Books Reviews & FAQs

Mis Wasmiti Hausa Novel Complete

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

WHATSAPP NO:
+2347039625239
[4/9, 1:47 PM] ‪+234 909 785 3276‬: 🕌🕋🐄🐄🐄🐄
📝💫Bismillahirahamanirahim***🌳🐄
Mi’wasmiti. Page 1⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
🕌🐄🐄🐄🐄🐄

Tafiya take cikin sauri sauri da Dan sassarfa tana tafe tana Dan mita da holo irin Na tsofaffi da sauri Na dan qarisa gunta Na Dan kalleta a nitse a take Na gano tsohur ba fillatace cikin hikima Na gaidata da yaren fillanci cikin Dan sakin fuska ta amsamin ba tare da ta tsayaba a hankali Na bita gami da cemata kakata ina zakije haka da sanyin safiya gashi sai sauri kike kamar wacce jirgi ke shirin tashi ya barta ..
Ta Dan juyo ta kalleni tare da ci gaba da tafiyarta tana mai cemin ba doleba nai sauri ai ko faduwa zanyi Na fasa bakina Na zubda haqaran robar sai Na hamzarta .ai shi yafi jirgi shi sama da jirgi yake in ya shirya baya jiran kowa kuma shi jirgi ai yana bada lkci. toshi bai bada lkci shi tamkar hadari yake inya fito tofa ba jira kuma shi kamar guguwane sarkin birkita taro….
Cikin mmk nace keko kakata waye wannan ? kuma a ina yake? Cikin surutunta da mita tace gidan kamannin zani zanyi aikene Dan yau zasu gembu cikin mambila ..da Dan sauri na bita nace gidan kamanni kuma ?su haka sunan gidan yake ? Wannan wacce irin kamace dasu ? Na jera mata tabbayoyin aiko ta fara bani lbri tiryan tiryan🐄🐄🐄

Zuriyar Alhj Muhammad babayo Wanda akafi sani da Mlm babayo kuma sarkin shanu Dan asalin jihar tarabane can cikin mambila. Matansa 2 yayansa 5 maza 4 mace 1 uwar gidan innayi tana da Yaya 3 maza 2 sai mece 1 babban dansu barrister Muhammad Bello Muhammad sai mai binshi doctor Aliyu Muhammad sai qanwarsu Aysha.Muhammad

Sai amariyar yayanta 2 duk maza Amadu shine babban danta sai hamisu
Duk da kasan cewar mlm babayo ba fillatanine baiyi qasa a guiwaba wajen ilmantar da yayansa ilimin zamaniba sunyi karatu mai zurfi

Barrister M.B.M Wanda suke kira baba bello yana da matarsa daya Nenne Aihuwarta 12 Amman yanxu haka yayanta 3 ne kadai sabida aihuwar wabi take Sadiya itace babba bayan aihuwar sadiya sai da tayi aihuwa 5 duk suna komawa sai Na 7 in ta sami da namiji mai suna Ahmad tokoran qaninshi Amadu bayan Ahmad ta kuma aihuwa 4 duk suna rasuwa sai ana 12 ta samu Allah ya barmata shi sunanshi Rabi,u…

Sai doctor Aliyu Wanda suke kira Abba da matarsa Ummi yayansu 4 Yusuf shine babban dansu sai Abubakar da Usman sai Autarta Aysha .

Sai Goggo Aysha wacce take Aure a Yola tana auren doctor Umar babban Abokin yayanta doctur Aliyu Abba kenan yayanta 3 Adam sai hydar sai Maryam

Sai Amadu Wanda suke kira baba matarsa 1 yayansu 2 Abdul sai Amira.

Sai baba Hamisu matarsa 1 dansa 1 Sadiq .

Kamanni Family zuriyace da ta samu wadata da rahamar ubangiji Allah ya musu baiwa tako ina ga ilimi ga kyau ga arziqi ga zaman lfy da qaunar juna da tsantsar shaquwa da tausayawa

Su yayan inna basu karatu sosaiba sai suka Koma makarantar Dan gote baba bello da Abba su suka budemusu wani katafaren filin seye da sayarwa mai suna kamanni family kuma su Amadu da Hamisu suna zaunnene da iyayensu acikin garin mambilan yayinda
bb bello da Abba suke cikin taraba da zugar iyalensu sai dai alqawarinsu ne duk weekend suke zuwa gaida iyayensu da qannensu

Years en Adam da Yusuf da Ahmad dai daine Sa.annine su randa akayi 40 en Adam a ranan aka aifi Yusuf ran sunan Yusuf kuma aka aifi Ahmad rayuwarsu Ahmad Abin Sha.awane da burgewa rayuwace mai tsafta sun kasance masu qaunar juna ga wani irin kamanni da suke fiye da tunanin mai karatu mutane da dama sukan dauka yan 3 ne sabida zallan kama fararene tas irin farinnan mai daukar hankali gasu kyawawa tamkar larabawa ga tsantsar cikar haiba gashin kansu tamkar indiyawa kamanin su kuma ya samo asaline sabida dukkansu da iyayensu suke kama sukuma iyayen kamane Na haiqan a tsakaninsu

Sabanin abinda ke sakaninsu sai hali haqiqa halinsu ya banbanta dana juna kamar yadda wasu al.amura suka banbanta a tsakanin su Adam irin mutanenane da zan iya cemusu fadi garas mgn dai da zaran tazo ransu toh fa zata fito yana da yawan surutu da abin dry gashi da raha

Ahmad bawan Allah damo sarkin haquri haka Allah yayishi shi mutumne mai haquri da tawakkali ga sauqin kai ga iya zama da jama,a gashi da fara.a ko yaushe fuskarsa Na dauke da murmushi Sam bai iya fushiba shi….

Ayagi sarkin fada mishkili kafi mahaukaci ban haushi muqu baya dry sai Abu ya baci Yusuf yadda wasu Al,amura Na rayuwarsa yasabawa sauran jama,a hakama halinshi shi Yusuf irin jarirenane da ake aifarsu da kaciya a jikinsu shi da kaciyarsa ya fito duniya tun tashinshi bai da yawan mgn haka kuma baison yawan surutu gashi da ra.ayin riqau ba,a juyashi yana da zuciya ga iya horon yara baison shishshigi da Sa ido ko Kadan madafacine sosai zakayi zaman shekara dashi bazakaga dryarsa ba haka kuma ko shekara 4 zakayi dashi da wuya kaga qwoyar idonshi kuma kab wanan halin bb bello ya gado yayinda shikuma Ahmad ya dauki haqurin Abba danshi Abba tamkar ba mai suna Aliyu bane. Amman duk da fadan Yusuf bayayi da su Adam sun shagu shaguwar da ba adadi tare suka tashi gida 1 daki 1 don dole mahaifin Adam ya haqura ya barshi a taraba tare sukayi marantarsu tun daga primary har xuwa university innada sukayi digiru ensu Na firko a qasar India Yusuf da Adam sun karanci medicine shi kuma Ahmad Abba ya sashi ya karanci business Amnan shi Yusuf yanxu haka yana karatu a jami.atul Madina enda yake qara karantar likitanci a musulunci Sai in sun Dan samu Hutu yake zuwa kamar yanzu tun cikin Ramadan yazo duk ya buwayi qannenshi mu samman Aysha da basa hada inuwa daya tamkar wuta da audiga haka kuma su Usman da Abdul d Rabi,u suma duk ya fara gungurarsu Amira ko dama cewa take suna zuwa bikin sallah bazata dawoba sai ya Koma Dan ita Amira a gaban bb bello take haqiqa kowa najin takaicin yadda Yusuf da Aysha basa shiri qiyeyyace sosai Yusuf yake mata wasu lukutan ji yake kamar ya karyata Ahmad kuma wata soyeyyace mai qarfin gske ke tsakaninsu hakama Adam da Amira

Kumuje zuwa dai Ku biyoni a hankali lbr Na can gaba 🐄🐄🐄

By garkuwan fulani
[4/9, 1:47 PM] ‪+234 909 785 3276‬: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
MI,WASMITI…..page 2⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Taci gaba da bani lbr su Usman da Rabi,u da Abdul ma Sa,annine hakama Aysha da Amira da Maryam …
Yusuf ya kasance mai zuciya tun yana dan yaronshi sanadin zuciyarshi yanzu haka yana da matsalar ciwon zuciya💔 tun suna primary school yana dan shekara 6 makarantar su da aka shigar dasu yinifom en makarnar dan gajeren wondone da yar riga Amman tunda aka dinka musu kayan Yusuf yake ta faman cin rai shi ala tilas bazai Sa gajeren wondo ba dan shi ya kasance mai kunyar bayyana jikinshi tako wanne bangare ne ba yadda ba,ayi da shiba yaqi Abba yace sai a shigar dashi wata makaratar nanma yaqi yace shi dai inda su Ahmad suke nan zaije dole akayiwa shugaban makarantar bayani da yake abokin bb bello basu samu matsala ba
Yusuf ya kasance mai kwarjini agun abokan kara tunshi kowa so yake yarabesa ko dan ilimin da Allah ya bashi

Wata rana a makarantar yayi fada da wani yaro Mujaheed aiko suka rinqa gudu dan ya samu ya yarama Amman ya kasa kamo Mujaheed ga mlmansu da suka shiga tsakaninsu shi kuma yace dole sai ya rama da aka hanashi ramawarne ya rinqa kuka cikin xuciya da takaici kuka yake har numfashinshi Na yankewa basuyi auneba ya fadi sumemme

Kai tsaye gida suka kawoshi Abba ya dugufa coto rayuwarsa da qyar aka samu ya farfado yana tasowa da kuka ya farka yana wlh ni sai Na rama bazan yardaba abi dai yaci tura dole aka nemo yaro yazo da iyayenshi yana zuwa Yusuf sai cewa yayi yazo gabansa ya duqa zai rama Abban mujaheed ya tura masa shi yana jeka ya rama aiko ya samu tsakiyar bayan shi ya rinqa dakamar duka gami da cemai wlh in baka ban haquriba bazan bar kaba yaro ya juya ya bashi haquri
To daga nan suka zama abokai

Ta dan zagaita surutun nata ta kalleni anitse tace to abinda yasa kikaga ina saurin Yusuf yazo nasan zai azalzalamusu su tafi ba tare da nakai aikenaba.””””
Na danyi dariya a raina nace hajia Zubaida ikon rabbi daga tabbaya daya taban bayanin da ya zarce zatona
Tacemin jikata ban sankiba gashi har mun saba daga ina kike haka nadan kalleta a nitse nace ni bakuwace daga jihar Adamawa nake sunana Aysha Ali Garkuwan Fulani kuma dama nazone gun Fulani yan uwana saiko nai Sa,ar cin karo da zuriyar sarkin shanu nima zasu barni Na kaimishi gaisuwar sallah ko? a madadin babana
tace sosaima kuwa ai suna son baki

⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Babban gidane Na gani Na fada acikin babban birnin taraba gate en gidan ma kawai abin kallone ga ma aikata tako ina jamin sarone masu tsaron barrister M B M cikin gidan muka nufa kai tsaye wani babban parlor mai kama da dakin taro cike yake da mutanen gidan cikin hikima Na zuba musu ido 👀 dan naga wani abin al,ajabi kamace ta gsky a fuskokinsu gaba dayansu shiga iri daya sukayi galilace mai kyau da tsada bb bello da Abba suna zaune kan kujera daya tamkar tagwaye sai dai Abba ya dan fishi tsawo sai Nenne da Ummi suma suna zaune wuri daya cikin shiga ta alfarma da ka gansu kaga jin dadi da kwanciyar hankili haqiqa Nenne macece mai mutunci da kawaici da tsantsar qawaunar dan wani ga alkunya bata iya gwada son yayanta sama da sauran yaran Ummi Na mutunta ta matuqa
Daga can gefe kuma su Usman ne suna dan hiransi.

Ahmad kuma da Adam suna tsakiyar porlon kan wani tattausan carpet Sai Amira da take ta zirga zirgan zuwa tadda Aysha wannan zuwanta Na 3 kenan sai ta tashi ta zauna da zaran Amira ta fita sai ta sake nadewa a borgo

Muna shigowa ba jimawa

Naji wani irin qamshi mai ratsa zuciyar dan Adam nan take parlon ya hargitse da qamshin mai dadin shaqa gaba daya Na maida hankalina kan qofar danafi zaton tanan qamshin ke shigowa

Cikin nitsuwa yake tfy da cikar kamala taku yake da salon girma hasken fuskarsa kamar tauraro⭐ komai najikinshi tamkar shi ya tsarawa kanshi kai tsaye gaban bb bello ya dan duqa ya gaidashi ya gaida su Nenne ya dan miqe yana gyara riqon da yayiwa briefcase enshi da woyoyinshi ya miqawa Ahmad hannu suka gaisa Adam ya dan harareshi cikin tsokana yace kai yaro ninefa babba ka fara gaida kanina ya qarishe mgnar yana dry
Ya dan kalleshi cikin salon ka isheni da shegen son girma

Abdul dake gefe yace good morning Hamma Yusuf a hankali yace morning Usman dake zaune gefen Abdul yace da kyau ba gaisuwaba ai yayi mgninka shi ko gaisuwar baiso dan haka ni bazan wahal da bakinaba Rabi,u ya danyi dry yace ni bari in gwada ya dan kalleshi da kyau yce Hamma Yusuf….. da sauri ya daga mai hannu ya yimai nuni da su taso su tf ya dan kalli bb bello yace baba mu tafiko

Sagal kaka ta amshe mgnar tana mai cewa kai Yusufa ni ban kai ka gaisheni bane komeye kana tafe kana yamutsa fuska kai dai har Abadan baza,aga fara Arkaba
Rabi,u ya ce toh ma ai Aysha muke jira tun dazu bata fitoba ya dan juya ya qarewa parlon kallo bata gun Amira dake manne jikin Ummi sai yanxu tace Hamma Yusuf ina da sauri ya dakatar da ita gami da cewa cikin mishkilanci da Alamun bacin rai yana mgn da dan fada fada ke tashi kije ki kirata in kuma ba hakaba wlh zan shigo Na babbalata muna fukar yarinya sai baccin tsiya ta iya da sauri ta nufi dakin
Kaka kuma taci gaba dacewa Amira kije kicemata jirgin✈ ya iso kuma har ya fara dirin tashi ta dan juyo ta kalleshi kanshi a qasa tace mutum baida aiki sai sababi ni wlh ai wannan turaren daka zubbuda zai sani mura Abu kamar anyi barin motar turaren ta kuma shaqar qamshi tai ajiyar zuciya tace gsky ka tsammin turaren dan wlh yamin dadi ya kalleta cikin murtuqe fuska ya dan tabe baki
Adam ya kwashe da dry yace kai kaka sharrinki yafi ta tsohuwar mota yanxufa kikace zai kasheki da turaren zai saki mura sai kuma kice ya baki duk sukayi dry yace Allah biyaye karka bata ta dan harari Adam tace toh dan hassada kada Allah yasa ya banin mana ga mai gidana zai sayamin ta fada tana kallon Ahmad ya danyi murmushi yace zanma dauko miki nashin matar
Tai dry cikin jin dadi Usman yace toh yaukuma menene saqon naki?
tce kai da Allah tafi daga can mai muryan mata kai sai shegen made Amman dai duk da hakan kafimin yusufa kam ta maida hankalinta kan Ahmad tece Ahmadu in kaje kace innayi ta baka naman raqumi nakeso….. aiko su
Rabi,u sun sami abin dry Yusuf ya kalleta yana cewa Aku kawai baki da aiki sai surutu sai shegen kwadayi ke dai nama nama kowa ya gaji da nama Amman banda ke
Edin tace nayi surutun so kake naita baqin hali irin naka baki kamar dinkekke andai ji jiki wlh kuma sai kaban turarenan ehe
⭐⭐⭐⭐
Kwance take ko a jikinta kamar ba ita ake jiraba cikin sauri Amira ta daka mata duka ke Aysha toh wlh ga hamma yusuf ya fito
Da sauri ta bude ido gami da zazzarosu 😳 ta diro daga kan gadon tana qoqarin cire kayan jikinta gaba daya jikinta bari yake tana shiga toilet tana Na Shiga uku 🙉 dan Allah Amira fitomin da kayana da mayafina da takalmi yau kam Na kade mugu ya samu dan dalilin jibgata

By garkuwan Fulani

Ku biyoni masu karatu wannan goron sallarkune daga gareni
[4/9, 1:47 PM] ‪+234 909 785 3276‬: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇 MI,WASMITI…..page 3⃣ Na Aysha Ali Garkuwa 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

9:55 PM*12-09-2016

Bayan ta gama yan gyare gyarenta ta fito sab da ita gonin sha,wa Doquwar rigace ajikinta tayi kib da ita cikin sauri ta dauki ribbon enta da dan kwalinta a hannu ta fito parlon tfy take cikin sauri sauri hankalinta gaba daya nagun Ahmad shiyasa bata lura da shi a gunba tana isa ta miqawa Ahmad en ribbon en gami da dan juya bayanta tce ya Ahmad gashi tufkemin gashina ga yan kunnena ma ka samin da sauri kasan yanzu za,aitamin masifa Karba yayi yana murmusawa ya dan matso yana tattara gashin da ya kwanta har kan kafadunta
Rabi.u ya dan kalleta cikin jin takaici yace wlh kedai kinji jiki kina mace Amman wai sai maza ke shiryaki….cikin tsiwa tace endin aiba kai nace kaminba ehe Yusuf dake tsaye a gefensu takaici ya gama cikashi yarinya ta bata musu lkci sannan ta fto tana musu rasar kunya cikin jin haushi ya ware tafin hannunshi zai shimfi da mata mari da sauri Ahmad ya dan jata jikinshi ya tura fuskarsa aiko marin ya sauka kan lallausar fusakarsa Adam ya dan juyo dan jin sauqar marin kai biyaye lfyarka kuwa ? a harzuqe Yusuf en yace wlh yau zakici dan banxan duka kaji muna fukar yarinya ya kalli fuskar Ahmad a take tai jawur abinka da farar fata hatta zanen yatsunsa sai da suka bayyana a kuncinshi ita kam tuni ta gudu gun Nenne cikin jin tsanarta ya kalleta ya kadai kai gami da cije lips enshi ya fita a fusashe
Amira ta kalleta shike nan Aysha kin kade wlh saikinfi fura kirbuwa agun Hamma Yusuf kika Sa ya mari ya Ahmad ai kinshiga tara..tai rau rau da ido tace dan Allah Ummi ki bashi haquri. Usman ya harareta yace Wlh ya dakakin dai Munafuka ba bakya tsoron kowaba tun yaushe muke jiranki sai kace kece uwarmu gaba daya..
Nenne tace yi shiru abinki bazai dakekiba
Bb bello ya miqe hadi da cewa kutaso mu tfi..

Motocin 3 ne a harabar gidan daya Usman ne ke jansu bb bello da Nenne sai Abdul da yake kusa dashi daya kuma Rabi,u ne ke jansu Abba da Ummi suna baya sai Anty Sadiya dake gefenshi a hankali suka fita harabar gidan sai dayar kuma Yusuf ne xaune a ma zaunin driver Adam ya zauna a gefenshi sai Amira da Aysha a baya Ahmad Na daga tsakiyarsu Aysha Na maqale da hannu Ahmad a jikinta duk ta rude

Kusan minti 20 da fitarsu bb bello Amman shiru yana zaune sai danne danne yake a lap top enshi tamkar ba masu shirin tfy ba Adam ya dan kalleshi cikin yanayi yadai yace haba biyaye tfy fa zamuyi kuma kai zamanka ai ya kama mu tfi ko shiru kamar badashi akeba sai gyara zamansa yayi ya dan kishin gida da jikin kujera Ahmad ya danyi mirmushi cikin muryar lallashi yace tuba muke yayana aimana afuwa a huce plss mu tf kasan Abba zai ta jiran isowarmu ya juyo ya kalleshi ya maida kanshi a hankali phone enshi ya fara suwa ya balle marfin motar ya fita gindin wata bishiyar manqoro 🌳ya zauna kan wasu kujeru da aka tana dan zaman mgn yakeyi kamar baison ya dan hada fuska yana mai cewa Rashida ni fa bana son fitina ai sauri kikayi aiki ne yamin yawa ko zaman kiranki zanyi cikin muryar gudun matsifarsa da tsantsar qaunarsa tce ayyah Yusuf yau kwana nawa bamuyi mgn ba kai baka kirana saidai in ni Na kiraka sallah guda bazaka kiraniba mu gaisa cikin gajiya da mitarta da surutun nata yace ya isa ya isa haka badai gashi yanxu mun gaisaba ni yanzu ina da abin yi da sauri tace dan Allah kar ka katse kiran Yusuf yaushe zakazo ne ? Barana ya bata amsa a gajarce ya katse kiran cikin jin takaici ta qurawa phone📱 nata ido a fili take cewa ya Allah ka mallakamin zuciyar 💛Yusuf ka juyomin hankalinshi gari Allah ka sassautamin sonsa a raina Rashida yar kano ce kuma tare sukayi karatu dasu Yusuf a India allah ya jarabceta da qaunar Sa a ranta shi kuma mishkilanci da taurin kai da ra,ayi sun hanashi maida hankali kan ko wacce mace

A hankali Ahmad ya zauna gefenshi biyaye ya kirashi cikin sanyi muryarsa tashi mu tfi ko ido ya zubawa fuskarsa hannu yasa ya shafa fuskar yace biyaye meyasa meyasa zakasa hannuna ya mari fuskarka Kasan kimar fuskarka gareni kuma kasa Na cutar da zuciyata bana qaunar duk wani abin da zai tabamin gangarjikinka da lfyarka wlh naji tsanar ta araina dan ta sani Na mari dan uwana da hannuna.
Cikin sakin fuska Ahmad yayi ajiyar zuciya ya shafa fuskartashi cikin murya mai nuna gskyar abinda yake fada yace biyaye zafin marin a fatata ya tsaya bai shiga cikin 💘 zuciya taba hakazalika komai kamin duk zafinshi bazanjiba Amman da marinnan ya taba fuskar Aysha Na da zuciyata zata soku da dafi 💘ya daura hannushi kan kafadarsa yaci gaba da cewa biyaye komai nakeso a duniya kana tayani son abin ya akayi ka kasa tayani son Ayshana meyasa zuqatanmu suka samu sabani kan Aysha ni duk zuqar numfashin da zanyi a duniya da nauyin qaunar Aysha nake janshi yayinda kai kuma da tsanarta kake Jan naka numfashin meyasa ya tsura mai ido cikin yanayin tabbaya idonsa sunyi jaa shi bai saniba mganganunshi qara samai tsanarta suke a cikin zafin nama da sauri ya nufi gun motar
Da garfi ya fixqota waje ya watsa mata mari ciki jin radadi tasa kuka ta dafe quncinta da gudu ta fada qirjin ya Ahmad tace Hamma Yusuf dan Allah kayi haqiri wlh bazan qaraba Amira kam tuni ta rakube jikin glass A hankali Ahmad yace ngd biyaye mu tafi tunda kayi abinda ranka ke so ya jata suka shiga
A fusashe ya figi motar
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
MAMBILA

Bayan isarsu baba bello da kadan suma suka iso parlon cike yake maqil da zuriyar bappa yaya bayan gaishe gashen da sukayi shidai yusuf su babba Amadu kawai ya gaisar ya koma can gefe ya zauna ya bude lap top enshi yai ta dan danne danneshi Sadiq yazo kusada shi ya zauna suna dan dubawa tare dan haqiqa yana qaunar yaron duk da ba wani mgn dashi yakeyi sosaiba

Abba ya kalli Ahmad dake zaune kusadashi yace Ahmad meya tsayda ku ? ya danyi murmushi yace Abba kawaidai mun tafi a hankaline ya jinjina kai yace toh kun kyauta
Bappa yaya ya dan kalli Yusuf daya murtuqe fuska yace kai Dudabe har yanxu baka Koma bane ya daqo ya zuba mai harara dan ba abin da ya tsana kamar kiransa da Dudabe da bppa yaya yakeyi yaci gaba da cewa Ahmad shi har yanxu hutun nasu bai qare bane ? Ehh da sauran lkci dai ya bashi amsa
Adam yace wai kai menaka da komawarsa ne ko a kanka yake zaune baba bello yace Adam haka naka dama kai inkazo dai toh sai kai ta sokano mana su innayi tamiqe tana nasan yusufa da tea bari Na kawo maka ta dauko flask en da cup ☕ta dire mai a gabanshi tace ga shayinka dan nasanka kananan kamar balarabe ya dan kalleta ya motsa bakinshi a hankali yace sai anjima zan Sha.ko Sadiq dake gefenshi Badon yana kallon bakinshiba da bazai San me yaceba inna ta dan tabe baki tace yayi ai In dai Yusuf ne ya iya gwatsale mutane Bappa Yaya yace Dudabe har baki 3 bai amsaba bai kalleshiba ya danyi dry yace Allah sarki Dudabe am mu muna sonka kamar mu mutu kai kuma kana qinmu kamar ka mutu duk suka danyi dry Adam ko dry yake hard a buga hannu yace madallah biyaye toh Bappa Yaya mu da bakwa son kuma ko zaku kaimu bola😂 haka dai sukai ta hira da nishadi hirar zumunci

By garkuwan Fulani
[4/9, 1:47 PM] ‪+234 909 785 3276‬: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇MI,WASMITI…..page 5⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
A hankali ya direta kan kujera hadi da manna mata kiss a goshi Nenne ta kallesu cikin qauna ta murmusa tace kai Abubakar kamar dama ita kadai kai kewarta da sauri cikin dry ya duga gaban bb bello ya gaidashi da Abban su Ummi farin ciki take sosai tanajin dadin yadda Abubarkar ke mu,amala da qanneshi tamkar abokan watsanshi zafi sosai takeji a ranta in taga yadda Yusuf ke hantarar su da donqofarsu Sam baya zama dasu yayi hira Sam abin bai mata dadi amatsayinsa Na shine babba
hira suke sosai tana maqale jikin ya Abubakar ga Ya Ahmad a gefensu Nenne ta kalli Amira tace toh kunyi ta mai hidima yanxu kuma kun xo kuna ta surutu Baku kawo mai abincin ba da sauri ta miqe gami da dauko abincin Yusuf dake gefensu mamaki yakeyi sosai a ransa kome su Ahmad keji da maqalema yara qanana basa ko jin kunyarsu da gudun karsu rainasu abin haushi yake bashi sosai ya sake kallon yadda Abubakar ya ke ta lallaba yarinyar har abin kyamama yake bashi ga uban surutu da suke zubawa kamar parrot ko bakinsu bai gajiya da cokoikoiwa cikin qosawa da surutun nasu ya miqe ya zai tafi a lkcin Kuma Abubakar ya dan ture Aysha a jikinshi yace Auta baki kawomin ruwaba fa ta miqe kenan sukayi ido 2 da dodon nata cikin razana da tsantsar tsoronsa jikinta har bari yake bata San sanda ta furta إنا لله وإنا إليه رجعون،الله‍م اجرني في مصيبتي وأخلف لي خير منه‍ا ya kalleta da kyau yana qoqarin gano me take nufi shine matsifar ko qaqa ai bata bari ya idda tunaninsaba ta juya da gudu tai dakinsu hakanne ya tabbatarmai dashi din take qoffa yayi ya girgiza kashi gami da cije lips enshi ya fita Sukama sukaci gaba da hiransu Ahmad dai ya gano Abinda Yusuf ke nufi Aransa yake mmki wai ace mutane uwa daya uba daya Amman basa taba haduwa gu daya kamar wuta da auduga

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

A hankali take tfy har ta iso qofar gidansu dai dai baking get in taga wasu maza su biyu zasu kai Sa,annin ya Ahmad kanta a kasa tana tfy cikin gaji tana kai gidan kaka sai shegen nisa in bakajeba tai ta mita tazo daidai gunsu da sauri dayan yace yauwa qanwata yaki ta dan kalleshi a nitse ta iso ta gaidasu suka amsa da fara,arsu dayan yace aha qanwata in kin shiga kicewa yayanki Yusuf ya fito mu tafi
Ta dan kallesu a yatsine tace ni bani da wani Yaya mai wannan sunan ehe ban sanshiba ta qarishe mgn tana qoqarin tfy da sauri suka kalli juna har suna hada baki wajen cewa ina ke yar gidannane ehh ta basu amsa da mmk sukace kuma kice baki San Yusuf ba ?
Ta dan juya ido tace ehh ni yayuna ba Yusuf sai ya Ahmad da ya Adam kuma basannan ta juya da nufin tfy a firgice ta zaro ido 😳ta dan ganinshi a bayanta juyawa tayi da sauri zata Koma inda ta fito cak ta tsaya sabida tsawar da ya watsa mata maza kixo ki wuce gida yarinya sai shegen yawon tsiya zan kamakine ya kada kai suka shiga mota itako tai cikin gida
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Bayan sallan 🕌isha Ahmad ya shigo gida a lokacin tare suka shigo da Abba ya ajiye mar jakarsa ya fito a parlor suka hadu da Aysha su Ummi Na zazzaune ya dan kalketa cikin salon tsantsar qauna ya dan shafa cikinshi yace Aysha yunwa nakeji a kawomin abinci dan Allah toh tace cikin zumudi tace ya Ahmad me zan dafa maka ?hankali cikin murmushi yace matayassara Ummi ta danyi dry tace inbanda abinka Ahmad gani ga Nenne duk baka tabbayemu abincinba sai itta zaka tabbaya ya dan Sosa qeya yace uhum Ummi ai gwara tun wuri ta koyi kula dani dan nasan Abbbana kam ya bani ita sai dai bansan me baba kuma zai ceba ya dan kalli Nenne yace Nenne inason Aysha inasonta a raina bana iya boye sonta a zuciyata💛 da Zahirina cikin wani yanayi Nenne ta kauda kanta daga kallon dan nata
abin qaunarta Tanajin Ahmad tamkar bugun zuciyartane ya matso gabanta ya rusuna yace Nenne banason yadda kikemin in namiki mgnar Aurena da Aysha
A hankali ta daura hannunta a tsakiyar kanshi tace Allah ya maka albarka kai da sauran yan uwanka baki daya Amin yace cikin jin didi ya juya ya tf part ensu

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
A harabar gidan ya samu Adam da Amira suna hira cikin nishadi SLM kawai ya musu ya wice ciki a parlor ya tadda Yusuf zaune kan kujera ya miqe qafafunsa kan Center table ya daura laptop enshi kan qafafun yana daukar lacturer ta online Jallabiyace a jikinshi ya gyara gashin kanshi gonin Sha,awa Sai qamshi yake kamar fure cikin qaunar juna suka gaisa da Ahmad ya dan kalleshi yace biyaye ina ka tsaya haka sai yanxu tare muke da Abba ya fada yana cire kayan jikinshi yaci gaba da cewa bari naje Na dan watsa ruwa ya tafi bedroom enshi kai tsaye toilet ya wuce

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
A hankali tai SLM gami da dire tiren abincin kan dining ta juyo cikin sanda ta tsaya saitin kanshi duk a tunaninta Ahmad ne dan komai Nasu iri daya hatta gyaran gashinsu Sam bata gane shine a gunba a hankali ta sunkuyo kanshi tasa bakinta daidai kunneshi ta dan hura issaka ta dan tura yatsunta cikin lallausar gashin kanshi mai qamshin gaske cikin rada tace I love u ya Ahmad tana maici gaba da wasa da gashinshi cikin daqiqa daya ya gano itace ya San ba mai haukannan sai ita a take ji wani malulun baqin ci da takaici duk illahirin tsikar jikinshi sai da ta tashi gaba daya ya harxuqo cikin fushi da zafin nama ya juyo kamar walqiya ta ganshi gabanta tunda ya juyo fuskarsa ta saki qara tana baya jikinta bari yake sosai gaba data ta fiddo idanta woje Ahmad dake toilet da sauri ya dauro towel ya fito cikin xafin nama yana ai dama nasani za,Rina sai ya sata kuka
Shikuma Yusuf hannushi har rawa yake cikin daga murya yace zonan bakince baki da nitsuba ba dama inada cikinki yau sai Na babbalaki gutsi gutsi ya fada yana gwada yadda xai ballatan ya daga hannushi zai yarfa mata marinshi mai bala,in zafi da Sauri Ahmad ya shiga tsakaninsu yace cikin salon kar ka daketa yace huce a kaina ninace ta kawimin abinci yasa hannushi ya dan balleta a jikinshi yace tf Aysha sai da safe ko aiko a guje tai cikin gida Amira kam dama tunda taji qaranta tai cikin gida cikin
Fushi sosai ya kalli Ahmad da Adam wlh kun isheni kun isheni abin yayi yawa ko kunya bakwaji qatti daku Ku liqewa yara qanana salon Ku jamin raini kallekafa biyaye da girmanka ka wani dauro towel a ququ girjinka duk yana woje yanzu da daurin ya kwance shikenanfa ka kade a gaban qanwar qanwar bayanka den tasoka ko ta rainaka Adam yayi dry sosai Yace toh me a ciki ba shikenan ba tasan German abinda zata aura ba 🍌 shi dai Ahmad shiru yayi sosai Yusuf kuma ke fada yayinda Adam ke qara tunzurashi A qufule yace Wlh Ku daina kiramin su nan in bakusan kunyaba Ni inajin kunya bira girma ya fadi Yaya Yaya ase yayun banzane

⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐

Mambila
Yau lahadi tun da sassafe suke shirin komawa cikin Tarawa dan sunyi hutunsu Na qarshen sati gaba dayansu daga kan Adam har zuwa kan Aysha suna zaune kan dining suna karyawa yayinda sukma manyan suna tsakiyar Palon sun da tattaunawa Aysha da Amira ke Serving ensu duk sun xubawa kowa suna tunani ya zasuyiwa Yusuf shi ba ,amai gwaninta Ahmad ne ya dan kalli Aysha cikin mgn da ido ya nuna mata shima ta hadamar tea cikin dan jin tsoronshi ta jawo cup ☕ta zuba mai tea duk hankalinta Na kanshi ta ina zaiyi matsifa Koma taji mari cikin tsoron har ta zuba mai gishiri a madadin sugar a cikin tea en
Shi kuma tunda ta fara yake kallon farshen dan qaramin yatsar hannuta Na hagu ta barshi wai ita gayu shi kuma kyamar farce yake a rayuwarsa
Ya kalli sadiq dake gefenshi yace kai. Sadiq Kawomin scissors enka toh yace gami da miqewa ya lura Sarai gishiri tasa shiyasa ya jawo cup en ya dan kurba dai dai lkcin Sadiq ya mi qamai ✂ ya karba ya tura mata cup en yace gishir a madadin sugar kasheni kike shirin yi ko toh ke zaki shanye yasa hannushi ya kamo dan yatsar ya dan dannan scissors en da niyar yanke farcen aiko ya hada da kan dan yatsar

Leave a Comment