Books Reviews & FAQs

Prince Kamal Hausa Novel Complete

[3/15, 10:21 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

By

🌹🌹🌹
Meerah💞

🌹 Also known as 🌹
Samira Ayuba🥰🥰

 

Wannan page na sadaukar dashi gareki my lovely daughter ****Ihsan****** Allah yarayamin ke bisa tafarki madai daici.

 

Dasunan Allah mairahama Mai jinkai

🅿️ 1️⃣_2️⃣

 

“Khamal kaunarka acikin jinin jikina take bazan iya rabuwa dakai ba, khamal kada kamanta dani arayuwarka zanyi zaman jiranka har kadawo gareni”

Hawayen dake gudana afuskarta ta share tare da dauko wata leda acikin jakarta ta mika masa.

“Ka karbi wannan Ina maka fatan alkhairi”, bata jira jinta bakin saba tashige motarta tayi gaba

Kasa cewa komai yayi saibin motarta da kallo wani irin kunci yakeji acikin ransa, tabbas wannan itace Rana mafi muni arayuwarsa, zancen zuci yakeyi yakasa Koda dogon motsi awajen, inama mutuwa ta riskeshi kafin wannan rana.

Hawayen dake gudana a lallausar fuskarsa yashare tareda duban ledar da Afra tabashi nantake wasu zafafan hawaye suka gangaro afuskarsa, tareda murmushi Wanda hausawa kecewa yafi kuka ciwo,

A hankali yafara daga kafarsa Yana tafiya kamar Wanda kwai yafashema aciki, tafiya yakeyi batare da yasan inda yadosa ba.

Kai tsaye Tasha ya nufa, motar da yagani kusa dashi yashiga batare da yasan inda motar tanufa ba.

Tafiya sukeyi acikin mota kowa da tunaninsa khamal dai hawaye kawai yake sharewa, a haka har aka isa garin Zaria, fitowa yayi yafara tafiya, kallo daya zakayi masa kasan yanacikin matsananciyar damuwa.

Yayi yawo sosai acikin garin harya gaji datafiya, baisan inda zashiba baisan kowaba arayuwarsa sai iyayensa dasauran Yan kauyensu da wadanda sukayi karatu tare sai Kuma Afra wadda tazama wani yanki acikin rayuwarsa

Marece yayi sosai kowa da sabgar gabanshi saidai akwai wani bakon al amari daya daurewa Kamal Kai shigowarsa wannan gari sbd duk Wanda yagani ahanya saikaji anakiransa da ranka yadade, wasuma harda sunkuyarda da Kai sukeyi alamar girmamawa wannan abu yana bashi mamaki sosai tunani yakeyi kodai al adar garince ahaka, da wannan tunanin yabar zancen.

A wata inuwace yayada zango duk da sanyin marece dake kadawa baihanashi gumiba sbd tsabar tashin hankalinda yake ciki, yadade awajen domin har sallar isha’i ma dayaje masallaci yadawo anan yakara zama, yunwa ke addabarsa gashi bashida kudi, Wanda yarage masa sukenan yabiya kudin motar daya shiga.

Aza kansa yayi bisa kunshin kayansa ya kishin gida, a haka bacci barawo yadaukesa

Kamar amafarki yaji ana tabashi, firgigit yatashi tsorace ganin wani dattijo zaune kusa dashi yakara tsora tashi batun mikewa yakeyi dattijon ya riko hannun sa yace “ranka yadade…..

By
meerah 💞
[3/15, 10:22 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻

🌹🌹🌹🌹🌹

By

🌹🌹🌹
Meerat💞
🌹Also known as 🌹
Samira Ayuba🥰🥰
08068971503

Na sadaukar da wannan page gareki mahaifiyata Allah yakara Miki lfy da nisan kwana💘💘

Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai

 

🅿️ 3️⃣_4️⃣

 

Batun mikewa yakeyi dattijon yariko hannunsa yace:

“Ranka yadade kazauna zamuyi mgn”

Zama yayi, duk da cewa baya son ganin kowa akusa dashi, amma zaiso wannan dattijon ya taimaka masa Koda da abinda zaicine….

“Ranka yadade kozaka iya gayamin sunanka, Da Kuma labarinka”

Kallonsa khamal yayi, tare da daure fuska, ya kauda kansa gefe, kamar bazaiyi mgn ba, dattijon harya fitar da rai dajin amsarsa, da kyar yabude baki yace “sunana khamal Amma abokaina sunfi kirana da 🤴 khamal”

Gyada Kai dattijon yayi, yace “awane gari kake, Kuma a Ina iyayenka suke, dannaga da alamar Kai bakone agarin, Kuma ga dukkan alamu kana cikin damuwa, domin tunda kazo wajennan nake lura dakai”

“Banida iyaye” yafada cikin kosawa da maganar.

“Ranka yadade dare yayi , kataso muje gidana idan kaso gobe saikaje inda kakeso”

“A’a bazan jeba, kabarni anan zanfi jindadin hakan”…

“Karka damu dana bazan takurama da surutu ba, danna ga alamar bakason yawan mgn, kataso muje kaci abinci” Yafada Yana mikewa tare da daukar kunshin kayan khamal….

Binsa yayi abaya batare da yace komai ba Dan koba komai zaisamu yaci abinci, da wurin kwana….

Washe gari misalin karfe 9:00am khamal yafito daga cikin dakin daya kwan, da kunshin kayansa.

Zaune yaga dattijon atsakiyar gidan, yace: “baba nizan tafi, nagode kwarai da taimakon da kayimin Allah yasaka da alkhairi”

Mikewa tsaye dattijon yayi cike da mamaki, yace “yaro ina zakaje haka da safennan, ko kanada Yan uwa agarinnan ne”?

“A’a baba bansan kowa ba a garinnan saikai, bazan iya zama anan ba sbd banason nadaura maka wani nauyi akanka”

“A’a khamal bazan barka katafi ba harsai nasan ko Kai wanene idan da hali saina taimaka maka”

Kallonsa khamal yayi sbd shi arayuwarsa Babu abinda ya tsana kamar lbrn rayuwarsa domin cike yake ban haushi, ko kadan khamal bazai taba bawa wani lbrnsa ba sbd shi kansa da abin ya faru akansa haushin kansa yakeji, balle kuma wani yasanda wannan mummunan lbrn ai tsabar sa kawai zaayi….

“Kamar yadda na fadama abaya banida iyaye, ni shegene dan tsintuwa ne, bansan kowaba, ahaka nataso harna girma”

“Su waye suka reneka harka girma kasan ciwon kanka”?

Gabansa ne yayi mugun faduwa, sbd shi ko amafarki baya fatan sake jin lbrn rayuwar da yayi tare dasu, cikin ransa yake furta natsaneku natsaku, inna laure Allah ya isa tsakanina dake….

Hawayen da suka gangaro masa ya share, yace: “sun rasu…….. 🤔

“Allah yaji kansu yayi musu rahama, ka kwantar da hankalinka ranka yadade kaiba shege bane, Kai dane, dan sunnah kamar kowa, karka Kara Kiran kanka da shege”

Zaro idanu yayi Yana kallon dattijon “bangane abinda kake fada ba, taya zakace niba shege bane bayan tsinta ta akayi acikin daji”

Murmushi yayi tare da dafa kafadarsa yace “iyayenka anan garin suke Kai babban mutum ne ranka yadade, duk Wanda ya ganka yasan Kai jinin Mai martaba ne sarkin garinnan, sarki Ahmada Abdus-salam”……..

By
Meerat 💞
[3/15, 10:22 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻

🌹🌹🌹🌹🌹

By

🌹🌹🌹
Meerat💞
🌹Also known as 🌹
Samira Ayuba🥰🥰

 

🌹🌹ELEGANT ONLINE WRITER’S✍️✍️✍️

(EOW)💘💘

Na Sadaukar da wannan littafi gareku masoyana Ina alfahari daku 💘💘💘

Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai

 

🅿️ 5️⃣_6️⃣

“Iyayenka anan garin suke Kai babban mutum ne ranka yadade, duk Wanda yaganka yasan Kai jinin Mai martaba ne sarkin garinnan, sarki Ahmad Abdus-salam”

Kallonsa khamal yakeyi ko kiftawa bayayi, farincikine fall aransa, Amma azahiri sai yace “baba dama iyayena suna raye shine suka yaddani adaji” wasu zafafan hawaye ne suka gangaro a lallausar fuskarsa.

Hannu baba yasa yashare masa hawaye ya dafa kafadarsa yace “ba yaddaka sukayiba khamalu sace ka akayi, kazauna danna baka labarin zuwana masaurata”

Zama yayi cike da sonjin lbrn da baba zai bashi game da iyayensa……

Kallonsa baba yayi sannan yafara da cewa “Ni sunana sanusi haifaffen garin zamfara ne muna rayuwa ne awani kauye dake cikin yankin zamfara, iyayena marasa karfine sosai muna Shan wahala sosai a kauyenmu, domin abincima ga gararmu yakeyi wani lkc, wannan dalilin ne yasa iyayena suka yanke shawarar dawowa nan garin Zaria wajen abokin mahaifina domin yasama mana irin aikin daya keyi agidan saurata, munzo cikin nasara kuwa inda aka dauki mahaifina aikin gadi nikuma da ban wuce shekara 10 ba akasani aikin bawa shukoki ruwa, ita Kuma mahaifiyata agida tazauna domin mahaifina yace bazatayi aikin bautaba”

Kallon khamal yayi yace “kaji dalilin zuwana wannan garin”

Khamal kallonsa kawai yakeyi batare da yace komai ba.

“Haka mukaci gaba da aiki agidan sarauta harna kai shekara 25 cikin wannan shekarar ce nayi aure na auri Khadija Yar jakadiya wadda kewa matar sarki hidima, ahaka mukaci gaba da rayuwa acikin gidan”…

Bayan wasu shekaru Mai martaba sarki Ahmad Abdus-salam ya Kara aure, sbd yasamu haihuwa domin shekararsu goma da hajiya Fulani Amma Allah baibasu haihuwa ba.

Ya auri hajiya Nafisa Yar babban attajirine acikin garin Zaria, anan Mai martaba ya bada umarnin abawa mamata Khadija jakadancin hajiya Nafisa sbd yabawa da halayenta nakirki, a duk masarautar babu baiwarda takaita rikon gaskiya da amana,

Bayan shekara daya da auren Mai martaba da hajiya Nafisa Allah yabasu haihuwar da namiji, Mai martaba yayi farinciki da wannan haihuwar sosai domin anyi shagali sosai aranar haihuwar, Mai martaba yayi kyauta wadda bata misaltuwa adalilin haihuwar 🤴🏻prince Yazeed, saidai kash…… a Daren ranarda aka haifi prince Yazeed a wannan ranar aka sace shi 😭😭😭”

Kuka ne yaci karfin baba sanusi Wanda ya hanashi ida lbrn……😭😭😭

Nima anan zan dakata harna share hawaye na sbd batan yarima Yazeed 😭😭😭😭😭

By

Meerat 💞
[3/15, 10:22 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

 

By
💞meerah💞💞
🌹 Samira Ayuba🌹🌹
08068971503

 

🌹🌹 ELEGANT ONLINE WRITER’S✍️✍️✍️

Sadaukarwa gare ku masoyana Ina alfahari daku💘💘💘💘💘💘

 

Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai

 

🅿️. 7️⃣_8️⃣

 

Hawayen dake gudana a fuskar sa ya share, kallon baba sanusi yayi yace “meya faru bayan batan prince Yazeed”…

“A Daren ranar bawan da yayi bacci acikin masarautar sbd tsabar firgici da tashin hankali, Mai martaba sarki Ahmad Abdus-salam yayi Suma fiye da goma kafin gari ya waye 😭😭😭 likitoci sundade akansa kafin asamu yadawo hayyacin sa.

Haka itama gimbiya Nafisa tayi jinya sosai a dalilin batan prince Yazeed.

Gimbiya Fulani itama tayi kuka kamar ranta yafita ganin tana gab da rasa mijinta abin alfaharin ta a dalilin batan yarima Yazeed…..

Bayan Mai martaba yasamu sauki har yadawo gida, yabada umarnin a daure matata Khadija, wadda itace jakadiya ga gimbiya Nafisa Kuma itace ke tare da prince Yazeed har lokacin da aka saceshi, wannan dalilin ne yasa Mai martaba ya bada umarnin daureta harsai dansa ya bayyana…..

Bayan daure Khadija Nima na fuskanci hukunci Mai tsanani awajen Mai martaba, nayi watanni a daure sai daga baya aka sakeni.

Mai martaba ya kamu da ciwo hawan jini, gimbiya Nafisa itama ta kamu da ciwo zuciya a dalilin batan yarima Yazeed.

Baya batan yarima Yazeed da shekara 10 gimbiya Fulani tahaifi yarta Mai suna khausar, kausar nada shekara 3 gimbiya Nafisa ta sake haihuwar yarta Mai suna khairat.

A haka rayuwar Mai martaba da gimbiya Nafisa ta kasance cikin kunci, sbd har yanzu Mai martaba bai samu haihuwar da namijiba”….

Kallon khamal baba yayi yace “yau shekara 34 kenan da batan prince Yazeed, har yau babu Wanda yasake jin lbrn sa, anyi nemansa kamar hauka Amma Babu shi Babu alamarsa..

A yanzu haka nasan Mai martaba yaji lbrn zuwanka garinnan, Kuma Koda yaushe zaka iya ganin fadawansa sunzo nemanka, domin tabbas zasu San nina daukeka Kuma hakan zai iya jawomin wani hukunci Mai tsanani awajen Mai martaba, Amma Ina neman kasa Mai martaba yayimin sassauci ranka yadade”, hawayensa yashare tare da sunkuyar da kansa kasa, dafasa Kamal yayi yace “ka kwantar da hankalinka insha allah Babu abinda zai sameka sai alkhairi”

Da karfi aka banko kofar gidan, Saida suka tsorata musamman baba sanusi dayayi imanin sai Mai martaba yayi masa hukunci Mai tsanani..

Fadawa ne suka dinga shigowa gidan sunfi a kirga, domin Saida suka cika gidan gaba daya, kasan cewar ba wani girma ne da shiba..

Ganin haka yasa baba sanusi da Kamal mikewa tsaye, gabadaya fadawan suka russuna kasa suna kwasar gaisuwa, gaisheka ranka yadade Mai girma yarima, magajin sarki, jikan sarki, Mai martaba sarki yabada umarnin a zo tare dakai ranka yadade…

Kallon baba sanusi yayi yace “baba Babu tabbacin cewa nine Wanda ake nema fa”😔

“Kamal babu Wanda zai kalleka yace kaiba Dan mai martaba bane domin kamar ku daya dashi Babu inda kabarshi, Kuma karka manta fa ka gayamin wadanda suka reneka a daji suka tsinceka, taya zakace kaiba Dan Mai martaba bane”?

“Hmmmmm” dogon numfashi khamal yasauke, harga Allah yanason haduwa da iyayensa, Amma yanzu fargabar zuwa garesu yakeji ko menene dalili oho!! Nidai nace kabar wannan tunanin tunda baka da Mai baka wannan amsar.

A kunne baba sanusi ya rada masa wata mgn wadda nikaina banji abinda ya gaya masaba, kallon baba sanusi yayi, gyada Kai yayi alamar yaji mgnr da yayi masa,.

Kallon fadawan Kamal yayi yace “muje ko” tashi sukayi suka buda masa hanya, a hankali yafara daga kafarsa Yana takawa saikace Mai koyon tafiya, dama salonsa kenan, shiyasa abokansa suke kiransa da prince khamal, sbd komai nasa cikin kasaita yakeyinsa, idan baka sanshiba, a schl ka fara ganin sa zakayi tunani shi Dan wani babban mutum ne, alhalin Kuma shidin rainon kauyene, ilimi ne kawai yasa yake gudanar da al amuransa cikin wayewa da kasaita..

Harya fara tafiya yatsinki muryar wani bafade na cewa dakai zamu tafi baba sanusi, gabansa ne yayi mummunan faduwa, sbd yasan cewa yau kashinsa yabushe tunda Mai martaba yayi kiransa a fada, a dalilin kamasa da akayi da magajin sarki…

Jikinsa ne yafara rawa kafin kace wani abu tuni baba sanusi yafara fitsari a wando 🤭 durku sawa yayi har kasa ya fara kuka mai tsuma zuciya..

Khamal ne yayi karfin halin danne dariyar sa yazo ya daga baba sanusi yace “ka kwantar da hankalinka insha Allah Babu abinda zai sameka idan Kuma har za’a hukuntaka a dalilin ka taima keni to tabbas ni zan dauki hukuncin da za’ayima” share masa hawaye yayi, a cikin ransa yanajin kaunar wannan dattijon, da Kuma tausa yinsa, “baba katashi ka cenza kayanka mutafi…

Tashi yayi jiki babu kwari ya shiga bandaki yayi tsalki, yaje ya cenza kayansa….

Tafiya sukeyi acikin mota kowa da tunaninsa, khamal dai yayi nisa sosai a cikin tunani yanajin kaunar iyayensa acikin ransa amma yarasa dalilin dayasa yakejin faduwar gabansa na tsananta, nan take a binda ya faru dashi a kyauyensu yafado masa arai, gaban sane ya tsananta faduwa nan take yaji jikinsa yafara rawa, tabbas idan yabari akasan da wannan lbrin to korarsa zasuyi bazasu taba karbarsa ba, dafe kansa yayi danjin yana sarawa, Ina bazan taba bari wani yasan da wannan lbrin ba, Yafada cikin ransa..

Fadawane suka yi cincirindo a kofar gidan, duk Dan tarbar yarima, kirari suka hauyi masa har aka wangale get din, wani dandazon tarone yagani Wanda yaninka wadan da ke waje, ciki ko harda sarki, da matan sa danya kasa zama a fada sbd tsabar zumu din ganin farincikin sa 🥰

A yau kowa na cikin farinciki musamman Mai martaba da gimbiya Nafisa….

By

💞 Meerah💞💞💞

Comments and share 🙏🙏
[3/15, 10:23 AM] Meerah 💞: 🤴🏻🤴🏻🤴🏻 prince khamal🤴🏻🤴🏻🤴🏻

🌹🌹🌹🌹🌹🌹

By

🌹🌹🌹
Meerah💞
🌹 Samira Ayuba🥰🥰
08068971503

 

🌹 ELEGANT ONLINE WRITER’S ✍️✍️

 

Da sunan Allah Mai rahama mai jinkai

 

🅿️ 9️⃣_🔟

 

Daidai ta parking din motocin sukayi, a hankali Mai martaba ya budewa khamal motar cikin so da kauna, fitowa yayi ya rungume mahaifina sa, da mahaifiyar sa.

Kallo daya zakayiwa wannan family kasan suna cikin farinciki….

AFRA

Kwance take a makeken bed room dinta Wanda yasamu komai na more rayuwa.

“Afra!! Afra!! Afra”!! Cikin tsawa da daga murya umma ke kiranta afalo, tanajinta amma ta share ta danta San bawata mgn Mai dadi za’ayimata ba.

Hawaye ne kwance afuskar ta, tuntana sharewa harta gaji ta daina.

Banko kofar akayi da karfi, “ke Afra wai ba kyajine anata kwala miki Kira Amma kin kyale”

Batace mata komai ba sai kokarin mikewa da takeyi, wucewa tayi tabar umma tsaye adakin tana binta da kallon tsana, kamar ba itace ta haifeta ba.

Afalo ta iske Abba zaune, itama zama tayi da kyar ta iya bude baki tace Abba Ina kwana.

“Da ban kwanaba Zaki ganni? Iye!!! nace da ban kwana ba Zaki ganni, to bari infada miki na tsada miki miji nan da sati daya zaayi auren ku”…

A tsora ce ta mike tsaye, “wlhi Abba bazan aure shiba, ni khamal nake so, shika dai zan aura”

Tasss! Tassss! Umma dake kusa da ita ta wanke ta da mari har sau biyu, “bazaki aure shiba Dan ubanki”

“Wlhi umma mutuwa zanyi idan baku auramin shiba” “kije ki mutu mana waya rikeki, to bari infada miki aure babu fashi, ko kina so ko baki so” Yana gama fadar haka ya fice daga gidan rai bace….

Da gudu ta shige daki ta fada akan kayataccen bed dinta, tana rusa kuka kamar ranta zai fita…..

Umma dake tsaye a falon tana ta faman zabga fada ita kadai, tace “wai anya ba cenzamin wannan yarinya akayi a asibiti ba Anya Yar Dana haiface da cikina? Kallon kofar dakin da Afra ta shiga tayi tace, “wlhi Afra Koda Zaki mutu sai anyi wannan auren baki isa ki zubar muna da mutunci ba, mezakiyi da khamal? Matsiyaci, Wanda bai gaji azzikiba, Dan tsintuwa wanda da ba’asan a salinsa ba, bandama rashin hankali irinna Afra wadda ta haifeshi ta jefar a daji ke mezakiyi dashi? Sannan babban abin takaici shine ya watsawa wadanda suka reneshi, suka ilman tarda shi, kasa a do, ya kunya tasu a idon jama’a, ya to zarta su, ke mezakiyi dashi…

Indai nice uwarki to wallahi baki isa ki aure shiba, sha sha Shar banza mara hankali wadda bata san abinda takeyi ba….

Duk abinda take fada Afra najinta a daki,

Dafe kanta tayi afili tace a’a khamal, baka aikata ba Kuma bazaka taba aikata irin wannan laifin da ake zarginka dashi ba, wlhi Koda zan rasa komai arayuwata saina fitar dakai acikin wannan halin bazan taba barin ana zarginka akan abinda baka aikata ba…..

Wayarta ta dauko tafara Kiran layin khamal, shiru ba’a daukaba, tunjiya take ta kiransa Amma baya dauka, wasu hawayene suka gangaro mata, kodai khamal yarabu da itane? Dafe kanta tayi, tafara tuna irin cin mutuncin da Abba yayi masa, da korar kare acikin gidannan, kuka tafarayi Mai daga murya, kamar mahaukaciya, umma ce tashigo dakin tana binta da kallo, abin duk ya daure mata kai, kodai Afra nada iskane bata saniba sai yau…

Hawa gadon tayi ta jawo Afra jikinta, tana cewa “lafiyarki Lau kuwa” kallon ta Afra tayi tace “umma khamal ya rabudani yaki daukar wayata tunjiya” tureta umma tayi cikin zafin rai tace ai haka nakeso Allah yakara tayi tsaki tabar dakin…

Afra tayi kuka a ranar kamar ranta zai fita, da kyar tasamu bacci yadau keta..

Afra tazama abin tausayi rabonta da abinci tunjiya, yauma bata da niyyar ci domin halin da take ciki Kamal daine zai iya fitar da ita aciki, gashi yatafi ya barta. Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro a fuskar ta, bazan iya rayuwa ba idan har babu Kai khamal…

Wani tunani ne yado mata arai, tashi tayi cikin hanzari ta dauki mayafinta da key din motar ta tafice daga gidan…

Bata tsaya ko inaba sai kauyensu khamal, bakin garkarsu ta tsaya tana tunanin ta shiga kota fasa, saude tagani ta fito daga gidan rike da tulun dibar ruwa da alama rafi zata tafi.

Tana ganin Afra tsaye akofar gidan ta koma da gudu cikin gida, fadawa tayi akan Inna laure dake tsintar wake, “ke meye haka Kuma Zaki fadomin idan nibaki tuna Zaki iya jimin ciwo, aiya dace ki duba Dan dake cikin ki”

“Inna wannan yarinyar ce fa Yar birni nagani a kofar gida”, “wacce yarinya Kuma?, Oh!! Ni laure wai meyasa Yan birni sukeda nacin tsiyane duk da ankori khamal din saita dawomin agida to mezanyi mata”?

“Inna shikenan ta rabani da khamal” saude ce ke mgn tanata faman kuka kamar karamar yarinya, Inna Dan Allah kidawomin da khamal wlhi bazan iya rayuwa ba idan Babu shi..

“Ke dallani matsa kibani wuri ai duk lafin kine da kinyi abinda boka yace aida haka bata faruba, kika kiyi kika je wajen wancen sha sha shan”….

“Wlhi Inna ba laifina bane nima naso na kwaci kaina Amma nakasa dan ya fini karfi”…

Gaban Inna laure ne yafadi ganin Afra tsaye tana kallon su Kuma duk taji abinda suke Fadi.

“Ke Kuma meya kawoki haka mayya anace, to karya kikeyi kurwar khamal tafi karfinki…..

Murmushi Afra tayi tana Kara shigowa cikin gidan, tace ” dama ban taba yadda da wannan sharrin da kuka yimasaba, ayau asirin ku ya tonu Kuma wlhi saina fallasa ku abainar jama’a. Tana gama fadin haka takama hanyar dakin datasan na khamal ne tashiga, dube dube ta hauyi cen taga wayarsa, ajiyar zuciya ta sauke tare da murmushi, daukar wayar tayi tafice daga gidan ba tare da tabi ta kansuba…..

Ta bude motar ta kenan zata shiga ta hangi ado Yana tafiya, rufe motar tayi ta nufi inda ado yake..

Gaisawa sukayi cikin farinciki, Afra ta kalli Ado tace “Ado wai abinda khamal ya aikata gsky ne ko”?

Nisawa Ado yayi yace “nima banyar da ba kokadan, Ina zargin Inna laure da saude akan abinda yafaru, domin saude tana tsananin son kamal, Koda ace tabbas ya aikata to ba ason ransa bane tirsasasa akayi”

“Nima banyar daba Ado nasan khamal sosai a schl, bazai taba aikata irin wannan danyen aikin ba, Amma zan cigaba da bincike koma menene saina gano gsky, Kuma saina Nemo khamal duk inda yake afadin duniyar nan”…..

Anan sukayi sallama takama hanya tashiga mota tabar wajen.

Gida ta nufa cike da farinciki, afalo ta iske umma ta hade rai, itama hade fuska tayi tazo zata wuce ta gabanta taji tace “daga Ina kike”?

Tsayawa tayi batare da tajiyoba tace “daga gidansu nusaiba”

Leave a Comment