Books Reviews & FAQs

Bafula Tana Hausa Novel Complete

🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*_BAFULATANA_*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

 

*Page – 1*

*WRITING BY :ZM CHUBAƊO*✍️

*WARNING! WARNING!! WARNING!!!*

*_THE BOOK BAFULATANA IS NOT FOR SALE, DUK WANDA YA SIYAR MIKI DASHI TO ƊAM DAMFARA NE WLLH, HKAA KUMA DUK WANDA YA SIYARMIN DASHI KO YA JUYA MIN SHI TA WATA FUSKAR BATAREDA SANINA BA ALLAH YA ISA🙅‍♀️_*

*_Da sunan Allah me Rahama me jinqai salati da ɗaukaka su tabbata ga manzon tsira Annabin mu Muhammad (S.A.W). Ya ubangiji kayi min katangar qarfe da duk wanda ke shirin ɗaga min hankali a yanar gizo Ko waneneshi Mace ko Namiji🤲 sannan kayi riqo da hannuna wajen Rubuta dukkan abinda ze amfani al’umar musulmi gabaɗaya._*

*_wannan littafi ba Sabo bane tsoho ne zan sake faɗaɗa muku shi ta yanda waƴanda basu karanta ba A baya zasu samu damar karantashi , amma sedai salon zesha banban dana farko kamar yanda sunan littafin ya canza Salo daga BAFULATANA zuwa BAFULATANA RETURN. Fatan Ubangiji yasa mu Amfana da darusan dake ciki_*

***

*_GYAMBU ((TARABA STATE))_*

Tafiya suke cikin daji tare da shanunsu wata matashiyar yarinya Ce wadda bazata wuce shekaru goma sha hudu ba se kuma dattijon dake kusa da ita da alama dai mahaifin ta ne, cike da damuwa yarinyar ta daga Kanta ta kalli mahaifin Nata cikeda damuwa tace “wllh Baba nagaji kawai ka tafi Gida idan na huta zan tawo da shanun ta Ƙare maganar Da damuwa akan fuskarta.

Tunda ta fara magana mahaifin nata Ke kallonta sannan Yayi murmushi yace “to Rabe Babu damuwa amma fa ki kula sosai Da kanki. a nitse ta amsa da to “Baba.

Shafa kanta yayi sannan ya juya ya Kama hanyar gida Ya barta a Dajin tareda Dabbobin, yana tafiya Rabe ta nufi wata Ƙatuwar bishiya dake gefanta ta zauna dan ta huta a nitse ta Ta fara cire Takalmin Robar dake Ƙafarta, tana Gama cirewa ta Jingina da jikin bishiyar bata jima da kwanciyar ba Wani gajiyayyen bacci ya Samu nasarar ɗauke ta sabda Tsabar gajiyar dake tareda ita, kallo daya Zakayi mata ka fahimci tana jin dadin baccin da takeyi.

A hankali iska me daɗi ta fara kadawa Tareda ƙamshin ƙasa wanda hakan ya gauraye a guri guda ƙamshin ya canza zuwa wani yanayi me daɗin gaske can kuma se aka fara iska me qarfi wadda itace ta zama sillar farkawar Rabe daga baccin datakeyi a hankali ta daga Dara-Daran idanunta Sama Tana kallon hadarin daya gauraye sararin Samaniya ya koma launin baki aiko da sauri ta mike tafara kada shanun tana fadin su kama hanyar gida cikin harshen fulatanci tayi maganar nan da nan shanun suka fara tafiya kamar yanda tace musu suna cikin tafiya Yayyafi ya fara sauka a hankali can kuma se ruwan ya balle kamar da bakin Ƙwarya, A maddin ta nemi maɓoya se kawai ta dinga tsalle tana murna Ruwan na sauka a jikinta tana dariya, Haka nan Ruwan yayiwa Rabe dukan tsiya amma itako ko a jikinta wai an tsikari kakkausa inji ‘yana magana lol.

Cike da annashuwa take tafiya tana tsalle tana kuma shiga cikin ruwan da ya taru a kan hanya Har Ruwan ya ɗauke Kasancewar kayan jikinta na farin Saƙi ne yasa Duk yayu jajir Sabida jar Ƙasar dake hanya, haka tai ta shiga cikin ruwan dake kwance bisa hanyar tana bin shanun.

 

Suka kama hanyar gida, basu jima ba suka iso gida seda ta fara kai shanun cikin garken su sannan ta Ƙarasa inda bukkokin su suke, da gudun ta ta Ƙarasa bakin Ƙofar da zata sada ta da Bukkar matar babanta da sallama ta shiga Ɗakin cikin harshen Fulatanci tace ” inna na dawo.

cike da bacin rai tare da tarin tsana take kallonta, cike da masifa tace ” Uwar me zan miki da kike gayamin kin dawo shegiya me mugun hali, Zaki fita ko sena fito naci ubanki shegiyar yarinya me baƙin jinin tsiya har yanzu kinƙi auruwa sabida baƙin jininki, uwarki ma a tsiyace ta Ƙare kuma kema a haka zaki Ƙare Tinda kikayo gadon tsiya. Inna ta ƙare maganar tana hucci kamar macijiya

Tunda ta fara maganar Rabe Ke kallonta cike da rashin fahimta dan harga Allah bata fahimci abinda Innah Lauren take nufi ba Sam, kullum tana gaya mata haka amma Sam abin Be taɓa damunta Kamar yau ba, tambaya ɗayace ke mata yawo a cikin zuciyarta a gameda maganganun inna laure shin meyasa kullum take Maimaita mata magana ɗaya babu canji? Shin meyasa take yawan tunani akan magar innar a yan kawanakin nan?

Tana cikin duniyar tunanin datakeyi ne taji Saukar murfin kwano a daman goshinta!

Inna Laure ce ta buga mata tana huci lokaci guda kuma ta suri kwanon dake gabanta ta
Cike da Mugunta ta jefi Rabe dashi Daidai saitin hancinta aiko nan da nan Jini ya fara fita a goshin ta Da hancinta, gigicewa ta juya tana nemam hanyar fita daga bukkar Tana Neman agaji sabida Jinin data gani yana Zuba daga hancinta da goshinta, sosai ta gigice sabida a Rayuwarta batason ganin jini komai ƙanƙantarsa tsoronsa take ji. Da gudu ta nufi hanyar garken shanunsu Tana kuka sabida batado Babanta ya dawo ya gani tabbas bazata taɓa jin daɗin haƙan ba.

Karo taji tayi da mutum cikeda tsoro taja da baya zata fati taji an riƙeta gam, mahaifinta ne malam moddibo,
Cike da tashin hankali yake firta “innanillahi’wainnah’ilaihirraji’un

Cike da tashin hankali ya Jawota jikinsa tare da kama goshin Yana dubawa da sauri, hannunta Ya kama suka nufi Ɗakinsa dan yasa mata maganin daze tsayar da zubar jinin, cikin ikon Allah kuwa jinin ya tsaya amma sedai goshin ya kumbura sosai kuma Yayi jajzir kasancewarta fara, a hankali take sauke numfashi sabida zafin da gurin ke mata cikin sanyi murya baban ya fara magana Kamar haka
“Rabi’atu kiyi haƙuri da rayuwa kamar yanda nake gaya miki kullum kuma dik abin da ze dinga hadaki da Laure ki dinga kauce masa sbda bata da burin daya wuce ta illatamin ke, sanin kanki ne bani da kowa Daya rage mini a yanzu seke, tunda na rasa mahaifiyarki nakejin a raina cewar na rasa wani Ɓangare na rayuwata, shikuma dan Uwana tuna kina jaririya aka nemashi aka rasa seda ga baya aka samu gawarsa a bakin hanya, A kwai cuwuka sosai a cikin Rayuwata wanda banaso ma na dinga tunasu sabida yanda zuciyata ke zafi a sanadinsu. A sanadin mutuwar ɗan Uwama muka dena bin titi da dabbobin mu Har zuwa lokacin da mahaifiyarki ta haifeki, tunda na rasa iyaye na ban Ƙara samun farin ciki ba seda na auri mahaifiyarki, amma itama daga baya Allah ya karbe Rayuwarya ta rasu ta barmin ke, tun kina shan nono a haka kina fara girma ina kula dake
Bayan rasuwar mahaifiyarki da shekara 2 malm iro yazomin da shawarar na Ƙara aure Kodan sabida ki samu rayuwa me in ganci, cike da damuwa na kalleshi nace ” Banƙi shawararka ba Iro sedai inajin tsoron wace mace zan Aura wadda zata iya riƙemin Rabe bisa gaskiya da Amana?
Har ga Allah bana so Rabe ta rayu da ciwon maraicin Uwa A Rayuwarta Ko kaɗan. da kulawa malm Iro ke kallon Aminin nasa
Yayi murmushi yace “indai wannan ne ba wata matsa bace Moddibo zan baka Ƙanwata Laure ka aura nasan zata riƙeta da Dukkan gaskiyarta fatana kawai ka Amince da wannan batun Kuma ka kwantar da hankalin ka.

badan zuciyata taso ba na Amince Da maganar Auren laure, koda
malam Iro ya fahimci zuciyata bata gama amincewa da mganar auren ba se ya sake murmushi a karo na biyu yace “indai Har ka amince ka aureta nikuma nayi maka alƙawarin zan zama me koyar da Ƴarka Rabe karatun addini Tayanda zata zama daban a cikin sauran yaran dake maƙotaka da Rugar mu. Ya ƙare maganar cikeda murmushi

Batare da tinanin komai ba na amince zan auri Laure. Ashe abinda ban sani ba shine sanadin tarwatsewar rayuwar gidana da farin cikin Ƴata ba Auro. Moddibbo ya Ƙare maganar Yana Kuka

A nitse Rabe ta rarrafo kusa da mahaifin nata ta rugumeshi tana kuka tare da share mai hawayen dake Sauka a saman kumatunsa da tafin hanunta, seda moddibo Yayi kuka me isarsa sannan Yayi shiru, cike da kulawa Ya shafi gefan fuskarta yace “kinci abinci Kuwa? Da sauri ta Ɗaga masa kanta alamar ae kuma a zahirin gaskia bata ci ba, Ta amsa masa da Ae ne kawai dan hankali n mahaifin nata ya kwanta

Moddibo yay murmushi yace “to maza tashi ki tafi daukar karatun don kar lokaci ya ƙure miki banda tsayawa wasa kinji Allah, ya albarkaci rayuwar ki Rabe na.
Ta amsa da amin sannan ta tashi ta nufi makarantar Allon malm iro inda take daukar karatu,

Dik da cewar su fulanin daji ne amma Sam hakan Be zama illa garesu ba Kuma be hanasu karatun addini Ba, duk cikin sa’ oin Rabe babu wacce batayi aure ba se ita da Ƙawarta Ruƙatu sune kawai suka rage a yaran da basuyi auren ba,
Rabe kyakkyawar yarinya ce kallo Ɗaya zakai mata ka fahimci hakn, tana da manyan idanu tare da gashin gira me yawa hancinta dogo ne sosai kamar na mahaifin ta sannan yana da dan fadi kadan, labbanta ma daidaita ne kuma suna da dan tudu kadan tanada yalwataccen gashin kai ma’ana yana da tsayi sosai Irin na Fulanin Asali kuma ƴan gado, Rabe doguwa ce Sosai tayanda tsayinta yafi ƙarfin shekarunta, kallo daya zakayi mata ka fahimci tana da kyau da diri irin na fulanin Usuli, Rabe miskilace ta ajin Ƙarshe magana ma ba damunta tayi ba Se idan ta zama dole, sedai Sam hakan baya hanata Gaida mutane

Rabe yarinya ma’abociya fara’a da son karatu hakan ne yasa malm iron ke Ƙaunarta sosai
Sbda tana gane karatu Cikin sauƙi, koda wasa bata sakewa samarin Rugar tasu wannan ne yasa suke cewa tana da girman kai , amma a zahiri sam ba haka bane Mutum ɗaya ne ya nace mata har seda yasa ta fara kulashi sabida baƙin nacinsa Ana kiransa da Suna BAMANGA shima baɗan Rugarsu bane ɗan Rugar dake maƙotaka da tasu ne, a nitse ta qarasa makarantar Abin mamaki babu wanda yazo se ita kadai, Ajiye Allon ta tayi sannan ta dauki tsintsiya ta share gurin Tass ta shimfiɗa tabarman kabar Dake jingine tahau ta zauna ta fara bitan karatunta dan a ranar zata wanke Allon ta

Tana cikin karatun ne Ruƙatu ta Ƙara so da sallamar ta amma Rabe bata Amsa ba Har seda takai aya sannan ta daga kai da murmushi ta ansa mata sallamar,
Ruƙatu tayi dariya tace “sannu sarkin hadda shine ko ki biyo min ko?? To ai gashi nazo nima kuma nasan dan ki rigani wanke Allo ne yasa kika tawo kika barni to ai na gane wayon naki
*_((duk wannan maganar cikin harshen fulatanci suke Yinta nayi haka ne dan me karatu ya fahimci gundarin labarin sbda idan nayi ammafani da harshen fulatanci ba lallai wani ya fahimci abinda labarin Ya ƙunsa ba))_*
Rabe tayi dariya Tace “Ruƙatu kenan keda zakiyi aure kwanan nan ai kin ma kusa ki dena zuwa makarantar Gabaɗaya saurin me zakiyi kuma?

Haɗe rai Ruƙatu tayi Sannan tace “to ai se munyi sauka zanyi Auren kuma yau saura sati biyu mu sauke da ikon Allah.

murmushi Rabe tayi sannan tace “to Allah ya nuna mana sati biyun.

 

*_Gareku masoyana kuma mabiya littattafaina, idan har salon yayi muku zan gane daga Yawan comment Ɗinga ga wannan littafi. Ima muku batan Alkhairi tareɗa baku tabbacin cewar wannan littafi ze zo muku da zarar na kammala littafina me taken KUYARDA DANI👏_*

Sonso Fisabilillah❤

Sushmah💋

 

Comment
Nd
Share
[3/3, 5:22 PM] Chubado Mohd: ❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
*BAFULATANA*
✨RETURN✨
🐄🐄🐄🐄
🐄🐄🐄🐄
❄️❄️❄️❄️❄️❄️
❄️❄️❄️❄️❄️❄️

*_Page: 2-3_*

*_A JIYA NAYI MISTAKE A MADADIN NA NACE GYAMBU ((TARABA STATE)) SENA SAKA GYAMBU ((ADAMAWA STATE)) A FARKON PAGE 1 MANTAWA NAYI CEWAR GYAMBU BA’A CIKIN JIHAR ADAMAWA TAKE BA A CIKIN JIHAR TARABA TAKE FATAN ZAKU FAHIMCENI MABIYA WANNAN LITTAFI😊_*

 

✍️____Da haka suka rufe hirar tasu sakamakon Ƙarasowar malam Iro gurin, cike da girmamawa suka gadashi ya amsa tare da sakin fuska yace ” An gaida Ƙawayen juna Idan har akaji maganar Rabe to da Ruƙatu ne koda Moddibbo. Malam Iro ya faɗi hakan yana murmushi

Suma murmushin sukayi Basuce komai ba kansu a sunkuye, Ruƙatu aka fara biyawa Allonta sannan aka biyawa Rabe Ma nata, suna kammala Karatun ba jimawa sukayiwa malam Iro sallama kana Suka kama hanyar gidajensu, a hanyar komawar ne sukai kacibus da Aliko Wanda ze auri Ruƙatu, Tun kafin su ƙaraso inda yake ya kafesu da idanu kamar ze cinyesu, turo Baki Rabe tayi sannan ta zinguri Ruƙatu tace “da alama nan gaba wannan maƙale matan naki har makaranta ze dinga binmu idan har ba’a ɗaura muku igiyar Aure ba. Rabe ta faɗi hakan yayin da take nuna mata Aliko

A nitse suke tafiya har suka ƙaraso inda Alikon ke tsaye cike da fara’a suka gaisa da Rabe ita kuwa Ruƙatu se Faman boye fiska take a bayan Rabe wai ita Ala dole kunyarsa takeji,
Basu jima a tsaye ba Rabe tayimai sallama ta nufi gida cike da tinanin Abinda zata tarar Na daga bala’in Inna Laure, siyasa taita wasa a hanya harta gama cinye sairan lokacin daya rage mata sannan ta kama hanyar gida sabida tasan mahaifin duk inda yake a wannan lokacin to ya koma gida, bata dawo gida ba se yamma liƙis kasancewar suna da nisa da makarantar, cike da fargaba ta Ƙarasa dakin da take kwana ta kwanta tare da sauke ajiyar zuciya.

A hankali ta firta Kalmar “Alhamdulillah Bisa rashin haɗuwar da basuyi da inna ba, Sabida har ga Allah batason duk abinda ze ƙara haɗata da inna Laure dan tasan haduwar Tasu ba alkairi bane, tana cikin wannan tinanin ne taji Antaɓa Labulan buhun ɗake jikin Ƙofar bukkar ta, da sauri ta mike tsaye A matiƙar tsorace har jikinta na Rawa sabida yanda tsoron ya tsirga mata Duk a zatonta innah Laure ce , da sallama ya shigo Ɗakin Yana kallonta Da mamaki sabida yanda yaga jikinta na rawa irin haka da gudu ta Ƙarasa gareshi ta rungume shi Gam Lokaci guda ta fashe Masa da wani irin kuka.

Shiru yayi yana sauraron kukan nata tamkar wadda ke shirin shiɗewa, sosai Yakejin kukan na taɓa zuciyarsa Sedai beyi yunƙurin hanata ba Donta damu damar yin me isarta, hannunsa yasa ya share mata hawayen dake zubo mata yace “kiyi haƙuri Rabe nasan Kinada Cikakkiyar hujjar Da zakiyi kuka sabida rashin dacen da kikayi da matar uba irin Laure, ki Ƙara haƙuri Insha Allah wata rana se labari kinji ?

Da sauri ta Ɗaga kanta alamar To.

A hankali Moddibbo ya kama kafadunta ya zaunar da ita a bakin katifar ciyawar dake Ɗakin yace “daga yau nayi miki Alƙawarin Cewar bazaki sake kukan rashin uwa ba Insha Allahu kinji Rabe? Be jira cewarta ba Ya Nufi ƙofar fita Daga bukkar zuciyarsa na zafi akan lamarin Laure.

Da sauri ta ɗago tace “baba Don Allah kayi Min Aure ko zan dena ganin innah Laure!

Cike da mamaki moddibbo ya juyo yana kallon Ta yace “Aure kikace Rabe? Ba tare da tinanin komaiba ta daga Masa kai alamar Ae,
Jikin sa a mace ya tako Har inda take zaune ya dafa Kafaɗunta cike da kulawa yace ” dagaske kike kina son aure Rabi’atou?

Ba tare da fargaba ko shakkaba tace ” Ae Baba Ina so Indai zan dena ganin inna. Ta faɗa tana kallonsa hawaye na zubo mata, harga Allah bata San me ake nufi da Kalmar Auren ba Kawai tana jinta a bakine Batareda da tasan tarin Abubuwan dake cikinsa ba kawai ta fada ne dan ta samu sauqi a zuciyarta.

Modibbo yayi murmushi yace “shike nan zan kawo miki mijin da zaki Aura har gida Tunda dai kince Auren kikeso kinji?

Da sauri ta washe baki cike da yarinta tace “to Babah yaushe zaka kawo Min shi??

Sosai Maganarta ta bawa moddibo dariya Don haka ya kasa cewa komai illa dariyar dayakeyi kawai, itama murmushin tayi
A hankali ya kama kumatunta yace “nan da ‘yana kawanaki kadan zan kawo miki shi Rabe na. yana kaiwa nan ya Fice daga bukkar ya nufi masallaci,

itama tashi tayi taje tayi alwala tayi sallah sannan ta ta nufi dakin Babanta, tana shiga Ɗakin ta sameshi a zaune yana Hada magunguna Gargajiya, dayake Abinda yakeyi kenan bada magani irin na GargajiYa, duk Rugar su shi ake kira idan rashin lafiya ya samu wani Kuma cikin ikon Allah ana dacewa da maganin Nasa Idan har ya bayar.
Da sallama ta shiga ta zauna Daga gefansa tayi shiru batare da tace komai ba, hakan ne ya Bawa moddibbo damar fahimtar yunwa take ji, be ce mata komaiba ya Ɗakko kwanon dake gefansa ya mika mata da sauri ta karɓa Ta buɗe faifan da ka rufe kwanon dashi furace da nono nana da nan ta kafa kai tafara sha Batare da ta sauke kwanon ba, daga yanda take shan furar ne abin ya bawa moddibo mamaki a nan zuciyar sa ta fara zargin anya kuwa Rabe taci abinci kuwa???

Tabbas ze Iya Ɗaukar komai Da Laure zatayiwa ƴarsa guda ɗaya tak a Duniya amma fa banda Horon yunwa, a fusace ya tashi ya nufi bukkar Laure ko sallama be mata ba Sabida yanda Ransa ya Ɓaci ya Hauta da bala’i kan cewa ze jure komai da zatai masa amma fa Sam banda yiwa gudan jininsa Rabe horon yunwa,
Tunda ya fara masifar Laure ke kallonsa cike da mamaki sabida tunda take da moddibo be taba Ɗaga mata murya ba balle Har yayi mata faɗa Irin haka, Ashe Dama haka moddibo yake?? Tabbas ta yarda ransa ya Ɓacci sosai shiyasa bata Tanka masa ba tunda ya fara fadan, idan Har tace zatayi magana tofa tabbas Zasuyi ɓatacciya donta lura komai ze Iya faruwa Wanda kuma ba lallai yay mata dadi ba,

Yana gama zazzaga mata Faɗan ja juya yay gaba ya barta da fargabar Faɗansa,
Yana Fita Ɗakinsa ya nufa da sallama ya shiga Ya zauna yay shiru yana kallonta, har ya fita ya dawo Rabe na zaune a inda ya bar ta Bata tashi ba Har seda ta shanye Furar tas sannan ta miƙa masa kwanon tace “Baba gashi na Shanye.

Murmushi Ya ƙirƙiro yayi Mata tareda shafa kanta Yace “Allah yayi Miki albarka Rabe. Tana kallonsa tace “Amin Babana

Hira suka dingayi dashi jefi-jefi tana tayashi tankaɗe maganin dake gabansa har suka gama sannan ta kwashe ta zuba masa a cikin Boronsa ((jaka)) dayake zuba magungunan a ciki, sun jima tana yi masa shirmen hirarta har ya gaji yace taje tayi bacci Dare yayi, nanfa Rabe ta Tubure ita fir Bazata tafi Ba seya rakata Har ɗakinta, haka kuwa akayi har Ɗakin ta moddibo ya Rakata Be fito ba har seda ta fara bacci sannan ya tofa mata addu’o’i sannan yay Fita ya Rufe mata ƙofar ɗakin da ƙofar karan dake gefe.

Wshe gari da zanyi safiya Rabe ta fito cikin shirinta na tafiya kiwo, sanye take Kayan farin Saƙi irin nasu na fulanin asali Ƙafarta sanye cikin rufaffen takalmi na roba Yalo shar dashi,
Ɗakin moddibo ta nufa da sallama sannan ta shiga ta zauna Daga Ɗan nesa dashi Kaɗan yana Karin kumallo,

da fara’a ya dubeta yace ” Matso kusa dani mana Rabi’atou na. Cike da fara’a ta qarasa jikn Baban nata cike da soyayya ta faɗa jikin sa Tana murmushi,
Tare sukayi Karin kumallon Safen dashi bayan sun gama ne suka fito tare Da ita Yana riƙe da hannunta A waje sukaci karo da Laure tana ƙoƙarin sauke ruwan zafin dake kan murhu. Hade rai Tayi kamar taga mutuwar ta Sannan ta ɗauke kai daga barin kallonsu,
A dan tsorace Rabe ta gaisheta, seda ta faki idon moddibo sannan ta watsawa Rabe wani ɗan iskan kallo Wanda hakan yasa da sauri Rabe ta koma bayan moddibo ta Ƙanƙameshi.

bece komai ba ya kama hannunta suka fice daga Gidan Ko waiwayen laure beyi ba
Suna fita garken Shanu suka nufa dan su fita kiwo,
A nitse ta kalli Moddibbo tace “Baba yau ni kaɗai zani kiwo Base mun tafi tare ba kaga se mu raba shanun Gida biyu Keman, kai kayi hanyar gabas nikuma nabi yamma idan muka dawo se’a ga Shanun waye sukafi Ƙoshi Idan mun dawo ?

Cike da kulawa yace mata to muje sena raba mana, da sauri take binsa cike da zumudin zata kiwo ita kaɗai,
Basu wani ɓata lokaci ba ya raba Musu shanun gida biyu ya Tisa nasa yay gaba itama tayi gaba Da nata, seda yay mata kashedin ta kula da kanta sosai kuma kada tayi nisa sosai Kuma banda bin titi sbda ya tsani bin titi A rayuwarda tunda ya rasa Ƙaninsa Zakhariya.

Tafiya take Hankalinta a kwance kallo ɗaya zakayi mata ka Fahimci tana cikin farin ciki mara misaltuwa, Yawo sukaitayi a Dajin Suna karaɗe ko ina, Har suka shafe kimanin Awanni a cikin Dajin seda suka Ɗauki lokaci Me tsayi sannan Rabe ta lura Da lokacin zuwa makarantar ta Yayi,
Dole Yasa ta kora shanun suka kama hanyar gida Badan Ranta yaso ba.

koda ta dawo seta fahimci babanta be dawo ba, Saɓanin kullum Lokacin daya saba dawowar, tambaya ɗayace keyi mata yawo a kwanyar kanta shine “meyasa Har yanzu Babanta be dawo Gida ba??

Ɓangaren moddibo kuwa Tafiya kawai yake tareda shanun Amma sam hankalinsa naga ɗiyarsa wadda ya tura daji da shanu batareda ya haɗata da kowa ba, addu’a kawai yakeyi Allah ya tsare mas ita da ikonsa, daidai kan kwanar daze yanka ya ɗauki hanyar Ya hangi mutum kwance Ƙasan wata ƙatuwar bishiyar Marke, Be kawo komai a ransa na harya ƙaraso jikin bishiyar kasancewar ta gefanta ze Ratsa ya kama hanyar gida Seyayi zaton ko hutawa Mutumin keyi sabida hali na tafiya amma daya Ƙaraso seyaga sabanin tinanin sa,
Yaro ne matashi sanye Cikin wata Dakakkiyar shadda light blue an masa dinkin Muhammed se faman yararin tsada da kyau takeyi kansa babu hula An Kafta masa wani Ƙaton Sara Daga gefan kansa ta hagu, hakama Ƙirjin sa da kuma bayan sa, gefan cikinsa kuma Alamace na sukar wuƙa babu abinda ke zuba a jikinsa se
jini.

dik da saran dake jikin sa hakan baze hanaka fahimtar kyau Da tsarin Halitta irin na matashin ba, cikin sauri moddibo ya Ƙarasa kusa dashi ya dago shi Lokaci guda kuma ya ɗora yatsunsa a saitin Wuyansa dedai babbar jijiyar dake kai saƙo zuwa ƙwaƙwalwa a nan ne ya fahimci Da sauran numfashi A taredashi, sabida tsabar Rikicewa yama rasa ta Inda ze fara bashi taimakon gaggawar,, (Emergency treatment )
Can wata dabara ta faɗo masa, nan da nan Moddibo ya Ɗaga matashin da ƙarfin tsiya Ya Dorashi a bayan Ɗaya daga cikin shanun ya Ɗaure shi Tamau a jikinta ta yanda baze faɗi ba Sannan ya nufi hanyar gida,
Sun jima Suna tafiya sannan suka Ƙara so gida.

a Ƙofar gida suka hadu da Wadda tun dawowarta taƙi yarda ta shiga gidan ta kafa ta tsare A waje tana jiran dawowar Modibbo,

Da sauri moddibo yace ta shiga da shanun cikin garke Ta ɗauresu ba tare da ta kula da mutumin dake ɗaure a bayan saniyar ba tayi gaba, da Ƙar moddibo ya kwanto shi daga jinkin saniyar Yayi hanyar dakinsa dashi, suna shiga ya kwantar dashi akan tabar marsa Sannan ya mike ya Ɗakko Boronsa dayake sa magani A ciki ya ajiye Ta daga gefe Sannan ya Ɗakko wata Ƙarya ya ajiye Wadda ke ɗauke da Ƙaho da kuma Aska a ciki se wani garin magani da kuma wasu manyam ganye masu kimanin girman tafin hannu duk a cikin ƙwaryar.

take moddibo ya Ya ɗauki wannan Askar ya shiga yanka rigar dake jikin matashin “Subahanallah Shine kawai abinda Moddibo Ya iya firtawa Kenan sabida yanda yaga jini ya taru a gefan Ƙirjinsa Da kuma irin saran Rashin Imanin da akayi masa, da alama seda aka dake shi sannan aka sareshi Wanda hakan ya bashi tabbacin Kashe matashin ake ƙoƙarin yi,
A nitse ya dauki Askar ya daidaici gurin da Ɓakin jinin ya taru sannan ya yanka nan da nan Mataccen jini Daya taru a gurin ya fara fita, a hankali ya shiga goge mai Jinin har seda ya gama gaba Ɗaya sannan ya shiga samai magani a jikin raunukan Dake jikinsa.

bayan ya gama sa masa maganin ne ya fito yana kwaɗama Laure kira, jikinta na rawa ta Ƙaraso tace ” gani mlm Lafiya dai ko?

Be kulata ba Yace ” maza ki kawo min ruwan zafi Yanzu-yanxu jiki na rawa ta tashi ta hada wuta ta Dora Masa ruwan zafin……

Leave a Comment