*_❤🔥BABU SO….!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_01_*
*_MALAYSIA (SABAH)_*
……….A hankali sautin kukan ke tashi tamkar mai rairashi da gayya. Sai dai daga jin yanda salonsa ke fita kasan tsabar daɗewar da maiyin nasa ya ɗauka yana yine ya kaisa ga galabaita. Kasa jurewa nai na kutsa kaina cikin gidan madai-daici da ke ɗauke da dukkan kayan more rayuwa najin daɗi. Falo ne babba masha ALLAH, sai dai duk girmansa banci karo da kowa a cikinsa ba. Shiru nai alamar tunani, (to ta ina kenan sautin kukan da yaja hankalina ke fita?) rashin mai bani amsa ya sani fara waige-waige a falon. Tabbas ba’a nan ɗin bane, hakan ya sani kutsa kaina dan zuciyata ta banni tabbacin a window da naji kukan ɗakine.
Takun sakkowa da stairs ɗin da’aka kawata adon falon da shi ya sani maida hankali can. Hamshaƙiyar mace kamila mai yanayi da fulanin ƙasar Nigeria ce ke taku cike da nutsuwa da kamala tamkar yanda shigarta ta kamala ta ƙawata mutuncinta ga mai kallo. Sam banyi zaton ko (zo na kasheki) ta sani da yaren hausa ba, amma a mamakina saina tsinkayi kamilar muryarta na ƙwala kiran sunan *_Anam!_* a ɗan kausashe. Ƙara kausasa muryarta tayi ganin babu alamar wadda take buƙatar ganin data kira da suna Anam ɗin ta fito.
“Anam! Idan har kika bari na shigo inda kike ki tabbatar sai jikinki yayi tsami kafin kibar ƙasar nan. Shashasha kawai wadda bata kishin kanta. To banda mara kishin kai wake ƙin tushensa? Ba kukan hawayeba kiyi na jini ma babu fashi zuwa Nigeria ki zauna agareki, k idan ma kika ƙuleni ALLAH kin koma can da zama kenan keda ƙasar nan sai yawo”
Sautin kukan da aka sake fashewa da shi ya sani waigawa da sauri, ƙyaƙyƙyawar budurwa black beauty mai ɗaukar hankali da sam bata kama da matar a yanayin jiki sai na kamannin jini kaɗan. A ƙiyasi na yanayin jiki kai tsaye zance bata wuce shekaru sha bakwai ba. Sai dai a mizanin hankali da sanin masu irin yanayin jikinsu wajen ɓoye shekaru zan iya karyata zuciyata. Amma kai tsaye ban san shekara nawa zan bata ba. Dan sam bata da wani tsaho, tana nan dai ƴar cif-cif ga karamin jiki ga rashin tsayi kamar wata ƴar kanwata can (😂🤣ban dai faɗi suna ba ato😜). Tabbas kyaƙyawa ce, dan duk da kukan da idanunta suka nuna alamun taci hakan bai hana bayyanarsu dara-dara ba duk da suna a cikin farin siririn gilashi. Ga gashin gira da dogon hancinta (kamar na bilyn Abdull🙄 saura wani yace ba haka ba, bansan jealous😒😜). Kai atakaice dai yarinyar masha ALLAH. Sosai hawaye ke cigaba da bin kumatun ta tamkar an bude fanfo. Matar daketa masifar ta sake zuba mata harara a kausashe tace,
“Haɗiye min kukan nan kafin nazo na sassafa ki a wajen sakarar banza”.
Da ƙyar ta shiga ƙoƙarin haɗiye kukan nata. Sai dai hawayen sunƙi riƙuwa. Cikin rawar murya ta dubi kamilar matar da take kamani da ita a ɗan fisge, “Mamie na tuba ALLAH na daina duk abinda baƙwaso ke da Abie ”.
“Dainawar taki ko cigaba bazai miki amfanin komaiba ai, dan zuwa Nigeria dai babu fashi tunda kin san abu mai muhimmanci ne zai kaiki. Dolene kije kiyi saves ɗinki a ƙasar haihuwarki kodan gaba zai miki amfani, dan nan ɗin da kika ɗauka ƙasar uwa da uba ta aro ce lokaci kaɗan ya rage mu barta muma ta ishemu”.
Kuka ta sake fashewa da shi tana daddaga ƙafa. “Ni wlhy bana son Nigeria, zafi, sauro ga shegen hayaniya. Ni basai nayi saves ɗin ba dan bazan taɓa rayuwar Nigeria ba balle har na damu dayin aiki saves yaymin amfani. Please Mamie….”
Cikin katseta Mamie taja wani tsaki. Kota kanta batabi ba ta nufi wata ƙofa a fusace tana faɗin, “Ki wuce driver ya kaiki wajen gyaran jiki dan Abie ɗinki yace da wuri zaku wuce, kin san kuma baya son wasa da lokaci”.
Kuka ta sake barkewa da shi kai kace Abie ko Mamie ɗinne aka aiko mata sun mutu. Harga ALLAH bata son zuwa Nigeria dan tana matuƙar wahala da yanayin zafinsu. Ga shegen sauro ɗinnan na kano tamakar kasuwancinsa sukeyi. Uwa uba zaman gidan Uncles ɗinta data tsana saboda mugun halin matar Daddy, na matar ma bai cika damunta ba dan sai ka shiga sabgarta take takuraka. Tafi tsanar babban ɗansa mai shegen baƙin hali da mugunta da har ya zarta uwar tasa. Sam bata ko ƙaunar ganinsa dan basa haɗa ko hanya bare shan inuwa guda, shiyyasa a mafi yawan lokaci idan taji zai zo malaysia take guduwa wajen Aunti Mimi. Da ance kuma zai je wajen aunty Mimi ɗin itama dake aure anan ƙasar malaysia ɗin sai ta gudo ta dawo sabah. Har ya gama zamansa bata yarda su haɗu. Kai itafa a kaf rayuwarta ma bai fi sau uku ta taba ganinsa ba. Tun kuma a ganin farko taji ta tsanesa saboda tsawa da yay mata dan ta fasa glass cup a mistake a gidansu, ita kuma ta murguɗa masa baki yako kama lips ɗin ya murje har sai da sukai kumburi duk da shekarunta basu wuci goma ba a lokacin ta kasa mantawa ta kuma kasa daina jin haushinsa. Hakama haɗuwarsu ta biyu sai da yay mata mugunta, kai idan bata mantaba ma dukansu yay ita da Aysha ƙanwarsa saboda sunje wajen bikin birthday na ƙawar Ayshan ba’a sani ba. Aiko dukan nan ya shigeta dan harda zazzaɓi kasancewar tunda ta tashi da wayonta da hankalinta ba’a taɓa dukanta ba sai shi mugu………
Ta jima a wajen tana saƙa mai fishsheta kafin ta haura saman stairs. Cikin mintunan da basufi sha biyar ba ta fito sanye cikin wando da riga ta ɗaura jibgegiyar rigar sanyi data kai mata har gwiwa kasancewar lokacinsa ne, duk da veil data naɗo a kanta kamar yanda larabawa keyi hakan bai hanata jan hular rigar da bakinta keda gashi mai laushi har saman kanta ba. side bag dake hanunta ta saƙala cikin wuyanta sai faman tura baki take. Duk da Mamie na zaune a falon tana yanka tufa ko kallonta batai ba….
“Mamie na shirya kuɗin to”.
Batare da Mamien ta tanka mata ba ta tura mata card ɗinta na ciran kuɗi. “Na gode ALLAH ya ƙara buɗi mai albarka”. Ta faɗa tana kama hanun Mamie ta sumbata tare da ɗagowa ta sumbaci kumatunta kamar yanda dai larabawa sukanyi. Mamie bata kulata ba, hakan yasa taƙi tafiya idanunta har sun cika da kwalla, dan tunda taga Mamien bata maida mata murtanin sunbar datai mata ba tasan har yanzun tana fushi da ita.
Haka kawai murmushi ya suɓucema Mamie, ta girgiza kanta da kamo hanun tilon ƴar tata da a kullum cikin jimamin ranar da aure zai rabasu take, dan ta tabbatar hakan na gab da faruwa. A ido zaka ɗauka Anam bata da wani shekaru saboda ƙaramin jiki da ALLAH ya bata. Sai dai kuma a zahiri shekarunta ashirin da uku kenan a duniya. Itama sumbatarta tai da ɗanjan kumatunta, hakan yasa Anam yin ƴar dariyar jin daɗi ta rungume Mamien. Mamie tai murmushi.
“To sarkin taɓara tashi kije ko ƙya dawo da wuri”.
“Okay Mamie bye”.
Batafi awa uku da fita ba sai gata ta dawo, ta kara wani irin ƙyau da kwarjini tabbacin taci gyara tako ina. Dan babu abinda fuskarta keyi sai shining da glowing, ga wani uban ƙamshi mai saka nutsuwar mai shaƙa. Fuskarta ƙawace da murmushi ta nufi ƙyaƙyƙyawan dattijon dake tsananin kama da ita dan shima black beauty ɗinne, amma kasancewar akwai jin daɗin rayuwa baka ganin komai tare da shi sai ƙwarjini da ƙyawun haiba. Ga baƙin sajen fuskarsa daya ƙara ƙawata ƙyawun nasa. Shima dai bashi da wani jiki, dan komai na Anam bashi da maraba da nashi, hakan na nufin dai kamaninta ɗaya da mahaifinta.
Zuwa tai ta rungumesa ta gefe tana dariyar farin cikin ganinsa. Shima fuskar tasa da murmushi ya riƙo hanunta cikin nasa. “Uhhm Mamana irin wannan ƙamshi haka kamar amarya”. Fuskarta ta ɓoye a kafaɗarsa tana dariya. “Nidai Abie ba wani amarya”. Dariya kawai yayi baice komai ba. A haka Mamie ta fito daga kitchen ta samesu. Fuskarta ɗauke da murmushi take kallon mijin nata abin sonta da ƴar tasu tilo ɗaya a duniya. Anam ta zame veil ɗin kanta tana nunama iyayen nata kanta daya sha gyara masha ALLAH, sai sheƙi yake da ƙamshi gashi da tsaho sosai. Gaba ɗaya kamaninta irin na Abie, gashin kai da gira zuwa gashi ido ne kawai irin na Mamie, sai ko maganarsu dake kama itama.
Sosai suka shiga yaba ƙyawun da gyaran nata yayi, cikin tsokana Abie ke faɗin, “Mamana kin zama kamar wata amarya da gaske, kodai kawai idan munje na aurar dake ma?”.
Idanu tai mugun zarowa, sai kuma ta kwaɓe fuska har hawaye na cikon mata ido. Lips ɗinta sai rawa suke tama rasa mizatace. Dariya Mamie da Abie suka shiga yimata, hakan yasata tashi da gudu ta haura sama. “Kin gani kin kunnata”.
“Na kunnata ko ka kunna abarka”.
Cewar Mamie tana murmushi. “To aini abin na damuna, idan na tuna wataran aure zatai ta barmu hankalina na matuƙar tashi, gashi shekaru sunyi nisa, kamata yay ma data gama saves ɗin nan kawai a wuce wajen Humairah”.
Ajiyar zuciya mai nauyi Mamie ta sauke. Murya a raunane tace, “Hakane ya dace, sai dai kuma a kullum cikin korar samarin take ai taƙi bama kowa dama anan ɗin balle Nigeria. A kullum kallon kanta take a yarinya”.
“To ai yarinyarce, duka yaushe kika haifamin ita. Ni badan auren ya zama doleba dana bar abuta naita kallo kawai”.
Sosai Mamie ke dariya, cikin riƙe baki tace, “Lallai ashe mu iyayenmu basa sammu kenan da aka ɗakko aka baku. Lallai ashe lokacin auren munada kallo kenan dan za’a sha show rabuwar ƴa da uba”.
“A zakusha kam. Dan mijin nan zai sha gargaɗi, shiyyasa nafi son ma ta auri ɗan Nigeria dan ƙasar nan ta isheni haka”.
“To ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi. Ya kawo nagari”.
Da amin Abie ya amsa cikin jimami da damuwar rabuwa da tilon ƴarsa.
*_Washe gari_* kamar yanda Mamie ta faɗa hakance ta kasance. Dan kuwa dai Abie da Anam sun wuce ƙasar haihuwarsu Nigeria. Tasha kukan rabuwa da Mamie duk da tasan bazatai shekaran Mamie bataje ba tunda ita sunce bazata zo ba har saita kammala. A jirgi barci ta dinga ramuwa wanda ta gagara yi a daren jiya saboda alhinin yin nisa da iyayenta datai matuƙar shaƙuwa da su take mu’amula da su tamkar ƙawayenta. Sune abokan shawararta, sune abokan kukanta, sune abokan dariyarta, sune abokan rayuwarta. Bata da kamarsu dan su tafi sani fiye da kowa a duniya.
*_04: 25pm_* jirginsu ya sauka ƙasar Nigeria Aminu kano international airport, a gajiye Anam take matuƙa duk da barcin da tasha, sai faman langarema Abie take, shiko lallaɓa abarsa yake dan yasan yanayinta bata son wahala sam. Abu ƙalilan ke galabaitar da ita tai laushi tiɓis. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali lokacin da suke fitowa idonsa ya sauka akan ƴan uwansa abin ƙaunarsa. Suma da alama idonsa na kansa, dan tuni suka nufosa fuskarsu ɗauke da murmushi. Abie yay azamar nufarsu shima suka rungume juna suna maijin farin cikin haɗuwa.
Sosai Anam take dubansu da murmushi, tana ƙaunar uncles ɗin ta kam, dan suma suna ƙaunarta. Matar big Uncle ɗin nata da ɗansa babba ne dai sai a slow, amma sauran matan small Uncle da yaransu duk bata da matsala da su musamman Aysha aminiya.
“Oh my Mah-mah welcome”. Uncle ɗin da suke kira da Daddy ya faɗa lokacin da suke sakin juna da Abie ya buɗe mata hannayensa alamar tazo garesa. Hanun trolley ɗinta ta sake da nufarsa a kasalance fuskarta ɗauke da murmushi ta matsa ya ɗan rungumeta ta gefe.
Small Uncle ɗinta da suke kira da Abbah yay murmushi tare da shafa kanta yana faɗin, “Ayya Mamana kina nan dai a ƴar ficikar ki ba tsaho ba girman jiki ga ragwantaka”. Fuskarta ta ɓoye jikin Daddy tana dariya da faɗin, “Lah Abbah na ƙara girma fa, kuma yanzu bana ragwanci”.
Daga Daddy har Abba da Abie dariya sukeyi, Daddy yace, “Nima dai ban gani ba, jibeki a galabaice a ƴar wannan tafiyar ta awoyi, shekara huɗu kenan ban ganki ba amma kina nan yanda kike fa”.
Sosai ta shagwabe masa ƙyaƙyƙyawar black beauty face ɗinta tana ƙyafta idanunta manya ta cikin glass ɗin da alamu suka nuna na ƙarin gani ne.
Ko amota ma Abie da Daddy da abbah dake a baya zaune tuni sun balle hira, itako kallon hanya kawai take dan tana gaba a gefen driver. Jikinta liƙis yake da gajiya, ga wani irin zafi dake shigar ƙofofin gashinta kamar ta fasa kuka dan bata ƙaunar zafi, shiyyasa duk sanda zasu zo Nigeria sai tai kuka bana wasa ba, idan sunzo kuma sam zaka sameta babu sakewa inhar lokacin zafi ne. Shiyyasa mafi yawan lokuta Abie yafi son shirya musu zuwa Nigeria a lokacin sanyi ko damuna saboda ita.
Sun sami tarba ta mutuntawa daga matan gidan guda biyu, wato aunty amarya da mom. Amma babu Big mom balle alamarta. Hakan ba sabon abu bane, shiyyasa daga Abie har Daddy da Abbah basu nuna sun damu ba. Yaran gidan dai duk sun wuce islamiyya, sai ma’aikatan ne keta shigowa suna mika gaisuwarsu domin duk wanda ya kwana ya tashi a gidan yasan muhimmancin Abie ga Daddy da abbah dama jama’ar gidan gaba ɗaya. Sai da suka kwashe kusan mintuna arba’in sannan Mommy ta shigo tana wani ciccin magani. Babu wanda yabi takanta harta samu waje ta zauna tana gaida Abie. Cikin sakin fuska ya amsa mata tamkar sauran ƴan uwanta, ya kuma tambayeta yara.
Duk wannan bidiri Anam na kwance a kujera lamo tana kallon kowa a galabaice, dan ma ta samu sauƙin zafin tunda suka shigo sanyin ac’n falon Daddy na ratsata. Gaishe da Mommy tayi itama a ɗan shagwaɓe, bata wani amsa mata da ƙyau ba. Sai taji duk babu daɗi har fuskarta ta nuna hakan dan ita yarinyace mai son kulawa. Hakan yasa Mom tai murmushi da shafa kanta cike da kulawa take faɗin, “Mamanmu har yanzu dai ke raguwa ce”.
A langabe Anam take dubanta har idanunta na nuna alamar tara kwalla. Murya a raunane tace, “Mom na gajine ga zafi”.
Dariya duk aka sanya a falon, aunty amarya cikin dariya tace, “Babbar magana. A haka za’ai saves ɗin kuma…..?”.
“Kema dai ƙya faɗa Hafsatu. Dan wannan ƴar taku ragwantarta harta wuce tunani, ina tausayama mijin da zaku mannawa”.
Mom da aunty Amarya suka shiga kare Anam da faɗin koma waye zasu iya dashi ai. Mommy kam sai faman taɓe baki take da yatsine fuska tamkar bata a falon ma….
A duk sanda suke a ƙasar gidansu dake jikin nasu Daddy ne masaukinsu, wannan karon kuma babu Mamie sai Daddy yace bai yarda su sauka anan ba duk da Abie ya nuna shi dai zai shiga can ɗin dan bazai so takura iyalan ƴan uwan nasa ba duk da kanine shi a garessu. Babu yanda su Daddy suka iya suka haƙura kawai suka barsa akan zuwa anjima sai ya shiga can ɗin yanzu masu aiki zasuje su gyara. Hakan kuwa akayi, masu aiki sukaje suka tsaftace ko’ina da taimakon aunty Amarya, ita kuma ta koma sashen Mom ɗin kodan kawarta Aysha da basu san da zuwanta ba dan su Daddy sun ɓoyema kowa. Duk da jin zafinta bata wanka da ruwan sanyi, dan haka ta haɗa mai zafi sosai tai wankan a bedroom ɗin Mom kafin su Aysha su dawo islamiyya, tana fitowa kobi takan abincin da Mom ta ajiye mata bataiba ta ƙure ac ta kwanta sai barci. Yin barcin nata babu jimawa sai ga yaran gidan an dawo dasu daga islamiyya cikin katuwar bus ɗinsu ta zuwa makaranta. Kowannensu sashen uwarsa ya nufa, mazan kuma suka nufi sashensu na samari duk da kuwa babu wanda ya haura ashirin a cikinsu.
Basu san da zuwan Anam gidan ba sai bayan sallar magrib, samarin suka fara cin karo da Abie a massallaci, ana idar da sallar isha’i sai gasu da gudu sashen Mom. Sune suka fargar da ƴammtan gidan, aiko cikin ƙanƙanin lokaci suka hargitse ɗakin Mom da hayaniyarsu wadda ta tashi Anam ɗin dake tsaka da jin daɗin barci dan bata salla tana fashi. Tsawa Mom ta musu dan tana salla amma suke ihun nan, tsitt bedroom ɗin yayi suna sauraren faɗan da take musu na wannan shirmen nasu. Sai da ta gama suka bata haƙuri tare da janye ra’ayin ƴar uwarsu suka bar ɗakin.
Kai kawai ta ɗan girgiza fuskarta da murmushi, dolene yanda suke murna da ganin ƴar uwar tasu ya birgeka. Ita kaɗaice ware a cikinsu amma suna nuna mata tsananin so kamar yanda suma kawunansu yake haɗe duk da dai wataran Mommy kan birkita kan yaran idan tanajin fitinarta, musamman idan ta takalesu basu kulataba sai tabi duk hanyar son zuciya ta cusama yaranta ƙananun magana a zuciya da zakaga sun janye jikinsu da ƴan uwansu har wataran ma kaga an taɓah faɗa, a wasu lokutan faɗan nasu nayin nauyi, amma wani sa’in sukan fahimci juna da wuri musamman idan wanda suke shakka a gidan yana ƙasar dan shi babu ruwansa ubansu yakeci gwargwadon iko. Duk da mutum ne shi mai haƙuri da rashin son yawan magana, sam baya son raini da damuwa. Sannan duk da halin uwarsa bazaka taɓa ganinsa ya nuna banbanci akan yaran gidan ba, matan kuma yana girmama kowa yanda ya kamata duk ɗa nagari yayi……..✍
KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.
DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL
IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)
BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)
KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
HAFSAT UMAR KABIR
ZENITH BANK
2270637070
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
07040727902
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09134848107
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
[10/16, 7:26 AM] Mariyamah: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO….!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_04_*
……….Kallon juna sukai cikin ido, tai saurin janye nata saboda wani irin harbawa da ƙirjinta yayi……
“Please Beauty ko details ɗinki ki bani mana”. Saurayin ya faɗa a marairaice. Ai kafimma ta bashi amsa mai gayya mai aiki ya fisgi motar da ƙarfi. Da sauri saurayin ya saki murfin yana mai yin tsalle gefe dan saura kaɗan ya takashi. Sosai yanzu kam Anam ta firgita, dan har hannunsa ta riƙo batare data sani ba. Tureta yay a jikinsa tare da mika hannu ya rufo ƙofar gefen da take ɗin. Sai kawai ta fashe masa da kuka tana kiran sunan Mamie da Abie. Bai nuna yama san tanaiba, saima hankalinsa daya maida ga motar dake bin bayansu, sai da suka hau titi sosai hasken solar ya bashi damar ganin fuskar guy ɗin da suka baro ne. Lip ɗinsa ya ciza da ƙarfi yana wani fici-fici da idanunsa, sai ya koma tafiya a slow-slow harya zam saurayin ya ɗan gota su. Gefen titi ya gangara, sai da yaga saurayin na ƙoƙarin dai-daita nasa gudun danya sauka gefe titi shima saboda ganin sun tsaya sai kawai yay warming motar da wani irin karsashi ya sake harbata saman titi tamkar shikaɗaine a kansa. Tabbas da ace akwai ƙasa babu abinda zai hanashi bulama saurayin ita.
Wani irin duka saurayin ya kaima steering ɗin a ƙulle da kufcewar damar daya samu. Ya kife kansa yana furzar da huci mai zafin gaske, dan harga ALLAH yarinyar ta matuƙar tafiya da dukkan imaninsa.
Kamar yanda ya fita a fusace haka ya dawo a fusace, ko parking bai gama daidaitawaba da ƙyau ta ɓalle murfin motar ta fice da sauri. Wani irin mugun kallo yabi bayanta da shi, sai kuma ya janye yanayin ƙwafa ya kashe motar ya fito. Zaune ya sameta kusa da Abbah tana zuba surutu, dan har yanzu suna a falon suna hira. Sosai takaici ya riƙe masa maƙoshi, ya harareta yana ɗauke kai da zube ledojin hanunsa gabanta. Fuskarta ɗauke da murmushi kamar ba itace ta gama kuka a hanyaba yanzu tace, “Jazakallahu khairan Yaya Shareff”. Ta ƙare maganar da masa gwalo yanda su Abba basu luraba sai shi.
Yi yay tamkar baima gantaba duk da tsaurin idonta na bashi mamaki, sosai ƙanensa ke shakkarsa a gidan, amma sam babu irin wannan tsoron da yake gani a idon ƙanensa tattare da ita. Kai tsaye take abunta garesa, abunda ya fuskanta dukane kawai bata so, dan tun dukan da ya taɓa mata ita da Aysha ta shiga hankalinta a lokacin har tana wasan ɓuya da shi. Sallama yayma su Abie dake saka masa albarka ya fita fuskarsa ɗauke da murmushin daya saka Anam sakin baki tana kallonsa da mamaki. Dan inba Abie ɗin ba da wahala kaga murmushi a fuskarsa, kullum fuska a ɗaure kamar ɗan raka gawa….
Washe gari da ƙyar Aysha ta iya tashinta danta shirya. Haka tai wanka tanata mitar ita barci bai ishetaba. Shiri tai cikin wando da riga, sai dai anan babu maganar fita a haka duk da zafi da ranar da akeyi a Nigeria, dole ta ɗaura abaya, Sosai tayi ƙyau kamar ka saceta ka gudu. ɓata fuska taketa faman yi dan bada son ranta tasa abayar ba, sai dai yanda Mamie ta gargaɗeta ta dingayi tunda tasan kayan nata duk ba irin na sawar Nigeria ba ne. Shiyyasa ta zubo mata abayoyi kusan goma tanata mita bata kulata ba. Kasancewar akwai sanyin safiya sai bata damu da saka abayar ba sosai.
Sashen Mommy suka nufa ita da Aysha, sai dai daka kalleta kasan ba’a san ranta bane. To amma kodan Aysha da kunya tace bazataje ba. Mai aiki kawai suka samu a falon tanata aikin gyarawa, suka gaisa Anam na amsasu cike da fara’a, dan haka kawai ita dai Ladi ke birgeta. Bedroom ɗin Mommy suka nufa daga nan, bayan sallama aka basu iznin shiga. Zaune suka sameta a kujerar mirror tana murza ɗauri, ganin aysha ta rissina tana gaisheta itama saita ɗan rissina batare data yarda sun haɗa ido ba. Bata amsa na Anam ɗin ba, sai Aysha data watsama harara… “A ina kika kwana?”.
“A sashen Mom ne”.
Aysha ta bata amsa cikin ɗari-ɗari dan tasan faɗa zata sha. Aiko kamar jira Mom ta rufeta da faɗa, ta inda take shiga batanan take fitaba. Itadai Aysha haƙuri kawai take bata. A tsawace tace. “Ɓacemin da gani shashasha da bata san ciwon kanta ba”.. Kafinma aysha tai yunƙurin fitowa tuni Anam tai waje ranta fal ƙarin mamakin masifar Mommy ɗin…
Da sauri tai baya jin suna neman yin karo da mutum. Ta tura baki gaba tare da ɗan matsawa gefe saboda hararar da yake watsa mata. Yana ƙoƙarin raɓata da nufin wucewarsa tai tunanin bugeta zaiyi, kamar ƙiftawar ido yaga ta zura da gudu ta fice. Idanunsa ya ɗan lumshe tare da girgiza kansa kawai. Anan ɗin ma yana ƙoƙarin shiga ɗakin Mommy Aysha ta fito tana sharar hawaye, rissinawa tai ta gaishesa, maimakon amsa mata sai ya jeho mata tambaya idonsa kafe a kanta, “Mike damunki?”.
Kanta ta girgiza masa. “Ba komai Yaya Mom ce, dan naje sashen Mom na kwana shine taketa faman faɗa, ni kuma saboda naga Anam ne tunda nasan idan mukazo nan bazata barta ta kwana ba”. Shiru yay yana cigaba da kallonta kawai, batare da yace komaiba kuma sai ya raɓata ya wuce ɗakin Mommy ɗin.
Anam kam sai da ta tabbatar tabar sashen sannan ta ƙara kumbura baki, sashen Gwaggo ma da tun jiya batako kallaba sai da Abie ya korata sannan ta tafi fuska a haɗe kamar zatai kuka. Bata son kakar tasu dan itama tasan ba sonta take ba. Koda ta shigo sashen tsohuwar a ciccije take. Tamkar bama tasan Anam ɗin ba take kallonta, hakan yasa itama Anam ɗin tsumewa tai kamar bama wajenta tazo ba. Cikin ƙunar rai Gwaggo ta ture ƙaton kofin shayin da take sha gefe tana kallon Anam cike da tsana,
“Fitsararriya cokalin banza. K ko kunyar kanki bakijiba sai yau kike zuwa gaisheni? Da yake baki da mutunci. to in bakizoba k ai ubanki shi yazo dan uwarki”.
Shiru tai taƙi cewa komai, hakan sai ya sake tunzura Gwaggo ta fara bala’i ta inda take shiga bata nan take fita ba. Ko motsi Anam bataiba ballema tai mata gaisuwar da akace tazo tayi, sai da ta tabbatar mintunan da Abie bazai zargi komai ba sun cika sannan ta gaida Gwaggo dake yayyafa ruwan bala’i da zage mata iyaye tai ficewarta batare da ta jira amsa ba. Biyota Gwaggo tayi tana ƙwala mata kira.
“Zuwairah!! Zuwairah!! yanzu nan ni kikema wannan ɗibar albarkan? To ko ubanki ai bai isaba, ke ko kakarki ma data haifi uban naki balle ke yarin….”
“Ki cinye kanki fitinanniyar tsohuwa”. Anam ta faɗa a hankali tana ƙara sauri dan ko muryarta bata buƙatar ji. Taji daɗin samun Abie harya shiga mota, dan haka ta buɗe wuf ta shige duk da bataji daɗin yin tafiyar da wanda ta gani zai jasu ba. Sai da suka fita a gidan gaba ɗaya Abie daya lura bata gaida Shareff ɗin ba ya dubeta ta mirror…..
“Anam!”.
“Na’am Abie ”.
“Kin gaida Yayanki kuwa?”.
Ido suka haɗa da shi ta mirror, ita ta fara ɗauke nata idon ganin kallon banzar daya jefa mata. “Abie na gaishesa tun ɗazun ma ai da muka haɗu a sashen Mommy”. Idanunsa da basu gama bajewar kumburin barci ba ya sake ɗagowa ya dubeta. Itako ta ɗauke kanta cike da basarwa. Abie kam daya yarda sai kawai yay murmushi da maida hankalinsa ga lap-top ɗin dake a cinyarsa yana dubawa, ta Shareff ɗince yake nuna masa ayyukan company duk da dama can komai za’ayi yana sanar masa. Sai dai a kullum cikin ƙara bashi wuƙa da nama yake da nuna masa duk yanda yayi dai-dai ne kawai. Koda suka iso inda zatai daidaita komai daya shafi hidimar ƙasar nata bata yarda tako kalla Ya Shareff ba, shima bai shiga sabgartaba dan koba komai yana jin nauyin Abie sannan shi sam baya wasa da yara dama can, itacema kawai za’ace ta ciri tuta a wajensa tana ƙarama.
Komai da taimakonsa shi da Abie ya kammalu, basu sami nutsuwa ba sai kusan azhar. Maimakon gida sai suka wuce company. Tunda akai
Companyn Anam batazo Nigeria ba, dan haka ta ɗan nutsu a kallon tsarin wajen da yanda ma’aikata keta kaikawo na daidaita kansu tun shigowar motar tasa. Koda suka fitoma sai gaisuwa ake miƙa musu cike da girmamawa da mutuntawa har suka isa katafare kuma haɗaɗɗen office da yaji komai na more rayuwa da saka nutsuwa ga mazaunin cikinta. Abayar jikinta ta shiga ƙoƙarin cirewa. “Wayyo Abie zafi”.
Yanda tai maganar ya sashi ɗan juyowa ya dubeta, ai da sauri ya ɗauke kansa ganin kayan dake a jikinta. Wando ne dayay matuƙar fidda surar jikinta da ƴar riga da itama bata ɓoye komai ba. Sun mata ƙyau sosai kuma dai-dai da halittarta ta masu ƙaramin jiki. Har veil ɗin data naɗa bata bari ba sai da ta yaye, ɗaurarren gashinta da yasha gyara ya bayyana, sai dai tuna gargaɗin Mamie yasata warware veil ɗin duk da ba wani girmane da shiba sosai taɗan yafa tana duban sashen da yake….
“Yaya Shareff Please kasa ac zafi”. Tayi maganar ne tamkar zata fasa kuka, dan da gaske zafine ya taso mata lokaci guda, har wani dimm kanta ke mata. Ta ƙasan ido ya harareta, sai dai baice komaiba ya ɗauka remote ɗin ac dake a desk ɗin office ɗin nasa ya kunna ɗin. Ajiyar zuciya ta sauke cike da jin daɗin jin yanda sanyin ya wani buso mata da faɗin, “Alhmdllhi, Abie ALLAH da kamar ana dafamin fatar jikina fa”.
Ƴar dariya Abie yay yana mai girgiza kansa da kallon Shareff dake ƙoƙarin buɗe wajen da yake gudanar da duk ayyukansa na zane. Babu mai shiga wajen sai shi kaɗai, sai ko Fharhan da Khaleel da yakan bama dama a wasu lokutan su kuma Engineers ne, dan company ɗin nasu aikinsa kenan, mai buƙatar zane amasa, idan da gini duk a haɗa, kai dai kawai ka ajiye kuɗi ne kaga biyan buƙata.
“Babana kaji fa wani shirme, dama zafi na dafa fata ne?”.
Murmushi ya ɗanyi cikin sanyin muryarsa da shafa kansa yace, “Abie akwai zafinne ai”.
“Oh ka goya bayanta kenan dai kawai”.
Murmushi ya sake saki mai faɗi fiye dana ɗazun. Sai dai baice komaiba, saima ɗan hararan Anam data saki baki tana kallonsa ganin murmushi a fuskarsa yayi. Itako ko gezau kallonsa take kamar ta samu hoton bango. Fuska ya ɗan tsuke da ɗauke kansa daga saitinta. Itama sai ta janye tana taɓe baki.
Tare da Abie suka shiga, yayinda gaba ɗaya hankalin Anam ke ga littafin data ɗauka mai tambarin company ɗin nasu da alama samples ɗin ayyukan sune a wajen. Koda taji shigewar tasu bata maida hankali kansu ba, ta jima tana kalle-kalle, wasu su birgeta wasu ta taɓe baki harta fara hamma. Sai kawai ta zame ta kwanta a kujerar………✍
KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.
DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL
IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)
BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)
KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
HAFSAT UMAR KABIR
ZENITH BANK
2270637070
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
07040727902
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09134848107
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!💃🏼💃🏼💃🏼
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*😭🙏🏽
[10/16, 7:26 AM] Mariyamah: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO….!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_02_*
………Alhaji Mustapha Ɗaher wanda akafi sani da (MD Shareff) shine asalin mai gidan. Tsohon soja ne dan kuwa suna sahun farko na sojojin da sukaima ƙasar Nigeria hidima tun a farkon ƙarni. Matansa uku. Uwargida Hannatu bata taɓa haihuwa ba har yanzu da tsufa ya risketa, sai dai ta riƙe ɗan matarsa ta biyu tamkar itace ta haifesa saboda zaman lafiya da sukai baka taɓa cewa kishiyoyine ba. Matarsa ta biyu itace Hajarah haihuwarta huɗu da shi. Muhammad shine babba wanda tun bayan yayensa ya koma hanun Hannatu da suke kira da (Gwaggo). Sai Halimatu itace ta biyu, sai Abubakar, sai auta Umar. Sai kuma amarya Juwairiyya nada biyu. Usman da Maryam. Rayuwar gidan MD Shareff rayuwace bahaguwa, dan kuwa dai Uwargidansa da matarsa ta tsakkiya kansu a haɗe yake, bazaka taɓa ganinsu ka ɗauka kishiyoyi bane. Amma Amaryarsa Juwairiyya a ware take a cikinsu, dan kuwa sam batajin daɗin zama da su sai ma ɗan karen azaba da ta dinga fuskanta daga garesu kasancewarta kurmiya. Juwairiyya nada matuƙar haƙuri da kawaici, duk da wahalar da take sha a hanun kishiyiyinta bata taɓa ko nunawaba a fuska balle ga wani sai dai idanunka ya gane maka. MD Shareff yayi iya bakin ƙoƙarinsa na ganin matansa biyu sun daina gallaza rayuwar amaryarsa amma hakan bai faruba har yabar duniya ya barta da sabuwar gwagwarmayar rayuwa a cikinsu.
Duk da tsana da tsangwama da su Gwaggo kema Juwairiyya da ware ƴaƴanta hakan bai hana yaran gidan tashi da ƙaunar juna ba, sai dai kuma Halimatu ta fita zakka a cikinsu, dan akwai shegen baƙin hali, sam bata yarda Maryam ta raɓeta duk da itace kanwarta mace tilo. Ahaka dai aka gungura har yara suka tasa Juwairiyya bata huta ba, ga shi babu miji, ƴan uwanta kuma sunƙi janta a jiki balle ta koma garesu taji sanyi, wanda ke ɗan tausaya matan yana ƙasar Malaysia yana karatun daya samu tafiya ta hanyar scholarship. Shima yayantane dan shi take bimawa. Haka tacigaba da haƙuri har ALLAH ya kawo Yayanta ƙasar Nigeria ganin gida tare da matar da yake aure wadda ya aura acan ƙasar Malaysia ɗin, amma ƴar Nigeria ce karatu take a hanun yayanta acan. Kowa ya nuna ƙin matar tasa itako ta nuna soyayyarta gareta dan bataga aibunta ba tunda musulma ce. Daɗin abinda tayi yasa Yayan nata da matarsa shiga suka fita wajen ɗauke mata Usman dake gab da kammala secondary school. Ita kuma ya saya mata gida tabar cikin su Gwaggo.
Wannan abu ya musu matuƙar ciwo, dan ƙiri-ƙiri suka nuna ƙiyayyarsu da kishinsu akan hakan, tare da dagewa wajen cusa tsanar Usman da Maryam a zuciyar sauran ƴaƴansu, ita dai tai musu sallama harda kukan sabon zama ta ɗauka diyarta Maryam da Usman ke kira Mimi suka koma sabon gidansu.
Rayuwa ta shuɗa, komai ya canja yara duk sun girma. Tafiya da Usman yasa Gwaggo da Mama jajircewa wajen ganin su Muhammad sunyi karatu mai zurfi dan kar Usman yafi ƴaƴansu. Sai dai shi UBANGIJI ba’ai masa dole, dan kuwa shike bama wanda yaso a kuma lokacin da yaso. Sun sami nasara sosai ta rayuwa saboda zukatansu cike suke da son ganin ɗan uwansu bai zartasu ba kamar yanda iyayensu kullum ke kwaɗaita musu, dan zuwa yanzu da gaske ƙiyayyar Usaman da nuna masa ƴan ubanci tai tasiri a zukatansu saboda huɗubar mahaifiyarsu da abokiyar zamanta. Sun buge gidansu na gado kasancewar babba ne sosai tare da siyen na maƙwafta dake son tashi suka ware ma Usman da Maryam nasu gefe su suka gina nasu a tare su huɗu tare da kason ƴar uwarsu Halima da tuni tayi aure, koda Usman yazo Nigeria yaga ɗan abinda aka rage musu baice komaiba, saima ƙoƙarin ganin ya samu kusanci da shaƙuwa da ƴan uwansa yake kamar da. Hakan bata samu ba, dan babu abinda suke masa sai ɗagawa da fariyyar sunada kuɗi yanzu, koda aka kaisa turai bai fisu da komai ba. Murmushi kawai yayi, dan al-amarin nasu yanzu dariya kawai yake bashi. Watansa kusan uku a Nigeria ya tattara mahaifiyarsa da ƙanwarsa Mimi suka wuce Malaysia, wannan ma ya sake ɗaga hankalin su Gwaggo, suka cigaba da tunzura su Muhammad.
Tsahon shekara huɗu bai sake waiwayarsu ba sai da aurensa da ɗiyar kawunsa tilo da suka haifa ya tashi, dan kawun nasa da matarsa mai suna Asiya haihuwarsu ɗaya mace Aysha Humaira, shaƙuwar dake tsakanin Usman da Humaira ta ɓaci dan kusan shine yay rainonta, Hakan yasa soyayya mai tsanani shiga tsakaninsu. A Nigeria sukazo akai bikin duk da ƴan uwansa nata masa wulaƙanci, shidai baibi takansu ba sai fatan shiriya yake musu.
Haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa shi da Humaira ALLAH bai basu haihuwa da wuriba har ALLAH yayma mahaifiyarsu Juwairiyya da Asiya rasuwa a ƙasar saudia sunje aikin hajji, mutuwar tasu ta samu asaline dalilin accident daya wanzu a cikin harami a wannan shekarar. Sun shiga tashin hankali sosai, wanda har yay sanadin kawunsa ya samu ciwo shima yabar duniya. Girma ya dawo hanun Usman, dan kuwa ragamar rayuwar ƙannensa biyu ta dawo garesa, wato dai Humaira data zama matarsa da Mimi. A wannan gaɓar ƴan uwansa sun kirashi sun masa gaisuwa, yaji daɗi har cikin ransa.
Bayan ya aurar da Mimi ga wani abokinsa dake anan Malaysia shima dai ɗan Nigeria ne babu jimawa ALLAH yayma Hajara (Mama) mahaifiyar su Muhammad ƴan uwansa rasuwa itama. Har Nigeria yazo tare da matarsa da ƙanwarsa Mimi dake fama da ƙaramin ciki, hakan da yayi sai ya sanyaya jikin ƴan uwan nasa dan kuwa su ko auran Mimi duk da ya basu hakkinsu ƙin zuwa sukai, hakama rasuwar mahaifiyarsa da kawunsa da uwar matarsa a waya kawai sukai masa ta’aziyya. Ya nuna musu hakan ba komai bane su manta kawai.
Ɗan shirin da suka samu a tsakaninsu a wannan karon ya samu damar sanin duk iyalansu, dan kuwa a baya basu taɓa yarda yasan fuskokin matansu ba ma balle adadin ƴaƴansu ba. Muhammad matansa biyu. uwargidansa Wasila ɗiyar ƙanwar gwaggo nada yara huɗu a lokacin, babban shine Al-Mustapha da yaci sunan MD Shareff mahaifinsu suna kiransa da *_Shareff_*. Sai Maheer, Binta, Ishaq da ƙaramin ciki da take kan laulayinsa. Wasila da yara ke kira Mommy a gidan ba wani sanin Usman taiba amma ta mugun tsanarsa saboda huɗubar Gwaggo, ƙinsa take tamkar itace ƴan uban nasa ba mijinta ba. a gefe tana matuƙar jin kishin yana rayuwa a ƙasar waje a ganinta kodai yaya ya fisu nasibin rayuwa. Ta shiga matuƙar takaicin ganin su Muhammad sun fara sakkowa akan ƙin ɗan uwansu da sukeyi, dan haka ta shirya sake haddasa sabuwar ƙiyayya a tsakaninsu kamar yanda Gwaggo ke ɗaurata akan hanya. Sai amaryarsa Ubaida da suke kira (Aunty Amarya) nada ciki tsoho itama haihuwa yau ko gobe, mace ce mai son jama’a da haƙuri, duk da ƙiyayyar iyayen miji da take fuskanta da iskancin kishiya ta zama mai haƙuri da kawaici a gidan. Sai matar Abubakar Mariya da suke kira Mom. Itama mace ce mai dattako da mutunci. Ba wani daɗin iyayen mijin nata takejiba saboda Gwaggo itace ke juya Mama, bata son kowa yay farin ciki a gidan sai ɗiyar ƴar uwarta. Amma haka taita kawaici da shanye haɗata fitinar da aka dingayi da uwar mijin tasu har ALLAH ya rabasu lafiya da ita. Itama dai yaranta biyu duk maza. sai dai tana da ciki ɗan watanni biyar. Umar dai yaƙi aure, hasalima ya zama fanɗararre a cikinsu sai addu’a. Tuni yana kudancin ƙasar sai ya gadama yake waiwayen kano tun daga karatu, su kansu ƴan uwan ba’a komai suke sakashi a lissafinsu ba. Rasuwar ma baizo ba sai bayan kwana bakwai duk da mahaifiyarsu ce. Kamar yanda ƴan uwansa suka gabatar masa iyalansu shima haka ya gabatar da tasa matar a garesu. Ƙyaƙyƙyawar bafulatana mai tarin ilimin zamani dana addini. Ga tarbiyya da mutunta mutane.
Babu laifin zaune babu na tsaye Mommy ta tsinci kanta da tsanar Humairah wanda babu makawa kishine kawai da hassada ke cin ranta, dan kuwa ko ba’a faɗaba Humairah ta fisu komai na rayuwa. Kasa biye ƙiyayyarta tai ta dinga nunata ga Humairah datai kamarma bata fahimta ba, dan mace ce data iya zama da mutane matuƙa, sai dai koda wasa taƙi bada fuskar da Mommy ɗin zata kawo mata raini.
Rasuwar Mama yasaka baƙin halin Gwaggo fitowa muraran gasu Muhammad. Dan kuwa sun fahimci Gwaggo itace ke tunzura mahaifiyarsu aikata wasu abubuwan ashe. Duk da tana nuna itace uwa a garesu kamar da can, a yanzu hakan baya hana ta nuna musu bata haifesu ba ko wani abu makamancin haka. Sannan a kullum burinta taga babu zaman lafiya tsakaninsu da ƴan uwansu biyu kacal da ALLAH ya basu, kai hatta lalacewar Umar sun fahimci Gwaggo nada kamasho dan kuwa dai shi da Muhammad sune ƴan ɗakinta, a yanzu kuma Shareff ma a hanunta yake yaron gaba ɗaya ya tashi a taɓare ga rashin kunya da rashin mutunci. A kullum cikin jibgar ƴaƴan anguwa yake da musu ƙwacen abu idan ya gani gashi baya son karatu sam.
Abubakar da yaran gidan suke kira da Abbah ne ya fara nusar da Yayan nasa Muhammad da suke kira Daddy abinda ke shirin faruwa, yana tsoron su sake samun bara gurbi bayan Umar a zuri’arsu. Sannan koba komai Shareff shine babba a ƴaƴansu lalacewarsa na nufin rugujewar sauran ƙanensa. Sosai Daddy ya fahimci Abbah, suka zauna shawarar matakin da zasu ɗauka akan yaronsu duk da gida ɗaya suke da Gwaggon sashenta daban itama inda suke zaune da Mama kafin rasuwarta. Suna a wannan halin Usman yazo Nigeria domin fara ginin wani fili daya saya, a ganinsa ya ƙyautu ya mallaki muhalli a ƙasar haihuwarsa. Zuwansa ya musu daɗi, dan basu ɓoye masa komai game da halin da Shareff ke neman shiga ba a hanun Gwaggo. Ya jimanta al’amarin tare da sanar musu subar komai a hanunsa shi zai ɗauke Shareff ɗin ya koma hanunsa insha ALLAH. Ba karamin farin ciki sukai ba, tare da ƙara ɗinkewa kamar komai bai faruba a baya. Ginin da yazo da niyyaryi a nesa da su sai suka hana hakan, suka tilastashi zuwa ya gina filin da suka rage masa tare da ƙara masa dana cikin gidansu kasancewar gidan nasu ƙatone sosai kowace mace ma da part ɗinta, ga kuma na Umar ma da babu kowa a ciki tunda yaki zama. Dan da farko ma na Umar ɗin sukace ya ɗauka yaƙi.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka fara ginin daya tada hankalin Gwaggo da Mommy, babu kunya suka tada rigimar basu yarda ba. Su su Daddy ma abin har mamaki ya dinga basu, dan sun rasa dalilin Gwaggo na son nisantasu da ƴan uwansu. Basubi takanta ba, dan a lokacinma ne suka nuna mata bore, a wajen Halima kawai ta samu goyon baya dan ita dama sai a hankalice. Wannan rigima bata kwantaba kuma maganar komawar Shareff hanun Usman ta sake tasowa. Nanma dai ansha ƙaramin yaƙi dan Mommy haukane kawai bataiba ɗanta zai koma hanun maƙiyanta. Tsiya ta dinga zazzagama Usman harda masa gorin haihuwa. Shi dai bai kulata ba kamar yanda bai kula Gwaggo da Halima ba. Iyakaci ma idan suna abun nasu sai dai yayi murmushi. A gefe kuma bai fasa shiryama Shareff tafiya ba.
A lokacin da zasu wuce dole sai sace Shareff akai daga gidan batare da sanin Mommy da Gwaggo ba, dama ita Halima tana gidan aurentane zuwa takeyi, itama dai yaranta uku ne a yanzu tana auren ɗan wan gwaggon dan ita ta haɗa….
Humairah da Mimi sunyi farin cikin ganin Shareff, sai dai kuma sam babu cikkakkiyar tarbiyya ga yaron. Dan ba ƙaramin wahala da azabarsa suka sha ba duk da kwata-kwata shekararsa tara ne a duniya lokacin. Haka Ruƙayya taita juriyar ganin ta sauya tarbiyyarsa ita da Usman. Basubi takan zagi da walakancin da Mommy ke kira a waya ta musu ba akan su dawo mata da ɗanta idan sunji haushi su haifa nasu. Gorinta na musu ciwo, amma sukaita dannewa tunda sun san domin ALLAH zasuyi ai da ɗan uwansu. Tunda dai sun san bazatazo ta ƙwacesa ba.
A hankali komai ya fara daidaita, Shareff ya fara nutsuwa da son karatu, ga kulawa yana samu da soyayya ga iyayen ruƙonsa. Shaƙuwa kuma mai nagarta ta gama shiga tsakaninsu. Bashi da kamar Abie da Mamie yanzu a duniya sai aunty Mimi da akoda yaushe yakanje gidanta kodan yaronta data haifa Su’ad. Shareff nada shekara biyar a wajensu ALLAH ya bama Mamie ciki. Zokaga murna da farin ciki wajensu, yayinda Mommy ta shiga baƙin ciki dan taso ace sun ƙare rayuwarsu ne babu haihuwa. Kuma har yanzu tana kan caccakarsu akan su maido mata ɗanta. Sudai basa kulata, dan ko ƙasar zasuzo basa zuwa da shi ma.
Mamie tasha rainon ciki har ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo ƴarta mace. Mommy da Gwaggo sun ɗanji sassauci dan a ganinsu darajar mace bata kai ta namiji ba. Dan haka suka shiga shigi da fici gidan malamai kai harma da bokaye akan wai a tsaida haihuwar Humairah. Humm abin dariya, dama basu wahal da kansu ba dan iya abinda ALLAH ya rubuto a ƙaddarar bawa shi kaɗaine rabon dazai samu ai dama. Ita dai batama san sunai ba, dan kuwa da ALLAH ta dogara. Su Daddy ne kawai sukaje Malaysia ganin gudan jinin ɗan uwansu, duk da Gwaggo taso binsu ganin ƙwaf sukaƙi. Yarinya taci sunan *_Juwairiyya_*, mahaifiyar su Abie kenan amma suna mata alkunya da *_Anam (Blessings of GOD)._*
Rainon Anam ya dawo kamar a hanun Shareff ne. Bashi da damuwa a yanzu sai ta Anam, daya dawo makaranta tana hanunsa, bacci ne kawai ke rabasu shima sai Mamie tayi jan ido. A haka aka yayeta ta buɗa ido da sanin Shareff matsayin Yayanta kawai. Dan kuwa duk wani gata da kulawarta tamkar ta koma hanunsa ne. Dan hatta wanka da abubuwan da uwa zatayi duk shike mata. A koda yaushe tana maƙale da shi kamar cingam. Hatta da Abie wani lokacin ƙiwa take masa sai shareef. Lokacin da take cika shekara shidda a duniya a lokacin Shareff ya kammala secondary school ɗinsa. Abie yay masa shirin wucewa jami’a a ƙasar Indonesia. Ya shiga damuwar rabuwa da ƴar ƙanwarsa, dan kuka sosai ya dingayi duk da lokacin yanada shekaru sha takwas a duniya dan ya zama ɗan saurayi abinsa. Haka dai babu yanda ya iya ya tattara ya tafi badan yaso ba. Yasha matuƙar wahalar kewar Anam a ƙasar Indonesia, dan da ƙyar ya haƙura ya maida hankali ga karatunsa kodan faranta ran Mamie da Abie ɗinsa. Fara karatun Shareff a ƙasar Indonesia ya ƙara bama Gwaggo da Mommy ƙwarin gwiwar cigaba da shiga da fita domin ganin hankalinsa ya dawo garesu, su kuma nisantashi dasu Mamie. Zuwa lokacin gidan nasu ya ƙara haɓaka da ƴaƴa. ALLAH kuwa ya amsa musu, dan kuwa dai a hankali rayuwar Shareff da hankalinsa suka fara dawowa Nigeria, ko hutu ya samu da yaje Malaysia dake kusa da shi gara ya wuto Nigeria. Takai yakan ma jima bai je inda su Abie suke ba. Sai dai abinka ga ikon UBANGIJI har lokacin soyayyar bayin ALLAHn nan na’a ransa babu abinda ya canja. Kawai dai baya son zuwa inda suke ne batare da yasan dalili ba, sai kuma Anam da sam a yanzu bayama ko san tunata dan babu dalili ya tsani yarinyar. ko Malaysia yaje babu abinda ya damesa da ita, wani lokacin ma kafin ya taho sai ya bugeta. Itako dama tama manta da shi tuni, rashin sakewar da yake da ita yasa basa shan inuwa ɗaya, ko inda yake bata kusanta balle ta nuna tama sanshi, idan kuma tsautsayi ya haɗasu ko hararta yay sai ta rama saboda tsiwarta.
A haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa Shareff ya kammala karatunsa ya zama cikakken *_Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff_*. Maimakon ya nufi Malaysia kodan nuna godiyarsa ga ALLAH ga waɗanda suke tsaye kan ɗawainiyar karatun nasa sai kawai ya nufo Nigeria. Hakan ya matuƙar bata ran su Daddynsa, yayinda Gwaggo da mahaifiyarsa Mommy suka bashi goyon baya da kariya. Sosai ran Daddy ya ɓaci har suka sami saɓani tsakaninsa da Mommy irin wanda basu taɓa samu ba. Ya kuma fito fili ya nunama Gwaggo kuskurenta. Aiko saita zauna ta dinga kuka wai su Daddy sun nuna mata ba itace ta haifesu ba. Shareta sukai, harta haɗa kayanta tabar gidan, ganin abin zaiyi tsamari Mom ta sanarma Mamie, itako ta sanarma Abie. Daga ƙarshe dai Abie ne yazo Nigeria ya kwantar da tarzomar tare da nuna shi bai ɗauka abinda Shareff ɗin yayi da wani ɓacin rai ba, abin birgewama sai yay zaman bashi shawarar mizai hana ya buɗe company kawai basai ya zauna neman aiki ba.
Sosai Shareff yaji kunya, ya dinga bama Abie haƙuri akan shima wani lokacin yana rasa gane kansane akan nisantarsu. Murmushi kawai Abie yay dan ya jima da fahimtar komai akan farraƙa yaron akai da su, bai kuma taɓa yunƙurin nuna ya sani ba tunda yasan dai Mommy akan abinda yake nata take hanƙoro mizaisa ya damu tunda shima ALLAH ya bashi tashi. Shareff bashi da kuɗin buɗe company, amma sai Abie ya bashi shawarar su haɗa gwiwa kawai…..
A haɗin gwaiwar ma Shareff baida ko kwatar kuɗin da zata gina company ɗin, amma sai Abie bai damuba shi ya bada duk kuɗin da ake buƙata aka kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci, ya kuma gargaɗi Shareff akan baya son Gwaggo da Mommy su sani, kawai suci gaba da tafiya akan shine ya gina abunsa. Sai dai sun zauna da lauyoyinsu an ajiye komai a rubuce tare da su Daddy matsayin shaida.
Ginin wannan company yasa Mommy fara hura hanci, a ganinta karan ɗanta yakai tsaiko shima. Har habaici takema su Mom da su Mamie ko kunya babu. Mamie ce kawai tasan gaskiyar lamarin, su Mom kam da aunty amarya suma duk tasu ɗaukar Shareff ɗinne ya gina da kuɗinsa. Gwaggo ma ta ɗau abun da zafi, dan ita taita tunzura Mommy akan su ƙara tashi tsaye su nisanta Shareff da su Abie wai kar wataran Abie yay tunanin haɗa Shareff da Anam aure tunda sunga ya kuɗance har yama fisa arziƙi. Wannan fanfi kuwa yay tasiri ga Mommy, dan tuni suka bazama shige-shige saboda ko’a mafarki bata fatar haɗa zuri’arta dasu Abie a duniya…..
Abubuwa da yawa sun faru bayan wannan, ciki harda karatun Anam da ko Nigeria ɗin ma sai jefi-jefi ake kawota, dan idan har suka zo ta dinga kuka kenan zafi-zafi. Anam yarinyace ƙyaƙyƙyawa black beauty, tana tsananin kama da mahaifinta a komai, sai dai akwai kamannin Mamie tattare da ita ta wasu wajajen. Yarinyace mai ƙiriniya da rashin ji, ga tsiwa. Sam ƴar babu ragice, dan ko cikin yaran da suka girmeta bata bari a cuceta balle sa’aninta, tanada baki sosai. A ɓangaren karatu kuwa sam bata da wani ƙoƙari saboda kasancewar ta yarinya mai son wasa, sai da su Abie suka miƙe kanta sosai sannan ta fara fahimtar karatu. Shekaru na karuwa gareta rauni daga idanunta na sake bayyana, dan takai idan abuna’a nesa da ita bata ganinsa, hakama da daddare idan waje babu haske mai ƙarfi bata ganin abu har saida lalube. Lokacin da su abie suka fahimci wannan matsala hankalinsu ya tashi, sai dai babu ɓata lokaci suka dangana ga likita, ya tabbatar musu idanunta nada raunin gani, amma zai ɗaurata akan magani da gilashi dazai taimaka mata. Wannan shine dalilin kasancewar eyeglasess a idon Anam koda yaushe. Abin mamaki kuma sam basa shan inuwa guda da Yaya Shareff. Hasalima haduwarsu tayi matukar wahala, idan ya fisge yaje Malaysia ma bata barin su haɗu sam, hakama idan tazo Nigeria baifi su haɗu sau biyu uku ba shikenan, a kuma duk haɗuwar tasu sai ya mata muguntar datake jin ƙarin tsanarsa a ranta kamar yanda shima haka kawai bai son yarinyar saboda tsiwarta da rashin kunya ido fiƙi-fiki injisa. Idan ma tana waje ya dinga ɗaure-ɗauren fuska kenan kamar an aiko masa da mutuwa, ko gaishesa tai sai ya gadama ya amsa shiyyasa tama daina gaidashi take nuna bama tasan ƙurar data kwasosa a duniya ba. Tuni company ya fara aiki cikin lumana da nuna ƙwazon shugaba kwata-kwatansa wato Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff. Da mafi yawan mutane sukafi sani da *_MM Shareff_* a taƙaice. Company ne da aka haɗa masu ƙwazo kuma ƙuraye, dan Ya Shareff bai yarda ya ɗauka ma’aikatan banza ba sannan sam baya wasa da aikinsa bai bama ma’aikatansa damar yin wasan kuma.
Jajircewar tasa tai matuƙar birge Abie, ya kuma ƙara tsayawa tsayin daka ta bayan fage yana bama Shareff ɗin gudunmawa dan yana matuƙar kaunar yaron har cikin ransa tamkar Anam ɗinsa ƴa ɗaya tilo.
To ayanzu dai ga Anam ta dawo Nigeria da shirin zaman shekara guda domin yin saves da su Mamie suka takura mata. Ga kuma ɓeranta da tuni yayi nauyi a Nigeria kodan hidimar kamfanin da mahaifinta keda kamasho mai ƙarfi a cikinsa da shares batare da Mommy da Gwaggo dake hura hanci sun sani ba………✍
_Ko yaya wasan zai kasance🤔? Kudai kawai ku zamto tare da littafin *_BABU SO…! MIYA KAWO KISHI? dan jin yaya cakwakiyar zata kasance. Littafine da yazo da wani irin sabon salo na musamman da nake tabbacin ni Bilyn Abdull ban taɓa zuwa muku da kalarsa ba sai yanzu. Domin kuwa ya taɓo zahirin rayuwa ne da zamanin da muke ciki a yanzu da rawar da tarbiyyar ƴaƴanmu ke takawa a social media batare da saninmu ba ko da sanin namu. Kar dai na cikaku da magana my guys, kumuje zuwa kawai dan duk wanda akai babu shi lallai ruwa tasha da shi kawai, saboda Zafafa biyar da gaske da zafinsu suke😉🥰🥰😘🚶🏻._
KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

Leave a Comment