*_🌳BAƘAR INUWA….!!🌳_*
_{Gara rana dake}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_Da sunan ALLAH mai ramahama mai jinƙai_*
*_Ya rabbi ina roƙonka da sunayenka ƙyawawa masu tsarki, ka bani ikon rubuta abinda zai amfaneni ni da al’umma. Ka tsareni rubuta abinda zai cutar dani da al’ummar MANZON ALLAH (S.A.W). Yanda muka fara lafiya ALLAH yasa mu kammala cikin farin ciki da kwanciyar hankali🙏🏻_*.
*_Ya rabbi ka gafartama mahaifina, ka ƙarama iyayena biyu mata da suka rage lafiya mai amfani.😭🙏🏻_*
_Littafin *BAƘAR INUWA* ƙirƙirarran labarine da baida alaƙa da kowa da komai. An yisane domin faɗakarwa, nishaɗi, ilimantarwa, harma da ban haushi ta wani sashe. Dan haka a wannan gaɓar ina son jan hankalin mai karatu, yayma kansa adalci yayma marubuci adalci._
*_A duk lokacin da mai rubutu ya kafa alƙalaminsa akan takarda ba yana nufin dole zai rubuta irin RAYUWARSA bane, ko irin RAYUWARKU. Malami yakan faɗakar ya tsoratar akan abinda ya dace. Haka shima marubuci yakanyi rubutu domin faɗakarwa ko nishaɗantarwa akan abinda rubutunsa yazo dashi. Idan yasa ƙyaƙyƙyawa, ba dole sai yanada irin wannan ƙyawun bane, domin kuwa kowa yasan a duniya akwai ƙyawawa. Idan yasa mai ƙarancin ƙyau (domin UBANGIJI bai halicci mummuna ba, kowa da irin ƙyawun da yay masa na halitta), ba dole sai yana a cikin wannan jinsin bane, sai dan rubutunsa a haka yazo. Idan yasa mai arziƙi, badan dole sai shima yanada arziƙin ba. idan yasa mai mulki, ba dole sai ya kasance jinin mulki ba. Idan yasa talaka, ba dole sai ya kasance talaka ba. Abinda kawai nasani alƙalamin marubuci zai iya taɓa kowa. Mai kuɗi, talaka, mai mulki, ɗan ƙauye, ɗan birni, musaki, mai ilimi, jahili, ƙyaƙyƙyawa, mai ƙarancin ƙyawu. Mai ƙyawun hali, mugu dama kowa da kowa. Duk kuma abinda ya taɓo idan zaka nutsu wajen zagaye cikin duniya koda ace da tunani ne sai ka samu mai kamanceceniya da LABARIN. Shiyyasa kuskure ne mai KARATU ya tsuke tunaninsa akan dole sai abinda ya sani MARUBUCI zai wallafa ko ya faɗa. Idan akasin hakan yazo kuma shi a gurinsa marubuci baiyi dai-dai ba. Karka manta ALLAH ya haliccemune yaruka daban-daban, jinsi daban-daban, yanki daban-daban, launi daban-daban, addinai daban-daban, yaruka daban-daban. Bai zama lallai sai abinda kai ka sani ko kake gani zai rubuta ba. MARUBUTA da yawa sun sha rubuta LABARANSU ko RAYUWARSU a littatafai daban-daban batare da kunsan nasu bane ba. Saboda basu fito sun sanarma duniya nasun bane ba. Dan haka ina roƙonku idan LITTAFI yazo muku, ku karanta kawai badan lallai sai yazama RAYUWAR wanda ya rubuta ɗin tazam dai-dai da abinda ke ciki ba. Kawai kadai duba darasin dake ciki ka amfana, akasinsa watsar, yi farin ciki da farin cikin da yazo dashi, dan wani abun akan rubutashine kawai domin ƙawata labari ko nishaɗantar da mai karatu wajen cire masa wata keɓantacciyar damuwarsa. Ina fatan za’a fahimceni_*
_Banyi wancan dogon bayanin bane dan na canja kowa, nayi ne kawai dan ya zama dai-dai da fahimtar ka a ƙwaƙwalwarka da tuntar da kai wanene MARUBUCI a taƙaice. Domin kuwa KOWA masoyin Bilyn Abdull ne, amma bai zama kallai ita ta zama abin SON kowa ba._☺️
*_Alhamdulillahi ZAFAFA BIYAR sun sake dawowa gareku da sabbin salo daban-daban. Muna fata ALLAH ya baibayemu da alkairinsa mu da ku dake tare da mu. Sannan muna roƙon wanda ma basu tare damu, kodan sauke haƙƙi kuzo dan ALLAH ku saya da kuɗinku badan zamu iya furta kalma mara daɗi gareku ba. Dan kuwa koda wasa bama fatan jifan wani ɗan uwanmu musulmi da kalmar (ALLAH ya isa akan littafi). Masu saya ku fitar, dan girman ALLAH kuji tsoron ALLAH. Badan mu ba, badan mun isa ba. Kuyi haƙuri ku daina aikata mana hakan, domin UBANGIJI ya hana zalunci a tsakaninmu._*☺️🙏🏻
_Masoya kumuje zuwa, domin kuwa yanzu za’a far share filin wasan, dan wannan karon tafiyar ZAFAFA ta dabance😉⛹🏻♀️⛹🏻♀️⛹🏻♀️⛹🏻♀️⛹🏻♀️_.
_____________________
*_Episode 1_*
………….Tafe yake tamkar iska zata kwasheshi ya faɗi dan sauri. Yayinda yake ƙananun surutai kai kace sabon kamune a hauka. Ya sake cin tuntuɓe a karo na biyu, sai dai cikin sa’a ya dafe bangon gwaguyayyen gidansa saɓanin ɗazun da sai da ya kai ƙasa. Dogon tsaki yaja zuciyarsa na sake hasala da kumbura har cikin maƙogwaro. Cikin son huce haushinsa da takaici yasa ƙafa ya daki murfin gidan na sa da duk ya cinye da tsatsa tsabar daɗewar da yay, dan tunda aka gina gidan banajin an taɓa sauya ƙyauran saboda koɗewa da ciccinyewar da yay na tsatsa tamkar tsohon drom ɗin ƙarfe.
Ball ya fara da butar da ke a farkon shigowa, inda alamu suka nuna toilet ɗinsu ne a wajen. Ta tafi ta daki ƙarshen bango, murfin yay gefe itama tai gefe.
Baba Nafi da ke alwalar magrib ta ɗago kai cike da nutsuwa da sanyinta ta dubesa. Sai kuma ta maida kanta ƙasa saboda uwar hararar daya zuba mata kai kace idanun nasa zasu zubo ƙasa ne.
“Kowanne shege da ke gidan nan ya fito!!”. Ya faɗa a kausashe yana dukan langa-langan da aka zagaye saitin inda yake tsaye matsayin kitchen ɗin girkinsu.
Cikin takaici da haushi aka bankaɗe labulen ɗakin tsakkiya, “Kai ko malam ka dinga sassauta ma zuciyarka mana dan ALLAH!, da wannan farar magriban da kowa ke ƙoƙarin kai abincin buɗa baki bakinsa maimakon a ganka bayan liman kana shirin gaida UBANGIJI sai ka lalace da neman masifa da tijarar hana iyalanka su susha ruwa cikin salama kamar yanda ka hana kanka?”.
Fici-fici yay da ido yana duban ta cikin ɓacin rai. Ya tattaro duka takaicinsa da damuwa zuwa cikin baki. Nunata yay da ɗan yatsa yana karkaɗa hannu cikin gargaɗi. “Larai ina rabaki da tararmun numfashi idan ina magana amma baƙya kiyayata. Na rantse miki da ALLAH idan ban sauke dukanin abinda na kwaso bisa kanki ba kice ba sunana DAUDA jikam mai ɗan-wake ba.”
Baki ta taɓe da sakin labulen, sai dai bakinta bai mutuba. Da ga cikin ɗakin take faɗin, “Can kaji da fitinarka ba’a kaina ba. Baka sauke haƙƙin bani abinda zanci a cikin wata mai falala ba bazaka sauken gangar ɗan bazakuɗa ba. Kai da ka kwaso abarka can ta ƙare maka ba Larai ba.”
Duk da ya jiyota sai bai tanka ba, ya cigaba da ƙwala shelar kiran kowa yazo gabansa. Shiru babu wanda yay tari tamkar kowa ya mutu a gidan. Wani ƙududun takaicin baƙin ciki daya taso masa daga tsakkiyar zuciya ya jawo da ƙyar zuwa maƙoshi ya fesar ta baki.
“Eh lallai ta tabbata an gama maidani ɗan iskan ƙasan gada, yo banda ana ɗaukata girman fadar karuwai harni dake amsa sunan maigida a gidan nan zanzo ina magana ku barni ina ɓaɓatu ga ƙwalon shege haihuwar tasha ko?..”
“Kayi haƙuri malam mudai salla muke wlhy, suma kuma nasan…..”
Wuff Larai tayo waje tana gyara zaninta dake neman ɓallewa saboda tsabar sauri, cikin harziƙowa ta tare numfashin baba Nafi mai maganar cikin sanyi da rashin son hayaniyarta “To annamimatu kinsan me? To muma sallar muke sai a maida sherin da ake son ƙulla mana cikin ciki ko?”.
“ALLAH sarki Larai nima ai abinda zance masa kenan bawai wani abu daban ba”. Baba Nafi ta sake faɗa a sanyaye.
Baki larai ta taɓe da juya ƙeya ta tura kallabinta disko gaban goshi, daddagaggiyar ƙeyarta ta bayyana. Murmushi kawai Baba Nafi tai da girgiza kanta ta ɗauke idonta gareta.
Duk abinda suke yana tsaye sai faman kumbura yake da harar ɗakin ƙarshe da ke jerin nasu baba Nafin. Sai dai baice uffan ba. Kusan mintuna biyar aka ɗaga labulen ɗakin aka fito. Mace ce ƙyaƙyƙyawa da bazata gaza shekaru talatin da biyar ba zuwa da bakwai. Daka ganta kaga ƴar duniya bugun farko. Sheƙeƙe ta dubesa shi da matan nasa ta watsar tana taunar chewing gum tamkar ba azumi aka kai ba yanzun nan.
“Wai Lafiya kaketa faman shela da farar magriba ko ruwa bamu kai bakinmu ba? Haba yadai kamata asan da da yanzu akwai banbanci, dan da kana juyamune muna haƙuri da tujaranka saboda kanada uwar kuɗinka a ƙugu, amma yanzu baka barinmu da cikinmu da hidimar ƴaƴanmu ka kuma haɗa mana da tijara da gadara *BAƘAR INUWA……”*
“Asabe! yanzu nan nine baƙar inuwar?”.
“Na tsakkiyar jeji ma kuwa, har gwara *RANA DA KAI”.*
Wata shegen dariya Larai ta bushe da shi, ta callara guɗa tana duban Asabe. “Kina birgeni amarya, idan mu latsamu a tauna baida wahala ke ai kin wuce kanwar lasa”.
Baki Asabe ta taɓe ta ɗauke kanta gefe. Wani irin ƙududun baƙin ciki ya sake kume Malam Dauda. Ya nisa tamkar bajimin sa dake a ganiyar tozon girma yana ballama Asabe ƙarfen ƙafarsa harara. Shikam ai auren bariki bai masa rana ba. Fuska ya sake tsukewa yana kai hannu ya kaɗo mutsiyar tuƙin tuwonsu dake rataye jikin kwanon kitchen ɗin.
“Matsalar mutum ce wannan kuma. Ina son naji wane shege ne tambaɗaɗɗe yaje wajen Jabiru mai shago ya amso lemon kwalba da cin-cin ɗin da matarsa keyi yace injini?”.
Kallon-kallo Nafi da Larai suka shigayi, sai dai komai babu wadda tace tunda sunsan shima yasan wadda zata iya wannan aika-aikar ai. Kuma shine ya bata wannan dama ɗin tun tana amarya, gashi yanzu tsahon shekaru goma sha bakwai har ƴan matanta na yawo galla-galla a gidan harsu huɗu komai ya gagara canjawa……
“Wai ba magana nake ba ne? Ko sai na maida ƙasan gidan nan zuwa sama ne!!?”.
Malam Dauda ya faɗa a matuƙar tsawace tsabar hasalar da zuciyarsa ke sake masa na baƙin cikin bashin da aka cimasa bayan baida ko sisi dana sharesan da akai yana magana. Nanma babu wadda ta tanka sai ƙarar taunar chewing gum ɗin Asabe kawai dake tashi ɗas-ɗas…
Matashiyar budurwa da zata iya kaiwa shekaru goma sha shida zuwa sha bakwai a duniya ta fito da ga ɗakin da Asabe ta fito ɗazun. Sanye take da dogon jijjab har ƙasa alamar salla tayi. Tana tsananin kamanni da Asabe tamkar tayi kaki ta ajiye. Cikin ladabi da nutsuwa takai duƙe tana faɗin “Abbanmu barka da dawowa? Ansha ruwa lafiya?”.
“A gidan ubanwa nasha ruwan? ke kuma zaki sake ɓatan rai!”.
Ƙasa tai da kanta ƙwalla na ciko mata ido, dan tanada zuciya matuƙa, sai dai tana da ƙoƙarin dannewa musamman akan mahaifanta guda biyu da halinsu baida maraba da girman haihuwar ƙasan gada.
“Kayi haƙuri Abbanmu, dama zance maka nice na amso lemon a wajen jabiru”.
“Buhun bu*a’uban nan kayyasa (😨🙆🏻♀️🙊😆). E lallai na zama ɗan iska haihuwar ƙasan gada kuwa da gaske. To ubanwaye ya aike ki!!?”.
Yanda yay maganar a tsawace ya sata runtse idanunta da ƙarfi tana haɗe kukan dake neman taso mata. “Kayi haƙuri Abbanmu, babu wanda ya aike ni. Babu abinda zamuyi buɗa baki ne da shi shiyyasa na amso mana, nace masa kaine ka aikoni dan inba hakaba bazai bani ba”.
Sake maƙurewa yay jikin bango tamkar tsohon ƙadangaren da ciwon sanyi ya buge yake shaƙo ƙamshin mutuwa.
“Ni DAUDA naga haihuwar jaraba jinin ladin ƙasan gada. Niko wai yaushe lalacewata takai har hakane a gidan nan ne wai? K dan uban uwarki har ni zaki laƙawa sheri ina fama da ƙishirwar azumi na? To wlhy ki rubuta ki ajiye sai kinyi nadamar hakan daga ke har uwar taki, dan nasan itace ta aike kin ta noƙe……”
“Kai Dauda sauraramin. To kodai dama dani ɗin kake bada itan ba da ka haifa? To wlhy ahir ɗinka wahainiyarka ta kiyayi ramata, inba hakaba kaima kasan na fika tsiya da tujara. Ka buga ƙafa kamar na karen mafarauta ka barmu cikin yunwa ga ruwa za’a sha saboda kafi kowa iya babbaku da tujara dan kawai an anso abin nera dubu guda injika shine zakazo tsakar gida gaban magauta da ƴan bani na iya kana zazzage min. To wlhy ina dai-dai da kai”.
“Tsssss!!!!”
Kakeji wani irin gigitaccen mari mai ƙara da alamar zaiyi ɗan karen zafi ya sauka bisa kumatun budurwar nan dake tsugunne ranta a matuƙar jagule, ta amshi laifin ne dama dan gudun karsu raba halin da suka saba a gaban kishiyoyin mahaifiyar tasu. Amma sai gashi dabarar tata batai ba.
Ta dafe kuncin jikinta na rawa. “Wannan marin na hanani zaman buɗa baki wajen Jabirunne da kikayi ke kuma. Saura na ƙaryar da kikaimun itama. Ke kuma Asabe yanzu banda lokacin mai lokacinki, amma ina nan tafe kanki..” ya ƙare maganar yana nuna Asaben.
Caraf Asabe tasha gabansa tana mazurai. “Wlhy ka sake taɓamin yarinya sai na rama mata. Kai barfa ganin uwa ban son ta, son kayana nake ras, idan kuma kaji ƙarya sake taɓata dai-dai nake da kai, danni a yanzu nake da naka lokacin. Banda kai dai kana cikin mazan da sai an tsoma kansu a wuta an ɗauraye musu zunibi ka fita baka ko bamu geron kunu ba dan mun samawa kammu mafita kazo har kana tara jijiyar wuya. To bara kaji ni ba matanka bane daka maida sakarkaru, idan kaji ƙarya kuma sake gwada bugunta ka gani, kaima kasan wacece Asabe autar hajiyar birni shalelen bahago dan mai…….”
Sai kuma taƙi ƙarasawa ta balla masa harara, ganin ya juya fuuuu zai sake ficewa. Taja tsaki da faɗin, “Da ka tsaya mana kaji ko zaka iya latsawa ka kwana lafiya ɗan gidan abun kwari mai yawo da tsinuwar uwa bisa kai”.
Wani irin kuka budurwar nan da har yau ke duƙe ta fashe da shi. Cikin masifa Asabe ta juyo kanta takai mata shiru dan tasan minene dalilin kuka. “Dan ubanki tashi anan kona huce kaf haushinsa a kanki mara mutunci. Ko dan dai nice jinin asara sai na zauna yana cin zarafina gaban kishiyoyi na masa shiru saboda ga jikar ta-salla wadda ta haɗiyi ƙur’ani dan haƙuri. K nifa bar ganina haka zan iya kakkaɓar daku nai gaba dama tausayinku ne yasa nake zaune a wannan gidan da tsiya taima katutu abincima sai anyi kwarakarsa a maƙwafta dan lalacewa”…………✍️
*Tofa jama’a bana ina mukazo haka? Ina alƙalamin namu ya kwasomu ya kawo😹😹?.*
_A cikakken Littafin BAƘAR INUWA kawai zamu samu wannan amsoshin. Naira ɗari uku me kacal, tare da duk zafafa biyar naira dubu ɗaya ne kacal. Karku bari ayi babu ku. Dan bakuga komai ba. Yanzu aka fara sharar filin wasan. Cakwakiyar sai wasan ya kankama😉. Dan duk wanda akayi babu shi ALLAH yayi missing🥺._
Taku
_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
___________________________
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*❤🔥
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
________________________
*_BAƘAR INUWA…_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form din kamar haka: –
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App… Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏻
*_Typing📲_*
*_🌳BAƘAR INUWA….!!🌳_*
_{Gara rana dake}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
_Irin wannan katoɓara haka🤭, inda nasa *(Bakatsinen bafulatani episode 2)* an samu mishkilane ba haka bane. Dan babu sunan wannan jihar a ƙasar NAYA. ku ɗauka matsayin mistake Please🙏🏻😹_.
________________
*_Episode 3_*
……….Shigarsu secondary school ya ɗan fara canja wasu da ga halayen Raudha, taɗan fara rage kwaikwayon halaye irin na mahaifiyarsu. Bata da yawan magana, bakuma tason taga iyayen nata na faɗa tamkar karnuka a tsakar anguwa kowa na kallonsu yana ALLAH wadai. Hakan kuma ya farune sakamakon ƙulluwar soyayya tsakaninta da malamin islamiyyarsu sayyadi Abubakar. Tun tana zama taita kuka idan suna raba hali harta koma tana nuna musu fushinta. A lokacin da suke ss1 farkon shigarsu wani faɗa da iyayen nata suka tafka har takaisu ga police station sakamakon yanzu Abbansu talauci ya masa katutu, takai ma nauyin gidan iyayen nasu mata ne ke ɗauka. Dan tunda kamfani ya kamashi akan satar kayan da yake jigila suka kafa masa kahon zuƙa, da yaga asirinsa zai tonu asabe ta zugeshi ya kwance tayoyin motar ya saida, motar takai shekara a ajiye, sai da komai ya lafa ya saidama ƴan gwangwan ita ya kawo kuɗin gida suka hau kai shi da Asabe da ƴaƴanta suka dinga cin daɗi sai ɗan abinda ake samma su baba nafi wataran. Acan kamfani kuma akace ya mutu. Ko shekara kuɗin basu ƙullaba komai ya ƙare, dan kuwa dai a ashararancin ɗan-azumi babu abinda ya canja na neman mata da busa sigari da caca. Tunda kuɗi suka ƙare zaman lafiya tsakanin Asabe da Dauda ya ƙaura. Kullum sune faɗa kamar kaji, taje ta nafko masa bashi dolensa ya biya ko bai ƙaunar ALLAH, idan yaƙi biya su tumu sama dan bala’i su dire bisa ƙasa. Dan kullum zancenta shine ya saketa bata halaka rayuwarta da ƙuruciyarta a ƙarƙashin runfar talauci. Shiko yace bata isaba tunda ta shigo ta shigo kenan. A randa taje ta cicciɓo masa wani bahagon bashi da har akazo aka saka wani filinsa kasuwa da yake ta burin gina mata aljannar duniya ta koma tun tana amarya ALLAH baiyiba ya sakasu yin faɗa na tashin hankali harda jima juna ciwo, shine aka kwashesu zuwa ofishin ƴan sanda daya saka Raudha tsananin baƙin ciki. musamman akan habaici da zagin da akema iyayen nasu akan sunyi dai-dai da juna kowa ɗan barikine ai, tunda dama a zauren dandi suka haɗu, wama ya sani koba zaman auren suke ba.
Wannan ƙananun magana sun matuƙar ƙona ran Raudha harta kaita da kasa kuka saboda bushewar zuciya. Kowa baije yay beilingn su ba, sai ita taje duk da ƙarancin shekarunta. Ƙyawunta da ganin ƙarancin shekarunta yasa d.p.o ɗin sonyin amfani da mutuncinta sannan ya sakar mata iyayenta. Da farko taso tai masa zagin ƙare dangi, sai kuma ta fasa saboda wani abu daya zo mata rai. A take ta amince masa akan ya sakar mata iyayen bayan kwanaki biyu zata kawo masa kanta. A tunaninsa bata da wayo, musamman da yay dubi da halin iyayenta na ƴan bariki. Kai tsaye ya sake su, tana ganin an fiddosu tai wucewarta gida ta barsu duk da magana da suka dinga mata. Ta rigasu zuwa gidan, dan haka kowa bai san itane taje ta fiddosu ba. Dama kuma tun a hanya suka taho suna hirarsu ta arziƙi tamkar basune aka amso hanun hukuma ba saboda tazubar ɗinsu.
Koda suka dawo gidanma sun kaɗa sun raya Raudha taƙi tanka musu, taƙi cin abinci ta kuma daina shiga harkar kowa a gidan. Tun suna ɗaukar al’amarin nata wasa harya fara cin ƙarfinsu, da ga ƙarshe dai suka haɗa baki da wani malamin islamiyyar su Raudha ɗin da suke yawan jin sunansa a bakinta da ganin tana tsananin girmamashi dan yana ɗaya daga cikin wanda suka gyara tarbiyyarta dake a bauɗe tunda farko sannan Raudha ta sakko harta nema gafarar iyayen nata (Sayyadi Abubakar). Dan Ya sayyadi Abubakar ya sanar mata su iyaye ba’a fushi dasu, ko wanne irin hali garesu lallaɓasu ake da ƙyaƙyƙyawan kalami. koda anji ciwo akan kuskurensu shanyewa akeyi ayi haƙuri. Saɓawa ALLAH ne kawai ba’a yarda kamusu biyayya akansa ba wannan haramunne.
Raudha taji wannan nasiha hartazo ta bama iyayenta haƙuri. Daga lokacin kuma ta dinga taka tsantsan da harshenta a kansu da fushinta. Idan ma taga abu zai basu saɓani ta gwammace ta amshi laifin ita koda zasu mata hukunci ne. Idan batasan tushen rikicin nasu ba kuma zatabi duk hanyar data dace ta sasantasu cikin hikima. Sai dai kuma kuka ya zame mata tamkar abokin rayuwa, dan sam bata ƙaunar halin mahaifan nata guda biyu ko kaɗan.
A yanzu haka Raudha da sauran ƴan uwanta na sauran ƴaƴan ɗakunan biyu sa’anninta suna akan zana jarabawar gama secondary school ne. A ƙalla shekarunsu Fatisa goma sha takwas, Raudha kuwa sha bakwai ita da Iklima da Binta. Kasancewar babu wani batun Noziri a karatun nasu yasa suka kammala da ƙarancin shekaru, musamman ma ita dasu Binta duk sun girme mata.
Halin talauci da fataran da suke ciki ga shegen son kuɗi na Asabe ya saka ƴaƴanta su Fatisa fara kaucewa hanya wajen biyema samari. Duk da kuɗin da yaran ke shigowa dasu na ban mamaki da kayan kwalliya basu sana’ar ko asi bai taɓa saka Asabe nuna damuwa ba balle tuhumarsu. Sai dai ma ta baje suci su sha mai daɗi tana kiransu masu farin jini. Tabbas *ZINA* tamkar sharri take, dan ƴar aikece komin daren daɗewa saita dawo cikin zuri’arka. Hakanne ya faru akan su Fatisa dama wasu a ƴaƴan mal ɗan azumi na sauran ɗakunan, dan kuwa cikin ƙanƙanin lokaci rayuwarsu ta ɗakko hanyar lalacewa Dauda naji na gani babu halin magana, duk da abun na ƙona masa rai da soya zuciyarsa. Dan ko yayi magana Asabe ta taresa da masifar cewar yanama ƴaƴanta sheri saboda shima aikinsane zina. Maƙiya masu baƙin ciki da hassada wa farin jinin ƴaƴanta na ɓoyewa bayan ƙofa suna musu dariya. Sai dai abinda Asabe bata sani ba na ƴaƴan ɗakintane ya fito, amma itama Larai nada Kangararru irin su Fatisa har su uku. Wani lokacin duk da gogewar ɗan-azumi a bariki, Asabe ta fisa bala’i, shiyyasa idan taja yaja sai ya sakar mata dan zuwa yanzu girma yaɗan fara kamashi, ga ciwo dake cinsa a tsaye na hawan jini wanda ko ba’a faɗaba asabe ce silarsa, gefe ɗaya taba ta gama cinye masa naman jiki sai ƙashi da jijiya da fata.
Halayyar su Fatisa na matuƙar ƙona ran Raudha, sai dai babu yanda zatayi dan ko tayi nasihar basaji. Ita kanta samarin na yawan kawoma rayuwarta hari, musamman daya kasance ta fisu ƙyau nesa ba kusa ba. Hankalinta yakan tashi matuƙa, shiyyasa akoda yaushe cikin suturta jikinta take da kayan mutunci harma da niƙab wani lokacin. Takan yawaita neman tsarin ALLAH daga ƙaddarar zina a gareta.
Rashin samo kuɗi da batayi yasa Asabe tsangwamarta a ɗakin fiye da kowa. Dan hatta Yasmin ta fita daraja duk da kuwa Asaben tafi son Raudha fiye da kowa acikin ƴaƴan nata. Sai dai lallaɓa da lallashin da take mata akan ta dinga kula samarin sai tafi su Fatisa samo kuɗi, amma Raudhan na bijirewa yasa ta ɗauka karan tsana ta ɗaura mata ita da su Fatiman. Kullum cikin caccakarta suke da magana mara daɗi. Da yake miskilace kuma bauɗaɗɗiya ko kulasu batayi ma balle ta nuna ta damu, fatanta kawai tai aurenta tana gama secondary school da ya-sayyadinta Abubakar da kowa yasan suna soyayya zuwa yanzun.
A ɓangaren sayyadi Abubakar shima babban burinsa mallakar Raudha matsayin mata. Dan haka suna fara exam ya sanarma iyayensa akai kuɗi. Sunyi farin ciki da farko dan basusan ƴar waye ba a Hutawa. Dan haka suka tambayesa acewar mahaifinsa sai sun fara bincike tukunna. Abubakar ya shiga fargaba, amma sanin Raudha yarinyar ƙwaraice mai kamun kai, kuma da ita zai zauna yasashi jin ƙwarin gwiwa.
Bayan kwana biyu mahaifinsa ya kirasa shida ƙanensa sukai masa wankin babban bargo, tare da gargaɗinsa ya fita sabgar Raudha bata fito cikin gidan arziƙi da mutunci ba, su bazasu haɗa zuri’a da ɗan-azumi ba. Idan ma ƙyawun yarinyar ke ɗiɓarsa yaje akwai ƙyawawa da suka fita ya nemo. Idan kuma ya sake koda yima Raudha magana ne ALLAH ya isa basu yafe ba. Itama sunje har gida sun gargaɗi ubanta akan ta fita hanyarsa. Daga karshe suka hanashi cigaba da koyarwa a islamiyyar su Raudha ɗin baki ɗaya. Sukama maida rayuwarsa can cikin birinin Ɗillo wajen wani ƙanin baban nasa dake can da iyalansa.
Wannan shine sanadin raba Raudha da Sayyadi Abubakar. Tayi kuka kamar yanda shima yayi nasa. Kusan dukansu sai da suka kwanta a asibiti dan ba karamar shakuwace a tsakaninsu ba. Halin data shiga yasa ɗan-azumi da Asabe zuwa har gida sukaima iyayen sayyadi Abubakar tas. Wannan ya ƙara harzukasu suka kara jin tsanar tushen Raudha da ƙyamar haɗa zuri’a da su.
Sosai wannan lalacewar aure taima Larai daɗi, dan kuwa tana ɗaya daga mutanen da suka sake lalata zancen auren, mahaifin Sayyadi Abubakar nada ɗan hali, shiyyasa tun yana zuwa wajen Raudha takeji baƙin ciki da hassadar hakan. Sai dai tabi duk wata hanyar rabasu hakan bai samu ba, sai gashi cikin sauƙi komai ya lalace. Da wannan damar tai amfani wajen zuwa har gida ta sakema Asabe da ɗan-azumi batanci fiye da wanda iyayen Sayyadi Abubakar suka jiyo ga wasu mutanen. Sai ka rantse ɗan-azumin ba mijinta bane.
Raudha ta ɗanɗana azabar rashin Ya sayyadi Abubakar har batasan mi take rubutawa a jarabawa ba har suka kammala. Bayan kammalawar tasu ta sake dawowa gida zaman sabuwar jiyya, a dalilin hakan ciwon Asthma ɗinta da bai cika karfi ba ya sake ƙarfi har takai yana yawaita tashi yanzu. Gefe kuma ga azababben ciwon mara idan zatai period har suma take wani lokacin. Dama dalilin ciwon marar natane sayyadi Abubakar ya yanke shawarar data kammala secondary school suyi aure kawai, sai ta cigaba da karatunta a gidansa. Sanda suna tare saboda tsabar kiyaye yanayin nata da wata ya kama zai kawo mata magunguna da allura ta ajiye, da abin ya fara mata za’a nemo wani yaron makwafcinsu dake da kyamis yay mata allurar. Ta hakane take samun sassauci sai abun yazo da sauƙi..
_Wannan kenan😚👌🏼._
*_Mun dawo labari_*🏃
Kiran sallar isha’i ne ya sata miƙewa da ga kwanciyar kukan da tayi, ta fito daga ɗakin baki ɗaya batare data ko kalli inda su Fatisa ke zaune suna hira da shewa ba su da Mommynsu. Sai ma Yasmin ce data miƙe zumbur tana ƙwala mata kira da faɗin, “Aunty R zanje”. Dan tasan massallaci zataje sallar asham. Bata tanka mata ba, dan ƴan miskilancin na kusa ne, sai dai ta mata alamar tai alwala. Itama kuma ta ɗauka buta ta ƙarasa inda sukeyin duk wani hidimarsu na harkar ruwa a gidan tai alwalar sannan suka fice……….✍
*_Humm Sayyadu Abubakar Abubakar ya tafi, wa kuma zaizo? Ta ina zaizo? Yaushe zaizo AMINATU Raudha?. Dukkan amsarku na cikin BAƘAR INUWA ne, dan bazan gaji da faɗaba ba’a fara komaiba har yanzun masu karatu. Kar dai ku bari a baku labari😉⛹🏻♀️⛹🏻♀️._*

Leave a Comment