7/1, 9:48 AM] Hassana Ɗanlarabawa🌹: *BAGAHON LAYI*
(SABON SALO)
BABI NA ƊAYA DA NA BIYU
©️Hassana Ɗanlarabawa.
EXQUISITE WRITERS FORUM
*AlhamduLillah! A karo na biyu ga ni na dawo cikin labarin BAHAGON LAYI (SABON SALO). Cigaban labarin Bahagon layi na farko, ina fatan za ku karɓe shi fiye da yadda kuka karɓi na farko, wajen kwararo sharhi kan labarin. Sannan ina roƙon waɗanda suke son tarawa su tara wa kansu, ba na son na yi nisa ai ta tambayata ana so daga farko, ba zan iya hanawa ba amma tabbas ina takura, gwara mutum ya fara karantawa tun yanzu. Ban yi alƙawarin dogon feji ko posting kullum ba, yadda ya samu ku karanta haɗe da uzuri, na gode.*
Gandamemiyar muryarsa ce ta karaɗe gidan a lokacin da yake ƙwala mata kira kamar na farauta.
“Angayu! Angayu! Angayu!”
Kiran da Malam Arabi ke ta ƙwalla wa matarsa kenan da ƙarfi cikin ɗaga murya. Sai daga can ta amsa sannan ta fito daga ɗakinta zuwa tsakar gidan da yake a hargitse da kaya ko’ina a watse, ya dube ta ya ga yadda jikinta ya yi butu-butu da ƙura, amma duk da hakan jagirar nan raɗau a fuskarta ta kalli gabas, tuƙeƙiya da ita kamar wadda aka zana ta da gatari. Fuskar nan tana maiƙo ta lafta basilin (Mai gurguwa), ga kwalli ma sha Allah ta rambaɗa kamar wadda za ta tafi tallan ganda, ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya abin ta cokalele a gaban goshi. Gaban Malam Arabi ta tsaya tana karkaɗa masa idanu wai ita fari take yi, ya dube ta daga sama har ƙasa ya tuntsire da dariya har da riƙe ciki.
Ta tsaya tana kallon shi yana ta dariya, da dai ta ga dariyar ta ƙi ƙarewa sai ta juya a fusace ta yi hanyar banɗakin tsakar gian ko takalmi babu a ƙafarta, ta je in da ta ajiye tsintsiyar kwakwarta ta ɗauka ta zari sili ɗaya ta nufo shi, tana zuwa ta miƙa masa tsinken tana riƙe da ƙugu da hannu ɗaya tana girgiza jiki, ya bi ta da kallo kafin ya fara ƙunshe dariyarsa, ya yi mata alamar tambaya da hannunsa kan me zai yi da tsinken?
Cikin ƙufula ta fara magana.
“Ka karɓa ka cire abin da kake wa dariya a jikina kawai Malam.”
Babu ɓata lokaci ya ƙarɓi tsinken wata dariyar na ƙara zuwar masa, kamar gaske ya ce.
“Rufe idanuwanki Angayuna, yanzu za ki ga abin da zan cire miki kuwa. Wanda ya saka ni dariya.”
Ta rufe idanuwan babu musu tana jiran ganin abin da zai yi, duk da uwar kwalliyar da ta zauna ta ɓata lokaci ta yi domin ya yaba amma don wulaƙanci yake mata dariya. Malam Arabi ya matsa dab da ita ya ɗaga tsinken ya zurkuɗa mata cikin hancinta, ta yi baya da sauri saboda raɗaɗin da ya ratsa ta tana kurma ihu, amma sai da ya samu nasarar ciro wani danƙareren curarren tasono da ya cike mata hanci.
Ta buɗe idanu a razane tana kallon shi, cikin masifa ta ce.
“Malam wai kashe ni kake so ka yi daman? Daga ba ka tsinke ka cire abin da kake wa dariya a jikina sai ka burma mini shi a hanci? To ko dai baƙin-ciki kake da hancina don ka ga nawa ya fi naka tsayi ko?”
Malam Arabi ya ɗago mata tsinken mai ɗauke da tasono yana nuna mata, ta yatsina fuska tana murguɗa baki ta ce.
“Mene ne wannan kuma?”
Yayi murmushi ya ce.
“Abin da na cire a jikinki ne da yake saka ni dariya. Ke yanzu don girman Allah nan fa wai kwalliya kika yi ko? Hanci fal tasono da majina, wai don Allah Angayu yaushe za ki nutsu ki koma tsaf kamar sauran mata ne? Ke sai son kwalliyar amma sam ba ki iya ba, mu nan malamai da kika gan mu babu abin da muke so irin mu ga matayenmu sun yi tsaf da su, saboda muna shiga cikin matayen Aljanu muna ganin yadda suke ɗaukar wanka, amma ni kullum na zo gidana sai dai tasono ya amsa mini sallama ta, kai Allah dai Ya kyauta halinki Angayu.”
Angayu ta ƙyalƙyale da dariya tana dukan cinya sannan ta dube shi ta ce.
“Au wai daman abin da kake wa dariya kenan? To ai ni ina sane na bar shi, domin wata ƙawata ce ta ba ni wani sirri, ta ce mini akwai fa’ida ga mata waɗanda suke barin tasono a hancinsu har mazajensu su gani, wai wani sirri ne na daban Malam!”
Malam Arabi ya riƙe haɓa yana shafa gemunsa cikin takaici ya ce.
“Ita kuwa wannan ƙawar taki a wane gidan mahaukatan take?”
Angayu ta zaro idanu ta ce.
“Gidan mahaukata kuma Malam? Billahillazi mai hankali ce ragas take!”
Ya harare ta yana zabga tsaki, sannan ya magantu.
“Wallahi ƙarya ne Angayu! Duk inda ta fito daga yankin mahaukata take. A rasa da abin da za a birge miji sai kwalliya da tasono? Wannan wane irin hauka ne?”
Ta ɗan yi shiru, sai kuma can ta tuna abin da ya ce a lokacin, kawai sai ta kwashe da dariya, ya kalle ta sosai ya ce.
“Dariyar me kike yi Angayu?”
Tana dariyar ba ta daina ba ta ba shi amsa.
“Malam ji na yi ka ce kuna ganin yadda matan Aljanu suke ɗaukar wanka da kwalliya, shi ne na ce mai zai hana ka kai ni su koya mini ni ma na dinga yi maka? Idan kuma ba za ka kai ni ba sai na je wajen Habiban Babalalo ta raka ni, na san ba za ta rasa sanin wajen ba ko?”
Malam Arabi ya sake danƙara mata harara da sakin tsaki ya ce.
“Wato dai tunda kika jiyo gulmar abin da ya faru tsakanina da shegiyar matar nan da ta cije ni a al’aura kika sa mini ido ko? To ai na gode wa Allah da cikin ƙanƙanin lokaci Allah ya yi mini sakayya, kuma duk da haka ban haƙura ba, ke nake so ki ɗauko mini fansar ke ta mini haddi da ta yi ta cije ni a al’aurata saboda ita tsinanniya ce! Kinga dai yanzu yau za mu koma bahagon layin da zama, to ina so ki shiga jikinta a hankali har ku saba sosai domin ki ɗauko mini fansa, yanzun nan mai kura zai zo ya fara ɗibar kayanmu ya kai BAHAGON LAYIN. Gidan da Ƙasimu ya tashi nan na kama mana tunda mai gidan nan ya uzzura mini na tashi zai yi bikin ɗan sa ya saka shi a cikin gidan nan.”
Angayu ta yi shewa ta ce.
“Ai kuwa an gama Malam, bari na shiga na ƙarasa fitowa da ‘yan komatsaina.”
Ya girgiza kai yana saɓa malum-malum ɗinsa da take rinjayar shi. Daga can waje ya ji ana rafka sallama da faɗin ma su kura sun iso don ɗiban kaya, da hanzari ya fice ya shigo da su, suka fara jidar kaya suna lodawa a kura domin tafiya za su tare a BAHAGON LAYI.
******
Harira ce durƙushe gaban mahaifiyar Sunusi tana ta rafka kuka da hawaye da majina shaɓe-shaɓe, har dai Inna ta gaji da jin kukan ta ɗaga kai ta kalle ta fuskarta cike da jimami, da ƙyar ta ce.
“Yanzu Harira ba za ki daina wannan kukan haka ba? Ki yi haƙuri mu ci gaba da zamanmu a nan mana, kinga dai zaman ki ke da Amina a gida ɗaya ba zai yiwu ba, saboda ba za ku zauna lafiya ba tunda ba shiri kuke yi ba. Harira na san halinki na tsokana, ita kuma Amina ba haƙuri ne da ita ba, ke yanzu ma ban da abin ki yadda gidan yake ƙarami ina zai saka ki ki zauna?”
Harira ta ɗaga kai tana kuka sosai ta fara magana.
“Wallahi Inna na gyara halina za mu zauna lafiya ƙalau ni da Amarya Amina, kuma ni ko wannan ƙaramin ɗakin da muke ajiye shirgi na yarda zan zauna a ciki, kuma babu wata rigima da za ki ji ta ɓullo tsakanina da Amina. Na yi miki alƙawari in sha Allah!”
Inna ta girgiza kai kawai, don ta san halin Harira tsaf sai dai ta ba wa wasu labari, shakiyyiya ce lamba ɗaya, za ta yi magana kenan Sunusi ya ɗaya labulen ɗakin Innar ya shiga da sallama.
Comments
share
Pls
*TALLAH!*
Sabon littafina mai suna *Mayafin Sharri:* Labari ne da ya bambanta da salon labaran da kuka saba karantawa, saboda yana ɗauke da sarƙaƙiyar da warwarare ta sai ni da zan jagoranci jan ragamar labarin. Akwai tarin muhimman abubuwa da za ku ƙaru da su. Idan kun shirya ni ma na shirya!
Za ku karanta labarin MAYAFIN SHARRI ne akan kuɗi ƙalilan wanda bai wuce Naira ɗari uku kacal ba (300) daga farkon labarin har zuwa ƙarshe, ga wanda yake da buƙata zai iya tuntuɓata kan lambar wayata kamar haka:
08080049548
Ko kuma kai tsaye a tura kuɗin ta wannan account.
0557998068 Hassana Labaran GT bank. Sai a tura mini shaidar biyan ta lambar wayata, ga waɗanda ba su da account za su iya turo katin waya na 300, amma MTN.
Na gode.
08080049548.
[7/1, 10:57 AM] Hassana Ɗanlarabawa🌹: I just published “BAHAGON LAYI (SABON SALO) BABI NA 3&4” of my story “BAHAGON LAYI (SABON SALO)”. https://www.wattpad.com/1242143368?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Hassy3333&wp_originator=C%2FsqYJShCWknnNybGyE7%2FDsuEuDscwjb8nFxgK6q5f0BuUe09txFPlVuEA7ti3jicySX64huwtXCg8j9hn8S%2BQr4xWgVdvWYmWgOwaGk51PWNOhHXDgGeBjS%2BHk6VNUK
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
BABI NA UKU DA NA HUƊU
©️Hassana Ɗanlarabawa.
EXQUISITE WRITERS FORUM
Inna ta amsa wa Sunusi sallamar da ya yi, ya ɗaga labulen tare da shiga ɗakin ya nemi waje ya zauna, kansa a sunkuye ya gai da Inna, ta amsa tana kallon shi. Ya waiwaya ya dubi Harira da ke gursheƙen kuka tana wage baki kamar sabon rami, ga wawulon bakinta ya daɗa faɗi ya wani wargaje. Ɗauke kansa ya yi ya mai da kallon shi kan Inna ya gyara zama ya ce.
“Inna lafiya kuwa wannan babbar kwabon ta zo ta saka ki a gaba tana kuka da ɓare baki?”
Inna ta sauke numfashi ta ce.
“Wallahi ni dai ɗannan na rasa ya zan yi da rigimar Harira, gabaɗaya ta ɗaga hankalinta akan tana son koma wa gidanta su zauna da Amaryarka tare, duk yadda na so na nuna mata gara zaman ta a gidan nan taƙi ganewa, tun abin ba ya damu na har tausayin ta ya fara ratsa ni a kan nadamar da ta yi.”
Da sauri Sunusi ya ɗaga kansa ya dubi Harira ya zabga mata wata arniyar harara. Sannan ya mai da kallon shi kan Inna fuskarsa babu walwala, a rikice ya fara magana.
“Wai shin Inna ba mun gama magana tun shekaran jiya a kan hakan ba? Na faɗa miki a yanzu Harira ba ta da gurbi a cikin gidana. Lafiya ƙalau nake zaune da Amina tsawon sati biyu da aurenmu kenan, amma wallahi Inna da zarar Harira ta koma gidan nan na san ba za ta bari a zauna lafiya ba, gara ta yi zaman ta a nan tare da ke zai fi kwanciyar hankali kawai, domin ba na son fitina haƙurina ya ƙare kan Harira.”
Harira tana jin abin da ya ce ta miƙ a gigice ta ƙara fasa kuka da mugun ƙarfi har ta razana su, ba ta yi wata-wata ba ta afka jikin Inna da ƙarfi tana ihu, har ta bugawa Innan gingimemen kanta a baki. Inna da azaba ta ratsa ta ta tunkuɗe Harira da ɗan ragowar ƙarfin da ya rage mata, saboda yadda ta ji dadashin bakinta ya ɗauki zugi, ragowar haƙoran ƙasa sun daki dadashin sama. Harira ta faɗo ƙasa ba ta tsinci kanta a ko’ina ba sai cinyar Sunusi a baje, da sauri ya ingije ta daga jikinsa ta bugo da garu, yana sakin tsaki ya mai da hankalinsa kan Inna da ta riƙe bakinta tana zazzare idanu saboda raɗaɗin da ke ratsa bakinta da kwanyarta, hankalin Sunusi a tashe ya ce.
“Sannu Inna! Allah ya sa dai ba ta ji miki ciwo ba? Ta kafa miki wannan ƙaton kan nata mai kama da duro!”
Da ƙyar Inna ta iya magana idanu a warwaje.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un! Harira ɗan ragowar bakin nawa na tsufa za ki ƙarasa mini? Me ya sa ba kya aiki da hankali da lura ne? Yanzu saboda Allah jikina fa tamkar na yara yake, bai kamata ki rufto mini a ka ba, ga shi nan za ki ruɓa mini ɗan ragowar bakina na taunar goro.”
Sunusi cikin ɓacin rai ya fara magana.
“To Inna ke ma dai ga shi nan a gaban ki ta gwada miki halinta irin na akuyoyi, so take yadda bakinta ya zama duk giɓi ke ma ta ƙarasa miki haƙoran ƙasa, muguwa azzaluma kawai! Wallahi ni Inna ba don kin takura ba da tun a wancan lokacin na sake ta, gabaɗaya zama da ita ya fice mini a raina Inna.”
Harira ta kuma ɗora hannu a ka ta zunduma ihu, yayin da Inna ta dubi Sunusi ta ce.
“Kul! Kar na sake jin maganar saki a bakinka, kai da Harira mutu ka raba takalmin kaza, ka ga dai Harira marainiya ce tilas ka yi haƙuri da ita da halayenta, ni dai ina tausayin marayan mutum ka sani, ka yi wa Allah Sunusi ka yafe mata ka sake ba ta dama ta ƙarshe, ka mayar da ita wancan gidan tunda ta yi alƙawarin gyara halayenta, in sha Allahu za ku zauna lafiya da juna ka ji ɗan albarka.”
Sunusi dai ransa bai so ba, babu yadda zai yi da Inna ne, amma tabbas mayar da Harira gidansa na nufin dawowar tarnaƙi cikin duniyarsa, ba don ya so ba ya girgiza kai ya ce da Inna.
“Shi kenan Inna ba zan iya ƙetare umarnin ki ba, na haƙura zan mayar da ita can ɗin, amma sai nan da kwana biyu saboda ina so mu tattauna maganar da Amarya Amina, domin mu ga yadda za mu ɓullowa lamarin.”
A take Harira ta fara share hawaye tana ɓangala dariya cike da murna. Sunusi ya danƙara mata harara, yayin da Inna ta yi murmushi cike da farin-ciki ta dubi Sunusi ta ce.
“Yauwa ɗan albarka ai kuwa na gode, kuma na yi murna da ka amince da magana ta, Allah Ya yi maka albarka, kuma ina so bayan ta koma ka sa rana ka kai ta Asibiti a saka mata haƙoran roba Sunusi, ba daɗi tai ta zama baki duk wawulo, idan aka dube ta a ka dube ni sai a za ci shekarunmu ɗaya fa.”
Dariya Harira ta saka, suka waiwaya suna kallonta cike da mamaki, Inna ke tambayar ta .
“Lafiyar ki Harira kike dariya?”
Harira ta kuma fashewa da dariya ta ce.
“Wallahi Inna wani abu na tuno, lokacin da azzalumin ɗansandan nan yake jibgarmu da kulki ya za ci ni tsohuwa ce, har da ce mini wai don kutumar ubana tsofai-tsofai da ni amma ina shiga cikin yara, kai gaskiya wannan ofisan bai da imani ko kaɗan wallahi, da ya yi wani tsalle ya dira kan ƙafar Habiban Babalalo ji kuke ɓararassss! Ya karya mata agara.”
Inna ta yi dariya tana girgiza kai, shi kam Sunusi mugun tsaki ya ja yana ƙara jin tsanar Harira a zuciyarsa fiye da baya.
******
Da daddare misalin ƙarfe tara na dare Sununsi zaune a falo kan kujera, yayin da Amaryarsa Amina take zaune a ƙasa tana matsa masa ƙafafuwansa, zuciyarsa tana ta bugawa yana so ya yi mata zancen dawowar Harira gidan yana jin tsoro matua, amma hakan ya daure ya yi gyaran murya yana murmushi ya fara bin ta da daɗin baki da kirari.
“Amarya ba kya laifi ko kin kashe ɗan masu gida!”
Amina ta washe baki ta yi fari da idanuwanta tana jin daɗin kirarin da Sunusi ya yi mata, shi kam ya dinga more wa kallon ta jibgegiya da ita a gabansa jikinta duk tsoka, duk in da ya duma hannu ya ji abubuwa sun cika masa hannu lumus! Ba irin Harira ƙeƙasasshiya da ko naman kirki babu a jikinta ba, sai ƙashi da tarin jijiyoyi raɗa-raɗa.
Can dai ya numfasa a ɗarare ya ce .
“Amaryata magana nake so mu yi ni da ke, dafatan za ki ba ni haɗin kai ki fuskance ni, sannan ki taya ni yi wa mahaifiyata biyayya a bisa abin da ta umarce ni da aikatawa?”
Amina ta yi ƙasa da idanuwanta cikin kunya tana murmushi, ya kalli saman idanuwanta sun sha eye shadow malam abin gwanin sha’awa, ta kuma ɗago idanuwanta ta sauke su a kansa ta na ci gaba da mammatsa masa ƙafafuwansa da hannuwanta masu cike da nama, sannan ta kalmashe murya ta ce.
“Kar ka samu damuwa, kai fa tamkar sarki ne! Ni kuma jakadiyarka, ka ga kuwa duk abin da ka umarce ni shi zan aikata babu musu!”
Sunusi ya ji kansa ya kumbura suntum! A ransa mamaki ya ke yi daman yana da irin wannan darajar bai taɓa sani ba? Ashe shi cikakken namiji ne amma Harira take mayar da shi aljihun baya? Sosai ya kwaye baki yana dariyar murna ya ce.
“Amma na ji daɗin batunki Amaryata, hakan ya nuna mini darajata a wajen ki ta kai ƙololuwa kenan, to babu laifi Allah Ya yi miki albarka.”
Ya ɗan tsagaita ya numfasa kafin ya ɗora da ce wa:
“Daman ba wata magana ba ce illa ɗazu da na je gai da Inna shi ne take mini wata magana, wai tana so Harira ta dawo gidan nan ku zauna tare domin ku haɗa kanku, hakan ne yafi cancanta a kan na barta can gidan, to ni kuma sai na ce wa Innan ta jira sai na nemi shawarar ki tukun, duk abin da kika ce da shi za’a yi amfani, saboda ba na son abin da zai zo yana ɗaga miki hankali muna zaman mu lafiya, kuma na san halin Harira ba kirki ne da ita ba kwata-kwata, tun kafin ki zama matata ma rikici ya haɗa ku kun ci uwar sabada a gefen hanya bare yanzu kun zama kishiyoyi, duk da Inna mahaifiyata ce ban isa na ƙetare umarninta ba, amma dai ina son na ji abin da za ki ce akan hakan tukun.”
Tunda ya fara magana ƙirjin Amina ke bugawa, tabbas ba ta son zama da Harira guri guda, saboda ita dai ba ta da haƙuri ko kaɗan, ba za ta jure iskancin Harira ba, kuma tana da saurin hannu, abu kaɗan take kai duka, ga Harira da tsokana, tabbas kuwa idan Harira ta ce za ta kawo mata iskancin da ta saba wataran za ta nakasa taa ko ma a ɗauki gawar ta, amma in dai ta sauya halinta to za su zauna lafiya, domin babu abin da ya fi zaman lafiya da kwanciyar hankali daɗi.
Duk da tunanin da ya gallabi zuciyar Amina ba ta bari Sunusi ya gane ba, kawai sai ta yi murmushi cikin siyasa da kissa ta fara magana.
“Haba Mijina! Yanzu har Innarmu ta yanke hukunci amma ka ce wai sai ka yi shawara da ni? Hakan ai bai dace ba, saboda darajar Inna a wajenka ta ninka tawa sau ba adadi, kuma ko babu komai ai Yaya Harira zuwa na yi na same ta, ba zan hana ta dawowa gidanta ba, ƙarewa ma ni zan kwashe kayana na mayar wancan ƙaramin ɗakin kawai domin ta dawo ɗakinta, idan ya so ragowar kayana sai a mayar da su gida har Allah ya hore maka ka gina naka gidan, fatan dai a yi mana addu’a Allah Ya ba mu zaman lafiya da juna.”
Da sauri Sunusi ya tare ta yana girgiza kai.
“Ba zai yiwu ki koma ƙaramin ɗaki ba Amina, sai dai ita ta zauna a can, daman ba wasu kayan kirki take da su ba illa kwaraɓaɓɓen gadonta da sari duk ya cinye shi, sai wata shegiyar tabarma da take shifiɗawa ma su zuwa kitso, ke za ki ci gaba da zama a nan ɗakin, ita kuma ta dawo wancan ƙaramin. Kuma Na gode da haɗin kan da kika ba ni Amina. tabbas! Yanzu na san na yi dace da mace ta gari mai faranta wa miji, Allah Ya yi miki albarka!”
Amina ta yi murmushi ta amsa da, “Ameen.”
Sunusi ya yi miƙa yana sakin hamma, Amina ta ɗaga kai ta kalle shi ta ce.
“Wai har ka fara jin bacci ne?”
Sunusi ya amsa.
“E wallahi bacci nake ji don a gajiye nake, yau kwangilar aikin wani bulo muka yi masu yawa duk jikina ciwo yake mini na gaji sosai.”
Amina ta miƙe da hanzari ta kamo hannunsa ta ce.
“Ai ban ga ta zama ba mijina yana tare da gajiya, mu je ɗaki na yi maka tausa ko gajiyar za ta warware.”
Sunusi ya miƙe yana murna da zumuɗi yau za a yi masa tausa, ya san ba ƙaramin daɗi zai ji ba yadda hannuwan Amina suke cike da nama, abin da Harira ba ta taɓa yi masa ba, duk da ya san ma ko ta yin ba daɗi zai ji ba sai dai ma ƙasusuwan hannunta su soke masa jiki.
Amina ta rungumo shi gefen jikinta, sai ga Sunusi ya yi ɗan tsurut da shi a hammatar Amina saboda ta ninka shi sau uku a ƙiba, suka shige ɗakinsu cike da son juna da farin-ciki.
Comments
Share
Pls
*TALLAH!*
Sabon littafina mai suna *Mayafin Sharri:* Labari ne da ya bambanta da salon labaran da kuka saba karantawa, saboda yana ɗauke da sarƙaƙiyar da warwarare ta sai ni da zan jagoranci jan ragamar labarin. Akwai tarin muhimman abubuwa da za ku ƙaru da su. Idan kun shirya ni ma na shirya!
Za ku karanta labarin MAYAFIN SHARRI ne akan kuɗi ƙalilan wanda bai wuce Naira ɗari uku kacal ba (300) daga farkon labarin har zuwa ƙarshe, ga wanda yake da buƙata zai iya tuntuɓata kan lambar wayata kamar haka:
08080049548
Ko kuma kai tsaye a tura kuɗin ta wannan account.
0557998068 Hassana Labaran GT bank. Sai a tura mini shaidar biyan ta lambar wayata, ga waɗanda ba su da account za su iya turo katin waya na 300, amma MTN.
Hassana Ɗanlarabawa.
08080049548.
Na gode.
[7/5, 10:39 PM] Hassana Ɗanlarabawa🌹: I just published “BABI NA BIYAR DA NA SHIDA” of my story “BAHAGON LAYI (SABON SALO)”. https://www.wattpad.com/1243818402?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Hassy3333&wp_originator=77XQkFwpBwcEosX9TjbQQNl625w3BIjdtf5VDI1EaZFJ%2FiP19VDGtInq1o%2BfjpBZ9kH0JDUYUmC1n0zzJko5IUXGGtNb9DM1f2REIebR7CQIw9qR8JQEQdsi3U4Bu%2FTX
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
BABI NA BIYAR DA NA SHIDA
©️Hassana Ɗanlarabawa.
EXQUISITE WRITERS FORUM
Washegarin ranar Habiba zaune a tsakar gidanta bayan fitar Babalalo wajen sana’ar shi ta askin. Wake ne a gabanta tana tsince mara kyau za ta surfa ta kai markaɗe, tun jiya Babalalo yake faɗa mata cewar yana sha’awar ya ci kulele (Alala), ita kam a dole za ta yi saboda ba ta son shi, in dai ta ci ɓata mata ciki yake yi tai ta tusa cikinta ya kumbura suntum! Wani zubin sai ta jiƙa ‘yar jar kanwa ta sha tukun take samun salama.
Sallamar da ta ji daga soro ya sa ta ɗaga kanta tana amsawa.
Wadda ta yi sallamar ta shigo tana taku ɗai ɗai a hankali, da sauri Habiba ta washe baki cike da murna tana faɗin.
“Lallai yau ashe ina da babbar baƙuwa, yaushe rabon ki da gidan nan Rauda?”
Rauda ta yamutsa fuska ta ja wata kujera ‘yar tsuguno da ke kusa da Habiba ta zauna, sannan ta sauke numfashi ta harari Habiban tana hura hanci ta ce.
“Hmmm! Ai Habiba ba ki da kirki ko kaɗan, gabaɗaya kin manta da ni a rayuwarki kina ta sabgoginki ma, wai shin ina gidana ina gidanki Habiba? Tsiranmu layi ɗaya ne fa. Amma kin ɗauke ƙafa daga gidana kwata-kwata kin daina nema na.”
Habiba ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye waken hannunta a ƙasa, ta dubi Rauda fuska cike da jimami ta ce.
“Hmmm! Ke dai bari kawai Rauda, ina cikin tsaka mai wuya da tashin hankali ne wallahi, tun bayan da abubuwa marasa daɗi suka faru da mu duk na yi sanyi, fita ma idan ba ta zama dole ba ba yin ta nake ba. Layin namu duk ya tarwatse! Oga Harira an samfa ta wata unguwa ta daban,Saratu tana gida Malam mai almajirai yana dila ta. Ƙasimu ya ɗauke Zahra’u sun koma wata unguwar ta daban, yanzu fa daga ni sai Shafa’atu a layin, ita ma ɗin ba ganin ta nake ba saboda takunkumin da Babalalo ya saka mini, wallahi Rauda ba ni da kwanciyar hankali duk a ƙuntace nake ji na kamar wadda ke cikin mari.”
Rauda ta yi murmushi tana sauke mayafinta daga kanta zuwa kafaɗarta, sannan ta dubi Habiba ta ce.
“Ai lokacin da abin nan ya faru na yi takaici Habiba, sosai na ji haushi fa, kuma ba haushin kowa na ji ba sai haushin ku, ban da ku mahaukata ne har ku zauna wani shirgegen ƙato ya dinga laftarku ku wajen huɗu, ba kwa wawuso ƙafafun arne ku nanashi da ƙasa? Ai sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi Habiba. Gaskiya kun ba ni mamaki, duk shaiɗancin ku amma kuka zauna wani ɗan iska ya dilliƙe ku a banza a wofi, ai wallahi da ina cikin ku lokacin da abin ya faru da kunga aiki da cikawa.”
Habiba ta sauke tagumi, ta dubi Rauda ta girgiza kai ta ce.
“Danƙari! Zance kawai kike Rauda, idan ba haka ba waye ya isa ya ja da hukuma? Ai Hukuma ta shallake tunanin kowa.”
Da sauri Rauda ta manna mata harara ta katse ta da ce wa.
“Za ki sa na danna wa hukumar ashar mai sifirin, ai ko shi ɗansandan ya yi muku hukunci ne ba bisa ƙa’idar aikinsa ba, ta yaya kuna matan aure ɗima-ɗima da ku amma ya keta muku haddin aure ya yi muku hawan ƙawara?”
Habiba ta ɗan yi dariya ta ce.
“Wane irin hawan ƙawara kuma Rauda? Sai ka ce waɗanda ya yi wa fyaɗe.”
“To mene ne bambanci da hakan?”
Rauda ta katse ta da tambaya, sannan ta ci gaba da ce wa.
“Ai bambancin kaɗan ne Habiba, mutumin da aka ce har tsalle ya dinga yi yana tumami a ruwan cikinku yana cafar nonuwan ƙirjinku.”
Habiba ta zaro idanu ta dafe ƙirji cike da tsoro, cikin rawar baki ta ce.
“In ji wane tsinannen maƙaryacin Rauda? A ina kika samo wannan labarin ƙanzon kuregen?”
Rauda ta taɓe baki ta ce.
“Yo zancen duniya yana ɓuya ne? Ni ma a gari na ji.”
Habiba ta girgiza kai ta ce.
“Kai mutane an yi tantagaryar munafukai kuma magulmata, wallahi hannuwansa ba su kai jikinmu ba, na san dai lokacin da ya gama kirɓarmu ya sa hannunsa yana ta tunkuɗo ƙeyarmu waje, ban da haka bai taɓa jikinmu ba wallahi.”
Rauda ta ɗan rage murya kaɗan ta ce da Habiba.
“Wai kuma da gaske mijin Amaryar ne ya kirawo ɗansandan aka tarfa ku cikin gidansa?”
Habiba ta ce.
“Hmmm! Shine wallahi Rauda, baƙin matsiyaci ba!” Ta faɗa fuska cike da jimami.
Rauda ta ce.
“Kuma har yanzu suna layin nan ba su tashi ba ko? Na ji an ce gini yake yi ba za su jima ba za su tashi.”
Habiba ta taɓe baki ta ce.
“Suna nan har yanzu baƙaƙen munafukai, ai kin san damunar bana ta yi gyara, ginin da ya fara ne ya rushe ya dawo baya, shi ne har yanzu ba su tashi ba.”
Rauda ta numfasa ta ce.
“Ya kamata kafin su bar layin nan ku ɗauki fansar abin da ya yi muku, wallahi idan ba ku rama ba kun yi asara duniya da lahira, ai rama cuta ga macuci ibada ne, ya kamata ki nemi Saratu da Harira da Shafa’atu ku haɗa kai ku ɗauki fansa, duk da dai babu Saratu a cikin ku lokacin da abin ya faru, amma na san za ta taya ku yin yaƙin, sai ta wakilci Zahra’u da ba ta nan kawai.”
Habiba ta yi kasaƙe cikin tunani, zuciyarta na kai kawo, ta ƙura wa Rauda ido ta ce.
“Ta yaya kike tunanin hakan za ta faru Rauda? Ni fa yanzu tsoron duniya nake ji domin ta koya mini hankali. Amma sai dai kuma kina zuwa da wannan shawarar na ji ta kwanta mini a zuciyata, yanzu me kike tunanin ya kamata a yi?”
Rauda ta yi murmushi ta matso jikin Habiba sosai ta kai bakinta kunnen Habiban ta yi mata raɗa. Habiba ta ɗaga kai ta kalli Rauda bayan ta gama jin maganar ta, suka kwashe da dariya suka ɗaga hannu suka tafa.
Rauda ta tsagaita da dariyar ta ta dubi Habiba ta ce.
“Ke na manta muna ta zance ban yi miki jaje ba. Ashe shagon Babalalo na aski ne ya ƙone, wai gobara da tsakar dare ko? Ni sai jiya Shafi’u yake faɗa mini, dalilin zuwana kenan ma dan na yi miki jaje!”
Habiba ta yi murmushi ta ce.
“Ai ba jaje ya kamata ki taya ni ba, murna ya kamata ki taya ni Rauda.”
Rauda ta zaro idanu ta ce.
“Murna kuma? Asara ta samu mijinki amma ki ce a taya ki murna Habiba? Ke kuwa wace irin zuciya ce da ke da kike murna da samuwar asara a kan mijinki?”
Habiba ta yi shewa tana buga cinya ta ce.
“Yo murna mana Rauda! Ai Babalalo mugunta ya so shirya mini ya yo mini kishiya, can dangin shi munafukai aka ba shi wata tsomalalliyar yarinya mai zubin ‘yan ruwa, in gaya mikj har fa ya tada ginin filinsa kaɗan ya rage ya kammala wannan ibtila’in ya same shi, gurin neman abincinsa ya ƙone ƙurmus” Yanzu tilas haka ya yi gwanjon gidan da ya fara ginawa ya sayar da shi ya samu kuɗin da ya gyara shagonsa, kinga ai yanzu tilas ya haƙura da auren da ya jajibo wa kansa ko? Tunda babu ‘yan matsabbai a hannunsa da zai yi hidimar auren da su, in kuma ba kan uwatar zai sayar ya yi hidimar auren ba.”
Rauda ta tuntsire da dariya kamar za ta kifa, sannan ta ce.
“Amma Habiba ba ki da mutunci wallahi, kuma fa da Babalalo zai sayar da kan babarsa da ya samu kuɗi wallahi, don na ga kan nata har rinjayar jikinta yake saboda girma.”
Habiba ma ta sheƙe da dariya ta ce.
“Yo ba ki ga shi ma Babalalon gadon ƙaton kai ya yi ba, kwanaki da muka zabga karo ya buga mini kansa wallahi na zaci dutsen Dala ne ya rufto mini, sai da na kwan uku ina jinyar kaina saboda ciwon kai, ai Allah Ya yi musu baiwar gingimemen kai, ni da atiringim.”
Suka kuma kwashewa da dariya suna tafawa. A daidai lokacin suka ji ana zabga sallama a soro. Habiba ta amsa da tambayar, “Wane ne?”
“Baƙuwa ce.”
Aka amsa daga soron.
“To shigo Baƙuwa.” In ji Rauda kenan.
Angayu ta shiga tana murmushi, duk suka bi ta da kallo ba su shaida ta ba, banda kallon fuskarta babu abin da suke yi. Ta sha kwalliya hoda fururu, ga jambaki baƙi ta lafta tamkar wata ‘yar daba, ɗaurin nan cokoko da shi a gaban goshi. Habiba ta matsa mata ta zauna kusa da ita kan tabarmar da take zaune, bayan sun gaisa ne Angayu ta dubi Habiba da murmushi ta ce.
“Na san ba ki shaida ni ba ko? Ni sunana Angayu, jiya muka tare a layin nan gidan da aka tashi, ni matar Malam Arabi ce, kuma na shigo mu gaisa ne mu saba da juna a matsayinmu na maƙota a yanzu.”
Ambatar sunan Malam Arabi da ta yi ya sa ƙirjin Habiba bugawa da ƙarfi, har abada ba za ta manta da wannan matsiyacin mutumin ba, duk lokacin da ta tuna shi sai ta hango azabar da ya gana wa bakinta da laɓɓanta!
Comments
Share
Vote
Pls
*TALLAH!*
Sabon littafina mai suna *Mayafin Sharri:* Labari ne da ya bambanta da salon labaran da kuka saba karantawa, saboda yana ɗauke da sarƙaƙiyar da warwarare ta sai ni da zan jagoranci jan ragamar labarin. Akwai tarin muhimman abubuwa da za ku ƙaru da su. Idan kun shirya ni ma na shirya!
Za ku karanta labarin MAYAFIN SHARRI ne akan kuɗi ƙalilan wanda bai wuce Naira ɗari uku kacal ba (300) daga farkon labarin har zuwa ƙarshe, ga wanda yake da buƙata zai iya tuntuɓata kan lambar wayata kamar haka:
08080049548
Ko kuma kai tsaye a tura kuɗin ta wannan account.
0557998068 Hassana Labaran GT bank. Sai a tura mini shaidar biyan ta lambar wayata, ga waɗanda ba su da account za su iya turo katin waya na 300, amma MTN.
Hassana Ɗanlarabawa.
08080049548.
Na gode.
[7/13, 10:03 AM] Hassana Ɗanlarabawa🌹: I just published “BABI NA BAKAWAI DA NA TAKWAS” of my story “BAHAGON LAYI (SABON SALO)”. https://www.wattpad.com/1246630771?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Hassy3333&wp_originator=w5w%2B1XqcwnJYjUL7XeBRkuMbAHp%2FyVOuxFpWvR5qejLDjIvrdXzxQ4nelOTyRnCJbS0Ulps60tYhWjwLTHBQKflhYoPH89NJjK%2FCLHU%2BkUmB2WgmrJW6YoOONoKyo9j0
*BAHAGON LAYI*
(SABON SALO)
BABI NA BAKWAI DA NA TAKWAS
©️Hassana Ɗanlarabawa.
EXQUISITE WRITERS FORUM
Habiba ta yanƙare haƙora, zuciyarta a jagule tana zuba yaƙen da ya fi kuka ciwo ta ce.
“Ayya! Ni kam dayake ban taɓa ganin ki ba shi ya sa ban shai da ki ba, nakan ji labarin ki dai a wurin yara, ke ce mai sayar da ƙosai da safe ko?”
Angayu ta gyaɗa kai da sauri.
“E wallahi kuwa, da ƙosai da awara duk ina toyawa da safe, haka nan ina sayar da gasarar kunu ma. Da fatan ku ma za ku zamo ɗaya daga cikin kontomana ku dinga saya?”
Habiba ta riƙe baki ta ce.
“Kontoma kuma? Mene ne kuma kontoma?”
Rauda da ba ta saka musu baki ba sai lokacin ta kwashe da dariya ta dubi Habiba ta ce.
“Ke ina jin dai Costomer za ta ce ko?”
Angayu ta buga cinya ta ƙyalƙyale da dariya da ƙarfi sannan ta ce.
“Ai kuwa kamar kin sani ƙawata. Kastoma nake nufi.”
Habiba kam dariya ta yi, a ranta tana faɗin.
‘Daga ganin wannan matar shuda ce ba ta da cikakken saiti.’
Angayu kam zama ta yi ta dinga zuba musu zance da so-ki-burutsu, idan ta yi wata maganar sai ta dubi Rauda ta ce.
“Haka ne ko ƙawata?”
Ita kam Rauda sai biye mata take yi suna shan shafta da kwasar dariya, domin ta fahimci Angayu irin matan nan ne ma su shegen surutun tsiya da bakinsu ba shi da linzami, duk maganar da za su furzar ba sa taunata suke fesar da ita.
Habiba dai takaici ne ya ishe ta. Angayu ta ƙi tashi ta tafi ga shi ba su gama hirar su ita da Rauda ba, karaɗin ta kawai ake ji tana buga zance, sai da ta kwashe kusan awa ɗaya sannan wani yaro ya yi sallama yana faɗin,
“Wai Angayu ta zo in ji Malam Arabi.”
Ai kuwa da hanzari ta miƙe ta shuri silifas ɗinta ta dubi Rauda tana faɗin.
“Bari na je na amsa kiran maigida, yanzu zan dawo ƙawata ai zan kuma tarar da ke ko?”
Habiba ta zaro idanu ta fakaici idanun Angayu ta lafta wa Rauda Harara, Rauda ta gane abin da Habiba take nufi shi ya sa ta yi murmushi ta ce.
“A’a ba lallai ki same ni ba ƙawata, wataran za mu sake haɗuwa ai, ni ma ba ni da nisa tsiran mu layi ɗaya ne, ni ina layin makarantar daren da mijinki yake koyarwa.”
Nan Angayu take cewa ai kuwa za ta kai wa Rauda ziyara, suka yi sallama ta fice da sauri suka bi ta da kallo, Rauda na dariya sai Habiba da take sakin tsaki tana hararar Rauda.
Rauda tana dariyar ta ce.
“Wai ni me na yi miki ne kika ishe ni da harara? Ni fa ba ni na sa mijinta ya jibge ki ya yi miki ganda ba balle ki ce.”
Habiba ta sake sakin tsaki ta tofar da yawu ta ce.
“Wai ke Rauda ba ki lura da wani curarren tasono da koriyar majina a hancin matar nan ba, anya kuwa kanta babu motsi? Babba da ita amma babu gyara da kintsi ta dinga fitowa haka ana kallon ta? Ni wallahi duk ta tayar mini da zuciya ma kamar na yi amai nake ji.”
“Kika sani ko mura take yi?” Rauda ta faɗa tana tuntsire wa da dariya.
Habiba ta ce.
“Kin manta uwar mura take yi, ko in ce miki firinji ne a kanta ƙarewar mura, to ko muran take yi ma ba za ta dinga gyara hancinta ba? Ni wannan da abinci nake ci ai da tuni ta haramta mini wallahi. Kuma wai a haka an ce mijinta yana kira ta zabari ƙafa ta tafi. Danƙari! Wannan miji zai yi kyakkyawan gani, ke daga ganin wannan matar nan kin san ladan noma ce, ƙila noma Malam Arabin yayi wa gyatuminta aka ba shi ladan ta daga ƙauye, wannan aba haka babu fasali!”
Rauda ta taɓe baki ta ce.
“Kada fa ki manta kin saba zama da ƙazamai Habiba, babbar aminiyarki Harira ma ai ƙazama ce ta bugawa a jarida wallahi. Sannan kuma ko ma ladan nomar ce ba shi ya ga zai iya ba? Yana son abarsa a haka.”
Habiba ta kama girgiza kai da hannu tana ce wa.
“Lala lala al mandudu kalas! Billahillazi huwar rahmanu duk ƙazantar Harira ba za ki ganta da tasono da mijina a hancinta ba, ita dai kawai ƙasanta ne ba ta gyarawa yake ɗoyi da wari, sai kuma ɗoyin hammata, kuma kwanakin baya kafin abubuwan nan su faru har turaren tsuguno da miski ta saya gun Zahra’u, kinga kuwa ai ta ɗauko hanyar gyara ko?”
Rauda za ta yi magana kenan wayarta ta soma ƙara, ta buɗe jakarta ta fito da ita tana dubawa. Ashe yayarta ce ke sanar da ita sun zo ba ta nan suna ƙofar gida. Nan Rauda ta ce su jira ta ga ta nan zuwa, domin ba ta yi nisa ba tana kusa.
Tana kashe wayar ta fara ƙoƙarin miƙewa tana gyara mayafin kanta, ta dubi Habiba ta ce.
“Habiba bari na wuce gida, yaya Abida ce suka zo ba na nan, ni ban ma san da zuwansu ba wallahi, ƙila yayen ɗanta Imamu ta kawo mini don jiya mun yi waya da Umman mu ta ce mini an yaye shi yau za a kawo mini shi, to ban ma yi zaton da uwar ɗan za a zo ba.”
Habiba ta sauke numfashi ta miƙe tsaye ita ma, sannan ta dubi Rauda ta ce.
“Wai ni kuwa Rauda ya kuka ƙare da wannan tsinannen mutumin mijin Abida? Haka kawai ya zamar da ita ƙaramar bazawara haihuwa ɗaya, amma dai kun maka ɗan iska a kotu ko?”
Rauda ta ce.
“Ai kam dai yana nan yana zabga nadamar abin da ya yi, kullum yana sintiri akan ta dawo gidansa ita kuma ta ƙi komawa. Yaya Abida ta sha wahalar wannan mutumin, kullum fa sai ya sha giyar shi yake zuwa ya tanana mata jikinta kamar wani ɗanyen nama. Hmmm! Bari na wuce Habiba hirarmu ba za ta ƙare ba, idan muka kuma haɗuwa ma ƙarasa kawai.”
Rauda ta faɗa tana yin gaba.
Habiba ta bi ta har soro tana yi mata rakiya, suka yi sallama Rauda ta wuce ita kuma ta juyo cikin gida ta fara ƙoƙarin wanke waken kulelen da za ta yi.
******
Amina ce zaune a tsakar gidan Shafa’atu, ta tasa Shafa’atun a gaba da ɗirmemen cikinta haihuwa ko yau ko gobe ta zabga tagumi. A hankali shafa ta gyara zamanta kan tabarmar da take kai ta yatsune fuska, saboda ciwon da take ji yana mintsinin ta kaɗan-kaɗan kamar mai naƙuda. Sai da ciwon ya lafa mata ta ɗaga kai ta dubi Amina ta ce.
“Wai ni me yake faruwa ne Amina? Duk na gan ki ba yadda na saba ganin ki ba, ko dai har kin fara shan gashi a hannun Sunusin ne? Hmmm! Wa ya gaya miki Borno gabas take? Kina murna wai ke kin yi Aure za ki sha soyayya da daɗi ko? An faɗa miki mazan yanzu mutunci ne da su? Tatattun ‘yan iska ne fa wallahi, a waje soyayya kamar za a cinye ki, da zarar kin shiga kin zama nama, kin ga duk ƙibar nan taki ko? Idan namiji ya minnira miki wani takaicin sai kin dawo kamar falwaya saboda rama.”
Amina ta sauke numfashi ta dubi Shafa’atu da cushasshiyar murya ta ce.
“Ni fa Anty Shafa babu abin da ya shiga tsakanina da mijina kike ta wannan subaɗaɗin, muna zamanmu lafiya wallahi, domin idan daɗi da soyayya suka yi mana yawa har goya ni yake yi.”
“Ya goya wa?”
Shafa ta ambata tana zabura har ƙugunta yana amsawa, sannan ta ci gaba da magana cikin zare idon mamaki.
“Wai Sunusin ne yake goya ki Amina? Sunusin da na sani mai baya kamar allon mayya ta ƙaƙa bayansa zai iya ɗaukan ki kina da girman buhun kwaki uku? Sake zance dai Amina!”
Amina ta ɓata rai ta ɗaure fuska katamau jin maganar Shafa’atu, nan da nan Shafa’atu ta shiga taitayin ta ganin yadda fuskar Amina ta ɗaure, kar ta je ta haye tsohon cikinta ta saka ta haihuwar da ba ta shirya ba.
Cikin ƙufula Amina ta ce.
“Ina ganin mutuncinki Anty Shafa, don haka kar ki sake cin mutuncin mijina gaskiya, na zo ne na faɗa miki damuwata saboda na ga kin fi kusa da ni a halin yanzu, idan kuma ba za ki saurare ni ba ne na ƙara gaba.”
Shafa’atu ta yi saurin tare ta da ce wa.
“Haba-haba ƙanwata, ki yi haƙuri wallahi zan saurare ki, mene ne yake faruwa da ya sanya ki a damuwa?”
Amina ta yi ajiyar zuciya, ta ƙura wa Shafa’atu idanu ta ce.
“Wani tashin hankali ne yake neman tunkaro ni ina zaune lafiya. Jiya Darling Sunusi yake faɗa mini wai Harira za ta dawo gidan da nake mu ci gaba da zama tare, to kin dai san halin Harira, kin ma fi ni sani tunda tare na ganku. Kuma ni ma kin san ni kamar zawayi nake ba ni da haƙuri, shi ne na zo ki ba ni shawarar yadda zan zauna da ita, don gaskiya ba zan ɗauki rainin wayonta ba, ban auri mijinta ba ma ban ɗauka ba balle yanzu? Idan ta ce za ta kawo mini iskanci za mu ci uwar sabada ne ni da ita!”
Wani irin zaro ido Shafa’atu ta yi, cikinta ya fara ƙululululu! A ranta take faɗin.
‘Harira za ta dawo? Tabbas za a sha dirama kenan.’
Musamman da jiya Kamilu yake ba ta labarin wai Malam Arabi ma ya dawo layinsu gidan da su Zahra’u suka tashi, Tabbas! BAHAGON LAYI zai ƙara shiga wata chakwakiyar kenan!
Comment
Share
Vote
Pls
*TALLAH!*
Sabon littafina mai suna *Mayafin Sharri:* Labari ne da ya bambanta da salon labaran da kuka saba karantawa, saboda yana ɗauke da sarƙaƙiyar da warwarare ta sai ni da zan jagoranci jan ragamar labarin. Akwai tarin muhimman abubuwa da za ku ƙaru da su. Idan kun shirya ni ma na shirya!
Za ku karanta labarin MAYAFIN SHARRI ne akan kuɗi ƙalilan wanda bai wuce Naira ɗari uku kacal ba (300) daga farkon labarin har zuwa ƙarshe, ga wanda yake da buƙata zai iya tuntuɓata kan lambar wayata kamar haka:
08080049548
Ko kuma kai tsaye a tura kuɗin ta wannan account.
0557998068 Hassana Labaran GT bank. Sai a tura mini shaidar biyan ta lambar wayata, ga waɗanda ba su da account za su iya turo katin waya na 300, amma MTN.

Leave a Comment