Books Reviews & FAQs

Mahaukaci Ko Boyayyen Masoyi Hausa Novel

MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI

BY

MARYAM YARMAMA

*DEDICATED TO*

MY FANS

 

_INTRODUCTION_

this is a interesting story that teach us more moral lesson about life,this,story has came with so many life styles and aloof our life leaving,i believe this long story will entertain readers

 

 

*APOLOGY*

AM SO SORRY MY FOLLIWERS I CANT CONTINUE ,THE STORY *CAPTAIN SHAYEEDA BUT I WISH ONE DAY I WILL CONTINUED,I NEED UR PRAYER

 

*starring*

Adorable minal

Stubborn gal aziza

Hansome guy annur

Play boy safwan

Ummi

Saudat

Hasiya

AND OTHERS……….

 

 

*VOTE OF THANKS*

zahrah bukar

Asykhaleel

Salma ali wada

Halal dady gal

Hauwa mamee

Maman hafsy(hajara)

Lubna(lalata writter)

Miss xoxo

Raz

Aisha gana

Pretty minnah

And others friends

 

 

 

*KANO CITY*

Kuka minal ta saki sakamakon mafarkin datayi na mahaukacin masoyi,kuka tafara tana wai yaushe zanga mahaukacin masoyina iye,mahaukacin masoyi ka nunamin kanka,meyasa kake firgitani a mafarki,wlh ina matukar kaunarka.

 

Aziza dake faman sharar baci tasha tsaki tace nifa minal kina damuna,da wannan banzan mafarkinki,haba dan Allah akanki akafara soyayya mutunmin ma dabaki taba ganiba amafarki kila ganshi,dan Allah kiyi mana shiru ko kuma inje inkira umma

 

 

 

Rufe baki minal tayi tana kuka mai tsuma zuciya tace yar uwata bazaki gane son danakewa mahaukacin masoyinnan bane,wallahi inna hadu dashi agaske wallahi kinji na rantse da Allah ko ya yake saina auresa

 

 

 

Razane ido aziza tayi tace yar uwa kina da hankali kuwa lalle kuwa zaki dakko ruwan dafa kanki ba kadan ba iye lalle ma,kinga kwanciyata saida safe

 

Minal ta doshi hanyar waje ta dauki ruwa a buta tadauki buta tayi alwala tazo tafara nafilfila tana rokan Allah ya bayyana mata mahaukacin masoyinta,

 

 

 

;::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

Washe gari,gidansu minal ko sanwar abinci babu,auta da yake bata jurw yunwa yarinyar shekara hudu,sai kuka take tana,wayyo cikina,zan mutu yunwa nakeji

 

Minal uwar tausayi ta fashe da kuka,ta kalli umma datayi tagumi tace umma yazamuyi ne,nifa nafi tausayin auta,kuma kinga tanada sickler karya tashi wlh ina tsoro

 

 

 

Umma cikin taurin zuciya tace to minsl yakikeson inyi mukune,saidai inzakije gidansu hasiya wajen baffa ki tambayo mana kudin gadonmu,insinki subada sai mu barsu da Allah

 

 

Hawaye yafara kwaranya a idonuwan aziza tace a a umma abarsu kawai,neye gado,mutum ma yana mutuwa yaba barin gado balle gado,ai kayan duniya na shedanne?a tsirara mukazo a tsirara zamu koma meye zai damemu,Allah zai sakamana kawai abar maganar gadonnan

 

 

Idon autane ya fara kakkafewa da sandarewa.

 

Minal ta rungumo auta tana ihun auta auta karkiyimin haka,umma mutafi asibiti,

 

 

 

Saka hijjabi minal tayi ta fita dagudu kan titi yana rungume da suta da numfashinta yake sama sama,

 

Su umma ne suka rufa mata baya

 

Adaidaitasau suka tara suka shiga,nasarawa hospital suka nufa,sunashiga aka karbi auta aka shiga dakin emergency da ita.

 

 

 

Likitane ya kira minal yana lashe baki,umma zata bishi yace a a umma ita kadai nace zatayi signing a office dina

 

 

Aziza tace anya umma likitannan akwai Allah a lamarinsa ,daga ganinsa dan iskane

 

 

 

Umma tace kul kidaina fadin zarcenan,ai Allah yana tare damu

 

 

 

 

Minal tsayawa tayi acikin office din,

 

 

 

Kanne ido likitan yayi yace baiwar Allah kizauna mana

 

 

A tsorace minal ta zauna,tana kallon kyakyawan likitan,matashi tace ina

…kwana

 

 

 

Murmushi yamata lfy matsowa kusa da ita yayi har suna iya gogon juna,minal a tsorace tace pls kaban takardan dazanyi signing mana

 

 

 

Lashe lebe ya tashi kamar zaije ya dakko takardan ,bayan minal yabi ya dafata,

 

 

 

Kuka tafara rusawa tana dan Allah likita banson irin wannan kuda aka sanku da taimakon al,umma

 

 

Kokarin sa bakinsa yake abakin minal,yana zura hannu a hijjabinta,kuka minal tasa;tayi iya karfinta ta hankadasa gefe,tafita da gudu

 

 

 

 

Karo sukaci da aziza,da take faman sharbar kuka tace kema minal yanaga kina kuka likitan ya gaya miki auta ta rigamu gidan gaskiyane?

 

 

 

Cikin mamaki,minal ta kalli aziza tace da gaske,auta ta ta tafi,

 

Aziza tace tabbas ta mutu saidai hakuri,yanzuma gawarta zamu dauka mu koma dashi

 

 

 

Kukan zuci minal take tana mudai haka rayuwarmu zai kasance ina umma

 

 

 

Jawo hannunta aziza tayi tace tana dakin da gawar auta take,bata wani tashi hankalintaba,Allah ne ya daukewa auta karshen wahalarta naciwon sickler dinnan

 

 

 

 

Minal kukanta yafito fili dataga wannan likitan kamar mutumin kirki yanata bawa umma baki,

Mamaki ya cika minsl to tawani kofa yashigo,har ya iso dakinnan

 

 

 

 

Yana ganin su minal ya kallesu da alaman tausayi a fuskarsa yace sannu yanmata sai hakuri,zaro dubu goma yayi yabasu yace gashi wannan asiya abin sadaka.

 

Aziza uwar son kudi ta kawo hannu da niyar ansa,minal ta amshe ta watsawa likitan kudin a fuskarsa tace munafukin Allah bama bukatar kudinka,meyasa tun wuri baku taimaki rayuwar yan uwataba sai yanzu zaka taimakemu

 

 

Ji tayi an bata mari tas,batason lokacin da ajijiya ya kamataba tafada jikin likitan da tafi tsana aduniya

MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI🦁*02

By

Maryam yarmama

Dedicated to

All my fans

 

 

 

_wannan shafin nakine *aunty yar mitsila* saboda kaunar da kikewa littafina,kina karamin karfin gwiwa,you are in tha part of my heart,i wish you more happiness and beautiful life and age_

 

 

 

 

 

Umma ce cikin kunar rai tace ke tsabar ke shedan ce anmana kyauta kinki ansa,to kisani gidanmu bada halinnan muka tashiba,har Mahaifinki ya koma ga mahallacinsa kullum mutane kyakyawar sheda akemai,

 

 

 

Tashi minal tayi ta durkusa agaban umma tace umma ki share hawayenki indai akaina ne bazaki sake kukaba,zakiyi alfahari dani,zanyu biyayya agareki har karshen rayuwata,ta kalli likita tace kayi hakuri mungode da kyautar da kamana

 

 

Likita safwan nan yaji yarinyar kaunarta ya kara dilmuwa azuciyarshi yaji gaskiya bazai iya rabuwa da itaba,yace bakomai muje insa a saukeku agida

 

 

Umma tace haba dannan kai da wahala haka ashe kanada kirki haka,

Minal azuciyarta tace,tab umma dakinsan me yake shirin yiminba

 

 

 

 

Haka suka fito daga asibitin suna kuka,safwan ya bude musu bayan haddaden motarsa,umma da aziza suka shiga,har minal zata shiga umma tace a a minal kishiga gaba,mana,nan yayi kadan kuma ga gawar auta

 

Minal tanajin an ambaci gawar auta ta rushe da kuka tana ashe dagaske auta ta mutu

 

 

Safwan ya kalleta da idonsa mai narkar da yanmata yace yanmata kishiga mana sai hakuri wanda ya mutu ya riga yamutu,sai hakuri

 

 

Takasan ido,minal ta gallamai harara tace ina ruwanka da kuka,kallon kafanta tayi sai yanzu ta lura kafarta ba takalmi,buzu buzu yake,kunyane yakamata tashiga motar shima safwan yashiga yana tukawa a sannu a hankali,yana satar,kallon kyakyawar fuskar minal daya rine da hawaye

 

Jin kukanta yake har ransa,amma ba yanda zaiyi yahanata

 

 

Minal kallon titi take,gano wani kyakyawan mahaukacin masoyin datake mafarki tagani,gashinsa yayi luf luf kamar ns indi,a ga idonsa dara dara,yana dauke da faffadar kirji,dogo;fari kal dashi,ga hanci har baka,amma kash daga ganinsa bashi da hankali,kai duk inda ake neman namiji,in aka cire safwan to mahaukacin masoyi yakai,domin safwan ba baya bane awajen kyauba.

 

 

Kara minal tasa tace likita ka tsaya ka tsaya dan Allah,naga wani abun dana dade ina muradi da nema

 

 

Cin burki safwan yayi,da gudu minal ta bude murfin mota,ta duba hagu da dama sama da kasa bataga abin sontaba,hawayene ya fara shatata a idonta,ta dawo cikin mota jiki asanyaye

 

Umma dake bayan mota takalli aziza tace wai meye minal ta tsayar da motane?

 

Aziza tace oho ita zataki tambaya,don inaga minal takusa zaucewa

Umma tace Allah ya kyauta

 

 

;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;,;;;;,,,;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;

 

 

 

A kofar gidansu minal likita safwan ya tsayar da motarsa,yana kallon rubabben gidansu cikin tausayawa da jimami,duk gidan ne yafi kowa muni a layin gabaki daya,

 

 

Bude musu motar yayi,ummi suka gani atsaye a kofar kyakyawan gidansu,tana ganinsu ta fara murmushin jin dadin ganinsu minal ta taho,ta dafa minal tace besty nashiga gidanku naga shiru lfy

 

 

 

Fashewa da kuka minal tayi,ta fara nunawa ummi gawar auta tana ihu da kukan auta ta mutu auta tabarmu aduniyar nan mai cike da wahala da kuncin rayuwa

 

Salati da ihu ummi ta zunduma ta nufi wajen umma dake rike da gawan auta,jijjiga auta take tana auta auta abokiyar kowa,auta akwai ki dashiga rai meyasa kika barmu innalillahi wa,innahilaihi raji,un

 

Makotane sukafara fitowa wasu nakukan rashin auta,wanda duk cikin yayan umma tafi shiga rai,da son wasa,kowa natane

 

 

Haka akafara zaman makoki

 

Umma da takejan chasbahana tacewa aziza taje gidansu abba ta gayamai rasuwarnan tunda yanzu shine uba,

 

Safwan sai hidima yake,komai shi yayi agidan mutuwarnan

 

 

Can anjima saiga aziza tashigo gidan da kuka tafada jikin umma tace umms wallahi ba Allah a zuciyar abbansu hasiya,haka yace bashi ya kashetaba balle yaxo,indai don abin sadakane wai saidai mu mutu bamuyi sadakarba,wai ahaka zamh kare ba rayuwar kwanciyar hankali

 

 

Yan gidan mutuwa suka fara jimami suna ta Allah ba tasaba saidaishi ya mutu badai kuba

 

 

 

Haka aka share zaman makoki ,komai safwan ne yakeyi,ya canja kamannin gidansu umma,an mai gini mai kyau,ya zuba kujeru da fridge,da t.v da jennareto,yacika store da abinci da komai.

 

Umma sai shimai albarka take,minal ko ajikinta ta tsani safwan,itadai burinta ta karacin karo da mahaukacin masoyinta

 

 

Abbane kanin babansu ya tako gidan ranar yazo da rashin mutuncinsa,yaga gida yayi kyau,nan ranshi ya sosu yace lallema matar nan,tafara tura yayanta duniyar karuwanci kenan

 

 

 

Shiga gidan yayi ba sallama,ga gidan an chanja shi harda tyles,wani uwar ashar ya dura yace ke karya ina kike kifito

 

Aziza dake goge tyles da mopping stick tace karka kara cewa uwata karya saidai na tsayanne bakin kare

 

 

Nufota yayi yace wallahi zanga uban daya tsaya miki agidannan kike cemin kare,

 

Aziza ta dankaramai harara tace to tsohan najadu inajiranka

 

 

Minal dake girki a kitchen tafito ta durkusa har kasa tace abba ina wuni

 

 

Abba yace ban wuniba munafuka yar iska,karere

 

 

Dafe kirji minal tayi tace abba nagode,ta kalli aziza tace haba yar uwa yakikeson karya umarnin mahaifiyarmu kinsan tashiga,gidan hajiya tace duk wanda yazo ya takelemu da fada karmu biye masa,pls ki daure kibi umarninta

 

 

 

Aziza tace to shikenan taci gaba da aikinta,minal takoma kitchen tanata girki

 

 

 

Abba sai zage zage yake,dayaga bawanda ya kulasa,yayi tafiyarsa

By

Maryam yarmama

 

MAHAUKACI KO BOYAYYEN MASOYI

BY

MARYAM YARMAMA

*DEDICATED TO*

MY FANS

 

 

 

*WANNAN SHAFIN NAKINE MAMAN HAFSAT,INA FATAN ZUMUNCINMU ZAI DORE HAR ABADA,KINA RAINA*

 

 

 

 

 

bayan kwana biyu umma ta aiki minal zuwa gidansu,abba ta karbo mata ankon bikin hasiya

 

Hijjabi ya wuce gwiwa minal tasa,tana cike da farin ciki yau,tayi mafarki tayi zata hadu da mahaukacin masoyinta mai kaunarta

 

 

 

Ta tsantsara kwalya dama gata chocolate colour ga hanci har baka ,ga ido ,tayi masifar kyau,minal nada hakuri,gason karatu,da saukin kai,batta da surutu so silent zaka ganta,

 

 

Tafiya take a sannu a hankali,kamar tana tausayin taka kasa,ji tayi an rike mata hijjabi ta baya,faduwar gabanta ya tsananta

 

 

Wani murya mai uban dadi taji abayanta yana anty ki gaya musu su daina tsokanata sunacemin mahaukaci

 

A hankali ta juy karo taci da wanda take muradi wanda koda yaushe yana manne a birnin zuciyarta,ya kara kyau dahaske,rufe ido tayi tanajin sansayar iska yana kadawa sonsa nakara narkuwa azuciyarta

 

 

Firgigit ta farka daga dogan tunanin da take sakamakon jin ya kara ambatar anty ki gayamusu su daina tsokanata

 

 

Kallon gefensa tayi,yarane sunfi ishirin sun tsaya suna kallonsa,dayan yaronne yace kash gaka kyakyawa amma ba hankali

 

 

Tabule fuska yayi yace anty ki gayamusu ni wlh

 

 

 

Minal ta kyalesa cikin sanyin murya tace,to ka sakeni zan gaya musu ,kallon yaran tayi tace haba kukuwa idan yayankune kodan uwanku ya ke da wannan laluran yazakuji iye?

 

 

Jikinsu yayi sanyi a hankali suka fara watsewa suna barin wajrn

 

 

Kallonta yayi yace aunty nagode zaki aureni,ki dinga korar min yaran

 

 

Dariya minal tayi tace hmmmm mai kyau ya sunanka?

 

Cikin alamun jin kunya yace sunana annur sunana aunty kiyi alkawari zaki aureni muryarki da dadi

 

 

Minal tace,a-a ni kadaina cemin aunty minal sunana ba auntyba ai zan aureka in Allah ya yarda

 

 

 

Ihu gami da tsallen murna yayi yace wooo aunty nagode dafatan zaki dingamin wanka kisamin pampers

 

 

 

 

Kunyane ya rufe minal tace kaga sai anjima ma hadu kasan gidanmu nan bayan layi kazo ka dinga karban abinci

 

 

Murna annur ya fara yafece aguje.

 

 

 

Jikin shaukin kauna minal takallesa tana in Allah ya yarda sai na auri annur na maidasa mutum kamar kowa

 

 

Tafiya taci gaba dayi abba ta tadda a kofar haraban gidansu maikyau yana ganinta tundaga nesa ya fara yar maula ki koma ai yau ba jumma,a ba

 

 

 

 

*pls my fans am so sorry ,this is a short page ,am so sorry,am studying*

 

 

Leave a Comment