Books Reviews & FAQs

Bayan Wuya Hausa Novel Complete

BAYAN WUYA…..

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*BY*
RUMANAH M. DIGGI
(Star writer’s)

*GODIYA*_ Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga buwayi gagara misali, Sarkin sarakuna, shugaban shugabanni, ubangiji makaidaici mai Kowa mai komai. Tsira da Aminci su tabbata ga shugaba ja gaba dan gata annabi Muhammad (s.a.w) da ahalinsa da sahabbansa da dabi’ahn sa baki Daya.

*GODIYA TA MUSAMMAN GA FARIN WATA ASSOCIATION WRITER’S ALLAH YA ƘARA BASIRA MUTANE NA INA ALFAHARI DAKU AKODA YAUSHE*

*SADAUKARWA* na sa daukar da wannan littafin gabadayan sa ga tashar EL_NAJEEB PRODUCTION YOUTUBE CHANNEL. Allah ka karamusu daukaka da nasara Ameen thumma Ameen

*Godiya* godiya ta musamman ga abokanan arziki da ‘yan uwana na gari bazan taba mantawa dakuba koda ina bakin kura

*Bismillahirrahmanirraheem*
BAYAN WUYA….

🅿️ – 1️⃣ to 2️⃣

*****AJAH ROAD*****
*LAGOS NIGERIA*

Duniya darasi!!! Hakika duniya darasi ce ga Wanda zai tsaya ya fahimta, rayuwa juyi-juyi ce a yayinda tamu rayuwar tayi mana juyin kwado daga ruwan sanyi zuwa ruwan zafi, hakika kaddara abace mara tabbas, kaddara kamar zanen dutse ce da babu wanda ya isa ya goge shi, yayinda tamu kaddarar take zane kamar kan taswira muna binta ɗaya bayan ɗaya.

Shekaru biyu da suka shuɗe rayuwa mukeyi mai cike da ƴanci da so da ƙaunar juna irin wacce iyalai keyi a tsakanin su. Mu biyu ne awajen iyayen mu Nida ƙanwata haka Kuma mahaifiyarmu itakataice wajen mahaifinmu ma’ana ita kadaice matarsa. Mahaifinmu ba talaka bane Haka kuma baza’a Kira shi da mai ƙudi ba sabida ko gidan da muke zaune ba gidan mu bane gidan hayane.

Mahaifinmu ABBIE HAMRAZ AWAIS yanada karamin shago Wanda yake hade da gidan namu, ya Zuba kayansa na trader a cikin shagon waɗanda baza’a rasaba kamar dai Kayan Miya irinsu magi, mai, bushashen danƙwa, da sauransu Haka Kuma ana siyarda shinkafa, spaghetti, indomie, da Toka, clean, slippers, dadai sauran kayayyakin amfani. Alhamdulillah mahaifinmu yana samun ciniki sosai sabida kayansa sunada arha ba Kamar na sauran ‘yan unguwar ba.

Haka ma mahaifiyar mu AMMIE FAHEEMA itama ba’a barta a baya ba domin tanayin ƴan Sana’oin ta cikin gida domin a rufawa juna asiri. Kanwata Aleena shekarunta goma ne zuwa sama sabida a wannan shekarar ce zata kammala karatunta na primary, yayinda nikuma nakeda shekaru goma sha biyu kuma ina jss one a wannan lokaci duk muna tare cikin rufin asiri, mahaifanmu na matukar nuna ƙauna agaremu ko kaɗan basason abunda zai damemu domin duk abunda muka nema muna samu a wajen su idan dai baifi karfisuba.

Yara biyu ne suka shigo gidan, bakunan su dauke da sallama, jikinsu sanya da uniform din islamiyya. Karamar ce naga ta rugo aguje kan Wata mata Dake zaune tana gyara shinkafa wacce da alamu ana shirin dafawa ne, “amminmu sannu da gida” yarinyar ta fada tare da ɗalewa kan matar “haba budurwa so kike yi karyani” ahhh amminmu idan na karyaki na hau ƙafarwa toh? Tana Shirin bata amsa ne sai ɗayar yarinyar tashigo tare da fadin Ammi inawuni ya aiki “lafiya kalau leeya andawo lafiya, da fatar dai anyi karatu kho” matar ta faɗa tana kallon yarinyar da najie ankira da LEEYA.

Ehhh Amminmu nayi karatu ta fadi tana nufar tilon dakin su Dake can gefen gidan, bayan tashiga ta cire hijab dinta ta Kuma ajiye Jakarta Sannan ta fito waje ta dawo inda matar take sannan ta karbi tirenda shinkafa ke ciki tare da fadin Ammi bari natayi, wallahi ammi yau nagaji sosai fa nayi tunanin ma an kare abincin, to gara sarkin ci ba’a kareba Yarinyar da ke kan ƙafar matar nan ta fada tare da yiwa LEEYA gwalo, dago hannu leeya tayi da niyyar ta rankwashi yarinyar sai matar ta rike mata hannu “kullll karki yarda ki dakammin yar budurwata wallahi” Turo baki leeya tayi sannan tace ammi kibari kawai nayi mata rankwashi ko zan cire haushinta, ta faɗa tana yamutse fuska duk da ba ganin fuskar tata nakeyi ba domin tana lullluɓe ne a cikin mayafi.

Subhanallah!! leeya haushin me kikeji nata kuma me tayi miki har da zakiji haushinta, sabida ta kiraki da gara ae gaskiya ta fadi matar ta fada tana shirin miƙewa zata tashi daga inda take zaune.

Ammi wai kinsan yau kasa muka dawo daga IFE kuwa? Komawa tayi zaune daga niyyar tashinda takeyi sannan tace kasa kuma leeya meya hanaku shigowa taxi yau, matar ta fada cike da mamaki a fuskar ta. wallahi ammi aleena ce ta kashe mana kudin taxi bayan kuma ta kashe wadanda Abbie yabata, kinsan ba class dinmu dayaba Saida aka tashemu sannan take gayamin wai kar ma na tara taxi domin ita ta kashe kudin taxi din, ammi haka muka dawo gida kasa.

Aleena da tunda aka fara magana hannunta ke dafe da gaba “tace Wallahi amminmu wasa nake ban kashe kudin ba nayi hakane kawai sabida mu koyi tafiya a kasa, mukoyi maintaining, Kinga yanzu ni budurwa ce, idan Bana tafiya a kasa Ina miji zai ganni balle nayi aure, ko so kike in wuce lokacin aure kamar yanda yahyah leeya ta wuce? Ta fadi maganar cike da yarinta tana ware hannayenta alamar tambaya, a yarinta irin na Aleena duk wacce ta kammala primary to itace budurwa kuma idan bata aure a wannan lokacin ba har wasu suka ƙare primary to waɗan can sun tsufa kenan, sun wuce lokacin aure, to ita yanzu take shirin zama budurwar, shiyasa kowa a gidan yake kiranta da sunan.

idan kuma baka kiranta da sunan budurwa to bakaibane wanda kuke shiri da ita ba. Dariya suka kwashe gaba dayansu sai yanzu na kula da Wani dattijo Dayake shigowa, dattijon ba baki bane, Kuma Kai tsaye bazaka kirashi da fariba, yanada dan tsayi, Haka kuma yanada matsakaicin jiki, a ƙiyasi zai iya kai shekaru 43 zuwa sama HAMRAZ AWAIS kenan datijjo mai kamala da haiba.

Tun sa’adda Aleena ta fara magana yana jinsu Shima maganartata ce ta bashi dariya. “Salamu alaikum” wa’alaikassalam duk suka amsa masa tare, leeya ce ta fara gaida shi sannan sai Aleena. ummu-aleena barka da gida “yawwa barka dai Abu-leeya ya shago? “shago alhamdulillah mungode Allah, Dubana na Kaiga wacce aka kira da ummu-aleena matar nan ce dake zaune tana gyara shinkafa, na ganta macece guntuwa mai faffadan jiki, duk da kasancewarta guntuwa a kallo daya bazaka kirata da guntuwa ba haka zalika ba doguwa bace, gata fara sol zubin fulanin maiduguri wato kanuri AMMIE FAHEEMA Kenan. Ke budurwa kike ko wa, ki tashimin a kafar mata karki karya min ita.

Abbie yau kasaka kudi a asusuna kuwa? Ina batun matata kina min batun asusu Aleena. Abbie nifa bazan tashi ba sai ka gayamin amsar tambayata. “to ban sakaba Amma kizo muje yanzu na baki ki saka da kanki, zabura tayi da gudu ta isa gun Abbie ta miƙa masa hannu alamar yabata, sunkuyo da kansa yayi ya raɗa mata Magana a kunne, sai ta jijjiga Kai alamar ta gamsu sannan tace to Abbie nagane.
Duk abin nan da suke da mamaki ammi da leeya ke kallonsu, leeya dai ta ƙasa hakura saida tazo tace Abbie wai asusu akeyiwa Aleena ita kadai ba daniba ta faɗi maganar kamar zatayi kuka.

har Abbie ya buɗe baki Zaiyi Magana Aleena ta karɓe da cewa “ehhh asusu yakeyimin ya ranki daɗi ko bakin ciki, nace daɗi ko bakin ciki, to koma dai menene Abbie asusu yakemin kuma kayan aure za’a siyamin tunda ke kinƙi yin aure Ni bazan zauna ina haɗa kafaɗa dake ba, Muna gwadin tsawo a gidan nan ehee Aleena ta faɗa tana rike kunkuru tana juya idanu kamar itace yayar ba ƙanwa ba. Leeya da taji dalilin yin yasa akeyin asusun ta juya tabar wajen.

𝙇𝙀𝙀𝙔𝘼𝙉𝘼 itace yaya a wurin 𝘼𝙇𝙀𝙀𝙉𝘼 ƴaƴan Abbie 𝙃𝘼𝙈𝙍𝘼𝙕 da Ammi 𝙁𝘼𝙃𝙀𝙀𝙈𝘼 basu kadai bane ƴaƴan amma sune araye, idan da za’a lissafa leeyana ita ƴa ta huɗu wajen su kawai dai yaran basa tsayi ne da zarar an haifesu wasusunsu ko sati Daya ma bazasu kai ba suke mutuwa, a haihuwar su ta biyu ɗane namiji yaron saida yakai wata biyar sannan ya rasu, haihuwar ta uku ma ɗane namiji saidai ya fara girma domin yana taka ƙafarsa ko ina shima yazo ya rasu ba ko ciwon kai, shiyasa koda aka haifi leeyana basu wani ɗaura mata soyayya ba saboda suna tunanin itama zata mutu ne kamar sauran ƴaƴansu saida sukaga kwanaki na tafiya, satuttuka nata tafiya, watanni sunata gudu, shekaru kuma suna shudewa hardai takai anyimata ƙanwa wacce aka sakawa Aleena murna da godiya ga Allah kam bazan iya faɗi ba kawai Ku misalta da kanku. koda yake basa saka rai ga ƴaƴan nasu har dai sukazo suna sakin jiki dasu a yanzu. Hamraz na matuƙa ƙaunar yaransa yayinda ammi FAHEEMA ke kokari wajen ganin ta tarbiyantar da yaranta.

Leeya dabance da aleena komai na rayuwarsu ya bambanta kamar tsarin zubin halittarsu da kuma tsarin halayensu, Aleena ta kasance rigimammiyace ta ƙin ƙarawa, yayinda leeya ta kasance mai sanyi a halayenta, Aleena batada hakuri ko kadan bata yafiya, yayinda leeya ta kasance bata ma shiga harakar mutane balle ta tsokano rigimar su saidai ita a tsokaneta, ko a hakan kuma Aleena ce take karɓewa, leeya ta kasance tanasamun tsokana a wajen mutane da kuma hantara da ƙyara saboda wani banzan dalili na mutanen, a kaf faɗin unguwar tasu da ma ECOCO LAGOS NIGERIA ba wani mahaluki daya taɓa ganin fuskar leeya idan ka cire Aleena, Abbie, da kuma Ammi.

Tun tana ƴar ƙaramarta ammi ta saba mata da hakan shiyasa koda da fara girma sai bata sha wahala ba wajen sabawa da ɓoye fuskarta ta. Sau dayawa idan suka fita an aikesu ko kuma zasuje makaranta idan har basu sami abin hawa tun a layinsu ba, yanada wuya sukai inda zasuje leeya bata haɗu da masu barazanar cire mayafin da take rufe fuskar ta dashiba, tun sa’adda taga mahaifiyarta bataso ana ganin fuskar ta, itama take ƙoƙari wajen ganin ta hana aga fuskar Tata Wannan kenan.

Leave a Comment