Books Reviews & FAQs

Mallakin Waye Hausa Novel

Compiled by Umar Dalha.

 

 

πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye*…….. 01

_Written by Queen Samy_πŸ‘ΈπŸ»πŸ’„πŸ’‹

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*America*
_California(Los Angeles)_
2011.

“Gidan yayi shiru banda sautin kukan mutanen dake ciki baka jin komai, wata Dattijiwan matace wacce bazata gaza shekaru 64 ba a duniya ta fito daga wani ‘daki hannunta ‘dauke da jaririya wacce a’kalla bazata wuce watanni 4 ba.
“Zama tayi tsakiyan yaran dake ta shar’ban kuka cikinsu an rasa me ba ma wani baki, itama wnn Dattijiwa kuka ne sosai ya kufce mata.
“Wasu maza guda biyu ne suka shigo ‘daya saurayi ne wanda bazai wuce shekaru 22 ba a duniya, farine sol kyakyyawa yanayinsa zai tabbatar maka shima cikin tashin hankalin yake, mutumin da suka shigo tare dashi yana dafe da kafa’dunsa wanda ko ba’a fa’da maka zaka gane mahaifinsa ne, dan kuwa kammaninsu ya ‘baci saidai kawai matashin ya ‘dan nun masa ‘kuruciya, mutumin bazai gaza shekaru 48 ba, a tare suka shigo cikin parlorn ai kiwa gaba ‘daya yaran suka mi’ke suka rungumesu suna kuka.
“Daddy is it true, mummy has gone…… “‘Yar budurwan ciki wacce bazata wuce shekaru 12 ba ta fa’di cikin tsananin kuka da tashin hankali, sosai mutumin da ta kira da daddy ya rungumeta kafin yace” Nadiya dukkaninmu ‘yan adam ne dukannninmu watarana zamu bar duniya, addu’a shi zamuyi wa mummyn ku Allah yasa ta huta Allah yasa kyawawan ayyukanta su bita.
“Sosai suke kuka, wasu ‘yan yara maza guda biyu wanda da gani kasan tagwaye ne baza wuce shekaru biyar ba a duniya suka rungume ‘dan matashin cikin suna kuka, ‘kan’kamesu yayi yana kuka shima sosai, sun jima a haka ko wanni na kuka kafin daga bisani ” Daddy ya ‘karasa ya kar’bi ‘yar jaririyan dake hannun dattijiwan nan yace” Amma kawota, Amma ta mi’ka masa ita tana gohe hawaye. Kallonta *Engr. Nazif Mumtaz* yake babu ko ‘ka’k’kautawa, tausayinta da sonta a lokaci guda yana ratsa ‘bargo da tsokansa, sosai ya rungumeta yana sharan hawaye.
“Haka ranan gidan Engr Mumtaz ya wuni cikin tsananin tashin hankali da alhini na mutuwar matarsa kuma uwar ‘ya’yansa.

“Zaune yake cikin ‘dakinsa ya ‘kura wa hoton mahaifiyar sa ido, har lokacin besaka komai a cikinsa ba, ya kasance yana tsananin son mummin sa gashi mutuwa ta masu YANKAN ‘KAUNA, Allahu Akbar dukkanin me rai dama mamaci ne, Allah ka bamu ‘karshe me kyau ameen.
“Amma ne tayi sallama a ‘kofan ‘dakin, yayi saurin ajiye hoton gefe gamida gyara zamansa, murmushi Amma tayi na ‘karfin hali kafin ta ‘karasa shihowa ‘dakin, hannayen saurayin nan ta ri’ke cikin nata kafin tace” *Irfaan* you need to be very strong, mu gode wa Allah Khadija ta samu kyakyawan shaida, muna ro’kon Allah yasa kyawawan ayyukanta su bita, snn ka tuna kaine babba cikin yaran nan idan bakayi juriya ka jawosu jiki ba, abun zaiyi affecting dinsu yanda baka tsammani. Addu’a shine gatan mamaci ba yawan kuka da damuwa ba…. ” Irfaan ya share hawayen idonsa ya rungumo kakansa yana fa’din ” Amma I still couldn’t believe that mummy passed away……. kasa ‘karasa maganarsa yayi dan kuwa sosai yake kuka, rungumesa Amma tayi tana basa baki ha’di da ‘karfafa masa gwiwa.
“Sanda Irfaan ya fito parlor ‘kannensa maza twins guda biyu suna zaune da gani kasan sun sha kuka, ‘karasawa yayi tsakiyansu ya zauna, ya ri’ko hannayensu, Amir da Aiman suka rungume yayan nasu Irfaan ya shiga shafa gashin kansu ba tarda ya furta komai ba.
“Engr Nazif kuwa ranar bacci tare yayi da ‘yar autarsa wacce suke kira da Nilam, koda Amma ta dubasa a ‘dakinsa dan kar’bo Nilam, gani tayi ya rungumeta sosai cikin jikinsa dan haka juyawa tayi cike da tausayawa ‘dan nata da jikokinta.

“Yau sati guda da rasuwan mummy, hankuka sun soma dawowa jikkunansu, duk da har yanzu Irfaan abin na tare dashi sosai.
“Zaune suke gaba ‘dayansu a wasu kujeru mai table a tsakiya wanda daga gani ba sai ance maka na sha’katawa bane dake a farfajiyan gidan, daddy na ri’ke da precious Nilam ‘dinsa, Amir da Aiman sunata wasa a can gefe, fruits ne a gabansu wanda aka yayyakan ‘kanana kaman friut salat cikin wasu cups masu ‘kasa me ‘dan tsini, ko wani cup akwai ‘dan stick a ciki wanda ake cin friuts ‘din dashi.
“Irfaan ne ya fito daga cikin gidan yana sanye cikin armless shirt red da faran three quarter ya ‘karaso fuskansa babu yabo babu fallasa ya gaida Amma da Daddy kafin ya zauna a ‘daya daga cikin kujerun, Nadiya ta mi’ka masa cup ‘daya tace ” ya Irfaan have some, ta’be baki yayi yace ” no thanks…. kallonsa duka sukayi kafin tace” zai taimaka maka da appetite. Girgiza kai yayi a karo na biyu kafin ya ‘karasa ya kar’bi Nilam dake hannun daddy yace ” come here Angel. Wasa yake kan yima Nilam tana dariya, shi kansa sosai yake dariya, su daddy da Amma harma da Nadiya saida sukaji da’din sakewan da Irfaan yayi.
“Bayan ya zauna ne Daddy yace” irfaan dama fitowarka muke jira, Irfaan ya ‘dago ido yana duban Daddy kafin Dady yaci gaba da fa’din” mun yanke shawarin komawa Nigeria in the next few days, what do you think.
“Shiru kaman nazaice komai ba sai kuma yace” is that really necessary. ?… “Daddy ya ri’ko hannunsa yace Son, hakan ne kawai zai mantar mana da rashi babban da mukayi a nan States, and your siblings ya kamata su san ‘kasarsu su san al’adunsu, I think lokaci yayi da zamu koma.
“Shiru Irfaan ya ‘danyi kafin ya ‘dago ya dubi mahaifin nasa yace” but Daddy what about my sch, na riga na fara university a nan….. ” shiru Daddy ya’danyi na wasu lokuta.,…. kafin yace ” yeah son hakane,…..” Amma ce ta katse su da fa’din” Yes dole mu bar States in a couple of days, na gaji da zaman nan snn mahaifinku ma gwara mu tafi ya samu yayi aure….. ai bata gama rufe baki ba Nadiya ta mi’ke tana masu mugun kallo kafin tace” Amma aure fa kikace, daddy ne zaiyi aure for heaven sake, this is ridiculous. Wllhi daddy bazaiyi aure ba, wato har kin mance mutuwan mummyn mu kina masa magan…..” Enough Nadiya, Irfaan ya daka mata tsawa, ma Amma ne ko ma Daddy kike ‘daga murya,…. Amma da Daddy kam mamakin kishi irin na Nadiya suke ji, ‘karama da ita har tana taya late mother dinta kishi…
” Kuka Nadiya ta fashe dashi ta shige cikin gida a guje, Irfaan na kwala mata kira inaaaa ko saurarensu batayi ba ta shige, Aiman da Amir dake gefe suna wasa ganin Nadiya ta shige a guje tana kuka yasa suma suka fashe da kuka a tunaninsu wani ne zai sake mutuwa, nan suma su Amir da Aiman suka rufa mata baya.
” Engr. Nazif idan akwai abunda yafi tsana tofah shine ‘bacin ran ‘ya’yansa, musamman da yanzu mahaifiyarsu ta mutu, yayi al’kawarin bazai sa su kuka ba, zai zame masu uwa da uba, zai kasance tare dasu a ko wani irin hali suke ciki… ” Da sauri irfaan ya mi’ke yabi bayan ‘kannensa….. Daddy yabisu da kallo kafin ya juyo yana kallon Amma yace” pls Amma you need to be more understanding with what they are going through, you shouldn’t have talk that way. Ki tunafa they just lost their mother, be kamata kimin maganar aure yanzu ba, especially at their presence.
“Kallon mamaki Amma tabisa dashi kafin tace” dole mu koma Nigeria, bazan iya tsayuwa inaji ina gani ‘dabi’un turawan yamma yayi tasiri a zukatan jikoki na ba,….. daga haka Amma ta mi’ke ta shige cikin gida.

“Knocking Daddy keyi a ‘kofar ‘dakin Nadiya amma fir ta’ki bu’dewa, ” Pls sweetheart, let us talk….cikin kuka take fa’din” no just go away, I don’t wanna see you, you going to marry another woman, aren’t you?.
“Daddy ya fuzar da iska yace” Sweetheart, let me in first, let’s talk about this….. juyawan da Daddy zeyi yaga Amir da Aiman suna shar’ban kuka, da sauri ya ‘karasa wajensu ya tsuguna ya rungumosu yana fa’din” what’s wrong boys…..” cikin kuka suke fadin” Adda Nadiya told us you’re going to abandon us, you’ll have a new family in Nigeria…….” Dafe kansa Daddy yayi a hankali ya furta” Lord of mercy” rungumesu yayi yace” that will never happen boys, I love you ultimately, I will never abandon you. Oya come here , ya manna masu kiss a gashinsu, kafin ya mi’ke yana ri’ke dasu suka soma sau’kowa daga stirs…….

πŸ‘ΈπŸ»QueenSamyNovelsπŸ˜πŸ’„πŸ’‹…….
[8/18, 20:21] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye* 02

_Written by QueenSamy_……..πŸ“

“Haka Nadiya taki bu’de ‘kofan nan har dare, gaba ‘daya hankulansu yatashi, da ‘kyar da magiya ta bu’de wa mahaifinta, lallashinta ya shiga yi kaman wata ‘karamar yarinya ita kuwa sai basar da dad din nata take, wnn mummunan ‘dabi’a na western people sosai yayi tasiri a rayuwan gidan Engr. Nazif Mumtaz,
“Daddy promise me you’ll not remarry. Nadiya tace cike da shagwa’ba, rungumota Daddy yayi yace” my dear stop thinking silly ok, for now kula da rayuwarku shine a gabana ba batun aure ba, your grandma wasa take kawai, ba sabida aure take so mu koma Nigeria ba, you see sweetheart, akwai Company din late daddy na a Nigeria *M&M Builders*, so ever since your grandpa pass away amininsa shi yake running company din, I think lokaci yayi da zan koma na kar’bi companyn dad dina na ci gaba da kula dashi, what do you think.
“Shiru Nadiya ta ‘danyi kafin tace” what about your job here in the States. Hannayenta daddy ya ri’ke yace “I’ll resign darling.
“But daddy are you sure we gonna have a better life there, I mean our sch and so on……..” Cike da ‘kosawa da tambayoyin Nadiya ‘karama da ita sai yawan magana, daddy yayi gyaran murya yace” of course honey that will be even much better. I promise you that.
“But daddy what about our friends here in the States, am sure we gonna miss them…. ta ‘karashe maganar tana turo baki.
“Daddy yace” sweedy pls stop making this so difficult okay, you’ll have a chance to say good bye to them okay… now let’s go and have dinner ok.
“A tare suka sau’ko downstairs daddy na ri’ke da hannunta, he’s so friendly to his kids…. “Amma tabisu da kallo kawai tana mamakin yanda gaba ‘daya ‘dabi’un turawa yayi tasiri a rayuwan gidan ‘danta.
“Da murmushi Daddy yace” kids tomorrow you’ll visit all your friends, and say goodbye to them ok…. Amir da aiman suka soma murna suna fa’din” yeeeey we leaving to Nigeria. Ta’be baki Nadiya tayi ba tare da tace komai ba.
“Irfaan ne ya shigo babu ko sallama sai cewa da yayi ” Hi everyone, daddy yace” Son let’s have dinner. Irfaan ya ‘dan yamutsa fuska yace” daddy I don’t feel like eating, just go ahead. Amma tabisa da kallo kafin tace” irfaan zo ka zauna kaci ko ka’dan ne, kallonta Irfaan yayi da manyan idanunsa harda wani juyasu kafin ywce” Okay granny just because you insist….. ” ya zauna a ‘daya daga cikin kujerun yana duban Nadiya, Spoon ‘din gabanta ya ‘dauka kafin yace” hey are you still mad, baki a tureta ‘dago ido tana dubansa….. “Daddy yayi karaf yace” Son eat up, is your favorite, murmushi Irfaan yayi ya soma cakalan abincin kaman me tausayinsa,
“So when are you guys leaving? Irfaan ya tambaya, daddy yace in a couple of days, Son be careful while you’re here alone okay….
“Irfaan ya gya’da kansa yace” you really don’t have to worry about that daddy, am not a spoiled child, kai da mummy raised me well, may she rest in peace, duka suka amsa da ameen.
“Daddy yace” duk da haka Son, you really need to be very careful, kaga yanzu ka soma karatu just level 2 kake, snn kace har masters zakayi kafin ka dawo Nigeria, so kaga dole na damu.
“Irfaan ya juyo ya kalli Amma yace” Amma you see daddy is treating me like a kid again, ko zamu zauna dake a nan States ne.
“Ta’be baki Amma tayi tace” Allah tsareni da ci gaba da zama a nan, yara duk baku san al’adunku ba kun ri’ke _al’adun wasu_ kuna koyi dasu, kaima da zaran ka gama sch zaka dawo Nigeria.
“Murmushi kawai irfaan yayi yace a ransa _me zai kaini Nigeria for goodness sake, I rather stay here all alone da na koma Nigeria_….. “Tattaunawa suka ci gaba dayi har zuwa lokacin da suka gama cin dinner.

“Nadiya ta dubi Amma tace” Amma zamu tafi da Nannyn Nilam Nigeria knn, Amma ta narka mata harara tace” akan me taje taci gaba da koya mata ‘dabi’un wasu, I’ll find her another Nanny a Nigeria. Nadiya tayi kicikicin da fuska tace pls Amma kinga mun yarda zamu koma Nigeria, pls do this for us, mu tafi da Patricia taci gaba da kula da Nilam, itace tasan Nilam tasan abunda take so da wanda bata so, pls Amma don’t say no, I beg of you…. ta ‘karaso ta haye jikin Amma tana ro’konta.
“Dole ba don Amma taso ba tace” alright fine, naji zamu tafi da Patricia amma da zaran Nilam ta soma wayo zamu sama mata nanny musulma a Nigeria wacce zata koya mata da’bi’u masu kyau. Nadiya ta ‘dan turo baki ba tareda ta kuma cewa komai ba. Daddy ma yayi na’am da shawarin Nadiya, dan kuwa Nilam bata yarda da kowa sai Patricia snn idan akwai abunda ya fi tsana tofah shine kukan Precious ‘dinsa….
“Kwana biyar suka ‘kara a Los Angeles kafin suka ‘daga zuwa gida Nigeria…..

*Nigeria*
_Abuja ( LifeCamp)_……..

“Unguwar LifeCamp dake birnin tarayya Abuja, unguwace wanda gidajen dake ciki ka’dai ya isa ya tabbatar maka da cewa gidajen masu hanu da shuni ne, ko wani gida yana jere cikin tsari da kyau, akasarin ginannukan gidajen bene ne.
“Gidan Engr.Nazif Mumtaz yana ‘daya daga cikin jerin gwanon gidajen nan, tsayuwa fa’din irin tsaruwan da gidan yayi ‘bata lokaci ne, dan kuwa komai na gidan me kyau ne abin birgewa gwanin sha’awa. Kyaun gidan yasa Nadiya taji da’din dawowa Nigeria, dan kuwa ita yarinya ce me bala’in son kyale’kyale.

*M&M (Mumtaz and Ma’aruf) Builders Of Company*

“Alhaj Ma’aruf ya kalli Daddy yace ” gwara da Allah yasa ka dawo dan dama ni gaji da ri’kon wnn mu’kami, dan shekaru sunja, nima ina bu’katan hutawa. Daddy yayi murmushi ya kalli Alhj Ma’aruf aminin mahaifinsa kafin yace” Baba na gode da ‘dawainiyan dakayita min da dukiyata Allah ne kawai zai biyaka.
“Girgiza kai Alhj Ma’aruf yayi yace” Nazif idan akwai wanda yafi cancanta ya mi’ka godiyansa to nine, dan kuwa mahaifinka Mumtaz ya gama min komai a rayuwa. Ya shiga bu’de files yana ciro takardu ya mi’ka masa kafin yace” an jima zamu kira meeting gaba ‘daya staff su hallara, the New President of M&M Builders is here.
” Daddy ya girgiza kai yace” A’a Baba you’ll remain the president, ni zan ri’ke mu’kamin Chairman, Alhj Ma’aruf ya girgiza kai yace” Nazif kai zaka zama president, besides kaine me highest shears a M&M builders, ni zan yi retire ne daga rana me kamar ta yau, kai zaka ci gaba da juya mun dukiyata…..
“Haka aka kira meeting a babban conference hall dinsu tareda Shear holders da kuma staff dinsu, aka gabatar da new President of Mumtaz Builders, …. “Daddy ya gabatar da kansa hadi da gaisawa da illahirin mutanen….

 

“Hajiya Karima ta cika tayi fam dajin irin batun da mijin nata yazo mata dashi, ita fah zama dashi take dan ta mallaki M&M Builders amma bacin haka me zaisa taci gaba da zama da wann tsohon wanda tasan nan bada jimawa ba zai zama gawa. “Mikewa tayi taci gaba da safa da marwa a cikin ‘dakinta, a hankali ta furta tabb inaa bazata ta’ba sakuwa ba, dole na san yanda zanyi na kar’ba wa tilon ‘yata Companynta…….

πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹……
[8/18, 20:21] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye* 03

_Written by QueenSamy_……..πŸ“

“Laila ce keta doka Sallama a ‘kofa amma ko ka’dan Hajiya Karima bataji ba, sosai hankalinta ya tafi ga tunanin da take, da mugun mamaki Laila ke bin mahaifiyar tata da kallo har ta ‘karasa shigowa cikin ‘dakin.
“Hajiya! Shiru hajiya karima bata amsa ba, Laila tayi gajeren tsaki ta shiga buga kujeran da Hajiya ke kai tace” Hajiyaaa! Wnn karan da ‘dan ‘karfi sai snn Hajiya Karima ta ‘dago tana duban Laila tace” Ke kuma yaushe kika zo….” Laila ta jakanta bisa sofa tana zame mayafin kanta take fa’din, nafi minti biyar a nan ina sallama baki jini ba, Hajiya tunanin me kike ne haka.
“Hajiya Karima ta sau’ke ajiyan zuciya kafin tace ke kuma daga ina?
“Laila tace na sau’ke Aziza gidan ‘kawarta shine na ‘karaso,. Hajiya wai meke damunki ne, kinsan fa likita ya hanaki yawan damuwa.
“Galala Hajiya Karima ta kalli Laila kafin tace” tunanin ‘dan isakan tsohon nan nake.
“Da mugun mamaki Laila ke kallonta kafin tace” waye kuma ‘dan iskan tsoho?
“Tsaki Hajiya ta buga kafin tace Alhj Ma’aruf……..
“Kan ubancan! Hakan Laila tace a fili. Ido cikin ido take duban mahaifiyar tata kafun tace wai dama Alhaji ne ‘dan iskan tsohon, mahaifi na.
“Tsaki Hajiya ta buga a karo na biyu kafin tace” yo meye idan ba ‘dan iska ba, har nice zai dubi tsaban ido na yace ya cire hannunsa a M&M Builders, wai ‘dan Late Alhj Mumtaz ya dawo daga States dan haka ya mallaka masa kampanin mahaifinsa.
“Laila ta gyara zama tace” Hajiya ban fahimci zancen ki ba, wai Alhajin ne ya mallaka ma wani M&M, kan wani dalili.
“Kan dalilin ubansa ne ya masa komai harta shears dinsa ubansa ne ya saya masa,……” Wai hajiya na tambayeki dama M&M *Mallakin waye*
“Tsaki Hajiya Karima tayi kafin tace” a iya sanina mallakin Alhj Mumtaz ne, amintaka dake tsakaninsu da Alhaji ya mallaka masa babban shear a company n da farko sunan companyn Mumtaz Builders ‘karshe har ya maida sunan kampanin ta koma M&M Builders wato Ma’aruf and Mumtaz Builders.
“Laila ta sau’ke ajiyan zuciya tace ” tab’dijam toh shi wann ‘dan nasa me ya dawo yi yanzu Nigeria. Hajiya tace matarsa ta mutu mana, shida uwarsa sun tarkaso sun dawo, dama uwar nasa tun mutuwan mijinta wato ubansa ta koma can American wajen ‘danta, sai yanzu ne zai tuna da kampanin ubansa, bayan Alhaji ya gama masa shan wuya, saida company ta ginu, tayi ‘kaurin suna a nahiyar Africa baki ‘daya, duk yammacin Africa babu kampanin da take shigo da ingantattun kayan gine gine irin M&M Builders, sai yanzu ne zai dawo ya mallaki kampaninsa.
“Laila ta girgiza kai ta furta bazai saku ba Hajiya, M&M *Mallakin mu ne*……
“Dariya Hajiya Karima tayi tace” haba ai duk wanda yasha tuwo da Karime tofah miya ya sha, na jima ina harin wnn Company ta zama mallakinmu nida ke da kuma ‘diyarki Aziza. Wnn dalili ne yasa na salwantar da rayuwar Hindatu matar Ma’aruf ta farko, snn na salwantar da rayuwar tilon ‘yarsa da jikansa…….” Da mugun mamaki Laila kebin hajiya Karima da kallo kafin tace “tilon ‘yarsa?? Me Hajiya take nufi?
“Ganin Hajiya ba a hayyacinta take zantuttukan nan ba yasa Laila mi’kewa tsaye tana fa’din Hajiya me kike cewa tilon ‘yar Alhaji, kinaso kice ni ba ‘yarsa bace ko me? Kinaso kice yaya Faty ce kawai ‘diyarsa?….. ” Sai snn Hajiya Karima tayi realizing me take cewa, da sauri ta ri’ko hannun Laila tana son zaunar da ita….” Girgiza kai Laila ta soma tana fa’din wllhi sai kin fa’da min komai waye uba na?
“Hajiya Karima ido a ‘ke’kashe tace” banso kisan wnn ‘boyeyyen sirri yanzu bam amma Allah ya ‘kaddari yanzu zaki sani.
“Laila, Alhj Ma’aruf da Alhj Mumtaz sun kasance aminan juna, Alhj Mumtaz ya kasance hamsha’kin ‘dan kasuwa wanda tun yana da ‘kuruciya Allah ya albarkaci kasuwancinsa, toh a dalilin amintarsu da Alhj ma’aruf yasa shi jawosa cikin kasuwancin, wanda bayan ya bu’de kampaninsa me suna Mumtaz builders daga baya ya maida sunan Companyn M&M Builders wato Mumtaz & Ma’aruf knn, ni kwa na kasance ina zuwa aikatau gidan Alhj Ma’aruf, a lokacin ina ‘yar matashiyan budurwa, ita kuwa Hajiya Hindatu ta girme mun sosai babu ma ha’di, sun jima da aure itada mijinta Allah bai basu haihuwa ba, kullum suna sha’awan ‘ya’ya musamman idan suka ga ‘dan Alhj Mumtaz da Nazif matarsa Hajiya Salma, kullum cikin addu’an Allah ya basu haihuwa suke amma shiru babu haihuwa.
“Watarana Hindatu take cewa ‘kawarta Salma itakam tana so mijinta ya sake aure ko Allah zai basu haihuwa. Salma tace kiyi ha’kuri Hindatu, haihuwa lokaci ne da zaran lokaci yayi sai kiga an dace…. tunda na la’be naji wann zance, dukda ‘karancin shekaruna a lokacin saida na shiga na fita nayi yanda nayi, Alhaj Ma’aruf ya aureni, Salma matar Alhj Mumtaz ita tayita bawa Hindatu baki lokacin da suka fuskanci nice a matsayin amaryar da akayiwo wa Hindatu.
“Muna zaune a haka shekaru suka ‘danja, Hindatu ta ri’keni tamkar ‘kanwa bata nuna min komai, nima de shiru babu haihuwa har abin ya soma damuna, ana haka kwatsam Hindatu ta sami ciki, aikuwa zo kiga murna wajen Hindatu da Ma’aruf harma da aminansu guda biyu suna taya su, nan fah hankalina ya tashi sosai, na shiga na fita amma Allah ya ‘kaddara sai Hindatu ta haihu, cikinta wata tara kuwa ta haifo ‘diyarta kyakkyawa. Nan kulawan Ma’aruf ya koma kanta kwacaukam dama yana tsananin sonta bare ta haihu, nan fa na koma tamkar saniyan ware a cikin gidan, shiru shiru ban samu ciki ba, har diyar Hindatu Fatima ta soma girma yarinya me shiga ran jama’a, mussaman Ma’aruf Fatima ta shiga ransa sosai dan sunan mahaifiyar sa taci.
“Ana haka naji ‘kishin ‘kishin Hindatu nada wani ciki gashi ni shiru, aifa nan nace banci ta zama harta ‘kasashen ‘ketere sai na tsallaka dan nemo magani, a wnn yawo nawa nayi yo cikinki, babu maganin da bansa wa Hindatu ta mutu ba ita da binda ke cikinta amma shiru, wata rana da daddare na shiga har ‘dakinta na mur’kusheta da pillow har ta mutu ita da jaririn cikinta da baifi na wata biyu ba.
“Kuka wajen Alhj Ma’aruf ba’a magana, babu yanda Salma batayi abata Fatima ‘diyar aminiyanta ba amma fir na’ki, nace kaji kini bini banza haka nayita falfala mata rashin kunya dole ta ha’kura shima Alhj ma’aruf nason kasancewa da Fatima dan tana debe masa keyawan uwarta. Bayan na haifeki ne kuka taso Fatima a matsayin yarki, koda Fatima ta girma takai aure aka mata aure, nan fa na soma tuanain watarana dukiyan Alhj Ma’aruf zai zama mallakinta ita ka’dai idan tana raye, a lokacin sunso juna ita da Nazif ‘dan Alhj Mumtaz da Hajiya Salma, amma fir naki bari suyi aure, dan kuwa sai abinda nace, hana Nazif auren Fatima danayi ba ‘karamin tashin hankali ya shiga ba, tindaga wnn lokaci yayi tafiyarsa can ‘kasar America yaci gaba da karatunsa, bayan tadiyansa na tilasta aka aurawa Fatima wanda bata so, dan kuwa Nazif shine masoyinta.
“Koda Nazif yaji Fatima tayi aure nan yace bazai dawo Nigeria ba, har ya sami wata wacce suka ha’du a makaranta ya aureta suka hayayyafa.
“Toh Fatima ta jima bata haihu ba, har kema kika kai aure, sanda naga Fatima ta samu ciki na tabbata watarana dukiyan Ma’aruf zai zama mallakinta da abinda ke cikinta toh tunda ga nan na mata asiri ta haukace ta shiga uwa duniya, wanda daga baya nace maku ta mutu, muka ha’da baki da mijinta bayan na cika masa aljihu da makudan kudi mukace ma Alhj Ma’aruf mutuwa tayi ita da abunda ke cikinta, har rana me kaman tayau bamusan yanda ta dosa ba, ko ta haifi abunda ke cikinta oho mata, ko bata sai Allah, amma boka ya tabbatar mani bata sake dawowa cikin rayuwata ba.
“Hajiya Karima ta ri’ko hannayen Laila tace” Laila duk wnn abubuwan danayi nayisu ne dan inganta rayuwarki dana ‘diyarki Aziza. Kinga yanzu ko Ma’aruf ya mutu dukiya de namu ne mu ka’dai, ni da ke da kuma ‘diyaki Aziza, snn ni nayi sanadiyan mutuwan Alhj Mumtaz duk dan wnn Company da ya tsolen ido ya dawo mallakin mu. Bayan na gama sa ran Nazif da uwarsa Salma bazasu dawoba kwatsam sai su dawo rayuwata. Bazai ta’ba sakuwa ba. Dole musan abinyi. Dole mu kashe mijinki ki auri Nazif…..
“A zabure Laila ta mi’ke tana duban Hajiya kafin tace” A kashe mijina kuma hajiya, tsaki hajiya tayi tace” yo se me? Ke barin fa’da maki Nazif yafi wnn mijin naki komai da kika sani, a sanin da na masa da kyakyawan saurayi ne wanke hannu ka ta’ba, balle yanzu da Amurka ta da’da goge fatarsa.
“Murmushi Laila ta soma kafin tace” Kai Hajiya baki da ‘dan’danin imani, aiko tundp a baya tun inda ‘kuruciyata idan nagansa yazo wajen yaya Fati wani haushi nake ji, dan bana mance kamanninsa, kuma har yanzu ina sonsa. Ta ru gume Hajiya tana fa’din shawarinki yayi Hajiya.

*4 years later*
*********************************

*Cibiyan goya marayu*
_Gidan marayu_….

“A hankali take takun sa’daf sa’daf har ta samu tafice daga ‘kofan, ta juyo tana kallon ta gefenta tace” Yusrah wllhi yaukam da wuri zamu dawo kafin Anty Larai ta capke mu. Yusra tayi dariya maras sauti tace” kai *Deejah* da’dina dake akwai tsoro, harara Deejah ta galla mata tace muje yana can ‘kasa yana jiranmu. A tare suka nufi yanda yayi parkin motarsa.
“‘Kwankwaswa sukayi ta glass din motan, aiko da sauri ya bude masu yana mayaudariyan murmushi yace” Deejah gayu bismillah, yamutsa fuska Deejah tayi tace ” kaga Safwan banson irin wnn kashe idon naka ni na fa’da maka ni ba ‘yar iska bace. Tsaki yusra tayi tace Deejah dan Allah ki shiga mu tafi kadin ‘yan sa idon Anty Larai su ganmu. Harara Deejah ta galla mata kafin ta shige gaban motan.
“Safwan kuwa dariya yayi yace a ransa kaji Deejah dai da wani maganar rainin hankali, tana aikin rawa a club tana ce mani ita ba ‘yar iska ba, ko ‘yar meye ita oho….. ” daidai nan sukayi parking a ‘kofar ” Amazing Club…..

πŸ‘ΈπŸ»Queen SamyπŸ˜πŸ’„πŸ’‹……….
[8/18, 20:23] Umar Dalha: πŸŒ–πŸŒ–πŸŒ—πŸŒ— *Mallakin waye*

_Written by QueenSamy_……πŸ“

“Safwan na gama parking ya fito da sauri ya bu’ewa Deejah, harda wani na’de hannunsa ta baya guda daya ya ‘dan sunkuya kafin yace” here we are gwanar rawa… “Murmushi kawai Deejah tayi kadin ta sako ‘kafarta ta soma fitowa, takalmin ‘kafar high hill ne sosai ba’ki me ‘dan farin duwatsu, tana sanye cikin ash din top ta ‘daura black boyfriend jacket a sama, wandon jikin red ne sai veil red data ‘daura a kanta. Deejah budurwa ce ‘yar kimanin shekaru 19 ba fara bace snn bata layin ba’kake, ba wani kyau sosai take dashi ba amma ba’a kirata maras kyau ba, tana da kyaunta daidai misali, hakan nan gashin kanta me tsanti da tsaho ne, kyaun jikinta shi yafi komai ‘daukan hankalin da yawan mazan da sukayi tozali da ita, Allah ya mata diri irin na wacce zaka gani kace lallai wann ta cika mace. Deejah gwanar son rawa ce wnn dalili yasa tayi ‘kaurin suna a Amazing Club, takan je tayi rawa akan Stage mutanen da suke club din susha kallo yayinda da yawa suke mata ‘barin ku’di, da yawan maza suna son kawo ‘ko’kon baransu wa Deejah amma babu fuska, dan haka nan take da azaban masifa, bata barin kota kwana balle tayi tsami, wnn dalili shi ya ceceta daga idon maza ‘yan bariki ma’abota zuwa club. Safwan ne ka’dai Deejah take kulawa shima ‘din dan babu yanda ta iya dashine, ko fa’da ta nemo Sadwan ke tare mata, tun tana hantaransa har ‘karshe suka koma tamakr abokai.

“Yusrah na taka mata baya Safwan na gefenta suka shigo cikin club din, nan fah waje ya kacame da ihu da shewa da pito, fa’di suke ga Deejah ga Deejah, wasu kuma na fa’din the Great DD wato Deejah Dancer, tana isowa kuwa ta shiga’daga masu hannu nan ta haye kan stage gamida cire jacket din jikinta tayi jifa dashi, nan fah aka kuma saka shewa, wa’kan da take tsananin so aka saka mata nan ta soma rawa kama babu ‘kashi cikin jikinta. Nana aka soma tururuwan zuba mata ku’di Yusra na tarawa.
“‘Karfe 11:30pm daidai Deejah ta sau’ko daga kan stage ta jawo Yusra suka ke’be tace” Yusee we need to leave this place right now, Yusee ta ‘dan ha’da rai tace kai Deejah daren fah da saura, Deejah taja tsaki a hankali kafin tace” Yusee kindai san yanzu dole Anty Larai ta saka mana ido sabida gulman mu da ake kai mata ya soma yawa, kinga dai kallon malaman addini take min, yanzu idan ta gane ni ‘yar rawa a Club ne, me kike tunanin zai biyo baya.
“Yusee tayi murmushi tace” toh Deejah mu daina wnn sana’a mana, am pretty sure ku’din da kika tara yanzu zai isheki ki soma karatun jami’anki. “Deejah ta sau’ke ajiyan zuciya kafin tace” wllhi Yusee inaso nayi university yanda baki tsammani, snn inaso watarana na rin’ka taimakawa Orphanage foundation, ina tausayin wa’enda suka tashi babu iyaye iri na, rawan da nakeyi a club yana ‘daya daga cikin burina na tara ku’di dan taimakawa marayun da suke Orphanage, ba zallan wnn ba kinsan rawa hubby na ne.
“Yusee ta saka hijabinta kafin ta mi’kawa Deejah nata tace oya saka mu tafi, Deejah ta kar’ba ta saka gamida cire dogon takalmin ‘kafarta kafin suka fito can gefen titi.
“Safwan na zaune na jiransu cikin club ashe su tuni sun fice. Ta glass yake hango su suna ‘ko’karin taran mashi. Ai a sittin Safwan ya mi’ke ya fito ya nufesu. Kallon mamaki ya bisu dashi kafin yace da ‘dan mashin din “malam jeka abinka.
“Deejah ta ‘dan hararesa kafin tace” kaga Safwan yanzu gari yayi shiru idan ka kaimu za’a iya ganinmu. Murmushi Safwan yayi kafin yace” Deejah bazan iya barinku ku tafi ku ka’dai cikin daren nan ba, duk da nasan kun saba wuce haka a waje, but this is very risk, is dangerous, someone might harm you, bai jira cewansu ba ya ‘karasa ya kawo motarsa har gabansu yace oya ku shige mu tafi.
“Babu musu suka shige, a cikin mota Safwan yake cewa” Deejah meyasa baku so asan kuna wnn sana’a?
“Wata uwar harara Deejah ta watsa masa kafin tace” malam kaga this is non of your business, idan zaka kaimu muje, idan bazaka kaimu ba, fine ai dama ba saka mukayi dole ba….” murmushi ya kuma yi kafin yace” Allah huci zuciyarki, ni da zaki bi shawarata ma da kin bari na turo maganar auren….. ” bai gama rufe baki ba Deejah ta dakatar dashi” Au me? Kaga Safwan ni bance maka aure zanyi yanzu ba, karatu nake shirin farawa, kuma da kaga bamu so asan muna zuwa club a Foundation ‘dinmu sabida kar a mana aure ne, anaji za’a ha’damu aure da koma waye, idan har kana so ala’karmu ta ci gaba toh kaja bakinka kayi shiru, idan lokaci yayi naga zan iya aurenka fine….” Da mamaki Safwan ke kallonta bata ta’ba kawo masa magana makamanciyar wnn ba, wani da’di ne ya ziyarci zuciyarsa, shikuwa ko yaushene yana iya jiran Deejah muddin zata yarda ta auresa.

“A can hefen layinsu yayi parking kafin suka fice, cikin san’da suka shigo Orphanage ta ‘kofan baya, dan dama har spire key na ‘kofar garesu. Suna shigowa suka samu kowa yayi bacci, kai tsaye ‘dakinsu suka wuce, suna shiga suka soma shirin bacci… ” motsin da sukaji ne yasasu saurin rufe idanuwansu kaman masu bacci.
“Anty Larai ce ta shigo ta tarar suna bacci, a hankali ta rufe ‘kofar tayi ficewarta, tana fita suka bu’de ido ha’di da yin dariya.

“Washe gari da safe, Deejah tayi wankanta ta fito cikin shiri dan dama tana ‘daukan ajin yara a makarantar su dake cikin Orphanage, kai tsaye wajen karywa ta nufa, Anty larai na zuba wa yara breakfast Deejah ta ‘karaso, haba nan fa yaran suka soma Anty Deejah Anty Deejah, nan Deejah ta soma wasa wa yaran nan kaman yanda ta saba, Deejah akwai farin jini wajen yara da manya dake rayuwa a Orphanage, wnn dalili ne yasa wasu suke hassada da ita.
“Deejah ta kar’bi abincin daga hanun Anty Larai ta ci gana da rabawa yaran, bayan ta gama ne tace dasu” Ok kids kowa ya wuce aji ina nan zuwa, banda makara duk wanda ya makara zan masa bulala, tana fa’da tana masu alamau da hannu fuskanta dauke da murmushi. Da gudu yaran suka nufi wajen wanke hannu suka wanke kafin suka doshi ajijiwansu.
“Anty Larai ta dubi Deejah tace” Deejah dama akwai maganar da nakeso muyi, Deejah ta dawo da hankalinta gareta tace na’am Anty. Anty larai ta dubeta tace” Deejah maganganu akanki da Yusra a Foundation din nan ya soma yawa, labari ya riske cewa kuma yawon dare….” Da mamaki Deejah ke kallon Anty larai kafin tace” Haba Anty, meyasa zaki rin’ka ‘daukan zantukan mutane akanmu, kawai de hassada suke yi damu, ta juya tana watsawa Tani dake can gefe harara kafin taci gana da fa’din “Anty fa’da mun wacce munafukar ne ta kawo maki wnn labarin ‘kanzon kuregen, yanzu taga yanda koyawa muafuki hankali, kawai dan sunga kinaso na shine bari a nemi hanyar rabamu, ta ‘karsa gaban Tani tana girgiza taci gaba da fa’din” wllhi duk munafuncin munafiki duk sa idon basa ide nan gani nan bari, haka zai ganmu da Anty Larai ya barmu….” Tani cikin ‘kuluwa ta mi’ke tana fa’din” ke da wa kike. ” Dake nake good for nothing hypocrite…. nan fah fa’da ya soma tashi tsakanin Tani da Deejah, a fusace Anty Larai ta ‘karaso tana masu fa’da, Yusra kuwa hayaniyar da taji yasata saurin fitowa cikin uniform dinta da alama makaranta zata dan ita bata gama sakandare ba,
“Sosai Anty Larai ta masu fa’da, Tani rai ‘bace ta bar wajen, Yusra sulum sulum zata wuce Anty Larai tace” zo nan yusra, Yusra ta zaro ido tace na’am Anty, kinjini sarai, Anty larai ta bata amsa, Anty zanyi lattin sch…. kallon da Anty larai ta watsa mata yasata saurin ‘karasowa.
“Ku fa’da mun gaskiya kuna fita da daddare kokuwa, ‘kwalla ne ya ciko idin Deejah, ganin haka yasa jikin Anty Larai yin sanyi, dan kuwa tana tsananin son Deejah, wani sa’in daughter ma take kiranta, wasu nannys a wajen ma Deejhn Larai suke kiranta. Da sauri Anty larai ta ‘karasa ta ri’ko hannun Deejah ta dubi yusra tayi mata alama da hannu kan ta tafi. Yusr hamdala tayi a ranta kadin ta fice.
“Hannu Anty larai tasa ta soma sharewa Deejah hawayenta kafin tace” Deejah, you’re like a daughter to me, bana son abunda zai sameki, tun tasowarki kimsan da haka, duk fa’din gidan nan babu yarinyar da nake so irinki, kowa ya maki shaida da hali na gari, ba yara ba ba manya ba, ina tsorin kar ki ‘bata rayuwarki. Dole na damu da jin zance da yake tashi a gidan nan, yau idan labarin nan ya isa ga gwamnati kinsan hukumcin aure za’a maku da kowaye, so banaso haka ta faru dake daughter, da inada halin turaki makarantar gaba da sakandare da na turaki, kin sani nan foundation zuwa sakandare kawai ake biya maku, nima ‘dawainiya sunmin yawa ne ga iyayena ga marayun ‘ya’yana, bacin haka kinsan babu abunda bazan maki ba…..” rungumeta Deejah tayi kafin tace” kiyi ha’kuri Anty larai, nima ina sonki donke uwace a gareni, mutane ne kawai suke neman rabamu, insha Allah bazan ta’ba baki kunya ba.
“Anty larai tayi murmishi tace” that’s my girl, maza jeki koyar da yaranki nasan suna can suna jiranki. Da murmushi ta wuce ta shige ajin yaran nan suka soma tsalle ita da yaran dan dama rabin karatunsu talle ne da rawa a ajin Deejah…

**************************************
*Maxico*
_Chicago_

“Yana zaune kan wata benchi dake gefen hanyan street ‘din da zai kaika _mexico city_ dake a birnin _Chicago_, shigan da yayi zai tabbatar maka lokaci ne na sanyi, yana sanye cikin gray shirt da blue jeans, ya ‘daura ba’kar jacket a sama hannayensa rufe ciki hand gloves, ‘kafarsa sanye cikin ba’kar booth, gashin kansa sai fifituwa yake alamun iska na ka’dasu. Kallon mutane yake yanda suke ta wucewa a lokaci guda kuma yana sipping hot coffee ‘din dake hanunsa.
“Wayansa ne ta soma ringing, ya ajiye coffe din a gefe kafin ya ‘daga wayan da fari’ansa ganin granny dinsa ce me kira.
“Hello my amazing granny, how you doing pretty.
“Murmushi Amma tayi kafin tace” Irfaan bazaka canza ba knn, yanzu kuma me ya kaika Mexico daga Los Angeles, jiya daddynku yace mun kana Chicago,
“Murmushi Irfaan yayi kafin yace” there you go again granny,…. da sauri Amma ta katse sa, kaga ni idan kana magana dani kayi hausa dan nasan yanzu da kyar idan baka mance hausa ba.
“Dariya me sauti Irfaan yayi kafin yace” Come on granny you know am not use it, I can’t speak it fluently. Koma de yaya ne haka nake so kamin, Amma ta fa’di,
“Murmushi yayi yace” Alright fine, na gama final exams dina so sai na ‘karaso nan Mexico zan ‘danyi spending couple of days, sai na koma States, daga nan kuma idan na kammala ha’da takarduna zan zo Nigeria na ganku, dan am damin missing you guys.
“Murmushi Amma tayi tace” muma muna son ganinka Irfaan, nan suka soma hira sosai da Amma kafin ya tambayi kowa, Nilam ne ta shigo ta girma tayi wayo, yarinya ‘yar shekaru hu’du, Amma ta bata wayan ta shiga masa surutun gwalamniya…

 

“Aziza ne kwance jikin Mum dinta Laila sai shar’ban kuka take, Laila ma sai matso hawayen ‘karya take. Hajiya Karima sai faman basu baki take, itama tana sharan hawaye.
“Amma tayi sallma ta shigo cikin parlorn dake cike da mutane ‘yan kar’ban gaisuwa, rabonta da Hajiya Karima tun mutuwan mijinta Alhj Mumtaz sai yau suka ha’du wajen kar’ban ta’aziyan mijin ‘yarta Laila, ga mamakin Amma sosai Hajiya Karima ta tarbeta sai nan nan da ita takeyi. Amma ta masu ta’aziya gamida shawarwari na ban ha’kuri wa Laila. Amma ta dubi Hajiya Karima tace Nazif yana tare dasu Alhj yana so ya shigo ya maku ta’aziya, da sauri Laila ta ‘dago kanta jin an ambaci Nazif. Hajiya Karima ta washe baki tace ya shigo mana, ta dubi wata yatinya dake gefe tace maza ce masa ya shigo. Amma tace a’a barin masa waya sai ya shigo.
“Engr. Nazif Mumtaz wanda a halin yanzu yake da shekaru 52 a duniya idan ka gansa zaka zata dan shekara 40 ne, yana sanye cikin ash din jampa da hula sallamansa cikin muryansa me cike da charisma ya daki dodon kunnuwansu, aiko nan Laila ta ‘dago kai tana binsa da kallo, bata yi tsammanin haka ya koma ba, ko gasan matasa ya shiga wnn zai lashe, sanda yake gaida Hajiya Karima sai nan nan dashi take, koda tace masa ga Laila su gaisa, bai ko kalleta ba ‘kasa yake kallo har suka gama gaisawa, Laila ko wani mayen kallo ta bisa dashi har ya fice, ta gama ayyanawa a ranta ta samesa an gama. Haka har bayan kwana uku Hajiya Amma tana zuwa kar’ban gaisuwan mijin Laila, ita kanta Amma tana mamakin canzawan da kishiyar marigayiya aminiyarta tayi wato Hajiya Karima, wani sabon ala’ka ne take son ‘kullawa a tsakaninta da Amma.

“Yau ta kama alhamis, Anty Larai ne zaune tana kallon labarun tara a NTA, nan ta hango gidan wani ta’aziya ana nunawa, kaman daga sama aka hasko fuskan uwar ‘dakinta da ta jima da barin ‘kasar nan ta koma America, zama ta gyara tana kallon, ai kuwa ba gizo take mata ba, ita ce dai Hajiya Salma jwar ‘dakinta a da kafin ta soma aiki da cibiyar goya marayu……

Leave a Comment