*_MAKAUNIYAR ƘADDARA😭_*
*_Bilyn Abdukk ce🤙🏻_*
*_Da sunan ALLAH mai rahama mai jinƙai. Ya UBANGIJIN al’arshi ka bani ikon rubuta abin zai amfani al’ummar MANZON ALLAH. Ka tsare harshena da alƙalamina rubuta abinda zai cutar da ni da duk wanda zai karanta littafin nan. Ka bani ikon rubuta abinda zai amfaneni duniya da lahira ni da masu karatun._*
*_Ina mai farin cikin sake dawowa a wannan karon tare da ƴan uwana, yanda muka fara lafiya ALLAH ya sa mu gama lafiya, UBANGIJI ya bamu kariya yay riƙo da hannayenmu baki ɗaya._*
*_Ya rabbi ka gafartama Mahaifina da sauran al’umma da suka rigamu gidan gaskiya. Idan tamu tazo ALLAH yasa mucika da imani. ALLAH ka wajabta mana tsoranka da soyayyar MANZON ALLAH😭🙏🏻._*
_Zafafa Next level_
*Page 1*
…………..“Inada tabbacin wannan itace tashar da zaki iya samun motar duk wani gari da kike buƙatar zuwa”. Mai napep ya faɗa dai-dai yana samun wajen fakin, da ɗan karkato kansa yana duban yarinyar dake a baya zaune.
Batace da shi komaiba. Sai ƙoƙarin kwance haɓar zaninta da takeyi jikinta na rawa. Ta miƙa masa ɗari biyar ɗin dake a ƙudundune saboda uban ƙullin da tasha a cikin zani. Baki ya buɗe kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya ɗan fisgi ƙudundunanniyar ɗari biyar ɗin daga hannunta yana ƙunƙuni ƙasa-ƙasa.
A yanzu ɗinma batace da shi komaiba, sai hawayen dake famar zarya daga idanunta zuwa kumatu.
Tsohuwar ɗari biyu guda biyu da naira talatin a sama ya miƙa mata fuska a tsuke.
“Nagode”.
Ta faɗa a karo na farko tana amsar kuɗin. Batare da ta jira amsarsaba ta fito daga Napep ɗin tana kalle-kalle da ƙoƙarin sake maida kuɗin daya bata a haɓar zani ta ƙulle kamar ɗari biyar ɗin ɗazun.
A kallo ɗaya zaka iya fahimtar ƙarancin shekarunta. Dan kuwa bazata wuce shekaru sha huɗu ba. A tsarin halitta batai kama da mai taɓin hankaliba, amma a yanayi zaka iya kiranta da mai ƙarancin hankalin. Duk da kuwa babu wani datti ko makamancin hakan a kaf illahirin jikinta.
Ƙara kai hannu tayi ta share hawayenta a karo na babu adadi, cikin rauni da alamun tsoron dake tattare da ita ta furta, “ALLAH gani gareka. Da kai na dogara, a gareka kuma nake buƙatar taimak……”
“Ƙanwata ina zakije?”.
Karaɗin wani kwandasta ya katseta batare da takai ƙarshen addu’arta ba. Kallonsa tai da jajayen idanunta dake a kumbure saboda kuka tace, “Danya”.
“Danya? Ƙanwata sai kinyi ƙarin bayani, dan nikam bamma taɓajin sunan wannan garin ba”.
Shiru tai alamar nazari, ‘Gaskiyar kwandasta ɗin nan. Danya dai garinsu motama bata shiga sosai. To amma idan bata mantaba lokacin da zasu taho da Hajji Lanti bayan sun fito daga Danya a mashin, a Gozarki suka kwana, washe gari kuma daga Gozarki sukazo kusada, anan suka sami motar Katsina’.
“Wai kodai bakisan ina kika dosa bane ƴammata?”.
Kwandasta ɗin nan ya sake katseta. Da sauri tace, “Kusada zanje”.
“……Kusa da kano, nesa da birnin katsina” kwandasta ya faɗa cike da barkwanci. ita dai batace da shi uffanba, sai ma faman waige-waige da takeyi, har yanzu akwai tsoron ko wani zai iya biyo bayanta tattare da ita.
“Kinga ga motar da zaki hau can ta kaiki Gidan mutum ɗaya. Inada tabbacin daga can zaki samu motar kusada ƴar ƙyaƙyƙyawa”.
“Nagode sosai” ta faɗa tana ɗan risinawa. Daga haka tai gaba da sassafa batare data sake bi takansa ba.
Tana isowa motar daya nuna mata ko jiran ba’asi bata tsaya yiba saboda jin kwandasta ɗin motar nata faman faɗin, “Charanci, kankia, Gidan mutum ɗaya, Tsanyawa, Bichi, har kano.
Can baya ta shige inda wata mata ke zaune ita da yaranta biyu da bazasu wuce sa’annintaba. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya dasa hannu ta gyara ɗan labulen jikin gilashin yanda take fatan ko su Hajiya biyota sukayi bama zasu iya ganinta ba. Duk da hakan kuma roƙon ALLAH take a ranta ALLAH yasa motar ta cika da wuri su tafi.
Addu’ar tata kuwa ta amsu. Dan ko cikin ƙanƙanin lokaci motar ta cika. Ita dai tana duƙunƙune cikin hijjab har kanta. Ko wanda ya shigo ya zauna a gefenta bata kallaba sanda ya shigo. Ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya jin motar ta ɗaga alamar zasu bar cikin tashar.
Sunyi tafiya mai ɗan tsayi data tabbatar sunbar cikin birnin katsina ta tsinkayi maganar kwandasta na ambaton kowa ya bada kuɗin mota. Ciro kanta tai daga hijjab ɗin bayan ta kunto kuɗin data ɗaure a haɓar zaninta na canjin mai napep. Jin matarnan mai ƴaƴa na tambayar “Nawane gidan mutum ɗaya” ya sata tsaida hankalinta tana jiran amsar kwandasta ɗin itama.
“Ɗari huɗu ne kuɗinki hajiya”. Ya bata amsa yana amsar kuɗin na kusa da shi.
Matar tace, “Haba ɗana adai duba. Wlhy jiya a ɗari uku-uku mukazo. Yaran nanma ɗari bibbiyu na biya musu”.
“Ai jiya kikace hajiya. Jiya kuma ba yau bace. Dan haka kuɗinki keda yaranki dubu da ɗari biyu ne”.
Zatai magana wani dake can gaba yay saurin amshewa. “A’a fa gaskiya ɗari uku ne, ni kaina ɗazun nan da safe nazo a haka”.
A take rigima ta kaure tsakanin kwandasta da matarnan da mutumin da yay maganar da safe yazo a ɗari uku. Da ƙyar dai aka tsaya akan ɗari uku da hamsin.
Ita dai yarinyarnan dama bata tanka ba. Ta miƙa masa ɗari huɗun da mai napep ya bata canji.
“Ƙanwata ina zakije?”.
A taƙaice tace, “Gidan mutum ɗaya”.
Canjin hamsin ya miƙo mata. Batare datace komaiba ta amsa ta maida a haɓar zaninta. Sai dai bata koma cikin hijjabinba tabi ayarin masu kallon hanya. Kasancewar motar mai lafiya ce bayan sallar la’asar kaɗan suka iso gidan mutum ɗaya. Danma sun ɗanyi tsaye-tsaye a hanya na sauke mutane.
A gidan mutum ɗayarma dai a rikicen take. Dan ba taɓa yin tafiya irin haka ba sai wannan karon. Sanda zasu tafi kuwa hajji Lanti ce tai musu komai. Da ƙyar ta samu ta tambayi wani yaro mai saida biredi inda zata sami motar kusada. Shine ya nuna mata. Tai masa godiya.
Ta iske ƙananun motoci kusan huɗu dake jere a kan hanyar da yaron yace mata itace hanyar kusada. Lokacin da suka tafi su tun daga cikin kusada suka shigo motar katsina.
“Ƴammata kusada ne?”.
Wani tsamurmurin saurayi ya faɗa yana nufota. Saurin ɗaga masa kanta tayi alamar eh. Cike da jin daɗi yace, “Yauwa taho muje, dama mutum ɗaya muke nema”.
Har cikin ranta taji daɗin hakan. Ya nuna mata jar motar data gama fita hayyacinta. “Yauwa shiga nan. Bayin ALLAH a matsa mata mu kama hanya ko”.
Cike da mita fasinjojin suka shiga muskutawa dan sama mata waje. badan wajen zai wadacetaba ta shiga ta zauna. Sai dai kasancewar ta mai ƙaramin jiki yasa bata takuraba matuƙa. Sai dai waɗanda ta tarar a ciki sunata faman mita sukam an takura musu. Direban ya cika haɗama da son kuɗi. Yanda direba bai tanka musuba itama bata tanka ba. Sai dai acan ƙasan ranta daɗi takeji zata koma gida taga Babanta da su Yaya Tinene, duk da su ba son ganinta sukeba.
Tsabar rashin isashshiyar lafiyar motar basu iso ba sai gab da magriba, dan sun kwashe kusan awa ɗaya da rabi a hanya. Ga tsaye-tsaye da suka dingayi ana sauke wasu da ɗauka a ƙananun ƙauyika har kusan sau uku.
Hankalinta bai tashiba sai da suka iso taga kowa na miƙawa direba ɗari da hamsin kuɗin mota. Cike da tashin hankali da fargaba ta miƙa masa naira tamanin ɗin da suka rage mata. Wani banzan kallo yay mata sheƙeƙe yana nuna kuɗin.
“Naga kina miƙamin murtala huɗu (80n), bakiga abinda kowa ke badawa bane?”.
Cikin rawar murya da cikowar ƙwalla a idanunta tace, “Wlhy su kaɗaine suka ragemani, dama ɗari biyar ce na taho da ita da ga katsina, to sai naba mai ƴar ƙurƙura……”
“K! dakata. Wannan damuwarkice ba tawaba. Inda kinsan baki da kuɗin mota da baki bari nayi jigilar ɗakkoki ba ai. Dan haka ni kuɗina kawai na sani ba wai yanda kika taho daga katsina ba”.
Sharr hawaye suka shiga sakko mata. Ta durƙusa a ƙasa zata fara roƙonsa, hayayyaƙo mata yayi da masifa. A take hankalin mutane ya fara dawowa kansu. Ita dai duƙe take tana kuka da roƙonsa.
A mutanen da suka taru wajen duk basu bata goyon bayaba. Acewarsu miyyasa bata faɗa masaba kafin ta shigo. Idan data faɗa in yaso saiya taimaketa. Suma ɗin haƙuri take ta basu ita dai, dan harga ALLAH batasan adadin kuɗin motar ba. Hakama direba da zugar mutane ke sake harzuƙawa yana mata tujara.
Tun tana roƙonsu a duƙe harta koma gurfane abin tausayi. A haka wani saurayi da tausayinta ya kamashi ya ciri naira ɗari ya bama mai motar. Daga haka suka sama mata lafiya. Har ƙasa ta duka taima saurayin godiya. Yace karta damu, tadai daina shiga mota babu kuɗi. Gara ma idan bata da shi ɗin ta dinga faɗa kafin ta shiga zaifi sauƙi. Godiya nanma tai masa ta miƙe riƙe da naira talatin ɗin daya sake rage mata tunada an biya mata ɗari.
A kusada ɗinma ba sanin ina zata gano hanyar garinsu tai ba. Dan tunda tasan kanta bata taɓa zuwa cikin Kusada ba. Iyakarta ƙananun ƙauyukan dake gefen ƙauyensu kawai.
Tana son tambaya tanajin tsoro, ga wani azababben ciwon ciki da takeji yana taso mata kaɗan-kaɗan. Duk yanda taso cigaba da tafiya sai ya gagara. Da ƙyar taja ƙafafunta zuwa wata runfa ta zauna. Da alama runfar mai yin faci ne. Kasancewar magriba tayi harya tashi.
Zama tai ta duƙunƙune kanta cikin kafafu jikinta na rawa. Ga wata irin zufa na keto mata ta ko ina saboda azabar ciwon ciki. Tun tana zaune har sai da takai kwance a wajen tana juye-juye. Bata damu da cinnakun daketa galla mata cizo ba a jiki, dan ciwon da cikin nata ke mata ya danne komai.
Tsahon lokacin data ɗauka a yanayin ciwone yasa har dare ya rufa bata saniba. Sai jin garin tai ya rage hayaniyar jama’a. Ba ciwon cikin bane kaɗai matsalarta harda Yunwa da ƙishi. Dan rabonta da abincin kirki tun jiya a gidan Hajiya. Abincin da aka bata a gidan da aka kaita ƙinci tayi sosai, dan tana tsoron taci su yanke mata kanta kamar yanda zuciyarta ke bata danshi suka kaita gidan.
Tashi tayi zaune a hankali tana ɗan waige-waige. Titin babu haske. hakama jama’a duk sun nufi gidajensu sai ɗai-ɗaiku. Duk yawan motoci da mashinan ɗazun yanzu babusu. Sai wasu da basu wuce uku ba. Mashinanma bazasu gaza haka ba. Sai fitilar mai shayi da take hangowa can a wajen da motocin ke tsayawa (Tasha).
Komawa tai ta kwanta. Dan haka kawai taji wani shegen tsoro ya turniƙeta. Ta rufe idanunta gam tana karanto abinda ta sani na addu’a. Cikin amincin ALLAH kuwa sai ga barci ya kwasheta. Da alama hakan nada nasaba da gajiyar dake tare da ita ta wahalar tafiya da gudun da taci kafin samun Napep..
★★★★★
Tun kiran sallar farko na asubahi ta farka da wani irin ciwon ciki. Murkususu ta dingayi tana kuka. Ta jima tana shan azaba kafin ya lafa mata. Zuwa lokacin anata ƙoƙarin shiga sallar asuba. Tashi tai a jikkace, dan yunwa takeji sosai. Ta taka a hankali zuwa inda massallacin tashar nan yake. Butocin da akai alwala ta dinga taɓawa harta sami mai ruwa. Ɗakkowa tai ta dawo wajen rumfarnan. Ta zagaya bayanta tai fitsari da yin alwala. Sauran ruwan kuma ta shanye. Sai a yanzune ta tuna ko sallar La’asar ɗin jiya batayiba. Rabonta da salla tun ta azhar da bayan idarwarta ta gudo.
A take ta fara maka sallolin nan batare da tabi tsarin daya dace na mai ramuwaba. Sai da ta gama jerosu har asubahi. Zuwa lokacin mutane nata fitowa, hakama masu mashina da motoci.
Da farko zaman kallonsu tayi. Daga baya kuma saita mike bisa shawarar zuciyarta. Ƙarasawa tai wajen mai shayin nan daketa ƙoƙarin ɗora tukunyar garwar shayinsa yana raira waƙar shata. bayan ta masa sallama ya amsa ta gaishesa da girmamawa dan babbane ba laifi.
“Baba dan ALLAH tambaya nake?”.
Ɗago kansa yay ya kalleta a karon farko. “ALLAH yasa na sani ɗiyata”. Ya faɗa da kafeta da kallon ƙurilla.
Kanta a ƙasa tana ɗan juya yatsun hannunta cikin juna tace, “Baba dan ALLAH inane hanyar Danya?”.
“Danya! Danya!?. To indai Danya dana sanice ta kusa da Gozarki hanyarta na nan gabas da mu”.
Jin sunan Gozarki ya sata kallonsa cike da jin daɗi. Ta kaɗa kanta fuskarta na sauyawa alamar farin ciki tace, “Eh itace baba”.
Yace, “To zaki zauna ki jira masu mashina dake shiga kenan. Idan kuma bazaki iya jiraba ki samu mai mashin anan ki biyasa talatin ya kaiki ainahin Gozarki ɗin anan zaki samu ƴan mashinan Danya”.
Taji daɗin shawararsa. Hakan yasata masa godiya. Duk da talatin din ta rage mata a jiki, kuma yunwa takeji gara tabi shawararsa. Babu wani jimawa kuwa ta samu mai mashin. Kamar yanda mai shayi ya faɗa talatin mai-mashin din yace zata bashi. Sai da ta bashima sannan ta hau.
Cikin mintuna ƙalilan suka iso Gozarki. Amma sai da ya kaita har hanyar ƙauyensu Danya. A take farin cikinta ya ƙara bayyana. Harta zauna da nufin jiran masu mashin dan babu wanda ya fito saboda akwai sauran safiya, sai kuma ta mike. Ba komai ta tunaba sai nasihar saurayin jiya daya cika mata naira ɗari. Bata da ko sile. Mizaisata zaman jiran mashin? Gara ta taka da ƙafa, duk da kuwa tasan akwai nisa. Amma ɗokin gata a kusa da gida sai ya gusar mata da komai har yunwar da takeji da rashin daɗin jiki.
Tafiya ta fara a doguwar hanyar jan birjin da batasan iyakar lokacin ƙarewarsa ba. Ga ɗan sanyin safiya na busawa kaɗan-kaɗan.
Tayi tafiya mai nisa ciwon cikin nan da batasan dalilinsaba a kwana biyun nan ya ƙara turniketa. Ƙarƙashin bishiyar dalbejiya ta samu ta zauna. Taci murƙususnta da kuka na wani lokaci kafin ta tashi ta cigaba da tafiya. Zuwa lokacin ƴan mashinan garinsu nata fitowa ɗai-ɗai da fasinjoji akai.
Kafin ta gama ankara rana ta ƙwalle. Ga yunwa na cigaba da ragaɗar hanjin cikinta. Haka ta cigaba da jurewa tana jan ƙafafu tamkar mai tsohon ciki. A lokacin da dukkan wani ƙarfinta ke gab da ƙarewa ne ta hango rufin ginin makarantarsu dake da matuƙar tsaho fiye da duk gine-ginen gidajen garin. Ta saki murmushin yaƙe idanunta dake ganin duhu-duhu na lumshewa. Sai faman sauke ajiyar zuciya takeyi da sauri-sauri. A hankali hajijiya ta fara juya mata hanyar, saiko gata ƙasa yaraf babu numfashi……….✍
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki💃🏻💃🏻.
*_★ AL-ƘIBLA_*💘
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*💖
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*💝
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*💓
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*💔
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za’a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
TEAM—-ZAFAFA BIYAR🔥😘🥰😍
[9/13, 3:44 PM] Mom Farooq: *_Typing📲_*
*_😭MAKAUNIYAR ƘADDARA!!😭_*
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
_________________________
Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg’s domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg’s sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg’s herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗
Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg’s domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali
Ina masu pimples
Tabo(spot)
Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance
Sister’s masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg’s insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba
Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki
Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu
Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself
100%tested nd trusted
Soap price:3k
Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free
Maiso kindly message 08062991549
Call 08064532391
Note:Babu inda zakusami mg’s herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏
Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝
Mg’s skincare
Mg’s bakery
You can still order ur birthday cake, cupcake,slice cake,meat pie,shawarma,samosa nd spring rolls for ur event @mg’s bakery
Kindly call or chat
07046881166
07067210195
08062991549
Masu bukatar abayas,takalma da jakunkuna,ashobe,laces d atamfofi, materials nd the rest
07046881166
👏🤝
_________________________
_ZAFAFA 5 NEXT LEVEL_
*Page 3*
…………Gajeje bata wani jima ba a ɗakin Inna tafito rai ɓace alamar dai wani rikicin suka sake tafkawa. Tana fita a gidan kuwa Inna ta fito a matuƙar hasale itama.
Ɗakin su Zinneerah ta shiga. Zinneerah dake zaune tana hawaye har yanzun sai jin saukar lafiyayyen mari tayi. Zabura tayi zata ƙwalla ihu Inna ta daka mata tsawa.
“Munahika yimani shiru kona lallasaki. Dan uban daya haiheki sheri da kikai shirin ƙullamani ashe? Wa billahillazi koda wasa kika sanarma wani a yanda kika bar gidanga sai na lahira ya hiki jin daɗi. Idan kuma kiji ƙarya don ALLAH ki hiɗi masu yanda akayi. Aradun ALLAH ubanki ma sai na ci masa bura-uba bamake kadaiba dan buhun ubanki. Lalatacciya kawai mai shegen nunkuhurci irin na uwarta”.
Ita dai Zinneerah kuka kawai take jikinta na rawa dan tsoron Inna da takeyi. Sai da ta gama zazzage mata ruwan bala’i iri-iri sannan ta fice a ɗakin.
Kuka kam Zinneerah ta shashi matuƙa. Ga ciwon da cikinta kanyi lokaci zuwa lokaci. Dawowar Sa’a gidan da kayan ɗanwake ta samu tsagaitawar kukan saboda lallashinta da Sa’a ta zauna yi. Ganin yanda Sa’a ta nuna matuƙar damuwarta yasata shanye sauran kukan nata dan ba yaune farauba a gareta ga halin Inna matar ubanta.
WASHE GARI.
Da safe kamar yanda ta saba kafin tayi tafiya tanayin sallar asubahi ta fito tsakar gida ta hau shara. Duk da sanyin dake busawa na sanyin safiya haka taima tsakar gidan ƙwal da shara, ta gyara turken dabbobin Inna ta zuba musu sabon abincinsu. Sannan tazo ta fara haɗa wuta. Cikin dauriya take komai, dan wani irin zazzaɓine ke ratsa dukkan ɓargon jikinta a hankali. Haka ta cigaba da daurewa harta kammala dukkan ayyukanta wajibabbu a gidan.
Babu wanda ya fito a mutanen gidan sai can gyallowar rana. Sa’a ce ta fara fitowa tana mata sannu, sai ga Tinene ta fito itama tana mika da hamma dan sai yanzu zatai sallar asuba. Can sai ga baba ya shigo gidan, da alama tunda ya fita salla masallaci bai shigoba sai yanzun.
Dukawa sukai har ƙasa ita da Sa’a suna gaishesa. Ya amsa idanunsa aka Zinneerah da ya kwana da damuwarta a cikin ransa. Murya ƙasa-ƙada dan kar Inna taji yace, “Zinneerah yaya jikin naki?”.
“Da sauƙi Baba”. Ta amsa kanta a ƙasa.
Kafin ya ƙara cewa wani abu Inna ta fito wuff. Da sauri yabar wajen saboda wani shegen kallo mai kama da harara data watso masa. Taja tsaki tana duban Zinneerah dake durƙushe har yanzu.
“Ki tashi ki ɗebo mani ruwan rahi dan randunan gidanga duk babu ruwa. Kuma na rahin yamma nakeso dan ruwansa yahi garɗi da haske”.
“To inna. Ina kwana?”.
A takaice ta amsa mata tana karasowa wajen murhun inda wutar da Zinneerah ta haɗa ta kama sosai.
Fuskar Sa’a babu walwala tace, “Inna dakin barta sai anjima rana ta ƙara dagawa sama, kinga akwai sanyi garin sosai”.
“To uwata, yanda kikace ai haka zanyi”. Inna ta faɗa a hasale..
Shiru Sa’a tayi, dan tasan gatse Inna tai mata.
Zinneerah dama bata tsayaba, tuni ta ɗauki botikin fenti da hijjab ta nufi ƙofar fita cike da dauriya. Hakan ba sabon abu bane a gareta, shiyyasa fita ɗibar ruwan a yanzu bai dametaba. Kawai yanda takejin jikinta babu daɗine matsalarta. Amma haka ta nausa kanta hanyar jeji domin ɗebo ruwa. Harta isa babban rafinsu da su kansu basusan iyakar inda ya tsayaba bata haɗu dako kare ba. Ta ajiye botikin a gaban rijiyar da aka gina a tsakkiyar yashi wadda bawani zurfine da itaba. Hasalima a gabanta ake duƙawa asa kwano a kwarfo ruwan dake kwance. Bismillah ta ambata tana saka kwanon cikin ruwan, sai da ta kwashe na ciki tas ta watsar waje sannan ta jira ya sake taruwa ta diba a botikin nata. Bayan ta cikashi taf ta miƙe da ƙyar ta ɗora bisa kanta.
Koda tai sallama Sa’a ce kawai dake wankin baki da gawayi ta amsa mata. Inna ko dake bakin murhu tana yanka tuwon dare daya rage tana jefawa a ruwan data saka a wuta ko kallonta bataiba. Hakama Tinene dake gefen Innar tana shan koko.
Sai da ta wanke duk randunan gidan guda huɗu sannan ta juye ruwan ta Sake komawa. Haka ta dinga kai kawo tsakanin gida da rafi ɗibar ruwa. Tun bata haɗuwa da kowa har mutane suka fara fitowa. harma da irinta masu zuwa sakkon ɗibar ruwan na rafi. Duk wanda ta haɗu dashi gaisuwar mutunci ce tsakaninsu. Har ALLAH yasa ta kammala gaba ɗaya.
Zuwa yanzu Inna ce kawai a gidan, Baba ya fice wajen sana’arsa. Sa’a da Tinene kuwa sun ɗauki tallar gyaɗa da Riɗi da itama tasan tata tallan na jiranta ne.
Sai da ta gama ɗauraye ƙafafunta da sukai futu-futu da ƙura tazo inda Inna ke tankaɗen garin ɗan-wakenta.
“Inna na gama ɗibar ruwan”.
Yanda tai maganar murya na rawa yasa Innar kallonta. Duk da yanayinta ya nuna bata jin daɗi hakan baisa Inna tambayarta ba. Sai ma sake tsuke fuska tayi da faɗin, “Zauna inason magana dake”.
Babu musu Zinneerah ta zauna duk da ranta fal tsoro.
Ƙare haɗe fuska Inna tai tana dubanta da ƙyau. A tsawace tace, “Miya maidoki garinga?”.
Sosai gaban Zinneerah ya ƙara tsananta faɗuwa. Murya na rawa tace, “Inna sune suka koroni. Sunce basa buƙatar baƙauya irina. Kuma saida suka shinhiɗa mani uban bugu da aibantani kahin su bani jikka biyu da rabi su sani a mota….”
“Munahika, halan wata tsiyar kika ƙulla masu acan? Saboda kina buƙulu da abunda zan samu na hassahi daga kuɗin aikin naki?”.
“Wlhy Inna ba haka bane. Matar gidance bata sona dai na rantse”.
“Ruhwa mani baki dan bantan ubanki. Ai hajji Lanti zatazo ne, zanji gaskiyar zance a gareta. Wa billahillazi naji saɓanin abinda kika hiɗi yanzu ina halakaki na halaka banza wohi babu mai sanin yanda akai. Ƴar banza, kinhi son mu zanna ga ƙugunki ga nawa a gida. Sabidda kina kishi dani tunda uwarki bata gida? To mu zanna ga hili ga mai doki ai. Dan uban mutum yayi idan yana iyawa dani ko. Tashi ɓacemin a ido kahin naita tsinarki har se zaman Danya ya gagari ubanki ma bake kaɗai ba”.
Mikewa Zinneerah tai tana shartar hawaye. Duk da cin zarafi ga inna ba yaune farauba a gareta. Sai na yau ɗin yay mata zafi ainun. Karon farko taji tana kwaɗayin son sanin inda mahaifiyarta ke rayuwa a yanzu.
Ɗakin kwanansu ta shige, ta faɗa akan yamusashshiyar katifar da Yaya Sa’a da Tinene ke kwana. Dan ita bisa tabarmar karauni take kwana kamar yanda Inna take buƙata. Dauɗaɗɗun kayan dake gefe ta jawo ta shiga rufawa a jikinta saboda sanyi da takeji.
Sosau ta ringa rawar sanyi tana sambatun zazzaɓi. Har tsahon lokaci babu wanda ya shigo ɗakin. ba kuma ta ƙarajin motsin Inna ba. A haka barci yay gaba da ita mai nauyi.
“Zinni!! Zinni!!. Wai dan buhun ubanki baki jina inata kware baki?”.
A firgice ta tashi zaune jin irin kiran da Inna ke ƙwalla mata tamkar ana yaƙi. Ta amsa a kasalance tana ƙoƙari janye kayan data nausama kanta gefe dan ta samu damar mikewa.
Fitowar tata yay dai-dai da shigowar Yaya Gajeje gidan da sallama. Inna ta sake tsuke fuska tana kallonta. sai kuma ta ɗauke kai ta maida ga Zinneerah dake fitowa tana rawar sanyi da yamutse fuska alamar bata da lafiya.
“Oh sannu ƴar gata! Ina nan tsaye ke kina can kina jan nashari a ɗaki? To kizo ki haɗa mani wutar ɗan wake kar rana tayi..”
Da sauri Yaya Gajeje tai saurin tare numfashin Inna, “Haba Inna, wane haɗa wutar ɗanwake kuma kike magana haka? Diba kiga yanda take rawar ɗari da alama bata da lahiya”.
“Mtsoww!!” Inna taja tsaki. Kafin ta cigaba da magana a hasale. “To ina ruwana da ciwon nata. A yanzu ma wagga duniya waye ke da lahiyar. Gajeje ki hita idanuna, karki kaini maƙurar randa zan maki bankaɗa wallahi”.
Murmushi Gajeje tai tana kaiwa zaune. Cikin kwantar da murya tace, “To inna idanma kin mani bankaɗa ai kin isane tunda kece kika haiheni. Ni dai kin sanni ban ganin gaskiya na riheta ai. Amma dai kiyi haƙuri ni bara na haɗa miki wutar tunda ita batajin daɗi. Harma sakin danwaken yau nice zan miki Innarmu kwantar da hankalinki”.
Baki taɗan taɓe. sai dai batace komaiba. Hakan yasa Gajeje fahimtar taci nasara. Tai murmushi da tura hannu a zaninta ta ciro leda dake a lalitarta ta bujen ciki. Goro ne da alawa da biscuits guda biyu ƴan goma-goma. “Innarmu ga kayan suna”. Tai maganar tana miƙa mata.
Ɗan sakin fuskarta tayi da miƙa hannu ta amsa. “Yo kuma ƙya bani duka. Su su Rabi’u fa?”.
“Karki damu na ba Salame ta kai musu nasu suma. Wannan nakine. Nima Agali ya bani shi bayan mun hito”.
“To, to maddala. Ni bamma sami leƙawaba yau na tashi da ƴar mashashshara ne. Sai zuwa anjima zanje nai masu an raɗa suna. Miye sunan ɗiyar ne?”.
“Ai Hadiza aka samu, sunan Innar Bilkin aka saka”.
“Tofa ɗigifi. Shi yanzu duk yawan gidansu ya rasa wazai saka sai sunan uwar matarsa?”.
Ƴar dariya Gajeje tayi tana yafito Zinneerah dake tsaye rakuɓe jikin bango da hannu. “Inna kenan, ashe babu daɗi Lawal ya sakama Ummita sunanki shima”.
Shiru tai bata tankaba. Dan an ƙure tsoguminta kenan.
Zinneerah ta zauna tana gaida Gajeje. Cike da kulawa ta amsa mata da kai hannu a jikinta. Jin uban zafin ya sata ambaton, “Ya subahana. Zinni ai masassara ce a jikinki sosai. Kin karya dai ko?”.
Ƙasa Zinneerah tai da kanta tana haɗiye hawayen dake neman zubo mata. Dan harga ALLAH yunwarma tanajinta mai tsananima kuwa. Saboda Inna batai mata tayin abinciba yasa ta haƙura.
Shirunta yasa Yaya Gajeje fahimtar bataciba ɗin. Tasan za’a rina. Dan innarsu lamarinta sai du’ai. Bata sake cewa komaiba kamar yanda itama Innar bata tanka musu ba. ta dai miƙe zuwa gindin murhun inda tukunya ke aje saman duwatsun murhun. Tuwone a ciki na dawa da aka yanka aka ɗumama. Duk ma ya zama gutsatstsari alamar masu gidan sunci. Yaya Gajeje da ranta ke mata ƙuna ta ɗauka kwano ta zubama Zinneerah, tare da koriyar miyar kukar dake gefe. Har gabanta takai ta dire tana fadin, “Maza ci na samu mai sayo miki magani nan gidan Rahine idan bata fita tallar kayan koli ba”.
Jan kwanon Zinneerah tayi gabanta, babu musu ta hau ci dan yunwa takeji sosai..
Inna dai bata sake tankawaba har Zinneerah ta gama cin tuwon nan. Yayinda Yaya Gajeje ta koma can wajen murhu tana haɗama Inna wutar ɗanwake da ƙoƙarin saka ƙatuwar tukunyar da take amfani da shi.
Kasancewar Yaya Gajeje a gidan yau sai ta samu ƴar salama. Dan har Baba daya shigo shima ya ɗan samu sakewar bata kulawa, harda siya mata awara.
Washe gari kam Inna bata saurareta ba. Duk da ta fahimci har yanzun bata da lafiya, dan ba’a ƙulla awa biyu Zinneerah bata raɓe gefe tana riƙe cika ba alamar dai cikin na mata ciwo.
Sai dai tsabar rashin tausayi ko’a fuska Inna bata nuna ta fahimtaba, daga ƙarshema tallar riɗi da gyaɗa ta sakata ɗauka. Da Sa’a tayi magana kuwa ta hayayyaƙo mata da masifa kamar zata daketa. Dole tai shiru tana maijin babu daɗi da halin mahaifiyar tasu.
★★★
Yau satin Zinneerah ɗaya kenan da dawowa da ga Katsina. Tun Inna na zuba idon ganin Hajji Lanti ta biyo bayan Zinneerah harta fara sarewa. Dan har ranta ta ɗauki alwashin sai Zinneerah ta koma, bazata taɓa yarda kuɗin data ƙwallafa ran samu su wuceta a banza ba.
A ɓangaren Zinneerah kam a kwanakin nan daka kalleta kasan bata da lafiya. Musamman yanda ta wani rame sosai. Gashi sam bata da kuzari a jikinta. Yanda ta saba aiki ada da kazar-kazar yanzu sam bata iya hakan. Komai zakaga tana yinsane da sanyin jiki kamar mara ƙashi. Inna tayi masifar harta gaji ta barta, sai dai zagi da tsina ne tana shansa, dan ranar har marinta tayi.
Yau ma kamar kullum tana gama ɗibar ruwa da dukkan aikinta na gidan tai shirin ɗaukar tallar riɗi da gyaɗa. Tinene kaɗai ta samu a tsakar gida tana suyar wainar fulawa. Inna kuwa ta fice barka wai.
Ɗakin Inna ta shiga ta ɗakko ƙaton farin botikin da aka cika da gyaɗa da riɗi, ta sake fitowa tsakar gidan. Cike da sanyin murya tace, “Tinene idan Inna ta dawo ki hiɗi mata na wuce”.
Kallon banza Tinene tai mata ta ɗauke kanta. Cike da rashin mutunci tace, “Inma wannan allagiran kike mawa kima cire rai yarinya, dan aradu baki cin ko ranyo anan”.
Murmushi Zinneerah tayi kawai ta fice, dan tasan inhar ta biyema Tinene zama su iya faɗa, itako bata da wannan ƙarfin yanzu kam.
Dai-dai fitowarta ƙofar gidan nasu gabanta ya faɗi. Tai ƙasa da kanta saboda cin karo da fiska mafi daraja a zuciyarta bayan ta iyayenta. Ba kowa bane face saurayinta Babawo wanda a yanzu ya maida akalar neman auren nasa kan yayarta Karima da yaya Sa’a ke bimawa. Babawo ya sota tun bata san kantaba. Da farko matsin rayuwar data tsinci kanta a hannun Inna dalilin rashin mahaifiyarta a gidansu Babawo yake tausaya mata. Shine silar cigaba da karatunta bayan gama firamare , shine ya tsaya tsayin daka harta shiga makarantar gaba da firamare (Secondary), tana aji ɗaya wani kawunsa ya zo ya tafi da shi kaduna. Bai dawo ba sai da ya shekara. Kamar yanda ta ɗokantu da zuwansa haka shima ya ɗokantu da ganinta. Yazo mata da tarin tsaraba, tare da burin iyaye su shiga akan maganar aurensu, a cewarsa data kammala aji uku na sakandire zasuyi aure. zai wuce da ita can kaduna sai ta cigaba a gidansa har sai taga ƙarshen biro. Hakan yama Zinneerah daɗi a zuciya da ruhi, sai dai kuma a kwana biyu da zuwan Babawo labarin ya canja alƙibla. Dan kuwa bai komaba sai da tsuntsun soyayyarsa ya tashi daga kanta ya koma kan yayarta Karima yar wajen Inna ta uku. Ƙiri-ƙiri ta gaza gane kan Babawon ta, ya canja mata gaba ɗaya. Kosan ganinta bayayi. Taci kuka sosai, ta kuma shiga ruɗani, dan har ciwo tayi. Mutane sunta kace nace akan wannan al’amari, wasu na faɗin asiri Inna taima Babawo ɗin, wasu suce kuma shine dai yake ganin Karima ta fiye masa tunda ita babbar budurwace wadda akema surutu akan rashin samun miji. Dan Karima shekararta sha takwas da wasu watanni, a ƙauyen kuma sa’annin su Zinneerah sune dai-dai aure ƴan sha biyu. Amma sai dai ita ƴaƴan Inna dama sukanyi jinkirin samun miji a ƙauyen saboda mugun halinta, shiyyasa ma har yau babu wacce ta taɓa aure a nan cikin Danya. Gajeje na kauyen Sanni, Atine na can Rimaye. Sai yanzu ga Karima da Sa’a waɗanda duk sun zama manyan ƴammata. Karima nada sha takwas Sa’a na sha shida. Sai Tinene sa’ar Zinneerah itace auta.
Bayan wucewar ruɗanin canjawar Babawo da shekara ɗaya da wasu wattani, dan har manya sun shiga maganarsa da Karima sai kuma Inna ta haɗata da hajji Lanti da tai sanadin kaita birnin Katsina da niyyar aikatau, inda ita kuma ta gudo ta dawo gida……..
“K! Wai baƙyaji ana miki magana”.
Tsawar da Babawo ya daka matace ta dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi batare data farga ba. Saurin haɗiye hawayen da suke neman zubo mata tayi tana girgiza masa kanta.
Ta ɗan risina kaɗan tana faɗin, “Kayi haƙuri Ya Babawo banji bane wlhy”.
Tsaki yaja yana taɓe baki da jifanta da wani irin mummunan kallo na tsana, wanda a da idan wani yay kuskuren yimata irin wannan kallon sai inda ƙarfinsa ya ƙare. A gadarance yace, “Kiramin Karima nace”.
Idonta ƙasa-ƙasa tana mai satar kallon yanda ya ƙara ƙyau da cikar zati tace, “Yaya Kareema bata nan, tana Rimaye wajen Yaya Atine, nima ban dawo na sameta ba”.
Tsaki yaja yay gaba batare da ya sake tanka mataba. Ta bisa da kallo cike da tsananin so da ƙaunar da take masa har yanzun. yayinda ƙamshinsa daya bar mata take jinsa mafi daraja da tsada a cikin iskar da take shaƙa. Duk da ƙarancin shekarunta zuwa yanzu tasan minene soyayya, dan shine ya rene ta akan bigirenta, tun bata fahimta harta fara ganewa da banbancewa, sai gashi rana tsaka rabuwa tazo musu bisa tafarkin MAKAUNIYAR ƘADDARAR da batasan sila ko mafarinta ba, tunda har yanzu bazata iya faɗin dalilin rabuwar tasuba balle dalilin komawar Babawonta kan yayarta.
Hannu tasa ta sharce hawayenta tana gyara riƙon botikin gyaɗa da riɗinta ta cigaba da tafiya ranta na mata zafi da ƙuna………….✍

Leave a Comment