskar Aliyu wanda a yanzu ba tare da ya ware idanun nasa ba sai motsa laɓɓan sa da yayi yana cewa “ Ya akayi?”.
“Ali ka taimaka kayi mana bayani wai wannan yarinyar Wacece? A ina ka same ta , a yanzu shirun nan naka bata da wani amfani idan har ba zaka faɗa mana komai gami da yarinyar nan ba to Meye amfanin mu na zama abokai kuma aminan juna?” … Muryar Areef ya katse su wanda yake maganan cike da nuna damuwar sa , don shi babu abun da yake shan wuya dashi gami da Aliyu Haidar irin Miskilancin sa da kuma Ƙafiyar sa. “Hummmm…” wani Gwauron numfashi Ali ya sauke kana ya ware idanun sa yana zuba su a bisa fuskokin su . Ganin yanda idanun Areef suka yi ƙwal³ tamkar zai saka masa kuka yasa Aliyu sakin Murmushin nan nasa Wanda idan yayi shi yake ƙara zama Arrogant, faffaɗan Hushiryar sa dake saman tsakanina fararen haƙoran sa na bayyana, wani sihirtaccen ƙyawun shi na fitowa . “To Meye na damuwa Abokai? Zan faɗa maku Wacece Ma’eesha, amma ku ɗan dakata na rarrashe ta tayi barci tukuna….Me ne kuka bata taci bayan fita na?”. Ya ƙare maganan yana ɗago Ma’eesha da a yanzu idanun ta suke a rufe tayi barci sai sauke numfashi take a hankali alamun tana cikin Lafiya.
Ibrahim ne yace “ Mun bata tea ne , sai Ragowar Talia ce da Adam ya girka muka bata ” . Manyan idanun Aliyu ne suka fito waje jin an ba yarinyar da a ganin sa a yanzu bai fi ta iya shan Golden moon ko cerelac da sauran abincin yara ba. A dai dai yanzu ma Golden moon yake ganin yafi kamata a bata ,wai amma sun bata talia .
“Talia fa kace? Talian kuka Bama wannan yarinyar ƙarama ta ina zata iya cin sa?”. Ali tama fi cin shi fiye da tea din da muka bata , Alamu ya nuna tana cin sa sosai . Bin su yayi da kallo kamin ya Lumshe idanun sa yana furta “ Ohk na fahimta ” .
“Yanzu Aliyu faɗa mana Wacece Ma’eesha?”….Areef yayi maganan yana dafa Aliyu, Kallon sa Aliyu yayi yana kai hannun sa tare da ɗago Ma’eesha yana ƙara Rungume ta tare da haɗata da ƙirjin sa yana jingina da gadon nasa . A hankali ya fara labarta masu yanda ya tsinci ma’eesha da kuma duk abun da ya faru bayan nan , zuwan sa gida da kuma Dawowar sa .
Yanzu Mami taƙi amsar ma’eesha? But why mum ….Katse Areef Ali yayi da cewa“ Saboda muma dukan mu bata raine mu ba , Sojojin gidan suka raine mu duka , a yanzu ma tace bazata raini Ma’eesha ba , a ganina marainiya ce kuma bata da gatar da ya wuce Ni. Girgiza kai Areef yayi yayin da Ibrahim ya matsa kusa da Ali yana cewa“ kayi hakuri haidar bamu fahimce ka ba da fari” . “Bakomai Aboki” .
Yanzu Zuwa gobe ka bani Ma’eesha na kaita wurin mummy na nasan ita zata riƙe mana ita har ta girma.
“Daaammm”. Ƙirjin Haidar ya buga da ƙarfi jin Furucin Areef na ya kai ma mummyn sa Ma’eesha .“No Ni da hannu na zan raini Ma’eesha, bana buƙatar kowa ya rainon mun ita , ina so ta samu tarbiyyar da duka bamu samu ba , Saboda gatan ta mu kawai aka yi , itako tarbiyya zan bata wanda nan gaba itama zata yi alfahari da kan ta” .
Shiru duka suka yi kana Ibrahim yace “haidar anan ɗin zaka iya ba Ma’eesha tarbiyya kar ka manta karatun soja fa muke yi wannan ce shekaran mu ta farko, dole mu maida hankali Tayaya zaka iya karatu da Raino? .
Zan iya Ali jarumi ne”! Komai nawa na daban ne , Rainon soja ake faɗa maka yasha ban-ban da sauran rainon da ka sani . Cike da bashi ƙwarin gwiwa Areef ya furta “ Yes of course Ali zaka iya yin fiye da haka , ai mu sojoji ne dole komai namu ya zamana daban dana Mutane,mu fa masu kare al’umma ne , Tayaya tun yanzu ba zamu iya kulawa da wannan yar yarinyar ba ?’. Komawa Aliyu yayi yana ƙwantar da kan sa bisa pillow kana yace“ that why you’re always my Best friend ever ” . Ku miyi barci saboda 3:00am muke da fita training.
**
Mami meke damunki tunanin mene kike yi haka? . Muryar Jidderh ya katse Mami wacce take zaune bisa Dinning table ta kasa sarrafa tunanin ta bisa abun da Aliyu ya ɗauko mata a jiya ” . Mamiii”. Jidderh ta kai hannu tana taɓa Mami tare da girgiza ta tana langwaɓe kai tare da ƙara Cewa “ What’s up? What are you thinking for…? ” . Humm no..no… Nothing . Mami tayi maganan Muryar ta na rawa , kana ta ɗan kalli jidderh dake sanye cikin shigar Sport wear na makaranta duba ga yau laraba ,ranan saka rigar Sport kenan a school din nasu . Murmushi Mami ta ƙaƙalo don bata son Jidderh tasan da labarin Aliyu da wannan Yarinyar da ya ɗauko , don tasan yanda jidderh ke zafin kishi da son yayan nata bata son taga kowa ya rabe su , to Taji labari bata babu sukuni kuma sai na kuka.
Sauke Ajiyar zuciya Mami tayi a zuciyar ta tana cewa “ Ai yaga ɓacin raina kuma ya fuskanci horo wurin babban don haka nasan tuni ya maida yarinyar nan , bani da lokacin ma ɓata shi a kan bibiyar wani hali suke ciki , don tuni ya fitar ma kansa da maslaha. Hannun ta takai tana shafa kan Jidderh kana tace “ Are You ready for school now” . Gyaɗa mata kai Jidderh tayi kana ta zauna a bisa kujeran ta inda nan ne wurin zaman ta permanent dama. A h natse mami ta fara bata breakfast ɗin ta , Duk da itama sauri take zata wuce Wurin aikin ta na police amma sai ta sauke jidderh a school sannan zata wuce. Ganin yanda take feeding ɗin Jidderh da hannun ta tamkar jaririya ya sani cewa“ Lallai Mami anya lamarin ki babu …..🤔to muje dai gaba muji yanda zata ƙare.
Ture kan ta Jidderh tayi daga ƙoƙarin da Mani take yi na kai mata soyayyar Irish din da take yi . Cikin sauri tasa hannun ta tana Fiddo da Wani white pepper warware shi tayi a bisa jikin ta tana nuna ma Mami zanen ta na jiya da tayi . Wow that’s very nice my baby 💃🏻 Wannan zane haka mai kyau? . Yes Mami see daddy here, While Boo mie seating in front of Dad kinga yanda yake haɗe giran nan da ya saba. Tayi maganan tana sakin dariya tare da nuna fuskar Aliyu Haidar , ta zana shi giran sa a haɗe , Gyefe kuma mami ne sai Yaya Khaleel dake sakin fara’a . Mami have you remembered any little thing about this? . Kin iya tunawa da wani abu ko kaɗan gami da Wannan zanen?. A’a baby na ban tuna da komai ba .
“Hinmm , wannan fa zanen shekara ɗaya da ta wuce ana gobe birthday din ya Aliyu ne muka zauna a haka yana fushi mara dalili , shi kuma yaya Khaleel na tsokanan sa baki ga dukan mu muna dariya ba ,shine kaɗai fuskar sa babu annuri?. Kallon zanen Mami tayi tana sakin dariya irin na Polisawa😹 don ita komai nata haka zaka ganshi woman like a boss . Haka take bata da wasa.
Girgiza kai tayi cikin sauri tana cewa “ Ohhhh Yes ”. Na tuna fa haka ya faru . So yau boo mie ɗina yake ranan zagayowar haihuwar sa haka ne mami atleast muyi surprising ɗin shi na yau. Mami ina so mu zauna a haka mu Biyar,bana son ko wacce baƙuwar fuska ta kutso mana cikin Ahali. Muna jin daɗin rayuwar mu a haka . Ina son Ya Aliyu Sosai,amma shi bai damu dani ba , ya Khaleel yafi shi Sona shi yake kulawa dani Sosai .
“Shiru ya isa haka babyn Ya Haidar , Wane ya faɗa Miki bai damu dake ba , ko jiya yazo kuma nasan don ya ganki yazo sai dai baku hadu ba. Mami ya Aliyu yazo? A’a ba don Ni yazo ba koda kuwa ya faɗa Miki hakan, yaushe zai dawo . Hannu Mami tasa tana lankafe takardar kana tace “ ki kwantar da hankalin ki , ai wannan ce shigar su ta farko 4 mount za su yi su dawo gida hutu . Kuma Kinga a yanzu sun yi kusan 3 mount nan ba da jimawa ba. Miƙewa Jidderh tayi tana daukar lunching box ɗin ta tare da cewa ” Mami na shirya mu tafi yanzu…..!
Ɓangaren Aliyu kuwa ƙarfe Uku na asuba suka fara shirin fita training exercise da suke yi na awa biyu kullum , Kallon Ma’eesha yayi da take barci yana ƙara rufa mata bargo kana yace dasu Areef mu tafi ko?. Fitowa duka suka yi su kusan shida suke rayuwa a babban Ɗakin kowa da gadon sa da kuma wurin mu’amalar sa .
Sojoji na hanga birjik dukan su da kayan exercise suna running round tare da ɗaga ƙafafun su , Hango Aliyu Yasa Khaleel saurin isowa inda suke cikin Muryar sauke nishin wahala ya furta “ Haidar ina ka shiga tun jiya? ” . Kallon sa Aliyu yayi yana fara training exercise ɗin ba tare da yaba Khaleel amsan tambayar sa ba sai cewa yayi “ morning ya Khaleel ”. Shafa kan ƙanin nasa yayi yana wuce shi tare da cewa ” ka kula yau Please kaji ban son ka sake wani laifi kaji? . Running up and down ya fara yi ba tare da yace da Khaleel komai ba…Kusan 5:30am sannan suka koma Wurin ƙwanan su . Don haka suke yi 7am su shiga class don karatu. Suna komawa Aliyu ya nufi Toilet ɗin su alwala yayo yana sallah kana ya juya yana kallon inda Ma’eesha ke ta barci har a lokacin. Miƙewa yayi yana ɗaura Towel a Kugun shi tare da nufar Toilet don ya watsa ruwa ya fito yayi shirin shiga aji kuma .
Mintuna Sha biyar ya dauka ya fito hannun sa ɗauke da ƙaramar Towel yana tsane suman kan shi . Areef ya gani da Ibrahim sai Adam suna zagaye da Ma’eesha da ta buɗe idanun ta tana Kallon su duka , Kaman mai tunanin wani abu akan su ,su kuma sai murmushi da wasanni suke yi mata suna kiran sunan ta “Ma’eesha , Areef na wasa da hannayen ta , don kuka ne basa so tayi . Ganin haka yasa Ali sakin Murmushi yana saurin ƙarikowa inda Suke. Da hannun sa ɗaya ya ɗagota yana Girgiza ta tare da yin wani tambul yana juyata sama zuwa ƙasa kan ta na kallon ƙasa yana dariya tare da cewa “ Kema Bara kiyi naki morning exercise ɗin ”. Innalillahi…Aliyu Meye haka? Bafa ƙashi a jikin ta”. Muryar Su Ibrahim ya katse shi a tare . Kallon su yayi yana kallon Ma’eesha dake ɓaɓɓaka dariyar ta babu alamun Taji tsoro . A’a dole itama zata rinƙa yin morning exercise sannan sai nayi mata wanka……………..!
*Wani aiki sai soja😱💃🏻Rainon soja zamu sha kallo🤍🤣 to masu karatu kar ku manta littafin rainon soja na kudi ne masu ɓukatar fara payment ga yanda tsarin yake. Regular group ₦500 vip group ₦1000 special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne ta wannan number 09061466409 yan Niger zaku turo da katin Airtel na 500f …kar ku manta wurin yi mun sharing zuwa ga masoya baki daya🙏🏻🕊️.*
[12/15, 1:59 PM] Abu~ammar: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story .*

Leave a Comment