Books Reviews & FAQs

Mugun Sartse Hausa Novel

KAFA’DI AlKAIRI KO KAYI SHIRU

 

My Novels

1.Nayi Rayuwa dake

2.Sanadin accident 2019

3.Sakayyar Cuta

4.Ruffiyar Zuciya

5.Hayatul Mahayat

 

TYPING……🖋

Mugun Sartse

 

Assalama alaikum ykk all fans gashi Allah yasake had’amu cikin wani saban book to Allah yabani ikon sadar da fad’akarwa da ilimantarwa had’ida nishad’i amma fa banyi al’kawarin yin typing kullumba sabida kunsan jiki da jini sannan dan Allah duk wadda ba’afara da’ita daga farkoba karta bini ta pc tace naturo mata gaskiya bazan iyaba karwata taga nashareta tace nayimata wula’kanci a a wallahi babu wula’kanci cikin rayuwata amma kuduba dawanne zanji typing ko posting ko amsama fans gaisuwa ko bayarda amsa da jinjina akan comments har yanzu wasu tambayata sukeyi Hayatul mahayat daga farko kunga kuwa aykine suka bani babba masuso kuyi ha’kuri zanyi document sekusamu nagode sosai fatan alkairi gakowa NPEEDY A AJI taku har kullum 🤝🏻

 

Bismillahir Rahamanir Rahim

 

🅿1 to 2

 

” Bikiram Bikiram Bikiram….. ” tsayawa tayi tana kallonshi cikin mamaki duk kiran datake ‘kwala mishi yana zaune a parlour yanajinta ‘karasowa tayi cikin lallashi tadafashi tasake cewa ” haba my Son kanaji sefama kira nikeyi amma shiru ka’ki amsawa ? ”

 

Ture hannunta yayi daga jikin shi yami’ke zaibar parlour batare dayace komiba saurin jawo hannun shi tayi cikin matu’kar damuwa tace ” haba Bikiram idan kayi fushi dani wallahi zan iya shiga cikin damuwar datafi tayanzu fuzge hannun shi yayi cikin tsadaddiyar muryar shi yace

 

” mah ni kibarni nagaji bakuma zan iya cigaba dayin ha’kuriba nace kikaini gurin mahaifina da d’an’uwa amma kin’ki kuma kin’ki sanar dani dalili yaya kikeso nayi mah zuciyana matu’kar zafi takeyi idan natuna bansan waye mahaifina ba bankuma ta’ba gani d’an uwana ba mah zanbar India naje Nigeria neman mahaifina mah kisanar dani idan niba d’an sunna bane k…… ”

 

Mari tasauke mishi akaro nafarko a rayuwar shi ri’ke kuncin yayi yazaro ido yana kallonta dandanan hawaye suka shiga gangarowa daga cikin manyan idanun shi kuka itama tasaki rungumoshi tayi cikin muryar kuka tace

 

” haba Bikiram maiyasa zakabari zuciyar ka takitsa maka wannan mugun tunanin Bikiram kai d’an sunnane cikakke seda d’inbin jama’a suke sheda aure na da mahaifinku amma kas cikin iyayen mahaifinka babu wanda yasan haka mahaifinka yazo India karatu anan muka had’u yanuna tsananin soyayya agareni tun ina shareshi har na’amince soyayya mai ‘karfi tashiga tsakaninmu koda yazo wajan iyayena akan maganar aurena mahaifiyata tanuna bata bu’katar hakan amma mahaifina yagoyi bayana sabida tsananin son dayake yimin sosai ‘yan uwana sukaji haushi akan na amince da auran d’an Nigeria batare dasanin kowa nashiba jin hakan yasa mahaifina cema mahaifinka yaturo iyayen shi amma mahaifinka tuni zuciyar shi takarye sosai yafarayin kuka agaban mahaifina cikin kuka yacema mahaifina ayanzu iyayen shi bazasu barshi yayi aureba sabida baigama karatuba amma dan Allah abashi aurena idan mukayi aure zamu zauna anan idan yagama karatu semukoma Nigeria yasan alokacin mahaifan shi bazasu hanaba mi’kewa mahaifina yayi yace

 

” Sameer hakan bazai yiwuba idan bazaka turo iyayen kaba tosede kaha’kura da auran ‘yata ” sosai Sameer yari’ke ‘kafarshi yana kuka mai tsuma zuciya ganin haka yasa mahaifina kamashi yatashi hannun shi yasa yashare mishi hawayen yace ” ha’ki’ka nagamsu da son dakakeyima Sareena kumazanbaka auran ta amma akwai sharad’i ”

 

Duk ranar dakatashi tafiya Nigeria tare dani zamutafi dan bazanbaka ‘yata katafi da’ita ita d’ayaba idan ka amince shikenan ” cikin farinciki Sameer ya’amince Sameer yayimin komi wanda akeyima duk wata ‘ya maigata kasancewar shi jinin sarauta kuma wanda iyayen shi kematu’kar jidashi dan duk yawan kud’in dayace yana bu’kata batare dajin komiba zaituro mishi sosai kowa yayi mamakin irin hudimar da Sameer yayi min ”

 

Bayan auranmu munzauna cikin gidan da Sameer yake wanda yazama gidane mai matu’kar kyau da tsari dukda mahaifina yabamu gida muzauna amma ya’ki dagani se mahaifina sekuma yayata mukayi hidimar auran amma mahaifiyata ko kallo bamu’ishetaba hakama sauran yayyena maza haka aka mammala komi

 

Sosai Sameer yake nunamin tsananin soyayya bai hanani cigaba da karatunaba yana karatunshi inayin nawa rayuwa maidad’i muke gudanarwa bayan 2 months dayin auranmu nasamu cikinku sosai nikeshan wahala har laulayin yashafi karatuna sosai mahaifiyata takeyin fad’a ganin haka yasa dole nike zuwa skul kodabazan iya fahimtar komiba

 

Seda cikinku yakai 11 months sannan nahaifeku kamar bazan rayuba kodana haifeku sedanakwashe 3 months bansan ina kaina yakeba balle nasan abindana haifa Aunty tadawo gidana dazama dole cikin wata na 4 nasamu lafiya sosai nayi farincikin samunku daganan nacigaba dayin karatuna bayan kun shekara 3 alokacin nasamu wani cikin lokacin mahaifinku yagama karatunshi amma baikoma Nigeria ba yanajira nagama nawa karatun semutafi tare

 

Matsawar da iyayenshi sukayimai yasa dole yashirya zuwa Nigeria akan cewa wata 1 zeyi yadawo sosai mukasha kuka d’an uwanka yari’keshi wato Kiram kam ya’ki sakinshi yanayin kuka mai tada hankali kasancewar an haifeshi da ciwon Zuciya tun yana jariri yasa ba’ason damuwar shi hakan yasa dole akashirya tafiya da Kiram yaso yatafi daku duka amma kai ka’ki sabida dama can kafi ma’kalemin

 

Haka Sameer yatafi shida Kiram har Airport mukayimai rakiya muda dady na sosai naji damuwar tafiyar shi musamman idan naganka kana wasa kai d’aya gashi tunda sukatafi kakoyi rigima sosai sekaita kuka kanakiran Kiram dukda baka’iya kiran sunan sosaiba sosai mukeyin waya bayan tafiyarshi amma abin mamaki tun bayan 1 week datafiyar shi yadena kirana idan nakira baya d’agawa hakan yasa hankalina yatashi sosai nafara tunanin lafiya kuwa amma bangaji dakiraba wata rana nakira mahaifinshi yad’aga cikin girmamawa nagaidashi amma wata irin tsawa yadakamin cikin fad’a yace

 

_inamai baki shawara kicire d’ana Sameer daga zuciyarki dan bazai ta’ba dawowa garekiba bana bu’katar gur’bataccen iri cikin zuri’a ta Sameer jinin sarautane bajinin banzaba nanda 2 weeks auran shi da yar uwar shi yar asali mai cikakkiyar nasaba kuma bahaushiya kinji nasanar miki duk da turanci yake sanar dani haka sabida alokacin banajin Hausa sosai_

 

” Bikiram bansan lokacin da phone d’in yafad’i daga hannunaba take naji wani irin juwa tana d’ibana dede lokacin kazo kana kuka ganin yadda kake kuka yasa nashanye nawa kukan ina zaune mahaifina yashigo cikin damuwa yace Nishah wannan gidan dakuke ciki ansameni ance kutashi sabida Sameer yakoma Nigeria kuma wai babu wata shedar datake nuna cewa ke matarshice shiyasa nazo ki kiramin shi ni idan nakirashi baya d’agawa ”

 

Jin wannan mummunar maganar yasa hankalina ‘karatashi sosai dole nasanar ma mahaifina abinda mahaifin Sameer yacemin sosai hankalin mahaifina yatashi amma senaga yadake nasan sabidani yashare kwashe kayanmu yasa akayi yakaini d’aya daga cikin gidajenshi dan gudin surutun mahaifiyata dana ‘yan’uwana cikin lallashi mahaifina yace

 

” Nishah banaso kisa damuwa cikin zuciyarki ki kwantar dahankalinki kina haihuwa zamuje Nigeria dole Sameer yatabbatar ma iyayen shi ke matarshice kinji nayi miki al’kawari kuma in sha Allah zasu amsheki matsayin surika ” sosai najidad’in maganar dadyn bayan kammala karatuna da 3 Months nazama cikakkiyar doctor nahaihu ‘ya mace mahaifina yayi mata huduba da Ayshah wato sunan mahaifiyar Sameer wato ‘kanwarka ilham

 

” seda ilham tashekara kai kuma kanada 4 years mahaifina yashirya mana tafiya Nigeria kuma har zuwan wannan lokacin mahaifinku bai’kara nemanaba mun isa Nigeria lafiya amma sede kuma kama hotel muka kwana sabida dare yayi washegari muka nufi cikin masarautar Gombe batare da shakkaba munsamu matsaloli wajan dogarawa da hadimai kafin akayimana iso zuwa fada munashiga nayi tozali da Sameer zaune gefan mahaifinshi ga Kiram zaune kan cinyarshi abin mamaki tasowa kiram yayi yari’keni yana murna kai ko rungumeshi kayi kuna murnar ganin juna

 

Cikin nuna farinciki Sameer yataso batare dajin kunyar kowaba yarungumeni amsar ilham yayi yana sumbatar kuncinta had’ida tambayata sunanta koda yaji sunan hamaifiyar shine farinciki yasa yasake rungume ni amma babu zato mukaga mahaifin shi yataso wankeshi damari yayi yafizge ilham daga hannunshi ya dangwaromin ita tasa kuka janye Kiram yayi daga jikina yace

 

” kamar yadda kukazo yanzu haka zakujuya dan bazan yarda d’ana guda 1 tilo yazauna da wadda ba yaran shiba kumama ba yar Nigeria kijuya keda yaranki Kiram kad’e nayarda Sameer yari’ke ” juyawayayi kan Sameer yace ” Sameer amatsayina na mahaifinka inamai baka umarnin kasaki wannan hindun matar taka kona tsine maka ”

 

Cikin gigita Sameer yakalli mahaifin nashi sannan yadu’kar dakanshi yace ” Nishah nasakeki saki 1 ya’karashe fad’ar hakan cikin shasshekar kuka mahaifina yanajin haka yadu’ka yad’aukeka yaja hannuna mukafito batare dayace komiba har muka fita daga cikin fada inajin kukan Kiram da shasshekar kukan Sameer sautin danakejin shi har yanzu cikin kunnuwana Hotel mukakoma har zuwa lokacin mahaifina yakasacewa komi sabida ba’kinciki kuma baihanani yin kukaba washe gari muka koma India cikin tsananin ba’kin ciki

 

Bayan mundawo mahaifina yabani takardun wannan gidan yace yabanishi kyauta nazauna nida yarana sannan yayimin al’kawarin ginamin Hospital nawa nakaina mahaifina shine yad’auki nauyin karatunku har kazama cikakken likitan zuciya itakuma ilham tazama ma’aykaciyar bincike ta CBI kuma shine yaginamin wannan Hospital d’in wadda mukeyin ayki cikinshi nida kai gashi ayanzu kanacikin sahun manyan masu kud’in India yau kaji dalilin dayasa banaso kayimin maganar mahaifinku kuma kaji dalilin dayasa kuka rabu da d’an uwanku Kiram sannan kaji dalilin dayasa na’ki ‘yarda mukoma saban katafaran hospital d’in daka gina sede nasa akazuba ma’aykata duk ‘karshen watan duniya ina turawa adubamin Kiram amma sede kass an cusamishi tsanata matsananciya cikin zuciyar shi yanada Company cikin garin Abuja nashi nakanshi banda Wanda yake dasu a ‘kasha shen ‘ketare amma yanzu yana Japan yatafi wani business dan shi yakaranta har yanzu yanafamada wannan ciwon zuciyar shiyasa ba’a ‘batamishi rai dukda kakan Ku bayasona amma yana masifarson Kiram wanda ayanzu suka canjamai suna Salman hakama kakarku dukda matar mahaifinku tahaifi yara 2 namiji da mace amma sunfi son Kiram akansu Son had’uwa da mahaifinku shine 🙆🏻Mugun Sartse💘 Wanda zuciyata tayi wanda har yanzu nakasa cireshi gashi har gobe yanacin Zuciyata da jikina

 

 

Son yanzu kanada damar tafiya Nigeria wajan mahaifinka ” ta’karashe fad’ar hakan cikin kuka rungumeta Bikiram yayi cikin nuna nadamar abinda yayi da danasanin wannan tambayar dayayi mata yace

 

” Mah kigafarceni akan tilastaki danayi akan sanin waye mahaifina gashi nasakin sake tuna abinda yayi sanad’in faruwar ba’kin ciki cikin rayuwar ki segashi nima bai’kareni dakomiba se samun ‘karuwar ba’kin ciki bazan sakeba mah bazansake tuna Nigeria ba balle mahaifina amma bazan iya manta Kiram ba mah ”

 

‘Dan bubbuga bayanshi tayi tace ” haba Son kabar kukan mana yanasani jin zafi cikin zuciyata kaji Son ” jinjina kai yayi dede lokacin wata kykkywar Budurwa tashigo jin sallamar ta yasa mah saurin share fuskarta shima Bikiram share tashi fuskar yayi cikin farinciki tazo tarungume mah tana gaidata juyawa tayi tarungume Bikiram tace

 

” barka da hutawa Brother ” duk cikin yaran Hindu sukeyin magana murmushi yayi yasumbaci kumatunta yace ” Ilham yaya aykin naki ? ” Murmushi Ilham tayi tace ” gaskiya yaukam brother ayki yagajiyar dani amma wai nanda 1 week zamuje Nigeria wani bincike d…… ” cikin fusata Bikiram yami’ke yace

 

” idan har sekinje Nigeria zakicigaba da ayki to daga yau kishirya barin ayki dan bazaki ta’ba zuwa Nigeria ba daga haka yabar parlour rai ‘bace ” binshi da kallo Ilham tayi cikin mamaki tundatake baita’ba tamke mata fuskaba amma yau segashi harda fad’a maikenan juyawa tayi zatayima mah magana tayi saurin mi’kewa tace tashi kije kiwatsa ruwa kizo muyi dinner ” daga haka itama mah tanufi bedroom d’inta sosai Ilham takeyin mamakin yadda yanayinsu yacanza tashi tayi tanufi bedroom d’inta zuciyarta cikeda tambayoyi

 

Nigeria

 

Gombe illahirin jama’ar cikin masarautar kowa kagani fuskarshi d’auke da farinciki sabida murnar dawowar yarima Salman fuska sake maimartaba Sameer yafito dan ayanzu shike mulkin masarautar Gombe dandanan akashiga yin kirari motocin da akajera yanufa dogarawa nabiye dashi bud’emai mota akayi yashiga yana shiga akarufe kallon matar dake gefanshi yayi cikin mamaki yace

 

” mama hadaku wajan taro Salman aydakun bari kunga bakuda lafiya sosai ” harararshi tayi tace ” rufamin baki yadda nikejin Salman cikin raina ayanzu yafi yadda nike jinka badan wannan masifaffan mahaifin nakaba da tuni nasa kadawo da matarka da sauran yaran tunda naji har yanzu batayiwani auran ba mahaifinka yakasance mai adalci da tausayi amma akan matarka bainuna hakanba dukda cewa musulmace amma yanaganin kamar shigowarta cikin zuri’ar mu zesa sunan zuri’ar tamu ya’baci sabida banbancin al’ada har gobe banagoyan bayan abinda yayimata ”

 

Ajiyar zuciya Maimartaba yasauke wato Sameer ahankali motocin suke tafiya sabida kasancewar Hajiya tanacikin tawagar zuwa Airport d’in kuma batason gudu a mota shiko maimartaba duk ya’kagu sabida yasan Salman bayason jira gashi ba’ason ‘bacinranshi agogon hannun shi yakalla 02:15 wata irin ajiyar Zuciya yasauke sabida Salman yasanardashi 2 jirginsu zai sauka amma gashi har 15 minutes ya’karu kuma basu’isaba

 

Airport

 

Wani kyakkyawan saurayi tsaye cikin harabar Airport fuskar nantashi a matu’kar murtuke sanye yake cikin shigar shigar ‘kananun kaya masu matu’kar tsada farine tass sumarkanshi kwance lif sefaman she’ki takeyi alamar tanashan gyara gata baka wuluk dogone ga hanci dogo har baka Salman kenan tsananin kama shida Bikiram duk fuskar mahaifiyarsu sak wato Neeshah kallon agogon hannunshi yayi akaro nababu adadi tsuki yaja yasake duban agogon hannu yasa yashafi sajan shi dagad’an nesa dashi kad’an wasu kyawawan ‘yanmata su 3 suma da’alama jiran zuwa d’aukarsu sukeyi d’aya dagacikin su wayarta tashiga ruru cikin zumud’i damurna tad’aga

 

” dagaske yaya Hisham tawajan ina kake ? ” dagacan ‘bangaran yace ” daga gefan damarki zakiganni ina waya najuyabaya ” cikin sauri tami’ke d’aya dagacikin ‘yanmatan tayisaurin kamo hannunta tace ” haba Samihat wannan irin zumud’i haka aygara kibari yazo ” Murmushi Samihat tayi tace ” haba Amina yaya Hisham nefa hmmm kinsan yadda nikesonshi muwa ? yanzufa kimanin 5 yrs kenan banganshiba nasan yanzu ya’karayin kyau sosai kinga tunda nakammala karatuna shikenan se maganar auren Mu nidashi ”

 

daga haka tajuya tanufi gurinshi cikin sauri shikuma dede lokacin yahangi wani Friend cikin sauri yanufi gurinshi dede lokacin Wayar hannun Salman tashiga ruru kallon wayar yayi dukda yaga mahaifinshi yake kiran baisa yad’aga cikin sauriba sedatakusa katsewa sannan yad’aga had’ida juya bayanshi dede lokacin Samihat ta’isa gurin batare dajin wata sakkaba tarungumeshi tabaya tana fad’in I miss u yaya na

 

Cikin matu’kar zafin rai Salman yajuyo hannu yad’aga yasaukemata mari 2 ajere cikin gigita Samihat tace kai d’angidan uban waye dazaka mareni ina mace kasan darajar mace kuwa ? ” sake d’aga hannu yayi zai’kara mata dogarawa suka iso zubewa sukayi suna kwasar gaisuwa da ban ha’kurin rashin zuwa akan lokaci tsawa Salman yadaka musa yace ” banabu’katar cigaba daganinku agabana cikin sauri suka mi’ke cikin taurin murya yace ” Al’ameen ” cikin sauri matashin saurayin wanda baiwuce sa’an shi Salman d’inba yaje yadu’ka fuska tamke Salman yace

 

” Inaso abincikomin wane da’ki’kinne mahaifin wannan wayuyar yarinyar sannan wace shasha shar uwarce tahaifeta sunike bu’kata subani ha’kurin abinda tayimin ” daga haka yajuya yanufi mota kafin yashiga motocin mahaifinshi suka iso cikin sauri akabu’de motar maimartaba nufo Salman yayi cikin murna dafarinciki rungumeshi yayi yanamai Welcome amma fuskar Salman babu alamun murna ko kad’an cikin damuwa maimartaba yace

 

” Haba my popster kayi ha’kuri kaji balefin dady bane Hajiya ce tamatsa semunjo tare kumakasan batason gudu amota please mana my lovely Boy kamo hannunshi maimartaba yayi kamar wani ‘karamin yaro suka nufi mota Hajiya ta’karaso tana sakin Murmushi nata fad’in barka da isowa farincikin masarautar mu ita dakanta tabud’e mishi mota yashiga shikad’e se driver kishin gid’a yayi yalumshe ido yana tunanin irin wula’kancin dazaiyima Samihat itace tafarko data zageshi duk duniya dole yahukuntata hukunci mafi muni cikin Rayuwarta

 

Bayan tashin motocin su maimartaba ‘kawayen Samihat suka iso kamata sukayi sunabata ha’kuri cikin zafin rai tace ni zai mara ni Samihat Wallahi senaga u……? cikin sauri Amina tace ” a a Samihat karki ‘karasa dan babu abinda zaki iya yima Salman nasan bakisan waye Salman ba to wannan dakike gani shine Farincikin masarautar Gombe idan kina neman masifa to kishiga gonar prince Salman kiyi addu’a Allah yasa daga wannan marin yarabu dake kenan karyasaka rayuwarki cikin ‘kunci data iyayenki ” tsaki Samihat taja tace ” Amina karki manta nimafa iyayena bamatsiyata bane kud’i suna’iyayin komi dan haka akaina Prince Salman zaiyi nadama kirubuta ki’aje ”

 

Dede nan Hashim ya’iso cikin fushi Samihat tajuya saurin ri’ko hannunta yayi cikin sauri yari’ke kunnanshi yace tuba nikeyi Cwt bby ” jin hakan yasa Samihat sakin ranta nufar motocin nasu sukayi zuwa gida suma su Amina haka

 

cikin farinciki maimartaba yadubi Salman yace ” my lovely boy yaya business d’in naka yanatafiya dede ko fatan kajidad’in zuwa Japan ? ”

 

tsayin lokaci sannan Salman yace ” komi dede Abba ” Jinjina kai maimartaba yayi ganin Salman bayason magana yasa maimartaba baisakecewa komiba suna isa akashiga murna busa masu algaita sukashigayi damasu sarewa anabud’e murfin motar su maimartaba Yarima Salman yafito afusace tsawa yadaka musu yace

 

” wannan wane irin shashancine kunsan banason hayaniya shine dazucika kunnuwana da busar sarewa daga dawowana duk wanda yasake yasake busha wannan abun to bamasenace komiba kunsan mai zefaru Abba nagaji dayawa ina bu’katar hutu sosai karwanda yashiga part d’ina har zuwa nanda gobe ”

 

daga haka yanufi hanyar part d’inshi cikin takunshi mai jan hankali Murmushi maimartaba yayi yanufi fada tareda dogarawa sunamai kirari itakuwa Hajiya tuni tanufi ciki tareda hadimai dan batajin dad’in abinda Salman yakeyi amma babu halin tsawatarmai sabida ciwonshi

 

wata kyakkyawar yarinya yar kimanin 17 yrs sanye dakayan bayi tanufi ‘bangaran d’akunan bayin cikin wani ‘karamin d’aki tashiga kaitsaye tafad’a kanjikin wata dattijiwar mata tasaki kuka maicin zuciya cikin kid’ima matar tace

 

” haba Iman wannan kukanfa ” kinsande banason damuwarki balle kuka kisanar dani dan Allah Iman ” tashi Iman tayi zaune ajiyar Zuciya tasauke tafuskanceta sosai tace

 

” Inna narasa maiyasa nake masifar son Yarima Salman kullum abin ‘karuwa yakeyi Inna har nafara rasa bacci akan tunanin shi Inna ina masifar jin haushin zuciyata datakeson marar imani kuma marar tausayi wanda yamaida wula’kanci tamkar ruwan shanshi maiyasa haka Inna ? ”

 

ajiyar Zuciya Inna tasauke tace ” sabida bakida hankali shiyasa kike sonshi Iman sonawa zance miki banason wannan shashancin amma ba lefinkibane yarintace Iman kirufamana asiri mufa bayine agareshi idan wani yasan wannan maganar tofa munshiga uku dan wallahi semunyi nadamar zuwanmu duniya Iman ke kad’e gareni karkiyi sanadin rabuwarmu mahaifinki yatafi yabarmu saura nidake dan Allah ‘yata kinaganin yadda Yarima Salman yake wula’kanta manyan ‘yan mata masu aji ga dukiya balle ke yarinya ‘karama kuma baiwa baiwarma mai yime shara ko matsayin maibashi ruwa bakikaiba tayaya kike biye zuciyarki akan wannan haukar kishiga hankalinki Iman ki…… ”

 

shigowar wata baiwa yasa Inna yin shiru hararar Iman baiwar tayi tace ” ke Iman kije yarima yanakiranki zaro ido Iman tayi tadafe ‘kirjinta tace ” innalillahi mainayi Zule ? ”

 

Tsaki zule taja tace ” wannan kuma idan kikaje kyaji daga haka tajuya tafita bubbuga bayanta Inna tayi tace ‘karki damu Iman tashi kije in sha Allah babuwata matsala cikin sanyin jiki tami’ke tatafi bakin ‘kofar part d’in shi tatsaya tanajin tsoran shiga muryar momy tajiyo tana waya wato matar mahaifin Salman maimartaba magana takeyi ‘kasa’kasa kamar haka

 

” habawa kede bari ‘kawata ay yau nasamu nasarar sakame wannan ‘kwayar cikin abinshan shi kinsan shi mayan shan so’bone to nahad’ame shi namusamman dayasha shikenan semushiga cikin mataki namusamman hmmm wallahi natsani Salman fiyeda mutuwata haba ina yanzufa nafito kumasedanaga yazuba so’ban cikin Cup k….. ”

 

Jin haka yasa Iman shiga aguke tabanka ‘kofar kamar anbiyota ganin yad’aga Cup d’in yasata sakin wata irin mahaukaciyar ‘kara afusace Salman yami’ke had’ida buga cup d’in soban da’kasa yanufota sha’ko wuyanta yayi yasauke mata maruka har 3 yaturata tafad’i tabaya yasa ‘kafa yashureta cikin zafin rai yace

 

” ke mahaukaciyar inace dazakishigomin aguje sannan kinsan banason ‘kara koyaya take shine zaki saki wannan mahaukaciyar ‘karar a in danike to wallahi kinjama kanki wahala maza kitashi ki kwashemin wa’innan kayan abincin kifita dasu sannan kigyara gurin bayannan kije cikin wancan lambun na ‘karshen cikin masarautar nan kiyi noma zansa aduba idan baiyiba hmmm duka aykin 50 minutes shasha shar banza kawai ” daga haka yajuya yanufi cikin d’ayan parlour nashi

 

binshi Iman tayi da kallo tana ri’keda kunshinta d’ayan idonta nazubda hawaye sabida tsananin azabar marin dan kam yayi masifar shigarta tashi tayi cikin zuciyarta tace nagodema Allah tunda nayinasarar hanaka shan wannan mugun so’ban kome tazuba cikinshi oho cikin sauri tashigayin abinda yasata gawani irin mugun ciwon kai dayasameta yanzu sabida zafin marin nan

 

yana shiga yazauna kan ‘kayataccen cushion d’inshi babu jimawa dazamanshi wayar shi tashiga ruri yana kallonta amma baid’agaba har seda akakira sau 4 sannan yad’aga dagacan ‘bangaran akace

 

” karka dahutawa yarima nasamo bayani akan wannan yarinyar kamar yadda kace yar gidan Governor Gombe ce maici ayanzu itace yarshi guda d’aya tilo yanamasifar jida’ita itad’in ‘yar gatace sosai bata ta’ba neman wani abu tarasaba mahaifinta yana shirin aurar da ita ga d’an wanshi Hisham yanamatu’kar sonta itama haka tayi karatun law a Japan ayanzu itad’in cikakkiyar lawyer ce k….. ”

 

dakatar dashi Salman yayi yace ” aykinka yayi kyau ” kashe wayar yayi yasaki Murmushi yace ” ni Salman senasa wannan yarinyar taji kamar bata ta’ba samun gataba aduniya senasa tayi nadamar zuwanta duniya ”

 

mi’kewa yayi fita yayi daga part d’in shi yanufi part d’in kakanshi samu yayi harda mahaifinshi da kakarshi da matar mahaifinshi da’alama wani mihimmin abu suke tattaunawa akai zama Salman yayi batare daya kalli kowaba yace

 

” kaka lokacin yayi zanyi aure kamar yadda kakeso anemomin auran yar Governor garinnan wato Samihat ” yanagama fad’ar haka yami’ke yafita sosai kowa yayi farincikin hakan dan kam sunjima sunajiran wannan lokacin itako Momy wani irin ‘bakinciki taji dan bataso hakanba sabida akwa wani wani tukgu datake shiryawa Murmushi tsohon sarki yayi yace

 

” tare za’ahad’a dana d’an uwanshi dake India wato Bikiram yar ‘kanina Na’ima koyanaso ko bayaso dan bazanyarda ya auri wata ‘kabilaba idan and’aura auran akaimai matar can atahomin da Ilham itama ayimata aure anan ”

 

cikin mamaki Hajiya tabud’e baki zatayi magana yami’ke yace ” kinsan idannace to babu canji karma kifara ”

 

Tofa lalle Tsohon Sarki kad’ebo dazafi

 

yawan Comments yawan typing idan naji sanyi sanyi nafi ruwa kwanciya

Leave a Comment