Books Reviews & FAQs

Mugun Furuci Hausa Novel Complete

706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄

*WRITING BY AMEENATU SANI*

*_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_*

*JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d’an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d’an yazama lauyan mahaifin yarinyar_.

*SADAUKARWA ga my friend DARMA*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

 

PAGE 1_5

“Haba Habeeb in baka fadaman damuwar kaba waye zaka fadamawa?, kasandai ni mahaifinka ne duk duniya babu Wanda yakaini sanka amma ace Abu na damunka kaki sanar dani haba barrister”

daga kwancen da Habeeb yake ya dago ya kalli mahaifin nashi yace “Abba saidai katayani da addu’ah amma ni inaji ajikina mutuwa, zanyi Abba Santa shine zaiyi ajalina Dan Allah kayafeman”

da sauri Abba ya matso kusa da Habeeb din yace “my son Dan Allah ka fadaman wacece kake so, kuma kake cewa Santa zai kashe ka itadin yar gidan ubanwa ye agarinnan?”

Habeeb yace “Abba zuciyata ta kaini da nisa salma bata sona tace har abada ba zata soni ba!”
atsawace Abba yace “Habeeb wacece salma nace”
Habeeb yace “y’ar gidan Alhaji Lukuman Wanda kuke Neman kujerar chairman kaida shi”.

Hular kanshi Alhaji Muhammad yacire yayi fifita da ita kana yaja ajiyar zuciya yace “lallal zuciya batada kashi, Habeeb gaskiya zuciyarka batayi maka adalci ba da har taso diyar abokin karawata, kasani sare koda ace Yarinyar tana sanka Alhaji lukuman bazai taba yarda ka aureta ba, nidai amatsayina na mahaifinka inamai baka shawarar. kayi hakuri da ita kaci gaba da addu’ah Allah yabaka wadda tafita”

tashi yayi yafita Yaja mashi kofar,
Karo sukaci da Hajiya Fadeela dake kokarin shiga dakin Habeeb da sauri tace “Alhaji lafiya dai, ko jikin Habeeb din ne ya matsa?” Girgiza kai yayi yace “wato Hajiya akwai matsala babba”
tire din Lemon da ta dauko ta saki kasa ya tar watse ta buga salati tace “Alhaji Dan Allah karka ceman Habeeb ya mutu, innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!” zata kwasa da gudu zuwa dakin Habeeb din Alhaji Muhammad ya dakatar da ita yace “Hajiya bai mutu ba amma lalle yana dabda mutuwa Wanda nikuma bazanbar hakan ya faruba indai ta sanadiryar yarinyar nan zai mutu”.
Hajiya tace “wace yarinya kuma Alhaji?”
Alhaji Muhammad yace “wato Habeeb duk ciwon nan da yakeyi Ashe saboda yarinyar gidan Alhaji lukuman ne Santa yakeyi ita kuma bata sanshi”.

Hajiya ta zaro ido tace “Alhaji lukuman dai danasani Wanda kuke Neman kujerar chairman?”
Alhaji yace “itafa, kuma kinsan dai yanda Alhaji lukuman ya tsaneni bazai taba bari Habeeb ya auri y’arsa ba”.

Kan kujera Hajiya Fadeela ta zauna ta dafe kai tana addua akan Allah ya sausautama Dan nata.

Bayan kwana biyu Habeeb bayaci baya asha rarrashi na gidan duniya iyayenshi sunyi amma yaki yaci duk yabi ya ramai kullum cikin fadin sunan Salma yake.

Yanzu haka Alhaji Muhammad ya dawo daga office yashigo ya sami Hajiya Fadeela sai magiya takema Barrister Habeeb akan ya daure yaci kada ciwuka su tarar mashi.

Jin gina kai Alhaji Muhammad yayi ajikin kofa can ya dago yace “Habeeb nalura kana san yarinyar nan dayawa,shikenan bari naje na roki Alhaji lukuman da yataimaka yabaka auranta koda kuwa bata sanka ne, ai ita macece zata soka wata rana”
Da sauri Habeeb ya tashi daga kwancen da yake yace “Abba mutafi tare kodan naganta na roketa ta tausayaman ta soni”.
Kai Abba ya girgiza yace “Habeeb jikinka babu kwari kabari ninaje insha Allah komi zaitafi daidai”
Habeeb yace “Abba Dan Allah mutafi tare wlh ko ganin ta nayi nasan zansami sauki”.

Da sauri Hajiya Fadeela tace “Alhaji kuje tarai din wata kila a dace”

Haka kuwa suka tafi tare sai gidan Alhaji lukuman…

*_Yawan comment yawan typing, masoya wannan salonshi na da banne👌🏻_*

*Ameenatu Sani ce*
08065522770
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄

*WRITING BY AMEENATU SANI*

*_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_*

*JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d’an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d’an yazama lauyan mahaifin yarinyar_.

*SADAUKARWA ga my friend DARMA*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

 

PAGE 11_15

Wani kallan ukku saura kwata yayi mashi kana yace “kaga malam tashi kaficeman daga gida please” yafada yana nuna mashi kofa
Alhaji Muhammad yace “nifa zuminci nazo mu kulla tsakani na dakai, domin ‘Dana yaga y’ar ka yana so”.
Sai a wannan lokacin Salma ta d’ago ta kalli alhaji Muhammad da Habeeb, dayake tunda suka shigo bata dago kai ta kalli kowa ba.
Shiko Habeeb yama shagala da kallanta kacokam hankalinshi na garaita jiyake kamar ya dauketa daga gidan yamaidata gidansu da gashi sai ita yanuna mata tsantsar qaunar da yake mata.
Salma idanunta ta tsayar kan Habeeb nan take taji wata wutar tsanarshi taqara ruruwa a zuciyarta da sauri ta taso daga inda take tana nuna shi da yatsa tace “waikai mayan inane?,dady miyakawo wannan marar zuciyar gidammu?nace bana sanshi bana kaunar shi amma dayake wawa ne yaki ya fahimta.”
Wani shi’umun murmushi alhaji Lukuman yasaki tare ta murza gashin bakinshi haryaji sanyi aranshi daya kasance Salma batasan Habeeb.
Yace “kinga daughter yishirunki banni dasu”
kallan Alhaji Muhammad yayi da ya daskare a tsaye tun jin irin kalaman da Salma ke jifar d’anshi dasu yace”kai kana tunanin har akwai ranar da zan iya hada jini dakai? To inkana tunanin haka kama daina tun wuri Dan zaren ba irin yadin bane,Dan haka ja d’anka kubarman gida konasa afitarman daku”
Alhaji Muhammad yabuda baki zaiyi magana Salma ta qaraso gaban shi tace “dama Kaine mahaifin shi? Haba shiyasa Ashe naji nakara tsanar shi Dan haka kajama d’anka kunne koshi mayene ni nafi karfin shi wlh kuma bazantaba sanshi ba koda zai mut……saukar mari taji akumatunta Alhaji Muhammad ya kasheta da qwararan maruka har biyu ya d’aura da cewa ” kedin y’ar gold ce ko lu’ulu’u da Habeebu bazai rabu dake ba?,marar tarbiya kawai” qarar Habeeb yaji ya fadi qasa dafe da zuciyarshi yasa bai qarasa maganar shiba yayi kan Habeeb din ya tallaboshi yace “Habeebu bude idanunka Dan Allah Ashe dama yarinyar batada tarbiyya kaketa wahalar da rayuwar ka a kanta?” Wani tari Habeeb yayi sai gudajin jini yabiyo baya daqyar yabuda baki yace “Abba mutafi gida”.
Alhaji Lukuman da wani baqin ciki yarufe zuciyar sakamakon marin da akaima y’arsa yace “kaini zakazo har gida kadakarman y’a, aiko wlh sainayi shari’a dakai koda wa kake takama”.
Afusace Alhaji Muhammad yace “andaka din kaje kayi abunda zakayi” yanuna Salma da hannu yace “ke kuma wlh inbakiyi wasaba sainayi Ajalinki Dan akan ‘Da na babu abinda bazan iyaba”
kama Habeeb yayi yace “muje habeebu”
Fita sukayi daga parlorn Alhaji Lukuman sai bala’i yake yanakiran “Muhammad in baka kashe man Salma ba kaiba Dan sunna bane kuma wlh kajira sammaci akan Marin dakayima y’ata”

 

Afusace Alhaji Muhammad yace ma isah driver yaja motar zuwa hospital aiko batare da bata lokaci ba suka isa medical hospital cikin kankanin lokaci likitoci suka hau duba Habeeb ganin babban ‘Dan d’ansiya babu lafiya
Kusan awa daya kana likita yafito daga dakin yasamu Alhaji Muhammad dake tsaye sai safa da marwa yake awajan yace ” yella6e muje office mana” Alhaji Muhammad yace yajikin habeebun doctor?” Likita yace da “sauki ranka yadad’e muje office” kana yayi gaba Alhaji Muhammad yabi bayan shi

Zama sukayi su duka kana doctor Auwal ya cire farin gilas din dake makale ga idanunshi yamiqama Alhaji Muhammad hannu yace “barka ranka shidade” musabaha sukayi kana doctor Auwal yayi gyaran murya yace “wato Alhaji, Habeeb Sam yakasa cire damuwa a zuciyar shi bayan nasheda maku zuciyarshi tanadab da kamuwa da ciwo amma ankasa daukar mataki akai” Zazzafar iska Alhaji Muhammad ya huro kana ya muskuta yace “nidai doctor Dan Allah ayi abinda ake ganin yadace wajan ganin Habeeb yasamu lafiya”

To “insha Allahu Alhaji indai za abi dokokin da za’a gindaya masa , kana ayi kokarin ganin ansa dashi da abinda yake so insha Allah zai samu sauki” takarda yajawo yayi Dan rubutu akai kana yamikama Alhaji Muhammad yace “ga wa innan magungunan za’a samosu saiyayi amfani dasu”
Karba yayi ya duba kana ya zaro kudi yamiqa mashi yace “doctor ayi amfani dasu wajan siyan duk abinda ake bukata”
Karba yayi yayi godiya kana yace “da ruwan da akasa mashi yaqare zaku iya tafiya gida”
Shima Alhaji Muhammad godiya yayi kana yabaro office din jama’ar dake bisa barandar sai gaisheshi suke domin sunganeshi dakin da Habeeb yake yashiga, yananan kwance lokaci guda harya qara wata irin rama bacci yake ga qarin ruwan da akasa mashi sai tafiya yake ahankali, wayar shice tayi qara zarota yayi ganin Hajiya Fadeela ce ya daga abangaran Hajiya Fadeela yana dagawa tace “lafiya dai Alhaji inata kira baka daga ba?” Numfashi yaja kana yace “inafa lfy gamu nan hospital Habeeb babu lafiya” arikice Hajiya Fadeela tace wace asibiti Alhaji!?”
“Medical hospital” kett ta datse wayar ta nufo asibitin…..

*_tofa kunadai ji yanzu akafara wasan,innaga comment yanda nake so zancigaba, gamai bukatar document din YANAR GIZO complete saiya tuntubi number ta👇_*

*Ameenatu Sani ce👌*
08065522770
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄

*WRITING BY AMEENATU SANI*

*_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_*

*JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d’an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d’an yazama lauyan mahaifin yarinyar_.

*SADAUKARWA ga my friend DARMA*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

 

PAGE 26_30

Wata irin tafiya Isah driver keyi a saman titi kamar yana tsoran kwaltar Alhaji Muhammad dake bayan mota hakimce yana duba jarida yadago yace “wai Isah mike faruwane kakejan motar kamar baka so?”
Bai kulashi ba yaci gaba da tukinshi, cike da mamakin shirun da Isah yamashi yakara magana “wai Isah hala bakaji minace ba ne?” Daidai lokacin kuma motar su Salma tawuce ai da sauri Isah driver yace “wlh Alhaji kaina ke ciwo” parking yayi a gefen hanya yace “Dan Allah Alhaji kaja motar nan wlh bazan iya tukinba yanzu juuwa nake gani” dayake Alhaji Muhammad sauri yake batare da wata damuwa ba yafito ya zauna wajan driver shi kuma Isah driver yakoma wajan mai zaman banza Alhaji Muhammad yaja motar da karfi suka tafi
Isah driver kamar bashine ya lankabeba yace kanshi na ciwo ba sai baza idanu a titi yake can yaga sunkusa taddo motar su Salma aiko ya fakaici idanun Alhaji Muhammad ya taka giyar motar da karfi jikake kuuuuuuuuuuuuuuuu gammmmm daki motar su Salma cikin minti daya wani mummunan hadari ya afku a titin domin ko motar su Salma tayi wani raga raga mutane suka taru sai sallallami ake ana San fito Dana cikin motar.
Alhaji Muhammad salati ya dauka tunda motar ta fizgesu shiko Isah driver kira yake Alhaji zaka kashemu to adaidai wannan lokacin motar ta daki tasu Salma motar na tsayawa Alhaji Muhammad yafito yana salati innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un agigice yanufi wajan motar mutane sun taru dayawa aka Ciro Salma da driver ko kadan ba wanda ke motsi da sauri aka sasu motar Alhaji Muhammad akatafi asibiti mutane sai kira suke “masu kudi basuda imani jibafa Dan yana Dan siyasa irin gudun dayake a titi”zagin Alhaji Muhammad kawai ake mutane dayawa suka bi motar zuwa asibiti
Isah driver irin cikin irin yarude din nan kira yake “Alhaji saida nace karkayi kisa karkayi” Amma kakijin maganata, innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un muyau munbani!”
emergency aka shigar dasu cikin yan muntuna likitoci suka taru akansu dayake a kusa da junction abin yafaru akwai yan Sanda a wajan ba asha wahalar ansar suba
Alhaji Muhammad duk yarude tunda yake tuki tsautsayi baitafa fada mashi ba sai yau kira yake “Dan Allah doctor’s karku bari sumutu wlh bada gangan ba” mutane sai kira suke Alhaji da gangan fa kature su irin gudun da kakeyi kamar titin ka”.
Shikuwa Isah driver fakar idanun jama’ah yayi yabar wajan,wata number yakira ana dagawa yace “Alhaji mai afkuwa fa ta afku muna medical hospital yanzu haka ketttt” yakashe wayar yadawo cikin jama’ah.
Wajan minti goma saiga motocin Alhaji Lukuman sun shigo harabar asibitin cikin sauri ya sauko daga cikin motar yashige emergency din daidai da likita ya fito nan yadakatar da shi cikin hausar dabata ida bin harshenshiba yace “yi hakuri mana muje ana dubasu” kira yake “doctor kataimaka itace diyata kwal a duniya karta barni Dan Allah”
da ‘kyerdai aka fito dashi daga ciki doctor yace “Kaine mahaifin yarinyar?”
Alhaji Lukuman yace “eh wancan kuma driver ne”
Da sauri Alhaji Muhammad ya matso yace “doctor ya jikin nasu?” Ai wata irin juyowa Alhaji Lukuman yayi nan suka hada ido da Alhaji Muhammad aiko yakaimashi wata cabka a wuya yace “Ashe Kaine ka bankeman Salma? haba Muhammad minayi maka a rayuwa da kake Neman rayuwar Salma Ashe da gaske kake saikaga bayan ta haba Muhammad”.
shidai Alhaji Muhammad baiyi tunanin Salma ce ya bankeba sai da yaga Alhaji Lukuman.
nan jama’ah sukayo caaaa anaba Alhaji Lukuman hakuri da ‘kyardai yasaki Alhaji Muhammad dayaji matsa a hannun Alhaji Lukuman
Nan doctor yace “yanzu dai Ku biyoni office nayi maku bayanin abinda ke faruwa”
Office din doctor sukaje waje yanuna masu su zauna kamun yafara koro masu bayani “to Alhaji saifa hakuri”..nan take gaban Alhaji Muhammad yafadi da sauri yace “innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un don Allah doctor karka ceman sun mutum” shiko Alhaji Lukuman wani shu’umun murmushi yayi cike dajin dadin kudurunshi yakusa cika.
Zaman glass din shi doctor ya gyara ganin yanda Alhaji Muhammad ya rude kana yace “cool down Alhaji babufa Wanda ya mutu Duk kanninsu suna numfashi saidai sunji jiki harkarama namijin da sauki buguwa ce yayi akai sai glass daya yanke shi a fuska ita kuma macen gaskiya tabugu sosai domin hannunta na dama yakare glass ya shigarmata a fuska saikuma kananun ciwoka Amma gaskiya bata farfado ba haryanzu mundai yimata allure Wanda zasusa ko tafarka ta farka a cikin hayyacinta shi kuma namijin ya farfado maybe ma zuwa anjima a sallamaishi because jikin shi da sauki.
Wata sassanyar ajiyar zuciya Alhaji Muhammad yasaki yace “alhamdulillahi Allah nagodai maka da katsareni da yin kisan kai!”.
Shi kuwa Alhaji Lukuman kaidagani kasan baiwani ji dadin labarin ba yanayin fuskarshi ta nuna hakan Amma inkagani saikace duk cikin jimami ne.
Alhaji Lukuman yanuna Alhaji Muhammadda yatsa yace “kuma wlh inasan kasani jinin diyata bazai tafi abanza ba dama kace saikaga bayanta to shine yanzu kanemi ka aikata ko?, to Wlh sainayi shari’a dakai koda kuwa zanyi yawo tsirara, yo anfada maka siyasa haukace Dazaka nemi kasheman diya?”
Cikin kwantar da murya Alhaji Muhammad yace “kayi hakuri Alhaji Lukuman wlh wancanma Dana fada *MUGUN FURUCI* ne nayi wlh bada gangan nabigeta ba tsautsayi ne yafada kaina wlh am….”dakata malam Adana kalaman ka ko kasamu nafada gaban alkali dannan bazasuyi wani tasiri ba” Alhaji Lukuman ne yakatse Alhaji Muhammad da karfi…

_gaskiya nakusa daina typing din book din nan_

*Ameenatu Sani ce*
08065522770
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄

*WRITING BY AMEENATU SANI*

*_Wannan labarin kirkirarran labari ne banyarda a juyaman shiba ta kowace siga_*

*JIGWAN LABARIN*_:Akan mahaifin da yayi *MUGUN FURUCI* Akan budurwar d’an shi inda kuma tsautsayi ya fada mashi, shikuma d’an yazama lauyan mahaifin yarinyar_.

*SADAUKARWA ga my friend DARMA*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

 

PAGE 16_20

 

Batare da bata lokaci ba Hajiya Fadeela ta iso hospital din alokacin Habeeb yasamu bacci sakamakon allurar da akayi mashi,cikin kujerun da aka tanada Dan masu dubiya suka samu suka zauna.
Bangaran gidan Alhaji Lukuman kuwa koda barin Alhaji Muhammad gidan sai ya koma yanata zagayan parlorn tare da buga hannu Hajiya Mariya ta muskuta daga zaunan da take tace “wai Alhaji wannan abun da yafaru duk miyaka woshi harda yake maganar zaiyi ajalin Salma?
Nisawa Alhaji Lukuman yayi kana yace ” banni dashi wlh danshi ko zai mutu bazai taba auran ya taba koda kuwa ita Salma tana sanshi bare ma bata sanshi”.

*______________________________*

Napep ce tayi parking gaban wani Dan karamin gida madaidaici mai karamin get wata kyakkawar budurwa ce tafito daga ciki hannu ta rike da jikka sai rigar lauyoyi sallamar mai napep din tayi kana ta fara tafiya cike da natsuwa kauran get din ta tura tashiga gidan bayada hayaniyar komi acikin shi amma gidan yahadu daidai na masu rufin asiri.
A parlor tayi sallama wata kyakkawar matace zaune a kan kujera ta fa dada murmushi a fuskarta tace “oyoyo ga *MEENAL* barka da dawowa!”.
Itama MEENAL murmushi tasaki tace ” thanks you Ammi” zama tayi a kan kujera tace washhhhh Ammi nagaji dayawa wlh”
Ammi tace ai MEENAL sai kin daure tashi zakiyi ki watsa ruwa ga abinci can na tanadar maki yau abinda kikafi so na girka a gidan” baki MEENAL tawashe tace kai amma wlh naji dadi sosai Ammina Bari naje ciki mikewa tayi ta kwashi jikkarta da kayanta ta shige dakin ta

Da kallo Ammi tabita harta shige cikin Dan madaidaicin dakin nata,da shigarta kayanta ta hau cirewa kana ta shige toilet takai 20mint da shiga kana tafito tana tsane ruwan kanta da Dan karamin towel basilin da kwalli kawai ta shafa tasa wata doguwar Riga baka da pink din hula yar yayi parlorn ta shigo a lokacin Ammi harta kawomata Abincin a tsakiyar daki zamatayi kana ta soma cin danwaken tana yima Ammi santi gami da bata labari.

 

______________________________

Kwanan Habeeb 3 asibiti jiki yayi sauki alhmdlh lillahi domin har ansalla maishi yana dakin shi shida abokin shi Hisham suna fira hisham yace “nikau barrister nabaka shawara mana!” Habeeb yadan muskuta kana yace “Inajinka”,Hisham yace ” Naga duk ka daura damuwa akan lamarin nan daya faru barrister yakamata kasanya hakuri da dangana a lamarinnan Salma dai ba ita kadai bace mace a duniyar nan ga mata nan k…… “Dakata Hisham shawara kace zaka bani koko umarni ne?”
Hisham yace “aikaga matsalar ka Habeeb kai ba’ataba fada maka gaskiya imdai akan wannan yarinyar ne, Salma tafito ta nunama duniya bata sanka ubanta ma ya nuna baya sanka Amma ka like mata why Habeeb?”.
Tashima Habeeb yayi daga kwancen dayake yashige toilet yace ” saikuma kayi da Wanda kagani”
Kai kawai Hisham ya girgiza ya haye gadon yayi kwanciyar shi

Alhaji Lukuman ne zaune a office din shi murmushi kawai yake saki yana sauraron labarin da Alhaji Bala ke bashi, saida ya gama tsab kana Alhaji Lukuman yace “Bala ka ganni nan wlh komi nasama gaba a rayuwata sainaga nasa maishi barai wata kujerar chairman, taibur din gabanshi ya buga hadi da mikewa tsaye yace kalleni nan Alhaji Bala badai su Alhaji Nabadi da Alhaji Sabo sun yi saranda da Neman kujerar ba? Hmmmm Alhaji Muhammad shi mai kunnen kashi yace ya nanan akan ba kanshi ba nasan zama chairman ba? To albishirinka yau saura sati naya zabe?”
Alhaji Bala yace “3”
Alhaji Lukuman yayi murmushi hadida zagayowa yafara taku daya bayan daya a office din kana yace “nanda Lokacin saina sanya Alhaji Lukuman nadamar shigowa gonata saina nuna mashi ruwa ba a San kwando bane domin kuwa kila kamun lokacin har mala iku sunyi mashi tambayoyin kabari”.

Idanu Alhaji Bala ya zaro kana yace “kana nufin kashe shi zakasa ayi kenan?, tonidai banbaka goyon bayan aikata hakaba domin mutane dayawa sai anyi zarginka ka ka daganan kujerar da kake so zaka iya rasata Ku…..hannu yadaga mashi yace ” babu Wanda zansa ya kashe shi sai hukuma da kanta”. Alhaji bala yace “taya kenan kuma zata kashe shi ?”
Alhaji Lukuman yace “wannan tambayar yakamata ace tunfar ko kayiman amma katsaya zaka bataman lokaci,kawo kunanka kaji shirin danayi amma zan fada maka ne saboda nayarda dakai banida wani amini daya wuce kai shiyasa”
Kunnanshi Alhaji Bala yakayo,rada Alhaji Lukuman yayi mashi daga bisani suka sheke da dariya Alhaji bala yace “kai Amma wlh dole aji tsoranka Lukuman wato kai akan dukiya babu abinda bazaka iya aikatawa ba ko?”
Alhaji Lukuman yakoma mazauninshi yace “kware kuwa Bala ciki ko harda salwantar da rai……….

________________________________

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*

*Assalamu Alaikum*

*Ina yan’uwa masu sha’awar shiga kungiya ta online writer? To albishirinku😊 kakar tayanke sa’ka👌 Kuma damace agare Ku sabuwar kungiyarmu mai suna 💫💫NASARA WRITER’S ASSOCIATION💫💫 tana maraba da kowa da kowa duk mai sha awar shiga kungiyar kinada damar shiga bako sisin ki👌*

*Ina tsofaffin hannu da sababbin hannu wa inda basuda kungiya? Maza hanzarta domin kasan cewa daya daga cikin members din cikin ta💃💃 domin a dama dake*

*Ina masu San gwada basirar su wajen fara fadakar da Al’umma ta hanyar rubutun Hausa novel? Kungiyar mu tana maraba da ke yar uwa indai kina da sha awar zama online writer*

*Domin neman Karin bayani saiku tuntubi daya daga cikin number’s din nan*👇
08065522770
08104335144

*NASARA WRITER’S ASOCIATION*
💫💫 _*{{Nasara abin so ga kowa ,domin marubuta da cigaban rubutu al’kalaminmu y’ancinmu.}}*_💫💫

*Ameenatu Sani ce*
08065522770
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI*👄

*Writing by Ameenatu Sani*

PAGE 31_35

Bayan komi yadaidaita Alhaji Muhammad yabiya duk wani kudi da aka bukata na asibiti, haryanzu dai hankalin shi baiwani kwanta ba addu’ah kawai yake Allah yatashi kafadunsu lafiya, waya yabugama iyalanshi yasanar dasu halin da ake ciki Amma ba a sanar da Habeeb ba.
Shimadai Alhaji Lukuman yasanar da Hajiya Mariya aikuwa ba karamin dadi taji ba jin cewa Salma bata mutu.
Asibitin duk suka shiryo suka zo duba su.

Alhaji Lukuman ne zaune a motar shi shida Alhaji Bala dubanshi yayi a fusace yace “wlh yanzu haka Isah beyi aikin nan yanda yakamata ba mswwww yanzu yatsira kenan?”
Wata dariya Alhaji Bala yayi yace “wlh harka bani dariya Alhaji Lukuman, ainasa duk tantirancin ka ya zarce duk yanda nake zato Ashe baikai ba? Ainasa yanzu wata maganar ake ba wannan ba”.
Wani kallo Alhaji Lukuman yayi mashi yace “kaga Bala karka tunzurani wlh kasandai halina ko? To shikenan cigaba da dariyar kagani”.
Alhaji bala yace “aidole nayi dariya, waima jira kai baso kake Salma ta mutu ba kuma laifin ya rataya akan Alhaji Muhammad ba?, Kuma sai aka samu akasi yarinyar bata mutu ba?” Alhaji Lukuman yace “aikasan burina kenan duniya naga an wulakanta Madu an mashi kisan wulakanci kamun kuma yamutu zuciyar shi ta buga,aini wannan shine babban burina wlh”.
Wani murmushi Alhaji bala yayi yace “to kwantar da hankalin ka burinka zaicika yau basai gobe ba”. Alhaji Lukuman yace “tayaya kenan?”
Alhaji bala yace “ai ida kasheta za ayi kawai tunda kace haryanzu bata farfado ba kaga daganan kowa yasan shine yakasheta koba haka ba?”
Alhaji Lukuman yace good haka ne Amma tayaya zata mutu?”
Alhaji bala yace “ta hanyar yimata allurar guba doctor ko nurse kawai zaka cika da kudi kace sokake ta mutu wlh da gudu zasu aika ta bakaga duk arna bane kuma kasandai arna da kudi”.
Hannu ya miko mashi suka kashe yace “wlh aikin ka nakyau bala kai babban shegene kasan takan duniya wlh, ai kuwa haka za ayi yanzu bari naje komi kenan zamuyi waya”
“Ok normal saina Jika”
kana ya sauka daga motar

Baiyuce ko inaba sai gida
Akan daya daga cikin kujerun parlorn ya zauna sai zuba murmushi yake yace “Madu (Muhammad) kabani indai da sharrina ne yanzu wasan yafara wlh sainaga ankashe ka har lahira kana hankalina zai kwanta”
Kiran number Hajiya Mariya yayi dayake tanacen asibiti tana d’agawa yace yi sauri dawo gida ina jiranki”
yanke wayar yayi ya cigaba da sambatun shi

Mintuna kadan saiga motoci sunyo mata rakiya tana shigowa parlorn tace “lafiya kuma?”

Wani murmushin yakara yi yace “zauna mana tana zama ya fara fada mata duk yanda sukayi da Alhaji bala saida ya ida fada mata kana ta zubamashi wata uwar harara tace “Amma wlh daga kai har bala bakuda imani ainasa tunda har Salma ta tsallake tarkon Ku nasa tatsira, to bari kaji wlh ko duniya za’abani bazan taba yarda a kashe Salma inaji ina gani ba, ai wannan maganar banza ce wlh karama Ku canza shawara”.
Wani naushi ya kaima kujera yace “waini miyasa banida sirrine? Miyasa komi zanyi saina fada maki? Da ace ban sanar dake ba aida baki isa kifada man magana ba to bari kiji wlh yanda na tsara shirin nan babu ubanda ya isa ya dakatar dani kuma yau basai gobe ba Salma zata mutu”.
Hajiya Mariya dataga yanda yake tada jijiyoyin wuya kuma tasan tabbas zai aikata komi yace saita Dan sabko tace “naji Salma zata mutu Alhaji Amma ba mutuwa ta har abada ba zadai ta mutu a idon duniya Amma mu agaremu bata mutu ba”.
“Kamar ya” cewar Alhaji Lukuman “kamar dai yanda kaji nafada inasan Salma bazan juri rashin ta ba Amma yau dinnan zamu fitar da ita kasar waje sai muhada baki da doctor yasamo wata gawa mai irin jikin Salma sai a rufeta kar mubari kowa ya bude gawar muce Salma ce ta mutu kaga ko yansanda zasuyi bincike basusan Salma ba saidai karmu bari Wanda yasanta yaga gawar ai shikenan ko?”

Wani banzan kallo yayi mata yace “Amma wlh Mariya bakida hankali taya hakan zata faru? ke wannan shawarar taki batayi ba ki canzata tun wuri”.
Nan dai Hajiya Mariya taita kawo mashi misalai harya gamsu da bayabinta yace “to bari naje su hadu da doctor
Din”.
Bayan yaga doctor sunyi magana nan danan doctor ya amince da bukatar Alhaji Lukuman Amma saida ya tura mashi makudan kudi ta account kana yace yanzu cikin dare zasu canza ita salmar Amma lalle yanzu su naimi jirgin da zai tashi zuwa anjima tana fitowa su wuce haka Alhaji Lukuman yabi shawarar doctor yaje ya kammala komi na tafiyar Salma nan da d’ayan dare jirgin zai tashi.

6:00am
“Innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un wayyo Allah ni Mariya Salma Dan Allah kitashi wlh bazan iya rayuwa babu keba wayyo Allah na!” Doctor kira yake “kiyi hakuri Hajiya kiyi hakuri”

Alhaji Muhammad yana shirin zuwa asibiti sai yaji ana buga kofa Hajiya Fadeela tace “daure Alhaji kayi break din bara naduba kowaye” kofar ta bude security din gidan tagani tace “lfy dai office?”
Cikin rawar murya yace “Hajiya babu Lfy ga police’s can bakin get sun tare ko ina yanzu haka gidannan zagaye yake da police’s kowa kaga fuskar shi kasan babu imani Hajiya kum….bai ida maganar ba saiga wasu police din su shigo wajen Hajiya Fadeela tace “yallabe Lfy ko” daya daga cikin police din yace “matsa babu hanya” suka shige ciki Alhaji Muhammad yadago yagansu zaiyi magana suka ce “yu a onda aress” Alhaji Muhammad ya zaro ido yace “Lfy!?”
“Alhaji anbamu umarni damuzo mutafi dakai In munje can kaji mikayi” Alhaji Muhammad yace “Toni miye hadina da police? Amma muje”
keyarshi suka tusa hajiya Fadeela tace “innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un miyayi maku Dan Allah?” Alhaji Muhammad yace “Hajiya nima nan kaina bansan minayi ba Amma in munje naji ai ciki da gaskiya wuka bata hudashi”
har ciki mota suka shiga kana sukabar unguwar da jiniyi…….

_Turkashi_

*Ameenatu Sani ce*👌
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄*

*Writing by Ameenatu Sani*

*NASARA WRITER’S ASSOCIATION*

36_40

Alhaji Lukuman ne gaban gawar Salma sai zabga kuka yake da sambatu kamar wani zautacce likitoci da yan sada sai hakuri suke bashi yayinda Hajiya Mariya take a wani gadon kwance wai suma tayi bayan angama duk abinda za ayi aka fito da gawa zuwa gida domin ayi mata sallah akaita makwancinta da kyar suka fito suka shiga mota sukabar harabar asibitin.
Ana fita da Alhaji Muhammad sai Hajiya Fadeela tai sauri ta dauko wayar ta kiran number Habeeb tashiga yi Amma Sam bata shiga wayar abokin shi Hisham takira yana dagawa tace “Hisham kuna tare da Habeeb?”
Hisham yace “a’a mummy bama tare yanzu dai ya fita”.
Hajiya Fadeela tace Dan Allah Hisham kace mashi komi yake yi yau ya baro Kaduna yazu gida”
“Lafiya dai mummy? Cewar Hisham?”.
“Hisham babu lafiya” kettt takashe wayar itama tabi bayan su

________________________________________

“MEENAL wai yau bazaki fita bane?” “Ammi wlh yau Sam banajin dadi kuma yau munada wata shari’a banajin fitane kawai”.
Ammi tace “lalle agajiye kike MEENAL yanda nasanki baki wasa da aiki to ‘kara ki huta Amma kitashi kiyi break saiki koma baccin”
“to shikenan Ammi”.
Fitowa daga cikin bargon tayi tashige toilet wanka tayi kana tayi brush ta fito shiryawa tayi kana ta samu Ammi a parlor tana kallo tace “Ammi kallo kike?”
“Eh ai kinsan shike debeman kewa da kin tafi aiki” murmushi MEENAL tayi tawuce tana cewa “aiko Ammi yakamata asamo mai tayaki fira because TV tana iya gundurar ki”
Kitchen tashiga ta dauko break din ta zauna kusa da Ammi suna kallo.
Tace “gaskiya Ammi yakama a nemo mai aiki a gidannan kinga ta tayaki fira ko yakika gani?”
Ammi tayi murmushi tace “aa yar albarka nikad’e ai zan iya zama kuma kinga y’ay’an y’an uwa suna zuwa duk suna debe Mani kewa”.
“Allah Ammi banaso kina kad’eci shiyasa nace haka”
“a,a MEENAL to lokacin da kikayi aure fa? Aikin gani dole na saba”.
Fuska MEENAL tarufe tace kai Ammi”.
Ammi tace “waike MEENAL miyasa duk lokacin da zanyi maki zancen aure sai kin nuna jin kunya Da alamun baki so? Kuma ni gidannan bantaba ganin inda yau wani saurayi yazo wajen kiba mike faruwa? ya kamata nasani domin yanzu kinkai lokacin da za ace kinyi aure Amma naga Sam baki da ra ayin hakan”
MEENAL ta aje cokalin hannunta takalli Ammi tace “wlh Ammi Sam banasan nayi aure nabarki kita wahala ke daya saidai in tare zamu”.
Baki Ammi tarike tace a ina akataba haka MEENAL?”
Baki ta tura gaba tace “abar maganar Dan Allah Ammi,bari nabaki labarin sari’ar da mukayi jiya”…..

Alhaji Muhammad zaune a gaban dpo
” Dpo yace “Alhaji Muhammad fatan kasan laifin mi kayi aka kawoka nan?”
Alhaji Muhammad yace “ranka ya Dade ni bansan mi nayi ba”.
Dpo yace “yazaka rainama hukuma wayau kace bakasan mikayi ba, to kisan kai kayi”
Zaro idanu Alhaji Muhammad yayi yace “kisankai kuma wana kashe”.
Dpo yace “yanzu dai mu umarni akabamu mu kamoka yanzu kotu za amika ka inkaje cen saikayi bayani”
“Innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un kisan kai kuma ni? haba yallabe ni din nayi kisa?”
Dpo yace “kai sajan” wani Dan Sanda ya shigo Dpo yace “Ku shiga dashi ciki ku rufe”
“Yes sir” kana ya cema Alhaji Muhammad “tashi muje”.

Ankammala hada gawa har an wuce da ita domin sadata da makwancinta
Yayin da mata sai rike Hajiya Mariya ake ana bata hakuri nan ko da tashiga cikin hijabi dariya take tayanda shirunsu ke tafiya daidai.

A gaggauce Habeeb ya dawo tunda ya duro garin yaji mike faruwa hankali tashe yanufa gida Amma mai gadi yamashi bayanin “ai babu kowa gidan anwuce da Alhaji police station Hajiya ma kila can tanufa”.aiko kiran Hajiya yayi ya tambayeta “wace station ce suke” nan tafada mashi ya wuce can shida Hisham….

*Ameenatu Sani ce👌*
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄*

*WRITTEN BY AMEENATU SANI*

*NASARA WRITER’S ASSOCIATION*

41_45

Da isarsu station din yaga Hajiya rakube a bango ta zabga uban tagumi hawaye sai zubar mata a fuska suke da sauri ya karasa gateta yace “mommy miyasa kike kuka ina Daddyn?” Hajiya bata iya cewa komiba illah hawaye da ke zarya akan fuskar ta Hisham ne yace “Habeeb Mommy bazata iya magana ba yakamata muga dpo” aikuwa haka akayi suka nemi aimasu iso wajan dpo batare da bata lokaci ba suka shiga bayan sun gaisa Habeeb yace “ranka yadade Sunana barrister Habeeb Muhammad *HM*”.
Dpo yace “ai nagane ka” Habeeb yace Ok to nazone akan maganar mahaifina bana garin ne akakirani miyayi yallabe?” Wani murmushin takaici dpo yayi kana yace “gobe case din zaikoma kotu kaji komi ya aikata” Habeeb yace “nidai nasan mahaifina bazai aikata wani mugun abuba yallabe adai sake bincike kamun akai kotu” dpo yace “ai laifin nashi a bayyane yake wannan ma basai an wahalar da shari’ah ba za ayanke mashi kukunci daidai da abinda ya aikata na kisanka”
murmushi Habeeb yayi yace “badai mahaifina ba gaskiya”
kafad’a dpo ya daga yace “Ok ainaga kai babban lauyane maizaman kanshi kuma ka kware wajan zakulo mai gaskiya da marar gaskiya nasan tabbas zaga gano gaskiya don haka zaka iya fara bincike wajan gano gaskiya kamun alkali ya bukaci hakan” kai Habeeb ya jinjina yace “insha Allahu yanzu don Allah ina bukatar ganin shi” dpo yace “gaskiya barrister kayi hakuri bazaka ganshiba a yanzu” murmushin takaici yayi kana yace “to shikenan”.

Bayan sun fito ne ya lallashi Hajiya akan sukoma gida komi zaizo da sauki insha Allah haka suka koma gida cike da jimamin abun..

Alhaji Lukuman kuwa bayan an rufo gawar da akakira da sunan Salma yanufo gida jama’ah sai gaisuwa suke mashi shikuwa sai share hawanyen munafurci yake yabukaci ganin dpo akan adaga kai karar kotu harsai an gama zaman gaisuwa amma acigaba da tsare shi.

Bayan kwana biyu da mutuwar, Alhaji Lukuman suka haduda Alhaji bala Alhaji Lukuman yace “to Bala kagadai shirina yanata tafiya daidai yanda na tsara babu matsalar da aka samu ko?”
Alhaji bala yace “hakane Lukuman nikaina ina mamakin yanda shirin ke tafiya daidai” wani murmushi yayi kana yace “to yanzuma wani shirin zan sake kullawa kuma nasan zaitafi yanda nake so”
Alhaji bala yace “to wane kuma shiri zakayi bayan gashi burinka zai cika nasan ganin bayan Alhaji Muhammad?”
Wani murmushin Alhaji Lukuman yakara yi yace “ai bazaka gane bane bala nifa wlh har abada bazan so ace Ahalin Alhaji Muhammad sunyi farin ciki ba, wai ko kanada labarin Alhaji Muhammad dan uwa nane ubammu daya dashi?”
Idanu Alhaji bala yazaro yace “Dan uwanka kuma? Taya yazama Dan uwanka?”
Alhaji Lukuman yace “manta da wannan, ni yanzu burina shine bayan an kashe Alhaji Muhammad sai kuma duniya ta zagi danshi Habeeb uwarsa ta tsine mashi kana daga baya itama uwar nasan yanda zanyi da ita”
Alhaji bala yace “taya kuma hakan zata faru?”
Alhaji Lukuman yace “ta hanyar yima Habeeb asiri a daran yau yazama shine lauyana kuma yayi tsaye tsayin daka harsai yaga nayi nasara alkali ya yankema Muhammad hukuncin kisa,
Kaga duniya zata zageshi akan yana lauya amma yagaza kare mahaifinshi uwar shi zata tsine mashi ta dalilin haka kila intaji za’a kashe Muhammad zuciyar ta ta buga nan take ta mutu kagani nayi nasara shikenan burina na shekara da shekaru yacika”.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°′°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Shiri take a gagauce tomin ta makara da hanzari tafito daga dakin ta tashiga dakin Ammi zaune ta isketa tana lazimi jiranta tayi hartakai karshe kana tace “Ammi Nina shirya zan wuce” Ammi ta dubeta tace “to ga break din ki can ki dauko ki karya kamun ki tafi”
“Aa Ammi wlh banada isasshen time lokaci na kurewa yanzu barrister umar yakirani ni ake jira zamu shiga meeting karfe shabiyu munada wata shari’ah kuma kinga Tara takusa”
Ammi tace “waike MEENAL miyasa bakisan karyawa ne inzaki fita? Tun dazufa nake tashinki daga bacci Amma kinki tashi dama nasan karshen ta bazaki karyaba zaki fita”
mikewa tayi tace “ayi hakuri Ammi bari natafi dashi can naci”
Ammi tace “to hakan yayi” tana kokarin mikewa MEENAL ta dakatar da ita tace “haba Ammi sha zaman ki bari na zuba”
Da sauri ta zuba abincin a kula tayima Ammi sallama tafita
abakin titi take tsaye tana tsaida mai napep bayan ya tsaya tafada mashi inda zata tashiga suka wuce
Da saukarta kawarta jiddah ta iso tace “kai Amma wlh MEENAL nawarki tayi yawa tunfa dazu nake tsaye wajannan ina jiranki Amma sai ceman kike gaki a hanya” dariya MEENAL tayi tace “sorry besty wlh Ammi ce tamatsa sainaci abinci bamma Ciba kinganshinan nazubo” karbar kular tayi tace “kai Amma Allah yasakama Ammi da alkhairi wlh kinsan kuwa yunwa nakeji tunda matsa maki akayi kawonan ninaci” kular MEENAL ta sakarmata tace “aidama ke a cici ce wlh saikita kaya, dazu Brs.Umar yakirani wai ni ake jira naga kuma kamar ba ashiga ba ko?”
Jidda tace “to aidai kinsan halin umar burinshi yazo ya ga kema kin iso shiyasa Amma yanzu za’a shiga” kai kawai MEENAL ta girgiza sukaci gaba da tafiya
Karfe shadaya suka fito daga meeting din suna zaune Jidda nacin abinci MEENAL ko waya take latsawa umar na gefansu sai surutu yakema MEENAL tana dariya sama sama can umar yace “wai madam ya maganar mu don Allah? haryanzu kinki bani amsa ta” MEENAL tace “ayya Barrister don Allah abar maganar nan kagadai yanzu akwai aiki gabana”
Barrister umar yace “to shikenan madam kardai kimanta Ina sonki! koba yanzuba ina jiran amsarki please” Jidda tace “lalle Barrister kaima sai wahalar da kanka kake akan wannan y’ar ba’kar” MEENAL tace “eh aba’kar kuma ya nace ko?” dariya sukayi su duka daidai da lokacin Jidda tagama cin abincin kuka tashi domin gabatar da shari’a

 

*_Ameenatu Sani ce👌_*
[4/18, 5:10 PM] +234 706 650 5625: *👄MUGUN FURUCI👄*

*Writing by Ameenatu Sani*

51_55

Da sauri ya karasa gareshi jijjigashi ya hauyi yana kiran “Habeeb! Habeeb!!” Amma Sam Habeeb baya motsi da kyar ya fito dashi daga toilet din kan gado ya shimfidar dashi yaciga ba da jijjigashi amma har yanzu shiru da sauri Hisham ya dauko ruwa masu sanyi a firiji ya shafama Habeeb a fuska wani dogon numfashi yaja kana ya sauke ajiyar zuciya amma baibude idanshi ba Hisham yace “Habeeb bude idonka mana” zuciya Habeeb ya dafe murya na rawa yace “ba..ni…..maaa…gaaani na”. Hisham yace “to, sannu Habeeb bari naje nakawo maka ko tea ne nasan bakaci komi ba tun jiya”. Baijira cewar saba ya bar dakin kasancewar ansan Hisham sosai a gidan shiyasa kai tsaye yanufi parlor mai aiki ya gani tana goge goge nan yamata magana “tayi sauri ta hadoma shi tea mai kauri” da “toh” ta amsa kana ta shige Kitchen mintuna Kad’an ta kawo tea din Hisham ya karba, kwance ya samaishi ya dafe kai da kyar Hisham ya lallabashi yayi kurba ukku da tea din kana ya ballar masa maganin da yake sha dayake akwai maisa bacci cikin kankanin lokaci ya kama bacci.
Bargo Hisham ya ja ya rufeshi da shi kana yabar dakin parlor ya fito yaga mai aiki yace “tayi mashi magana da Hajiya”, bayan mintuna Kad’an saigata tana saukowa Kaida ganinta kasan tasha kuka
zama tayi akan kujera Hisham yace “ina kwana Hajiya?”
Hajiya tace “lafiya lau”
Hisham ya gyara zama yace “am Hajiya Dan Allah kiyi hakuri akan maganar da Habeeb yayi, wlh baida lafiya wannan abun daya faru duk ya rudar dashi yarasa nutsuwar shi,yanzu haka na ba shi magani harya samu bacci insha Allah daya farka zaidawo normal”
Hajiya tadanyi murmushi tace “bakomi Hisham Allah yabasa lafiya”
“Amin Hajiya” cewar Hisham kana ya kara da “fadin Hajiya nazone akan maganar daddy to da muyi maganar da Habeeb amma nasamu baida lafiya yanzu ya kike ganin za mu fara bullo da maganar?”
Hajiya ta fashe da kuka tace “wlh Hisham Alhaji bai kashe wannan yarinya ba kawai ajalinta ne ya biyo ta hannunshi” nan tacigaba da kuka kamar ranta zaifita
Hisham yace “kiyi hakuri Dan Allah Hajiya insha Allah babu abinda zai faru da daddy, yanzu bari na je station din naji ina akatsaya inma takama naje har gidan Alhaji Lukuman din sai naje”
Hajiya tace “to Hisham an godai Allah yasaka da alkhari”
Hisham yace “amin Hajiya ai duk yima Kaine”
Nan yasa kai ya bar gidan..

Dariya suketa shekawa a mota Alhaji bala yace “gaskiya Lukuman kai din bakaramin shu’umi bane hahahahaha” Alhaji Lukuman murza gashin bakinshi yayi yace “waikai Bala haryanzu baka ida Sani naba ko? To bari kaji da wannan hannun nawa na kashe mahaifimmu Dan kawai na mallaki dukiyar sa kaga kuwa ai babu Wanda bazan iya kashewa ba, Muhammad ne kawai bazan iya kashe shi da hannu naba nafiso a yimashi kisan wulakanci a gaban idanu na”
Alhaji bala yace “wai to Alhaji Lukuman jiya kace man shi Muhammad din mahaifinku daya to taya hakan ta faru?”
Kamun Alhaji Lukuman yayi magana wayarsa tafara ringing dagawa yayi ya amsa wayar kana bayan ya gama yace “Bala taka mota muje”…

Leave a Comment