Hausa Novels

Ranar Nadama Hausa Novel Complete

🔱🔱🔱🔱🔱🔱

*RANAR NADAMA*

🔱🔱🔱🔱🔱🔱

 

*WRITTEN BY SIS NERJA’ART✍*

 

*INTELLIGENT WRITERS ASSO…®📚*
{On Ward Together}

 

*PAGE 1*

Ahmad meyasa kake irin haka, miye laifina a ciki, duk soyayyar da kanuna min a baya ban ta6a tunanin haka daga garekaba yanzu saboda kawai kyautar da ubangiji yabamu zaka butulce min, na rok’eka kataimaka kaja ‘ya’yanka jikinka kamar yadda sauran iyaye sukeyi, kar ka mance wasu ma suna nema ammah basu samuba, kaduba kaga yadda kabanzatar da rayuwarsu kamar ba kaine mahaifinsuba, ka ajiye duk wani buri naka a gefe domin ubangiji shi yake azurtawa sannan idan yak’addara zakayi kud’i toh ‘ya’ya basu isa suhanaba.

Cikin tsawa yace ke Maryam! Ya isheki haka indai abinda yakawoki d’akina kenan tashi kifita dan bazaki ta6a canza min ra’ayina ba, yaran banza ai tun farko na ce miki ni ban shirya fara tara ‘ya’yaba ko ban gargad’eki da hakaba?

‘Dago idanuwanta tayi da suka kumbura saboda tsananin kukan da take tace toh ya zanyi bayan haka ubangiji yatsara min rayuwata sannan ‘ya’yana da ubansu ba na shege bane yaran.

Zancen banza da wofi ai kinga matsalarki tun lokacin da kika samu ciki na farko saida nace kizubar kizubar ammah kika k’i saida kika haifeshi saboda kin rainani ak’arshe saida kika ajiye min ‘ya’ya d’aid’aya har ukku a gida, toh bari kiji ina k’ara tunatar da ke wad’annan ‘ya’yan banda alak’a da su ban haifaba naira d’aya tawa bazata ta6a kuka ba wajen siyan koda ace maggi ne bare ma asa ran zan siya masu abinda zasuci, keda kikeson ‘ya’yan sai kije gaki gasu nidai ban shirya fara haihuwa ba sai na cika burina naga na samu aiki mekyau nayi kud’i sannan in auri wadda zata zataso ra’ayina inyaso daga baya idan nafara son ‘ya’yan sai ta haifa min, haba ina amfanin ace daga aure anfara tara maka ‘ya’ya kai kana fama da kanka sannan a k’ara aza maka wani nauyin ke ni duk ma lokacin da kikazo min da maganar yaran chan ji nake kamar inrufeki da duka, dan haka kitashi kibani waje ko insa6a maki yanzun nan.

Jinjina kai tayi hawaye suna cigaba da zuba daga idanunta tace naji zan fita ammah inaso kasani ubangiji shi zai raya min su insha Allahu zan basu farin cikin da duk wani me uba zai samu kaikuma ba zance komai ba saidai ince kaje Allah yashirya ka,,,mik’ewa tayi fuuuu zata fita har ta kai k’ofa yace idan kin fita kice ma ‘ya’yanki kar insaki inji maganarsu dan bacci zanyi inko sukayi gigin tashina toh sai na sa6a masu agidannan.

‘Dan guntun murmushi tayi cike da takaici sannan taficce.

Tana fita tsayawa tayi tagoge hawayenta sannan tawuce d’akinta tana shiga tasamu yaranta biyu zaune sunyi jugum, murmushi tayi taje kusa dasu tazauna tare da janyo yaron da bazai gaza shekaru shidda ba tace Ya dai Sadeek wa yata6a min ku?
Kallon fuskarta yake kamar zaiyi kuka yace Umma kema Abbah fad’a yayi miki irin wanda yakeyi mana?
Shafa kansa tayi tace a’a Sadeek ba fad’a yayi min ba.

Toh kuma Ummah fuskarki kamar kinyi kuka kuma munjiyo yana maki fad’a,,,cewar d’ayar yarinyar da bazata gaza shekaru goma ba.

Murmushi tayi tace ke Safiya baku dai ji sosai ba ammah ba fad’a yayi min ba kawai dai k’waro ne yafad’a min a ido kuma na cire kin gani?.

Toh Ummah meyasa Abbah baya sonmu? Ko bashine babanmu ba?

Da mamaki take kallon d’an nata ganin shi yayi maganar chan tace Sadeek ka cika magana dayawa toh wanene babanku inba shi ba? kawai dai dan kuna rashin ji ne saisa yakeyi maku fad’a ammah da kun daina shima zai daina.

Toh Ummah kice mashi nidai bazan k’ara rashin ji ba yadaina dukana da min fad’a, kema Yaya safiya kin daina ko?

Safiya da tayi shuru tana sauraren maganar mahaifiyartasu da bata yadda da hakan ba dan tasan wayau ne kawai takeyi masu juyawa tayi tana hawaye.

Shikenan Sadeek zan fad’a mashi yanzu dai kayi shuru Abbanku bacci zaiyi kar kutasheshi.

Cikin sauri yakalli k’ofa cike da tsoro yace Ummah nayi shuru na daina magana kice ma Abba kar yadokeni irin wanda yayi min rannan.

K’wallah ce tacika mata ido tunowa da tayi dukan da yata6a yi ma d’an nata lokacin da yana wasa shikuma yana bacci kan ya farka shine yakamashi da duka, cikin ranta tace lallai ba k’aramin duka yayi mashiba da har sadeek yakasa mancewa, kwantar da yaron tayi saman cinyarta tana shafa kansa nan da nan shima yayi bacci.

Kallon Safiya tayi da take ta hawaye tace ya dai safiya ko yunwa kikeji?

Kamar jira take nan tafara sheshek’ar kuka tace ummah.
Safiya menene kuma abun kuka daga tambaya? Yanzu dai kiyi shuru kinga Abbanku bacci yake kar kitasheshi.

Goge hawayen fuskarta tayi tana me kallon umman tasu.

Sallamar da akayi ne yasa gabad’aya suka waiga tare da amsawa, wata matashiyar budurwace da bazata gaza shekaru goma sha takwas ba tashigo chocolate colour ce tana da kyau sosai da kaganta kaga zubin buzaye doguwa ce bata da jiki sosai da kaganta kaga kamarsu da matar da take zaune, cire hijab d’inta tayi tace ummah sannunku da hutawa.

Batare da ta kalletaba tace yauwa Meerah andawo islamiyyar?
Eh ummah na dawo kinga nima yau har so Malam Munir yayi yakoreni saboda kud’in makaranta saida nabashi hak’uri sannan yabarni yace gobe indai ban kawoba sai ya koreni.

Allah sarki ai insha Allahu zaku biya nima ba jin dad’in rashin biyan kud’in nakeba kinga su Safiya tun jiya aka korosu Allah dai yarufa mana asiri.

Ameen Ummah, juyawa tayi takalli Safiya da tayi shuru tace Safiya ya dai yau bama za’ayi min magana ba?
Murmushi tayi tace sannu da dawowa Aunty Meera.
Hmm yauwa,
Ai Abbanku yake bacci saisa kikaga ta nutsu haka.
juyawa tayi takalli Ummansu tana shirin yin magana suka had’a ido gabanta saida yafad’i tace Ummah me yasameki? ya naga idanunki sunyi ja haka?
Murmushin k’arfin hali tayi tace bakomai.
Juyawa tayi ga Safiya tace Safiya me yasamu ummah?.
Aunty Meera abbah ne.
Runtse idanunta tayi tana jin wani irin ba dad’i a ranta dan tunda ta ambaci abbah tasan toh tabbas fad’a yayi ma ummansu, muryar ummah taji tana cewa gidanku safiya me abban naku yayi min bance maki k’waro bane yafad”a min a ido ba?
Shuru safiya tayi tana turo baki.
Bud’e idanuwanta tayi da suka cika da k’wallah tace Ummah meyasa Abbah yake miki haka? Na tabbata ba k’aramin 6ata maki rai yayi ba dan kina da hak’uri bakomai bane yake sawa kicanza haka, kokad’an bana son ganin 6acin ranki a duniya banason inga komai ya ta6a min ke.

Haba Meera meyasa kike biye ma zancen safiya nifa ba abinda Abbanku yayi min baccinsa ma yake yanzu kinga tashi kicire kayan nan kid’auko wannan hamsin d’in kisiyo mana garin kwaki dan nasan yunwa kukeji.

Cike da ladabi tace toh ummah sannan tamik’e tanufi wajen kayansu duk dahaka tana jin k’unci acikin ranta.

Tana cire kayan tad’auko wata kod’ad’ar atamfa tasaka sannan tad’auko hijab d’inta tasa tace ummah na tafi.
Adawo lafiya.
Allah yasa ummah, Aunty Meerah inzo muje?
Eh Safiya zo muje.
Tashi tayi tad’auko hijab d’inta cikin jin dad’i tabi yayartata.

Suna fita Maryam zugum tayi tana tunanin halayyar mijinta da kwatakwata takasa gane kansa shidai kullum magana d’aya sai yayi kud’i.

Koda suka dawo ana gab da kiran sallar magrib alwallah sukayi gabad’ayansu sukayi sallah bayan sun gama Meerah bata tashi daga saman sallayarba saida tayi karatun alk’ur’ani sannan taje takwad’a masu garin suka zauna suka ci.

Bayan sallar isha’i shirin bacci sukayi duk suka kwanta ammah Meerah bata runtsa ba tana ta tunanin rayuwarsu haskota ummah tayi da touchlight tace Meerah me kike har wannan lokacin bakiyi bacci ba?

Murmushi tayi tace bakomai Ummah kawai dai baccinne baizoba.

Hmm Meera kenan na fad’a maki kidinga cire damuwa a ranki kucigaba da taya Abbanku da addu’a itace maganin komai.

Toh ummah insha Allahu zamu cigaba da yin addu’ar.
Yauwa kokefa yanzu kisamu kiyi bacci.
Juyawa tayi d’ayan side d’in tare da runtse idanunta.

Ummah ita kanta tunanin takeyi jin motsin d’iyartata ne da yayi yawa yasa tahaskata taga idanunta biyu, aranar kasa rintsawa tayi tana tunanin abinda zata samo ma yaran nata suci da safe dan ko naira d’aya bata da ita, har wajen k’arfe d’ayan dare idanunta biyu nan tatashi tayi nafila sannan taje takwanta.

Washe gari koda suka tashi suna gama sallar asuba zaune tayi saman dardumarta tana tasbihi inda Meerah take karatun alk’ur’ani.

Tana gamawa addu’a tayi tashafa sannan tajuyo takalli ummansu da tayi shuru kamar me tunani cike da damuwa tace ummah.
Juyowa tayi takalleta tana murmushi tace minene Meerah?
Ummah meyasa kikeson zama cikin damuwa.
A’a Meerah ni tasbihi nake kinga tashi kije kikoma bacci tunda kingama tilawar.
nan saman dardumar takwanta tana me kallon mahaifiyartata
Ganin haka yasa Ummah tacigaba da tasbihinta d’inta daga k’arshe takwanta itama.

Chan wajen k’arfe tara Sadeek ne yatashesu yana cewa yunwa yakeji, Ummah hankalinta saida yatashi ganin abinda take tsoro shi yafaru.

Ganin yadda ummansu tashiga damuwa yasa Meerah tamik’e batare da tayi magana ba zuwa tayi tawanke bakinta sannan tad’auko hijab d’inta tafita, kitchen taje tad’auko d’an bokin plastic tafita.

Wajen wata me koko taje da take chan gaban layinsu tana zuwa tatarar da ita tana suyar k’osai ga bokin koko nan a gabanta, duk’awa Meerah tayi cikin girmamawa tagaishe da matar tace babah ina kwana?

Kallonta tayi fuskarta a sake tace lafiya lau Meerah koko zaki siya?

Duk’ar da kanta tayi tace Eh Babah dan Allah kitaimaka kibani bashi insha Allahu zuwa anjima zan kawo maki.

Shuru me kokon tayi sai chan tace kin tabbata ‘yar nan zaki kawo min zuwa anjima? Dan gaskiya bana son bada bashi.
Insha Allahu zan kawo maki babah.
toh shikenan kawo wajen na nawa za’a zuba maki?
Na talatin.
Zuba mata tsohuwar tayi tabata nan takar6a tare da yin godiya sannan tatafi.

Tana isa gida Abbansu yana fitowa daga cikin d’akinshi cikin shirin fita cikin sauri Meerah tadurk’asa k’asa cike da ladabi tace Abbah ina kwana?

Wani irin kallo yawurga mata sannan yawuce yafita.

Tana tsugunne k’asan har yafita inda sabo ta saba da hakan dan magana bata had’ata da shi, mik’ewa tayi har zata wuce taga wata takardar nama da yafiddo daga d’akinshi, wajen takardar taje tad’auko tabud’e taga nama ne yaci sai kitse da k’ashi kawai yabari wucewa tayi tanufi d’akinsu tana shiga tasamu Ummanta tana ta lallashin Sadeek akan yayi hak’uri, safiya ma zuru tayi tana zare ido saboda yunwar da takeji.

Bokitin hannunta ta ajiye cikin sauri sadeek yazo wajenta nan tace safiya d’auko maku cup kusha koko, cikin sauri Safiya tamik’e tace toh Aunty.
Ummah ce tace Meerah ina kika samu kud’in da kika siyo koko?

Duk’ar da kanta tayi tace kiyi hak’uri ummah bashi nakar6o wajen babah.
Haba Meerah kinsan dai bana son cin bashi meyasa kika ciyo bayan bamuda kud’in da zamu biya?
Kiyi hak’uri bazan sakeba insha Allahu zamu biyata Allah zai bamu.
Jin tace Allah zai bada yasa tace toh Allah yashige mana gaba, wannan ledar fa ta mecece?
Daman su khalil nakawo mawa kitse ne ciki da k’ashi wanda Abbah yafito da su.
Shuru Ummah tayi batace komai ba dan daman indasabo toh sun saba da hakan.
Kokon suka zuba duk suka sha bayan sun gama Ummah tamik’e taje tayi wanka tana fitowa Meerah tashiga.
Bayan sun shirya ummah tace Meerah yanzu ya kikega za’ayi?
Shuru Meerah tayi dan ta gane abinda mahaifiyartata take nufi chan sai tace Ummah ko wankau zamu kar6o gidan Hajiya luba da tace asamo mata mewanki, kinga sai muyi mata a nan gida a maimakon muje chan muyi idan mun gama sai inje inshanya mata a chan gidanta tabiyamu kud’inmu.

Kina ganin babu matsala Meerah?
Eh Ummah insha Allahu babu.
toh shikenan kije ki amso.
Cikin jin dad’i tace toh ummah nan tamik’e taje tad’auko hijab d’inta tafita, tafiya take a nutse kanta sadde a k’asa har ta isa gidan koda da d’an nisa ammah a k’asa taje, gidane babba ba laifi da kaganshi kasan masu gidan suna da rufin asiri sosai, kasancewar a da tana d’an zuwa ko shara ko wanke wanke yasa megadin be hanata shigaba.

Tana shiga tagaisa da gudar matar da take tsakar gida sannan tashiga d’akin Hajiya Luba bakinta d’auke da sallama.
Hajiya luba da take zaune saman cushion amsa mata tayi tana d’an yatsine fuska, daga k’asa tazauna tagaisheta cike da girmamawa nan ta amsa.
Kanta sadde k’asa tace Hajiya daman Ummah ce tace ince kibada wankin naki zanikai maki.
Ita wadda zatayi wankin bazatazo nan tayi min ba salon inbada kayana ayi min k’azanta? Nifa ba kowa nakeson ba ma wankiba dan ma mewankina baya nan, salan aje ayi min yak’i fita.
Kiyi hak’uri hajiya zaya fita insha Allahu dan matar ta iya wanki sosai sannan nan gidan za”a zo ashanya maki idan angama.
Toh shikenan indai basu fitaba bazan biya ko naira ba.
Cikin jin dad’i Meerah tace toh hajiya mun amince.
Tashi muje kid’auka.
Tashi tayi suka shiga bedroom d’in hajiyar tabud’e wardrobe d’in nan tasa Meerah tad’auko marassa wanki tahad’a waje guda kaya sunkai kala goma sha biyar, sabulun wanki ukku tabata Meerah tace sunyi yawa,
Wane yawa sukayi indai ba so kuke suk’i fitaba.
Shuru tayi batare da tayi magana ba.
naira d’ari biyu tabata tace d’ari asai ruwan wanki kar asaki ayi mata da na rijiya sannan d’ari kuma tahau abun hawa saboda wankin suna da yawa.
Godiya Meerah tayi mata nan Hajiya Luba tak’ara jaddada mata tace ma mewanki kar fa kayanta suk’i fita.
Da toh tabita sannan taficce da kayan.
A k’ofan gate d’in gidan tatsaya tasamu me adaidaita tahau yakaita har k’ofar gidansu tabiya naira arba’in.

Tana shiga nan tafayyace ma ummanta duk yadda sukayi da hajiya luba itama ta ji dad’i sosai nan tasa Safiya tasamo masu meruwa tasiya jarka ukku, ita da Meerah suka zauna suka fara jibgar wannan wankin koda suka kusan gamawa Ummah tayi tayi da meerah tabarshi ita ta ida ammah tak’i saida suka gama tare.

Suna cikin d’auraye Abbansu Meerah yadawo gidan hannunsa rik’e da leda bakin k’ofa yatsaya yana kallonsu fuskarsa babu alamun walwala nan Sadeek da Safiya da suke wasa duk suka nutsu.
Meerah ce da mahaifiyarta sukayi mashi sannu da zuwa banza yayi masu yanufi d’akinshi yana shiga yak’walah ma ummansu kira, amsawa tayi tatsame hannunta tad’auraye sannan tawuce tanufi d’akinshi.

Tana shiga cike da ladabi tazauna tace gani megida,
Ledar da yashigo da ita yamik’a mata yace ga wannan shinkafa ce gwangwani biyu ga kuma kayan miya nan da nama kije kiyi min shinkafa da miya idan kin gama kiraba abinci kashi ukku kici kashi d’aya kiban kashi biyu.

Kallonsa kawai take ganin yadda yake maganar cikin rashin damuwa, girgiza kai tayi tace megida yaran fa?
Harararta yayi yace ina ruwana wannan ai basu dameniba nakine sai kisan yadda zakiyi da su danni banda kud’in da zan ciyar maki da su ai tun farko daman na fad’a maki, nidai kije kiyi min inkingama kikawo min ki ajiye sannan kikula kar kibari suyi min k’azanta danni wad’annan k’azaman yaran naki banaso suna gittawa inkina girki, yanzu bari infita zuwa anjima zan dawo ana neman mu ne akan screening d’in da za ayi mana nad’aukar ma’aikata.

In dasabo ta saba da halayyarsa dan kusan kullum daman indai zaice tayi mashi girki toh haka yakeyi mata
cikin sanyin jiki tace toh shikenan megida Allah yataimaka yabada sa’a.
Ameen,
Toh saidai baka bada kud’in icce ba.
Kai kedai kinga matsalarki bakida aiki da nace kiyi min girki sai kince kud’i mtsww “yaja tsaki”.
Allah yahuci zuciyarka toh ai ba iccen ne.
Naira d’ari yaciro yamik’a mata yace gashinan in kin siyo sai ki ajiye min canjina.
toh insha Allahu.
Na dai fad’a maki kikiyaye kar k’azaman yaranchan suje min wajen abinci.
Shuru tayi nan tad’auki kayan tafita takardunsa yad’auko shima yaficce fuskarnan a d’aure k’yam dan indai zaiga ‘ya’yannan duk dariyar da yake zaibi yad’aure fuska.

Yana fita Meerah kallon mahaifiyartasu tayi cike da damuwa dan duk ta jiyo maganganun da Abban nasu yayi, ajiye ledojin da yabata tayi tazauna tatisasu a gaba tana kallo.
Duk’awa tayi tana me cigaba da d’aurayar wankin da sukayi har tagama still dai ummanta na zaune.
Matsowa tayi kusa da ita tare da tsugunnawa k’asa tace ummah.
‘Dagowa tayi takalleta tana murmushi tace Meerah har kin gama d’aurayar ko?
Eh ummah dan Allah kidaina sa damuwa aranki akan abinda Abbah yakeyi kar fa kimance ubangiji shi yake taimakonmu.
Shikenan Meerah nima ba damuwa nasa ba kawai ina tunanin wani abune
toh kawo ingyara maki kayan miyan.
kibarshi kawai kid’auki kayan kije kikai ma Hajiya luba tunda a chan za’a shanya mata bari inba Safiya tasiyo min icce.
Toh ummah, nan tamik’e taje tacanza zane sannan tad’auki kayan da sauran sabulum da yarage tace ummah sai na dawo.
adawo lafiya meerah da ido tabi d’iyartata cike da tausayi dan tasan yunwa takeji kawai dai tana daurewa ne.
tana fita tasamu me adaidaita tasaka bokitan kayan yakaita har k’ofar gidan, ma’aikatan gidanne suka taimaka mata suka shigar mata da kayan nan tashanya sannan taje tasamu Hajiya luba zaune tana cin naman kaji shi kuma abincin gashinan a gefe an ajiye alamun anci an k’oshi, duk’awa tayi cikin ladabi tace hajiya anwanko gasu chan na shanya miki.
Mik’ewa tayi da cinyar kaza a hannunta tana yaga tace ina zuwa bari indubo.
daga bakin k’ofa tazauna tana wasa da yatsun hannunta har hajiya luba tadawo saida tazauna mazauninta sannan tace eh ba laifi wanki yayi dan naga fes anwanke k’asan zanen
Murmushi Meerah tayi sannan tad’auko sauran sabulan da aka rage tace Hajiya ga sabulan da suka rage.
Yatsina fuska tayi tace mezanyi dasu kije kawai kinyi wanki da su yanzu ga wannan tamik’a mata d’ari biyar tace kud’in wankin kikai mata.
Hannunta yana rawa takar6a tare da yin godiya tamik’e zata tafi, plate d’in abincin tamik’a mata tace d’an fidda min wannan waje inkuma kinga karnuka kiwatsa masu suci.
kallon abincin tayi taga jalop rice ce me kyau, cikin ranta tace wannan za’a ba karnuka mu muna chan muna neman wanda bai kaisaba,,da toh tabita tafita.
tana fita leda tasamu tajuyo sannan takai plate d’in kitchen takama hanyar gida yanayin tafiyarta kawai zaka gani kagane akwai nutsuwa atare da ita saida tabiya gidan Babah tabiya kud’in kokon da takar6a sannan tawuce gida.

 

 

_Comment_
*Nd*
_Share_

 

 

_Sis Nerja’art✍_🔱🔱🔱🔱🔱🔱

*RANAR NADAMA*

🔱🔱🔱🔱🔱🔱

 

*WRITTEN BY SIS NERJA’ART✍*

 

*INTELLIGENT WRITERS ASSO…®📚*
{On Ward Together}

 

*PAGE 2*

Tana komawa tatarar da Ummanta tana girkin inda su Safiya da Sadeek suke zaune sunyi zuru zuru, cire hijab d’inta tayi tana cewa Sadeek ba dai yunwaba?
Sheshekar kuka yafara yace Aunty Meerah yunwa nikeji.
Toh in yunwa kukeji ai hak’uri zakuyi bakuga na kusa gamawaba da na gama zan zuba maku kuci,,,cewar ummansu.
Ledar da take hannunta tamik’a ma Safiya tace jeki kijuye maku wannan a plate sai kuci.
Cikin jin dad’i safiya ta amsa tace menene a ciki Aunty meerah?
Kije kijuye sai kigani.
Ummah rufe tukunyar miyar tayi tajuyo takalleta tace Meerah menene kika samo masu?
Murmushi tayi tace abinci ne?
Abinci kuma? Siyowa kikayi?
Zama tayi sannan takwashe duk yadda akayi tafad’a ma ummansu.
Jinjina kai ummah tayi tace toh shikenan Allah yasa mudace.
Ameen ummah kud’in fa yaza’ayi da su?
Kicire maku d’ari ukku kud’in wata sauran kuma sai ki ajiye munga abinda za’ayi.
Toh ummah, kawo inkama maki girkin.
A’a Meerah kibarshi kar Abbanku yadawo yayi ta fad’a.
“toh shikenan ummah dan dai kar yayi fad’an da sai inkama”.
Kar kidamu Meerah kije kuci wanchan d’in kafin ingama.
Juyawa tayi takalli su Safiya da suke ta cin abincin hannu baka hannu k’warya tace a’a ummah suci kawai kinga baida wani yawa.
Toh kisiyo ko awara ce kici dan nasan dai yunwa kikeji.
A’a ummah bana jin yunwa.
Toh shikenan.
Bari inje inwanke mana kayanmu da sauran sabulun da hajiya luba tabamu kafin lokacin islamiyya.
Haba Meerah kizauna kihuta mana kibari ko zuwa gobene sai kiyi.
Allah ummah ban gajiba bari kiga yanzu zan gama ai baida yawa.
Toh shikenan Allah yayi miki albarka.
Ameen ummana “Mik’ewa tayi tanufi d’akinsu tad’auko duk kayansu da ba wankakkuba ta ajiye nan tafara sa6awa.

Ummah tana gama girkin zuba mashi nashi tayi a cikin kula wanda yace tad’auka kuma tad’ibar ma su Safiya da sukace basu k’oshiba sauran tazuba a roba tace ma Meerah ta ajiye wankin tazo taci.
Meerah ganin abincin ba wani me yawa bane kuma ummantasu bata ciba yasa tace a’a ummah kici ni gari zan sha idan na gama zan je insiyo na naira goma.
Haba Meerah kinsan banason irin wannan halin taya zanci ke bakiciba kici kawai ni zan ci garin kwakin bari inba safiya tasiyo min ke kizo kici sai kicigaba da wankin.
Allah ummah na k’oshi.

Kai kai kai me nake gani haka mi kika zuba ma yarannan suke ci, ba dai abincin nawa bane kika basu? “Cewar Abbansu da yashigo gidan”.

Safiya saurin ture plate d’in tayi inda Sadeek yajanye hannunshi daga cikin kwanon tare da yin narai narai da ido kamar zaiyi kuka.

Ko bakiji ina tambayarkiba zakiyi min banza?
Haba Megida kaima kasan bazan ta6a bada abincinkaba wanda fa kace inci ne nabasu.

Toh barkanki hakan yayi ke me ‘ya’ya ai sai ki ta zama da yunwar nidai yisauri kikawo min nawa inci inkoma inda nafito dan sauri nake, kallon Sadeek yayi yace wannan yaron sai yatsareni da wad’annan k’wala kwalan idanuwan nasa ka janye idanunka daga kaina ko sai na mazgeka?

Cikin sauri Sadeek yaduk’ar da kansa k’asa.
Wucewa Abbansu yayi yana fad’a yashige d’akinshi.
Ummah girgiza kanta tayi cike da takaicin abinda mijinta yakeyi ma ‘ya’yan nasu, tashi tayi tad’auki abincin nashi tanufi d’akinshi.

Tana zuwa kawai ajiye mashi tayi tajuya zata fita yace au bama zaki zuba man ba dan kin raina ni dakaina zan zuba?
Batare da tayi magana ba taduk’a tana zuba mashi tana gamawa yace yauwa ajiye min sauran chan wajen sai da anjima zan ci.
Ajiyewa tayi tare da d’agowa takalleshi tace shikenan?
Au kuka ma zakiyi me nayi miki da zakiyi min kuka?
Goge k’wallar da tazubo mata tayi tace ni bakayi min komai ba koma me kayi kanka kayi ma ‘ya’ya dai nakane.
Lomar da yasaka bakice yayi saurin had’iyewa yace inji ubanwa yace nawa ne? Naki dai ke kad’ai, da ace kinsan yadda natsani ‘ya’yannan da baki barsu a gidan nan ba.
Tsana fa kace megida?
Eh tsana ko dan bana son ‘ya’ya ban saniba ko nan gaba zanji ina son yara.
Murmushi tayi tace toh Allah yakyauta nidai ina son abuna.
Toh kiyi ta sonsu mana ina ruwana ‘ya’yan ai naki ne daman sai kisamo masu uba.
Jin yana nema ya ida 6ata mata rai yasa tayi saurin juyawa tafita tabar d’akin ko ta kan su Sadeek bata bi ba tashige d’akinta.
Tunda Meerah taga haka tasan maganganun da abbansu yasaba fad’a ma ummansu ne yafad’a yau ma.
Murmushin k’arfin hali tayi tare da maida k’wallar da take shirin fitowaba gudun kar su safiya sugani sudameta da tambayoyin da zasu iya sata kuka, cikin sanyin jiki tacigaba da wankinta chan sai ga abbansu ya fito da plate d’in abincin da yaci abakin k’ofar d’akinshi ya ajiye yamaida d’akin yarufe, ganin zai fita yasa tace abbah adawo lafiya.
Ko ta inda take baibi ba yaficce abunsa.

Tana gama wankin ruwa tazuba tayi wanka jikinta har rawa yake saboda yunwa naira ashirin tad’auka tasiyo garin kwaki tazo tajik’a tasha da sugar.

tana lura da ummansu bata cikin walwala kawai dai tana danne damuwartane, sa su safiya tayi sukayi wanka sunayin sallar la’asar suka kama hanyar islamiyya.

Bayan sun tafi ummah wanke wanke tayi sannan tasha garin da Meerah tajik’a masu.

Bayan sun dawo daga makaranta a tsakar gida suka zauna suna bitar karatun da aka koya masu inda Meerah take gyara ma su safiya inda basuyi daidaiba har aka kira sallar magrib tasasu sukayi alwallah sukaje sukayi sallah.

Suna zaune nan sukaji shigowar Abbansu yana Alhamdulillah Allah abun godiya.

Ummah ce tamik’e tafita fuskarta d’auke da fara’a tace Megida lafiya? Ko ansamu aikin?
Fuskarsa d’auke da murmushi yace kedai bari maryam ai al’amarin ubangiji babbane kinga duk wahalar da mukasha yau ankar6i takardunmu anmana screening ke atak’aice dai ance za’a d’aukemu aiki ance nan da kwana biyu mukoma.

Kai masha Allah ammah gaskiya naji dad’i Allah abun godiya daman haka lamarin ubangiji yake.

Hmm kedai bari kinga yanzu mafarkina saura kad’an yazama gaskiya daman nace maki insha Allahu sai na cika burina nan ba da dad’ewaba zanyi kud’i kinga sai inyi rayuwata cikin farin ciki.

sakin baki tayi tana kallonshi.
Kefa matsalata da ke kita ma mutum wani irin kallo.
Toh me zance megida watau har ma ka hango kayi kud’i tun baka ma fara aikinba nidai shawara zan baka karik’e gaskiya.
Fara’ar da take fuskarsace taragu yace toh toh toh anzo wajen watau bak’in ciki zakiyi min da aikin da zan samu.
Me kuma yakawo abun bak’in ciki megida?
Dakata kar kisaki kimin wata maganar banza watau kina bak’in ciki inyi kud’i in auro mace wadda ra’ayinmu zaizo d’aya tasoni fiye da yadda kike sona, ke alk’ur’an saidai ma kiji haushi ammah ‘yar boko zan aura dan ita tadace da ni da ace baki haifi yarannan ba da k’ila tuni na biya maki kud’i kinyi karatu muncigaba da zamanmu.
Murmushi tayi tace eh kuma kayi gaskiya d’an boko sai ‘yar boko wayayya duk da haka Alhamdulillah nasan ba jahila bace da karatuna bakin gwalgwado sannan bazan ta6a damuwaba koda ace mata ukku zaka k’ara aurowa kakawo gidannan tunda ba saman kaina zasu zaunaba.
Hehehe lallai sannu marar kishi toh shikenan zakigani zan baki mamaki bari dai burina ya ida cika.
Allah ubangiji yacika maka burin naka “tunowa da a tsakar gida suke yasa tajuya tawuce d’akinta saboda bataso tana biye mashi a gaban yaransu”
Tana shiga tasamesu zaune jugum sunyi shuru kallon Meerah tayi tace Meerah miye na tagumi kuma?
Bakomai Ummah.
Toh kidaina babu kyau.
Toh.
“Ummah wai meyasa Abbah kullum sai ya yi maki fad’a?”
Sadeek ba fad’a yayi min ba magana ce muke.
Toh ummah idan nagirma nayi kud’i zan siya maki mota da gida.
Zama tayi tana murmushi tace Allah yasa Sadeek d’ina.
Nikuma ummah zan kaiki makka inbaki kud’i masu yawa.
Yauwa Fiya kice zaku maida ni hajiya.
Sosai ma ummah sai kinje makka sau goma.
Toh Allah ya ida nufi.
Kefa Yaya Meerah me zakiyi ma ummanmu? Cewar Sadeek.
Murmushi tayi tace komai na farin ciki da jin dad’in rayuwa ina da burin inyi ma ummana domin itace komai nawa.
Cikin jin dad’i ummah tace nagode sosai Meerah Allah ya ida nufi, shima mahaifinku inaso yaci moriyarku yasan ku ‘ya’yan halas ne.
ammah ummah shi fa baya sonmu.
A’a safiya yana sonku kucigaba da yi mashi addu’a Allah yasa yagane gaskiya.
Ameen ya rabbi “sukace gabad’aya”

Washe gari bayan sun tashi kasancewar Monday ce Meerah shiryawa sukayi saida sukasha koko sannan sukayi ma ummansu sallama suka kama hanyar makarantar boko.
Saida suka biya suka kai Sadeek makarantarsu ta primary da batada nisa da tasu sannan suka wuce tasu makarantar a JSS section Safiya ta shige inda Meerah tawuce SS section tana shiga har ta wuce taji ana k’wala mata kira ta baya.
murmushi tayi tatsaya jin muryar k’awarta har ta iso suka sakar ma juna murmushi nan Meerah tamik’a mata hannu suka gaisa, K’awarta Sa’adatu tace Ameerah kwana biyu kin 6oye.
Kedai bari sa’adatu kinsan weekend sai a slow lokacin hutu ne kuma ga islamiyya.
Duk da haka dai kyau ace kina d’an lek’oni watau daman dan ind’auke k’afa da zuwa gidanku saisa baki zuwa namu gidan.
A’a Sa’adatu ba haka bane kinsan yanayin abun.
kullum haka kike cewa har gashi muna shirin gama school nan da watanni.
Ganin students ana korasu Assembly hole yasa suma suka wuce cikin sauri suka nufi hole d’in.
Suna isa nan sukabi layi kowa yanutsu aka fara assembly ana gamawa suka wuce suka nufi class d’insu, tunda suka zauna Meerah shuru tayi kasancewar magana bata cika damuntaba Sa’adatu tun tana magana ganin bata cika maido mata da amsaba yasa tatashi takoma sit d’in gabansu tazauna suna hira har saida malam yashigo sannan tatashi takoma sit d’insu.

Malam Sani bin class d’in yayi da kallo yace ina class captain?
Mik’ewa Meerah tayi tace yes Sir.
ammah yau baku share class d’innan nakuba why?
Shuru tayi tarasa mezatace dan tasan har da rashin zuwanta dawuri yasa ba’ayi sharaba.
ko bakiji me naceba?
Muryarta tana rawa tace Sorry Sir today i came late dan time d’in da nazo ana assembly.
Heee! u ar a class captain but kina late, why are you came late?
Shuru tayi.
Oya nabada 5 minutes ayi sauri ashare class d’innan kafin indawo
Ohk Sir Thanks
Yana fita kallon ‘yan class d’in tayi tace masu shara yau sufito suyi kun dai ji abinda yace,,, komawa tayi tazauna batare da tak’ara cewa komai ba.
Ganin haka yasa sa’adatu tamik’e tace ko bakuji abinda akace ba masu shara sufito.
Fara tashi sukayi suka fita suna d’aukar tsintsiya dan sunsan Assistant Class captain Sa’adatu mafad’aciya ce.
Tashi sauran ‘yan class d’in sukayi duk suka fita nan aka fara sharar.
Har suka gama sharar bai dawoba Sa’adatu tace Meerah kodai za’aje akirashi kinji shuru har kusan 20 minutes bai dawoba
Hmm uhm nidai babu inda zanje dan banson zuwa wannan staff room d’in nasu.
Toh ai tare zamuje.
Sai kin dawo nidai bazanjeba.
Toh sarkin tsoro kedai kin cika tsoro kamar cinyeki zasuyi.
Banza Meerah tayi mata batare da ta k’ara kulataba.
Wucewa Sa’adatu tayi tafita taje takirashi.
Dawowa tayi tace ya ce bazaizoba saboda yanzu saura 10 minutes yarage period d’insa yafita dan haka kowa yayi nazarin littafinsa.
Nan class d’in aka fara surutu wasu suna murna akan rashin zuwansa inda wasu suke ficcewa.
Ta6e baki Meerah tayi tace Allah dai yakyauta.
Kekuma me kike ma Allah yakyauta “cewar sa’adatu”
Toh ai naga daman ba son shigowar yakeba yanzu ya samu mafaka sai yace bamuyi sharaba ina ma amfanin irin haka mutum yayi ta cin albashi ammah baya aiki yaci haram.
Dariya sa’adatu tayi tace haram fa kikace?
eh man kina gani malaman nan d’aid’ayane suke k’iyaye k’a’idar shiga sukoya yadda yakama mancewa suke da ubangiji zaiyi masu hisabi akan haka dan ko naira d’aya kaci ba ta ji6inkaba toh akwai ranar hisabi.
Hakane kuma musamman ma malaman nan namu na makarantar gwamnati ba kowane yake kiyayewaba, ni takaicina duka baifi 5 months muyi SSCE ba ammah duk akwai abubuwa dadama da ba’ayi manaba.
Toh ai kinga sauk’inma muna zuwa library muyi searching da badan haka ba da bansan yadda zamuyiba,
Kuma kinga kad’anne daga cikinmu suke hakan sauran ko duk basu damuba wasansu kawai suke da anyi masu magana sai suce ai ba kud’in iyayensu bane gwamnati ce tabiya da ace na iyayensu ne da sunfi maida hankali.
Ai saisa akafi raina makarantunmu na gwamnati ammah fa ba laifi muna samun koyarwa mekyau ga wasu malaman ga yawanci malamanmu suna da ilimi sosai.

Shigowar malaminsu me second period ne yasa suka katse hirar tasu suka nutsu.

Bayan sun tashi tare da sa’adatu suka fita suka nufi gida suna tafiya suna hira sama sama dan alokacin Safiya har ta tashi kasancewar k’arfe d’aya suke tashi sai tabiya tad’auko Sadeek suwuce gida.

Suna cikin tafiya sai ji sukayi kamar ana binsu a baya, sharewa sukayi suka cigaba da tafiyarsu sai ji sukayi anmasu sallama Meerah tsuke fuska tayi batare da ta amsaba, sa’adatu ce kawai ta amsa tare da kallon Meerah dan tasan halin mutuniyartata lokaci guda take canza fuska indai za’a nemi atsaidasu suna cikin tafiya.
wani saurayine yamatso yana murmushi yace ma sa’adatu sannu ‘yanmata.
Yamitsa fuska tayi tace sannunka.
dan Allah indai ba damuwa inason magana da wannan k’awartaki.
kallon Meerah tayi da ta ida had’e fuska tana mecigaba da tafiya tace malam kayi hak’uri matar aurece.
Haba malama nima ai mijin aurene.
Toh ai sai kayitayi mu bamuda lokacinka.
K’ara sauri sukayi suka barshi nan tsaye cike da takaici dan yaso yayi ma Meerah magana ammah baiga fuskaba.

Gaskiya k’awata kin iya shan k’amshi idan kikaga maza saikace kinga dodonni.
yoh miye inba dodonninba haba saikace mayu sudai idonsu idon mata.
Kai Meerah ai ba duka aka zama d’ayaba.
oho dai.
Ya dai kamata kifara kulasu kar mugama makaranta ace kifito da miji nidai kinga na kama dahir da mun gama za’ayi bikkinmu da Auwal.
Murmushi Meerah tayi tace kod’aya aure baya agabana sa’adatu ni burina d’aya shine da nagama incigaba da karatu har incimma abinda nake buri.
Chab ke babba ce toh miye burin da kikeso kicimma?
Wannan kuma sai lokacin yayi zaki ganema idonki.
toh Doctor Meerah Allah ya ida nufi dan nasan shine babban burinki kiga kin zama likita, mudai karatunmu yana a gidan mazajenmu dan ni aure nafiso.
Ameen ya rabbi, kudai da anyi magana sai aure ke ni kwatakwata aure baya gabana dan maza duk basuda amana.
Ke Meerah wa yafad’a maki haka ai ba duka aka taru aka zama d’ayaba saidai inbaki dace da masoyin gaskiyaba da zaki gwada da kinji dad’in soyayya.
keda tadama sai kiyi ta yi ammah ni bana burin hakan, yanzu dai shige kwanarku kar garin surutu kiyi ta zurawa.
Dariya Sa’adatu tayi tace toh ai dole na ji abun naki babbane.
Sai dasafe malama danni ba zan tsaya hiraba gida zani.
Toh Meerah Allah yakaimu nima ai ba hirar zanjakiba saboda yunwa nakeji so nake naje gida inci abinci.

Sunayin sallama Meerah cigaba da tafiyarta tayi a nutse har ta isa gida, tana isa lokacin abbansu yana zaune a waje yana kallon Titi, cike da girmamawa taduk’a tace Abbah barka da hutawa.
Cikin tsawa yace dallah tashi kiban waje watau munafurci zakiyi min ubanme zan baki?
Cikin sauri tamik’e tace kayi hak’uri Abbah babu abinda zaka bani.
Mtsw munafurcin banza ke adole ga uwar ladabi, kin 6ace min da gani ko sai na taso.
cikin sauri tashige gida tana mamakin halin abban nata cikin ranta tace Allah yaso babu mutane a wajen da sai naji kunya.
tana shiga tasamu su ummah zaune suna shan fate, cire hijab d’inta tayi tare da tsugunnawa tace sannu ummah barka da gida.
Yauwa Meerah sannu da dawowa, ya makarantar?
Alhamdulillah
masha Allah, Allah yataimaka.
ameen ummah.
Aunty Meerah sannu da dawowa.
yauwa Safiya da sadeek kun dawo kuma ko?
Eh Aunty Meerah mun rigaki dawowa yau ma.
Ai haka nakeso sadeek kudinga rigana dawowa kuci abincin ummah.
wai hayaniyar me naji abbanku yana yi a waje?.
murmushi tayi tace bakomai umma.
Ba dan ta yadda da maganartaba tace tashi kije kicire kayan kizo kid’auko fatenki kisha.
mik’ewa tayi tace ai har wanka sai nayi tukun.
toh shikenan kimaida hankali kigama kizo kici dan nasan kina jin yunwa.
toh ummah bari inyi sauri, nan tawuce d’akinsu.

Cire kayan tayi tafiddo tawanke sannan tafad’a wanka bayan ta fito saida tayi alwallah tajw tashirya sannan tafito tad’auko abincinta tazauna taci.

Bayan ta gama shiryawa tayi tasa su Safiya suka shirya sunayin sallar la’asar suka kama hanyar islamiyya.

Ummansu tana ganin sun fita tatashi taje d’akin abbansu da taji ya shigo lokacin yana zaune yana fiffita da mafeci, ganinta yasa yace toh ya akayi?
Murmushi tayi tace megida ko sallama fa baka amsa min ba.
Na amsa saidai inkece bakijiba Allah yasa ba kud’i zaki ce inbakiba dan banda su.
kallon kud’in da ya ajiye gefenshi tayi sannan tagirgiza kai tace a’a ni basu suka kawoniba dan Allah inaso inje gidan Hajiya binta.
Me akeyi gidan hajiya binta?
Zumunci.
Aikin kenan yawo gida gida daman taya zaki iya rik’e yara duk gashinan kin fita hayyacinki saboda neman kud’i indai suka gaji da rok’on da kikeyi masu ai sun koroki.
Nidai tambayarka nayi inje ko a’a?
Kiyi ta tafiya mana ni ina ruwana ammah kar kisaki kikai dare.
toh nagode, nan tajuya tafita.

Tana komawa d’akinta hijab d’inta tasaka tarufo d’akin tafito a k’asa tataka kasancewar daga layinsu zuwa nasu babu nisa sosai.
Tana isa sallama tayi saida tayi sallama sau biyu sannan aka amsa mata tare da cewa ashigo.
shiga tayi tasameta zaune a parlournta ganinta yasa hajiya binta tad’an rage fara’ar da take fuskarta tace au da kece?
Zama tayi tace eh nice Hajiya Binta ya gidan?
Lafiya, ya yara?
Alhamdulillah.
ina fata dai lafiya naganki a wannan lokacin.
murmushi tayi tace kai Haj binta lafiya ce man takawo ni.
Toh ai shikenan dan da na ganki sai hankalina ya tashi.
Murmushi kawai tayi dan indasabo tasaba da halin ‘yar uwartata da gabad’aya inzatazo wajenta sai ta canza mata fuska saisa ma su Meerah basu son zuwa in ba ita tamatsa masuba akan suzo sugaishe da ‘yar uwartata.
Gashi abinci ya k’are saidai and’aura na dare “tafad’a atak’aice”.
a’a ni a k’oshe nake Alhamdulillah.
toh ai shikenan, rannan na gamu da wannan mijin naki baice miki ina gaisheki ba?
A’a ni bai fad’a min ba ammah Binta shine ko kishigo mugaisa sai kiwuce zumunci fa ba abun wasa bane.
kinsan dai yanayin hidimata ba kowane lokaci nake gidaba.
Ammah ai kina zuwa gidan Yaya Muh’d shi dan yana da rufin asirinsa ko?.
Toh ai shi namijine kuma yayane kefa k’anwace taya zan rik’a zuwa gidanki.
Murmushi tayi cike da takaici tace shikenan dai ammah inaso kisani shi zumunci bashi ga me kud’i bai ga talakka sannan babu ruwanshi da k’arami ko babba, iyayenmu da suna raye akullum shawarar da suke bamu akan murik’e zumunci ammah kwatakwata bakuson ayi nice kawai nake k’ok’arin lek’o ku.
kema ai saboda baki da shi saisa kike zuwa inda muke, ammah ni da yaya muhd muna k’ok’arin lek’a juna dan matarsa ma tana zuwan min nan.
Matar yaya muhd d’in?
Eh man.
Shuru tayi batace komai ba “dan ita takwakwata bai ta6a lek’a gidantaba bare matarsa ko yaranshi”.
Kinga ko mu muke zumunci.
Hakane Allah yabar zumunci, yanzu bari intashi intafi gida dan yara sun kusa dawowa.
Toh shikenan akwai fa tsaki idan kina so ind’auko maki dan kinsan ni ba amfani nake da shi ba tuwo kawai muke da garin.
Eh inaso man ko dambu munyi da fate.
toh shikenan bari inkawo maki.
Zama tayi tana jiran yayartata chan tadawo d’auke da wata leda kusan cike da tsaki sai gudar kuma tamik’a mata tace ga garin kwaki nan sai kik’ara da shi dan yara suka matsa asiyo masu ammah sunce bai masu dad’iba tsami gsreshi shine suka daina sha Allah yasa ma baiyi komai ba.
Murmushi tayi tace toh nagode sosai.
Dari biyar tad’auko tabata tace wannan kuma kinyi amfani da ita.
Ta yi mamaki sosai dan tunda take da ita wannan ne karo nafarko da tata6a bata d’ari biyar, godiya tayi mata sannan tatashi tad’auki ledojin tafita.
Agaida gida kawai Hajiya Binta tace mata batare da ta d’an rakataba, bata damu da hakan ba daman in da sabo ta saba da halin ‘yar uwartata da kwatakwata bata ma so ace ‘yar uwartace saboda ita talakka ce, ita kuma tana auren miji me kud’i.

Tana komawa gida tatarar da mijin nata zai fita yace har andawo daga maular.
Eh Megida na dawo tunda kai baka iya bamu ai gwara muje muyi maular.
Hakan ya yi kin kyauta nidai bazan ta6a badawaba.
Ta6e baki tayi tawuce d’akinta.

Koda su Meerah suka dawo daga islamiyya ganin tsaki da kwaki yasa tace ummah ina muka samu wannan?.
Gidan hajiya Binta.
fara’ar da take fuskar Meerah ce taragu tace kai ummah wallahi banso kikajeba matar da kwatakwata bata zuwa gidan nan sannan bata ganin mutuncinki bare na ‘ya’yanki.
Meerah sai naje ai ‘yar uwatace koda ace tana yankan naman jikina bazan ta6a barintaba dan banaso zumuncin mu yawatse.
zumunci kuma? tun yaushe ummah su fa basu taka inda kike saidai ke kike zuwa.
toh ya zanyi wannan kuma matsalarsu ce nidai Allah yana gani inayi domin shi, kar kusaki kudinga duba da yanayin mutum meerah ku dai duk abinda zakuyi kudinga yi saboda Allah.
Tausayin ummanta duk yakamata dan tasan ita tana son ‘yan uwan nata biyu sosai, “tace toh ummah insha Allahu muma zamuyi koyi da ke”
Yauwa Allah yayi maku albarka, yanzu zo kije kisiyo mana rogo da k’uli muk’wad’a muci ko ma kiba safiya kawai tasiyo.
Ummah bari kawai inje kinsan safiya da ta fita sai ta tsaya wasa.
Hakane kuma toh yi sauri kinga magrib ta gabato.

Leave a Comment