Books Reviews & FAQs

Cuta Ta Dau Cuta Hausa Novel

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

 

_Shafi na ɗaya_

 

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan ALLAH, Mai rahama, Mai jin ƙai._

……..“Ango! Ango!! Ango!”. Itace kalma mafi rinjaye da tafi fita a bakunan taron matasan dake cike da ƙofar gidan. Yayinda wanda suketa faman kira da angon bakinsa ya kasa rufuwa dan farin cikin da yake a ciki a wannan rana data kasance ta aurensa da masoyiyarsa mafarkinsa. Magana da ɗaya daga cikin abokansa ya gwargwaɗa masa a kunne ta saka shi jan hannunsa suka koma gefe. Cikin ɗan nuna yanayin damuwa da hasala ya ce, “MB ya akai haka kuma? Nifa bana son matsala wlhy, duk abinda zan ɓatama Love rai bana son shi musamman a wannan ranar ma data kasance mana ta daban…..”
“Na sani kwantar da hankalinka, kaima kasan dai bazan bari wani abinda zai ɓata farin cikinka faruwa ba JJ. Na faɗa maka ne kawai dan kar kaga an samu canji, dan yanzu haka ma nariga na daidaita matsalar, wajen da aka samu yanzu ɗin ma yafi wancan komai…”
“Amma karka manta wajen farkon muka saka a invitation card”.
“Hakan bazai zama matsala ba shima, dan kusa-da-kusa suke, dabarar da zamuyi zamu ajiye su Nure a ƙofar wancan hall ɗin duk wanda yazo sai su turosa inda aka canja ɗin. Yanzu sai ka sanarma amarya kawai, ko hakan baiyi ba?”.
“A yayi, kunyi ƙoƙari, ALLAH ya bar zumunci bari na sanar mata”.

*_DINNER HALL_*

Matuƙar ƙyau da ƙayatuwa wajen yayi tamkar dama tun farko nan suka shirya yin shagalin. Kalar decoretions ɗin wajen kalar ankon ƴammatan amarya da suka sha ƙyau har suka gaji, haka suma abokan ango shar da su. Shigowar ango da amarya ta shafe duk wani ƙyawun kowa a wajen, dan adonsu na musamman ne. Atake hasken flash ya shiga tashi tako ina, tsakanin wayoyi da camaras, a gefe mc na faman kwarzantasu, yayinda dj ya saki wani cool music mai ratsa zuciya. Ta ko’ina dai taro ya cika taro kam sai masha ALLAH, abokan ango da ƙawayen amarya nata taka rawar gani irin na bajinta tare da dangi takowace ɓangare. A yanda aka tsara komai zaka iya saka masu bikin a layin masu hannu da shuni, sai dai sam ba haka bane ba, ana dai tsaka tsaki, wato babu tsiya babu hamshaƙin arziƙi. Sai dai akwai rufin asirin ALLAH ta kowanne ɓangarorin guda biyu. Anyi taro an tashi lafiya kusan ƙarfe ɗayan dare, ango na son maida amaryarsa gida da kansa yayarta tace karya damu yaje gida ya huta zasu wuce da ita. Babu yanda ya iya dole ya haƙura suka dunguma shi da abokansa zuwa hotel da suka kama. Amarya da danginta suma suka wuce nasu gida dan sai gobe in sha ALLAH za’a miƙata gidan mijinta…..

*_WASHE GARI_*

A kaf ƴan rakkiyar amarya babu wanda baiyi santin gidan da aka kawota ba. Dan kuwa dai gida ya cika ya tunbatsa komai zam. Tabbas angon yayi ƙoƙari sai kuma fatan a zauna lafiya. Bayan kammala ƴan kai da kawo na al’ada da rabe-raben kayan gara kowa ya kama gabansa aka bar amarya da ƙawayenta. Sune suka sake gyare mata gida ana faman raha da wasa da dariya komai ya koma kan saitinsa. Sai dai amarya bata da wani kuzari tattare da ita, ba komai ya jawo hakan ba sai ƴar fargabar da aka san duk wata amarya kamila da ita a irin wannan ranar, dama ita gata bamai yawan hayaniya bace, ko ƙawayen ma ba wasu ne daban ba, daga ƴan uwa sai maƙwafta da aka tashi tare. Bayan idar da sallar magrib kowacce ta shiga sake gyara kwalliyarta sukai zaman jiran abokan ango. Ƴan halak ɗin kam basu taushe hannu ba, dan idar da sallar isha kaɗan suka iso gidan. Amarya dai na lulluɓe, yayinda ango yay tsallen turare ɗan goma zuwa inda take ya zauna kusa da abarsa kamar zai rungume, itako tana ta faman matse jiki waje guda abinka da farin shiga ga kunyar baƙunta. Suko abokan ango nata faman masa shaƙiyanci da ido yana musu daƙƙuwa ta ƙasan riga da sakin murmushi. A haka dai akai ƴan abubuwan daya dace tsakanin abokan ango da na amarya, zuwa tara da rabi ango da yaga basu da niyyar basu filin ya murje idanu ya korasu waje. Sun fito suna dariya, yayinda MB babban amininsa ya sinna masa wasu ƙwayoyin magani tare da miƙa masa gorar ruwan hannunsa yana faman ƙyafta masa idanu da masa magana a hankali. “Adai yi tuƙi a hankali, dan wannan motar ƙirar larabawa ce, idan bakai wasa ba amaimakon horn ƙira’ar Alkur’ani zakaji”. A tare suka kwashe da dariya tare da cafkewa bayan ya afa maganin batare da tambayar na miye ba ya kora da ruwa. Ango JJ ya ce, “Shege abokina, kune malaman duniya, dan shugaban mai jan ƙyalli ma a ƙarƙashin koyarwarku yake baza komarsa”. Dariyar suka sake kwashewa a tare, MB yay gaba yana saɓa babbar riga da faɗin, “Idan da matsala kai dai kai kirana da wuri na turo makanike dan ka samu damar fita shan iskar yammaci, na barka lafiya a tuna da maƙota kar’a ishesu da…” bai ƙasa ba ya wani kashe masa ido ɗaya yana ficewa a gate ɗin. Shi dai ango JJ rufe gate ɗin yay yana cigaba da dariyarsa. Kafin ya juya cikin gidan ransa fes yau ranar baje koli ta duniya a cikin rayuwar sa…
Shuuu!! Aka gitta kamar ta gefensa a dai-dai yana kai hannunsa ga handle ɗin ƙofar, kamar zai share da tunanin iskar sanyi data fara kaɗawa ce sai kuma dai ya ji an sake gitta masa yana ƙoƙarin tura ƙofar. Wawwaigawa yay damansa da haggu sai dai kuma babu kowa, cikin nuna halin ko’in kula ya ɗage kafaɗu da taɓe baki ya ƙarasa shigewa a falon.
“Amarya kin sha ƙamshi, amarsu baƙya laifi koda kin kashe ɗan masu gida!”. Ya jero kalaman kirarin tamkar shine ya fara ƙirƙirarsu saboda tsaruwarsu a bakinsa kai kace waƙace a bakin shata ko barmani coge. Bai damu da jin ba’a amsa mar ba, ya murzawa ƙofar key harda gyara labulaye da ƙyau. Turus yaja ya tsaya ƙirjinsa na bada wani irin turururumm tamkar sautin gangar Ado gwanja a tsakkiyar filin biki. Wayam falon babu komai, duk kayan alatun nan da aka ƙawata falon da shi  tamkar wata almara babu su babu alamar su. (Kai ina, wannan almara ce JJ dawo hankalinka) wata zuciya ta ayyana masa. Yawu ya haɗiye da ƙyar, tare da sakin murmushi mai kama da kuka shi adole yana son dawo da hankalinsa jikinsa. Bakinsa na rawa da karkarwa ya furta, “L-o-v-e!” a rarrabe yana runtse idanunsa da ƙarfi. Ba’a amsa mar ba yanzun ma dai, dan haka ya sake ƙarfin halin buɗe ido ɗaya da ƙyar, da sauri ya sake buɗe ɗayan ma ya shiga waige-waige yana haɗiyar yawu da sauri-da-sauri. Yanzu kam falon komai ya dawo kamar yanda yake a da, sai dai kuma kalar kayan ta canja. (JJ! Farin ciki fa ke neman juyar maka da brain, ka daidaita kanka mana). Kansa ya shiga gyaɗawa kamar tsohon ƙadangare cike da son gamsar da kansa akan dole, sai kuma kamar wanda aka ingiza ya nufi bedroom da sassarfa, yana tafiya yana waigen falon. Har ɗan datse hannunsa yake wajen ƙoƙarin rufe ƙofar bedroom ɗin da danna mata key saboda yanda jikinsa ke rawa. Cikin dauriyar azabar dake ratsa masa hannun da ya datsa ya jingina da ƙofar yana sauke nannauyar ajiyar zuciya irin ta na sha da ƙyar ɗin nan. Yakai minti ɗaya a haka kafin ya dai-daita kansa da ƙyar yana sauke ajiyar numfashi a jajjere. Kasancewar sai ka ratsa ɗan lungu daga jikin ƙofar kafin ƙarasawa tsakkiyar bedroom ɗin sosai saboda bathroom dake a wajen ya bashi damar share gumin ɗaya tsatstsafo masa da dai-daita yanayinsa da ƙyar sannan ya cigaba da tafiya a takun da bai gaza huɗu zuwa biyar ba. Bedroom ɗin ƙato ne, ga kayan gado yaji masu ƙyau dan iyayen amarya sun taka rawar gani suma. Ƙoƙarin hana kansa kallon komai yake saboda abinda ya baro baya, dan haka ya nufi gadon kansa tsaye dan yasan dai anan zaiga amaryar tasa sarkin kunya da nutsuwa. Sai da ya kai zaune yana faɗin, “Afuwan Love na barki ke ɗaya, na sallami waɗan nan ƴan matsalar ne, kin san in su MB na waje bakin mutum baya hutaw……”
Ya kasa ƙarasawa sakamakon abinda idonsa ya gane masa. Wata irin murɗaɗɗiyar macijiya ce baƙa ƙirin an mata wata kwalliya da kalar jaja-jaja mai haske kamar ƙwan lantarki. Ba’a labaran tatsuniyoyi da wasanni ba, ko’a film ɗin ƴan India da suka sabayin na macizai bai taɓa cin karo da irin wannan maciji mai girma ba. Rawa jikinsa ya farayi kamar mazari, har takai yana zamewa a saman gadon zuwa ƙasa batare daya farga ba. Gab ya kusa kaiwa ƙasa daɓar yaji an riƙoshi…
“D lafiya kuwa? Miya faru kake irin wannan kakkarwar har kana ƙoƙarin faɗuwa ƙasa?”.
Nutsatstsiyar muryar amaryarsa ta ratsa masa kunne, yayinda lallausan tafin hannunta da tunda ya riƙesa a wajen dinner jiya abin ya kasa barin ransa ke riƙe da shi a yanzu ma. Kusan a tare ita da shi suka zube a ƙasan, dan ya riga ya taho gaba ɗayansa, sannan ya fita nauyi. Faɗowarta jikinsa ya sakashi sakin wani irin ihu tamkar wanda aka farkar a barci da ruwa mai sanyi. Yay wani irin mamuƙeta illahirin jikinsa na rawa. A hankali ta saki ƙara da faɗin, “Wayyo D zaka karya min awazzu.”
Kafin yau idan yaji wannan zazzaƙar muryar tata ji yake yafi kowa sa’a a duniya. Amma a yau maimakon hakan wani irin rawa da kakkarwa jikinsa keyi, ga zufa ta wanke masa illahirin jikinsa tamkar wanda yay wanka. Zumut ya miƙe tamkar wanda aka zabura ya shiga waige-waige, sam babu komai a gadon, sai ma gyaran da yasha na musamman ga filos da aka jera a kansa tamkar an zana a takarda. Sake juyowa yay da sauri yana kallonta da nuna gadon da yatsa, sai dai bakinsa ya kasa furta komai, sai ma rawa da pink lips ɗinsa sukeyi. Cikin rashin fahimta take kallon gadon itama, sai kuma ta dubesa da alamar tashin hankali a tattare da ita. “D! dan ALLAH miya faru, wlhy kana sake rikitani nikam. Jibafa yanda kake zufa. Kana nuna min gado kuma ni banga komai ba a wajen.”
(JJ ka nutsu, karfa ka ɓata wannan daren mai muhimmanci a gareka mana) wani ɓangare na zuciyarsa ya faɗa cikin tsawatarwa. Kansa ya shiga jinjinawa tamkar zuciyar tasa na kallonsa ne, ya haɗiye busashen yawu tare da sakin murmushin yaƙe ga amaryar tasa. “B..ba komai Love, dama fa ina gwada ki ne kawai naga amaryar tawa jaruma ce ko matsoraciya.” ya ƙare maganar yana damƙo hannunta cikin nasa da ƙyau. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi, sai kuma ta duƙar da kanta tana ƙoƙarin janye jikinta daga nashi dan kunya. Yanayin nata ya sake sakashi dawowa hayyacinsa da tuna masa shi ɗin fa ango ne. Ƙoƙarin haɗiye komai yake yi, duk da hakan abune mai wahalar gaske a garesa, amma dai zai gwada yin wannan jarumtar ya gani. Ayatulkursiyyu ya karanta a zuciyarsa yana tattofawa a kaikaice. Sai da ya tabbatar ya ɗaure ɗakin ɗamm acewarsa, kafin ya ƙara ɗan samun nutsuwar sake maida hankalinsa ga amaryar tasa da kanta dai ke a sunkuye.
A karo na farko ya jawota jikinsa ya rungume tsam yana sauke tagwayen ajiyar numfashi, yayinda ita kuma ta shiga masa rawar jiki irin na farin shiga, sai dai bata hanashi ba ko yunƙurin janye jikinta har kusan mintuna biyu daya saketa dan kansa. “Yau dai ga ni ga Love a gida ɗaya, ɗaki ɗaya a matsayin ma’aurata”. Ya faɗa yana sake riƙo hannunta duk biyu cikin nasa da ƙyau tare da gyara zamansa ya fiskanceta. Murmushi ta saki tana ƙara ƙasa da kanta tare da jan mayafinta ta rufe fuskarta. Shima sai ya saki wata ƴar siririyar dariya cike da nishaɗi, hannu ya kai ya yaye mayafin yana mai ɗago haɓarta ta yanda zaiga fuskanta da ƙyau.. Wata muguwar zabura yayi baya yana mai waro duka idanunsa waje jikinsa na karkarwa batare da ya ma sani ba ya furta, “Anoosha!!”.
Cike da salo tai masa luuu da idanu tare da sakin sassanyan murmushin da a fuska ɗaya ya sanshi kuma ya taɓa ganinsa, bai kuma sake ganinsa ba. Tsabar kiɗimewa da shiga ruɗani har yana bugewa da gado wajen zabura da ƙoƙarin tattara babbar rigar jikinsa alamar zai kwasa a guje yaji caraf an riƙesa…….✍️

*_😂😂Tofa babbar magana, wai ango JJ mijin amaryar da ko sunanta bamu sani ba mi shika hwaruwa ne hakanga kuma? Anya kuwa ba….🥱Bara dai na iya bakina abinga walle bana hiɗi bane🤣🤣._*

_Alhamdullahi inata alƙawarin gareku na yin free book ALLAH bai ƙaddara hakan ba sai yanzu. To Amin afuwa gani zan cika alkawarin in sha ALLAH. Ina fatan wannan littafi zai ƙawatar da ku tako wace fiska, cakwakiya, nishaɗi, ƙalubale, ƙaddara, son zuciya, kai abubuwane da yawa ya wawuso tako wace fuska, zakuma ku fahimci saƙon da yake son isarwa, dan salon na musamman ne, idan nace na musamman ina nufin na musamman a gaba ɗaya musamman ɗin😉👌.

*Kumuje zuwa gidan ango muji yaya zai ƙare da wannan daren farko nasa, dan naga na musamman ne fa 🚴🚴🚴😆😆🤫🤫.*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

 

_Shafi na biyu_

……..“Ai babu gurin zuwa, saboda da hannunka ka rufe duka ƙofofin guduwar Mr JJ ango mijin amarya Alimah”. Muryar da baya jin zai manta a rayuwarsa ta ratsa kunnuwansa. Dauriyarsa ta ƙare, hakama ƙarfin halinsa ya kai ƙarshe. A take jikinsa ya fara rawa kar-kar. Gashi an riƙesa irin riƙon da ko numfashin kirki ya gagara yi. Jin saukar numfashin mutum a fuskarsa ta saka shi buɗe idanunsa da sauri. A matuƙar razane ya fasa gigitacciyar ƙarar data ɗauke numfashinsa gaba ɗaya sai gashi ƙasa wanwar a sume…..

A firgice ta buɗe idanunta itama tamkar wadda aka farkar da ga nannauyan barci. Waige-waige ta fara ƙirjinta na wani irin luguden daka. To ita yaushe ma barci ya ɗauketa ne, ba yanzu babu jimawa suka shigo ɗakin nan tare da angonta JJ ba. Dan fitarsa babu daɗewa rakkiyar abokansa ko cikakken minti biyu baiyi ba ya dawo, batama jin yabar jikin ƙofar falon. Cike da zumuɗi da aka san duk wani ango da shi ya koma ya zauna inda ya tashi a kusa da ita. Batare da yayi magana ba kawai ya jawota jikinsa ya rungume yana shinshinar wuyanta. Kunya ta sakata shiga wani yanayi, a take jikinta ya fara mazari ta shiga noƙewa. Dariya ya sakar mata cikin kunne da faɗin, “Ai yau dai kunya ta ƙare Love, miya rage kin zama matar JJ, JJ ya zama mijinki. Please ki ajiye wannan kunyar da safe ƙya maidata dan kin san yau ɗin ta musamman ce fa”.
Bata iya tace da shi komai ba, dan a matsanancin tsorace take ga kuma kunya. Sai dai hakan baisa ta hanashi yin yanda yaso da ita ba. Bayan ya gama shinshinar ta ne da rungumeta ya ɗakkota cak zuwa wannan ɗakin yana faɗin, “Yanzu dai muje muyi sallah kafin komai ko. Dan nasan matar tawa ustaziya ce”.
A karo na farko ta sakar masa murmushi, tare da tura kanta a jikinsa dan kunya takeji matuƙa kamar me. Dan tunda take a rayuwarta bata jin wani ya taɓa riƙe mata hannu, sai a jiya wajen dinner da JJ ya aikata hakan gareta. To ita dai tasan sun shigo ɗaki, daga haka kuma bata san miya faruba sai ƙarar ihun nan da bata san daga ina ya fito ba da ya farkar da ita, a yanda kuma taga kanta alamu sun nuna barci tayi. Gadon ta sakko da sauri, sai kuma tai tsamm ta dakata saboda jin motsin ruwa a toilet ɗin ɗakin, hakan na nufin JJ na ciki kenan. Numfashi ta ɗan sauke a hankali, tare da komawa ta zauna tana gyara mayafinta, zuciyarta na tabbatar mata wanka ya shiga kenan, ita kuma barci ya ɗauke ta, ihun da taji kuma maybe a maƙwafta ne. To amma abin mamakin anan taya tayi barcin? Haka cikin ƙanƙanin lokaci? Rashin amsa ya sakata ɗan sauke numfashi kawai.. dai-dai nan JJ ya fito a toilet ɗin babu alamar wanka yayi sai dai ko alwala. Kanta ta duƙar ganin ita yake kallo, shi kuma ya saki murmushin da har ta iya jiyo sautinsa da ga inda take tare da faɗin, “Naga a takure kike, jeki falo ki jirani”.
Kamar mai jiran jin hakan ta mike zumbur, har harɗewa take wajen fita tana mai sauke ajiyar zuciya, sai dai mamaki fal kanta dan sai take jin kamar wani banbarakwai hakan nan….

(Bake kaɗai ba amarya, ni kaina fa man kai na ya tsiyaye. Dan na gagara fahimtar komai, shin JJ ɗin ne ba mutum ba ko ke kanki? Masu karatu ko akwai mai amsa min?🥱😆🚴).

★★…..

A ɓangaren JJ ango kam zubur ya miƙa tare da sauke nannauyan numfashi alamar farfaɗowa da ga sumar da ya tafi. Gaba ɗaya jikinsa babu wani ƙarfi a yanzu, dan tun bayan numfashin da ya kawo cikin zabura sai kuma ya koma laƙwas kwance yana maida idanunsa a hankali ya sake lumshewa. Falaƙi da Naasi ya fara karantawa a zuciyarsa yana ɗan buɗe ido kaɗan, shiru babu motsin komai, sai wata iska mai daɗi dake ƙaɗawa. Kamar wanda aka bama ƙarfi ya miƙe zaune dingangan, waige-waige ya shigayi idanunsa a buɗe sosai mamaki fal kansa na ganinsa a baranda kwance wanwar, tabbas a waje yake, ya kuma kasa iya tuna komai da ya faru. Babu alamar akwai wani abu da zuciyarsa ke ayyana masa kuma, sai ma wata nutsuwa da yake ji ga zuciyarsa na tabbatar masa faɗuwa yay kenan bayan yama abokansa rakkiya, dan abinda ya fara tunawa kenan kafin gittawar da akai masa lokacin da yake ɗaura hannunsa saman handle ɗin ƙofa, sai kuma abinda ya faru na shigarsa falo dama ɗaki, hakan na nufin komai daya faru a mafarki ne ba zahiri ba dai kenan. A take ya gamsu da hakan, dan kamar an masa wanki ƙwaƙwalwa ne ma ya kasa tuna komai a yanda ya kamata balle yayi tunani irin na mutane masu hankali. Sai ma amaryarsa da ta zo masa a zuciya. Miƙewa yay tamkar wanda aka tsikara, ya gyara zaman babbar rigarsa da hula sannan ya ɗaura hannunsa a handle ɗin ƙofar ya murza a hankali yana sakin wani murmushin farin ciki.
A inda ya barta nan ya sameta, tana lulluɓe dai har yanzu cikin mayafinta. Sai ƙamshinta daya gama gauraye falon mai shegen daɗi. Taku ya cigaba dayi cikin shauƙi da bajinta zuwa gareta. Kusa da ita daf ya tsaya batare daya zauna ba ya zuba mata shu’uman idanunsa da suka sake ƙanƙancewa. Tsahon mintuna biyu kafin ya kai durƙushe ƙasa tamkar ɗa a gaban uwarsa. Hannu biyu ya saka ya ɗaga mayafinta ƙyaƙyƙyawar fuskarta mai alamun rashin yawan hayaniya ta bayyana. Ga kwarjini irin wanda aka san amarya da shi tattare da ita. A hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da kamo hannayenta da take matsewa cikin juna ya riƙe, sun sha jan lalle da baƙi sai sheƙi suke. Ɗagosu yay zuwa bakinsa ya sumbata tsakkiyarsu ɗaya bayan ɗaya. Sosai ta sake ƙanƙame jikinta da sinne kanta na kunya…
“Babu gaisuwa Love?”.
Ya faɗa cikin wata irin siririyar murya. Kanta ta sake sinnewa cikin tata muryar da ke rawa ta ce, “Kayi haƙuri ina yini”.
“Ai baƙya laifi amarya koda kin kashe JJ ne ma. Dama wannan golden voice ɗin nake son ji ne. Ina miki Barka da zuwa gidanki, fadarki. Alƙawarin ALLAH ya cika yau gani ga Love ɗina a gida ɗaya matsayin ma’aurata. Babu abinda zance da UBANGIJI sai godiya. Kisa a ranki har abada bake ba kishiya, ko’a aljanna ke kaɗai ce”.
Murmushi ta saki a karo na farko, sai dai bawai ta amshi kalaman nashi bane da muhimmancin riƙewa, dan duk da ƙananun shekarunta kuma ita bamai yawan hayaniya bace da taron ƙawaye tanada iliminta. Tasha jin yayunsu na faɗin yarda da irin waɗan nan kalaman a bakin namiji yaudarar kaine kawai..
Shiko tuni murmushin nata ya kashesa, dan a tunaninsa kalamansa sunyi irin tasirin da yake buƙata. Tashi yay daga ƙasan da yake ya koma saman kujera kusa da ita, gaba ɗayanta ya jawo ta koma saman cinyarsa ya rungumeta tsam-tsam yana sauke numfashi da sauri-sauri. Dan maganin da MB ya basa ya fara aiki. Itako gaba ɗaya ta gama rikicewa da kunya da tsoro, sai dai batai yunƙurin jaye jikinta ba kamar ɗazun. Tsahon mintuna uku suna a haka kafin ya ɗago fuskarta, kallonta yake tamkar a yau ya fara ganinta, anan ɗin ma dai yaja wasu mintuna biyun cur sannan ya miƙe ɗauke da ita yana faɗin, “Muje muyi sallar godiya ga ALLAH sannan kici abinci da ga nan sai ki…..” ya ƙarasa faɗa mata cikin kunne yana sakin wata siririyar shaƙiyyar dariya. Itako jitai gaba ɗaya ta rikice, gashi yana ɗauke da ita, sai kawai ta sake cusa kanta cikin jikinsa har suka iso ɗakin bata yarda ta ɗago ba. Ba ɗakin da ya kaita bane ɗazun, ta fahimci hakanne lokacin da yake sauketa a kofar toilet ɗin yana faɗin, “Je kiyo alwala bara na rage rigar nan tamun nauyi. Kanta a ƙasa ta amsa da to, ya bita da kallo har sai da ta shige sannan ya juyo yana murmushi da ƙoƙarin cire babbar rigar tasa. Cikin sauri ya ƙarasa janye rigar daga fuskarsa ƙirjinsa na wani irin harbawa. Sai kuma ya waiga da sauri ya kalli ƙofar toilet ɗin, sake waigowa yay ya kuma kalli gadon. Amaryar tasa dai ce data shiga toilet akan idanunsa yanzu zaune a tsakkiyar gado kuma tana murmushi. (Kodai ƙwaya MB ya bani ne) ya faɗa a zuciya jikinsa na rawa, da sauri ya juya baya zuwa ƙofar toilet ɗin. Buɗewa yay ya leƙa. Alimah amarya dake ƙoƙarin fara alwala ta ɗago da sauri.
“Sorry” ya faɗa bakinsa na rawa tare da ja mata ƙofar ya rufe yana juyowa. Yanzun kam gadon wayam babu kowa, yana nan tsaff da shi a gyare tamkar yanda suka shigo suka samesa.. Sautin kuka ne ya fara ratsa ɗakin a hankali har ana shashsheka, da sauri ya buɗe idanunsa daya lumshe na jin relief da farko ya fara waige-waige. Jin zai faɗi ya sashi kaiwa zaune bakin gado, a bisa tsautsayi bai zauna da kyau ba ya zame kasan carpet wanwar. Sai kuma ya miƙe zaune dingangan zuciyarsa na wani irin gudu a cikin ƙirjinsa. Ƙaruwa sautin kukan yake, sai dai babu kowa a ɗakin sai shi kaɗai ɗin dai Alimah bata fito ba. Cikin tsumar jiki ya dafe hannayensa duka biyu ƙasa da nufin jan jikinsa koda da rarrafe ya kai ga toilet yaji ya camɓalasu cikin laima mai kauri da ɗumi, da sauri ya ɗago duka hannayen, yay bala’in waro idanunsa waje tare da maida kallonsa ga ƙasan. Tabbas jini ne malale a duka ɗakin tamkar yanda tiles yake, ga sautin kukan nan na ƙaruwa. A karo na farko JJ ya fashe da kuka kawai idonsa a hanyar toilet komai daya faru ɗazun na dawo masa a zahiri. “Na shiga uku ni Jazool. Mike faruwa dani?…” ya sake ɓarkewa da kuka…..
Dariya ce ta karaɗe ɗakin a maimakon kukan da ake rairawa da farko. Kamar kaɗawar iska a cikin kunnensa aka gwargwaɗa masa, “Oh oh mazan fama kuma da kuka haka. Karka bada maza mana JJ ango” sai kuma aka ƙyalƙyale da dariya mai cika kunnuwa data sake rikita JJ. Kamar ƙyaftawar ido aka kuma ɗaga shi cak aka sauke saman lafiyayyen gadon ɗakin da yasha shimfiɗar alfarma. Yana ƙoƙarin zabura ya miƙe aka rungumeshi..
“Uhhm my D ina kuma zaka? Kasan fa wannan daren na musamman ne a garemu”. Aka faɗa masa a cikin kunne ana kaima wuyarsa sumbata. Bashi da zaɓin da ya wuce wage baki ya ɓarka ihu kawai ko zai samu agajin wannan tashin hankali da ga maƙwafta, sai dai me yana wage bakin caraf aka cafke harshensa cikin wani salo aka hau sumbata tare da sake ƙanƙamesa tamau. Duk yanda JJ yaso yin wani yunƙuri ya kasa hakan, yana ji yana gani aka suleshi zigidir. Kafin a sakar masa baki tare da jirkicesa ya koma ƙasa akai masa rumfa. Fuskar amaryarsa ce ta bayyana a idanunsa, ta sakar masa lallausan murmushi da kashe mar ido ɗaya cike da salon so da ƙauna…
“My D! Ya kake abu kamar wani matsoraci. Karfa ka manta wannan shine dare mafi girma a wajenmu. Daren da kake ta faman zumuɗin zuwansa da lissafinsa.” ta ƙare maganar cikin wata iriyar shagwaɓaɓɓiyar murya tana shafo fuskarsa.
Jujjuya kansa kawai yake hawaye na gangaro masa. Magana yake son yi amma da alama sautinta ya gagara fitowa, sai lips ɗinsa ke wata irin rawa ga hawaye ga majina ga zufa sun masa sharkaf a ƙyaƙyƙyawar fuskarsa ma’abociyar shan gyara iri daban-daban. Sumbata ta sake kaima lips ɗinsa tana dariya, sai kuma ta ɗagashi zaune itama tana zaman harda tamkwashe ƙafa suna fuskantar juna. Ita dai sanye take cikin tufafinta harda mayafi, shiko an masa zigidir sai faman kare jikinsa yake da hannu. Dariya ta sake kwashewa da shi tana kallon yanda yake mammatse jiki. Cikin dariyar take faɗin, “Haba angona minene kuma na ɓoye jiki bayan so nake na kalleka da ƙyau yau ɗin nan. Karfa ka manta ka zama Alimah, Alimah kuma ta zama kai. Jiya aka ɗaura mana aure, yau aka kawoni gidanka. Miya rage kuma garemu banda baje kolin soyayya D?. Koka manta kana tare da Love ɗinka ce, ƴar shilar yarinyar nan mai shekaru goma sha bakwai kacal. Mai tarbiyya da ilimin addini. Kamila ga kunya kullum tana a cikin hijjab. Ƴar malamai da bata san komai ba sai zuwa islamiyya da aikin gida. Haba My JJ”. Ta ƙare faɗa da salon shagwaɓa a yanzun ma har tana turza ƙafafu a gadon. Sake ɓarkewa da kuka JJ yayi lokacin da idanunsa suka sauka akan ƙafafun nata. Dan amaimakon ƙafa shikam kofatai ya gani irin na shanu da dokuna. Ganin ƙafar yake kallo yana kuka itama ta kalli ƙafar, sai ta ɓarke da dariya harda kwanciya kafin ta tashi zaune da ƙyau tana haɗe fuska tamkar ba itace ta gama dariyar ba. Haɓarsa ta kamo tare da matso da fuskarsa gab da tata ta sumbaci lips ɗinsa, sai kuma ta zuro wani irin dogon harshe kamar ana fitowa da abu a rami ta fara lashe shi. Luuuu kawai yayi ya sake sumewa……..✍️

 

_😂😂😂 Gaskiya JJ kana bada maza a wannan al’amari . JJ na buƙatar addu’a fa🚴🚴🚴🚴😆🥱_

*_ALLAH ka gafarta ma iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*

 

 

 

*_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

 

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

 

_Shafi na uku_

 

……..Da murnarsa ya shigo gidan yana faman washe baki. Tun a farkon tura ƙofar soron gidan yake ƙwala kiran sunanta tamkar mai shela. “My Queen! My Queen! Kina ina ne? Wai nikam. Fito! Fito ki gani fito My Queen!!”.
Har cin tuntuɓe take wajen saurin fitowa da ga bayin, tsabar yanda ta fito a rikice saboda kiran da yake faman ƙwala mata bama tasan da botikin wankansu da akoda yaushe yake a bayin ajiye ba ta fito. A ƙaramin tsakar gidan da bai wuce cin tabarma biyu ba sukaci karo. Kafin ma tace wani abu yayi wani kalar jawota ya rungume tare da ɗagata cike da farin ciki ya shiga juyi da ita. Ɗan ihu ta fara mara sauti tare da roƙon ya sauketa tana faman ɓoye fuskarta cikin jikinsa. Shiko duk da yasan bata son hajijiya sam bai sauketan ba, sai faman dariya ma yake abinsa yana cigaba da juyinsa. Sai da yay mai isarsa sannan ya afka ƙofar dake kusa da su, falone matsakaici dan kujerun da aka ƙawatasu da shi ma a mugun matse suke. Tsakar falon kuwa bai wuce girman sallaya ba, direta yay a saman doguwar kujerar yana hakki. Itako ta sake ƙanƙamesa har yanzu fuskarta na jikinsa. Sai da kusan mintuna biyu suka shuɗe taji hajijiyar ya saketa kafin ta ɗago kaɗan tana tura baki da kwaɓe fuskan tamkar zatai kuka.. a shagwaɓe ta ce, “Haba Husby so kake kaga bayana ne?”.
Dariya ya ƙyalƙyale da shi, cike da nishaɗi ya furta, “Ai mai ganin bayanki sai kin juya My Queen. Wlhy wani farin ciki ne na shigo da shi wanda na tabbatar idan kika jishi yau ƙyautata sai ta kasance ta musamman ne”.
“Woow Mijina bani nasha mana”.
“Ai dole kisha kuwa Matata, sarauniya ta, dan haka rufe idanunki”.
Ruf ta sufesu murmushi na sake ƙawata kansa a black beauty fuskarta mai wani irin sirrin laushi da sheƙi. Ga ɗan ƙaramin bakinta da yafi komai ƙawata sirrintaccen ƙyawun nata. Hannunta na dama ya kamo cikin nasa, yana cigaba da murmushin ya ciro abu a aljihunsa ya saka cikin hannun nata ya rumtse yana faɗin “Zaki iya buɗewa”. Buɗewar tai da sauri tare da ware tafin hannunta, ta ɗan zubama keys ɗin idanu zuciyarta na wani irin rawa-rawa. Sai kuma ta ɗago da sauri tana kallonsa da girgiza kanta. “Husby ka ɓaddani ALLAH. Keys ɗin miye haka?”.
Ido ɗaya ya kashe mata tare da jawota jikinsa ya rungumeta har zanin dake ɗaure a jikinta na kwancewa. Basu damu da hakanba su duka, suka ƙanƙame juna. A cikin kunnenta ya gwargwaɗa mata maganar da ta sakata ɗagowa da sauri tana kallonsa idanunta gaba ɗaya a waje. Cikin rawar lips idanunta na ƙiƙƙiftawa ta furta, “Naka fa Dafeeq?! Taya hakan zata kasance bayan nasan ko key na keke bamu da hanyar samunsa a gidan nan balle mota har ma da gida”.
“Ikon ALLAH kenan Deejoh na.”
A hankali ta ce, “Hakane. Sai dai komai ai yana da sila. Tayaya hakan ta kasance?.”
“Karki damu zan sanar dake komai. Amma fara mun haƙuri naɗan watsa ruwa ki bani abinci kuma naci. Dan yunwa nake ji ALLAH sosai. Banci komai a cikin nan nawa ba tun karin da mukai da safe”.
Duk da zumuɗin son jin da take haka ta daure ta danne. Cikin ƙarfafa kanta da ture abinda ke tsikarin zuciyarta ta miƙe tana murmushi. Fita tai a falon, babu jimawa ta dawo. Kusan a tare suka ɗaga labule, dan haka ta ɗan jaye baya ta bashi hanya. Fita yay yana sakar mata murmushi, ta maida masa murtani cike da son ƙarfafa kanta. Numfashi mai nauyi ta sauke lokacin da take sake kaiwa zaune a kujera idanunta akan keys ɗin nan dai. Ta kafesu da ido zuciyarta na ci gaba da kai-kawo. Haka kawai take ɗan jin kamar tsoro a ranta, sai dai bata san dalilin hakan ba, domin a zahirance ba tsoron ya kamata ace tana ji ba, murna ya kamata ace tafi kowa da wannan alkairin da ya samesu. Badan komai ba sai dan tuna baya, tuna baya akan rayuwarta da Dafeeq kafin aure, tuna baya kafin zamowarsu ƙarƙashin aure. Tuna baya bayan zamowar tasu ma’aurata har zuwa yau ɗin nan da suka wayi gari a matsayin da suke kafin wanda ke neman canjasu a yanzun nan…
Sunanta shine Khadijah, ɗiya ta farko a wajen iyayenta. Tana da ƙanne huɗu duk mata, sai namiji ɗaya daya kasance autansu. Mahaifinsu ba mai kuɗi bane, sai dai mai ƙarfin hali ne da wadatar zuci. Wannan imanin nasa ya sakasu tashi a gidansu matsayin ƴan gata, bama gidansu kawai ba har a cikin dangi da yaran anguwa sun kere tsara. Dan komai mahaifinsu tsaye yake wajen musu dai-dai ƙarfinsa. Hakama mahaifiyarsu tana nata ƙoƙarin da sana’arta ta saida kayan sanyi da kayan miya irinsu kuka, kuɓewa, magi, gishiri, daddawa. Kai duk dai wani nauyin kayan miya na gargajiya zaka samesa a wajen mahaifiyarsu. Dan haka gidansu ya kasace ɗaya daga cikin gidaje da ake zirga-zirga na sayayya. Ƙoƙarinta da ƙwazo a makaranta ya sakama mahaifinsu burin ganin tayi karatu mai zurfi ita da ƙannenta, amma kasancewar itace babba sai ya zam ita aka fara ƙoƙarin ginawa. Lafiya lau ta kammala primary ta shiga secondary ɗin dake ƙasan layinsu ta ƴammata, sai dai makarantar iyakarta jenior ce. Wato iya aji uku. Matuƙar ƙwazo da himma ta bada a karatunta, inda ta kasance ɗaliba mai ɗaukar first class a ajinsu tun daga jss 1 har zuwa jss 3. Sun zana jsce cikin nasara da jin kewar rabuwa da makaranta, musamman ita data kasance mai farin jinin malamai saboda ƙwazonta. Dan randa akai musu walimar fita ta samu ƙyaututtuka daban-daban da suka saka iyayyenta farin ciki tare da sake jin ƙaimi akan tsaya mata cigaba da karatu. Sun ɗanyi zaman gida har jarabawa ta fito, inda ta samu nasarar samun wata makaranta dake can wata anguwa, sai dai ita haɗe take ƴammata da samari. Makarantar babbar makarantace dan duk ɗalibin daya kasance a cikinta sai mai ƙwazon gaske. Saboda akan tsinto yara ne masu ƙwazo sosai daga makarantu daban-daban zuwa nan a duk shekara, itama ƙwazonta ya bata wannan damar. Tayi farin ciki matuƙa da zamowarta ɗalibar wannan makaranta mai farin jini da kowa ke fatan ganin ya sameta, hakama iyayyenta sunyi murna mara misali. Anan ɗin ma lissafin bai canja ba, dan ta matuƙar dagewa a tarm ɗin farko itace ta ɗauki ta ɗaya a ajinsu, ta kuma sami ƙyautar yarinya mai tsafta da kuma rashin yin latti. Iyayenta sunyi matuƙar farin ciki tare da ƙara ƙarfafata, dan har ƙyauta baba ya mata ma, hakama Inna ta siya mata kaza guda ta soya mata tace taita ci har ƙannenta na kukan an nuna musu wariya. Ta gama ss1 lafiya, a tarm ɗin da suka shiga ss2 komai ya fara, dan shine farkon labarinta tsakaninta da _Dafeeq Abubakar Ja’e_…….

★★★★

A hankali yake buɗe idanunsa da sukai wani masifar nauyi. Da sauri ya ɗan rumtsesu ya sake buɗewa again. Sai dai yanzun ma dai a hankali yake motsasu. Fankar dake juyawa kaɗan-kaɗan ya zuba ma su na tsawon sakanni goma. Tun yana kallonta dishi-dishi har idanun nasa suka fara gani tar-tar. Tabbas ba gidansa bane, dan anan ɗin normal selling ne saɓanin gidansa da akaima sabon lafiyayyen p.o.p da yasha fitulu. Sake ware idanun yay da ƙyau tare da motsa jikinsa, jin hannunsa na dama yay masa nauyi sosai ga zafin daya ratsashi saboda fisgar da yay masa ya sashi ambaton “Wash ALLAH na”.
A karo na farko duk wanda ke ɗakin suka juyo garesa, sai kuma duk suka zabura kowa na ambaton sunansa. Idanunsa ya sake buɗewa da ƙyau yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya. Mahaifinsu ne, sai yayunsa biyu da abokinsa MB da SJ, sai ƙaninsa guɗa ɗaya. Jin yanda suka rufesa da tambaya da sannu ya sashi motsa bakinsa da yay nauyi a hankali ya furta, “Abba ina ne nan ɗin?”.
“Asibiti ne Jazool, an kawoka ne baka da lafiya tun jiya”.
Yayansa ya bashi amsa cike da nuna alhini da tausayawa. Da ɗan sauri JJ ya dubi hannunsa, ganin ruwa ake ƙara masa ya sashi yarda da zancen yayan nasa. Ƙoƙarin tashi yake zaune sai dai ya kasa, cikin sauri MB da yayansa na biyu suka kamashi. Zaunen suka tadashi, tare da jinginasa jikin bango da Nuhu ya gyara filo suna cigaba da masa sannu. Kai kawai yake iya gyaɗa musu shi dai, ransa fal mamakin miya kawosa asibiti shi kam.. Idanunsa ya rufe ruf, tamkar wanda ake sarrafawa da remote sai kuma ya buɗe da sauri jin abinda MB ke faɗa…
“Sannu kaji abokina, gaba ɗaya ka ɗaga mana hankali, amarya da ya kamata ace ita ke jiyya sai kuma kai a naku labarin amarcin ya juye kaine kwance a gadon asibiti? Ni dai ALLAH yasa ba pills ɗin dana baka bane ya jawo maka wannan bala’in tun jiya ake abu ɗaya kamar bazaka rayu ba”.
Rawa jikin JJ ya farayi, ya ɗan juya ya dubi sashen da Abba da Yayunsa suke, can ya hangosu a bakin ƙofa alamar magana sukeyi, sake maido idanunsa yay kan MB da SJ dake tare da shi kawai. Muryarsa na ɗan rawa ya ce, “Yaushe aka kawoni nan? Waye kuma ya kawoni?”.
SJ ne ya bashi amsa yanzun kam da “Tun jiya da safe aka kawoka. Amaryarka ce kuma tai kiran Rabi’ah tana kukan cewar azo a taimaketa ka mutu kamar yanda Nuhu ya sanar mana. Hankali tashe su Yaya Mujee suka nufi gidanka. Inda aka taddaka yashe a ƙasa baka numfashi kuma duk an jimaka ciwo a fuska da jikinka kamar da farauta, itama amaryarka jikinta duk jinin da yake biyo mata ta hanci da gefen baki alamar dukanta akai…”
Da wani irin gudu abinda ya faru tun daga barinsu gidan zuwa komawarsa ciki ya shiga dawo masa. A take jikinsa ya fara kakkarwa. Muryarsa dake a disashe na rawa ya ce, “Duka? Ita Alimah ɗin?”.
“Ƙwarai da gaske, dan tare ma aka kawoku asibitin nan, sai dai ita tun jiyan aka sallameta bayan Doctor ya dubata sosai, ya kuma tabbatar da marinta akai bakinta da ya fashe, jinin hancin kuma haɓo ne tayi. Kaiko an yayyageka da farauta ne aka jijji maka ciwukan nan. Dalilin sumanka ne dai har yanzu basu ce komai akansa ba, dan jiyan ma da ƙyar aka samu ka farfaɗo kusan sha biyun dare, shine sukai maka allurar barci sai yanzu ne kuma kake farkawa”.
Cikin rawar lips mamakin zantukan MB ras akan fuskarsa ya buɗe baki zaiyi magana, sai dai shigowar likita tare da Abbansa da yayunsa ya hanashi cewa komai. Duk fita likita yace suyi, yayinda shi kuma ya shiga duddubashi yana jera masa tambayoyi akan yanda yake ji a yanzu. Da ƙyar ya iya bama likitan amsa da cewar shi yanzu baijin komai, sai kansa da yay masa nauyi da kuma mararsa.
“Insha ALLAH suma zasu sakeka. Ciwon kan normal ne na daɗewa da kai a sume. Na maran ne dai ƴar damuwa itama kuma bamai tada hankali ba. Da ka samu kasancewa da matarka zaka koma normal. Pills daka sha ne suka haifar maka da hakan. Amma sai ka kiyaye gaba dan bincikenmu ya tabbatar mana daka jima kana amfani da irinsu, hasalima ƙarfin maganin da rashin sauke nauyin da suka saukar maka ne ya haddasa maka sumar nan kayi kuma nauyin farfaɗowa. Ka godema ALLAH ma kuma da baka samu haikema yarinya a wannan yanayin ba tunda naji ance amarya gareka, dan ƙarfin maganin nan zai iya sawa ka mata babbar illa musamman idan ta kasance virgin. Dan ALLAH ku dinga bincike akan abu kafin kuyisa, dan hakan wautace sosai. Musamman idan mukai dubayya da su yaran da ake kai muku basu san komai ba, binsu a hankali akafi buƙatar kuyi tunda al’amarin ba damben gwada ƙwanji bane ba. Kaga gashi nan wajen ceton kanta ta jijji maka ciwo itama ka jimata ciwon ta hanyar marinta da kayi. Hakan ai kaga baida amfani sam a daren farko fa kuma….” Likitan ya ƙarasa maganar cikin zafi-zafi. Shi dai JJ kallonsa kawai yake kansa a wani irin juye. Dan gaba ɗaya yama gagara auna maganar doctor ɗin a muzubin hankali kona fahimta. Shi harma a yaushe yay yunƙurin yin wani abu da Alimah. Ya san dai yasha pills kam tabbas, yana kuma cike da ɗokin yin shagalinsa, amma bai ko ɗau hanyaba. Kai shi bama wannan ba fa, abinda ya faru tsakaninsa da Alimah ɗinne abu mafi girman ɗaga hankali da buƙatar yin tunani, sai kuma yanda yaji labarin na neman canja kansa zuwa wani bigire daban a bakin wannan likitan. Ɗan zabura yay zai sauka a gadon har yana buge likitan. Da mamaki ya ɗago da ga rubutun da yake ya dubesa, ganin yana neman direwa a gadon yay saurin riƙesa da faɗin, “Ya ALLAHU! Lafiya kuwa?”.
“Babu ita Doctor, Alimah nake son gani”.
A halin da JJ ke ciki da yanda Doctor ya fahimci al’amarin akwai banbanci, dan haka yay murmushi yana ɗan laɓe bakinsa. “To baban soyayya kwantar min da hankalinka nan Please. Indai amaryace yanzu zaka ganta har nan inda kake duk da ma dai zamu sallameka ne muma kaje gareta a yau ɗin nan in sha ALLAHU kaji”.
“Doctor plea….”
“Shiii!!!” doctor yay saurin katsesa. Daga haka ya juya yana fuskantar ƙofar da faɗin, “Zaku iya shigowa”………✍️

Leave a Comment