🪄…JUYIN KWAƊO…🪄
_Daga ruwa zuwa ruwan zafi_
From the writer of:
YADDA ƘADDARA TA SO
LABARINSU
HASKE
ƘADDARA CE
ArewaBooks @SalmaAhmadIsah
Wattpad @SalmaAhmadIsah
*Gabaki ɗaya labarin JUYIN KWAƊO, da littafin kansa. Na sadaukar shi zuwa ga ZAHRA ROYAL STAR and NAINARH KD NKD’S. Your love and acceptance mean everything to me. Thank you for being my safe space and my forever friends.*
بسم الله الرحمن الر حيم
*Page-01*
*MK Fencing Academy,19th Floor, The Binary by Omniyat, Business Bay, Dubai, UAE.*
ARMAN IƘBAL.
Babu abin da yake tashi a ko ina sai hayaniya da iface-iface, sai kuma sautin sara da sukan takkuba. Kuma ko ina jini ne ke zuba… A tsakiyar wannan hatsaniyar yaƙin yake tsaye, can ya hango wani mayaƙi ya taho da gudu ya iyo kansa, hannunsa riƙe da wani takobi me tsananin kaifi, ya kawo masa sara da ita…
Tahowar sukan takobin cikin tunaninsa ya yi dai-dai da tahowar sukan takobin abokin karawarsa a tsakiyar filin hall ɗin koyon wasan takobi na MK fencing academy. Cikin zafin nama ya buɗe idonsa, sannan ya yi azamar kaucewa sukar takobin wasan. Cike da ƙwarewa kuma ya yi amfani da nasa takobin ya kaiwa abokin nasa farmaki, farmakin da ya yi nasarar kai shi ƙasa, hakan yasa ya zamo zakaran wasan, domin shi ne ya lashe!.
Malamai da ɗaliban wasan na takobi suka shiga tafa masa, hakan yasa ya juya kansa ya fara binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, a hankali yake fitar da numfashi, domin wannan mafarkin da ya saba yi ido biyu yau ma ya raɓe shi, ya rasa mece ce alaƙarsa da wannan yaƙin da yake yawan yin mafarkinsa ido biyu ko cikin bacci. Ba ya jin ya taɓa tsallake sati ɗaya ba tare da ya yi mafarkin wannan yaƙin me firgitar da ɗan adam ba.
Shi dai ya san ba a haifeshi a ƙarnin da aka yi yaƙin ba, amma kuma ya rasa dalilin da yasa a ko da yaushe yaƙin yake raɓar rayuwarsa. Hannu ya kai ya taɓa farin glasses ɗin da ba ya taɓa rabuwa da su duk rintsi, kasancewar yana fama da lalurar rashin gani, wadda aka haife shi da ita. Da ace kuɗi yana samar da lafiya ya tabbatar da mahaifinsa Sayid Iƙbal Alhadi zai ƙarar da duk dukiyar da ya mallaka domin sama masa lafiyar ido.
Amma tun yana ƙarami ake fafutukar naima masa maganin da zai warkar da idon har zuwa yanzu da yake da shekaru talatin da ɗaya a duniya ba’a dace ba. Hakan tasa aka haƙura aka ƙyale maganin, ya ci gaba da amfani da glasses ɗin da da taimakonsu kaɗai yake iya ganin abin da Allah ya yassare masa ya gani.
“Muna tayaka murnar lashe wannan gasa Arman! Fatan nasara!”
Faɗin ɗaya daga cikin malaman dake koyar da su wasan takobi cikin harshen larabci. Yayin da yake miƙa masa award ɗin da aka tanada domin zakaran da ya lashe wannan gasa da aka saka a tsakanin ɗaliban makarantar. Hannu bibbiyu yasa ya karɓi award, sannan ya yi murmushi me kyau, tare da furta.
“Na gode”
Ya juya ya kalli abokansa da yake koyar wasan tare da su, ya ɗaga musu award ɗin, suka saka tafi har da masu ihu, shi dai murmushi kawai yake, har ya sauƙa daga kan stage ɗin wasan. Ya nufi ɗakin sauya kaya dake cikin hall ɗin, a nan ɗakin da ya shiga ya sauya kayan fencing ɗin da suke jikinsa, ya mayar da kayan da ya zo da su. Wato black plain hoodie, wadda ya ɗorawa red bomber jacket a sama, da blue jeans sai baƙaƙen canvas ɗinsa.
Sannan ya nufi backpack ɗinsa ya buɗeta ya saka award ɗin da aka ba shi, kafin ya ɗauki wayarsa dake ciki, ya buɗe da fatan ganin missed call ɗin abokinsa ADAM, amma babu alamar ma ya kira, dan haka ya ja tsaki, ya buɗe wayar ya nemo lambarsa ya sake aika masa kira, a karo na barkatai a ranar, dan tun kafin ya shiga fencing class ɗin yake ta kiran wayarsa.
*House No. 34, Street 12, Al Mankhool, Bur, Abu Dabhi, Dubai.*
ADAM ALI ABBAS.
“Adam! Adam! Adamm! Wai ba za ka buɗe ƙofar nan ba!?”
Wata bahaushiyar mata ke faɗi, cikin harshen hausa, yayin da take tsaye a jikin ƙofar ɗakin da take a kulle, yanayin shigar dake jikinta kaɗai zai sanar maka da ƙabila da kuma ƙasar da take. Duk da su mazauna ƙasar ta Dubai ne bai sa ta daina saka kayan al’adarta ba, a matsayinta na ainahin ‘yar ƙasar Nigeria, kuma bahaushiyar arewacin ƙasar.
Daga cikin ɗakin da take buga ƙofarsa kuwa, wani matashi ne tsugunne a ƙasan desk, ya lulluɓa da blanket har kansa, yanayin tsoro shi ne kwance a kan fuskarsa, ban da rawar ɗari ba abin da yake, kamar wanda ya kwana a cikin fridge.
Ɗakin bai cika girma ba, amma yana ɗauke da kaya masu kyau da sauƙin kuɗi, kallo ɗaya za ka yi wa ɗakin ka san cewa na mai ɗaukan hoto ne. Dan ko wace kusurwa ta ɗakin na ɗauke da hotunan mabanbanta abubuwa, da kuma hotunan cameras da ma cameras ɗin na zahiri, tarkacen da ɗakin ya cika zai sa ka san cewa ɗakin matashi ne. Daga wajen ɗakin, matar nan ta ɗazu da take ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin ta girgiza kanta cike da takaicin halin ɗan nata.
“Allah ya raba bawa da wahala!”
Ta faɗa kawai, sannan ta juya ta dawo ɗan ƙaramin falonsu dake ƙasan gidan, wanda ke ɗauke da kyawawan furnitures masu kyau. Tana shirin wucewa kitchen ɗin dake haɗe da falon wayar Adam ɗin dake a falon ta yi ringing kamar ɗazu. Dan yawan kiran wayar da ake run ɗazu ne yasa ta gane cewa Adam ɗin bai fita ba, shi ne ta je domin duba shi, amma sai ya ƙi buɗe ƙofar ɗakin.
Wata shawara ce ta faɗo mata a rai, hakan yasa ta nufi wayar tasa ta ɗauka ‘Bin Iƙbal’ shi ne abin da aka rubuta a matsayin sunan wanda yake kiran, kuma ta gane cewa abokinsa Arman ne, dan haka ta ɗaga wayar, ta sanarwa Arman ɗin halin da Adam ɗin ke ciki.
Daga ɗayan ɓangaren, Arman ya sauƙe wayarsa ƙirar iPhone ‘yar yayi yana dariya a nutse, ba sai Maaman Adam ta yi dogon bayanin abin da yasa ya shiga ɗakinsa ya kulle kansa ba. Dan ya san dalilin ba zai wuce ya kalli wani horror ko Zombie movie ba, ya san abokinsa da tsoro kamar farar kura. Kuma ga shi da naci, dan duk yadda ya kai ga tsoron horror film ɗin sai ya kalla daga zarar sabo ya fito, Allah yasa yanzu haka bai kwanta zazzaɓi ba.
Kansa ya sake girgizawa yana ɗaukan backpack ɗinsa, ya goyata a bayansa yana kama hanyar barin Business Bay, sai da ya fita daga building ɗin sannan ya fara dialing numbern ɗaya ƙawar tasu wato IVANA!.
*Repton school Dubai, Nad Al Sheba 3, Abu Dabhi, United Arab Emirates.*
IVANA SAGAR.
Zaune take a kan maroon bowl chair, sanye take cikin farar hoodie da baƙin distressed jeans, ƙafafunta cikin farin canvas, baƙin dogon gashin kanta kwance a gadon bayanta, yayin da hannayenta ke kaɗa guitar ɗin dake kan cinyarta. Farar balarabiya ce, kyakkyawar gaske, me manyan idanuwa da dogon hanci da madaidaicin baki me ɗauke da farar fata me haske.
Murmushi ne kwance a kan fuskarta, yayin da take kallon ɗalibanta da take koyawa kiɗan guitar zaune a gabanta. Dukansu sun nutsu suna sauraron daddaɗan kiɗan guitar ɗin da take… Wayarta dake aje a gefenta ce ta kaste musu darasin, ta hanyar ringing ɗin da ta fara.
Hakan yasa ta dakata da kaɗa guita ɗin, ta kalli wayarta dake ruri, alamun shigowar kira ‘Rafiƙi’ (Abokina) shi ne rubuce tare da heart emoji a gaban sunan, kuma kaf duniya mutum ɗaya ne ta yi saving numbernsa da hakan.
“A’aziruni lahza! (Excuse me please)”
Ta faɗi cikin harshen larabci tana duban yaran ɗabilan nata. Sannan ta juya ta ɗauki wayarta, ta ɗaga kiran Arman dake shigowa.
“Shu wainak halla? (Yanzu kana ina?)”
Ta tambaya ba tare da ta bari ya yi magana ba, dan ta san sun yi da shi a kan yau yana da gasa tsakaninsa da abokan koyon wasan fencing ɗinsa.
“Ai dai kya bari mu gaisa ko?”
Arman ya faɗa daga ɗayan ɓangaren, sai ta yi murmushi, tana cire handle ɗin guitar ɗin daga wuyanta, sai da suka gaisa, sannan ya sanar mata da dalilin kiranta.
“Na kira Adam Maama ta ɗaga, ta sanar min da tun jiya ya kulle kansa a ɗaki, ya ƙi fitowa. Da alama ya kalli wani horror film ɗin ne”
Ivana ta kwashe da dariya tana rufe bakinta, dan ita ma ta sa halin abokin nasu.
“Yanzu kana ina?”
“Na baro business bay a motata”
“Mashi (Okay) ka biyo ta nan sai ka ɗaukeni”
“Ɗayib (Okay)”
Ya amsa, sannan ya aje wayar.
*
Arman ya kwashe da dariya yana kallon Adam da yay tsuru-tsuru da shi, saboda yanda yake a tsorace. Ivana ta ɗan yi guntun tsaki tana dafa kafaɗun Adam dake basu labarin film ɗin ban tsoron da ya kalla daren jiya, wanda ya hana shi sukuni har zuwa yau ɗin nan.
“Shifti? Huwa am yadhak alaiyyi” (Kin ga ba? Dariya mayake min)
Adam ya faɗi yanayinsa na nuna damuwar da yake ciki, dan har yanzu a firguce yake.
“Armaan la ad tadhak!” (Armaan kada ka sake dariya)
Ivana ta gargaɗe shi, sai ya ɗora hannunsa a kan bakinsa, yana son toshe dariyar dake cinsa, amma ya kasa. Ivana ta girgiza kanta, sanan ta tura Adam suka fara tafiya tana kwantar masa da hankali. Arman ya biyosu yana ci gaba da ƙyaƙyatawa Adam dariyar mugunta. Da haka har suka shiga Cavo Espresso Bar dake kusa da inda suke, har suka zauna Arman bai daina dariya ba, ko ya so ya danne daga sun haɗa ido da Adam zai ji dariyar da taso masa.
“Ivana kalli yaskut! Wa illa rah irja’a ala bait” (Ivana ki saka shi ya yi shiru, idan ba haka ba zan koma gida).
Ya faɗa yana kallon Ivana. Ivana ta ɗakawa Armaan duka a baya tana faɗin.
“Da ƙyar muka saka shi ya fito daga gida, yanzu kuma idan ka ci gaba da masa dariya ko zai koma gida ba zan yi ƙoƙarin hana shi ba”
“Asif (Ku yi haƙuri)”
Faɗin Arman yana toshe bakinsa. Ivana ta sake dafa kafaɗar Adam da har yanzu yake a dame.
“Laik Adam! Shabah mu haƙiƙi! Killu mazah! Wa ma bi kaffu!”
(Ka ga Adam, fatalwa ba gaskiya ba ce, duka shiri ne, kuma ba su da ban tsoro).
“Me ya sa za ki faɗi haka? Bayan ni na ganta da idona, wata doguwa, me dogayen farata, idonta ja… Wayyo Maama”
Ya ƙarashe yana rufe fuskarsa, saboda fuskar fatalwar da ya hango. Ivana ta sake dafa shi.
“Ihda! Halla rah jiblak shai. Biddak shai mu?” (Ka nutsu, yanzu zan kawo maka shayi, kana son shayi ko?)
Ya jinjina mata kai yana kallon Arman dake ta ƙoƙarin danne dariyar da ke ciyo shi. Ivana ta gyaɗa kai, sannan ta miƙe ta zagaya ta nufi wurin da zata yi order. Cup uku na shayin ta karɓa, sai dai a yayin da take shirin juyawa ta yi karo da wani mutum da shi ma yake ƙoƙarin zuwa wurin.
Farko kofunan shayin dake jere a kan tray ta fara kalla, da ta ga ba su zube ba sai ta kalli mutumin da ta yi karo da shi. Wani kyakkyawan matashin balarabe ne, wanda ke sanye da baƙar suit, kalar farar fatar jikinsa me ɗaukar hankali ce, haka ma kammaninsa, dogo ne, kuma me matsakaicin jiki, yana da faffaɗan ƙirji, sannan sumar kansa na cikin asken high pade. Yana da buɗaɗɗen ido, wanda yake ɗauke da shuɗiyar ƙwaya, sannan hancinsa dogo ne sosai, ga bakinsa dai-dai wa dai-dai, yana da saje da kuma gemu, wanda suka ƙara masa kyau.
“Ana ba’atazir! Ma intabahat!” (Ki yi haƙuri ban lura da ke ba ne).
Ta ji muryasa me daɗi ta furta, sai kawai ta jinjina kanta, alamun ba komai, sannan ta raɓa shi ta wuce, har ta koma table ɗin da su Armaan suke bai daina kallonta ba.
“Rifaƙ (Guys) ko kun san cewa yau Chris Brown zai yi live performance a Coca-cola Arena?”
Faɗin Arman yana nuna musu takardar sanarwa a cikin wayarsa. Adam da Ivana suka dubi juna.
“Wai yau?”
Adam ya tambaya yana aje cup ɗin dake hannunsa.
“Eh yau, duba ka gani”
Ya miƙa masa wayar , Adam da Ivana suka haɗa kai suna karantawa.
“Za mu je ne?”
Cewar Ivana.
“Akid! (Of course)”
Arman ya bata amsa. Domin duk inda za su je ko za su fita shi ne ke biyan duk kuɗin da za’a kashe, ko cinema za su je shi zai sai musu ticket. Saboda kaf cikin su ukun babu wanda ya kai mahaifinsa kuɗi. Dan mahaifinsa babban ɗan kasuwa ne, wanda yake da kamfanunuwa masa masu zaman kansu.
Shi Adam photographer ne, yana aiki tare da wani kanfanin magazine, ita kuma Ivana musician ce, tana koyar da kiɗan guitar a Repton school Dubai. Sannan tana aikin kiɗa a waƙoƙi idan har an buƙata, duk cikinsu shi Arman ɗin ne ba shi da aikin yi, ba wai dan ba’a naima masa a gidansu ba. Sai dan shi a rayuwarsa ya tsani duk wata harka da ta shafi kasuwanci.
Duk da ya taso a gidan da ake kasuwanci, kuma hakan ya samu asali ne daga nakasar gani da yake fama da ita tun lokacin yarinta. Tun a tasowarsa kawunsa, yayan mahaifinsa ya saka masa ƙin harkar kasuwanci, dan a ko da yaushe abin da yake faɗa masashi ne.
“Harkar jagorancin babban kamfani kamar Alhadi Group of Companies ba na makafi ba ne”
Ya sha faɗa masa hakan tun ba shi da wayo har ya taso ya yi wayo, tun ba ya gane abin da kalaman ke nufi har ya zo ya gane abin da kalaman ke nufi. Sannan tsangwamar da ake yi wa mahaifiyarsa a halinsu ya ƙara cusa masa ƙiyayyar kasancewa ɗaya daga cikin ahalin Alhadi a ransa.
Kuma suna nunawa mahaifiyarsu wariyar launin fata saboda ita ‘yar Pakistan ce, su kuma ahalin mahaifinsa larabawan Qatar ne. Shi da ƙanwarsa Gulzar kaɗai iyayensu suka haifa, kuma bayan shi babu wani wanda zai iya gadon kasuwancin mahaifinsa sai Faisal!. Ɗan yayan mahaifinsa da shi ma ya bada tasa gudummawar wurin cusa ƙiyayyar son karɓar jagorancin Majmu’at Shirkat Alhadi (Alhadi Group of Companies).
Zama shugaban Alhadi Group of Companies shi ne babban burin Iƙbal, wato mahaifin Arman. Kuma saboda yana yawan takura masa a kan batun kasuwancin yasa suka fara raba gari. Dan a yanzu Arman ba ya jin yana da maƙiyi sama da kujerar jagorancin gammayar kamfanunuwan Alhadi.
Alaƙarsu da su Adam ta samo asali ne tun daga makaranta, abin da ya sa tafiyarsa da su ta yi nisa shi ne su ba su tsangwamarsa dan yana da ƙarancin lafiyar ido. Kuma sam ba sa ɗaukan cewa bai kai ba, dan yana saka glasses ɗin da za su taimaka masa wajen gani, saɓanin yanda ya taso ana nuna masa cewar tun da ba ya gani shi makaho ne.
“Na ga kamar sauran awa ɗaya a fara wansa fa!”
Adam da ya ci gaba da karanta takardar sanarwar ya faɗa, sai duk su ukun suka dabi juna, kamar wanda suka haɗa baki, haka kowa ya finciki jakarsa suka ruga da gudu zuwa waje, Ivana na faɗin.
“Gara mu yi sauri kafin tikitin ya ƙare!”
Ai a ɗari suka shige motar Armaan ƙirar Ferrari venon, Adam ya figi motar zuwa Coca-cola Arena, kamar yanda suka yi zato ticket ɗin ya kusa ƙarewa. Dan duk da haka sai da suka bi layin siyan tikitin. Yayin da suke bin layin siyan tikitin, Adam ya shiga bawa Adam labarin film ɗib da ya kala jiya. Shi kuma Arman sai kwasar dariya yake, kamar daga sama ya ji an kira shi da sunan da ya fi masa na mutuwa ɗaci a kunne.
“Marhaba makaho! (Hello makaho)”
Idonsa ya rintse, dan ko ba’a faɗa ba ya san wa ya mallaki muryar, dan haka ya buɗe idonsa yana gyara glasses ɗinsa, wanna ita ce ɗabi’ar da ya fi yawan yi, ba ya haura minti goma ba tare da ya gyara zamansa glasses ɗinsa ba, ko da ko bai zame ba. Ya juyo yana kallon Faisal tare da wata budurwa tsaye, dariyar da ya ga Faisal ɗin na yi ita ta fi baƙanta masa rai.
“Ashe kuma makafi ana ganinku a wurare irin wannan?… Na ɗauka makafi ba sa zuwa kallon live performance!”
Ya ƙarashe yana sheƙewa da dariya, budurwa dake tare da shi tana taya shi.
“Ka ga malam! Babu wada ya buƙaci jin ra’ayinka a nan, dan haka bama son tada zaune tsaye.”
Ivana ta dakatar da shi, dan ko kaɗan Arman ba ya iya tanka masa ko ƙanwarsa Sakina idan suna aibanta shi, idan suka taɓa Gulzar ko mahaifiyarsu ne dai ba ya shiru.
“Yi haƙuri malama, ba da ke muke ba, da wannan makahon muke…”
Ya yi fasali yana yin taku uku zuwa gaban Arman, sannan ya yi kamar zai rungume shi, ya kai bakinsa saitin kunnensa yana murmushi, sannan ya furta.
“Jin daɗi da sharholiya irin wannan ba ta kamaceka ba, ka fi dacewa da yin bara a gefen hanya!”
Ya ja baya yana dariya, Ivana ta riƙi kwalar rigarsa a fusace za ta mayar masa da martani, Armaan ya jata baya yana girgiza mata kai. Haka Faisal da budurwasa suka wuce suka barsu a wurin suna dariya.
“Da ka bari na mayar masa da martanin da zai hana shi ba ci daren yau. Amma ka hana”
Arman ya girgiza mata kai.
“Maganganu irin wannan na saba jinsu tun tasowata, ba shi ne mutum na farko da ya fara faɗin hakan ba, dan haka ki share kawai”
Ya ƙarshe yana ɗauke kai, cike da damuwa Ivana ta kalli Adam da bai ce komai ba, dan ba zai ce ɗin ba, tsoro ba zai bari yace komai ba, ko shi ya je ya takalo faɗa Ivana da Arman ne ke tare masa, amma ba ya iya taɓuka komai.
*House No 27, Street 45, Mirdif, Dubai.*
Motar Armaan ta faka a gaban ƙaramin gidan da bai cika girma ba, amma duk da haka ko daga waje ma yana da kyau. Ivana dake gidan baya na motar ta buɗe ta fita, sannan ta goya jakar guitar ɗinta a baya, ta rufe motar tana kalon Adam da Arman dake gidan gaba.
“Me kuka shirya mana zuwa gobe?”
Arman da Adam suka dubi juna, sannan Adam ya sake subanta yana girgiza kai.
“Babu wani abu, sai dai idan mun haɗu zuwa goben”
Ta ɗaga hannunta suka yi fits bump, sannan ta ɗaga musu hannu ta nufi gidansu. Ƙofar shiga gidan ta buɗe, ta shiga, sannan ta rufe ƙofar tana cire takalman dake ƙafarta, ta saka wasu dake aje a bakin ƙofar, sannan ta nufi falon gidan dake a farkon gidan.
“Assalamu alaiki ya Yumma!”
Ta yi wa mahaifiyarta dake zaune a falo tanq cin fruit sallama, fuskarta ɗauke da murmushi, ita ma tsohuwar matar na ganinta ta fara murmushi, Ivana ta risina ta sumbaci kan mahaifiyarta, sannan ta zauna kusa da ita tana cire jakar guitar ɗin dake bayanta, tare da ajeta a gefe, ta gyara gashin kanta tana faɗin.
“Shu yalli ɗabaktil yaum ya Yumma”
(Yumma yau me kika dafa?)
Mahaifiyar Ivana me suna Khadija, wadda Ivana da yayarta Hala ke kiranta da Yumma tace.
“Shish taouk”
“Ba na jin yunwa sosai, dan mun tsaya a Al Fayrooz lounge mun ci abinci tare da su Arman, dan haka ki zuba min kaɗan”
“To”
Cewar Yumma, sannan ta miƙe ta nufi kitchen ɗinsu dake haɗe da falon, dan wata gajerar katanga ce kawai ta raba kitchen ɗin da falon, komai dake cikin falon ba shi da tsada, kuma kayane irin na da, dan a cikin gidan aka haifi Ivana da yayarta Hala, wadda a halin yazu ta yi aure, har da yaronta guda ɗaya.
Mahaifinsu ya rasu tun da ƙarancin shekarunsu, hakan ya sa suka taso ba su san shi ba sai Yumma, suna da rufin asiri dai-dai gwargwado, kuma ba su ɗauki rayuwa da zafi ba.
Ivana ta miƙa hannu ta ɗauki apple ɗin dake cikin wani bowl a kan center table, tana shirin fara cin apple ɗin idonta ya kai kan wata magazine dake aje a kan center table ɗin. Sai ta aje apple ɗin ta ɗauki magazine ɗin da hannunta na dama, yayin da take saƙala gashinta a bayan kunnenta da hanunta na hagu.
Ba komai ya ja hankalinta zuwa kan magazine ɗin ba face hoton dake jikin bangon magazine ɗin. Gani take kamar ta san mutumin cikin hoton, shiru ta ɗan yi tana son tuno inda ta taɓa ganin mutumin. Fuskarsa a yammacin yau ta da ta ganshi ta haska a cikin kanta. Ƙwarai kuwa, shi ne mutumin da ta haɗu da shi a Cavo Espresso Bar, sai ta shiga karanta bangon magazine ɗin. ‘Business week’ shi ne babban maudu’in abin da magazine ɗin ta ƙunsa.
Sai ta zarce zuwa kan sunansa dake gefe guda, Sayyid UWAIS FAZIL… Ta sake kallon fuskarsa tana furta sunan a kan leɓenta.
“UWAIS!”
Ta furta sunan ba tare da ta ji komai a ranta ba, saboda ɗan adam ba shi da ikon hango abin da ke tunkararsa a gaba, ba shi da masaniyar abubuwan da za su faru da shi, sai na wanda suka riga suka faru da shi.
“Ki ci Shish taouk ɗinki”
Yumma ta faɗa tana aje mata Shish taouk da ta zuba a cikin plate, Ivana ta aje magazine ɗin tana murmushi, sannan ta kalli Yumma tana ɗaukan plate ɗin, ta soma cin abincin tana bata labarin yadda live performance ɗin da suka je suka kalla yau ya kasance.
Bayan ta gama cin abinci ta nufi upstairs, dan gaba ɗaya ta gaji bacci take ji, ƙofar ƙaramin ɗakinta ta buɗe, ta shiga ciki tana kallonsa kamar baƙonta. Ɗakin sam ba shi da girma, amma ya ɗauki duka kayanta da take ajewa a ɗakin, akwai gadonta ɗan siriri na kwanciyar mutum ɗaya.
Wanda ke ɗauke da baby pink duvet, sannan akwai pillows manya da ƙanana, sannan akwai wardrobe da ba ta cika faɗi ba, akwai kuma desk ɗinta, sannan dressing mirror. Mafiya yawan abubuwan dake ɗakin pink cokor ne, hatta da stikern dake jikin bango pink ne.
Miƙa ta yi tana rataya jakar guitar ɗinta a sama, inda ta saba ajeta, sannan ta nufi bathroom, ta ɗauro alwala ta dawo ɗakin, wardrobe ɗinta ta buɗe, ta ɗauki mayafi a ciki, ta yafa a kanta, sannan ta tada sallah a kan center carpet. Sai da ta gabatar da sallahr isha, sannan ta yi wanka ta sauya kaya zuwa night wear.
Tana hamma ta bi lafiyar gado ta kwanta, tana rayawa ranta cewa me ake da rayuwar da babu gadon bacci, ita a duniyarta babu abin da ya fi birgeta sama da lallausan gado, dan ko a kan sofa ba ta iya bacci.
_________________
_Ehem! Ehem! Ehem!_
_Salmanians! Ga wata sabuwar tafiya! Me ɗauke da abubuwan ban al’ajabi._
_Tafiyar ba me sauƙi ba ce kamar yanda za ku ɗauka!. Dan haka sai ku shirya da kyau._
_JUYIN KWAƊO zai zo a Book 1 and 2. Book 1 shi ne free, book 2 ne zai kasance paid a kan ₦400_
_Kuma za ku iya samunsa a ArewaBooks, domin akwai complete book 1 a can_
_Sai ku shirya, ku gyara zama, domin jin yanda rayuwa za ta yi juyi da waɗannan abokai uku, kuma juyin ma irin na kwaɗo, daga ruwa zuwa ruwan zafi._
#Bahaɗejia
#Candy
#SalmaAhmadIsah
#JuyinKwaɗo
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
. 🪄…JUYIN KWAƊO…🪄
©️Salma Ahmad Isah
SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah @Wattpad
Page-2
*House No. 106, Street 14, Jumeirah Bay Island, Abu Dabhi, Dubai.*
Gidan na ɗaya daga cikin manya manyan gidajen dake hamshaƙiyar unguwar ta Jumeirah. Dan ko a yanayin gininsa za ka san an kashe kuɗi, ballantana ace ka samu damar kutsa kai ciki. Motar Armaan da ta ɗauko hanya tun daga unguwarsu Adam da ya aje a gida ta faka a gaban gidan.
Ya kashe motar, sanna ya cire seat belt ya fito yana jan jakarsa dake a wurin me zaman banza, ya goya jakar a bayansa, sannan ya juya ya fuskanci hamshaƙin gidan. Glasses ɗinsa ya gyarawa zama ta hanyar saka ɗan yatsansa manuniya ya tura bridge ɗin glasses ɗin, sannan ya nufi kyakkyawar ƙaramar ƙofar shiga gidan. Dan gidan ba shi da wani compound, wanna ƙofar ita ce da ka buɗeta za ta sadaka da gidan, hatta da garejin aje motocinsu na daga gefen ƙofar shiga gidan.
Hannunsa ya kai kan inda madannan sirrin buɗe ƙofar gidan suke manne a jikin ƙofar, daga gefe kuma door bell ne, wanda aka yi shi domin baƙi, dan idan har ɗan gidan ne babu buƙatar ya danna door bell, tun da duk sun san kalaman sirrin da suke buɗe ƙofar. Lambobin ya saka, nan take ƙofar ta buɗe, ya shiga yana kallon masu aikin gidan dake kaikawo, sanye cikin uniform iri ɗaya.
“Haidar!”
Ya yafito ɗaya daga cikin masu aikin, Haidar ɗin ya nufo shi yana amsa masa cike da ladabi, Arman ya miƙa masa mukullin motarsa, sannan yace.
“Motata tana waje, ka saka min ita a gareji, idan ka saka key ɗin kuma ka aje shi a nan”
Ya nuna masa wani abu me kama da basket dake aje kan wani cupboard dake farkon gidan, wanda ya ƙunshi tarin makullan motocin da mutanen gidan ke hawaya. Kuma daga jikin cupboard ɗin ma za ka iya hangen manya manyan motocin dake garejin, dan akwai ɗan glass dake wurin da zai baka damar hakan.
Haidar ya karɓi key ɗin, sannan ya nufi ƙofar fita, yayin da shi kuma ya kutsa kai cikin kyakkyawan gidan, bayan wani ɗan gajeren corridorn dake bakin ƙofar shigowa, za ka iske hanyoyi uku, ɗaya ita ce wadda zata sadaka da upstairs, kuma duka ɗakunan kwanan gidan suna sama. Ɗaya kuma ita ce wadda za ta sadaka da living room, wanda yake ƙunshe da sitting areas guda biyu, tare da dinning area, sannan akwai kitchen ta kusa da dinning area.
Kuma ta cikin falon za ka fita harabar garden ɗin gidan, dake ƙunshe da swimming pool. A kusa da swimming pool ɗin kuma akwai kujerun zama, wanda aka saka su a ƙasa, kamar dai zurfin swimming pool ɗin, kuma tsakanin wurin da suke da swimming pool ɗin glass ne kawai ya raba, ta yanda kana iya ganin ruwan cikinsa idan kana zaune a wurin.
Da farko hanyar da za ta sada shi da upstairs ya nufa, amma sai ya juyo ya fasa bi ta nan, dan ta cikin living room ɗin ma akwai wani stairs ɗin da zai kaika sama. Ya bi ɗayar hanyar da za ta kai shi living room, komai dake cikin living room ɗin gray color ne, daga can dinning area ya hangi mahaifinsa Iƙbal Alhadi, tare da mahaifiyarsa Zahra Ali, zaune suna dinner.
Wurin ya nufa yana kallon Imminsu, wadda ita ma ta ankara da shi, yana isa inda take ya sunkuya ya sumbaci kanta, sannan ya kama hannayenta ya sumbata.
“Masa’ul khair ya Immi (Barka da yammaci Immi)”
Zahra ta yi murmushi tana kallon ɗanta, ta shafa kansa tana amsawa.
“Shu wa aina Gulzar?” (Ina Gulzar ne?)
Ya tambaya ganin bai ganta tana dinner tare da su ba, Immi ta amsa masa da.
“Ab us ne khaana khtm krte dekha aur kamre mein waaps chla gaya”
(Yanzu ta gama cin abincinta ta koma ɗaki)
“Ɗayib ana rayih (Okay ni ma na tafi)”
ya bata amsa cikin harshen larabci, saɓanin ita da ta masa magana da harshen Urdu, ba wai dan bai iya mayar da amsa cikin yaren ba, sai dan ya san ita ma Immin tana jin larabcin.
A wasu lokutan ma idan za su yi magana tsakanin su uku sai su dinga haɗa larabci da Urdu, saboda Urdu shi ne harshen Zahra. Ba tare da ya yi wa Abby magana ba ya shiga ƙoƙarin barin wurin, sai dai tun da ya tsaya a wurin shi Abbyn ke binsa da kallo, ya lura da yanzu sam Arman ba ya son masa magana, saboda daga ya masa magana zai tado masa da zancen zama shugaban kamfanin Alhadi.
Kuma ya lura da ɗansa ba ya son maganar kamfanin ko abin da ya shafe shi, idan zai iya tunawa ma rabon Arman da kamfaninsu tun shekaru biyar da suka wuce, lokacin da suka yi murnar cikar kamfanin shekaru 30 da kafuwa. A yanzu babban burinsa bai wuce Arman ya zama shugaban Alhadi Group of Companies ba. Domin ba ya so ya mutu ya bar gadon kujerar shugabancin kafanin a hannun ɗan ɗan uwansa Faisal.
A cikin halayen arziƙi Faisal ba shi da guda uku ƙwarara, kuma sam bai yi kama da wanda zai zama shugaba na gari ga ma’aikatan kamfanin ba, sannan a ƙa’ida, idan har Arman ya ƙi amincewa da karɓar shugabancin kamfanin to Faisal shi ne wanda zai karɓi kujerar. Ƙoƙarin karkato da hankalin Arman shi ne abin da yake ta son yi tun kafin lokaci ya ƙure musu, amma shi Arman ya kasa ganewa.
A ko da yaushe yana ɗaukan kansa a ba jowa ba, ya bar zuciyarsa ta mutu, saboda an ce masa dan yana da matsalar gani ba zai iya zama jagoran kamfanin Alhadi ba. Kuma saboda yanda ake aibata lalurar tasa yasa ya tsani duk wata harka ta kamfanin.
“Armaan ina zaka je ba ka gaishe da Abby ba?”
Immi ta dakatar da shi, hakan ya sa ya juyo, ya kalli Abby da shi ma ke kallonsa.
“Masa’ul khair Abby”
Ya faɗa daga nan inda yake, dan a yanzu ko kusantar Abby ba ya so, daga ya kusance shi zai ji kamar yana kusantar kamfanin Alhadi ne. Abby ya sauƙe numfashi yana kallon ɗansa, sannan a hankali ya jinjina kansa yana amsawa, Arman na jin ya amsa ya juya ya nufi sama.
Dan sam ba ya ma son zamansa da Abby ya yi tsayi, dan daga sun ɗan jima a wuri zai fara masa maganar da ta mutuwarsa ta fita daɗin sauraro a kunnensa. Yana shiga corridorn ɗakunansu ya hangi Gulzar na nufowa downstairs da alama wani abin za ta yi a ƙasa.
Farar matashiyar da za ka iya kira da balarabiya sanye take da baƙin wide black jeans, da farar blouse top, ƙafafunta cikin fluffy sliders farare, dogon gashin kanta kuwa sai reto yake a bayanta. Ita sam ba ta kama da indiyawa, saɓanin Armaan da kammaninsa suka sirka da na Immi, ita Gulzar sak Abby ce, wayarta ce riƙe a hannunta tana latsawa, da alama ma ba ta lura da shi ba.
Arman ya yi murmushi yana gyara zaman glasses ɗinsa, sannan ya fara taku a hankali yana nufarta, sai da ya je dab da ita sannan yace.
“Me dogon gashi!”
Ya faɗa da ƙarfin da ya razana Gulzar, har wayarta na suɓucewa a hannunta, ta kalli wayarta da ta faɗi ƙasa sannan ta dube shi tana haɗe girar sama da ta ƙasa, ta kai masa duka a ciki tana faɗin.
“Duk ka bi ka tsorata ni!”
Arman ya dafe wurin da ta daka a cikinsa yana dariya, sannan ya sunkuya ya ɗauko mata wayarta, ya miƙa mata, ta warce wayar tana harararsa.
“Idan ka sake min irin wannan sai na faɗawa Immi ta min maganinka”
Ta faɗa tana nuna masa ɗan yatsa, Armaan na dariya ya dafata tare da juyata suka nufi ɗakinsa.
“Ina am imzah! Bas, mu aksar (Wasa fa kawai nake miki ba komai ba)”
Gul ta mintsini cikinsa tana faɗin.
“Kada ka sake min irin wannan wasan”
Armaan ya saketa yana dafe inda ta mintsi ne shi.
“Yarinyar nan kin iya mugunta”
Gul ta matsa daga jikinsa, dan ta san halinsa, yanzu zai ce zai riƙe mata gashinta da ta fi so, dan ko sau ɗaya ba ta jin ta taɓa rage tsayinsa.
“La wain rayiha? (Ina kuma za ki je?)”
Ya tambaya yana kallonta, ta ruga da gudu, shi ma ya bi bayanta zuwa ɗakinsa. Gul na shiga ɗakinsa ta faɗa kan gadonsa tana dariya. Shi kuma yana shigowa ɗakin ya yi tsaye yana kallonta a kan gadonsa. Kansa kawai ya girgiza, ya nufi wurin da ya saba aje awards ɗin da yake samu a wasan fencing da yake yi.
Ɗakin nasa na da girma, komai na ɗakin brown da fari ne, gadonsa na daga bangon yamma na ɗakin, yayin da balconyn dake cikin ɗakin yake ta bangon gabas, ta yanda daga hasken rana ya fito zai sauƙa kan gadon, dan slide glass door ce a wurin.
Akwai dressing mirror da ‘yan wasu tarkacensa a ɗakin, yayin da closet ɗinsa ke cikin banɗaki. Babu tarkace da yawa a ɗakin, amma komai ka ga a ɗakin sunan kuɗinsa yake furtawa, dan kallo ɗaya za ka masa ka fara ƙissima tsadarsa. Daga kusa da chest drawern da ya saba jera awards ɗinsa kuwa, hotunansa, da wanda suka ɗauka shi da su Gulzar da Immi, da nasa shi da su Ivana ne manne a ko ina.
“Ni fa kallon mara aikin yi nake maka aki! Ni ban ga dalilin da zai sa ina koyon wasan takobi ba. Bayan ni ba a 18th century nake rayuwa ba. Yanzu kai ya waye, babu wanda yake faɗa da takobi, da ma koyon harbi kake da sai na ce dama-dama!”
Ya juya ya kalli Gulzar dake zaune a tsakiyar gadonsa tana danna wayarta. Lokaci guda kuma wannan yaƙin da ya saba yin mafarkinsa ya kutso cikin tunaninsa. Shi kansa ba ya ce ga dalilin da yabsa yake son koyon wasan takobi ba, amma haka kawai iya sarrafa takobi ke burge shi.
“Ba ni na zaɓi fencing ba Gul! Fencing ne ya zaɓeni”
Ya bata amsar yana cilla mata backpack ɗinsa, ta cafe jakar tana kallonsa sanda ya shiga bathroom. Wayarta ta aje a gefe, sanna ta buɗe jakar, ta soma fitar da wasiƙun dake ciki, wanda yawancinsu ‘yan matan dake sonsa ne ke turowa.
“Aki waɗannan fa? Ko tsofi ne?”
Ta tambaya da ɗan ƙarfi, dan ta ji ya kunna ruwa, alamun wanka zai yi.
“Satin da ya wuce aka aiko da su!”
Shi ma ya bata amsa daga cikin bayin, Gulzar ta buɗe ɗaya daga ciki, sannan ta fara karantawa a bayya ne.
“Zuwa ga kyakkyawan tauraron wasan fencing da babu kamarsa a MK fencing acadamy. Haƙiƙa ka iya sarrafa takobi cikin ƙwarewa, kana bawa takobi umarni cikin iko da burgewa, ka haɗu sosai Arman!…”
Gulzar ta zaro ido tana rufe bakinta.
“Aki ai wanna ‘yar makarantarku ce”
Tana jiyowa dariyarsa a cikin bayin, kafin taji ya bata amsa da.
“Ba ɗaliba ba ce, malama ce!”
Ita ma Gulzar ɗin kwashewa ta yi da dariya, sannan ta aje wadda ke hannunta ta ɗauko wata ta shiga karantawa, har Armaan ya fito daga bathroom ɗin sanye cikin blue polo shirt da baƙin cargo trouser. Ya tsaya a jikin dressing mirror yana busar da sumarsa da ya jiƙa yayin wankan da ya yi.
“Ke dan Allah ki aje wannan wasiƙun da ba ƙarewa suke ba”
Gulzar ta kalle shi ta cikin madubin da yake tsaye a gabansa, sannan ta aje wasiƙun agefe, ta saka hannunta a cikin jakar, ta fito da tikitin Coca-cola Arena da suka siya ɗazu. Ta karanta tikitin, sannan ta kalli Arman tana faɗin.
“Wai yau Chris Brown ya yi live performance kuma ka je amma ba ka faɗa min ba?”
Ta tambaya tana sauƙa daga kan gadonsa, Arman ya aje dryer dake hannunsa, sannan ya juyo ya kalleta.
“To ai abin ne ya zo a ƙurace!”
Gulzar ta iyo kansa da gudu tana faɗin.
“Ai ka iya ɗaukan abokanka zuwa wurin! Ni kuma ka barni a nan”
Shi ma gudun ya saka ya fice daga ɗakin, tana biye da shi har zuwa saman gidan, dake ɗauke da sitting areas, daku ma runfunan shaƙatawa. Masu aikin gidan kuma ma aikin tsaftace wurin, Arman ya zauna a kan kujera yana kallonta.
“Ki yi hakuri mana me gashi”
Gulzar da take a fusace, ta sa hannu ta mayar da gashinta da ya suƙo mata kan fuska zuwa baya tana huci, sannan ta zauna kusa da shi tana ture shi.
“Ni dai ka cuceni”
Ta faɗa tana sake ture shi, hakan ya sa glasses ɗin dake idonsa ya faɗi ƙasa, duhu ya mamaye sashin ganinsa, dan daga zarar ya rabu da glasses ɗin babu abin da yake gani face duhu. Cak ya tsaya yana motsa idonsa da babu abin da yake gani da shi, hannunsa ya miƙa kan inda yake zaune, yana laluben glasses ɗin nasa, dan ko tafin hannunsa ba ya iya gani, ita ma Gulzar ɗin sai a lokacin ta lura da shi.
“Ya Ilahi ana asfe aki” (Wayyo Allahana ka yi haƙuri Yayana)
Ta faɗa tana ɗaukan glasses ɗin nasa da ya faɗi ƙasa, ta goge shi a jikin rigarta, sannan ta saka masa shi. Glasses ɗin na hawa kan fuskarsa ya fara gani, sai ya raintse idonsa, sannan ya buɗe.
“Mein bahut off-sori hoon bhradaar, mein iss ka matlab nahin tha…”
(Ka yi haƙuri Yayana, ba da niyya na maka hakan ba)
Ta faɗi cikin harshen Urdu tana dafa kafaɗunsa, sai ya riƙe hannunta yana girgiza mata kai.
“Ma fi shi, insi halla (Ba komai fa, ki manta kawai)”
Gulzar ta jinjina kanta, sannan ta miƙa hannu ta ɗauki Hummus daga cikin kayan maƙulashen dake kan teburin kusa da su, ta miƙa masa.
“Za ka ci?”
Ya ɗan yi murmushi yana gyara zaman glasses ɗinsa, sannan ya karɓa daga hannunta, ita ma ta ɗauki wani bowl ɗin suka fara ci tare.
“Yau mun haɗu da Faisal a Coca-cola Arena”
Arman ya faɗa yana kallonta, ita ma sai ta kalle shi tana gyara zama.
“Ya faɗa maka wani abin ko?… Kuma me ka masa?”
Ta jero masa tambayoyin, sai ya yi dariya yana shafa sumarsa dake cikin askin curly top, dan har sauƙowa take kan goshinsa.
“Ban masa komai ba, kuma ban ce masa komai ba, Ivana ma da ta yi ƙoƙarin ce masa wani abin hanata na yi”
Gulzar ta harare shi.
“Shi ya sa gaba ɗaya ya bi ya rainaka, ba finka ya yi a haife ba amma kullum gainka yake kamar ƙaninsa. Ni ba za ka burgeni ba sai ka yarda ka karɓi shugabancin Alhadi. Ba ma ni kaɗai ba daga lokacin za ka bawa kowa na ahalin nan mamaki”
Arman ya ɗaga kansa sama yana kallon taurarin dake ko ina a sararin samaniya.
“Shugabancin babban kamfani kamar Alhadi Group of Companies ya fi ƙarfin makaho kamar Arman, bara a gefen hanya ita ce tafi dacewa da shi!”
Gul ta ja tsaki tana aje bowl ɗin hannunta.
“Wannan ra’yin wasu mutane ne da ban, kuma idan har ka ci gaba da faɗin haka kana nufin shugabancin ya fi dacewa da shashashan mutum kamar Faisal?”
Armaan ya kalleta yana ɗage kafaɗunsa.
“Ban sani ba!”
Gulzar ta ɗauke ka tana juya idonta, kuma idon nata bai sauƙa a ko ina ba sai a kan saman gidan su Faisal dake ɗan gaba da nasu. Daga nan inda suke tana iya hango Faisal da ƙanwarsa Sakina zaune a saman nasu gidan, masu aikin gidan zaune a wurinsu suna musu hidima.
“Kalli can”
Arman ya kalli inda take kallo.
“Yanda Sakina take ji da kanta kai kace ita matar sarkin Dubai ce. Ko a makaranta ba ta da ƙawaye sai ‘ya’yan masu kuɗi. Kullum jin kanta take kamar wata sarauniya, tana kashe kuɗi ta yi yanda ranta yake so. Shi kuma Faisal, lalataccen ɗan da babu uban da zai yi alfahari da shi, a ƙalla ‘yan matansa sun kai sha bakwai, babu hotel ɗin da bai taɓa zuwa ba a Dubhai, har ɗaki yake da shi a Burj Khalifa, yanda yake wadaƙa da kuɗi za ka ɗauka cewa babansa ne a kan kujerar shugabancin Majmu’at Shirkat Alhadi, daga an taɓasu za su ce su ne Faisak (FAISAL AND SAKINA)! Humm! Abin haushi”
Ta ƙarashe tana mayar da gashinta dake kan kafaɗunta zuwa bayanta, Arman ya yi dariya.
“Komai lokaci ne Gul, ki ƙara haƙuri”
Ta masa wani irin kallo, sannan ta ɗauke kai.
“Lokacin ba zai ƙare ba har sai ka karɓi shugabancin Alhadi.”
“Wannan lokacin ba zai taɓa zuwa ba”
Arman ya bata amsa zuciyarsa ɗaya. Da Gulzar ta ga takaicin ɗan uwan nata na neman kasheta sai ta miƙe ta bar shi a wurin.
“Gobe laraba, ka shirya zan rakaka wurin Doctor Ƙuraishi”
Ta faɗa tana barin wurin, Armaan ya yi dariya, Dr Kuraishi shi ne likitan idon da yake duba shi tun yana ƙarami.
*House No. 34, Street 12, Al Mankhool, Bur, Abu Dabhi, Dubai.*
ADAM POV.
A razane ya kalli tvn da Maama ta ƙure Volume ɗinta, razannaniyyar ƙarar da ta fito daga cikin tvn ce take naiman sawa ya saki fitsari yana zane.
“Maama dan Allah ki rage Volume ɗin nan”
Ya faɗa yana marairaicewa, kuma cikin harshen hausa, dan a gida sam ba ya larabci ko wani yaren da ba hausa ba, sai idan ya shiga cikin abokansa ne yake magana da wani harshen, tun da su larabawa ne, saɓanin shi da ya kasance ɗan bahaushe.
Maama ta yi tsaki, sannan ta kashe kayan kallon gaba ɗaya, ta dawo ta zauna kusa da shi kan sofa, inda yake zaune a tsorace yana cin abinci, Maama ta dungure kansa tana faɗin.
“Kai dai ka ji jiki. Na rasa a ina ka kwaso wannan shegen tsoron, kai ba mace ba, amma tsoro kamar farar kura, na rasa yaushe za ka daina wannan tsoron, ni dai ina jiye maka ranar da tsoron nan naka zai kasheka kana tsaye.”
Ya ƙifƙifta idonsa yana haɗiyar abincin dake bakinsa.
“Ya kamata gobe ka je wurin aiki, tun da yau ba ka je ba”
Ya jinjina kansa, dan har yanzu a dame yake.
“Akwai sauran wani aiki da shugabanmu ya bani. Ina so na ƙarasa kafin gobe”
Maama ta ɗauki wayarta, sannan ta miƙe tana faɗin.
“Ya kamata dai, kuma saura ka sake kallon wani film ɗin ban tsoron, wallahi ko ta kanka ba zan bi ba”
Sai ya ɗan yi murmushi yana kallonta, har ta bar shi nan zane a falon, a ƙalla yanzu kimanin shekaru biyar ke nan da rasuwar mahaifinsa. Kuma tun bayan lokacin ya rage daga shi sai Maama ne kaɗai suke rayuwa a gidansu. Mahaifinsa yana aiki a wata asibiti dake nan Dubai, kuma aikin shi ne abin da ya rabo shi da mahaifarsa wato Zamfara Nigeria. Dan shi kansa Adam ɗin ma a nan Dubai aka haife shi, kuma har bayan rasuwar Mahaifinsa ba su koma Nigeria ba, saboda shi ma yana aiki a nan.
Salma Ahmad Isah ✍️
_Har yanzu somin taɓi ne, domin muna duba da rayuwar jaruman namu ne, kafin mu tsunduma cikin labarin… Ku fai kada ku gajiya, ku biyoni domin jin yanda za ta kaya…_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
. 🪄…JUYIN KWAƊO…🪄
©️Salma Ahmad Isah
SalmaAhmadIsah @ArewaBooks
SalmaAhmadIsah @Wattpad
Page-3
*Moorfields Eye Hospital, 20 street Al Razi Building 64, Block E, floor 3, Dubai.*
ARMAN POV.
“Buɗe idon a hankali”
Dr Ƙuraishi ya bawa Arman umarnin yayin da ya gama duba masa idonsa. Arman ya buɗe idonsa a cikin hasken da Dr Ƙuraishi yake haska idonsa. Amma babu abin da yake gani face duhun da ya saba gani, saboda shi bai san banbancin da yake tsakanin idonsa na a rufe ko a buɗe ba, tun da duka biyun abu ɗaya yake gani.
“Kana iya ganin wannan hasken?”
Dr Ƙuraishi ya tambaya.
“Ba na ganin komai Dr babu komai sai duhu”
Dr Ƙuraishi ya kashe fitilar da ya haska idon nasa, sannan ya ɗauki glasses ɗinsa dake aje a gefe, ya mayar masa shi idonsa yana faɗin.
“Za ka iya sauƙowa”
Arman ya gyara zaman glashin, sannan ya sauƙe ƙafafunsa ƙasa, ya ɗauki canvas ɗinsa dake aje a ƙasa, ya saka a ƙafarsa, sannan ya dawo cikin main office ɗin Dr Ƙuraishi, inda Gulazar ke zaune tana jiransu.
“Babu wani ci gaba!”
Dr Ƙuraishi ya faɗa yana miƙawa Gulzar takardun lafiyar idon Arman ɗin. Gulzar ta karɓa, sannan ta kalli ɗan uwanta da shi ma yake kallonta.
“Za mu iya tafiya?”
Ya tambaya yana murmushi, shi sam bai ga wani abin shiga damuwa ba, dan ya san sam babu ci gaba a lafiyar idon nasa, ba dan Gulzar ɗin ta takura masa ba ma da ba zai zo ba, dan tun daren jiya ta yi booking appointment. Gulzar da gaba ɗaya take a dame ta miƙe, sannan ta ɗauki bag ɗinta ta rataya a kafaɗarta, ta bi bayansa suka bar office ɗin.
Suna tafiya a hanya ya dafa kafaɗarta yana bata haƙuri, kamar ita ce marar lafiyar ba shi ba. Har suka shiga mota suka nufi hanyar gida Gulzar ba ta sauƙo ba. Sai da suka kusa kaiwa unguwarsu kiran PAn Abby ya shigo wayar Gulzar.
“Alo Falak ya kike?”
Ta faɗa bayan ta ɗaga kiran, daga ɗayan ɓangaren Falak ta amsa, sannan ta faɗi dalilin kiran nata.
“Agha (Honorable person) Iƙlab ne yake son ganinki yanzu a kamfani”
Ta tattare girarta tana ɗagawa Arman hannu alamun ya dakata, ya dakatar da motar yana kallonta.
“Lafiya yake naimana?”
“Eh yace yana son ganinki ne”
“Ɗayib jaye! (Okay gani nan zuwa)”
Ta sauƙe wayar tana kallon Arman.
“Abby yana son ganina a kamfani, dan Allah ka kaini can”
Ba tare da yace komai ba ya jinjina kansa yana gyara zaman glashin dake idonsa, sannan ya ja mota ya juya akalar tuƙin nasa zuwa Alhadi Group of Companies. Duk kuwa da ya jima rabon da ya je kamfanin, amma tun da ta buƙata ba zai ƙi kaita ba.
*Majmu’at Shirkat Alhadi, Al Saaha street, Lobby C, Downtown Burj Khalifa, Abu Dhabi, Dubai.*
“Jininka ya hau da yawa Sayid Iƙbal (Mr Iƙbal). Ya kamata ka riƙa sauƙaƙawa kanka”
Faɗin likitan Sayid Iƙbal, yayin da yake tattare blood pressure monitor ɗin da ta yi amfani da shi wurin duba hawan jinin nasa, saboda haka kawai ɗazu ya yanke jiki ya faɗi ba gaira ba dalili. Zaune yake a kan wata boudoir chair, yayin da suit ɗin da ya cire daga jikinsa ke rataye a jikin chair ɗin. Ya lumshe idonsa yana shafa damtsen hannunsa da aka cire abin blood pressure monitor ɗin a jiki. PAnsa na tsaye a gefe, haka ma babban abokinsa Sayid Nusayr (Mr Nusayr), duka sauna cikin karafaren office ɗinsa dake ma’aikatar ne.
“Ni zan wuce”
Cewar Dr, yayin da ya gama haɗa kayan gwajinsa, sai a lokacin Sayid Iƙbal ya buɗe idonsa, sannan da ido ya yi wa Falak alama da ta raka Dr, ta jinjina kanta tana nunawa Dr hanya.
“Mu je na rakaka Dr”
Daga haka suka fice daga office ɗin. Suna fita Sayid Nusayr ya zauna kusa da Abby yana masa sannu.
“Bai kamata ka riƙa saka damuwa a ranka ba Iƙbal”
Abby ya kalle shi yana sakin hannun dress shirt ɗin dake ƙasan suit ɗin da ya cire, dan bayan suit ɗin akwai waist coat a ƙasa. Zamansa ya gyara yana shafa sumar kansa da ta fara sirkawa da fari, alamun tsufa ya fara masa sallama.
“Dole na shiga damuwa Nusayr! Sam Arman ya kasa fahimtar abin da nake son nusar da shi, ba na so na faɗi na mutu na bar shugabancin kasuwancin da na sha wahala kafin na kafa shi a hannun da ba na gari ba. Da ace Akhi Anwar da kansa ne yake son shugabantar kamfanin na bayan raina ba zan ji komai ba, amma Faisal yake so ya danƙawa shugabancin nan, ya nuna shi ba shi da sha’awar ci gaba da kasuwanci. Arman ba ya son karɓan abin da yake nasa, Gulzar mace ce, kuma har yanzu tana da ƙarancin shekaru, sam ba za ta iya shugabantar babban kafani kamar wannan ba… Na rasa abin da zan yi!”
Nusayr ya girgiza kai cike da tausayin abokinsa.
“Ka yi haƙuri Iƙbal, ka ci gaba da addu’a, da yardar Allah ba za ka mutu ba har sai ka ga Armaan a kan waccan kujerar!…”
Ya ɗan yi fasali yana nuna hamshaƙiyar kujerar dake office ɗin, sannan ya ci gaba da faɗin.
“A matsayin shugaban kamfanunuwan Alhadi..”
Abby ya yi murmushi me sauti.
“Wannan shi ne mafarkin da na daɗe ina yi, kuma da dukkan fatan duniya nake roƙon Allah ya sa ya zama gaskiya kafin na bar duniya”
Kafin Nusayr ya kai ga faɗin wani abu Gul ta buɗe ƙofar office ɗin ta shigo a dugunzume. Tana ganin Abby zaune ta fara hawaye, ta nufe shi da gudu ta faɗa kansa ta rungume shi tana kuka.
“Abby!?”
Abby ya shafa dogon gashin kanta dake cikin style ɗin long wavy. Yana murmushi, a da Arman ne yake masa haka, saboda a baya Arman ya fi kusanci da shi fiye da kowa. Amma a yanzu Arman ya fi gudunsa fiye da kowa, kuma ba komai ya ja hakan ba face maganar gadon kamfani da yake yawan yi masa.
“Abby me ya sameka?”
Abby ya sake yin murmushi yana shafa gashin kanta.
“Lafiyata ƙalau, kawai na ɗan ji jiri ne, sai na yi kamar zan faɗi, amma babu abin da yake damuna”
Ta kwanta a jikinsa tana kallon Sayyid Nusayar dake murmushi.
“Ammu Nusayr wai haka ne?”
Sayid Nusayr ya jinjina mata kai.
“Abby ka dinga kula dan Allah.”
Ta ƙarashe tana kallon Abby, Abby ya share ƙwallar da ta zubo mata yana gyaɗa kai, sannan ya sumbaci kanta yana kwantar da kanta a kafaɗarsa.
“Ina ɗan uwanki? Imminku ta faɗa min cewa tare kuka fita da shi”
Nan da nan ta ɓata fuska.
“Yana reception, wai zai jirani a can”
Abby ya girgiza kansa, dan ya sam dalili, wato shi ba ma zai shigo ba, ballantana ya ga office ɗin da bathroom ɗinsa ma ya fi shi muhimmanci a wurinsa.
“Ki yi haƙuri, Akuki (Ɗan uwanki) zai daina duk wannan abin da yake”
Ran Gulzar a ɓace tace.
“Ai sai dai idan zamanin baya yaje ya dawo, sannan ne zai sauya ra’ayinsa, taurin kai ne da shi kamar mutumin wancan zamanin!”
Abby ya dungure mata kai.
“Kin taɓa ganin wanda yaje zamanin baya ya dawo?…”
Ta turo baki tana tura gashinta baya, sannan ta kwanta a jikinsa tana zuba masa shagwaɓarsu ta autanni.
*
“Asirul laimun wu bass (Juice ɗin orange ma ya isa)”
Ya bawa ma’aikacin kamfanin da ya tambaye shi abin da yake son sha amsa. Ma’aikacin ya amsa da to, sannan ya bar wurin, Arman ya ɗaga idonsa yana kallon katafaren reception ɗin kamfanin dake ƙasan ma’aikatar. Gaba ɗaya jinsa yake kamar zaune a kan ƙaya, dan ko kaɗan ba ya son abin da zai haɗa hanyarsa da ta kamfanin nan, kamar yanda Faisal ya saba yi wa rayuwarsa karan tsaye, haka ma yau ya masa.
“Makaho!?”
Idonsa ya rintse yana gyara zaman glasses ɗinsa, kafin ya buɗe idon nasa ya ɗaga kai ya kalle shi, sai dai yau ba shi kaɗai ba ne, akwai Sakina tare da Anwar mahaifinsu. Kansa ya kawar daga barin kallonsu, dan haka kawai ya ji zuciyarsa na hassala da dariyar da suke masa.
“Kaya ka kawo kamfanin ne?. Dan na san ko cikin ma’aikatan dake wurin nan babu makaho irinka” Cewar Sayyid Anwar yana dariya.
Arman ya dunƙule hannunsa yana haɗiyar yawu da ƙyar, dan yau ji yake kamar ba zai iya ɗaukan cin zarafin da suke masa ba.
“Ai ko a cikin masu shara babu makaho Abbu, ballantana a cikin masu kawowa kaya”
Sakina ta faɗa tana tata dariyar. Arman bai tanka musu ba, kansa kawai ya sake sunkuyarwa, saboda yanda mutanen dake kusa da su suka fara kallonsa.
“Allah sarki makaho! Su fa da ma makafi ba su da wani aiki da ya wuce bara a gefen hanya… A taimaka min da sadaka! A taimaka”
Faɗin Faisal yana kwatanta yanda mabarata ke bara. Arman ya miƙe da sauri zai mayar musu da martani muryar Abby ta kaste shi.
“Arman!”
Ya tsaya cak da shirin dukan da yake son kaiwa Faisal yana huci, ya dunƙule hannunsa da mugun ƙarfi yana jin kamar ya daki bango ko zai huce. Abby da Gulzar da suka sauƙo ƙasa tare suka tsaya a wurin suna kallonsu.
“Me yake faruwa?”
Abby ya tambaya yana dafa kafaɗar Arman. Amma sai Arman ɗin ya kauce, ya kalli Gulzar.
“Idan kin gama ina mota”
Yana gama faɗin hakan ya juya zai bar Building ɗin kamfanin. Har ma’aikacin da ya tafi kawo masa ruwan laimo na binsa da shi yana faɗin ga ruwan laimon nan ya kawo masa, amma bai tsaya ba ballantana ya karɓa. Tun da Gulzar ta ga haka ta san cewa wata baƙar maganar Faisak (FAISAL AND SAKINA) suka faɗawa ɗan uwanta da har ta sa ya shiga wannan halin.
“Me kuka gayawa ɗan uwana?”
Ta tambaya tana raba idonta a kan su ukun. Amma babu wanda ya amsa mata, sai murmushin da suke suna duban juna.
“Wai ko kunya ba ku ji?… Sakarkaru kawai!”
Ta faɗa rai a ɓace, sannan ita ma ta juya ta bi inda ɗan uwanta ya bi ba tare da ta yi wa Abby sallama ba. Daga Anwar har FAISAK ba su ji haushin abin da Gulzar ta yi ba, dan sun san su ne a gaba.
“Na ji an ce ka faɗi da fatan ba wata matsalar ba ce?”
Sayyid Anwar ya tambaya yana duban Abby da murmushi, Abby dake cikin jin rashin daɗin halin da yaransa ke ciki ya girgiza kansa.
“Na ji sauƙi”
“To sai a kula nan gaba, dan wata ƙila idan an faɗi ba lalle a tashi ba!”
Faɗin Sayyid Anwar yana murmushi, tare da taɓa kafaɗar Abby, sannan ya ja yaransa suka bar Abby cike da zullumi.
*FACT MAGAZINE, Building 8, Dubai Media City, Abu Dhabi, United Arab Emirates.*
ADAM POV.
Sanye yake cikin baƙin dress trouser, da farar sweat shirt, kafaɗarsa rataye da briefcase ɗinsa, ƙafafunsa cikin moccasin dockside. Sumar kansa me ƙarfi irin ta Africans na cikin askin crew cut. A ɗarare ya ƙarasa seat ɗinsa dake cikin na tarin ma’aikatan kamfaninsu ya zauna yana raba ido. A hankali ya aje briefcase ɗinsa a kan table, sannan ya buɗe system ɗinsa dake kan table ɗin, ya ciki gaba da aikin da bai ƙarasa ba.
Adam baƙi ne a kalar fata, kuma dogo ne, sannan yana da kyau dai-dai gwargwado, dan a fuskarsa ba ka ce ga abin kushe ba. Yana tsaka da aikin da yake wani cikin abokansa na wurin ya lallaɓo ta bayansa, ya shammace shi yace.
“Booom!”
Da ƙarfi, hakan yasa Adam ya zabura har yana ɗaukewa ƙafafunsa daga ƙasa, zuciyarsa kuwa kamar ta fasa ƙirjinsa ta fito tsabar tsoro. Sai jujjuya ido yake yana haki, abokin nasa da ya tsorata shi ya kwashe da dariya yana tafa hannu. Haka sauran abokan aikinsa da teburan aikinsu ke kusa da nasa suka taya shi dariyar.
“Matsoraci!… Ka gama aikin da shugaba ya baka?”
Abokin nasa ya tambaya yana duba system ɗinsa, Adam ya masa banza yana sauƙe ƙafafunsa da ya ɗora a kan kujera zuwa ƙasa, tare da dafe ƙirjinsa dake barazanar ɓallewa.
“Haisam bana son irin wannan, kuma ka sani”
Ya faɗa cikin son nuna ɓacin ransa a kan abin da Haisam ɗin ya masa, Haisam na dariya ya dafa kafaɗarsa yana faɗin.
“Ka yi haƙuri abokina, a duk sanda na ganka cikin tsoro nishaɗi kake bani”
Adam ya galla masa harara yana ɗauke kai. Har Haisam ya ƙaraci surutansa bai ce da shi uffan ba. Har ya ƙyale shi dan dole, ya ci gaba da aikin dake gabansa, kafin landline phone ɗin dake kan teburinsa ta shiga ruri. Shi ma ringing ɗin wayar sai da ya kusa tsorata shi, da ƙyar ya saita kansa ya ɗaga wayar.
“Sabahul Khair Ustaz (Barka da safiya shugaba)”
Ya faɗa bayan ya ɗaga wayar, dan kira ne daga wayar ogansu.
“Barka da safiya, da fatan ka gama aikin da na baka?”
Ya jinjina kai yana faɗin.
“Eh Ustaz na kammala shi”
“Ina son ganinka yanzu a office ɗina”
“Hadir Ustaz (To Shugaba)”
Daga haka ya aje wayar, ya ɗauki system ɗinsa ya miƙe ya nufi office ɗin ogan dake can wata kusurwa ta ma’aikatar. Sai da ya ƙwanƙwasa ƙofar gilashin dake ofishin, dan ko daga nan inda yake yana iya ganin ogan nasu zaune a kan kujerarsa yana cin shawarama, sai da Ustaz ya ba shi izinin sannan ya shiga da sallama.
Shugaban ya amsa sallamar da ya yi yayin da yake zama a kan kujerar ofishin nasa. A ladabce ya buɗe system ɗinsa, sannan ya miƙawa Ustaz. Ustaz ya karɓa, ya shiga duba ayyukan yana jinjina kai, alamun sun burge shi.
“Hotuna sun yi kyau Adam. Kuma na ji daɗin ganinsu a haka… Lalle na jinjinawa ƙoƙarinka”
Adam ya yi murmushi me sauti yana faɗin.
“Haza wajibi Ustaz (My pleasure shugaba)”
Ustaz ya jinjina kai shi ma yana murmushi, sannan ya aje guntun shawarman da bai ƙarasa cinyewa ba, ya kalli Adam, kana ya furta masa dalilin ƙaddarar da za ta zama silar juyin rayuwarsa.
“Nan da wattani biyu masu zuwa gwamnatin Dubai na shirin bamu kyautar karramawa, a wannan bikin da za’ayi ina so mu gabatar da hotuna masu kyau da jan hakali. Hotuna irin wanda ba’a saba ganinsu ba, kuma ina so ya zama kai ne wanda zai zo da hotunan… Da fatan za ka zo min da abin da zan yaba”
*Dubai Miracle Garden, Street 3, Al Barsha South, Dubai.*
IVANA POV.
“Na gode”

Leave a Comment