Written by
*UMMU SAFWAN*
&π
*MSS HAFSY*π
_PRAISE BE TO ALLAH THE LORD OF THE WORLD, THE BENEFICIENT THE MOST MERCIFUL_ππΌ
*ALLAH KABAMU IKON ISAR DA SAK’ON DA MUKESON ISARWA*ππΌ.
*muna godia ga masoya, muna sonku kamar yadda kuke loving namu*
~we love you all~ππ»
*1*
“Umma wallahi nagaji da ganin irin halinda kike narashin sanin darajar ki agidan nan”
Umma tace” haba jannart ai mahak’urci watara na yakan zam mawada ci, kiyi hak’uri wata rana sai labari” jannart tajuyo ta kalli mahaifiyar ta da hawaye ki bimata idanu tace” umma yanzu kina nufin saboda kawai muna aiki agidan su shikenan sai suyita wulak’anta mu?, haba umma kigafa abinda sa’ad yayi miki yau da safe.shin umma bamu wai da kowane mu aduniya?”
Umma tai doguwar ajiyar zuciya tace” munada su jannart kuma suna nan araye basu mutu ba wata rana zankaiki”
Jannart tace” umma meyasa bazamu je yanzu ba?”
Umma takamo hannu y’arta tace” zan nuna miki danginki amma bayanzu ba, saboda nafison nayi nisa da y’an uwana”
Jannart tace”meyasa umma wai kullum nayi miki magana sai kice rayuwa haka ta gada?, shikenan mu ahaka zamu k’are wulak’ancin yau da ban nagobe daban?, gaskiya umma da sake”
Umma tace” hmm yaro kenan duk yadda za’a nuna ma yaro ba wajen yake hange ba, inda ya hango nan yake ganin dai-dai. Jannart kimanta da duk wani wulak’ancin da ake mana agidan nan wata rana sai labari ke idan ma labarin tai nisa wallahi baza asamu mai badawa ba.saboda haka kirek’e Allah arayuwar ki zakisha mamakin abinda zai maidake wata rana duk wahalar da kike sha wata rana bazakisha shi ba jannart kiyi hak’uri Allah yana tare damu”
“To naji umma kuma insha Allah bazan sake damuwa da halinda muke ciki ba saboda Allah na nan”
Umma taji dad’in abinda jannart ta fad’a sannan sukaci gaba da hirarsu har barci ya d’aukesu.
Safiya nayi jannart tafara aikin datasan natane tun sassafe saboda idan tabari gari yai haske ta dunga shan masifa kenan awajen sa’ad, hakan yasa takeyi da safe.
Sa’ad room da salim ne kawai bata addressing nasa ba, gashi har rana tayi ba wanda yafito ballantana tagyara hakan yasa ta komawa d’akinsu don ta d’an huta kafin su fito.
Tana kwance sai ji tayi ana kwala mata kira, ko alahira taji muryar tasan mai shi dasauri taje ta tarar dashi atsaye ta durk’usa har k’asa tace”ina kwana yaya sa’ad”
“Daban kwana ba zaki ganni?, wato ke jannart ce kowa kike yanzu iskancin naki ma yawuce yanda ake tunani har yake kik’i gyaramin room d’ina?”
Yana magana yana tada jiji yoyin wuya.
Tace” don Allah kayi hak’uri wallahi ba haka bane gani nayi baka tashi ba kuma ka hana ashiga maka d’aki kana ciki shiyasa”
Yace”ok nayi maki sharri kenan?, yayi nagode amma wallahi yau saikin gane kuren ki”
Yana magana yana cire belt, ito sai faman bashi hak’uri take amma shi ko ajikinsa.
Ya d’aga kenan yaji ance” karka sake ka daketa”
Dasauri jannart tajuya tace”don Allah Ya salim kataya ni bashi hak’uri wallahi ba da gan-gar nak’i masa gyaran d’aki ba please”
Sa’ad yace” hmm kina tunanin ya isa yahanani dukan kine?”
Salim yace”haba bro sa’ad meyasa kake yin haka ne?, yarin yar nan muryar tane yatasheni daga barcin danake yi tana baka hak’uri amma kak’i.kuma inajin ranar dakace karta sake shiga room naka when you are not awake please don’t be annoyed”
Sa’ad bece komai ba ya wuce room nashi.
Salim ya bishi da kallo sannan ya maida kan Jannart yace” kiyi hak’uri kinji?, sannan kuma kirink’a kujema kanki dukan Sa’ad duk abinda zai saki kiyi shi on time kinji?”
Tace” to nagode ya Salim kuma Insha Allahu zan kiyaye”
Yace”to shikenan tashi ki tafi”
Tawuce side d’insu sannan shima yai nashi d’akin.
urs
*stylishlady*
[8/14, 6:49 PM] Aisha Galadima: *RANAR D’AURIN AURENA*ππ»
Written by
*Ummu Safwan*π
&
*MSs Hafsy*π
*page 3*
By
*Stylishlady*βπ»
Tagama kukanta awajen sannan tafara linke kayan tana maidasu inda ya kamata, sannan ta gyara masa d’akin tsab dashi azuciyar ta ko cewa take” Allah kasa idan yadawo yace yayi saboda ba’a iya masa kwata kwata arayuwar shi”
Tafito kenan daga d’akin saiga mommy ta fito dasauri ta gaida ita, bawani amsawa tayi ba saboda ita haka take bata cika kulasu ba
Daddyne ma keson zaman su amma da ta mommy ne bazama zasuyi ba, shiyasa kome sa’ad yayi batayi masa fad’a.
Ta d’an numfasa tace” ke sonake kije kasuwa siyo min Abu”
Jannart jiki namata rawa tace” to mommy amma yaya sa’ad yabani aiki”
Tace”aikin me yabaki?”
“Abinci zan dafa masa”ta fad’a cikin gigi cewa
Mommy kam murmushin dariya tayi saboda ita bason Jannart take ba gwanda ma mamanta tana d’an sonta tace” Banda damuwa da wannan abunda nasani kawai shine zaki min kasuwa, idan kuma bazaki bane saiki fad’a min”
Hawaye na zuba tace” zanje mommy idan yaso Ina dawowa saina d’ora”
Kota kanta mommy batayi ba tashige d’akinta,
……………….
Ummah nacin uban wankin dake gabanta taga Jannart na hawaye, hankalinta bak’aramin tashi yake ba idan taga y’ar ta nakuka tace” meya faru kuma Jannart bana ga sa’ad ya fita ba keda waye?”
Tashare hawayen ta tace” mommy ne ta aikeni, gashi Yayah sa’ad yabani aikin abinci kuma idan yadawo ban gama masa ba kasheni zaiyi”
Wani hawaye na bin fuskanta tace”bazai kasheki ba Jannart saboda bashi ya halicce kiba karki damu Allah yana sane damu, tashi kije dasauri kidawo saiki d’ora karya dawo yaga baki dafa ba” Ummu tana sake share mata hawaye.
Jiki ba kwari haka Jannart ta mik’e tare da d’aukan hijabi tace” bin umarnin uwa yana dakyau domin ance bata tab’a zab’ar maka abinda zai cuceka saidai aganina tawa tazab’i ganina cikin k’as k’an tacciya maras y’anci tare da sadaukar da Farin ciki da gangar jikin y’arta inda ake ganinsa ba mutun ci”
Tana kaiwa nan tayi tafiyar ta , ummah dai kasa cewa komai tayi saboda tasan bata kyautawa y’arta ba nazab’ar mata irin rayuwar dasuke ciki
Ba yadda ta iya yazamar musu dole domin gujewa danginta dakuma dangin mahaifin Jannart.
Around 3:00
Jannart ta dawo gabaki d’aya agajiye take ga kaya hannunwan ta sunyi ja saboda ledojin dake hannun ta, tashiga ma mommy dashi ko kallonta batayi ba ballanta na tayi mata sannu.
Hakan baiyiwa Jannart ciwo ba saboda dama hakan yake,
Sauri takeyi saboda aikin sa’ad daba a samu ba gabaki d’aya ta rikice tashiga kitchen tafara aiki tahad’ a girkin baifara tausaba tace bari to taje tayi sallah kafin yayi.
Tana shiga d’akinsu kotsayawa batayi ba tashige toilet Don d’auro alwala, gudu gudu take harta samu ta idar kafin tajuya ta gaida ummah.
Fitar takeda wuya saita had’a Ido da sa’ad gabanta yayi rass don ganin yanayin sa, zata wuce kenan taji ya fisgota sai room nashi ya jefata kan gado tare da zare belt yana fad’in “yau zaki gane kurenki shegiya Mai Kama da aljanu, nizakiyi wa rashin mutunci nace ki dafa min abinci kitafi yawon ki?, yau zanga Mai kwatanki gidannan”
Tarik’e k’afan wandon shi tana magiya tace” Wlh Yayah sa’ad ba yawo natafi ba mommy ceta aikeni Don Allah kayafe min na d’orane najeyin sallah kafin ya k’arasa”
Yace” wato mommy zakiyiwa k’arya ita danaje har d’akinta na tambayeta Kota aikeki tace a’a shine yanzu kike min k’arya ko?, zaki gane kuren ki harda wani kintafi sallah angaida limamiya” yana magana yana sake mata belt a jiki, itako sai faman hak’uri take bashi amma maras imaninko ajikinsa.
Anakan haka saiga salim yadawo tundaya parking motar shi yakejin kukan Jannart ransa ab’ace yashigo room d’in sa’ad tare da kwace belt d’in dake hannun shi, Jannart naganin salim tayi gudu taje bayanshi tana kuka Mai ban tausayi.
[8/14, 6:49 PM] Aisha Galadima: *RANAR D’AURIN AURENA*ππ»
Written by
*Ummu Safwan*π
&
*MSs HafsY*π
*Page 4*
By
*Stylishlady*βπ»
Salim yace” Haba bro meyasa kake yin haka ne?, why she’s also part of us”
Sa’ad yace”listen stop shouting at me at the present of this bullshit”
Salim ya juya yace”Jannart kijirani ad’akina Ina zuwa”
Yadda ya fad’a hakan tayi sai faman kuka take, tana fita sa’ad yace” bro kad’aina had’ani da Jannart kana dangan tamu dasu the are our house made”
Salim yace”hakane amma ai musulmai ne kaga Ko y’an uwan mune, please kadaina azabtar da yarinyar nan she’s too young for that koma ba hakaba mace cefa, bai kamata ba idan tayi maka badai dai ba you can correct her ta yadda zata gane batare daka westing energyn kaba please bro wata Rana zaka nemita ma Baka ganta ba”
Sa’ad yawani ya mutsa fuska yace” bana tunanin idan muka rabu da wannan Mai suffan aljanun zan nimeta, kuma da kake cewa nakirata nayi mata magana idan tayi min badai dai ba to gaskiya I’m too expensive for that little bro”
Salim nata nuna mishi yadda zai daina cin mutun cinsu amma sa’ad Ko sauraron sa bayayi haka ya tafi room nashi Dan ganin ya Jannart take.
Yana shiga ya tarar da ita adurk’ushe sai faman kuka take,yace”Jannart tashi kizo”
Jiki ba kwari ta taso yace”meke had’aki da bro sa’ad meyasa bakya guje duk wani laifin da zai sa yaduke ki?”
Hawaye na zuba tabashi labarin abunda yafaru tsab , tausayi tabashi yace”kiyi hak’uri watarana sai labari kinji” yana magana tare da share mata hawayen dake bin fuskan ta, sannan ya bud’e brief case d’in shiyabata magana tareda cewa ta dannan jikinta da ruwan zafi.
Haka tai godia tare da fita daga d’akin ta nufi hanyar kitchen domin duba abinda ke wuta, Allah Ko yasota be k’oneba ta d’iba ta Kai mishi
Tana shiga ta tarar dashi kwance Akan gadon sa yana kallon ceiling ajiyewa tayi tare da duk abinda tasan zai buk’ata tayi hanyar fita kenan yadaka mata tsawa”ke haka umman taki takoya miki ajiyewa mutum abinci batare da sanar masa ba?”
Ta cuno baki na rashin kunya tace” ummah na basa’an wasan kabane nadad’e da fad’a maka kadukeni kamar bazaka barni darai ba amma wallahi Banda sa uwata aciki”
Yai y’ar dariya yace”shidama mutum idan akace maka jakine to ba yadda zakayi ka y’anta shi, abinci zanci yanzu anjima zamu had’u”
Ya bud’e abincin yafara ci ita kuma tafice warta, azuciyarta cewa take idan kakama ni karka barni darai mugu azzalumi kawai.
………………..
*Waiwaye adon tafiya*
Mallam attahir d’an kasuwane cikakke Wanda mutane dayawa suka sanshi, ba a k’asarnan yatsaya ba harda k’asa Shen waje yana gudanar da kasuwan cinsa, yana tareda uwar gidan sa hajiya Fatima itama tana kasuwancin ta nasiyar da gwal Allah ya azurtasu da d’a guda d’aya wato abubakar sadiq,tunda dagashi Allah bai sake basu aihuwa ba shiyasa suka tattara soyayyarsu suka d’ora akanshi saidai duk dahaka bai hanasu nuna mishi halin rayuwa ba tare da mutunta d’an Adam, ba abinda ya Nima yarasa yayi makarantar primary har zuwa secondary duk a cikin garin maiduguri, sannan yatafi Egypt Don cigaba da karatun computer science acanne yahad’u da wata itama y’ar Nigeria ce tazo karatunta na journalist wato hauwa’u itama dai y’ar masu dashine amma bakamar Abubakar Sadiq ba.
Soyayyar Mai k’arfi tashiga tsakanin su har sukayi alk’awarin aure bayan sun kammala karatu, Allah Ko cikin ikonsa suna gamawa aka d’aura musu aure tare da zama cikin garin Kano.
Bayan shekara d’aya Allah ya azurtasu da d’a namiji wato *Sa’ad* yataso cikin gata da Jin dad’i tare da shagala domin ita hauwa’u batason ayiwa sa’ad fad’a kome yayi dai daine hakan Ko bak’aramin b’atawa Abubakar Sadiq rai yake ba saboda ta nunawa d’anta talaka ba abinso bane harwani lokaci tana cemasa Wai mayune, bayan shekara d’aya Darabi Allah yasake bata namiji *Salim* Wanda tun daga shi bata sake haihuwa ba,
Saidai shi Salim halin mahaifin shi yad’akko yanason kowa tare da tausayawa itako Mommyn nasu halin Salim haushi yake bata.
Aiki yataso mata gashi bamai d’aukan nauyin yaranta tashiga Neman y’ar aiki amma batason yarinya sai Wanda tad’an manyanta, Ana haka sai k’awarta tasamo mata mahaifiyar Jannart shine sa’ad yad’auki karan tsana yad’orawa su Jannart kan cewa su talaka wane abin kyamane, tun daganan sa’ad kebasu walaha tareda cin mutunci daddy dai bai saniba idan yana nan su Jannart suna d’an samun sa’ida amma dazan yayi tafiya saboda aikinshi natafiya ne baicika zaman gida ba hakan yasa mahaifiyar sa’ad da d’anta suke cin karansu ba babbaka.
[8/14, 6:49 PM] Aisha Galadima: *RANAR D’AURIN AURENA*ππ»ββ
Writing by
*UMMU SAFWAN*
&π
*MSS HAFSY*π
Page *2*
By
_Ummu Safwan_βπ»
“Tafiya takeyi tana sharar hawayen dake zuba a kan fuskarta,
Kai tsaye wurin umma ta nufa Wadda take zaune tana wanke wanke gefen d’ayanta kuma tarin kayan wanki ne wad’anda ke jiranta.”
Ummu na ganinta tana kuka ta girgiza kai cike da tausayin ‘yar ta ta,
domin duk abinda ke faruwa a kan kunnenta tanaji, ita dai ta rasa kalar tsanar da Sa’ad yake yiwa jannat.”
Kai tsaye jannat taje kan k’afar Umma tafad’a ta saki wani kalar kuka mai sauti kwanin ban tausayi.”
Dakatawa da wanke wanken Umma tayi da ta d’ago kan jannat ta shiga share mata hawaye “kiyi hakuri jannat wahala ba mutuwa bace, kici gaba da hak’uri kamar yanda kikaga inayi,
wata rana sai labari, ki dinga yin taka tsantsan da duk wani abinda kika San Sa’ad zaici maki mutunci a kansa.”
Tashi kitafi ki gyara masa d’akinsa kiyi masa duk wani abinda ya umurceki domin ki samu ki tsira da mutumcinki.”
Mik’ewa tayi jiki ba kwari tafara tafiya snn ta juyo ta kalli UMMU idonta cike da hawaye tace “Umma zanyi biyayya gareki a matsayinki na mahaifiyata domin kinfi muradin ganinmu haka a cikin k’angin bauta, hakan yafi soyuwa ranki,
akan ki kaini wurin dangin mahaifina ko kuma ki nuna mun ‘yan uwana.”
Tajuya taci gaba da tafiya.”
D’akin Sa’ad ta nufa. Wanda take tafiya kamar wacce kwai yafashewa a ciki. Tana gafda kaiwa k’ofar d’akin taci karo dashi ya fito daga d’akin cikin hanzari yana tafiya yana d’aura agogon hannunsa alamar sauri yakeyi.”
Wata kalar harara ya wurga mata mai cike da tsana da kyamata, yazo dafda ita, ya taka mata k’afa ya murza da k’arfi, wanda bata San lokacin da tasaki kukan wahala ba tana fad’in “Allah kayi hak’uri karka karya mun k’afa.”
Jin kukanta da magiya yasa Salim saurin fitowa daga d’akinsa da Sauri dan ganin meke faruwa.”
Sa’ad yana ganin fitowar Salim ya kauda idonsa yayi kamar bai ganshiba, ya kuma danne k’afar da k’arfi cikin wata sigar mugunta, yana “fad’in idan kika kuskura kika bari na dawo baki kammala mun aikin da na sanyaki ba saina lahira yafiki jin dad’i, matsiyaciya kawai mai sufar Aljanu. Daina kallona,
Kuma kisani yau ke zaki dafamun abinci domin bana ra’ayin cin abincin tsohuwar uwarki, yana kaiwa nan ya sauke k’afarsa daga kan tata yayi tafiyarsa wanda yayi dai dai da zuwan Salim wurinsa, kafin ya kawo har ya ficewarsa.”
Gurfanawa yayi kusa da ita yana kallon k’afarta wanda tayi jajir har fatar wurin ta fara turb’ewa akan kyakkyawar k’afarta, ransa ya b’aci
yashiga bata hak’uri tare da kwantar mata da hankali.”
Girgiza kai tayi alamar godiya ta share hawayenta tanufi d’akin Sa’ad domin ta aiwatar da aikinda ya sanyata wanda ya zame mata dole.”
Da shigarta d’akin komai na d’akin anyi d’ai d’ai dashi harda kayan da ke cikin wadrup duk anfirfito dasu.” Girgiza kai tayi tana tausayin kanta domin tasan harda mugunta tasanya Sa”ad ya warwatse kaya hakan.”
A Hankali take tak’a k’afarta wanda takejinta tana mata wani rad’ad’in zafi ta k’arasa shiga cikin d’akin.”
Bata ankaraba saiji tayi ta taka robar ruwan faro wanda aka shanye ruwan akayi jifa da gorar,
Darjewa tayi ta fad’i k’asa, da sauri ta rik’e k’ugunta tana fad’in “wash Allah na bayana k’afa ta amma ina ba wanda yasan tanayi.”
[8/14, 6:49 PM] Aisha Galadima: *RANAR D’AURIN AURENA*ππ»ββ
Writing by
*UMMU SAFWAN*
( _Fareeda Basheer_)
&
*MSS HAFSY*π
_Stylishdy_
Page 5
By
_Ummu Safwan_βπ»
Abincin yakeci yana wani ya mutsa fuska sai kace wanda yakecin kashi.”
Ba wai dad’i ne abincin baiyi ba A’a kawai wulak’anci ne irin na sa’ad.”
Tunawa yayi da maganar da ta fad’a masa ta k’arshe akan uwarta,
da tace “duk abinda zaiyi yayi akanta amma kadda ya sanya uwarta a ciki.”
Wato tana nufin na daina sanya uwarta kenan?”
Wato ita har ta isa ta fad’a min hakan?”
wacce uwarta a gidan nan?” Wnn k’azamar uwartata har wata abace gurina?.
Cikin zafi ya ture abincin daga gabansa ya mik’e tsaye yana huci yace “bari naje na wulak’antaki na kuma wulak’anta tsohuwar uwartaki naga wanda ya isa ya rama maku a gidan nan.”
A fusace ya fito daga d’akinsa,
Sai dazo a bakin k’ofa ya kuma juyawa ya koma ya d’auko plate d’in abincin da ya faraci ya fito da shi d’auke a hannunsa.”
Sai da ya fara lek’awa d’akinsu inda suke kwana yaga basa nan snn ya nufi kitchin a can ma basa nan inda yasaba ganinsu a bayan gida suna zama idan suka kammala aiki a can ya nufa.”
A can ya hangosu zaune jannart tayi matashi a kan k’afar umma da alamar kuka takeyi umma tana lallashinta tare da share mata hawaye.”
Kai tsaye ya nufi wurin yana huci basu San da zuwansa ba. Sai dai sukaji anwatsa masu abinci a jiki, musamman umma da gaba d’aya jikinta ya b’aci da abinci har zuwa fuskarta arzikinta d’aya abincin baya da zafi ya riga da huci.”
Wata kalar zabura sukayi jannart tayi saurin mik’ewa tsaye tana masa kallon tsana,
Idonta ya cika da hawaye,
Zatayi magana umma ta d’aga mata hannu alamar kadda tace komai tayi shurunta.”
Ta kuma waigawa ta kalli mahaifiyarta dake zaune tana kakkab’ar abincin dake jikinta tana murmushin k’arfin hali.”
Yace “matsiyata ubanme kukeyi a nan?”
Ya kuma nuna umma yace dake nake bada Aljanar ‘yarki nakeba domin kece sa’ar yina ba itaba.”
Cikin murya k’asa k’asa Umma tace “kayi hak’uri sa’ad meya faru ne?” Ai duk mun kammala aikinmu,
Idan wani abin mukayi maka kafad’a sai mubaka hak’uri.”
D’aga murya yayi da k’arfi ya katseta tana magana yace “rufemun baki harma tambayar abinda kukayi kikeyi dake da wnn munafukar ‘yar taki.”
To bari kiji abinda nake buk’ata dake a yanzun kitashi kije kiyi wanka ki canza wad’an nan tsumman kayan jikin naki ki shiga kitchen kidafa mun abinci ki kawo mun a d’akina ina jiranki.”
Kuma kisani da zarar kin wuce minti talatin saina lahira yafiku jin dad’i, kuma daga lokacin kun daina aikin a gidan nan.”
Sai dai kutafi can Ku iya da tsiyarku dangin matsiyata waya sani ma ko maitace ta koroku a garinku.”
Hak’uri umma take bashi, wanda jannart take tsaye wuri d’aya takafeshi ido wad’anda babu abinda ke zuba a idonta sai ruwan hawaye zuciyarta na tafasa.”
Bai damu da ganinta a hakan ba dama domin ya tusguna mata ya kuntata mata ya bak’anta mata yasanya shi yayiwa uwarta wulak’anci a gaban idonta.”
Domin ya nuna mata ita ba kowa bace face ‘yar aiki kuma k’ask’anttaciya, wanda yafi tsana a kan komai a rayuwarsa.”
juyawarsa yayi,
yayi tafiyarsa,
Zuciyarsa cike fal take da farin ciki.”
Umma ce ta janyo jannart zuwa jikinta wanda ta k’afe wuri d’aya a tsaye kamar bata motsi saboda bak’in ciki,
Tashiga bubbuga bayanta tana bata hak’uri tare da tofa mata Addu’oi,
Sai a lokacin jannart ta sauke ajiyar zuciya ta fashe da kuka mai sauti tana fad’in Umma ki taimakemu ki taimaki rayuwarmu ki mayar damu wurin danginmu, ki nuna mun dangin mahaifina.
Umma idan kuma ni shigiyace bana da uba ki fad’amun gaskiya, zan d’auki kaddara, sai ki fad’amun inda danginki suke mukoma can muci gaba da rayuwarmu cikin ‘yanci kamar yanda kowa keyi.”
Umma ta doka mata tsawa “kull jannart kadda na kuma jin kin kira kanki da shegiya, ke ba shegiya bace kina da gata kamar yanda kowa yake da gata,
To idan hakan ne umma meyasa kika baro gatanki kika zab’i mu zauna muyi rayuwar wulak’anci da k’unci.”
Zan fad”a maki dalili amma ba yanzun ba, kiyi hak”uri tashi mutafi lokaci na tafiya daga lokuntan da aka d’ibarmun.”
[8/14, 6:50 PM] Aisha Galadima: *RANAR D’AURIN AURENA*ππ»
Written by
*Ummu Safwan*π
_(Fareeda basheer)_
&
*MSs HafsY*π
*_Godia muke Masoya da irin k’aunar labarin da kuke yi,comment d’in ku namana sweet Plss kuci gaba zan zan ne_*π―
*Page 7*
By
*Stylishlady*ππΌ
Tunda yafurta haka yayi waje itama mommy binshi tayi abaya tare da nuna Jannart da d’an yatsa, while sa’ad jiyake kamar yatashi yakashe Jannart dake faman kuka
Murya k’asa2 yake magana”ke bazaki tashi kifata min ad’aki bane?”
Cikin rawan jiki ta mik’e takai bakin k’ofa kenan yace”kuma wallahi karki zaci nabarki ne saboda mahaifina baitab’a marina ba tunda aka haifeni sai yau,akanki akafara nima zan fito dasabon muguntar da akanki za’a fara Jannart baiwata zaki zama saboda wannan marin saikin biya shi fita min” yak’arasa magana cikin zafin rai da takaicin sanin Jannart arayuwar shi
Gani yake kamar ba d’an lelen daddy ba Wai yaushi ya Mara, ya dunk’ula hannun shi tare da cewa” zakisan koni waye”.
Jannart tana shiga d’akin su dakuka umma maima kon ta lallashe ta saita fara yimata fad’a” Jannart ashe bakyajin maganar danake fad’a miki?, naja miki kunne amma abanza kenan yanzu kin jawo anyiwa sa’ad fad’a harda Mari gaskiya……”
Kasa k’arasa maganar tayi saboda ganin irin kukan da Jannart keyi gabaki d’aya sai tausayin y’arta yakamata tasan ba Jannart ce silan faruwar hakan ba amma Don tanuna mata hak’uri dazaman duniya tareda koda kanada gaskiya ba kowani lokaci ake Baka itaba ba domin kawai azauna lafiya, tare da taking action d’in uwa tagari bata goyon bayan d’anta koda shine da gaskiya Plss (iyaye murage son yaranmu hakan shine silan lalacewar al ummar yanzu da kowa nayiwa yaro fad’a amma ayanzu bahaka bane agabanki d’anki zaiyi ba dai2 ba amma saiki rufe idonki kice shine da gaskiya Plss arage koma samu cigaba tare da samun lahiran mu baki d’aya Allah yasa mudace).
Jannart tace”Haba ummah yazakice haka kamar bakisan waye sa’ad ba?, kawai daga nayi mishi magana shine zai fara zakina tareda cimun mutunci harya cewa waike…”
Kafin ta k’arasa ummah ta toshe mata baki tace”banason jin meyace,amma ba Don niba kiyi hak’uri tare da danne zuciyar ki da duk wani abunda sa’ad yake yimana Jannart idan munada rayuwa zakisha mamakin gaba”
Itadai Jannart bata sake magana ba, cigaba tayi da kukanta ummah nabata hak’uri tare da mata nasiha har barci ya d’auketa sannan ummah tazame jikinta ta d’auro alwala sallah ta gabatar tare da rok’on Allah ya kawo k’arshen walahar takesha aduniya sannan Allah karya dauwa mar da Jannart cikin bauta yanuna mata Farin ciki…tana kaiwa nan tafashe da kuka domin halin da Jannart ta tsinci kanta bak’aramin d’aga mata hankali yakeba tason y’arta kuka take kamar zata mutu Don bak’in ciki, kukanta yatada Jannart dasauri tazo kusa da mahaifiyar ta tadafata tace”meyasa meki ummah na meyasa kike kuka haka?”
Umma ta d’ago murya cikin kuka tace” tausayawa rayuwar ki nake Jannart tunda na haifeki dasati d’aya dakika ji dad’i baki sakeba kullum cikin wahala kike, Jannart yabazan ji tausayin kiba?, abunda sa’ad yafad’a miki gabaki d’aya naji shi da kunne na
Kuma duk ninaja miki dana zab’a rayuwar haka amma gujewa wahala nayi duk ta tsewa tar dake daga sharrin fad’awa mugaye Wanda basuda Imani koka d’an”
Jannart tace” wayesu kuma wani irin hali zasu sani?”
Ummah tace” zan baki labari amma bayanzu ba zakisan wace ce ke dakuma dalilin dayasa nazab’i zama anan, y’ata kiyafe min?”
Jannart tace” ummah kidaina kuka Don Allah, kuma bakimin komaiba dazaki nemi yafiya awajena ni y’arkice kinsan dalilin yin haka da rayuwata banyi dana sanin kasancewa y’arki ba, ummana ke umace tagari”
Cikin kuka Jannart ke magana
Hakan yayiwa ummah dad’i nan suka d’aga hannu sama suna rok’on Allah yaciresu daga k’angin wahalar dasuke ciki,
Safiya nayi Jannart tafara aikinta ita kuma ummah nahad’a break fast masa takeyi damiya saboda daddy nason shi sosai hakan yasa tunda tasan yadawo yasata yi.
Jannart harta gama shara wanke2 takeyi saiji tayi sa’ad ya kwala mata Kira dasauri ta nufi room nashi tana zuwa ta durk’usa har k’asa ta gaidashi cikin shan toka ya amsa sannan yace” me ake dafawa agidan na breakfast?”
Tace”masa da miya tareda kunun gyad’a”
Yace”ok ni inason abinda kika lissafa?”
Tace”a’a bakaso”
Yace”ok tsabagen rashin mutunci ne yasa bazakizo ki tambayeni Mai zanciba kika bari yunwa takashe ni ko?, Jannart Wai menai miki kikeson ganin bayana agidan nan?”
Cikin rawar murya tace”kayi hak’uri,me zakaci?”
Yayi kwafa yace” shegiya Mai muryar jinjiraye harda wani me zakaci?, ke duk namijin da akaiwa wallahi yahad’u da bala’i tareda masifa domin ke kullum saikin janyo mishi magana Jannart”
Yakira sunan ta kamar abin kirki dasauri ta amsa
Sannan yace” Anya keba dangin aljanu bane?”
Nairai2 tayi da Ido tace” wallahi niba dangin subane”kamar zatayi kuka shikuma yace” ok naji amma Don Allah kidaina yin kamar wata auta domin shagwab’a ba karb’arki take ba Sam”
Itadai batace masa komai ba yagama maganar sa annan yace” kisoya min chips and egg with ginger tea”
Yana fad’an haka yatashi ya shiga toilet ita kuma tafita domin aiwatar da sak’on sa’ad.
Cikin lokaci bamai yawaba ta aiwatar da aikin sa’ad sannan tad’auka ta nufi room nashi takai bakin k’ofan shiga kenan sai jitayi ance good morning queen of beauty, dasauri ta juyo Don ganin waye Yayah Salim tagani tayi y’ar smiling tace” Ina kwana Yayah” ya d’an jingina da wall yace”nak’i ansawa bayan nagaida keda suna Mai dad’i kink’i amsawa?
Kunyace ta isheta ta sunkuyar da Kai yace”ok kikaiwa sa’ad abinda ke hannun ki kizo ki amshi tsarabar dana kawo miki daga k’asar waje”
Yana kaiwa nan yayi d’akinsa, ita kuma tashiga kaiwa boss abinci
Tana shiga taganshi d’aukeda system a hannun shiyana latsawa ta ajiye tareda cewa” ga abincin”
Yi yayi kamar baijiba azurciyar ta cewa tayi”sai shegen jidakai da miskilanci kamar yafi kowa”
Tasake cewa”Yayah sa’ad ga abincin ka nagama”
Sai alokacin ya responding yace”ok sannu saidai cewa zanyi ban godeba because bawani Abun kirki kikayiba, yanzu zanci abincin inason kuma nafita saboda haka yau inason kiyiwa d’akinnan kwalima kishare shi tas tareda wankemin bayan gida, idan kin gama ki wanke kayana ki gogesu sannan abinci sakwara nakeson ci kuma ki tabbar kin goge ko Ina dakyau Ina fatan kin fahimta?”
Ta d’ago da idanu jajaye tace”eh naji”
Yai dariyar mugunta yace”Yauwa Anty Jannart, crying beauty idan zan fita zansa nar dake saiki fara akan lokaci ko?”
Kai kawai ta d’aga mishi hawaye nabin fuskarta, tasan d’akinnan ba datti yayi ba kawai salon mugunta ne irinna sa’ad.
Shikuma Farin ciki yakeyi yace”muje zuwa Jannart da sa’a Abubakar sadik kikeyi”.
[8/14, 6:50 PM] Aisha Galadima: *RANAR D’AURIN AURENA*ππ»

Leave a Comment